← Book details Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 20

Sashe 1

Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read


FATIMA DA ZARAH🎀

Na

Autar marubuta

Wannan kagaggen labari ne dani Autar marubuta na zauna na kirkire shi .Ban kuwa yi dan kowa da komai ba, idan ya yi kama da tsarin rayuwar wasu ma auratannn, tom ni dai kawai arashi ne mai kashe auren wawa.🎍

Editing d'in ma a wannan karan bai samu ba🙏

________________________________________

*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><

Page 1 _5

SAUDIYA

Dawowarsu ke nan daga asubiti , Najib da Ahmad tare da mahaifiyar su da bata da lafiya, eh tabbas wannan iyalin kana iya ganin tsantsar soyyayar mahaifiyar su , bama dai wannan ba tafkeken gidan da suka shiga ga wasu motoci a zube a harabar gidan .

Gida Nigeriya ✔

"A duniya bani da burin da ya wuce na mallaki Zarah,tabbas rayuwata dan ke aka yi ta , wayyo Zarah , Zarah ina kaunar ki sama da dukkan ma'anar kalma ina miki san da babu misali , Allah ya bani ke matsayin matata habibty."

Wani saurayi ne had'ad'ad'd'e mai kimanin shekaru 29 yake zayyano wannan kalamai yana daga kwance a kan gadonshi .

Ba tare da ya sani ba mahaifiyarshi tana ta saurararshi , da abin ya ishe ta , ta fara kiran sunanshi
"Kamal , Kamal."

Sam bai ji kiran mahaifiyar tashi ba ya zurfafa cikin matukar kewar Zarah , sai da mahaifiyarshi ta sa hannu ta dungure 'kafar shi da ya jinginar jikin bango sannan ya dawo hayyacinsa .

Murmushi ya yi kafin ya tashi zaune yana sosa 'keya

"Mommy ina kwana ." Kamal ya fad'a yana sunkuyar da kai kasa

"Bazan amsa ba mara kunya , tun yaushe na shigo d'akin , kana can kana zantukan hauka a kan wannnan yariyar ." Mommy ta yi maganar kamar mai shirin kaiwa d'an nata duka

a Kamal mi'kewa tsaye yana ri'ke hannunta yana cewa, "Yi hakuri dan Allah mommy, wallahi bansan kin shigo ba haba masoyiyata uwata ta kaina."

Mommy ta yarfe hannunshi daga hannunta cikin muryar saukakawa ta ce, "Ba shakka tun da ka mai dani kakarka , sai ka fito break fast."

Tana gama maganar ta fita tana murmushi tare da godewa Allah da wannan yaro da ya bata .

Shima bayanta yabi kafin ta 'bace masa suna isa teburin cin abinci Hajjiya ta zauna a kujerarta ta kusa da Alaji Mansur

Kamal ma ya ja kujera dake tsakanin 'kannenshi biyu Nasir da Laila sannan ya zauna .

Alaji mansur ne ya fara tashi daga karin kumallon bisa godiya ga Allah ya shiga ciki

a wannan lokacin ne Nasir ya yi maza ya koma kujerar Alaji.

Wani kallo mommy ta jefa masa tare da cewa ,"Me ya sa baka da kunya ne Nasir , ka raina kowa mene haka ne ."

Sum-sum ya tashi ya koma inda ya bari yana cewa, "A yi hakuri mommy."

Kamal dariya ya yi sannan ya dubi fuskar Nasir da duk babu annuri yana cewa, "Karka damu na gidana idan na yi aure d'akinka guda wallahi a gidana."

Mommy ce ta yi dariya tana cewa, "Eh tabbas kuwa ya kashe auren ."

Dariya laila ta kwashe da ita harda tuntsurawa, fuskar Nasir kuwa sam yaki sakinta

Bayan Laila ta shanye dariyarta da 'kerrr ta dubi kamal tana cewa, "Yawwa Yaya Kamal ni fa ban ta'ba ganin Aunty Zarah ba."

