Babi na Sha Biyu1⃣2⃣
Dan Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 28 min read
(MANCY 🤱🏻)
Daga kai tayi ta kalli Farin Wata da ya haske tsakar Gidan, ta sa hannunta daidai saitin zuciyarta ta karanta: Allahumma La Sahla illa ma ja'altahu Sahla, wa anta taj alal hazna iza shi'ita Sahla.
Saboda wani radadin da taji zuciyarta na yi ba tare da wani dalili ba.
Da kyar ta isa dakin, ta bude k'ofar a hankali ta raba ta shiga, sai dai zama tayi dabas kan Katifar, zuciyarta ba komai ciki sai tunanin DanMakaho.
Muryarshi ya dawo kwakwalwarta inda yake cewa "tausayina kike ji ko Sona kikeyi? In tausayina kike yi, ki bari bana bukatar a ji tausayina, in kuma Sona kikeyi shima ki bari bana buk'atar a so ni".
Kamar yana gabanta tace "ni fa ba tausayinka nakeji ba, kai din ne nake So" ta idasa hawa kan Katifar don yin bacci. Sai dai me? Tunanin Dan Makaho na nan mak'ale a zuciyarta.
"Huh!!!"
Ya fada Cike da mamaki da takaici.
Ta ya tace haka? Ta yaya ta iya fada mishi haka? Wani irin guts ne da ita? Karfe sha biyun dare? Ta yaya ta iya kallonshi har cikin kwayar ido tace mishi tana sonshi? Wace irin Macece? A ina aka taba haka? Haka sukeyi a Kudu? Tambayoyi ya ta ma kanshi.
Daga bisani kuma Ranshi kuma ya soma baci, don me za tace mishi tana Sonshi? Don me zatace dagaske take sonshi? Ko zolayarshi takeyi? Was she mocking him?" Hannu ya sa a cikin tulin sumanshi ya zube kan Gado don yin bacci, sai dai me? Tunanin Labiba da kalamanta ba su bar zuciyarshi ba.
Asuba ta gari
ZaiLab
*****
Alhaji Abu Shamsu na Tuk'i cikin kwarewa da iyawa, a lokaci guda yana taya Mamanshi da kawarta fira, a wani bangaren kuma yana daga kai ya kalli madubi daidai saitin Maryama da ke ta kuka a hankali.
K'awar mamarshi ta juyo tace "Ki bar kuka Maryama, ki gode Allah wallahi da bata nakasa ki ba, kishiya ai bala'i ce, nima haka na sha wahalarsu, aure na 4 duka banji dadi kishiya ba, amma da nayi hakuri, wallahi gashi na ci ribar hakuri".
Hajiya tace "kiyi hakuri, na san tunanin yaranki ke damunki, inshaAllah ba wata damuwa, kin ba Allah ajiyarsu shi zai kula miki dasu, ki kwantar da hankalinki kije kiyi Iddah ki samu miji kiyi aure.
Mancy dai murmushi tayi ba tace musu komai ba, suka dinga tafia har suka isa Kano, Unguwar Yayanta ta fada, da kwatance suka isa har Gidan Yayan, an ci saa ya na nan ta shiga Gidan, suna ganinta duk suka tashi, Matarshi ta rik'ota.
Maryama Lafia? Mun ga motar kaya akace daga Gidan Alhaji Zaki, shin Lafiya?" Wani kuka ta fashe da shi wanda ya tada hankalin Yayanta Umar da Matarshi.
"Yaya Baban Zaid ya Sakeni, Saki uku ya min Yaya" a tare suka rafka salati "Maryama me kika mishi?" A gurguje ta basu labari, sosai suka jinjina ma lamarin, ran Yayanta ya baci, har yana ikirarin sai yaje Katsina ya ma abokinshi rashin mutunci.
Hakuri ta hau bashi tana gaya mishi ba yin kanshi bane, sannan ta tuna mutanen da ta bari a waje, da sauri ta mike tace ba ita kadai bane, Yayan ya fita ya isa gurinsu Alhaji Abu Shamsu, Maryama ta shigo da Hajia da kawarta, ta basu ruwa a buta suka kama ruwa sukayi Sallar Laasar.
Alhaji Abu Shamsu ya ba Yaya Umar baki, ya mishi nasiha, Yaya Umar ya ji dadin dattakon Alhaji Abu ya mishi Godia sosai, ya tambayeshi in shi dan Kano ne, Alhaji Abu yace "Abuja yake da Iyalinshi, sun zo bin Jirgine zuwa Abuja don Mamarshi ba zata iya zaman Mota ba daga Katsina har Abuja, sai kuma kawar mamarshi da zasu aje a Rijiyar Zaki, Yaya Umar ya jinjina kafin suka dan yi fira, sukayi musayar number kafin suka musu Sallama.
Bayan tafiansu ne tayi wanka ta yi sallah, ta kulle kanta a Daki ta cizga kukanta son ranta, Yaranta sune damuwanta, wani hali suke ciki? Bata ma son sani, ta fi so ta yarda da cewa suna nan lafiya lau, bata son ta karaya har ta kirasu su ma ta karya masu da zucia don tana da htabbacin in har dai ta kira daya daga cikin Dalo ko Zaid to shakka babu sai sun sa kuka, har ta biye musu ba za a samu mai lallashin wani ba daga cikinsu, nan ne ta dau alkawarin kashe wayarta har sai ta samu natsuwa a cikin ranta.
