← Book details Dan Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 20 OF 20

BABI NA TALATIN 3⃣0⃣

Dan Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 84 min read

(FASA K'WAI 🥚)
(YAFIYA🤗)
(FARINCIKI😃)


Zaid ya runtse ido hawayenshi na fita, yace "Beebbs ina sonki da duk wani numfashin da nake ja ina saki, na san kina sona, ba sai kin sadaukar min da ranki ba, ba sai kin min haka ba, beebs donAllah ki bari, na rok'eki da Allah".
Labiba ta kyafta idanuwanta so biyu tace "Ina Sonka Sabida Allah, abin Alfahari na ne ace yau akwai ni a jikinka, in Allah ya sa an dace, zamu rayu tare, in ba haka ba, zamu mutu tare".
Yace "kinsan hakan na nufin kin kashe kanki da kanki, kinsan hukuncin wanda ya kashe kanshi?".
"Ni ba haka nake nufi ba, Allahn da rai na ke hannunsa ya san Zucia na, ya san niyyata, zaa dibi Hanta ta a dasa maka, end of discussion ".

Kyaleta yayi ya runtse ido tare da juya mata baya, gwalo ta mishi tare da maida hankalinta kan k'ofar da aka turo.
Dr Habib ne, Dr Ali yace "za a tura kudin Surgery account din Asibiti before a shiga da shi Operation Room".

Labiba ta dan kalleshi tace "Ohh, I thought Government Hospital ne, gwamnati ba ta biya ba?".
Dr Habib ya kalleta, yana son Confidence dinta yace "Gwamnati na dai tallafawa, amma ai ana biyan Aiki, ba kamar private hospital ba, sosai ba zaki hada kudin da na chan ba, akwai sauk'i rangwame sosai".
Tace "Okay nawa ne?".
Yace "ga takardan nan kije bursary department, ki basu zasu baki bank details da transaction slip ki biya sai ki kaima cashier ta baki receipt dai ki kawo mana".

Zaid na jinsu yayi lamo, hankalinshi ya dan kwanta, ya san bata da kudin da zata biya, ko da 20k ne balle ya san sai ya fi.
Direct chan ta nufa da taimakon sign boards.
Ta bada slip din, a computer akayi danne danne aka mata printing.
Expenses din naira dubu dari uku da saba'in.
Gaban Labiba yayi mugun sarawa.

Chabda, in ba a biya kudin nan ba zata iya rasa Zaid ko? Aikam ba zata iya jure rashinshi ba, ya kama ko meye zatayi don ta samo kudin nan, dakin Ta koma hankalinta a dan tashe.
"Kanaji ba?".
Banza yayi ya kyaleta.
Tace "Masoyin, na fa san ba bacci kake ba".
Ya juyo fuska daure yace "Meye?".
Tace "Wai kudin Aikin 370k".
Yace "Alhamdulilah, your Liver is safe".
Tashi tayi tace "kayi ka gama, zan je neman taimako".
Yace "Ina? Tace ko ma ina ne, ko bara ne i will do it, but ganin bamu da time zan rok'a su mana bashi zamu biyasu".
Zaid kallonta kawai yakeyi, sonta na tsaga hantarshi mai ciwo, komai nata na burgeshi, wautarta na kayatar dashi.
Cikin wasa yace "ke kika aje su da zasu miki aiki Kyauta? Ohh bashi kika ce ko? Tsoron ki sukeji Ko?".
Ganin yana son maida abun wasa tace "ka yi ka gama, banda lokacin wannan yanzu barin je in ga Dr Ali".

Har ta kai gaban k'ofa ta choge ta tsaya, mai ta tuna oho, maida kofar tayi ta rufe ta dawo cikin Dakin Zaid na kallonta.
Mai take shirin yi?
Wayarshi ta dauko ta kunna, har tayi 19%.
Har gabanshi ta tako ta dauki yatsarshi ta dangwala a wurin thumbprint wayar ta bude.
Hoto yaga ta daukeshi kusan guda uku, kafin ta dauki takardan hannunta hoto.
Kallon Mamaki yake binta dashi.
Matsawa tayi dan gefe amma yana kallonta taka danne danne a wayarshi.
Baayi minti 3 ba yaji wayar tayi ringing.
Amsawa yaga tayi ta sa wayar a Kunne.

Tana jin muryar ta san hankalimta a tashe yake "Hello? Zaid meya sameka? Me ya faru?".
Labiba ta amsa a ladabce "Assalam Alaikum Mancy, Sunana Labiba Ahmad Dakata".
Da sauri Zaid yayi yunkurin tashi amma ya kasa.
Mancy tace "wacece ke? Me ya samu Zaid? Ina yake?"
Labiba tace "Ya na bukatar Emergency Open Liver Transplant Surgery".
Kusan da karfi Mancy tace "Lahaula wa la kuwatta illa billah, Zaid din? Me ya sameshi haka?Liver Transplant fa kikace"

Labiba tace "Emergency ne,Hantarshi ya fara damage, suna so a cire infected area a saka wani, an samu donor, amma ba a samu kudin Aikin ba".
Da sauri Mancy tace "DonAllah zan kiraki, Ina zuwa".
Mancy ta kashe wayar ta fita,dalo ta bi bayanta.

Wai Beebs ke baa gaya miki magana kiji? Ba kya jin maganata ko? Ba a isa a hanaki abu ba ko?".
Kulle idonta ta tayi ta bude, murya ta sassauta tace "ya kake so ayi?".
Shima ya saukar da murya yace "kar ki wahalar da kanki, ki bar Hantarki, Hanta fa ba kamar k'oda bane, aka samu matsala, akwai yiwuwar daga ni har ke babu mai tsira".
Tace "to ai yafi nayi ta zaman jiran gawan shanu, yafi ace na zauna banyi komai ba, yafi ace na kasa taimaka ma wanda nikeso, donAllah mu bar maganar nan, Mancy tace zata kirani".

Zaid yace "Beebs ba kya jin magana".
Ta murmusa tare da mikewa don amsa kiran Mancy tace "nima ina sonka".
Harara ya galla mata ta fits tana daria.

Alhaji Abu Shamsu ya karbi wayar yana magana da Labiba, itama Office din da ta bar Dr Ali da Dr Habib ta nufa, ta ba Dr wayar, nan ya ma  Alhaji Abu Shamsu bayani, da cewar an samu Donor wani bawan Allah, kamar yanda Labiba tacr musu su ce.
Alhaji Abu yayi ma Dr Ali Transfer din kudin, tare da basu go ahead din yin aikin.

Hankalin Mancy da Dalo ya kasa kwancia, sun kasa daurewa sai kuka suke, Alhaji Abu yace "Ku shirya ku bi jirgi gobe, sai Jawad ya rakaku".
Mancy ta dan ji sanyi, don gobe da sassafe zasu tafi, duk nadama ta mata katutu, bata ganin laifin kowa sai nata, itace sila, da bata barsu a Kt ba, da baiyi shaye shaye ba, da bai jama kanshi cuttutikan zamani ba, laifinta ne, in ta rasa Zaid yanzu bata san ya zatayi ba.
Alhaji Abu ya cigaba da kwantar mata da hankali yace "InshaAllah komai zai wuce, zai warke, Allah zai tada kafudunshi.

Bayan an gama komai ance su shirya kasancewar taci Abinci shima yaci suka kara 5hrs kafin su yi aikin, sai gab da Asuba zaayi aikin.
Zaid ya dan runtsa, ita kam ta fito waje.
Zama tayi kan kujera tana tunani.
Tsoro ya dan kamata, data ga dai dagasken aikin zaayi, ba zata fasa abunda tayi niyya ba, ba kuma tayi nadaman zuwa katsina ba, amma In bata rayu ba bayan aikin? Ya kenan? In ta mutu fa? Iyayenta fa, ya kamata ta nemi yafiyarsu, gwara su san halin da take ciki k'ila adduarsu ta bita.
Da sauri ta kunna wayarta ta ga messages da yawa bata bude ko daya ba, ta shiga create message ta hau typing, tana yi tana kuka, ta kusa daukan minti talatin tana yi kafin tayi marking ta tura ma Maminta da Abbansu.
Sai da ta tabbatar sun shiga kafin ta kashe wayar.

E D O

Cirko Cirko sukayi, Mami har tayi kuka ta gode Allah, ba wanda bai zo ba, kowa tambayar kanshi yake ina Labee ta shige.
Da yawa sun zata kidnapping Labiba akayi, Amma kidnapping har gida? Ko ta fita baa sani bane suka ganta suka sace, maganganu kala kala dai, kowa da abunda yake sak'awa.

Message ya shigo ma Abbansu lokacin wayar na hannun Abba yana amsa gaisuwar jaje da ake kira ana mishi.
Da dan murna mai sauti yace "Labee Ce, Labee ta yi sak'o".
Tuni aka yayyabeshi aka zagaye shi kowa na son jin meye a cikin message din.
Abba bai yi boko ba amma ya iya karatun hausa da k'arfi ya fara karanta message din

*"Abbanmu da Maminmu, zan fara da neman yafiyanku, ku yafe min don Girma da darajan Allah, kar kuyi fushi dani, ku saka min Albarka danAllah Abbanmu da Maminmu, yanzu kuce Allah ya miki Albarka Labee"
Abba ya kalli Mamin a tare suka ce "Allah ya miki Albarka Labee".
Abba ya cigaba da karantawa *kunce? Yauwa".*

*"Allah ne shaida, kun min tarbiya kun nuna min So amma na muku laifi babba, na fita bata da saninku ba, nayi abunda mutane da yawa zasuyi tunanin banda mafada ne ko banda magayanmasu min fada, na manta da halin da zaku shiga, na tsallake na fita, na san hankalinku dole ya tashi, to wallahi ina Katsina, eh fa Katsina na zo ni daya".*
Nan duka parlorn suka dau sallalami.
Ja'ira ashe Katsina ta tafi.
*"Kuyi hakuri, kuce Allah ya shiryaki Labee" Abbansu ya girgiza kai cike da takaicinta yace "Ya Allah ka shiryaki Labee" ya cigaba da karantawa "yauwa kunce?".*
*"To, Wallahi Abbanmu, nazo Katsina naga Zaid baya da lafia, bansan yanda zan muku bayani ba, amma wallahi baida lafia sosai, Hantarshi ta baci shine ake neman wanda zai taimaka a diba nashi a dasa a nashi, shine ba a samu wanda zai bashi ba, shine fa nace a diba nawa".*
A tare suka "Lah Illah ha illallah Muhammadan rasulillahi sallalahu alayhi wa salam".
Mamin wani jiri taji ya debeta.
Da kyar Abban ya iya mik'a ma Yaya Haruna wayar ya cigaba daga inda ya tsaya.

*Gabanku ya fadi? "DonAllah kuce Inalillahi wa ina ilaihir rajiun*".
*donAllah kuyi hakuri, bansan me zanyi bane, taimakon da zan iya mishi kenan, ku sakani a addua, bansan ko zan tashi ba bayan aikin, bansan ko zan rayu ba, shiyasa nace barin sanar daku, ku sanyani a addua, in akwai abunda nafi yarda dashi a rayuwan nan wallahi be wuce Adduarku ba, ku min Addua Iyayena, in na mutu ku yafe min ku sanya min Albarka, in kuma Allah ya sa na rayu in na dawo ku hukuntani wallahi, zan dauka, ni din mai laifi ce*

*"Mami  wallahi dubu biyar dinki na dauka, nidai wallahi karki ce sata ne, amma dai ki yafe min, in Allah ya sa na warke, na fara aiki zaki fi kowa jin dadi a rayuwa, zan zame miki abin alfahari, kuce ma Baban Amira yayi hakuri ya yafe min, na bashin ciwon kai da yawa, Mami in mamansu Samira na miki fada ki daina mata shiru, in samira ta miki rashin kunya ki mareta, in Yaya Zaliha ta haihu ta samu mace kice a sanya mata Labiba, ace kar ta zama kamar goggonta, ta rayu da kyau, haha kamar ina bada wasiyya ko? ba fa wasiyya bace, zan dawo inshaAllah, nasan Mami zaki gurji rayuwata da dorina zaki bugeni? Ina sonki, donAllah kar hankalinku ya tashi, ku mana addua, Allah ya sa a dace, karfe 4am zaayi aikin, addua donAllah, kar ku manta, a gaida min su Samira, ina son su duka, Abbanmu Maminmu, kuce Allah ya miki Albarka Labee".*

Kafin a kai karshen Wasikar, an kira layin wayar kashe, masu raunin zuciya tuni suka fara kuka, barin ma Samira da ke kuka wiwi kamar an ce mata Labeen ta mutu, sai da Abbansu ya tsawatar, yace "kai ku kwashi iyalanku ku koma gidajenku, ku kuma ku wuce ku kwanta".
Ba wanda ya iya cewa komai aka fara fita daya bayan daya.
Yaya Hajara wanda mamarsu daya da Labiba ta rik'o hannun Mami ta jata zuwa dakinta.
Mami ta ci kuka sosai, ranar batayi bacci ba tana kan dardumarta tana kai kukanta ga sarki mai Sama, Allah ya raya mata diyarta ya kareta a duk inda take.

K A T S I N A

4:40am

Batayi bacci ba itama, Zaid dinne yayi gyangyadi ya farka, har nurses suka shigo dauke da kayan da ake ba marasa lafia su saka in zaa musu aiki.
Labiba ta amsa Zaid ya mata Alama da ta zo taji.
Matsowa tayi da kunnenta daidai bakinshi.
Yace "beebbs, kina da halin chanza hukuncinki, kina da halin cewa kin fasa, ki chanza tunani kafin ki makara".
Labiba tayi murmushi tace "ni dai na gama magana, ina kan bakata".
Zaid ya girgiza kai yace "Allah ya shiryaki mai taurin kan tsiya".
Daria tayi sosai tace "Nima ina sonka Masoyi".
Ta shige toilet.

Jim kadan Labiba ta fito daga toilet sanye da kayan theater, murmushi tayi data ga an chanza ma Zaid irin kayan sunyi anko, gadon gefe da aka tanada don ita ta hau, nurses kam suka gungura Zaid da Labiba a kan Gado zuwa Operation Room.
Kowacce Adduar da yazo bakin Labiba yi takeyi.
A cikin OR idanunsu akan junansu bacci ya kwashesu sakamakon allurar da aka musu ta

Drs suka dukufa kansu suka farka su sukayi duk wani abunda suke bukata cikin kwarewa kafin suka dinkesu.
A zahirance aikin ya tafi daidia, zaace it's successful sai a jirayi farfadowansu..
%%^^

Ana Sallahr Asuba Mutanen Edo suka shiga Mota, Baban Amira ne da Abbansu da Mami, da an biye ma Mutanen Gidan, sai kowa ya bisu, Maminma da k'yar Abbansu ya yarda ta biyosu, wani tsohon direban Abbansu ke tuka motar a Golf din Abbansu.

Su ko mutanen Abuja karfe 9 jirginsu ya tashi daga Abuja zuwa Kano, daga Mancy sai Dalo sai Jawad, Abba yace in basu dawo zuwa jibi ba zasu biyosu.
Da suka isa Kano Yaya Usman Yayan Mancy ya zo ya dauke su a Airport.
Sai da suka biya Gidanshi kafin ya ba Driver Mota ya kawo su Katsina basu tsaya ko ina ba Sai General Hospital.

Ba su sha wuya ba suka gano Dakin da aka kai Zaid da Labiba bayan am fito da su daga OR.
Basu farfado ba nurse ta sanar dasu.
Mancy tace "DonAllah zan shiga in ganshi".
Nurse tace "da dai kin bari sun farfado".
Mancy ta matsa, nurse ta bata umurnin shiga ita kadai, tana shiga ko ta saka kuka ganin yanda Zaid yake kwance lifeless, gefenshi ta kalla ta ga wata yarinya kyakyawa kwance itama a dayan gadon.

