← Book details Dan Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 7 OF 20

Babi na Sha Bakwai 1⃣7⃣

Dan Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 14 min read

(K'AMSHI☺)

Cikin wata iriyar murya yace "K'AMSHI" Dariya tayi tace "Zaid dina ni kadai" hakan da ta fada ya sa shi tunawa da Labiba, da sauri ya waiga ya ga bata wurin da ya barta dazun, ya sake juyowa ga Yesmin yace "yaushe kika dawo?".
A tak'aice tace "jiya"
"Ba ki gaya min zaki zo ba?"y
"Ba zai zama zuwan bazata ba in na gaya maka"
Dan guntun murmushi yayi yace "K'amshi".
Itama murmushin tayi tace "Zaidun k'amshi".

Daga gefe ya ga travelling bag dinta yace "oh baki ma shiga cikin gidan ba?" tace "eh zuwana fa kenan" yace "okay kije, zan zo cikin Gidan, barin yi Sallah"
Gaba tayi tace "alright sai ka shigo" tafiya tayi ta bar wurin da k'amshinta kamar ko da yaushe, ciki ya shige shi kuma don yin sallah.

Daga Window Labiba ke lek'ensu, jikinta rawa yakeyi sosai, ranta ya sosu, kallon fuskokinsu ya tabbatar mata da cewa akwai tsantsar soyayya a tare dasu, "uhmm wannan itace Mai Aji? Gashi nan suna ta zabga k'walisa, dama ya na da kamar wannan mai zai yi da ita Mara Aji? Uhm su masu Aji".
Da k'yar ta bar wurin ta kabbara sallahr La'asar, zuciyarta na mata zogi.

Da sallama ta shiga Parlon duk suka hau shewa , Annah ta rugo ta rungumota "oyoyo Aunty Yesmin" itama ta rungumeta tayi "oyoyo Annahn Aunty Shafa" sukayi daria baki daya, "Dr Yasmin" Hudu ya fada cike da k'auna da Bege.
Murmushi tayi tace "Uncle Hudu muna lafia?" Ba ta jira amsar sa ba ta zauna kusa da Aunt Shafa tace "Aunty Ina wuni?" Shafa ta amsa ta na tambayarta mutanen Gidan.
Sunyi Minti 10 suna magana kafin Zaid ya shigo da Akwatin Yesmin.

Cewa yayi "K'amshi, ga Box dinki" da sauri ta tashi yan parlon suka bita da muguwar harara, tace "har kayi Sallahn?" yace "Yup" tace "sai ina?" yace "zan shiga na ga Dalo sai na dan fita".
Gaba tayi don zuwa dakin Dalo tana fadin "wai har yanzu Dalo baki bar zaman daki ba? Haba sai kace wata Mata mai Takaba?" Zaid ya rufa mata baya yana daria, a tare suka shiga dakin, aikam Dalo taji dadin ganin Aunty Yesmin dinta, Zaid yace "nidai ma fita, sai bayan Maghrib kuma" byebye k'amshi tace, dalo ta gyada mai Kai.

"Wai ke ba nace ki dinga fita parlo ki na zama ba? taso muje" da sauri Dalo tace "donAllah ki barni a wurin zamana, please" Yesmin tace "Waye yace daki shine wurin Zamanki? My friend taso muje Parlo inda mutane suke".

"Dalo tace banyi sallah ba" Yesmin tayi hanyar k'ofa tace "kiyi sallah ina jiranki kizo, in baki zo ba, ni zan zo". Dalo tace "Yes Ma".

Tunda ta fito daga dakin Dalo "Aunty Shafa take tarbanta da harara har sai da Yesmin ta zauna kusa da ita taja zabga murmushi.
Aunty Shafa'atu tace "Kinga Abunda ke hada ni dake kenan ko Yesmin? Na gaya miki ba ruwanki da yan iskan chan, wurina kike zuwa, ba wurinsu ba, ni kika sani ba su ba, haka wanchan zuwan da kikayi sai da mu kayi fada da Mamanki ta kanki, indai abunda zaki dinga ja min kenan ki bar zuwan man Gida gaskia".

Nan da nan Yesmin ta chanza fuska tace "Kinga Aunty Shafa ba sai kin min gorin Gida ba, yanzu zan bar miki Gida, kuma ki sani wallahi sai nace Mommy ta zame hannunta a cikin Lamarinki kaf".
Da sauri tace "haba Yesmin, ni ba gorin Gida na miki ba, baki fahimceni ba, kiyi hak'uri, kin san you are always welcome, kawai dai banson ganinki da Dalo daDan Makaho".