Bayan Wata 5
Har ta gama Iddah bata nemesu ba, duk da Yayanta yayi ta rokonta kan ta rok'esu amma ta k'i, ko Zaid ya kira ta wayan Yayan yace a ba Mancy kin k'arba takeyi.
Haka ta kasance a Gidan Yaya Umar, ta na k'okarin ganin cewa ba ta zauna cikin damuwa ba, yaran Yayanta na debe mata kewa, har tau bata kunna wayarta ba, yanzu so take ta fara ko da neman aiki ne dama da kwalinta na nursing, dama shi Alhaji Zakin ne yace be yarda da aiki ba shiyasa batayi ba, yanzu ko dole ta nemi aiki don ba za ta zauna haka ba.
Gabaki daya suke zaune a Parlon cikin Gida, wayar Yaya Umar yayi Ringing, cirowa yayi daga Aljihunshi ya ga mai kiran.
Alhaji Abu Shamsu ne.
Bayan sun gaisa ne yake sanar mishi da cewa ai yana kofar Gidanshi.
Zumbur Ya Umar yayi "Ah aha, ka ja zance da yawa, ga ni nan fitowa". Ya kallesu yace "Bak'o mukayi, Alhaji Abu Shamsu ne".
Mancy da Matar Yayanta suka kalli juna suna neman karin bayani, amma yayi gaba don shigo dashi.
Parlornshi ya kaishi, suka gaisa sosai sukayi firan bayan rabuwa. Yaya Umar ya tambayeshi yaya Mahaifiyarshi? Ya sanar dashi cewa ai har ta gama hutun a Abuja tana Katsina, yanzu ma daga Katsinan yake yaje gunta.
Yaya Umar yace "Allah sarki, Allah ya ja kwana". Alhaji Abu ya amsa da Ameen.
Shiru suka danyi kafin Alhaji Abu yace "Alhaji Umar ina Maryama?" Da murmushi yace "aff kaga na shafa'a ban kirasu kun gaisa ba".
Yace "bakomai, dakata dai kaji Alhaji Umar, tun tuni na so zuwa Gidan nan amma na dakata saboda Maryama na cikin Iddarta, na yanke hukuncin zuwa bayan Iddarta shiyasa na zo yau, hak'ikanin gaskia tun randa muka dawo da Maryama take cikin tunanina, na tausaya mata, kuma ina son Aurenta in har zata amince dani".
Yaya Umar da murna yace "me zai hana in har Maryama ta amince da kai, barin turo maka ita dai ku tautauna in har ta amince sai ayi wallahi" Alhaji Abu Shansu yaji dadin hakan ya gyara zamanshi shi kuma ya shiga ciki.
Maryama dauki ruwa kikai parlo, akwai bak'o na nan na jiranki. Da mamaki ta kalli Yayanta tace "Yaya Bak'o kuma? Daga Ina?". Murmushi yayi yace "Yi Maza kije Maryama, ya na jiranki".
Mik'ewa tayi ta shiga kitchen don hado tray dama akwai Hijab cikinta straight parlon Yayanta tayi, tun daga k'ofar Parlon take jin wani daddan kamshi, nan gabanta ya shiga dukan uku-uku, kafanta yayi sanyi amma haka ta shiga da sallama, ganin mutumin da ke zaune ne ya sata karasawa cike da mamaki, amma sai ta dake ta fara mai murmushi.
Gaishe da shi tayi sosai da faraa a fuskarta, ya amsa shima cike da jin dadi, tambayar Hajiarsu tayi ya gaya mata tana Katsina lafia, shima tambayan mutanen gidan yayi ta amsa da Lafiyar kowa lau.
Shiru suka danyi kafin yace "Mancy"
Da sauri ta dago kai ta kalleshi cike da Mamaki, murmushi yayi yace "haka naji Zaid ya ce miki rannan a Gidan Sarki".
Sadda kanta tayi tana wani murmushi sakamakon irin kallon da Babban mutum kamar Alhaji Abu yake mata.
"Nasan zuciyarki na cike da tambayoyi kan me ya kawo ni ko? Ba tare da bata lokaci ba Mancy, so nake na shiga cikin jerin Zaurawanki don neman Aurenki, hak'ika bayan rabuwan mu na kamu da sonki duk da a farko tausayinki nakeyi amma daga baya na lura So ne, shiyasa ko da na ba Mamata labari ta karfafa min guiwa kan na nemeki".
Mancy tayi shiru ta cigaba da wasa da yatsunta.
"Uhmm?"
Ta dan dago tace "ni yanzu har wani aure zanyi? Ina da kamar Zaid? Sai dai in jira aurenshi".
Yayi yar daria yace "Shekararki nawa?"
Dan turo baki tayi tace "43" murmushi yayi yace "duka nawa kike? Ni ina da 65 shekarun babban Dana 32, amma bance na tsufa ba sai ke? Kuma ni fa ban ma yarda kin kai ko 25 ba".
Dariya ya sata sosai tace "Shekarun Zaid fa kenan".
Ji yayi ta sake burgeshi, har ranshi yake jinta cikin sanyin murya yace "Maryama, mu ba yara bane, bakiyi tsufa ba, koma kin tsufan nikam gani nakeyi kamar yar shekara 18 kike, ina so naji ta bakinki, in baki amince dani ba ba zan miki dole ba".
Shiru tayi ba tace komai ba
Ganin Shirun na neman yawa ne ya sashi cewa "ina iya baki Lokaci, kiyi shawara kiyi tunani, har zuwa jibi da nake shirin komawa Abuja".