Mancy sosai ta ke jin haushin kanta, ba zata daina jin laifinta bane, itace sila, itace ummul abaisin shigan Zaid wannan yanayi, da bata barsu ba, da bai tagayyara ba haka, da kyar ta iya fita daga dakin.
Ta dawo inda su Dalo da Jawad ke tsaye.
Jawad yace "Mancy muje Gidan Uncle Usman muyi Sallah mu ci Abinci, in yaso sai mu dawo Anjima".
Mancy ta girgiza kai tace "Aa Jawad, bana jin zan iya tafiya na bar Zaid, zan jira ya farfado, ka tafi da Sadiya".
Dalo ta mak'e kafada tace "zan jira farfadowan Yaya Zaid".
Jawad yace "To bari naje Gidan, zan taho da Abinci, naga famfo chan kuyi Alwalla kuyi Sallah, sai na dawo".
***

Hudu ne a Gidan Hajia Er Rabi don yi mata gaisuwan Yasmin.
Ya shiga Parlon yana ta tafka uban Sallama, muryoyi yake ji amma zai rantse ba na Mutane bane.
Tashi yayi zai fita yaji an daka mai tsawa.
"Hudu, Shafa'atu ta tarwatsa min farincikina, Shafa'atu ta sa na rasa Farincikina, wallahi sai ta gwammace bata shigo duniyan nan ba, sai tayi nadamar sani na, ta jirani kawai".
Yanayin yanda ake maganar ya sa Hudu fita gidan a Guje fitsari na bin wandonshi.

Yanda ya koma Gida hankali a tashe ya tabbatar musu cewa ba lafia, Shafa'atu tace "Wai Hudu uban me ya sameka? na lura tunda ka so danne Dalo ka fita hayyacinka, duk ka zama wani lusari, barinje Jifatu na dawo".
Ya bita da ido, Annah ta galla mai harara ta wuce dakinta.
Yafi minti 10 zaune kafin ya tashi
ya nufa dakin Alhaji Zaki.
Dakin yaji a kulle, sai ya fada dakin Yayarshi.

Direct Wardrobe dinta ya nufa.
Ya bude yan kunne da sarkanta zinari ya kwashe kusan set 4 ya zurasu a wando.
Yayi 'yan bincike bicinkenshi duk abunda ya gani wanda zai kawo mishi kudi sai da ya dauke, kudi kau ya kwashe tas kusan 200k.
Ya samo leda ya cikashi da karikitai ya fita.

Ya fita jikinshi na bari.
Ya hadu da Anna, tace "Uncle Hudu ina zaka da kayan Mummy?".
Banza yayi ya k'yaleta, tayi saurin rikoshi, ya juya ya mareta tare da sake mata nushi a ciki dama ya dade yana jin haushinta.
Tana kaiwa kasa ya fita a guje, maigadi na mai magana yayi banza dashi, saarshi daya ya ci karo da dan Achaba a kofar Gida ya hau yace "muje kawai".
**

Shafa'atu ta shigo gidan a fusace sakamakon kiran da Annah ta mata tana ambaton sunan Hudu.
"Wallahi Hudu kace zaka ma Annah Tumasancin da kakeyi sai naci ubanka, in wannan tsohuwar ta kyaleka ni ba zan kyaleka ba, ina Hudun yake?".
Annah da ke rik'e da kumatunta ta na kuka tace "Mommy Uncle Hudu ya kwashe miki kaya, duba dakinki ki gani".
Hankali tashe ta shiga dakin kamar zata kife, maajiyarta ta gani a hargitse, ta dubata ga babu kudinta, babu zinarints, babu duk abubuwa masu mahimmanci, wani ihun sunanshi tayi "Huduuuuuu, ni zaka ma Sata? Wallahi sai na kasheka".
Wayarshi ta shiga nema tana kiranshi amma baa dauka ba, daga karshe taji wayar a kashe.
Sosai hankalinta ya tashi domin tas Hudu ya yasheta, bata da komai a dakin, huci take kamar kura cikin fushi tace wallahi ko birnin sin kaje, sai na sa Er Rabi ta dawo min da kai, shege butulu mara godian Allah".

Garin zai bari, zai je ta fara rayuwa inda ba wanda yasanshi.
Bank ya nufa ya ciro kudi kafinya wuce Tasha ya hau Motar Kano.
A kano ya sayar da sark'okinshi a wulakance a wurare daban daban.v

Jawad ya dawo Asibitin wurin k'arfe 3 da coolern Abinci.
Zaune ya ga Mancy kan wata tabaarman da bai san inda ta sa mota ba, Dalo kuma na kwance kan cinyarta.
Jawad yace "Bai farfado ba? Mancy ta gyada kai alamin eh, yace "to ga Abinci kuci, Antisco na gaidaku tace "inshaAllah in mutane sun ragu zata zo ganinshi".
Mancy murmushin karfin hali tayi tace "Yaya jikin Uncle Usman din?".
Jawad yace "ah da sauki yace ran Monday zai fara Azuminshi".
Tace "Allah ya k'ara Sauk'i".
Yace "Ameen, wai wannan barci take?".
Mancy tace "Eh bacci takeyi".
Tsugunno yayi kusa da ita a hankali yace "Sadyy, tashi ki ci Abinci".
Bude ido tayi ta zube kanshi.
Mancy tace "Oya tashi kuje chan ki ci Abinci kinji Dalo?"
Baki ta turi cike da Shagwabab ta tashi.
Jawad yace "Mancy ke fa?"
Tace "Jawad, wallahi ba zan iya ba, bari dai Zaid din ya tashi".
Jawad ya kada kai ya bi bayan Dalo da ta fita daga Amenity zuwa wani wuri da aka tanada don fira.

Yace "Oya zuba kici"
Dalo ta shagwabe fuska tace nifab na k'oshi, banson Mancy tayi magana ne kawai amma wallahi banjin yunwa".
Hararta yayi yace "baki isa ba".
Ya bude coolers din ya zuzzuba mata a plate yace "Eat".
Zata yi magana ya sha mur yace "ina wasa dake? Ki cinye duka ko na miki dure".
Shagwabe fuska tayi tace "Ya Jawad ba fa haka akeyi ba".
Ya harareta yace "haka akeyi, eat up".
Murmushi tayi ta sa hannu tana cin abincin, shi ko Jawad kallonta kawai yake yana mamakin yanda yake sakewa gabanta.

Sai da yayi Sallahr Laasar kafin ya shiga Asibitin.
Suma zaune suke kan tabarma, Dr da nurses suka ga sun nufo dakin da Gudu.
Mancy tayi saurin mikewa ta rufa musu baya.
Tana shiga ta ga idonshi a kan nata
"Alhamdulilah Zaidu na ka farfado".
Ta nufeshi da sauri ta rungume yana a kwance ta shiga kissing dinshi cikin jin dadi, Dalo ma ta rukunkume yayanta tana kuka.
Shidai yana kwance yana binsu da ido.
Nurse tace kuyi a hankali kar ku fama mishi aikin da akayii.
A galabaice yake kallonsu, ya ma Dr Ali ido da yazo yaji
Dr Ali ya matsa tare da daura kunnenshi saitin bakinshi.
A wahalce yace "Labibaaa".
Dr yace "Sorry bata farfado ba, Alluran bai saketa ba".

Mancy ta kalli Labiba da ke kwance kamar Matatta takawa ta farayi zuwa gadonta tace "wai itace ta yi donating Liver dinta?"
Dr Ali yace "Eh itace, ta damu jiyan nan har sai da dai aka yi Aikin nan".
Dalo ta matso wurin tace "Lahh Mancy, k'anwar Mallam Muhammad ne".
Mancy tace "Wa?".
Dalo tace "Makwabcinmu, Mijin Aseeyah".
Mancy tace "yana da kanwa ne?".
Dalo tace "eh daga garinsu ta zo karatu ne".

Jin haka ya sa Jawad yin sauri zuwa gadon idonshi ya gane mishi Labiba.
Gabanshi ya fadi, yayi saurin kallon Zaid da yake kallon gadon amma baya iya komai, ya hango hawaye kwance a idon Zaid.
Jawad yaji jiri na dibanshi.
Da bango ya jingina.

Mancy tace "Dr, akwai wanda yazo gunta?".
Dr yace "anya kuwa babu fa".
Mancy tace "to ya haka?"
Chan ta mik'e tsaye tace "ko dai ba su sani ba? Kar dai yarinyar nan ta bada Hantarta ba btare da sanin Magabatanta ba?".

Dr ya k'ara da cewa "Gaskia bana tunanin sun sani, ita kadai tazo jiya, ta sha kuka, ta kuma nace kan sai anyi aikin cikin gaggawa, nikuma gaskia i had no choice saboda i was desperate to help my friend recover, shiyasa mukayi operating kanta".
Mancy tace "Without consulting her Parent or Guardian? Is this how you do things here?".m
Ganin Ran Mancy ya baci ya sa Dr Ali yace "Sorry, amma she's an adult, ita ta zabi hakan".
Mancy tace "Dubeta Yarinya ce fa, banji dadi ba gaskia sam".
Dr Ali ya ma Nurses ido suka fita shima ya sabe don ya saba dokar Asibiti.

Mancy tace "Sadiya zo kije Gidan Mallam Muhammadu donAllah kice yazo Asibiti, kira Drivern, no ba time ki hau keke napep".
Sadiya tace "to ta fita".
Mancy ta rik'o hannun Labiba tana jin Son Labiba na ratsa duk wani bargo na jikinta.
Zaid kam baida karfin yin komai,hawaye kawai ke sintiri a idanunshi.

Dr Ali ya sa nurses maida Zaid Amenity tunda ya farfado, aka gungurashi kan Gado aka bar Labiba a ICU.
Dalo ta bi gadon Zaid.
Mancy kam ta tsaya tana leken Labiba ta window don ba a so ana shiga ICU.

Jawad kam bai san mai ke mishi dadi ba.
Duk wani karonsu da Zaid ya shiga dawo mai, sai yanzu ya gane, ashe Son juna suke? Ashe kishinshi Zaid yake in ya ganshi da Labiba yayi ta wasu abubuwa."
Itama Labibar, Wani irin so take mishi haka? Da zata sadaukar mishi da rayuwanta.
Haaa ga matar da zai aura kwance magashiyan rai hannun Allah, matar da zai aura ta ba Saurayi Hantarta, saurayin ma wani bashi ba? Lallai akwai matsala, akwai babbar Matsala".
Yana ganin wucewar Dalo, ya kasa binta domin jikinshi yayi sanyi sosai.
***
Sadiya ta isa Anguwarsu, ta dade tana kallon Gidansu, kafin ta shige Gidan Mallam Muhammadu da Sallama.
Aunty Aseey ta fito da Amsa sallamar tana wata kamar Dalo.
Dalo ta murmusa suka gaisa.

Tace "ya Abuja? Ance kin koma chan".
Dalo tace "Eh,Aunty Aseey Baban Amira fa?".
Tace "yana chan Edo fa".
Ta yi shiru, da dukkan alama ba su san meke faruwa ba.
Aunty Aseeyah tace "Lafia kuwa?".
Dalo tace "Mancy ce ta aiko ni, Labiba na Kwance a Asibiti".
Aunty Aseey tace "wace Labibar?".
Dalo tace "Labiba taku".
"Ban fa gane ba, Labibar mu ai tana Edo".
"Aa ta na nan, a Asibiti, an mata operation".
Cikin rashin gamsuwa tace "tsaya kiga na kira miki ita".
Aunty Aseey ta kira number Labiba tajita kashe, tace "barin kira baban Amiran".
Da kyar ta sameshi. Yana dauka suka gaisa tace "Ina Labiba wayar ta be shiga".
Yace "Afuwan Asiya, ban kiraki ba, gamu nan a hanya, inshaAllaj kafin Maghrib mun iso Katsina".
Tace "kai da wa? Da Labiba?"
Yace "Aa, da su Abba da Mami".
Tace "Labibar fa?".
Tana jin karaya a muryarshi yace "Asiya Labiba  na nan Katsina, sai munzo zakiji komai".
Aunty Asiya ta kalli dalo, ta amince da maganarta tace "ga Dalo nan tazo wai Labiba na Asibiti wai har operation an mata, meke faruwa Baban Amira? Dama Labiban bata da Lafia?".
Da sauri yace "Wai har anyi? Wani Asibitin ne?"
Ta tambayi dalo, tace "General Hospital".
Yace "Ga mu nan InshaAllah sai munzo".
Ya kashe waya.

Aunty Aseey tace "me ya faru da Labeen? Menene?".
Dalo ta warware mata zare da abawa.
Da gudu da shiga daki ta fizgo Hijabinta ta ciro mukullan gida tace "Muje, dalo muje".
Tace "Yaran fa? In sun dawo?"
Tace "muje in sun ga gida kulle sa shiga makwabta, inallilahi Allah ka tashi kafadar Labiba, wallahi Labiba bataji".
Ita dai Sadiya bata tofa komai ba suka hau Napep suka nufa Asibiti

Suna Isa Asibitin Mancy ta rungume Aunty Aseeyah.
Ta window aka nuna mata Labiba
Kuka take tace "Wallahi Aunty Maryam Labiba bata jin magana, babu yanda ba ayi ta rabu da Dan makaho ba amma ta ki ji, daga Edo fa ta saci hanya tazo, zataci ubanta na sani, bari su Abbanmu su zo".
Mancy dai yak'en dole takeyi, ta na jin yanda ake kyamar danta kamar wani mai najasa, da alamun Asiya ta manta wacece ita a wurin Zaid da batayi wasu zancen ba.
Mancy tace "ni in ga ta farfado ya fi man komai, ta farfado ko meye zai biyo baya".
Suna zaune jigum jigum.

Gidan Kakansu Jawad ya wuce, bayan sun gaisa ta tambayeshi sanadiyar zuwa, ko wannan karon ma budurwa aka zo gani, dan tsaki yayi yace "wace budurwa? Yaron Auntynmu akayi ma Aiki dashen Hanta, shine na rakosu, Abba bai kiraku ba? Suna General a ICU be san surutu ya shige chan k'urya yana ta fira da zuciyarshi.
Kakar tashi ta kira Abba ya kara mata bayani, haka tayi ta kiraye kirayen wayan 'yanuwa ta na cewa suje su dubo Dan Mancy a Asibiti.
    Da yawa 'yan Anguwan Alk'ali sunje ganin Zaid amma an hanasu ganinshi saboda yau ya fito daga OR, zasu iya stressing dinshi, saidai su gaisa da Mancy, su koma, sosai su ka ma Mancy kara a matsayinta na matar danuwansu.
**

Antisco da Aisha sunzo, ta kawo musu Babban Darduma da Basket din Abinci suka shimfida daga Waje don baa zama a cikin ICU.
Mancy tace "ai da baki wahala ba Antisco, wanda Jawad ya kawo dazun da saura, ya jikin Uncle dinsu".
Antisco tace  "haba ai ba wani abu, ke dai Allah ya basu Lafia".
Aisha tace "Aunty Aseey, me kike yi a nan, waye be lafia?".
Aunty Aseey dai cikinta ya duri ruwa bata iya cewa komai ba.
Antisco tace "kin santa ne?"
Aisha tace "Lah, matar yayan besty ce"
Antisco tace "Ah haba, Allah sarki, Mancy surikarki ce, kanwarsu Jawad zai aura".
Gaban Mancy ya fadi tace "Labiba Jawad ke So?".
Antisco tace "kin ma san Labiba kenan,ah Lallai Jawad baya jin kunya ya baki labarin budurwarshi?".
Mancy ta girgiza kai tace "na shiga uku na, dazun Jawad naga ya fita rai bace, ashe dalili kenan?".
Antisco tace "me ya faru da Jawad?".
Mancy tace "Antisco, Matar da Jawad zai aura, ita taba Zaid Hantarta aka diba aka dasa mai".
Aisha tace "Kaiii, Labiba ta ba danki Hanta? Ina ta sanshi Mancy?".
Ikon Allah.
Mancy dai bata sake magana ba, Aishar ma haka, ba wanda ma dai ya sake cewa komai.

Anty Aseey ta rafka uban tagumi tana jiran isowarsu Mijinta.
Har su Antisco suka karashi zamansu suka yi musu Sallama tare da tabbatar musu da cewa zasu dawo gobe.