Harara ta zabga mata ta ja akwatinta ta yi dakin da take sauka in tazo. Hudu kam bin bayanta yayi cike da k'auna.
Shafa ko ranta a bace ta zaro waya don Kiran "Er Rabi".

YASMIN wacce aka fi sani da k'amshi a Jami'ar Oxford University dake England.
K'amshi kamar yanda 'yan Nigeria masu karatu a England suke ce mata, k'amshi kyakyawa ce doguwa sosai mai dan diri, kamar sunanta K'amshi 'yar k'amshi ce, in ta zauna a wuri ta tashi shikenan gurin zai dauka da k'amshinta, ko handshake tayi da friends dinta to sai fa ta bar tambarin k'amshinta a hannun mutun K'amshi yar gayu ce sosai.
Akwai wani K'ungiya na 'yan Nigeria masu karatu a UK (UKKSA) United Kingdom Kastina Students Association, ne ta ke haduwa da Zaid Ali Zaki wanda shine Vice president of the Association, k'amshi ce Treasurer.

Suna gaisawa don baida shariya ko kyaliya, sosai Guy din ke birgeta, daga gaisuwa ba abunda ke hadasu amma ta na so alak'arsu ta wuce gaisuwa.
A hankali a hankali haduwarsu ta fara yawa don akwai wani gaggarumin taron da zasuyi na
(UKKSA) wanda Taron zai hada da Shugaban k'asn Nigeria, Gwamnan Katsina, Director na Scholarshi board na Katsina, shiyasa suke haduwa sosai a kwanankin nan, aikin da suke yi ne ya sa suke yawan haduwa tare.

Kowa na son shishige ma K'amshi amma ita yar shan k'amshi ce, sai wanda ta za6a take magana, amma sai gashi tana son shige ma Zaid amma bai wani bata fuska ba bayan gaisuwa, a hankali taji ta na matuk'ar son shi, sosai take so ya furta mata kalmar so don ba za ta iya gaya mishi tana sonshi ba.

Ajinta take ja, don abun kunya ne ace kamarta K'amshi yanda tayi suna a universities din England musamman Cambridge da Oxford ace ta bada kanta wurin Namiji ai yawa ne, shiyasa take kama kanta, bata bari son Zaid ya fito fili ba balle a gane, Makarantansu ba daya ba balle ta dinga ganinshi har ta kasa hakura wata rana ta tareshi ta furta mai So, sauk'inta kenan ba su faye haduwa ba sai sunzo Meeting suke haduwa, bayan anyi Taron kuma bata sake ganinshi ba.
Wannan Kenan.


SHEKARA BIYU DA SUKA SHUDE

Hajiya Shafa'atu ta kalli Hajia Er Rabi ranta na k'una tace "wallahi ba zai yiwu ba, shekaru 15 nayi a banza?" Er Rabi ta katseta da cewa "Aa fa Shafa'a, bukatar da kika rok'a an biyaki fa, kince kina so ki dawo Dakinki kuma ki mallake mijinki, ba ki dawo ba? Baki mallakeshi ba? Sai dai in ba ki saka Alhaji Ali wani abu ba, ba tunanin zai maki ya biya maki buk'atarki, Ai wallahi in baki gode mai ba, ba kya butulce ba".

Da fada Shafa tace "Yo ina amfanin mallake mijin, Tunda dan sa na daga hannu ko abun duka ya dakeka? Ina amfani? Kalla fa jikina duk shatin Belt, wallahi yaron nan haka ya hadeni da Hudu ya shaude mu da Belt, nidai wallahi ai man maganinshi, ba fa zata yiwuwu ba".

"Yanzu dai shima zai dawo k'ark'ashinki, sai yanda kikayi dashi, burinki ma zai cika na ganin ya bar Gidan, don shima zaki mallakeshi kamar Ubanshi, tashin farko ki mai umurni da barin K'asar gaba ki daya ba tare da ya k'ara dawowa ba, ita wannan kanwar ta shi kuma karamar Alhaki ce, murjeta kawai zakiyi".