Tace "to shikenan nagode".
Ba jimawa ya mata bankwana sukayi sallama ta shiga ciki ta ma Yayanta magana ya koma wurinshi ya rakashi har Gate ya sake jinjina mai dagaske yake sonta yake da Aure.
Da daddare ne Yaya Umar Ya kirata suka yi maganar Alhaji Abu Shamsu, Shawara ya bata a matsayinshi na Yayanta, yace "kar ta dakusar da kuruciyarta, kar ta manta Alhaji Ali saki Uku ya mata in ma tana tunanin koma mishi ne, tace "haba Yaya, tana sonshi amma wallahi ya fitar mata a rai, ba ta tunani ko aure ta sake ta fito zata iya sake aurenshi, ta hakura dashi" yace "to Ina ganin ya kamata kiyi tunani kan Alhaji Shamsu, ba zan miki dole ba, amma kar ki bari Alhaji Abu Shamsu ya subuce mata".
Godia tayi ta tashi ta koma dakinta.
Ta san ba zaiyiwu tayi ta zama a gidan Yayanta ba, duk da Uwa daya Uba days, yau da gobe sai Allah, Alhaji Abu baida wani aibu a zahiri, Zuciyarta tayi ta karanto mata shawarwari, har tayi naam da Alhaji Shamsu.
A ranar da zai tafi ya dawo, nan ta mishi Albishir da ta amshi bukatarshi, sosai ya nuna murnan shi, yace "zai basu Wata Biyu su Fahimci Juna, kuma ya na fatan suyi Bincikenshi kafin nan don da Wata biyu ya cika zasuyi Aure. Ita gani take kamar anyi gaggauwa amma shi cewa yake bata lokacin me zaayi.
Haka Alhaji Abu Shamsu yake zuwa Kano duk bayan Sati bibbiyu, har Mancy ta sake jiki suka shak'u sosai, suna fahimtar juna a lokaci daya kuma Yaya Umar na binciken Alhaji Abu Shamsu.
Wata rana suna tsakar Gida suna Zance kan Carpet, Alhaji Abu yake ce ma Mancy, in sunyi aure ta karbo su Zaid, Mancy tayi murmushi tace aa su yi zamansu a chan abunsu, yace "wai saboda me? Tace haba ina zani da manyan yara kamarsu? Dan shekara 25 da 'yar shekara 16?" Yace " to menene? Zan dauki nauyinsu, zan kula dasu a matsayin nawa" tace "aa Alhaji, ka barsu wallahi nagode sosai". Yace "to a dauko Macen" tace "aa ba wanda zaa dauko cikinsu, zasu dinga zuwa mana hutu". Ya juya kai cikin rashin jin dadi yace "to shikenan".
Ba su san shigowan mutum ba, sai dai suka ganshi tsaye kansu, hawaye ne ke kwaranyowa daga idanuwanshi, duk yayi bak'i ya rame ya jeme.
Da sauri Mancy ta mik'e zata rik'oshi yayi saurin yin baya kamar wanda wuta zai taba.
Alhaji yace "lafiya wanene ne wannan?"
Baki na rawa Mancy tace "ZAID".
Alhaji da faraa yace "Mallam Zaid muna lafia?".
Ba tare da yace ma kowa komai ba ya juya zai fita daga Gidan.
Mancy ta bi bayanshi tana kwala mai kira amma yak'i tsayawa.
Murya a kausashe tace
Zaid Aliyu Zaki kar ka sake ka fita daga gidan nan.
Chak ya tsaya. Ta taka har gabanshi ta tsaya tana kare mai kallo, idanuwanta suka ciko da hawaye amma sai ta dake, hannu ya sa zai murza idonshi ta rike hannunv.
"Baka ganni da bako bane Zaid?".
Juyawa yayi ya karasa inda Alhaji Abu ke tsaye yace "Ina Wuni?".
Alhaji Abu Shamsu ya amsa da Fara'arsa. Zaid ya juya ya kalli Mancy kafin ya dawo da dubanshi wurin Alhaji Abu yace "Daddy, ka aureta ka tafi damu Gidanka DonAllah".
ZAID mancy ta fada a kausashe.
Alhaji Abu yace "zan so hakan Zaid, zan so na hadaku da nawa 'yayan, kuma 'yayane, InshaAllah zan ga hakan ya faru".
Mancy tace "to lallai ka manta da maganar Aurenmu, na fasa ba zanyi ba kuma".
Alhaji Abu ya rikide yace "haba Maryama mai yayi zafi? Kiyi hakuri, dama ai sai da amincewarki zan daukesu, kiyi hakuri, ni niyyata masu kyau ne". Da sauri tace "Allah ya baka ladan Niyya, amma zasu tsaya Gidan ubansu" "Faqat".
Wani murmushin takaici Zaid yayi yace "Mancy, kina son mu kuwa? Mancy? Wace irin Uwa ce zata dafkar da Yaranta kamar wasu kayan wanki, ta tsallakesu ta yi tafiyarta, ta k'i waiwayonsu, ta ki nemansu? Ko sun nemeta ta guje musu? Mai muka miki? Ko mai na miki? Mai dalo ta miki? Eh Mancy?"
"ZAID mu shiga ciki mu gaisa ya kake?" Ta na mai nuni da Alhaji Abu da ke tsaye da Ido.