Tafiyarsu Antisco ba dadewa ba Mutanen Edo suka iso, kasancewar suna wajen ICU yasa basu sha wahalar ganesu ba.
Su ka k'araso.
Aunty Aseey ta rik'o hannun Mami saboda da kyar take tafia kafarta ta kumbura sosai saboda zaman Mota, sai sannu Aunty Aseey ke jero ma surukarta.
Ko ba a fada ba ansan Mamin Labiba ta sha kuka.
Mancy kamar ta goya su sai gaisuwa take kwasa.
Yaya Muhammadu yace "Hajia ashe kina nan, ina Labibar?".
Mancy tace "kuyi hakuri bata farfado ba".
Mami tace "Labiba ta mutu ko?"
Mancy tace "aa wallahi, allurar ce bata saketa ba".
Mami tace "amma shi dan naki ya farfado?".
Mancy cike da kunya tace "eh ya farfado".
Abba yace "muje mu ganta".
Lokacin Visiting ya wuce wai ba zasu barmu mu shiga ba.
Baba Muhammadu yace bari na ma security magana.
Da kyar aka samu ya bari suka shiga da niyyar suna ganinta zasu fito.
Mami ko sai da tayi magana ta na kuka tace "Labiba in kin Tafi na yafe miki, wallahi na yafe miki, Allah ya rahamsheki, in kuma baki tafi ba Allah ya tashi kafadunki, Zuciyar Mami na zafi, ki tashi ki lallasheni, kice Mami zuciyar ta bar Zafi haka nan ga ki nan, donAllah".
Da kyar Baban Amira ya fitar da ita ganin kuka take sosai.
Abba yace "Labiba kin san dai Dukkan nan sai kin sha shi ko? Ki tashi in zaneki, ki tashi hakan nan".
Ganin shima kukan zaiyi ya sa shi fita da sauri.
Mancy tace "Sannunku kun sha Hanya, ku zauna donAllah ku ci Abinci gashi nan".
Yaya Muhammad yace "Mami kiyi hakuri ki zauna ki ci Abinci"
Mami ta kauda kai.
Mancy da durkusa a kan guiwowinta tace "ba dan ni ba, kiyi hakuri donAllah, laifi laifina ne da banzo da wuri ba, wallahi da ina nan ba zan taba yarda a bude diyarki har a diba wani sassa na jikinta ba, donAllah Mama kiyi hakuri, dole ranki ya baci, donAllah kiyi hakuri ki ci Abinci".

Abba yace "ashe mutum be san ya dauki k'addara ba? To ko cewa akayi Labeen ta mutu ne? Amina bani son dogon zance, zauna ga Abinci kici".
Zama tayi, Abba ya zauna, Yaya Muhammadu ya zauna, sai kanenshi Hamza shima ya zauna.

Jikina rawa Mancy ta bude cooler din Abincin Gidan Auntisco ta zuzzuba musu Faten Dankali da Shinkafa.
Ko wanne ta kai mishi gabansh, tayi serving dinsu.
Ta ja hannun Dalo suka wuce chan Amenity dakin da Zaid yake.

Sun gama cin Abinci Abba yace "muje mu gano shi Masoyin Labeen".
Fit Mami tace "ba inda zani".
Abbansu yace "kinga Amina ki shafa ma zuciyarki salama, to in Allah yace lokacin Labiba yayi kumburin da kike shi zai maidota? Ke baki san kaddara ba, maimakon ki ta rokon Allah ya bata lafia ya tashi kafadunta kin tsaya kina fushi? Har kina ma da lokackn Riko? Haba itama kinga hankalinta ba kwance yake ba, danta na chan shi kadai, amma ta na nan zaune gun diyarki har sai da mukazo, wallahi ki natsu".
Nasiha ya mata kafin ta yarda zataje ta ga Zaid.

**
Zaid na ganin Mancy yace "ta farfado?"
Mancy ta girgiza kai cike da tsoro.
Rufe ido yayi kawai ya kawar da kai.
A ranshi yana fata in mutuwa Labiba tayi Allah ya dauki ran shi, ba zai iya rayuwa babu ita ba".

Mancy na ganinsu ta mik'e tana taba Zaid, Zaid bude idonka kaga  Baban Labiba ne da Mamarta.
A hankali Zaid ya bude idanunshi,  yana ganinsu yayi yunkurin tashi Abban ya maidashi, yace "ka adana k'arfinka, zaka buk'aceshi".
Zaid yace "donAllah kuyi hakuri, laifi na ne, wallahi laifi na ne, Labiba batayi komai ba, nine mai laifi, ni zaku hukunta, ni zakuyi fushi da, Labiba batayi komai ba".

Mami ta ji son Zaid da tausayinshi, tace "inshaAllah zata farfado, kayi hakuri".
Ba su k'ara minti Uku ba aka gunguro gadon Labiba.
Duk suka mik'e suka tarbesu.
Ta farfado, daga kallon fuskarsu kasan suna matukar farinciki.

Kwance fa take ba ta wani k'arfin kuzari tace "Ina Zaid? Yaya jikinshi, Dr yace ya farfado, yana ina".
Da dukkan alamu sambatu ne, bata san su waye ke kanta ba.
Mami ta kalleta sosai, kallon da take mata in tayi laifi.

Kamar zata gudu tace "Lahh, Maminmu, kiyi hakuri kar ki bugeni, wallahi aiki aka min yanzun na farfado".
Daria ta ba Mami, Mami tace "Allah ya baki lafia Labee, sai na miki dukan tsiya, bari dai ki warke".
Labee ta turo baki tace "kuyi hakuri".
Nurse tace "haba Mama, ya kuna haka ne? Daga farfadowanta kun fara sa ta kuka? Abeg ku fita visiting ya kare sai gobe kuma".
Haka nurse ta tarkata su ta kora waje.
Mancy ta dawo wai tayi mantuwa, ta duka kan Labiba ta na murmushi tace mata "In maminki ta gama dukanki nima zan miki nawa, waya ce miki ana satan hanya a zo gun saurayi? Kika bashi Hantarki? Da icce zamu bigeki".
Ta durkusa ta manna mata kiss a goshi tare da gyara mata kwancia zuwa gefen Damarta.
Mancy na kaucewa idonta ya fada kan na Zaid da ya tsura mata ido, wani Sonta na cizgarshi.
Nurse ta gama duba ruwa da jinin hannun Labiba, kafin ta fita ta barsu su biyu cikin daki irin na mutum biyu daya.

Lumshe ido sukayi a tare Zaid yace "kin wahala ko?".
Ta murmura tace "aa ba wahala, kai fa?".
Yace "Sannu Kinji".
Tace "Nagode"
Yace " for what?".
Tace "for Staying alive, nagode daka warke, ina ma Allah Godia da ka rayu".
Zaid yaji hawaye na zuwa mishi, wannan wani irin So take mishi, like yanzu fa ta samu kanta ta farfado amma she's still worried about him.
Murmushi yayi yace "focus and recovering and take that beating from Mami".
Ta marairaice fuska tace "Zaka karbar min Bulala?."
Yace "aa gaskia, bulala fa na kine, ke za a zane, ni meye nawa na shisigi? Kawai ki karbi bulalanki da kanki kizo muci gaba da gashi".
Tace "yanzu Masoyi ba zaka iya tsayawa a dakeka mai makon ni ba?".
Zaid ya girgiza kai yace "Nope".
Tace "waiyo heartbreak, let me just die now".
Ya wani zaburo yayi saurin komawa sakamakon zafin da yaji gefen na mishi, ya cije baki, ta na lura dashi.
Yace "Kar ki sake, kinsan how worried you got me? Labiba da baki farfado ba, da bansan ya zanyi ba".
Ya kalli Sama yace "Allah kar ka barni da iyawata ban iya komai ba, Allah ka bar min Labiba".
Tace "Ameen Masoyi".
Yace "Ina Sonki".
Tace "Ina sonka Masoyi".
Soyayyarsu suke zabgawa a gadon Asibiti, ba su da wata damuwa.

Su ko Darduman Waje suka zauna suna dan fira jefi jefi.

0000000000

Tun da garin Allah ya waye take surkullenta.
Wani k'ok'o ta dauka ta fita dashi a hannunta, ta kira aljannarta da ke binciko mata abunda take so tace "je duba man kiga ina Dan Makaho yake?".
Ko minti daya batayi ba ta sanar da ita cewa Dan Makaho na Asibiti kwance.
Hankalinta ya tashi "kar fa ya mutu, diyarta bata mutu ba don shima ya mutu, dole ya rayu ya ji dadi kamar yanda Yasmin ta mishi fata, ta manta rayuwa ba a hanunta yake ba.
***

Tun da ya dawo take mishi mitan Hudu, bai ji dadi ba sam, hakuri yake bata yana cewa kar ta damu, zai siya mata sabbi, chan sai taga yayi shiru tare dafe kanshi, wani irin Ja Idonshi keyi, zufa ke keto ma Alhaji Ali Zaki kamar yana dakin Gidan Biredi.
"Alhaji baka lafia? Tashi mu tafi Asibiti"
Bai iya ce mata komai ba ya tashi ya fita ta bi bayanshi, Annah ma ta bisu a baya.
Mota su ka shiga, har yanzu kwakwalwarshi juyawa take yana ganin abubuwan da suka faru kamar film.
Tuni ya fara tari ba k'ak'autawa, ganin ya amayo wani K'aton dutsi ya sa Hajia Shafa'atu kara gudun motarta don ta tsorata sosai.
Sai sannu suke jero mishi ita da Annah.
General Hospital suka nufa.
Emergency suka nufa.
Fitowar su kenan suka hango Er Rabi da ke tunkarosu ta kallesu daya bayan daya.
Shafa'atu tace "Er Rabi ina kika shiga tun jiya wayarki bata shiga , Daddyn Annah na kawo Asibiti baya jin dadi".
Cike da umurni tace musu "ku biyoni".
Tayi gaba rungume da k'ok'onta a kirji, tafia sukayi a k'afa har Amenity ba wanda ya tambayeta din me kamar ta rufe musu baki.

A bakin k'ofar ta gansu zaune da alamun Sallahr Isha'i suka idar.
Mancy da Dalo na ganinsu suka mike tsaye.
Alhaji Ali yayi saurin durkusar da kai , Shafa'atu kuma na ma kawarta ido don me suka zo nan?.
Er Rabi tace "Yauwa, nayi farincikin ganinku a nan, ni da na zo gurin Zaid na fasa k'wai ashe kuna nan".
Shafa'atu ta tabo kawarta.
"Menene? Bangane ba Er Rabi, me ke faruwa ne?".
Er Rabi ta murmusa tace ina Zaid? Ina so komai zaayi a gabanshi?".
Mancy a dan tsorace tace "me ya faru? Zaid na kwance bai lafia an mishi Surgery, menene?".
Er Rabi tace "Kwai zan fasa, zan tona ma Shafaatu Asiri kuma zan tona ma kaina Asiri, ni dinnan nan da kuke gani, bokanya ce ni".

Mamin Labiba da Aunty Aseeyah suka saurin mik'ewa cike da tsoro.
Baban Muhammadu da Abbansu ma suka mik'e Er Rabi tace "duk kuyi mun shiru, kar wanda yayi katse man magana".
Kamar ta sa kwado ta rufe musu baki ba wanda ya iya magana, duk wanda yayi yunkurin magana sai ya ji ya kasa da alamu siddabarun ta musu ta fara magana.

"Sunana Hajia Er Rabi, ke Maryama kinsanni." Ta kalli Alhaji Ali tace
"A yau Zan fasa k'wai, Matarka Shafcy bata da Aminiyar da ta wuceni, bayan ka mata kishiya, ta haihu ka so danka fiye da kowa da komai, bayan ka saketa, na kaita wurin wani bokana, baban Annah kenan".
Annah ta gwalalo ido. Er Rabi ta harareta tace "Eh Babanki Boka ne, babanki shi yace ta dawo bayan shekara Sha biyar zata samu Alhaji Ali Zaki, zata juya shi yanda take so, ba zai mata gardama ba, zata mallakeshi amma sai bayan Shekara 15, bayan shekara 15 ta dawo Dakinta sakamakon Asirin da baban Annah ya tafka, shiyasa a ranar da ta dawo gida aka ma Maryama Sakin Wulakanci, ya juya ma 'ya'yanshi baya sai abunda tace yakeyi, ta rabaka da Danginka da komai sai abunda tace kake so".
Shafa'atu so take tayi ihu, so take ta sa Er Rabi yin shiru, me yasa take mata haka? Meyasa take tona mata Asiri?" Gashi ta kasa ko da motsi, Er Rabi ta kafe su, ta sa sun k'ame k'am.
Alhaji Ali Fitsari yaji kawai na zuwa mishi ta k'afa.
Mancy da Dalo kam hawaye ke kwaranyowa daga idanuwansu.
Sauran kam sai zare idanuwa suke.

Er Rabi ta cigaba "Ni ba wannan bane damuwa na, damuwa na shine Zaid, zuwa nayi na rok'eshi gafara na kuma cika burin marigayiya Diyata da ina jin ta fi son Zaid a kaina, Sonshi take har ta koma ga Allah, har ta mutu tana rok'ona na kare mata Zaid, na tayata sonshi, ta na so na kula mata dashi, ta na son Zaid, ni kuma ina son abunda Diyata take so, yau na fasa k'wai, zan kuma zare hannuna daga duk wani abunda zai sa Zaid din Yasmin ya cutu ko wani masoyinshi".
Er Rabi ta fasa k'ok'on hannunta wani bak'in ruwa da k'adangare suka fito daga ciki.

Er Rabi ta kalli Sama tace "Yasmin... kinji dadi? Na cika miki burinki".
Er Rabi ta kalli Shafa tace "Dalilinki na rasa diyata, dalilina duniyarki zata juya".
Ta wuce ta k'yallesu chan suka fara motsi.
Aunty Aseey tace "K'urungus k'aryar 6era ta k'are".
Shafa'atu ta ja hannun Annah da gudu suka shige Mota babu wanda ya kulasu.
Alhaji Dakata ya musu nuni da su koma ciki, Mamin Labiba da Aunty Aseey suka matsa gefe don ba su wuri tare da barin Alhaji Ali, Mancy da Dalo kamar ba su da lakka a jiki.

Alhaji Ali ya kalli Dalo da rinannun idanuwanshi yace "Sadiya, Ina Zaid?".
Dalo ta fashe da kuka ta rungumo Babanta. Kamar jira yake ya fashe da kuka.
"Baba nayi kewanka".
Baba yace "Darlingg".
Sadiya tace "Ba darling ba dalo".
Cikin hawaye suke daria.
Baba ya kalli Mancy zuciyarshi yaji kamar zata tarwatse.
Yana son Matarshi sosai, Shafa'atu ta rabashi da ita har tayi wani auren.
Yace "Maryam, yaya kike?".
Mancy kasa magana tayi tana cin kuka.
Ina Zaid? Yana ina? A zo a diba Hantata a bashi, in ma Zuciyata za a sa mishi, a cire nawa a samishi donAllah, ku ceci yarona, ina son mishi magana".
Mancy na kuka tace "Baban Zaid, an riga anyi Surgery din, Zaid na nan ya farfado, nurses ne suka koromu wai sai gobe".
Baba yace "ku kaini wurinshi donAllah".

Da kyar aka barshi ya shiga.
Yana bude kofar ya hada ido da Zaid.
Kallo daya Zaid ya mishi ya hango k'auna, soyayya, nadama, ban hakuri a ciki.
Baba kuwa karasawa yayi gadon Labiba, kamar zai fashe da kuka yace "Sannu ko? Sannu, Allah ya baki lafia".
Labiba tace "Ameen nagode".
Baba yace "kin gode? Da me? Ki bari kawai yarinya, Kiyi shiru donAllah".
Labiba ta bishi da ido har ya karasa gadon Zaid.
Dafa goshin Zaid yayi yace "Sannu, me ke maka ciwo?"
Da tsantsan mamaki Zaid yake kallon babanshi yace "babu komai, ban dai da karfi".
Baba yace "dama karfi ba yau ba, yau fa akayi aikin, dole kaji kasala, sannu".
Zaid kai ya daga, Baba ya kallesu a tare yace "Ku warke da wuri kunji".
Kai suka sake dagawa.
Ya fita.
Labiba ta ja dogon numfashi tace "I think this is actually your Father, he is back".
Zaid da ma ya rasa abunyi yace "Wannan shine baba na, tabbas, Allah Nagode".'

Ya na fita ya ci karo da Mancy ta na waya, da alamu da Mijinta suke waya don ya dan ji maganar samasama inda take cewa "Goben zaka taho? To Allah ya tsare min kai ya kawo min kai Lafia Mijina".
Dam ya ji gabanshi ya fadi wani abu ya sokeshi a zuciya.
Tana waigowa ya kirkiro murmushi.
"Sannunku, kun sha fama".
Murmushi kawai yayi.
Ya wuceta ya nufa Gunsu Alhaji Dakata, Sallama ya musu ya mika ma Abbansu hannu kamar zai durkusa, Abban Labiba duk tausayinshi ya kamashi.
Ba abunda Alhaji Zaki yake sai zuba Godia yana gode musu.
Kan darduman suka zazzauna.