Kamal da jin maganar Laila ya wani yi mutuwar farin ciki a zaune yana murmusawa
Ba tare da ya cewa Laila komai ba ya fara dunmiyawa tunanin Zarah.

Iyalan gidan Alaji Mansur ke nan tsohon soja ,babban mutum mai magana guda .

Yana zaune da matarshi Hajjiya Amina wato mahaifiyar Kamal , tare da d'ansu guda daya tilo shi ne Kamal, sai kuma Laila wacce ta taso a gidan tun tana karama sakamakon rasuwar mahaifiyarta 'kanwar Alaji Mansur.

Sai Nasir wanda Hajjiya ce ta d'anko shi daga kauye tun yana sheakara 18 a wajen yayanta da suke uba daya.Ya dawo nan suna zama tare.

Anan cikin wani katafaren gida kuwa yasha ban-ban da wancen suma dai suna zaune kan teburin cin abinci irin nasu na gayu suna karin kumallo .

Da gani babu tambaya zaka gane wane mai gayya mai aiki mai wannan gida a cikinsu , sanye yake da jallabiya fara babu far'a a fuskarshi yana shan shayi
Duk da kuwa tarin kayan abincin dake kan teburin bai d'auki komai ba ,
Daga karshe yaja dogon tsaki ya tashi ya bar wajen

Wasu manyan mata ne fara da ruwan tarwad'a da suma suke zaune suka kalli juna ,
Yayin da kowacce taci gaba da cin abincinta.

Gidan Alaji Mustapha ke nan , shima tsohon soja ne ,sannan babban aboki ga Alaji Mansur, sai dai shi Alaji Mustapha iyalinshi ba kamar na Alaji Mansur ba ne , kusan kullum 'bacin rai yake 'kunsa a wajen matansa .

'Ya'yanshi guda 6 ne wanda duk suna raye sun girma, guda uku suna nan Nigeria a kusa dashi , Khalid da Habib wanda su ne mazan , sannan sai Fatima wacce ita ce kad'ai mace da Allah ya ba shi .

Hajjiya Binta da Hajjiya Rukayya, a halin yanzu su ne matan Alaji Mustapha, wanda kowacce tana da yaro guda daya

Sai kuma uwar gidanshi matarshi ta farko kafin su rabu , Hajjiya Samira wacce ita ce mahaifiyar Fatima, sannan kafin Fatima tana da wasu yaran maxa su uku wanda kusan su ne manyan 'ya'yan Alaji Mustapha

Amma a halin yanzu basa Nigeria, suna can Saudiya wajen mahaifiyar su
ita kuma fatima tana gaban mahaifinta

Duk da cewa Hajjiya Samira mahaifiyar Fatima bata gidan Alaji bata kuma kasar , hakan bai hana su Hajjiya binta cigaba da kishi da ita ba ,
Sakamakon yadda ta fisu 'ya'ya da kuma yadda Alaji yake yawan yabon ta har yau musamman idan yaga d'iyarta Fatima.

Zan so kiran dukkan 'ya'yan Alaji Mustapha yanzu domin gabatar mana da kansu , sai dai duba ga tafiyarmu da nisa da kuma tsawon jiran da zami na saudiya su zo yasa na fara cewa daku

Faruk shi ne d'an Alaji Mustapha na farko wanda yanzu haka soja ne a saudiya , sai kuma Ahmad wanda yake kasuwanci shima a can kusa da mahaifiyar su, sai Najib d'an jarida
Sannan autar Hajjiya Samira Fatima wacce take nan Nigeria tana aikin lauya 🎓

Sannan Habib dan Hajjiya binta , soja ne , tare da Khalid dan Hajjiya Rukayya duk sojoji ne .
Wannan su ne iyalan Alaji Mustapha.