Bai damu da ba su kadai bane ba, yace "Mancy,kika tafi kika barmu, bai isheki ba, kika kashe wayarki baki neme mu ba, Mancy Mu kira Baba Umar, ko su Walid da Ummi, su baki wayar ki kashe ki ce zaki neme mu, baki taba neman mu ba? And now zaki ce min Ya nake? Really Mancy? Ya nake? Do i look alright to you? Bakiga nayi bak'i na rame ba? Bakiga na k'azance ba? To na ma fi kyan gani kan Dalo, ita in kika ganta so daya ba zaki so sake daga ido ki kalleta ba, saboda rama".
"Mancy Gidan Ubanmun da kike ta ik'irari bamu da wani gata ko galihu, Idi yafi mu matsayi a Gidan, Mancy ba wahalar rayuwar da ba ma gani, ba kallar Sharri da kazafin da baa mana, Mancy me muke ci a Gidan Uban da ba zaki bari a dauke mu ba, nan Kano zanzo sai da naci bashin Naira dubu daya wurin Eskaley, Mancy kamar ni yau ni ke ci bashi? Huh. DonAllah ki firda mu daga wannan k'angin, ki tafi damu duk inda zaki, Babanmu ba sonmu yake ba ba zai damu da duk inda zamuje ba, bai k'i mu shiga dunia ba, think of our Future wanda nawa ya fara rugujewa, da kanshi wanda kike son Aura ya miki tayin daukar mu amma kin hana, wai saboda me? Anjima sai kice kina Sonmu, kalar soyayyar taki kenan?".
Ganin yana magana ba tare da ya tuna wa yake ma magana ba ya sa ta daga hannu ta mareshi.
Dakata wa yayi tare da matse kuncinshi.
"Har Gobe, har abada ni Mahaifiyarka ce, ka san yanda zakayi man Magana". Kai ya sadda k'asa yace "kiyi Hakuri Mancy, ki yafe min, amma DonAllah ki tafi damu".
Alhaji Abu yayi tunanin tafia ya barsu don yana ganin kamar zasu zo su kebe, yayi hanyar Fita da sauri Mancy ta dakatar dashi ta hanyar cewa "dakata Alhaji, donAllah ka dawo, akwai abunda nikeso dukanku ku fahimta, mu zauna".
Alhaji ya dawo ya zauna
Shima Zaid din Zama yayi a bakin Carpet.
Mancy ta fara "Alhaji Nagode kwarai da kala Soyayyar da kake nuna min, na san Son da kake min ne ya shafi Yarana, nagode kwarai amma donAllah indai bani nace maka ina so ka taimaka ma Yarana ba kar kayi komai". Alhaji yayi mamakin Mancy Sosai, shakka babu bata da kwadayin abun dunia.
Ta kalli Zaid tace "Zaidun Babanshi, Mancy bata kyauta ba da bata nemeku ba, Mancy tayi laifi ku yafe mata kaji?" Kauda kai yayi yana son murza idonshi ta rik'o hannun tace "Haba DanMakaho na" murmushi ya subuce mishi don Mancy ba ta kiranshi da sunan sam sai in tana son sa shi daria.
Tace "to ka fahimceni, wallahi duk runtsi duk wuya baku da Gidan da ya wuce na Mahaifinku, kun fiso na tafi da ku Agolanci? Kama san meye hakan? Kana da Shekara 25 kake so ka bar Gidan Ubanka ka koma Gidan Mijin Mamarka? Haba Zaid kayi tunani mana, ban yi hakan ba don bana sonku, na yi hakan ne don na kwatar muku yancinku, ku zauna Gidanku, ku ma Mahaifinku Biyayya, ku maido da sonku zuciyarshi, ku samu albarkarshi".
Murmushi Zaid yayi yace "Ya riga da ya Tsine min, ta sa ya tsine min Mancy". Ba ta san lokacin da ta fashe da Kuka ba. Ganin haka Alhaji Abu yayi saurin Mik'ewa ya zaro kudi a Aljihu wanda zasu kai dubu 20 ya damk'a ma Zaid a hannu yace "barin tafi Zaid, kangaida Dalo, ku cigaba da Addua, Allah baya bacci". Yayi Gaba Zaid ya mik'e ya bishi a baya, Mancy kam bata yi yumkurin mikewa ba.
Sosai Zaid ya ma Alhaji Abu Godia, ya rakashi har Mota kafin ya dawo Gun Mancy dake durkushe a gurin, Zaid ya cigaba da bata labarin tun bayan rabuwar su zuwa yau da ya yanke hukuncin biyo Mancy. Sosai take Kuka kafin ta share hawayenta, Zaid ya yi zaton ta janye qudurinta amma da yaji tace "Allah ba ya bacci, ku cigaba da hakuri, gaskia zatayi halinta, kuma in dai ba saba mishi kayi ko addininka ba, to bakinshi ba zai bika ba, ba zai kamaka ba" ya gane cewa tana kan bakanta.
"Mancy ya maida tsine min fa kamar wak'a ko karatu, wata rana ko zai kamani". Mancy tace "Allah yana tare da ku Zaidu" sanin Mancy yar magana daya ce ya sashi mik'ewa don shiga ciki, ya san Magiyarshi da duk abunda zaiyi ba zai chanza mata raayinta ba, Mancy kaifi daya ce, ajiye mata kudin da Alhaji Shamsu ya bashi yayi, riko hannunshi tayi ta bashi kudin, tace na kune, ni banda kudin da zan baku da na k'ara maku, muje ka ci Abinci ka koma Katsina".
Murmushin takaici Zaid yayi yace "ba ma zan kwana ba?" Ta gyada kai tace "eh ba zaka kwana ba".