Alhaji dakata yace to ai dare nayi, ba zamu ta zama a nan ba, Muhammadu dauki matarka ku wuce Gida, yaranku na chan na zaman makwafta".
Baban Amira yace "to Baba da wai ni na kwana da Labiba, ai ba a barsu su biyu a Asibiti ba".
Alhaji Dakata yace "aa sam, ni da Maminku zamu kwana, kai dai ka dauki Matarka da Haruna".
Alhaji Ali yace "Aa Alhaji, ya zaayi ka kwana? Mallam Muhammadun ya kwana".
Mancy tace "aa duk ni zan kwana duk ku tafi masauki".
  Aunty Aseey tace "Mami muje Gida".
Mami tace "ni zan kwana gidanki?".
Aunty Asy tace "Mami lalura ce, ni bama ki taba zuwa Gidana ba".
Mami tace "ba kuma zanzo  ba  ehe".
Daria sukayi, wai ita bata zuwa gidan danta na fari.

Dalo ta rada ma Babanta a kunne "Baba daga Edo State suke, ba su da inda zasu kwana".
Alhaji Ali yace "to Abunda Za ayi, Shi Muhammadu ya tafi da Matarshi gida, Alhaji da Hajia ku tafi Masauki, Hajia Maryama kema ki tafi Masauki, Asibiti ne, ICU baa jinya, amma yana da kyau wani ya tsaya a nan".
Baban Amira yace "Ni zan kwana".
Mancy tace "Aa fa ni zan kwana da yarana".
Alhaji Ali yace "kin tambayi Mijinki? Ba zaki kwana ba gaskia".
Be jira amsar kowa ba ya matsa gefe, yana waya ya dan jima yana waya kafin ya dawo.
Cikin Mintuna da ba su wuce 20 ba Motoci 3 suka zo harabar Amenity.

Alhaji Ali yace "Alhaji ga Mota chan, Driver zai kaiku Masauki Please, kuje chan ku huta, gobe da safe zai maidoku".
Zasuyi gardama Baban Amira yace "donAllah Abbanmu kuje ku huta, kun sha tafia".
Abba yace to shikenan Muhammadu muje ka bude mota ka bamu kayanmu"
Mami tace "Sai da safenku".
Mancy tace "to mungode kwarai".
Alhaji Ahmad Yayi gaba Matarshi na binshi a baya.
Alhaji Ali ya kalli Yaya Haruna yace "kaima bisu, akwai wurin kwananka" da sauri ko ya bisu.

Ya kalli Dalo yace "ku ina zaku kwana?".
Dalo tace "Baba in zo muje Gida?".
Kallonta yayi, beyi mamaki ba don ta nemi izinin binshi Gida.
Yace "Dalo kizo muje Gida".
Mancy ta mata ido, alamun kar taje, har ta manta abunda Hudu ya so mata? Ga Shafa'atu.
Dalo tace "kar ki damu Mancy, Babana zai kareta daga sharrinsu".

Alhaji Ali ya kawar da zancen yace "Dalo ki raka Mamarki Masaukinta, driver zai kawo ki Gida, kuje da Matar Muhammadu".
Ba tare da ya kalli Mancy ba yace da Baban Amira "Sai da Safenku".
Mancy ta masu Sallama suka shige dayar Motar ita da Dalo da Aunty Aseey.
Suka tafi Gidan Uncle Usman, gidan Antisco.

Baban Amira ya gunguro Motarsu ya kawota gaban Asibiti, Alhaji Zaki kuma ya fada Dayar Motar driver ya ja, suna fita daga Asibitin baki daya ya fashe da wani irin Kuka.
Yafi 1hour yana rike kukanshi, yafi 1hour yana son kukaye bakincikinshi, yafi 1hour daya yana son samun salama ta hanyar kuka.
Driver ya dan tsorata yace "Alhaji"
Alhaji ya goge hawayenshi yace "ka hau Machine ka tafi Gidanka" driver ya bi umurni.

Da ya tuna abunda ya ma yaranshi shekaru kusan 4 da suka wuce sai ya  fashe da kuka mai tsuma zucia.
Shafa'atu itace ta rabashi da dukkan wani farincikin shi, sai da yayi kuka son ranshi kamar wani dan k'aramin yaro kafin ya ja Mota don isa gida kafin Dalo taje ta iske baya nan.
*****

Bata da damuwa don ta san aikin da Mallam ya mata ba zai taba karyewa ba, ta yaya ma zai karye?  Don Er Rabi ta yi barazanar fasa wata er k'ok'o sai ta tsorata ta karaya? Haba dai, Aikin da akayi shekara 15 ana yinshi? Ai bata da haufi har yanzu Alhaji Ali na bayan tafin kafarta zata takashi ta murje hannunshi ba tare da komai ya faru ba.
Ita ba komai ya bata haushi ya bata mata rai ba irin yanda Hajia Er Rabi ta tona mata asiri gaban  mutane, yanda Diyarta ta tsareta da tambayar in ita diyar bokace, ita Er Rabi zata ma haka? Aiko zatayi mugun nadama, don wallahi sai tayi maganinta.

Yana isa Gida yaga Motar Shafa'atu.
Lallai matar nan bata da kunya, mai ta dawo yi? Ko kayanta tazo kwashewa?".
Tsayawa yayi a bukka yana jiran Zuwan Dalo, kusan 20 minutes sai ga ta ta iso Driver ya sauketa.
Ta shigo tace "Baba ya baka shiga ciki ba?"
Ya murmusa yace "ke nake jira"
Tace "to mu shiga".
Yace "ina Matar Muhammadu?".
Tace "ta shiga dayan gidanchan kwaso yaranta".
Baba yace "Halimattus Sadiya".
Dalo ta kalleshi da sauri, da wayonta bata zaton ya taba kiranta da sunan nan.
Yace "Baba Mutumin Banza ne ko? Kin tsani Baba ko?"
Da sauri ta rufe mishi baki tace "Baba donAllah kar ka fara, kar ka fara".
Yace "Sadiya, ban kasance Uba nagari a gareku ba, na wofintar daku, na fiffita bare a kanku, na zabi wasu a kanku, na laanceku, na zalunceku, kuyi hakuri, ku yafe ma tsohon banzan nan".
Dalo na kuka tace "Haba Baba, meye haka kakeyi? Wallahi wallahi ban taba tsanarka ba a rayuwata, kai Mahaifinmu ne, mun son kai mai son mune, kar ka bari komai ya tsaya maka a rai, mun san komai da ya faru ba yin kanka bane, asiri gaskia ne, yayi tasiri a kanka, wallahi ko kadan ban rikeka a rai ba ko a da, na dauka hakan kamar fim ne a shafin rayuwata, fim din kuma ya kare, Babana ya fi na kowa kuma ina sonshi fiye da kowa".
Ta ja hannunshi suka shige Gida ba tare da barinshi yayi magana ba.

Suna shiga Gidan suka ga Shafa'atu zaune kan kujera tana karkada k'afa.
Tana ganinsu ta mik'e tsaye.
"Alhaji wani irin iskanci ne zaka dade a waje kuma yanzu ka dauki Sadiya? Uwar me zata mana? Ba ta koma gun uwarta ba".
Wani Mari da ya mata ta rantse taga taurari kusan dari lokaci daya.

Cikin k'unanrai yace "baki da kunya  Shafa'atu, kunya bata isheki ba, har kina iya dawowa Gidana?".
A tsorace da fargaban da zuciyarta bata gama aminta dashi ba tace "ni zaka mara? Nan ba gidan aurena bane? Ina zani!".
Yace "Ke Jahila ce wallahi, to in sai na miki gwari gwari, daga lokacin da Asirinki ya tonu, aure ya kare tsakaninmu, ki fitar min daga Gida".
Aiko da sauri ta fita, ina ta ga ta zama? Ai chan zata nemo hatsabibin boka ya kashe mata Er Rabi, ya mallake mata Alhaji Ali, ba zata dawo gidan nan ba, sai ta mallake Alhaji Ali kaf dinshi".
Bata bi ta kan Annah ba da ke ta kwala mata kira.
Annah ko ta dinga binta kamar Jela.
^****^

Jawad kam tun da ya bar Asibitin bai koma ba, a daren rannan ya yanke ma kanshi hukuncin rabuwa da Labiba.
Aure? Ba zai iya aurenta ba ma, bayan ya san ga wanda take so, ai babu ma maganar aure, ba zai yiwu ace ya aureta amma zuciyarta da ruhinta suna wurin waninsa, gwara ya barta ta auri wanda take so, shima Allah ya hadashi da nashi, Allah ya hada kowa da rabonshi.

A Gidan Er Rabi.

Sam ya shiga dakin Uwargijiyarshi don yaji ta shiru, kwance ya ganta shameshame kan carpet kumfa na fita daga bakinta.
Ga wani magani a hannunta cikin er kwalba da alamu maganin ta sha.
Ajali ne yazo? Kashe kanta tayi? Lokacinta ne yayi? Allahu Aalam, ba wanda ya san mai ya kashe Er Rabi.m
Shi dai Sam ya bude Wardrobe dinta ya dau abunda zai dauka ya cika wa bujenshi iska.


Bayan Barinsu Gidan Alhaji Ali, Gidan k'awarta Hajia Clean suka tafi, ta gaya mata yanda Er Rabi taci amanarta, Hajia Clean tace karki damu, ni ai bana zuwa ma Er Rabi da matsalata, ina da bokana aikinshi kamar yankan wuka ne" donAllah muje ki rakani".
Tace "ki bari gari ya waye, dare yayi fa".
Tace "aa wallahi, da zafizafi ake bugun karfe, so nake na ci uban kowa wallahi".
Tace "kina da kudi?"
Tace "ina dashi a account".
Tace "kwaso su tas, yanda zai miki aiki da kyau".
Tace "Annah ta zauna a nan, zataje ta dawo".
ATM tayi ta zari makudan kudin a bankinta, tas ta kwashe kudin. Ta koma gida Hajia Clean.
Hajia Clean ta dauketa suka hau kauye chan gaba da Ajiwa.
Boka sarkin k'arya har bayan kwana sukayi  wai yana aiki sai wurin karfe 12 na safe ya gama aikin, sai da ya karbe mata kudinta, ya bata wata 'yar hoda yace da ta shafa shi gaban goshin Alhaji Ali Zaki to ko kisa kika ce yayi sai yayi.
Da murna suka koma.
.....
A daren Jiya Alhaji Ali baiyi bacci ba, zuciyarshi zafi take, zai iya rantsewa ya kamu da hawan Jini.
Da farar Safiya aka kawo musu breakfast, Alhaji Ali ya umurci Dalo da tayi wanka zasu fita.
Bayan tayi wanka suka fita hannu rike da juna.
Gidan Mahaifanshi ya fara zuwa.
Da mamaki aka dinga zuwa daki daki aka tada masu bacci aka sanar dasu ga Yaya Ali yazo.
Nan da nan gida ya kaure da Yaya Ali ya dawo garesu, cikin lokaci k'alilan, dangi duk suka zo gidan, don yin barka.
Alhaji Ali ya ba 'yanuwanshi Labarin abunda ya faru.
Su Aunty furera sai da sukayi kukan jin dadi suka dinga tsine ma shafaatu.
"Wallahi Yaya da Police station ka sa aka kulleta, Shedaniya ce, barin irinsu masifa ne".
Yace "Bakomi, Allah zai mana Sakayya".
Ya nemi gafararsu suka ce bai musu komai ha, tunda ba yin kanshi bane.
Ya dade tare da Danginshi, ina zaa saka dashi da dalo akeyi, kowa na son ya burgeshi, nan da nan aka fara cika cooler don zuaa ganin Zaid ya gaya musu Zaid baiji dadi ba, suna ta yabon Zaid don yana zagayowa jefi jefi.
Nan aka sanar dashi Mijin Mariya diyar kanwar Mamarsu ya rasu.
Da mamaki yace "Mariya tayi Aure?"
Shiru sukayi, basu manta wulakancin da ya musu ba da sukaje neman taimako suna so ai mata kayan daki.
"Kai Kai, Allah ya tsine miki Shafaatu, ban yafe miki ba, kin shiga tsakanina da Yanuwana, Allah ya mana sakayya suka amsa da Amin".
Zuwa sukayi suka mata gaisuwa, Goggonshi ta kebe dashi tace "Mariya ta kusa fita takaba, in kana so ka nemeta".
Alhaji Ali yayi saurin kallon Dalo.
Dalo tayi daria tace "Allah Baba ka aureta, ai Aunty Mariya mai kyau ce".
Ya harareta, bai dai ce komai ba.
Goggo tace "Mariya na da hankali, da kuruciyarta, ko shekara 34 bata yi ba, yaruwarka ce, tun da kai ka ki auren zumunci, amma yanzu shi zamu maka, ko ka ki ko ka so".
Yayi daria yace "Ban ma k'i ba ina so".
Tayi daria tace ja'iri.
Bai bar Family house ba sai da aka kawo mus trailer na kayan abinci, ko wani gida sun samu buhu uku uku na shinkafa da kwalayen taliya, jarkan mai, har ta ashanar da zasu kunna sai da aka kawo
*****

Mancy ta iso Asibitin dauke da breakfast wanda Antisco tayi, bayan sun gaisa tace ya masu jiki, Baban Amira yace "ah jiki da sauki".
Ta kallesu tare da murmusawa bacci suke gabaki dayansu".
Tace "Mallam Muhammadu ka tafi gida kayi wanka, zan zauna dasu".
Yace "to ya tafi Mancy ta zauna ta jira har farkawansu".
Suka gaisheta Labiba tace zata shiga toilet Mancy ce ta taimaka mata har toilet, ta dawo da ita, ta basu breakfast, ta ba Zaid na shi ta hada ma Labiba tea ta na bata a baki, kunya duk ta kama Labiba. Zaid kam yaji dadin yanda ya gansu.

Ta isa Gidan maigadi yace ai sun fita, Asibiti ta nufa bata ga kowa ba sai Mancy.
Mancy tsoro ya kamata. Kar ta musu wani abu, waya ta kira Sadiya tace "ina Babanta? Ga Shafaatu nan tazo".
Aiko dalo na gaya ma Baba suka nufo Asibiti a sittin.


#1love
#DM
#anatare
#SonSoFWA
#nagode

Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉

💃🏻AURE 💍

K'ARSHE

Zaid ya kalleta yace "me kike yi a nan?".
Tace "ashe baka mutu ba, naji haushi".
Yace "Ki fita daga dakin nan".
Shafaatu tace "Ubanka nike jira yazo, in yazo sai na tabbatar da ba zaku sake ganinshi a rayuwarku ba".
Mancy tace "Ashe abunda kika min da 'ya'yana bai isheki ba?"
Shafaatu tace "kar ki sake ki dameni, bari zan jira shi a waje".
Mancy ta basu labarin abunda ya faru jiya da daddare sosai sukayi Al ajabi.

Sai ko gasu sun iso da danginshi kusan su 12.
Tana ganinshi ta warwaro Powder din ta nufeshi gadan gadan zata shafa mai a goshi.
Tuni K'anin Alhaji Zaki ya tande mata k'afa ta fadi k'asa, kamar jira suke suka fara dukkanta Mazansu da Matansu, ko wannensu na fanshe bakincikin da suka k'unsa sanadiyarta. Ihu takeyi sosai.

Tuni sun mata Habo baki ya kumbura ido ya kumbura jini ta baki, ita burinta ta shafa mai Powdern nan a ka.
Rirriketa sukayi Alhaji Ali ya tako gabanta yace "Tsakanina dake sai Allah ya isa, ba abunda zance miki, sai tsinuwar Allah su tabbata a kanki, Allah ya saka mana tun a duniya, da ni da yarana ba zamu taba yafe miki ba, Allah ya sa ki wulakanta ki kask'anta anan dunia, Allah ya isa, mai sama mai kowa mai komai zai mana maganinki".

Wani daria ta fashe dashi wanda duk wanda yaji ya san bana lafia bane.
Chan sai taji muryan Mallaminta Baban Annah yace "ba na ce karki hada aikina da nakowa ba? Karshenki yazo".