Shewa sukayi tare da chafe wa "Allah ko kawata? To yanzu meye abunyi?" Er Rabi tace "kar ki damu kawata, zan hada maganin zuwa gobe, zan turo miki Yass gobe"
Sake chafewa sukayi Shfa tace "Shegia kawata, wasa wasa kin fa zama wata bokanyar kanki".
Dariya tayi tace "ke ko yau da gobe ko? Da su dinga cinye mana kudi ai gwara mu mun ci ma Mata kudi, ai kinsan samu nayi Baban Annah ya hadani da Aljannah guda wallahi Miliyan Ashirin na sayeta".

Ran Shafa bace tace "wallahi kar na sake jin kin kara furta Baban Annah, salon taji? So kike ace baban diyata boka ne? Banson iskanci fa Er Rabi". Wayan cewa Er Rabi tayi tace "yi hakuri kawata, gobe zan aiko Yass barin tafi". Sum sum ta tashi ta bar Gidan Alh Zaki tana mai borin kunya.

WasheGari

Uwa Uwa ce ko da uwar banza ce, ita ta san ba tayi dacen Uwa ba, ita ta san Uwarta na daga cikin Matan da ke cikin Halaka in har Allah bai shiryar dasu ba.
Uwarta ta kasance Matsafiya kuma Bokanya mai yin Shirka, ita kuma tana da kwamasho wurin taimaka mata wurin isar da sakwannin ga masu yin shirka kawai don kyautata mata kamar yanda ta ke kyautata mata itama.

Uwarta ce gatanta tunda har ita ce take biya mata bukatunta, Ubanta bai da mararraba da Mattace tunda baida say a gidanshi, mamarta itace Gidan, itace ke musu Providing komai na buk'atunsu, ita ke dawainiya da ita da Uban nata,ita kadai ce diyarta to Son duniyarta ta daurama tilon gudan Jininta, shiyasa tayi muk'u muk'u ta turata karatun Likitanci a Oxford University,  ta bata Mota, ta kaita kasar waje karatu, ta bata duk wani jin dadi na rayuwa meyasa ba zata mata abunda take so ba?.

Tana yin ma Uwarta Biyayya don ta kyautata mata kamar yanda take kyautata mata. Ta san tana cin haram tana rayuwa irin ta haram, amma son Mahaifiyarta ya rufe mata komai bata ji bata gani.

Murza Sitiyari tayi cikin k'warewa har ta isa Gidan Alhaji Ali Zaki, honk tayi a ka bude mata ta shiga da Motarta, sak'on ta dauko a wata paper bag ta shiga Gidan da Sallama.

Ta na shiga Cikin Parlon, shi kuma ya fito daga Kitchen dauke da Plate a hannu.
Idonshi na hagu ya murza a hankali yace “Yesmin K’amshi?”.
Bakinta wanda ya dade a bude tace “Zaid?? Kai ne? Me kakeyi anan?” Murmushi yayi yace “Me nakeyi a Gidan ubana?” Da mamaki tace “You mean this is your House?” Girgiza kai “This is My Father’s house”.

Nan da nan K’wak’walwarta ya kaita ga tunani, maganar mamarta taji a kwanyar kanta kamar a lokacin ake gaya mata.
“Ki ce ta saka mai wannan a k’ark’ashin Gado, wannan kuma ta barbada mishi a gaban daki da ya tsallaka shikenan zai shiga Duniya”.
Wannan kuma a yi hayak’i dashi, duniya zata manceshi, ba wanda zai tunashi balle ya damu da inda ya shiga, ita kuma Sadiya a bata wannan ta sha itama zata shiga duniya, ba zata ma hadu da yayanta ba a duniyar da zata shiga balle su shaida juna balle su tuna Gida”.

Wani zufa ya keto mata, bakinta na rawa tace “Aunty Shafa’atu mamarka ce?” Fuskarshi ya sauya , kamar ba zai amsata ba yace “Matar Babana ce”

Baya baya ta fara yi, kafin ta juya da gudu ta bar wurin, da sauri Zaid ya bi bayanta yana kiranta “K’amshi” amma bata juyo ba.
Kafin ya k’arasa gunta har ta shige mota, ta yi horn aka bude mata ta fita daga gidan a sittin.
Mamaki kamar ya kashe Zaid a tsaye, lafiyanta kuwa?”.

Tuk’i take cike da ganganci, Allah ya kaita Gidansu Lafia, tana shiga ta wuce dakinta straight.
Tunani barkatai.
Istighfari ta fara yi, kuskure daya, kuskure daya zatayi ta kai Zaidun ta ga Halaka, saura kiris ta batar da Zaid a shafin Duniya, Inalillahi, yaron da Mamarta da Aunty Shafa’atu suke son halakawa Zaidunta ne, Zaidunta fa, kai bata yiwuwa wallahi, sai inda karfinta ya k’are”.