Mai makon yaji haushinta sai cewa yayi "Ya Rabb" zuwa yayi ya rungumeta sosai yace "nayi Kewanki da Yawa Mancy, ki kunna wayarki ki kira Dalo donAllah". Kai ta gyada mishi ya shiga ciki gurin Danginshi, sun ko ji dadin ganinshi sukayi ta rungumeshi suna fira, Ya gaida Kawunshi da Matarshi, Walid ya jashi zuwa Dakinsu, Ummi ta zubo mai Abinci, yayi Sallah Asahar da Laasar kafin ya mike don haraman tafiya, Walid ne ya fito don saukeshi a tasha, yaso sake kebewa da Mancy amma tak'i yarda. Haka ya musu Sallama Walid ya daukeshi zuwa Tasha.
Sai Gab da Isha'i Zaid ya isa Katsina, tun a hanya yace yau shagali zaiyi shi da kanwarshi, daga tasha ya wuce Chimex don siya musu Shawarma, ya tsaya a Mansho Suya ya siya Gassashen Kaza, ya siya musu Lemu da ruwa, kafin ya tsaya a Wani Shago ya siya ma Dalo Chocholates kafin ya hau Machine ya wuce Gida, sai da ya tsaya ya biya Eskaley dubu dayanshi kafin ya karbi World na dubu biyu, ya dan zuk'a kafin ya wuce Gida.
Yana Shiga Gida ya hau kwala ma Dalo Kira, babban parlo ya shiga ya gansu gabaki daya banda Dalo, hanyar Dakinta yayi yana kiranta da k'arfi, fitowa tayi da murna ta rungumeshi cike da jin Dadi "Ya Zaid ashe gun Mancy kaje baka tafi dani ba? Ya Zaid nayi waya da Mancy na, Mancy na ta kirani" Zuba musu ido yan Parlorn Sukayi, Shafaatu bakinciki kamar ya kasheta, wannan farincikin da sukeyi ya fi daga mata hankali, bata so ta ga ko da hakori daya ne ya fito da sunan daria, ranta ya baci.
Kasa hakuri tayi tace "DanMakaho tafiya kayi? Wa ka gaya ma zakayi tafiya?" Kallonta DanMakaho yayi yace "Kar naje gun Uwata? Sai na nemi izini? Kin yi kadan na nemi izininki" ya kalli Dalo da ta ki bari ranta ya baci yace "muje daki Dalo, muje kiga abunda na siyo miki" tsalle ta daka tace "Allah Ya Zaid naji dadi ko ba ka siyo min komai ba, da Mancy na nayi waya, kuma tace za mu dinga waya kullum" daria yayi wanda ya kara bak'anta ran Shafa, yace "muje Daki kar su huce.
Binshi Dalo tayi sai ji sukayi tace "ina zaki da daren nan? Dakin Yayanki? Ke karuwa ce zaki bi namiji dakinshi?" Zaid ya mika mata ledojin yace jeki gani nan zuwa ta bi umurnin Yayanta. Zaid ya taka har Parlo inda suke tsaye yace "Uwarki Ce Karuwa"
Hudu ya taho Zaid yace "kar ka soma, Agolan banza, ka san kayi gigin wani Abu bugun burauba zan maka yanzu".
Ya kalli Annah, yace "kinyi Asarar Uwa, Agola".
Ya kalli Shafa da take tsaye kamar an disata yace "Ni da Dalo muna nan zama daram a Gidan Ubanmu, baki isa ki koramu ba, ba ki isa ba wallahi, ko me zakiyi kiyi, ko me zaki sa ya mana ki sashi, amma baki isa ki sa ya koremu ba don ba inda zamu wallahi, in kinga mun bar Gidan nan, to Aure mukayi".
Ya juya yayi tafiyarshi, sai huci rai bace tace "bari Ubanka ya dawo" daga bakin kofa ya dakata yace "sai dai shi da kika raina, kar ki fasa hada mu da Mahaifinmu nikuma ba zan fasa miki duka ba, kinga ba wani abu bane don DanMiji ya bigeki" ya sa kai ya fice.
Wani ihun Bakinciki Shafa ta sake, Hudu da Annah sukayi kanta, bangaje su tayi ta wuce daki ta rufe.
DanMakaho Ya iske dalo a daki har ta fara cin shawarmanta dadi kamar ya kasheta.
"Yaya nagode nagode this is the happiest day of ny life tun bayan tafiyar Mancy".
Daukan shawarman yayi shima ya zauna yace "Nasani Dalo, i know".
Alhaji Abu Shamsu ya isa Gidanshi da Dare, yau ne yayi shirin gaya ma Uwargidanshi Hajia Lubabatu da Iyalanshu batun Aurenshi wanda zaizo a sati 3 masu zuwa.
Da Sallama ya Shiga Parlon Inda suke jiranshi gabaki daya.
Hajia Luba da Yaranta biyu Abdulhafeez da AbdulMajeed suna sanye cikin shiga ta alfarma.
Sannu da zuwa suka mishi gabaki daya, ya amsa da fara'arshi.
Direct Dinning Area suka wuce don yin Dinner.
Suna ci suna sha suna fira cikin jin dadi da soyayyar junansu. Alhaji yace "nikam Abdulhafiz ina Ummita ne? Kazo kana cinye min abincin gida" daria sukayi gabaki daya yace "Abba ta tafi Biki Kaduna sai ranar Lahadi zata dawo" Hajia tace "Ai Gauro ne bai da mata" suka sake daria.