Gida ne na alfarma wanda ya gaji da had'uwa tabasss an zuba daula a wannan gida , domin gida ne da ake yawan misali da shi
wannan gidan bana kowa bane face gidan Alaji Sale mashahurin mai kudi da yake da hanyoyin samu bila a dadin masha Allah

Daga cikin falon gidan wata kyakykyawar halitta ce zubin karshen hutu take kwance kan d'aya daga kujerun alfarmar falon na farko

Ga dukkan alamu dai chatin take , sai dai idanunta na kaiwa kan agogo tai sauri ta tashi ta shige wanka

Babu jimawa ta fito tana zun'buro baki gaba , musamman ma ganin mahaifiyarta Hajjiya Sa'adatu ta shigo

kamar kuwa yadda tai tsammanin jin mahaifiyartata zata mata magana haka taji .

"To ke kuma lafiya Zarah kike fushi."?

Hajjiya Sa'adatu ta tambaya

" Mommy na gaji bana son suna asubiti da rana wallahi. " Zarah tai maganar kamar za tai kuka

Kawai dariya Hajjiya ta yi mata kafin ta ce , "Wallahi wannan mitar ce bana so , shi ya sa kawai nake jiran ranar da zaki tafi gidan Kamal na huta ."

Da jin haka Zarah taji wani shauki mai hade da kunya ya ziyarce ta , hakan ya sa ta nemi kofar dakinta da gudu ta shige

Dariya Hajjiya Sa'a ta yi ta samu guri ta zauna , zaman ta ke nan sai ga Alaji Sale ya shigo , yayin da wasu samari kyawawa masu kama da Zarah suka biyo bayanshi

Alaji Sale salisu duk wata hanyar samun kudi ba ya bari , haka ya d'ora yaranshi a kai , hakan ya sa arziki kullum gudana yake

Babban d'anshi Mahmud, wanda ya yi nisa a kasuwanci , sai Zarah da tai karatu a kasar misira , wanda yanzu haka likitan zuciya ce , sannan d'aya daga cikin marubuta masu matukar hazaka da masoya

Sai ’karaminsu Umar shima dai ....

Anan cikin gidan Alaji Mustapha, farin ciki ya ishe shi sakamakon ziyarar Alaji Mansur da ya kawo masa

Bayan sun ci abinci sun sha sannan suka fara hira suna ta'bo 'bangarori da dama

Ana cikin hirar ne Alaji Mansur ya ce ,"Ni kam ya maganar matarka Samira ne ."

Dariya mai cike da ya'ke Alaji Mustapha ya yi kafin ya ce ,"Ka ji ka Alaji da wani zance , ka ce dai tsohuwar matata mutuniyar kirki, ai wallahi na yi rashin mace ta gari kawai sai dai Allah ya maida alheri ,ka ga shekaru nawa da rabuwar mu amma tana zuciya ta."

Cikin tausayi Alaji Mansur ya kalleshi ya ce ,"To Alaji Mustapha ni bama wannan ba , ya Fatima take akwai maganar da nake son yi a kanta ."

Numfashi Alaji Mustapha ya aje kana ya ce ,"Fatima ai wallahi tana shan wahala , yarinyar nan ta girma ,tarbiya da mutunci ba a magana , amma duk da haka su Hajjiya Binta basu da abin wulakantawa kamar ita."

Alaji Mansur ya ce ,"Shi ya sa na zo maka da wani zance Alaji domin kasan Fatima 'yata ce."

Murmushi Alaji Mustapha ya yi yana cewa ,"Fad'a mini kai tsaye Alaji Mansur. "

Haka Alaji Mansur ya sanar da Alaji Mustapha abin dake ranshi , nan take farin ciki da sabuwar kaunar juna ta rufe su , musamman Alaji Mustapha abin dai ba a cewa komai

Lokacin da Alaji Mansur ya tashi tafiya , har bakin get wajen mota Alaji Mustapha ya rakoshi sa'ilin da yake cewa ,"A gaskiya na jima ban ji farin ciki irin wannan ba , ka gama mini komai Alaji, wannan shi ne abota , Allah ya bar zumunci."
Chapter 1 · 0% Book details