Ta dade zaune kafin ta shiga toilet tayi Alwala tayi sallah, ita bata taba shirka ba, amma tana yadawa, Allah ka yafe mata.
Knock taji a kofarta, da k’yar ta bude.
Mamarta ce.
“Yasss yadai? Munyi magana da Hajia Shafa’atu tace “bakije ba, baki kai saqon ba? Ya akayi?”.
Dan guntun tsaki tayi tace “Oh Mommy wallahi ban dan jin dadi, har na fita kuma najini wani iri, shiysa na dawo” Er Rabi ta kamota “ayyah sorry Yass baby, sannu muje in baki paracetamol” Yesmin tace “Mommy karki damu nasha, ina so na kwanta ne”.
Er Rabi tace “Ayyh my baby shiga ki kwanta kinji, ki huta sorry”.
Er Rabi ta kira Hajia Shafa’atu ta shaida mata diyarta bata da lafia amma da ta warke InshaAllah zatazo aikota.

Bayan kwana biyu Yesmin ta fito tace “zata kai ma Hajia Shafa’atu sak’o”.
Er Rabi tace “Yass dauko kayan na k’ara miki bayani” k’amshi tace “ban manta ba, amma tuna min” haka Er Rabi ta sake mata bayani.

Yasmin ta fita daga Gidan a Motarta bata tsaya ko ina ba sai a wani Islamic Chemist, ta buk’aci a bata garin Zogale da garin habbatus sauda, da garin tazargade dana ‘da’d’doya, fasawa tayi ta hadesu guri gura tace wani sassak’e garesu? Sukace akwai na baure akwai na mangoro, tace duk a bata. Haka tayi hadadden magungunan ta biya ta shiga Mota ta wuce Gidan Alhaji Zaki.

Hudu na Parlo ya daura k’afa daya kan daya ya jiyo wani k’amshi na k’amshi, da sauri ya mik’e tsaye gami da hade miyau da ya ci karo da kyalyawar halitta na K’amshi, cike da shan k’amshi tace “Aunty Shafa na nan?” Baki na rawa Hudu yace “barin kirata ta na ciki”.
Samun wuri tayi ta daura k’afa daya k’an daya, tana kadawa a hankali.
Jim kadan sai ga Aunty Shafa ta fito da sauri hards rungumeta, itama ta rungumota.

“Yass ya kike ya jiki? Ashe bakiji dadi ba?” “Wallahi kam Aunty amma da sauki”
“Ya sSchool ko an gama?”
“Aa da saura, saura shekara daya”
“Inye Doctor Yesmin, yanzu ina sak’ona?”.
Cike da bariki k’amshi ta kalli Hudu, hudu yayi saurin cewa “kar ki damu Baby, ni k’anin Aunty, na san komai”.
Aunty Shafa tace “kar ki damu Yasmin”.

Ta ciro k’ullin da ta siyo yanzu a Islamic Chemist kamar yanda Mamarta ta mata bayanin wadan chan magungunan, haka ta mata bayanin a wannan “gasu Aunty, wannan a ba yarinyar aAbinci, wannan shi zaa saka a krkashin gado, wannan shi za a barbada a k’ofar dakinshi”.

Aunty Shafa tace “Hudu Dan Makaho na nan?” Yace “eh ya na nan” tace “to sai ya fita sai mu shiga dakin.
Hudu yace “to hakan zaayi”.
Mikewa tayi tace “barinje in adana” Hudubya zauna kusa da k’amshi, tayi saurin tashi ta rufa ma Shafa’atu baya.

K’amshi ta musu Sallama ta tafi, ta so ganin Zaid amma bakomai, ta san inda yake, zata cigaba da kareshi, wannan shine son da take mishi.

Mankas na barin Gidan Hajia Shafaatu da Hudu suka shiga dakinshi, suka daga Katifarshi suka wurga Sassaken iccen Mangoro da na baure.
Gaban dakin kuma suka barbada Garin Habbatus Sauda mai Zogale, ta dafa Abinci ta barbada garin Hibban a cikin Abincin Dalo ta mik’a mata ransu k’al yau zasu shig duniya.

Har bayan Isha’i bata ga Dalo ta fito ba, Zaid ya dawo, bin bayanshi sukayi suka ga ya shiga daki.
Su ka tsaya jiran tsammani amma shiru, a kan idonsu Dalo ta fito da plate din Abinci alamun ta cinye tas. Mamaki ya kamasu.