AbdulMajeed yace "Abba da kaje Katsina ka ga Aisha?" Abba ya kurba ruwa yace "na ganta wai har ta kai SS2, ikonAllah yara suna ta girma". Umma tace "amma ka dai san dalilin da yasa Majeed ya tambayeka ko ka ga Aisha ko?" Majeed ya fara shurin Umma da kafa kan tayi shiru ta fara Dariya tace "to ba zan fada ba" Abdulhafiz yace "ni zan gaya ma Abba in ke baki gaya mishi ba".
Abba yayi daria yace "na san Zancen, ai sai ta gama Secondary zamuje ayi magana". Shidai Abdulmajeed kunya ya kama shi. Suka cigaba da cin Abinci kafin suka gama, suna niyan tashi ne Abba ya dakatar da ita, ta zauna su kuma suka wuce parlo.
Ya kalli Ummar yace "Hajia Luba, akwai abunda nake so na gaya miki".
Ta tattaro nutsuwanta ta bashi, "Hajia Luba, kin tuna Maryama wacce na baki labari? Da muka zo Abuja da Hajia?" Kai ta gyada tace "eh naganeta wanda Mijinta ya saketa ko" Alhaji Abu ya gyada kai sannan yayi dan Jim, kafin yace "So nike na Aureta".
Dimmm taji kafin ta dafe kirjinta tace "Aure kuma Alhaji? Wani irin Aure?" Yace "afuwan, donAllah kar ki daga hankalinki".
Nifa bangane ba, a kan wani dalili zakayi aure? In tausayinta kakeji ka bata jari mana, ba sai ka aureta ba, baka sakr aure tun kuruciyarka ba sai yanzu? Haba Alhaji".
Lallashinta ya fara yi, amma bata tausu ba ta cigaba da bude murya har sai da Abdulhafiz da Abdulmajeed suka zo.
Abdulmajid yace "Abba meke faruwa?"
Kafin Alhaji Shamsu yayi magana Umma tayi karaf tace "Majeed ni Abbanku ke son tonawa asiri, wai aure zaiyi, yana da Yara kamarku wai zai sake aure, ko Autanshi Jawad na neman shekaru 25 shine yake son tona min asiri".
Duk da sun ji maganar wani iri amma ba su nuna ba AbdulMajeed ya karasa gunta ya dafa kafadarta yace "Umma donAllah kar ki tada hankalinki".
Cikin karaji tace "Aure fa zaiyi, mai na rageshi dashi?" Abdulhafiz yace "Haba Umma, menene haka kike shirin yi? Ba mu taba jin kanku ba, menene don Abba zai kara aure? Umma ba a kanki zai ajeta ba, Umma Abba ba zai ki yin adalci tsakaninku ba, in Abba yau ya kawo wacce zata raina ki, kinsan mu Yaranki ba zamu yarda ba, donAllah ki kwantar da hankalinki, kiyi fatan a kawo maki ta gari wacce zaku zauna ku sake kwantar ma mahaifinmu da hankali" Abdulhafiz ya kalli Abbansu yace "donAllah Abba in wacce kake son aura zatazo ta tarwatsa maka farincikin Gidanka ne DonAllah kayi watsi da lamarin, amma in har zata kwantar maka da hankali ta k'i tada hankalin Mahaifiyarmu to Allah ya kawota Lafiya".
Fuuu Hajia Luba ta wuce daki, Da sauri Alhaji Abu yace "wallahi Maryama ba ta daga cikin Mataye masu tarwatsa farinciki Gida, in kuka ji labarinta zaku tausaya mata kuma zaku so ta kasance Aunty a gareku".
Abdulmajeed yace "In har ba zata daga Ma Mahaifiyarmu hankali ba to kana da goyon bayanmu Abbanmu, zamu tayaka shawo kan Ummanmu".
Hadesu yayi ya rungume yana sanya musu Albarka, Madallah da yara masu hangen nesa.
Da ban baki da Nasiha suka shawo kan Hajia, aka dai samu ta sauko daa fushin da tayi da Abbansu.
Biki ya matso aka sake gyara Gidan aka ware mata dakuna Biyu a cikin Gidan.
Zaid da Dalo kullum sai sunyi waya da Mancy, sun san zatayi aure, Mancy tace "suyi zamansu ba sai sunzo ba.
Haka aka daura Auren Maryama da Alhaji Abu bisa sadaki naira dubu 30 a nan kano, kamar auren Fari haka abokan Alh Abu suka zo.
Danginsu sunzo, Abdulhafiz da AbdulMajeed suka dauko Matar Babansu tun daga Kano har Abuja, ba ruwansu da taya Mamansu kishin haukan nan wanda yawancin mata keyi in aka ma Mahaifansu kishiya.
Nan aka danyi Walima wanda da shawararsu Majeed Hajia Luba ta hadashi. Dangin Maryama suka damk'a ma Hajia Luba Maryama, ba yabo ba fallasa sun karbi dangin Mancy, aka musu adduar zama lafia.
Da dare Alhaji Abu ya hada iyalanshi ya musu Nasiha ya musu fada ya masu fatan Allah ya hada kawunan su.
Abdulhafiz ma ya musu Nasihan zama lafia don kwanciyan hankalin Mahaifinsu, ya gargadesu kan su toshe kunnuwansu da ga jin tsegumin mutane.