Kamar an kunna mata battery ta fashe da daria "Hahahah, Alhajina, ni ce fa Matarka Shafaatu, ka manta ka tsani Dan makaho, ka tsine mishi ko zan ji dadi".
Da k'arfi kamar Lasfika ta fara tona ma kanta Asiri.
Nan dangin Alhaji Ali suka sake rufeta da duka kamar dama jira suke, mutane suka zagayesu suna kallo kamar film.
Daga dakin su suna jiyo duk abunda ke faruwa a wajen Amenity.
Ba me ce ma kowa komai, suna mamakin irin aikin sharrin da Shafaatu ta tafka.
Zuwan Alhaji Ahmad Dakata ne ya tsaidasu, yace "haba, ku kyaleta, so kuke ku kasheta? Kar ta mutu a hannunku, ku badata ga Hukuma".

Saketa sukayi, ko zafin da jikinta yakeyi bataji, mikewa tayi ta kakkabe jikinta tace "K'uran ko a jikina , ta musu gwalo".
"Alhajina tsaya in shafeka da hodar nan mana, boka yace "da ya taba goshinka zakayi duk abunda na saka".
Danginshi ka sa jurewa sukayi, wani k'anenshi mai zafin rai ya fincikota ya sata Mota, ya shiga ya Jata ya je ya yasar a wajen Asibitin kamar wata Bola.
Nan ta fara tsince tsince tana tattarawa a rigarta, chan sai ta ji wani shagon saida films na tashi da sautin kida, rawa kawai ta saka mai karfi, hankalin mutane ya dawo kanta, tunbur tayi haihuwar uwanta, wani maigadi ya biyota ta arta a guje, lokaci guda ta fita hayyacinta duk ta haukace ta susuce.
*
Hajia Clean aka gaya ma angs Hajia Shafaatu ba bin bololi a Hanya, Hajia Clean ta tsorata da taje ta gane ma Idanunta, dawowa tayi ta fattataki Annah tace ta fitar mata a Gida.
Annah taje ganin Mamarta a inda Hajia Clean tace ta ganta, tana ganinta ta kasa karasawa saboda warin da Mamarta keyi, Shafa ko na ganin Diyarta ta dinga binta da Gudu, Annah ta zabure ta ruga a guje tana kiran a taimaketa Mahaukacia na binta.
Annah ta samu wani shago ta boye, nan taji wani dan daudu na cewa yana da ikon sa yanmata yin kudi, Annah tace "ya taimaka mata" yace to baki da damuwa zakije ko ina ne? annah tace "ko ma ina ne zani wallahi".
Yace "kar ki damu, ni zan chanza miki rayuwa, zakiyi kudi".
Washegari Annah ta bi dandaudun nan Lagos tafiar Mota ce, dukta wahala.
Wannan shine Silar shigan Annah Dunia.
****

Kwanansu Zaid bakwai a Asibiti sosai suke jin dadin jikinsu, kullum zuwa ganinsu akeyi, har 'yan bencin eskaley sunzo, ana gobe zaayi Sallama Dr Ali ya bukaci a je a ma Zaid Xray a ga status dinshi.
Nurse tazo ta tafi dashi.
Akayi aka dawo dashi sai bayan 4hrs Dr Ali ya bukaci Labiba da Zaid a office dinshi.
**
Dr Ali yace "Zaid, na kiraku ne nan don na gaya muku status dinku duka".
"Labiba you are fit, amma kai Zaid akwai wata 'yar karamar matsala wanda in ka kiyaye to ba wani abu bane, ribs dinka is affected yayi bak'i, in baka bar hayak'i ba it can backfire anytime and you wont be lucky as you are now, amma in dai zaka dinga shan magani, kuma ka daina shan Sigari to lafia lau, and then zaka dinga samun frequent attacks, in dai kana shan magani, komai zai zo da sauki".
Zaid ya murmusa yace "Nagode Babana, na bari wallahi".
Dr Ali yace "Allah Sarki Yasmin, da kina nan da sai kin fi kowa jin dadi Zaid ya bar Hayak'i".
Zaid yayi murmushi mai ciwo yace "Yasmeeen, Allah ya rahamceki, Allah ya biyaki da Aljannah".
Labiba ta amsa da Ameen.
Dr Ali yace "barin je round"
Ya mik'e ya tafi ya barsu.

Labiba tace "kayi Missing dinta ko?".
Ya girgiza kai yace "fiye da tunaninki, nayi missing Yasmin, banda abunda zan biyata da shi, Yasmin ta mutu lokacin da ban taba zato ba, amma na ji mata dadin Shahadarta, Allah ka amshi Shahadar ka sa Yasmin na cikin walwala yanzu".
Labiba ta amsa da "Amin, sai ka mata takwara in mun haihu".
Zaid ya dan kalleta yace "Aure? Aure zamuyi?".
Ta daga mai gira tace "Yesss".
Yace "bakiji yanzu ance zan dinga samun attacks ba? I can die any time in nayi wasa da magani".
Tace "Sai mu jira mutuwarka, sai nayi takaba".
Ya kalleta confidence din na nan, sarcasm din na nan yace "i am serious, nifa ba zanyi aure ba, kar nayi aure na mutu at young age, na bar matata maybe da diyata ko yaro a karamin lokaci".
Labiba ta harareshi tace "aure kam zamuyi".
Yace "ba zan iya ba, zan ha'inceki na aureki yanzu, i am still sick wallahi, aurenki saura wata daya ke da Jawad".

Tace "to ka na nufin na baka Hantata a Banza? Kai tsaya ma kaji, wallahi baka isa ka zauna ba aure ba, ba kuma ka isa ka auri wata ba ni ba, Hantata a jikinka sai ka auri wata banza chan? Chabda, shi kuma Jawad ai he is not stupid, na san wallahi ba zai aureni ba, ya zaayi ya aureni bayan ya san abunda nayi, bayan ya san akwai wanda nikeso?".
Zaid ya kalleta cike da kauna yace "wa kike so?"
Tace "Zaid Ali Zaki nakeso".

Yayi daria yace "In Abbanki zai bani ke ina so".
Tace "Abbana zai baka ni InshaAllah, ehen Mallam, kadai ji ance ka bar shan hayaki ko? Wallahi duk randa na kamaka da ko lighter ne sai mun dawo Asibiti an sake budeka an ciro Hantata an mayar min cikina, ba zan yarda ka kona min Liver ba".

Yayi dariya yace "au Gori zaa min?"
Ta harareshi cike da k'auna tace "an maka goruba ma ba gori ba, kaidai ka kiyaye".
Yace "Yes Ma".
**
Suna fitowa daga Office din suka ci karo da Jawad.
Zaid ya dan kauda kai tare da yin gaba.
Jawad ya rik'o shi tare da cewa "Masoya, soyyayan har a office din doctor?" Ba wanda ya iya cewa komai.
Yace "Ya jikinka Brother?".
Zaid yace "Na ji sauk'i Alhamdulilah"
Jawad yace "Thanks to Labiba ko?".
Zaid yayi shiru kafin yace "Yes, thanks to Labiba kam, kar ka damu i know shes your wife to be".
Jawad yayi murmushi yace "Nooo, You can have her".
Sukayi saurin kallonshi ya gyada "kai yace kai take so, ko ba shi kike so ba ni kike so?".
Da sauri ta gyada kai "aa shi nakee so". Yayi daria yace "Allah ya barku tare, in an dauko maganar zan gaya musu na bar maka ita".
Zaid zai yi magana Jawad yayi gaba abunshi.
%%%%

A tare aka sallamesu.
Alhaji Dakata ya tattara Iyalanshi suka tafi Masaukin da Alhaji Ali ya basu.
Alhaji Ali ya kalli Dalo yace "zamuje gidan ne?".
Sadiya tace "Baba lets go on a date, ni da kai da Yaya Zaid".
Baba yayi daria yace "Ni Masoyinku ne da zaku date dani?".
Dalo tace "sosaii Ma".
Baba ya kalli Zaid yace "Muje?".
Murmushi yayi yace "Muje Baba".
Alhaji Abu yayi murmushi tare da mik'a ma Alhaji Ali hannu yace "to Alhaji a sha Soyayya da 'ya'ya lafia, mu bari mu isa gidan Hajia".
Yak'e kawai yayi tare da gyada kai.
Mancy ta ma yaranta byebye ta shige motar Mijinta, Jawad ya rufa musu baya.

Alhaji Ali yaga Mancy ta shige Motar Mijinta sosai ranshi ya sosu, ya kamata ya cireta a ranshi, ya san cewa ta mishi nisa, don yana da tabbacin ba zata rabu da Mijinta ba don ta dawo gunshi, abu ne da ba zai taba yiwuwa ba, ya san ta wuce mai nesa ba kusa ba, dole ya cireta a ranshi, ya zama dole ya hakura da ita
**^^**

Dakin ya zamana daga Labiba sai Maminta da Abbanta, tunda suka zo sai yau suka kebe.
Labiba cike da kunyansu tace "wallahi na san ban kyauta ba, wallahi Mami nasan na tada nuku hankali ranku bace yake".
Mami tace "Labiba baki da hankali, baki san ciwon kanki ba, ance miki So Hauka ne? Wani irin rashin tunani ne haka, namiji kike ma wannan zazzafan So? Baki san Namiji ba dan goyo bane".

Abba yace "Amina, godiar da zakiyi ma Allah kenan?"
Tace "dole fa a mata fada, bata kyauta ba, wani irin abune wannan? Yarimya ta task tundaga Edo State, tazo wai Katsina gun saurayi? Haba wannan rayuwa da mai tayi kama".
In akwai abunda Labiba bata so to fushin Iyayenta, nan tashiga basu hakuri tana kuka.
Tsakanin da da mahaifi sai Allah, nan suka yafe mata tare da mata fada sosai.
@@@

Zama sukayi a k'ayattacen wurin cin abinci, kowa ya fada abunda zai ci, a ka kawo musu, sai da suka gama ci kafin Baba yace "Zaid, ni fa kunyarka nikeji, ban san ta ina zan fara ba".
Zaid ya murza idonshi yace "Baba kunyan me fa?".
Baba yace "Zaid, ban kasance uba nagari wanda zakuyi alfahari dashi ba".
Zaid yace "Nagane inda ka dosa Baba, ba zan yarda ka nemi gafara na ba, ni wanene da zaka roki gafara na".
Baba yace "Zaid, na zalunceka, da bakina na laanceka, nine silar fadawan ka shayeshaye, na maka Illah".
Zaid yace "ba a hayyacinka ba, na san Babana na sona, a hayyacinshi ba zai taba furta min mummunar kalma ba, ban manta ba a da kana fada da duk wanda ya kirani da sunan DanMakaho, a cewarka sunan Banza ne, ta yaya zaka furta wani zagi da bakinka? Baba wallahi ko a da na san cewa ba yin kanka bane, shiyasa ban taba rikeka a raina ba".
Dalo tace "Baba nagaya ma tun ranar, wallahi muna sonka fiye da duk wani Namiji a duniyar nan, kar ka roke mu komai, mu zamu rokeka yafiya in bamu kasance 'ya'ya nagari ba".
Baba yace "Haram wallahi, kune ko 'ya'ya nagari, ina sonku fiye da komai wallahi, ku yi hakuri na kawo wacce ta rusa mana farinciki, ba zan taba yafe ma Shafaatu ba, gashi tun a dunia ta fara ganin sakamakonta, ina da Labarin ta haukace an kamata an tafi da ita Asibitin Mahaukata.
Tabe baki sukayi irin ko a jikinsu.
Yace "donAllah ku rokar min Mamarku gafara, ta yafe min".
Dalo tace "Allah Baba bakomai, kowa fa ya san duk abunda kayi ba yin kanka bane".
Yace "nidai please ku ce ta yafe min".
Zaid yace "InshaAllah Baba".
Baba yace "Zaid ka tuna Aunty Mariya?"
Zaid yace "Eh Baba, Mijinta ma ya rasu".
Baba yace "ka sani ohh nine dai bansani ba".
Zaid yace "me ya sameta".
Baba yace "wai Goggo wai na aureta".
Daria suka sa gabaki daya Zaid yace "to Baba ayi mana, ai dama ba zai yiwu ka zauna haka ba ba mata".
Baba yace "kun Amince?".
Sukace "dari bisa dari".
Yace "Allah ya muku Albarka ya sa ku gama da dunia Lafia".
Suka amsa da Amin.

Baba yace "Zaid Credentials dinka na nan, Alhamdulilah ban salwantar da su ba, Masters dinka kana da shaawar komawa London kayi ta?".
Zaid yace "Aa baba, barni in huta for now".
Baba yace "to shikenan, da degree dinka ai zan samo maka aiki mai".
Zaid ya yi alwashin tashi ya tsaya da k'afarshi yace "Baba, zan gabatar maka da abunda nike so nan ba da dadewa ba".
Ya kalli Dalo yace "ke kuma fa? Karatu ko Aure".
Dalo tace "Lahh Baba aure fa kace? Chab nawa nike ni? Ni gaskia Baba ka bari".
Baba yace "amma na fa ce ko karatu, bance aure zan miki ba, why are you focused on the last option?".
Zaid yace "because its what she wants, Aure take so Baba".
Baba yace "Exactly".
Dalo ta turbune fuska wai zatayi kuka.
Baba yace "wallahi Zaid ba zan kyaleka ba ka sa min yarinya kuka".
Sukayi daria, tare suka kasance aranar gabaki daya kafin suka koma gida Gab da Maghrib.

A na Gobe 'yan Edo da 'yan Abuja zasu koma garinsu suka hadu a wakeken Parlorn Alhaji Abu Shamsu dake nan garin Katsina.
Alhaji Abu Shamsu ya bude taro da addua.
Yace "To abubuwa da yawa sun faru, wanda duk abunda ya faru yana daga cikin pegin layin k'addararmu, dubararmu ba zata iya hanata faruwa ba.
"Alhamdulilah Allah mungode maka, Allah ka sa duk mu ci wannan jarabawar, Allah kanyafe mana duk mu yafi Juna, kuma wannan zumuncin Allah ya riga ya hada babu mai rabawa".

Alhaji Ahmad Dakata "ya dora nashi jawabin yana kuma mai bada hakuri, tare da cewa Jawad yayi hakuri da Labiba, don kamar ya kwareshi ne in ya bashi Labiba, Labiba zata cigaba da Makaranta har Allah ya kawo mata wani Mijin".

Alhaji Abu yace "wani Miji? Ai Allah ya kawo mata tuni da dadewa".
Sun san inda ya dosa Alhaji dakata yace "anya amma Jawad Adalci in aka ba Zaid Labiba?".
Alhaji Abu yace "yo saboda me? Da Zaid da Jawad duk 'ya'yana ne, ko ni ba zan aura ma Labiba kowa ba sai Zaid, Sadakinta na hannunka ka manta wanchan mancewa nayi da naje Edo, so nayi nace nazo neman auren ma Zaid Aure na ce Jawad subutan baki ne".

Alhaji Ali Zaki yace "wai ya ake ta min passing passing da diya ne? In ba ku so ku bar min ita, na kaita madina tayi karatu ta kawo min balarabe, ha'an".

Sukayi daria Alhaji Abu yace "Allah baka hakuri su masu diya".
Alhaji Dakata yace "ni dai koms meye sai naji daga bakin Jawad, in har be amince ba, wallahi sai dai ciwon so ya kashe Labee, sai dai ta auri wani ba Zaid ba".
Jawad yace "Abba wallahi bakomai, na bar mishi ita, na yarda, Zaid ai danUwana ne, Allah ya kara musu Son So"..

