← Book details Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 20

Sashe 13

Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zarah da jin tambayar ta Fatima ta yi wani murmushi na kasaita kafin ta ce.
"Kin manta wace ni , dactor Zarah babu abin damuwa in sha Allah."

Fatima ta kauda kai da takaicin yadda ta samu amsar a gun Zarah.

Bayan sun dawo gida misalin karfe 2 daidai ne Hajjiya Samira ta ce .
Su barta a falo domin bata jin bacci

Haka suka so ta kwanta ta yi bacci amma ta ki

Har asuba ta yi tayi sallah, ta zauna a falon tare da carbi

A lokacin Fatima ta shigo, yayin dasu Kamal suka dawo daga masallaci.

Hajjiya ta kalli Fatima tana cewa.
"Fatima tafiyata fa na nan yau zan koma saudiya."

Kafin Fatima ta ce komai ma .

Kamal ya fara cewa .
"Haba mommy ta ya zamu barki ki tafi saudiya ko baki da gata ai sai haka , gaskiya babu inda zaki je."

Murmushi hajjiya ta yi tana cewa.
"Duk na tada muku da hankula amma ina baku hakuri ."

Lokacin zarah ta shigo tana ajiyar zuciya da cewa .
"Haba mommy duk muna kaunar ki , babu wani abu a ciki , Allah muke fatan ya baki lafiya kawai ."

Cikin jin dadin yadda Fatima ta ji maganar Zarah ta kalleta tana fadin .
"Na gode Zarah, kin yi mini komai bazan manta da hakan ba ."

Wata harara Zarah ta dokawa Fatima tana cewa.

https://chat.whatsapp.com/BxsOc6eKfrTAE5lgAlJQHQ

FATIMA DA ZARAH🎀
Na
Autar Marubuta

_______________________________________

Editing❌

*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><
https://www.facebook.com/profile.php?id=61550626300848

Page 30 & 31

"An ce miki ke ce kawai kike son mommy ne ."

Hajjiya ta yi murmushi hira sukai ta yi har gari ya waye .

Zarah ta kawo abinci aka karya sannan ta danko magunguna ta bata .

Fatima ta ce .
"Gaskiya kishi nake duk kinbi kin rike mini mommy komai ke kike mata ."

Zarah ta yi dariya tana cewa.
"Wallahi Fatima ina kaunar mommy a cikin jini na ."

Kamal ya yi murmushi

Nasir ne ya tashi tsaye yana cewa.
"Bari na shirya na tafi makaranta, mommy Allah ya kara miki lafiya ."

Ta yi murmushi ta ce.
"Amin ."

Ya wuce daki domin shiryawa .

Kamal shima ya tashi tsaye yana cewa.
"Mommy bari naje gidan Alajin mu na dawo ."

Hajjiya Samira ta ce.
"To Allah ya tsare dan Allah ka gash she mini da Hajjiya Amina sosai d sosai ."

Kamal ya ce.
"In sha Allah zata ji , domin ma ba dadewa zan ba yanzu zan dawo in sha Allah."

Sannan ya kalli Fatima yana cewa.
"Ai da kin shirya na aje ki , tunda Zarah karfe 9 zata fita har ma kin dawo ki zauna da mommy."

Fatima ta ce.
"A'a kaje kawai Allah ya tsare , sukai sallama ya tafi."

Zarah ta kalli Fatima tana cewa.
"Yau kina da aiki ne daban ."?

Fatima ta ce .
" A'a zanje bada basu takardu ne kawai asa mini hannu ."

"Okay to kije ki shirya , zan shirya na jira ki , idan kin dawo na tafi asubitin ."

Cewar Zarah

Fatima ta ce .
"To."

Tana tashi tsaye Hajjiya Binta ta shigo da sallama.

Duk ran Fatima kawai ya baci

Zarah ce ta amsa sallamar, yayin da Hajjiya Binta tana hango Hajjiya Samira ta taho da gudu tafa fadin .

"Oyoyo oyoyo Hajjiya ta ."

Ta rungume Hajjiya Samira dake zaune cikin karfin hali.