**
Zama sukeyi da juna tsakani da Allah, ko wacce burinta ta burge Mijinta, Kishi irin na Yan Bariki sukeyi, Hajia Luba ta lura Mancy bata zo da raini ba, bata da matsala ko kadan, shiyasa ta kwantar da Hankalinta suke zamansu, Mancy ko ta na biye da ita, abunda yake dan sosa ran Hajia Luba shine yanda Abdulhafiz da AbdulMajeed ke son Mancy, komai Mancy Mancy, harta Matar Abdulhafiz ko ta zo Gidan da sun gaisa da Hajia Luba sai ta wuce dakin Mancy ta shantake, in Abdulhafiz yazo daukarta da ya shiga gun Mancy to fitowarshi ba lokacin ba sai sun sake bata lokaci, ta rasa mai suke cewa. Duk da ta san Mancy da son labari da jan fira shiyasa ta saye zuciyan kowa.
A duk lokuttan da suka shude tun bayan Sabon auren Mancy, ta kan tura ma su Zaid kudi duk wata, shiyasa ba ya rasa kudin zuk'an World.
Akwai wani Rana da Mancy ta aiko musu da kaya Shadda laces da atamfa kai harda provisions cike da Ghana Mustgo, Zaid yaje Tasha ya karbo, yana zuwa Gida ya kira Dalo ya na nuna mata Sak'on Mancy, kamar daga sama sai ga Alhaji Ali da Hajia Shafa.
Hajia Shafa tace "wannan kayan fa?" Banza Zaid yayi da ita ya cigaba da firdo da kayan ya na nuna ma Dalo, daka mishi tsawa Alhaji Ali yayi yace "bakaji ana magana ba? Wadannan kayan daga Gidan Uban wa suke?" Shiru yayi bai da niyyar amsawa.
Dalo tace "Mancy ta aiko mana dashi".
Sai da gabanshi ya fadi ya bi kayan da Ido. Hajia Shafa tace "ina ta samu kudin siyan wadannan kayayyakin tana zawarci?".
Dalo ta zuro baki tace "ta fa yi Aure".
Gaban Alhaji Zaki ya fadi da sauri yace "Maryamaa Tayi Aure?" Hajia Shafa da tsoronta kar ace Mancy Auren Kisan wuta ta yi don ta dawo dakinta, da sauri tace "to sai me in Auren tayi?" Nan ya fara "Sai me in Aure tayi? Ina abunda ya damemu da aurenta, zancen banza zancen hofi?".
Zaid tsaki yayi ya fara maida kayan cikin Ghana, Aunty Shafa tace "wai yanzu kai Alhaji ce mata sukayi kai baka daukar nauyinsu ne? Baka basu ci ba ka basu sha da zata aiko musu da provisions? Har da kayan sakawa, harta lipton don tonan asiri? Duk k'okarin da kakeyi a kansu ba sa gode ma ba sa godeAllah? Sai sun ce baka musu?" Ran Alhaji yayi dubu ya baci, yace "Allah ya tsine muku marasa gode Allah, duk abunda nike maku ba kwa gani?" To wallahi ba ku isa ku tona min Asiri ba, kamana ace ana turo da irin kayyayaki nan kamar na Mabuk'ata a gidana, ina Samson, kuzo ku k'onemin Kayayyakin nan".
Da Gudu Samson yazo don cika Umurnin Alhaji, Zaid yayi yunkurin hanawa amma Alhaji tuni ya fara tsinanshi, Dalo ta runtse Ido ta riko hannun Zaid, ta jashi baya, suna hange aka cinna ma Kayan Wuta.
Fargaban Hajia Shafa ace Mancy auren kisan wuta zatayi, ta samu Sarari ta kira Er Rabi ta gaya mata fa Mancy tayi aure a yi bincike a ga wata aure. Nan ErRabi ta kira Hajia Shfa tace "ke Maryama ta fi karfinmu don tana Auren Wani k'usa" nan kuma sai bak'inciki ya kaure.
**
Ran Mankas ya baci Ainun, amma Dalo ta taushe shi, ba su gaya ma Mancy ba, itama bata daina turo musu Sak'o in ta samu dama ba.
Ba da dadewa ba Mancy taje Dubai ita da Alhaji da Hajia Luba, ta musu Tsaraba, ta aiko musu dashi bayan dawowan su.
wani Jallabiya Dalo ta saka cikin tsaraban Dubai, Annah na ganin kayan taji Kayan sun mata kyau, cewa tayi ta je ta cire ta bata, dalo ta kalleta da mamaki, kafin ta bata amsa sai dai ji tayi Hajia Shafa tace "ina kika samo rigarnan? kije ki ciro ki bata kafin ranki ya baci, don munafunci ba Babanku ya hanaku karban abubuwa daga gurin Mahaifiyarku ba? Kije ki cire ki kawo ma Hannah ko yau Babanki ya tsine miki a karo na ba adadi. Jiki na rawa ta shiga ta ciro ta ba Annah, Annah ko ta fuzga taje ta chanza.
Annah ta ci kwalliya wai zata Gidansu kawarta, ta fita tana karairaya wurin inda ake prking Mota, kamar daga Sama sai ga Zaid, a Hak'e yake don yanzu ya zuk'i world yace "Ke wannan ba rigar Dalo bace? Tace "Aa" hr yayi gaba ya dawo baya yace "danubanki ba rigarta bace? Uwar wa ya siyo miki? Zaki gaya min gaskia ko sai na yankaki?" Da sauri tace "A ra min tayi" damk'o wuyarta yayi yace "cire don ubanki" jiki na rawa tace "barin je daki zan bata abunta" daka tsawa ya mata yace "a nan zaki cire danubanki".