Alhaji Abu yace "Fak'at, Hajiyoyi me zaku ce?".
Mancy tace "ai kun dai gama Magana, in aka raba Zaid da Labiba ai Nigeria ta mana kadan, don wallahi guduwa zasuyi".
Mami tace "in dai ba so kuke kunmata wani auren ba, Zaid ya zo yana bukatan dashin Zuciya Labee ta kaso aurenta ta je ta bashi ba to wallahi tun wuri ku aura mata shi, tunda dai ta ji tagani 'yar kutsun uwa.
A kayi daria yace "Na bawa Zaid Labiba".
Alhaji Abu yayi daria yace "na amsarwa Zaid Labiba".
Duk sukayi Hamdala.
Zaid ya saukar da kanshi yana ma Labiba Signal tare da kashe mata kannenen idonshi, ita ko bata ma kalleshi ba balle ta tankashi.
%%%

Da Yamma Aisha tazo wurinta ranta bace tace "wai ke yanzu Besty shikenan ba zaki auri danuwana ba?"
Labiba tace "danuwanki fa yace baya sona, ba zaiyi ba wai".
Harararta tayi tace "kafin yace baya so ai ke kikace ba kya so".
Labiba tayi murmushi tace "Allah zai ma Jawad zabi nagari, nidai ya min".
Aisha tace "dan Shaye shayen?".
Dif Labiba ta dauke wuta tace "kar ki sake bana so Aisha".
Bata taba ganin baci ran Labiba ba sai yau hakan ya sa Aisha wayancewa.
"Yi hakuri, yanzu Abu Sadik ai dole ya hakura da ke".
Labiba tace "bawan Allah".
Aisha tace "yanzu wai har da ke zaaa tafi Edo? Makarantar fa?".
A takaice tace "Abba ya cireni".
^^^^
Alhamis Aunty Mariya ta fita takaba, Jumaah aka daura mata Aure da Alhaji Ali Zaki.
Bayan anyi gyare gyare a Gidan ta tare tare da 'ya'yanta biyu wanda Alhaji Zaki ya bukaci ya rikesu.
Zaid da Dalo sun tafi Kano gidan Yayan Mancy Daga chan suka nufa Abuja.

B A Y A N 'yan kwanaki.
E D O
Labiba ta kira Aunty Bilkisu Matar da taimaketa a hanyar Katsina.
Bayan sun gaisa tace mata "Labiba ce".
Aunty tace "Allah Sarki Labiba, ya kike ya jikin Dan Makaho?".
Tace "Aunty baki manta ba?".
Tace "ina Zan manta beebs? Ai dan Makaho ya tsaya min a rai, tausayinshi nakeji".
Labiba tayi daria tace "Aunty wallahi jikinshi ya warke sosai, next month aurenmu".
Aunty tace "ke haba bari donAllah".
Labiba tace "wallahi kam".
Sosai Aunty Bilki ta tayasu murna ta musu fatan Alheri.
Tace "baya da raayin Civil Defense dinne?".
Labiba tace "kinga ko gaya mishi ma banyi ba".
Tace "to InshaAllah, in yana so ki bashi Email address dina yanzu zan turo miki, kice ya turo CV dinshi da address din".
Labiba tace "yanzu kuwa zan Aunty, zan sake kira, gaida min da kannena".
Aunty Bilki tace "zasuji inshaAllah".

Numbershi ta latso.
Dauka yayi full of energy yace "Yes bee to the beebs bae to be".
Daria tayi da jin iyarshegenshi.
"Wai Masoyin kana son aikin Force?".
Yace "Soldier?"
Tace "Nope Civil Defense".
Yace "Sosaiii ma, zaki samo min ne?".
Ya tambayeta cikin wasa.
Tace "eh in kana so".
Cike da zolaya yace "ina so Comptroller Labiba Ahmad Dakata".
Tace "Send your CV to the email address din da zan turo maka yanzu".
Yaji she sounds serious yace "babe are you serious ?"
Tace "stop asking too much, just send the cv, zan kiraka anjima i love you".
Kita ta kashe wayar, ko 30seconds baayi ba ta tura mishi email adress din, da mamakin Labiba ya tura Cv dinshi ma address din.

Aunty Bilki ta kirata, Labiba na dauka tace "Zaid Aliyu Zaki? Age 27".
Labiba tace "wai har ya turo?".
Aunty tace "eh wallahi, ina son masu zafin nama, inshaAllah zanyi kokari naga ya samu, inshaAllah".
Labiba tayi ta zabga godia tare da sa mata Albarka.


K A T S I N A

'Y A N B E N C I N E S K A L E Y.

Su 4 Zaid ya ma jagoranci har Parlon Baban.
Cike da Ladabi da biyyaya suka gaida Alhaji Ali Zaki tare da zama kasan Carpet.
Alhaji Ali yace "duk ku gaya min A ina karatunku ya tsaya".
Eskaley yace "ni ban taba zaman Aji ba".
Terro yace "Ni tun Primary ban cigaba ba".
Haruna yace "ni ina da Diploma".
Master yace "ni ina da Secondary School Certificate.

Alhaji Ali yace "Alhamdulilah,
ina so kuje kuyi tunani ku dawo ku gaya min burinku, wani sanaa kuke so ku fara? Zan baku jari".

Dadi ya mamayesu.
Master yace "ai Baba a nan zamu gaya ma, ba wani tunani".
Yace "ina jinku".
Yace "nidai Baba shago nike so a bude min a sa ka min lemuka da yogurt a sawo min blender da generato, a saka min freezer , zan dinga dama fura da yogurt ina saidawa, a sama ko a buga min tambarin Master Fura da Nono and juices".
Daria suka sa, Baba yace "an yi an gama".
"Kai fa Eskaley?"
Yace "Baba ni dai so nake a fadada min Kiosk ina a cika min Shago a habaka min shi, duk unguwan nan nikadai ke da shago".
Baba yace "ba kiosk ba, wannan shagon gefenka Empty naji ance ana neman me siya, zan kama maka in cika maka shago da provisions kayi ta saidawa".

Terror yace "ni dama Baba chan da na iya irin Takalma da Jakka Handmade, ina so a bani jari da shago na dinga yi".
Yace "to naji"

Kai kuma Haruna me kake so?
Haruna yace "Baba ina da diploma na, ina so na koma Makaranta na hado Degree dinnan, sai na dinga bussiness".
Baba yace "bussiness din me?".
Haruna yace "ko Shadda haka".

Yace "to naji, dukkanku zan baku naira dubu dari biyar, miliyan biyu kenan."

Ina Aljannah su sakashi, godia kawai suke kwasa, suna sanya mishi Albarka, "suna cewa sai Baba, mungode, Allah ya kare mana kai, ya sa ka fi haka, Allah ya maka Gwamnan Katsina, Allah ya kareka daga sharrin Mahassada".
Baba yace "To Amin nagode, amma fa da sharadi".
Suka natsu yace "ba cash zan baku ba, Idrisu zan sa duk ya siyo muku abubuwan da kuka lissafo da kudinku, don kar ku kashe su a banza".
Suka ce "mun yarda wallahi, mun fi so dama a siyo mana komai".
Yace "kuma duk wanda na sake naji ko na gani yana shaye shaye, to zan amshe abuna".
Haruna yace "nidai Baba na bar World na bar Sigari, dama wallahi rashin abun yi ne ya sa nake sha, amma yanzu haram".

Master yace "ni tun da naga Mankas kwance ya kusa warewa nace na bari don kar na baro ma kaina aiki uwayena basu da kudin biya a man aiki, Allah nidai na bari".

Terror yayi shiru, don ya san karya ne yace zai bar shan sigari lokaci guda, ya riga ya zame mishi jiki yace "nidai baba kar na ma karya, InshaAllah ba zaka ji ko ka gani ba, amma dai ka sani a addua, zan bari"
Baba yace "Allah ya sa, nidai na gaya muku, randa na ganku ko naji labari, zan amshe abuna ne, kaifa Eskaley ance kai ke sayar da world din yace "Wallahi Baba na bari".

Yace "kaifa Mallam Zaid?".
Zaid ya murmusa, Soyayyar Mahaifinshi na tsaga bargonshi da jinin jikinshi ya murmusa yace "Baba ni ai na bari, Labiba tace in ta kamani ina shan sigari wai zata sa a budeni a ciro mata hantarta
A maida mata cikinta wai ba zan kone mata hanta ba".
Sukayi daria ga baki daya yace "Diyata ta min daidai, to ku tashi ku tafi Allah ya muku Albarka".
Nan suka dinga shi mishi Albarka suna Gode mishi.
Cikin kwana biyu ya cika musu Alkawarin da ya daukar musu.

Kamar Shekarun Baya, haka aka dawo, ko wani Gida a Tudun Matawalle akwai kwanon Abincinsu a Gidan Alhaji Zaki, amaryarshi bata da kyashu bare hassada, duk wani mai neman taimako gidan yake zuwa, ya taimaki Danginshi, ya taimaki Na waje, kowa na yabawa da Alhaji Ali Zaki.

A B U J A

Jawad ya shigo Parlorn ya iske Mancy da Umma sai Abdulmajeed, Mimi na bacci.
"Jawad yadai?"
Yace "Mancy wai Sadyy har yanzu bata dawo ba?"
Ta kalleshi tace "Jawad Chan zata kwana".
Ya zaro Ido "don me zata kwanar musu a gida kamar basu da gida, nidai ta dawo".
Mancy tace "kamar dai wani gida taje? Gidan Abdulhafiz ne fa, matarshi take tayawa aiki ka sam tayi nauyi, ya gaji ne ba zai iya dawowa da ita ba yace sai gobe".
Jawad yace "yo ita 'yar aiki ce da zaa dinga daukarta tana tayin aiki? Nidai barinje in daukota gaskia".
Mancy tace "kayi hakuri Jawad gobe zai dawo da ita".
Jawad yayi dan guntun tsaki ya latso wayar baban yayanshi yace "Hello Yaya, ga Abba nan na ta fada wai ka dauke mishi diya, yace gobe da sassafe ka maido mishi diyarshi kar ya bata maka rai".
Jin muryan Abba sukayi a baya yace "karya ake mun, ni da bansan ma anyi ba?".
Umma tace "Wai Jawad, Wai Abbanku zai maida Dalo Katsina gun Babanta".
Gaban Jawad ya fadi ya zaro ido yace "Abba wai dagaske? Meyasa? DonAllah kayi hakuri, ba Babanta yace ya bar maka ita aure ya rabaku?".
Abba shima ya biye yace "ai Auren zan mata a Katsina".
Ya zaro ido sosai, sai chan yaga suna dariya, sai ya gane ashe zolayarshi suke
Jawad ya bubbuga k'afa cike da shagwaba
Su Mancy suka sa daria baki daya.
Abdulmajeed yace "ana so ana kaiwa kasuwa"
Ya murguda baki yace "ina ruwanka?".
Abdulmajeed yace "ko kayi making move, ko ma hadeta da Aisha nayi Mata biyu rana daya".
Jawad yayi hanyar kofa yace "in ka fasa".
Dariarshi sukeyi sosai Abdulmajeed yace "Mancy Your Boy is In love".
Mancy tace "ai na lura da kanwar taka itama ta na yinshi"
Alhaji Abu ya kalli Iyalanshi cikin dadi yace "Alhamdulilah"..

Washegari Yaya Abdulhafeez ya dawo da Dalo da safe don daga gidansu zai wuce aiki.
Suna kan table suna breakfast.
Sukayi Sallama tare da gaisar dasu.
Abba yace "Yadai? Wannan sammako haka? Kamar ana tsiranku".
Abdulhafiz yace "Abba ance kana ta fada, shiyasa nace in zan wuce aiki zan maidota".
Jawad ya dinga ma Abba Signal da yace eh don in ya gane karya ne zai bata mai rai.
Abba yace "yo eh, sai a dauke man 'Yar yainyata haka akeyi?".
Dalo dai tayi ta daria.
Umma tace "kuzo kuyi breakfast".
Dalo tace "wallahi a koshe muke".
Mancy tace "zo ki kwashe wanda aka ci".
Tace to Ta zo tana hada plates din da aka bata iya daukanta ta nufa kitchen.
Kamar an tsunkureshi ya mik'e yana hada cups yace "dama kitchen din zanje".
Ba wanda yace komai Illah murmushin da suke ta zabgawa.

A Kitchen ya isketa tazo wucewa ya rufe mata hanya.
"Sadyy kikaje gidan Yaya kikayi zamanki ko, kin sa zuciana wahala, yana ta missing dinki".
Bude idanuwanta tayi alamun hakuri tace "i am sorry, zuciyar ta daina Zafi, maganin tazo".
Yace "ni dai kar ki yarda ki sake nisa dani, jiya su Ya Majeed har da zolayana suke".
Shagwaba yake ta zuba mata shi ala dole dan auta.
"Ina ruwansu da kai da zasu zolayeka? Ka rabu da su, zanyi maganinsu".
Yace "Ina Sonki kinji?".
Murmushi tayi ta sadda kai k'asa tana daria.
Yace "wallahi sai kin fada yau, kullun in ta fada ba kya fada?"
Hannu ta sa duka biyu ta kulle fuskanta.
Ya sa cokalin hannunshi ya k'wankwashe mata hannu budewanta yayi daidai da futar "Ina Sonka nima".
Lumshe ido yayi yace "Princess"
Lumshe ido tayi tace "Prince".
"Umma, Mancyy wallahi ga su nan suna soyewa a Kitchen".
Umma tace "Me suke soyawa kuma?".
Mancy dai daria take kasa kasa
Dalo kamar ta shige k'asa saboda kunya.

Alhaji Abu yace "to abu yayi kyau, barin gaya ma Alhaji Ali, in zaa iya hade bikinsu Zaid wallah duk aurar da ku nake in huta"
Da gudu Dalo ta shige Daki.

Alhaji Abu ya kira Alhaji Ali, a handsfree aka saka wayar bayan sun gaisa Alhaji Abu yace "wai wasu sabbin tsuntsayen soyayya muka samo, nace ko dai mu aurar dasu mu bige aiki?".
Daria Alhaji Ali yayi yace "Wa da wa?".
Alhaji Abu yace "Diyata da Jawad"
Cike da jin dadi Alhaji Ali yace "Sosaiii ma, ai kawai a buge aiki".
To sai ka gaya ma su Labaran cewa Su uncle Usman dinsu zasu zo neman aure da saka ranar ran jumaa"
Alhaji Ali yace an gama.

Haka ko akayi, a karshen satin aka kai kudin neman aure, da sa rana Family house dinsu Alhaji Ali zaki.
Shirin Biki ake tayi gadan gadan.
Kullum sai Umma da Mancy sun shiga kitchen.
Alhaji Ali ya turo 2mil wai a ma Dalo kayan daki.
Alhaji Abu ya kirashi yana fada "diyarka ce da zaka turo kudin kayan daki?".
Alhaji Ali yace "Allah Nagode, diyarka ce, wai da gudummuwa ce na turo, amma in ba a so a maido min abuna".
Alhaji Abu yace "baka isa ba, wanda yace ka turo".
Sukayi daria.

A Gidan Yaya Abdulhafeez, Flat ne Uku 3 bedrooms each, Abba ya gina ma 'yaranshi gida tun kafin Abdulhafiz din yayi aure, nan zasu zauna duka.
Sai ya kira Zaid a waya yace "to Ni dai bansan inda kake son zama ba, zaka zauna a Abuja in samo maka aiki ka hadu da yanuwanka?".
Zaid yace "Abba, nidai Katsina nake so, nan nake son Zama, aiki kuma akwai abunda nike jira".
Abba yace "to ba laifi, ka nemo gidan da ya maka, ni zan siya".
Zaid yace "Abba Baba ya bani Gida a Goruba road".
Abba yace "shifa Baban naku karambani, wa ya aikeshi baka Gida? To dama abunda na yi ma su Jawad nike son yi maka, to amma tunda an rigani, zan siya maka Mota kai da Matarka, sannan na samaka chanji a account".
Cike da jin dadi Zaid yayi ta zuba godia.

Alhaji Ahmad Dakata ya ma Labiba da Samira kayan daki, duk abunda aka siya ma Samira an siya ma Labiba, komai iri daya ne.
Zaid yace "ba sai sunyi komai ba, Baba ya gyara gidan".
Tace "ai da bakuyi wahala ba, nan ma anyi komai".
Yace "kuma sai anyi wahalar daukosu daga Edo?ai kawai a barsu"
Hayyakoewa tayi Labiba tace "a yi yaya dasu? wallahi, sai an sa min kayan da Abbana ya min".
Ganin rigima take neman tada mishi yace "to Baby, ba abun fada bane, sauki nake nema".
Tace "to angode amma sai an kawo".
Yace "Allah ya kawo lafia".
Ita fa zuciyarta a wuya yake, kowa ya tashi zai ce "wallahi ki rage son Zaid, wata rana zai miki wulakanci, namiji butulu ne, da ka nuna mishi So, wulakanci ke biyo baya"
Da sun fara maganar nan tashi takeyi ta barsu sai suce ba ta son gaskia..