Murmushi ta sakar mata suka fara gaisawa , Fatima ta tabe baki ta nufi dakinta .

Zarah ta gaida Hajjiya Binta yayin data fara kwashe kayan abincin da suka ci tana kaiwa wajen da ya dace .

A lokacin Fatima ta fito suka gaisa da Hajjiya Binta, har wani soyyaya take nuna mata wai dan ta ga a gaban mahaifiyar ta ne .

Fatima kuwa abin duk kona mata rai yayi ta kalli Hajjiya Samira tana cewa.
"Mommy bari naje yanzu zan dawo in sha Allah."

Ta ce ."To Fatima Allah ya tsare ."

Fatima ta fita .

Nasir yana shirin tafiya makaranta ne wayar shi ta fara ringin yana dubawa ya yi murmushi ya daga tare da karawa a kunne .
"Hello dan Alaji ka fito ke nan , nima ina hanya ."

Daga can bangaren Nasir yaji abokin nashi yana cewa.
"Kai gaye sha zamanka wallahi professor ba zai zo ba nima ka ganni ina gida ."

Nasir ya kwashe da dariya yana cewa.
"Alhamdulillah naji dadi wallahi ka ce kawai mu huta ."

Daga can ya ba shi amsa da cewa .
"Eh wallahi sai mun hadu kawai ."

Nasir ya kashe wayar yana murmushi yana cewa.
"Ahhhhh yau ba lecture ai kawai bacci zan ."

Ya hau gado tare da wayarshi .

Anan falo kuwa Hajjiya Binta tana ta yiwa Hajjiya Samira hira ba tare da tasan ma bata da lafiya ba .

Lokacin Zarah ta shigo tana cewa.
"Mommy bari na shiga ciki na shirya kafin fatima ta dawo ko kina bukatar wani abin ne ."?

Hajjiya Samira ta kalli Zarah tana cewa.
" Bana bukatar komai 'yata Allah yayi miki albarka. "

Zarah ta yi murmushi ta nufi sashinta

Shigowar kira na biyar ke nan wayar Nasir, Abba Alaji ya dame shi da kira

Nasir ya girgiza kai yana cewa.
"Zan koya maka hankali Abba."

Kira na 6 yana shigowa Nasir ya daga ya kara a kunne .
"Hello Nasir wallahi yanzu zan shigo gidanku yunwa nake ji Allah."

Wani 'bacin rai ne ya daki zuciyar Nasir yayi ajiyar zuciya yana cewa.
"Abba kai wanne irin bakin maye ne mara ilmi mara zuciya, jahili kawai , to wallahi na rantse maka idan ka taka kafa kazo , zan maka rashin mutuncin da tunda ubanka ya haife ka ba a taba maka ba ."

Yana gama maganar ya kashe wayar ya kwanta cikin bacin rai

Suna cikin hira Nasir ya turo kofa
Ciki da mamaki hajjiya Binta ta kalleshi tana cewa.
"Kai kuma lafiya Abba wajen wa ka zo a wannan gidan."

Abba Alaji ya sosa keya yana cewa.
"Wajen Nasir mana ai a bokina ne ."

Hajjiya Samira da hankalinta bai kwanta dashi ba ta kalleshi tana cewa.
"To ai Nasir yana makaranta."

Abba Alaji ya dubi lungun-lungun gidan sannan ya lura da inda dakin Nasir yake sakamakon lokacin da ya shigo dashi da dare
"Bari in shiga na duba ." Ya sha ta gabansu
Ya nufi dakin Nasir

Hajjiya Binta ta yi murmushi tana cewa.
"To idan ya shiga yaga baya nan ya fito ai ."

Hajjiya Samira ta hade rai tana cewa.
"Wane kuma wannan."

"Yanzu baki gane shi ba , yaron Alaji Sani ne fa yayana ."

Hajjiya Samira ta yi ajiyar zuciya

Cikin wayantar da zancen Hajjiya Binta ta ce .
"To Hajjiya d'an ko mini turare na kinsan kamshi ba a wasa dashi ."