Har kwana biyu ba wani labari, cike da damuwa ta kira Er Rabi tace “ke ba wani bayani, yara na nan kamar mayu, ba wanda yayi yunkurin barin Gidan”.
Da mamaki Er Rabi tace “Be yiwuwa, maganin da Er Lale da kanta ta hada fa” cikin fushi Shafa’atu tace “koma Er dada ce magani beyi ba” Er Rabi tace “kwantar da hankalinki, yesmin zata kawo miki wani hadin, ki turo 800k”.
Shafa’atu tace “Er Rabi dubu dari 5 na baki fa shekaran jiya”.
Er Rabi tace “Yo Shafa’atu wannan maganin babba ne, zaifi aiki wallahi, ke ko miliyan ne in zaki samu biyan bukata ai sai kiyi ko?”.
Hajia Shafa’atu tace “Hmmm, zan miki transfer”.

Haka Er Rabi ta sake hada wani Maganin ta ba Yesmin, Yesmin ta zubar a hanya taje ta sake hado wasu tarkacen wannan karan hardasu dakakken Citta da masoro, bayanin kadai take kaiwa.

Har Sati daya ya wuce Ba wani bayani.
Cike da Masifa tace “Er Rabi ban fa san Iskanci da kutumar uba, don iskanci sai tura miki kudi nake kina cinyewa ba kya biya min buk’ata, 1.4 fa kikace ma tura maki”.

Er Ravi tace “wallahi kina ban mamaki, indai burinki zai cika ko nawa na ce ai kya bada ko? Da danake miki aiki baya ci? Wannan DanMakahon akwai babban kariya a tattare dashi, shiyasa asiri be kamashi, shine fa wannan karon nake son aika Er lale taje da kanta ta karya Asirin ta dauke shi ta kai birnin Sin ta dire”.

Shafa’atu ta yi jim tace “zan turo Miki 1.4 amma donAllah ki tabbatar Aikin nan wannan karon yayi”. Er Rabi tace “shikenan ba ki da Matsala, zuwa nan da sati daya zan turo Yesmin”.
Sukayi Sallama.

Bayan Sati daya Yesmin tazo Gidan da sak’on Mamarta wanda ta chanza a Islamic Chemist.
Da Zaid ta fara haduwa ta bishi da kallo taga duk ya wani kazance, kamar ba Zaid mai k’walisa ba.

Da murmushi yace “K’amshi”
“Zaid Ali Zaki”.
“Wai me kike zuwa yi Gidanmu, rannan kinzo daga ganina kika ruga a guje”
Tace “sorry Zaid, ya kake?”
Yace “baki amsani ba, me kike zuwa yi gidanmu?”.
“Ina zuwa gun k’awar Mamata ne”
Dan hade rai yayi yace “wacece kawar mamanki? Anan gidan?”
Tace “Aunty Shafa’atu”
Fuskarshi ya daure tamau “yace wurin Shafa’atu kike zuwa? Itace kawar mamarki? Nice”.
Ya yi gaba ta bishi a baya tana cewa “zaid menene? Ka saurareni”.
Yace “ke nifa ba ruwana dake, i have nothing to talk to you about”.

“Ka tsaya menene don na zo gaida kawar Mamata?”
Yace “Bakomai, kar ki kara nuna kin sanni, banda wata alak’a dake, na tsani duk wanda ke tare da Shafa Algus, ko da kuwa kece”.
Shan gabanshi tayi tace “Allah? Uhm Zaid? Tsana? Da ka sani da ba kace haka ba, ko da yake i dont blame you”.
“You have no idea what i have been doing for you, what i am still doing for you”.
Ya kalleta da dan mamaki yace “Uwar me kike min? To ki bari mana, in ma wani abu kike man uban wa ya saki?”.
Cike da bakinciki tace “Really Zaid? Really?”.
Yace “Yes K’amshi Really”.

Murmushi tayi tace “ba zan bari ba, you will thank me someday”. Ta wuce ta shige cikin Gidan ta barshi tsaye, da mamakinta ya bita da kallo, da ya ga kanshi zai fashe ya dauko world ya hambada kafin ya fara wani tafiya kamar tsallen kwadi har ya shige boysquaters”.

#1love
#DM
#anatare
#FWASonSo
#nagode

Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉
Chapter 7 · 0% Book details