Yan Bencin Eskaley suka hado mishi gudumuwar naira Dubu dari 25k suka hada each.
Da farko yace "ba zai ansa ba".
Master yace "kai yaro ka amsa wallah mun fika kudi don business mukeyi kai ko mai baka saidawa".
Daria Zaid yayi yace "Yan dunia, ku zo musha World don murna".
Master yace "uwar World zami sha, kana so Baba ya anshe tallafi ne ne"
Daria yayi ya musu godia.
Suka ce ka kaimu Gidan Nene.
Yace "wallahi Nene damuwa ce".
Suka mishi magiya ya rakasu.
Ashe leda sukayo mata.
Sai da sukayi drama a gidan Nene tace wallahi ka bar ganin zakayi aure, sai na saka daki karfe ukun dare na ci ubanka dariya suka saka.

B I K I  B U D U R I

Katsina Duk suka gangado.
Ba tare da yin wata bidiah ba
Ran Asabar din Satin aka daura Auren AbdulMajeed Abu Shamsu da Amaryarsa Aisha Usman
Da kuma Jawad Abu Shamsu da Amarayarsa Halimatu Aliyu Zaki a sadaki naira dubu hamsin.
Da Aishar da Sadiyar duk Abuja a ka kaisu gidajensu.
Sati na sama suka garzaya Edo don daurin Auren Labiba.
Duk da ance ma dangi yan katsina an hutarshe da su ba sai sunje ba duk wahala ce amma Edo ta kwashi mutanen Katsina da yawa.
Bayan an daura auren Aminu Shehu da amaryarsa Samira Ahmad Dakata aka daura auren Zaid Ali Zaki da Amaryarsa Labiba Ahmad Dakata da Sadaki naira dubu hamsin.
Text ya mata _Burina ya Cika, Alkawarin Allah ya cika, ina tayaki murna Mrs Zaid Zaki, ina tayaki murnan zama matata_".
Murmushi kawai tayi kafin ta yi sujudul shukur, wai yau itace ta amsa sunar Matar Zaid? Allah mai iko.
A ranar Hajia Bilki ta kirata tana neman afuwa bata zo bikinta ba. Labiba tace "haba Anty ai ba komai, babu ma abunda akayi sai Wedding Fatiha".
Tace "to Albishirinki, consider this as my Wedding Gift, Anyi recruitment, Zaid ya samu One Star 🌟".
"Allahu Akbar Allahu Akbar, nagode Aunty Allah ya biyaki da Aljannah".
Tace "Ameen, Allah ya bada saa, in kun gama Amarcinku nan da 3months zaije training".
Dadi kamar ya kashe Labiba, kasa hakuri tayi sai da ta kirashi ta bashi good news.
Duk da mutane sun mishi yawa sai da ya matsa gefe ya nuna murnarshi yace "wai ke ina kika samu hanyar CD?".
Tace "wallahi wata baiwar Allah ce take sonmu take son taimaka mana".
Yace "Alhamdulilah, Allah ya biya baiwar Allahn nan da Aljannah".
Ta amsa da amin
Yace "zan kiraki, muna pictures da mutane, ina sonki kuma".
Kit ya kashe wayar".

A ranar aka dauki Samira aka kaita gidanta da ke Birnin Edo, washegari kuma aka tafi da Labiba zuwa Abuja daga Abuja aka dauketa a Jirgi zuwa Kano, daga Kano suka iso Katsina duk a gajiye ba a tsaya da ita ba ko ina sai gidanta.

S O Y A Y Y A R U W A N Z U M A

Tana zaune a bakin gado, shi kuma yana daga ƙasa akan rug mai laushin gaske.
Hannunsa na kan cinyarta. Wani karamin kurji ya fito masa wajen gemunsa, a hankali take kokarin fasa mashi kurjin, ba abunda yakeyi sai shagwaba da lalaci a dole zafi yake ji.

"Wasshhh" ya sake fadi a karo na kusan goma. Amma wannan karan harda tura baki sosai tareda jan kansa baya. Kallonsa tayi tareda sakin masa murmushinta wanda ke kawatar mata da fuska.

"Haba Mijin, ka tsaya na gani mana, Haba Masoyi." Ta karasa maganar tareda tallabo mashi fuska.

"Ni gaskiya banaso"

"Just this once, I promise." saita daga hannu daya sama alamar ta rantse. Langwabe kai yayi ya tsaya.. kafin ya kafeta da kannannen idanuwanshi,
Wai yau gashi ga Labiba a matsayin ma'aurata.
Kallonshi tayi ta ga yana kallonta.

"MIJIN" tace cikin muryan da bai wuce raɗa ba. Bai amsa ba saboda hankalinsa baya kanta. "BABE" ta sake kiranshi, amma bai motsa ba, bakinta ta hura mashi iska kadan a wajen fukansa wanda yayi zumbur ya dawo hayacinsa.

"A penny for your thought," tace tana murmushi. Riko hannunta biyu yayi ya daura kan fuskarshi, ya shafa kumatunshi da hannunta sannan ya sumbacesu su biyu. Idan da sabo yaci ace ta saba da irin kallon da Zaid ke mata, kokuma wani abin dayake mata na nuna so da kauna. Amma kullum kamar sabon shafi ake budewa.

Kullum sanshi yana daɗa ƙaruwa daga ɓargonta har duka ilahirin jikinta. Kowane Sonsa na gaɓoɓinta yana amsa irin soyayyar da Zaid yakeyi mata.

Janyonta yayi ƙasa zuwa inda yake zaune, ya tallabo fuskarta Ya hada idanuwansu. Baice komai ba bayan kallon kallon da sukeyi. Duk jikinta yayi sanyi, Zaid yanada wani kwarjini wanda bata taba ganiba. A murya ƙasa ƙasa yayi magana.

"Ki daga fuskan ki." bata kula ba illa murmushi. Wai yau itace take kunyansa sosai. Tama rasa ganewa da gaske ta kasa kallonsa ne ko tsabaragen iya shege ne. Ta tuna irin liver dinta lokacin datake zuwa dakinsa, amma yau gashi a matsayin mijinta amma tayi bala'in laushi.

"Ki daga please, badan halina ba sai dan soyayyar danake maki."

Bin umurninsa tayi ta kalleshi.

"What are you doing to me beebsss?" yaja sunar sosai chan cikin makoshinsa. Kai zaka zata shiya rada mata shi. Ita kanta a lokacin tasan cewa tunda tazo duniya babu wanda ya taba kiran sunan haka, Yafi zama akan bakinsa kamar danshi aka halicce ta.
_Dan shi mana aka halicce ta, she's surviving for him. Rashin sa zai zame mata barazana a rayuwarta_ ta tuna.

Magrib aka soma kira, ba ita kadai ba harshi yana bukatar hutu sun sha jigilar hanya, a gajiye suke, ba abunda zasu iya yi, yau hutu kawai zasuyi.
Labiba ta zame mashi tamkar world wanda he is addicted to a da. Duk yanda yake muradin shan World ko wani Sigari duk yanda yake san sha ko kadan, input dinta duk yafi mashi zugi. Har tsoro yake ji saboda soyayyar ta yayi mashi babban kamu.
Idan yaje sallan magrib zama yakeyi a masjid yana tilawa har a kira isha. Text ya tura mata kafin ya dawo.

We were once on separate paths
We knew nothing of each others existence
I agonise by the thought of that
Indeed they were my darkest time
Fast forward to the present
You have become part of me
Like my very own DNA....

Bata karasa karantawa ba ta lumshe ido sai murmushi takeyi. Kalaman Zaid yana dama mata lissafi sosai. Tana kan sallaya sanda ya dawo. Dakin yana kamshin turaren wuta wanda ke ci daga burner a chan kurya gefen socket. Sannan ga AC an kunna madaicin. Dole duk fushinka da gajiya idan ka shiga zakiji ka soma sauka. Gata itama fuskanta yana glowing, yasan ba komai bane illa yawan alwala daya haskaka mata shi. Idon ta a rufe yake, amma zakaga karamin murmushi yana tashi daga kasan leɓanta. Shima kwanciya yayi gefenta ya sakalo mata hannu yayi wrapping dinta sosai.
Sunfi minti kusan biyar a haka. Saiya juya da ita ya kwantar da kansa akan kirjinta, bata hana shi ba illa matse ido tana murmushi. Shima rufe idon yayi numafshin sa yana hawa da sauka. Hannunta ya saka hannunsa saiya harde biyu.

A zuciyarshi yana son Labiba.
Labiba Alheri ce, itace Alherinshi, Cikin ransa baya komai illa gode mata yanda take sonshi, yanda ta tsaya tareda shi a lokacin da yake ba kowa ba, a lokacin da bai da wani gata ko galihu, yanda ko sau daya batayi judging din mugayen ɗabi'unsa ba. Yanda koda yayi mata wani abin take tausasa zuciyar ta ta kuma yafe mashi.
Lokacin da yake dizgata amma bata hakura ba, yanda ta take maganar kowa don ta kasance tare dashi, bata guje shi ba.

Yasan ba zai taba biyanta ba, Babu wani abin duniya dazai fanshe abinda tayi, saidai zaiyi amfani da karfinsa yayi kokarin ya kawo mata duk wani jin dadin rayuwa..
Ta mashi halarci sosai, ba zai taba taking dinta for granted, shi ba butulu bane, zai gwada mata Namiji dan Goyo ne.
Duk da ba zai biyata ba, amma alkawari ne, tana cikin adduarshi a kowacce sujaddarshi .Addu'a ya ke binta dashi da fatan zata gama da duniya lafiya.

"I love you Babe," ya fada a bayanne.

"I love you more Sugar," ta fada itama.

"Ina Sonki Matar".

"Ina Sonka Mijin".

"Ina Sonki Sosai".
Tayi daria tace "Sosai nake Sonka".
"I love you baby" tun tana amsawa har ya ji ta shiru.
Haka yayita nanatawa wanda saida dukan ilahirin jikinsa ya gasgata abinda ke fita daga bakinsa. Komai na jikinsa ya aminta da soyayyar ta. Daga kansa yayi ya kalleta yanda take barci cikin natsuwa, wai har tayi bacci, gajiya ce ba komai ba.
Wani hawaye ya ziraro masa daga idanu.
Bai share ba ya barshi yana zuba.
Tausayinta ya kamashi.
Allah kar ka bashi ikon zaluntarta, Allah ka bashi ikon biyan Soyayyarta da k'auna.

He needs her now more than ever, itace battery din rayuwar sa. Kamar yadda waya ba zatayi aiki idan babu battery ba, shima haka yake ji da ita. A hankali ya tashi ya sumbaci goshinta, daga nan sai kumatun ta, sannan ya daura akan bakinta. Bayan nan ya daga ido ya kare mata kallo saiya daura kansa kuma akan kirjinta.

Bazai taba gajiya da sauraran yanda Zuciyarta ke bugu ba. Bugun bana komai ba illa bugun sunanshi watau ZAID.
***^^^

Yau Babbar Bak'uwa garesu
Hajia Aminene Mamman zata zo, Tun Safe ta rasa me zatayi don ta burge Nene.
Bata sanwa, amma don ta burge Nene sai da ta sa Zaid ya jona mata Gas.
Yace "really? 3days after your Wedding zaki fara abinci?"
Gira ta daga mai alamun Eh.
Yace "Dagaske Beebbs ki daina matsa ma kanki, wannan Tsohuwar baki iya mata, wallahi gwasule ki zatayi".
Tace "nidai ka barni, sai na mata, ka kira min Balele na aikeshi kasuwa".
Yace "to Allah ya bada Saa".
Ta murguda mai baki tace "Ameen".

Parlo ya koma bayan ya aiki Balelle kasuwa ya fara kallo.
Balele yaje ya dawo ya kawo mata duk abunda ta aikeshi.
A sannu sannu ya dinga jin kamshin abinci na shigo mishi.
Sai da tayi kusan 3 hours a kitchen kafin ta fito tayi setting table.
Zaid yace "Whats Cooking? Ya bubbude coolers, yaga cooler daya pepper chicken, daya Fried rice, daya tuwon semo da egusi da ya ji kayan miya da k'amshi.

Yace "Lallai Beebs, baa ma Mijin abinci ba, shine aka ma Nene?".
Ta langwabe tace "kar ka damu, zaka ga shagalin da zan maka kai kadai".
"Okay oo I hope she will be impressed though".
"Nikam kana kada min gaba, ka kyaleni".
Yace "okay oo, sai muje muyi wanka, kafin ta karaso".

Drivern Gidan Lema ya shigo gidan Zaid da misalain karfe 2:30 na rana.
Nene ta fito rik'e da Basket din Abinci a hannu.
Ta shiga Gidan da Sallama.
Tsaytsaye sukayi suna jiran shigowarta.
Idon Labiba ya kai kan Basket din hannun tsohuwar da ta shigo.
Sannu da zuwa ga Nene ga Nene.
Zaid ya karbi Basket din, Nene ta rungume Labiba.
"Yau ga ni ga Matar takwaran Zaidu bawan Allah".
Labiba ta durkusa ta gaidata.
Nene ta amsa cike da kulawa.
Har kan kujera ta jata suka zauna suka sake sabon gaisuwa.
Nene tace "Wallahi kina min kama da jikata Nasiba, don dai Seebi ta fiki dogon hanci".
Labiba ta murmusa tace "Allah Sarki".
Zaid yace "in ma so kike kice Seebinki tafi Matata kyau ba yarda zan ba, matata tafi kowa kyau".
Tace "Kai dai ka sani dan nema,".
Labiba tace "Nene muje kan table muci Abinci".
Nene tace "wallahi yunwa kau nikeji, da na gama Abincin ko ci banyi ba nayi wanka na taho".
Ta mik'e tsaye tace "takwaran zaidu bawan Allah dauko Baskyat din".
Kan dining suka nufa gaba ki daya.
Zaid yace "wannan Coolers din fa Nene, me ke ciki?".
Ta amsa daga hannunshi tace "Abinci na dafa mana muci mana, me ake zubawa dama a cikin cooller".
Da sauri ya kalli Labiba yace "ai ta miki abinci, kala kala ma, gasu nan kan table".
Nene tace "Too, daga kawoki shekaran jiya har kin fara sanwa? Wace amarya ke abinci a wannan lokaci".
Yace "sai da nagaya mata fa, tace sai tayi na tarban Nene".
Nene ta murmusa tace "Allah sarki, kuma gashi nima nayi Abinci, nace ma Aisha bari na dafa ma Matar takwaran Zaidu bawan Allah abinci, amma tunda kin dafa, ai sai ku aje ku dinga dumamawa kuna ci".

Da sauri Zaid yace "Aa mu dai ci yanzu dake".
Harara ta zabga mishi tace "wannan fa da na dafa, ya kake so nayi dashi?".

Yace "Amma kya ci abincin Amarya ko?"
Tace "ba zanci ba, nace ba zan ci ba".
Ta bubbude coolern ta dauki cokali ta dibo miyan kubewanta danye ta riko hannun Labee ta lasa mata tace "lasa kiji".
Labiba ta sa a baki.
Nene tace "tsakaninki da Allah abincinki ya kai nawa dadi?".
Labiba tayi daria tace "ina ma zaa hada? Ai ban taba jin miya mai dadin wannan ba".
Cikin dadi Nene ta tafa hannu tace "yauwa 'yar gari, shi mijinki da baa mishi gwaninta har ya fara yan surutai, nifa ba kowa nake ma abinci baa, amma ina ji dake shiyasa na dafa miki".
Labiba tace "aiko nagode sosai".

Labiba ta sauke Abincinta na kan table, ta daura na Nene, ta kai mata kitchen.
Zaid ya bi bayanta, yana cewa "kin gani ko? Na gaya miki, matar nan ba a iya mata, kinga ta wahalar min da ke".
Labiba ta harareshi tace "meye wahala? Chabda, nikam burgeni tayi, ba ta da bakunta".
Zaid yace "kyab, nenen zata miki bakunta? Shes full of wonders".
Tace "oya muje tana jira".
Suna fitowa suka ga har ta zuzuba musu a plate.
Tuwo ne miyan kubewa danye da yaji tantakwashi ga man shaniu na tashi.