Hajjiya Samira ta yi murmushi na yake tana cewa.
"Tom bari na shiga ."
Ta nufi dakin Fatima inda kayanta suke

Doctor zarah ta shirya , rigarta ta likitoci kawai zata sa ta fito .

"Uwarka ta yi asarar haihuwa Abba, ta haifo maye kuma annoba mara jin magani , wallahi ina tabbatar maka da iyayenka sun san kai zasu haifa dasun kasheka tun kana ciki .

Na ce ka rabu dani ka bar rayuwata haka , amma kaki shege matsiyaci kawai."

Nasir yayi maganar cikin matukar hassala

Maganar ta batawa Abba Alaji zuciya hakan yasa ya kalleshi yana cewa.
"Ni kake fadawa wannan Nasir."?

Nasir cikin wata sabuwar fusata ya ce .
" Eh din ai takaita ma na yi domin kafi haka , idan kuma ka yi zuciya ka barni har abada. "

Cikin bacin rai da bakin ciki da takaici Abba ya juya ya fita cikin mahaukacin yanayi .

..............

Zarah ce da Hajjiya Binta kan Hajjiya Samira dake kwance a kasa

Cikin tashin hankali zarah ta fara kiran .
"Mommy tashi mommy mene ya same ki."

Yadda suka ga yanayin nata yasa su matukar tashin hankali

Hajjiya Binta ta kwallah kara tana kallon Zarah da cewa .
"Shi ke nan kin kasheta , kin kasheta hankalin ki ya kwanta ."

Ta rushe da kuka
Zarah ta kalli kwalbar turaren da Hajjiya Samira ta dauko daga gefe tana sake fashewa da kuka .

Lokacin Kamal ya shigo tare da Hajjiya Amina wato mahaifiyarshi
Zarah wani
Tashin hankali taji ya ziyartar mata zuciya dajin abin da Hajjiya Binta take fada

Da gudu su Kamal suka yo kanta yana tambayar .
"Mene ya sameta mommy mene yake faruwa Zarah."

"Ta kasheta ta kasheta ."
Hajjiya Binta ta cigaba da fada tana kuka

Lokacin Fatima ta turo kofa daidai da sanda take maganar

Zarah mutuwar tsaye ta yi ta kasa cewa komai kawai hawaye ne suke zubo mata .

Da gudu Fatima ta karaso tana jefar da takardun hannunta
"Innalillahi mene ya faru da mommy mene yake faruwa."

Ta zube a kasa gaban mahaifiyar tata tana kiran sunanta tana jijjigata

Zarah ta sake fashewa da kuka

Fatima cikin kuka ta kalli Zarah tana cewa .
"Mene ya sameta dan Allah Zarah."

Kafin Zarah ta bude baki ta yi magna Hajjiya Binta ta sake fadin .
"Ta kasheta hankalin ta ya kwanta innalillahi wa inna'ilaihir raji'un ."

Fatima ta kalli Zarah cikin wani mummunan yanayi da matukar mamaki , Zarah ta kalli Kamal ta sake fashewa da kuka

Sannan ta ce .
"Dan Allah kamal mu kaita asubiti bai kamata mu zauna ba ."

Ta fadi kasa tana cigaba da kuka

Hakan kuwa akai duk suka rankaya asubitin cikin mummunan tashin hankali.

Nasir kuwa yana daga daki yake jin komai, saidai tashin hankali ya hanashi fitowa , saida suka tafi asubitin ya hau mota yabi bayansu .

Koda suka isa cikin asubiti Zarah bata shiga inda aka aje Hajjiya Samira ba

Dactor Ahmad ne cikin kwarewa ya shiga aikin shi

Suna cikin tsananin jiran fitowarshi ne , dactor ya fito

"Allan da ya baku shi ne ya amsa ina baku hakuri dactor Zarah."

Ya karasa maganar sanda Nasir ya shigo , tare kuma da kallon zarah.

Autar Marubuta

07040805269
WhatsApp only.
Chapter 13 · 0% Book details