Ihu ta kwala "Mummy" Mari ya katse mata hanzari, ya ja rigar tun daga Sama har kasa ya dire, ya fincikota ya kwabe mata rigar tas, kuka ta fara sosai ga cin mutunci gashi ya farka rigar. Allah ya so ta da vest a jikinta amma sharara ne har ana ganin Bireziyarta.
Shafa ta fito hankali tashe tana tambayar Annah me ya faru? Be bi ta kansu ba ya barsu a gun bayan ya dauki farkaken rigar ya saka a Bolan kusa dashi yayi hanyar dakinshi yana cewa da kuci arzikinmu gwara kowa ya rasa.
Ranan Har Daki Baba ya bi Zaid ya na ta tsinanshi kamar zai ari baki, shi ko Zaid din ko a jikinshi.
***
Watan Mancy 9 ta haifi diyarta Mace mai kama da Babanta, sosai akayi murnar samun karuwa a cikin Dangi balle duk yaran Alhaji babu Mace, dangi daga Katsina da Kano sukayi ta zuwa barka.
Hajia Luba ma ba a barta a baya ba don ta nuna Son Jaririyar.
Ranar Suna diya taci sunan Hajiar Alhaji Abu wato Halima amma ana ce mata Mimi.
Mimi na da Wata Biyar Autan Hajia Luba ya dawo daga Makaranta da sakamonshi na Masters wanda ya hado a Malaysia.
Jawad Miskili ne, shine Autan Umma, yasan Babanshi yayi aure amma ba ruwanshi da Mancy, daga gaisuwa shikenan, be iya shiga wurinta ya zauna kamar yanda yayyinshi keyi, indai Sun hadu a Parlo yana mik'a hannu ya karbi Mimi don Mimi son kowa ce, baya ganan bai da matsala da Mancy.
Wannan Kenan.
Jaje suka sake yi ma Juna a Massalaci, Alhaji Ali ya sake tabbatar ma Mallam Muhammad kan cewa kar ya damu shi zai sake gyara Bangon Gidan.
Kamar jiya Aunty Aseeyah ta tafi Gidan Iyayenta ta bar Labiba da niyyar in 10 tayi zata wuce Makaranta.
Kamar Jiya haka ta sake sando ta shiga dakin Mankas, yana zaune yana cin Bread da k'wai.
Kallo daya ya mata ya dauke kai, ko sau daya tunaninta bai fita daga kwakwalwanshi ba.
Da murmushi ta ce "Ina kwana YaZaid".
Shareta yayi ya cigaba da Breakfast dinshi ta k'araci zamanta bai tankata ba, ta mik'e da murmushi a fuskarta tace "ni na tafi Makaranta sai na dawo". Tak bai ce mata ba, haka ta fita ta barshi zaune ya bi bayanta da ido,ta tsallaka blocks ta fice abunta.
Runtse ido yayi ya bude, zuciyarshi na mishi wani irin zugi, sigari ya dauko ya fara zuk'a cikin Zafin nama.
Washegari
Haka aka sake Wani Ruwan Saman Ginin ya sake Rushewa, sau 3 kenan kasancewar lokacin damina ne kusan kullum sai anyi Ruwan Sama.
Hajia Shafa tace da Alhaji "wai kai ke da kudin banza? Kar ka sake ka kara gyarawa, in banda son banza shi ba zai gyara ba? Kuma su ma ake rufa ma Asiri tunda tsakar Gidansu ake gani, in abun ya dameshi ya gyara, kai kar ka k'ara Gyarawa kaji ai?" Da sauri Alhaji yace "Ba zan kara gyarawa ba, ai Muhammadu akwai son banza, ai kudin ba a bishiya nake katso su ba, in bai gyara ba ruwanshi". Da murmushi tace "yauwa Alhajina".
"In har ba damuna ta tsaya ba, Ginin nan ba zai bar rushewa ba"
Cewar Yaya Muhammad cike da damuwa.
"To ya zaayi" inji Aunty Asiya.
Baban Amira yace "wallahi ni kunyan Alhaji Zaki ma nike, ace duk rushewan da bangon yakeyi ko so daya ban taba gyarawa ba?" Tace "Ai ya san baka dashi kar ma ka damu". Yace "bari InshaAllah zan gaya mishi a bar gyaran haka har sai ruwa ya tsaya, in ba haka ba Allah na tuba asara zaayi tayi, anayi yana rushewa" Aunty Asiya tace "eh gaskia, Allah dai ya rufa Asiri".
A zuciyar Labiba kuwa ba ma taso a gyara, ita bata k'i a zauna a haka ba, hakan ne zai sa ta ga Sanyin Idaniyarta, sosai take jin shi a ranta, yanzu ma Jira take Baban Amira ya fita ta faki Idon Aunty Asiyah ta shiga.
Aiko yana fita tayi sadap sadaf ta fada Gidan Alhaji Ali.
Ba tare da jira ba ta fada dakin Zaid wanda daidai yake da fitowanshi daga Toilet daure da Towel a k'ugunshi.
Da sauri ta runste Idonta shi ko cikin zafin rai ya fincikota ya wurgata kan Gado yace "yau sai kin ci Ubanki, Wallahi yau ba zan daga maki ba".
Gadangadan yayo kanta...
Ghen Ghen.
Whats about to happen? Anyone?
Vote and comment line by line please
#1love
#DM
#FWASonSo
#anatare
#nagode
Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