Zaid yace "ni fa ba zan ci tuwo ba, abincin Matata zanci"
Nene tace "Alkuran ba zaka ci ba, ni na dafa maku abinci kace ba zakaci ba? Uban kutura yayi kadan".
Yace "wai ya Nene zakizo Gidana ki min iko".
Tace "a gaban Matarka zan lakada maka shegen duka, ka zauna ka ci tuwon nan, ko na danne ka na maka dure".
Baki ya bude, ya san zata iya, ya san zata aika, ya zumburo baki ya zauna.
Labiba ta dinga Daria.

Nan fa suka kwashi mulmula bibbiyu.
Nene tace "ahap sai gashi an cinye ana tande hannu, waya ce ma borno gabas take?".
Zaid yace "aidai an fi karfinmu ne".
Tace "kai Arr, bangaya ma ba sai ga 'yayan albarka Tero, haruna Eskaley da su Master sun kawo min abubuwan arziki, turmin Atamfa jiya da leshi da turarruka, da takalmi da mai da sabulun wanka da na wanki, wai na sanya a Albarka a sanaarsu".

Yace "kin manta ni na ka wo su? Kuma atamfa ne ba leshi, kuma ba kwanan na bane an kusa wata daya da yi, amma kina magana kamar jiya suka kawo".
Harara ta zabga mishi tace "ai dai sun fi wani da ko hakin ashana bai taba siyo man ba".
Yace "ba zai taba siya ba in jiranshi ake".
Tace "kai dai ka sani mak'on na mak'ok'o masu cin katako".
Yace "eh din naji".
Labiba ba abunda takeyi sai daria, ai kawai taji tana son Nene kuma ko kadan bata 6ata mata rai ba

Nene tace "Kinsan haka mijin Jikata Seebi yake da shegen feleken tsiya, don dai shi dunkum ne, be magana".
Labiba tace "Allah sarki, Katsina suke aure?".
Nene tace "Katsina? Haba, jikata na Landan, Ingila take aure, nima ai na taba zuwa".
Zaid ya ma Labiba ido alamun tsaya kiga ni.
Yace "mu fa an ishemu da wata Seebi, wai seebi na aure a London"
Nene tace "wallahi tana Landan, tambayi mamarka kaji,chan take aure".
Zaid yace "Mu dai ba mu yarda ba, yanzu haka tana Kano zaa raina mu ace tana London".
Nene tace "Wallahi aa London suke, tsaya ma ka ga hotonmu da naje muka dauka".
Ta mike ta koma parlorn don daukar wayarta.
Daria yake kasa kasa yace "so nake na k'uleta fa".
Labiba tayi daria chan k'asa tace ai na ga alama, na dagoka.

Nene ta dawo, har ta dauko wayar Ta nemo hotunan don ba inda bata shiga da Android Phone dinta. Ta nemo pictures din da suka dauka a chan zata nuna musu kenan.
Zaid yace "ai rana bata karya, a nuna mana mu ga Zahiri".
Nene ta tsaya, tana kallon Zaid, ya ma rainata, ita kuma harda biye mishi.
Zaid yace "In dagaske ne a nuna mana mana mu ga Seebi a London".
Nene tace "karya nake danuwarka".
Ya fashe da daria Labiba dai ta dan sha mur.
Nene tace "zanci ubanka takwaran Zaidu bawan Allah, zan gurza maka rashin mutunci".
Yace "Haba Neneta".
Ta harareshi tace "Gidanmu zani".
Labiba ta riketa tana kyaleshi Nene ai ba wurinshi kika zo ba.
Nene ta harareshi tace "Uziless (useless) muje daki mu barshi, mai tsamin jallabiya, Allah ya sa baka taho dashi ba dai nan".
Daria Zaid yayi yace "Naji, ya san ta k'ule, yau haka zaa karashe ranan da mitan Nene.

Har bayan Magrib Nene na gidan.
Sai chan aka zo daukarta.
Labiba ta je yi mata take away din gara.

Akayi akayi Nene ta tafi da Abincin da akayi dominta tace "sam ba zata dauka ba, kawai sai a ga na koma gida nikiniki da abinci, ba zan dauka ba to".
Zaid yace "haba Nene ta bata lokaci ta miki abinci ba ki ci ba, kika hanamu ci kuma sai kice ba zaki tafi dashi ba? Haka akeyi?".
Tace "wani ya sata? Iyayi, wace amarya ke abinci? Ba zan dauka ba wallahi".
Zaid yace "to wallahi nan gaba kika sake zuwa ko ruwa ba zamu baki ba".
Tace "naci ubanku kuwa daga kai har ita din".
Yace "haba Nene, kar ta jiki mana".
Tace "yo sai na kirata na fada a gabanta".
Yayi saurin cewa "yi hakuri, kina iyaawa.

Labiba ta shigo dauke da ledoji gara cincin da dubulan da alkaki cike da ledoji.
Nene tace "Thank you Thank you".
Ita Labiba taga Nene 'yar gayu tace bari ta burgeta irin da turancin nan tace "Nene mungode, we appreciate your visit, May God Bless you".

Nene tace "Keeee, ni zakiyi wa turanci? Baka gaya mata baa turanci a gabana ba? Ko zagar min uwa kikayi?".
Labiba tayi saurin girgizai kai a daburce tace "wallahi Aa, ba zaginki nayi ba".
Ganin hankalinta ya tashi ya sa Nene daria tace "ja'ira har ta tsure, to nasan ba zaki zageni ba, turancin ne banso, wanda ya man turanci gani nake kamar ya zagar min uwa".
Labibs ta murmusa tare da sakin ajiyar zucia.
Nene tace "To Thank You, Sorry, Byebye".
Ba ta jira cewarsu ba ta fada mota Driver ya jata.

Zaid ya rungumo Labiba yace "Yau dai kin ga Nene".
Naunauyar Ajiyar zuciya tayi tace "Yau naga Nene".
Yace "Haka fa take, ai Nene damuwa ce, yanzu zata kwance maka zani a kasuwa, kuma ta manta ma ta gurza ma".
Tace " hahaha i love Nene already".
Ya sungumeta in bridal style ya na tafiya da ita.
Yace "Wanchan Abincin ya zamuyi da shi?"
Tace "mu kai gidan Baba".
Yace "nikadai zanje".
Tace "harda ni"
Yace "Nope".
Tace "pleasee".
Yace "Naqi wayon".
Tace "Haba Mijin".
Yayi daria cike da kauna.
Washegari ta karbi ziyarcin yan Bencin Eskaley.
***
B A Y A N S H E K A R A D A Y A

Duk Amaren bara sun haihu.
Ko wacce da diyarta Mace
Diyar Dalo Ummansu Jawad aka ma takwara.
Diyar Abdulmajeed kuwa taci Maryam.
Samira ta samu Fatima
Sai Labiba, Labiba ta haifi YASMIN.
**
Bai manta lokacin da Labiba za ta haihu ba, tana kallon Dadin kowa a arewa 24, ta kalla na minti 30 nakuda ta taso mata gadan gadan, baya Gida yana Chan Tudun Matawalle gun Baba, ta kirashi tace “ka dawo”.
Sai ko gashi ya dawo ya dauketa suka tafi Asibiti, motsi dubu sannu yake mata, tun karfe 9 suke abu daya sai karfe 12 ta haihu, da Zaid aka karbi Haihuwan don kin fita yayi, fitowar kan jariri kadai ya kauda kai saboda ya kasa jure ganin Labiba cikin azaba irinta haihuwa.
Kukan Jariri yaji.
Da sauri ya amsheta tare da rungumeta
Mace ce
“Mace ce?”
A kunne ya rada Mata “Barakallahu Fiki YASMIN, Allah ya miki Albarka”.
Sannu da godia ya jera ma Labiba ya kai 1000.
Zaid ya zauna ya tsantsara text ya tura ma Contacts dinshi.

*Alhamadulilah Allah has blessed me with a beautiful girl. The Father, Mother and daughter are in good condition.*

Asubar Fari Aunty Mariya, da Aunty Aseeyah suka zo Asibitin dauke da ruwan Zafi da kayan tea.
“Ja’iri jiya da na ke cewa ka daina barin diyar mutane ita kadai me kace?”
Yayi daria yace “Aunty kinsan muna gama maganar nan da ke ko minti 3 banyi ba ta kirani, ina shagon Eskaley kawai na wuce”.

To tunda garin Allah ya waye Zaid ke amsa kiran yan barka
Asibiti kuwa tururuwar zuwa ake, bayan an ga lafiayarsu aka sallamesu suka koma Gida.

Jawad ya kira yi ma Zaid barka.
“Haba Bro, ya zaku kira mu yanzu? Ka san dai babyta batayi kwari ba? Jiya sukayi 40days, yanzu ka sa dole Princess tace sai tazo wani Katsina Suna”.
Zaid yace “ka ma isa ka hana, Matata da tsohon cikinta kuka sa tazo Abuja Suna, ai wallahi sai kun rama mana bamu yarda ba”.
Jawad yayi daria yace “harda wani cewa The father the mother and daughter are all in good condition, kamar kai ka mata haihuwar”.
Zaid yayi daria yace “Ai ina jin na fita wahala, ni nayi nakudar na ji jiki sosai”.
Daria sukayi yace “to Allah ya raaya”
Ya amsa mai da Ameen.
Ran suna yarinya taci sunanta *Yasmin Zaid Ali Zaki*
Wannan kenan.

Shafa’atu? Babu wanda ya san inda take babu wanda ya san ko tana mace ko a raye, babu wanda ya san duriyarta abunda yafi ko wanne mahimmanci, babu wanda ya damu ya san duriyarta.
Tuni sun mance da rayuwarta kaf.
^^^^

Labiba ta gama Diploma dinta zatayi joining Umaru Musa Yaradua zasu bata level2.
Dalo kuma tana Nile University inda take karantar Biology, gida take kai Lubna in zata lectures.
*

Jiya Yasmin ta shiga Shekara 1 da haihuwa, a gida suka mata celebrating 1year birthday.
Zaid ya fito sanye da kayan shi na civil Defense ya fito fes abunshi.
Kallonshi kawai Labiba takeyi, sai kamshi yake zubawa, tace “Wallahi Ni dai ban taba ganin wanda Uniform suka mishi kyau ba kamarka, kamar don kai a ke yin khaaki dinnan”.
Daria yayi tare da manna mata kiss a baki ya, ya amshi Yasmin a hannunta tare da manna mata kiss a goshi.
Bacci take amma sai da yayi mata magana Yace “Daddy zaije aiki, ina son Yasmin da Mummynta“
Labiba na kallonsu cike do Soyayya.

Tace “Zanje Gida, Aunty Mariya tace Baba bai ji dadi ba”.
Zaid yace “Ciwon kai ne fa, kuma stress ne, aunty maria can exaggerate ehn”.
Labiba tace “kai ko Mijin, dole ta damu, Miji ai ba wasa ba”.
Ya kalleta tare da ida kashe mata kannanne idonshi yace “haka akeji in banda lafia?”
Tace “abunda ya fi haka ma”.
Daria yayi sosai ta rakashi har Mota tace “Motar nan tayi dattii fa, ka dauki tawa”.
Yace “ko jiya an wankeshi, k’ura ne”.
Tace “kar ace ma dirty dirty”
Yace “in dai ba ke zaki ce min ba ni ina ruwana da mutane?”.
Tayi daria tana kallonshi zaune a mita yanda yayi kyau, Khakin nan ya kara mishi girma da kwarjini a idonta”.
Wani tunani tayi tace “kasan bamu taba Zancen Mota ba? In short kafin aure me ma mukayi wanda couples keyi? Nothing, dama a dawo min da yanmataccina”.
Dariya yayi yace “i am late, sai na dawo, i love you kinji baby?”.
Tace “i love you too”.
Yayi daria yayi horn Maigadi ya bude mai Gate.

Wurin karfe 4 ta ja Motarta zuwa Tudun Matawalle da Abinci Basket biyu, daya na Gidan Aunty Mariya daya na Aunty Aseey.
Sai da ta fara shiga gaida Baba Aunty Mariya tace “yo ai tun safe ya fita wai yaji bacci”.
Ashe Zaid na gidan ya fito daga dakin Baba don shi yake mishi shara yace “ba na ce miki ya warke ba? Aunty kawai ta zata mijinta zai gangara ne”.
Aunty Mariya ta harareshi tace “zan bata ranka”.
Dariya yayi sosai Labiba tace “kyaleshi Aunty zan tayaki miki maganinshi”.
Daria sukayi yace “nidai na tafi, a gaida Baba”.
Zaid ya masu byebye ya tafi ya barsu nan, ta dan jima kafin ta shiga gidan Baban Amira
Kafin Maghrib ta koma Gida daga Gidan Aunty Aseey, tace su Amira su zo mata weekends ita da Sabit.

Bayan Isha’i ta tsanyara wankanta ta shirya cikin wani Material fitted gown, kamar bata haifi yasmin ba, yasmin barcinta takeyi.
Ta daura dankwalinta tana jiran dawowan Mijin.
Taji dirowar Motarshi.
Ta feshe jikinta da turare, mai makon ta ji shigowarshi, sai ta ga wayarshi.
Dauka tayi tana mamakin kiran “Hello”.
Yace “Beebs, gani nazo, ina waje?”.
Shiru tayi me yake nufi?
Taji yace “Ko jan aji zai hanaki fitowa? Zaki shanya Saurayin?”.
Tace “Oh My God, sorry boyfriend gani nan fitowa”.
Da sauri ta bude wardrobe ta dauko wani karamin gyale wanda take sawa da Jallabiya ta yafa a kafadarta, ta sake feshe kanta da turare, ta sa ma Yasmin Pillow ta kareta a tsakiyar gado ta fita waje tana rangaji kamar Bishiya.

Daga Mota yake kallonta, Sonta kamar ya fasa zuciyarshi, yana kallon yanda ko wani gaba na jikinta ke motsawa.
Fitowa yayi ya bude mata Motar ta shiga ya rufe ya zagaya ya zauna”.
Kara musu Ac yayi.
“Ina Yasmin?”
Tace “sleeping”.
Hannunta ya rik’o yace “Girlfriend”
Tace “boyfriend”
Yace “to nazo Zance, a min Tadi”.
Daria tayi ta ga Ledar Havillah Ice cream tace “Lahh Ice cream”.
Yace “dallah ba haka sukeyi ba, jan aji zaki dinga yi, ni zan miko miki ki karba”.
Tace “oh okay to bani”.
Yayi daria yace “Baby ga Ice Cream na siyo miki”.
Kamar dagaske ta kawar da kai ita kunya.
Daria suka fashe a tare.
Ice cream din ya fasa yana bata a baki yace “haka saurayi da budurwan zamani sukeyi ko?”.
Tace “ni ina zan sani, nima yau na fara”.
Yace “a sannu zamuyi k’ara’i”
Tayi daria
Ice cream din lebenta ya lashe, sun nisa da abunda sukeyi suka ji Yasmin ta chanyara Ihu.
Ai sakin Ice cream din sukayi suka fita a guje gudun ko wani abu ya faru da ita.
Zaida ya riga shiga dakin Ashe Farkawa tayi taga ba kowa.
Da sauri ya dauketa ya rungumeta a kirji yana rurrugata.
Labiba ta harari Yasmin da tuni tayi lamo ta koma bacci a kafadar Babanta tace “Yas you ruined our date, ina Zance da dan Saurayina kin katse mana Jin dadi”.
Zaid yayi daria yace “i love you both”.
Labiba ta rungumesu duka tace “ina sonku ku duka”.
*Tabbas Wannan Zaidun Labiba ne*

THE END? Yes Mankasss ya k’are.

*Alhamdulilah, Allah nagode maka da ka bani ikon gama wannan Labari na DANMAKAHO, Allah ka yafe min inda nayi kuskure, abunda na rubuta daidai Allah ka sa alumma su amfana dashi*”.

*DAN MAKAHO na ku ne Ma su yin Soyayya domin Allah*
*ALLAH KA KARA MANA SON MASU SON MU*
*Allah ka bamu ikon yin Soyayya ingatacciya, halalliya kuma muyita domin ka*

*Ina rokon Yafiya da gafarar duk wanda ya samu bacin rai Dalilin Dan Makaho*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION* _*Nagode*_

_Bibilicious freaking fans_ _Nagode_ Son So Fisabillilahi ❤❤

Allah ya hadamu da Alherinsa, ya sa mu cika da Imani.

#1love
#DanMakaho
#anatare
#FWASonSo
#nagode

*Biebee Isa*
Chapter 20 · 0% Book details