← Book details Dan Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 10 OF 20

BABI NA ASHIRIN2⃣0⃣

Dan Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

(KALLON KALLO👀)

Yesmin K'amshi ta fito sanye da wata doguwar jallabiya mai kyaun tsiya, daga bacci ta tashi  a dakin Aunty Shafa, k'amshinta ya cika gurin.
Hudu ne kadai a Parlo, Auntyg Shafa'atu sun fita da Annah.
Hudu na ganinta ya ji wani abu ya fizgeshi, da murmushi ya taryeta har ta zauna ta daura k'afa daya kan daya.

Bude hak'oranshi yayi yace "Yas Yas, Allah ua miki kyau wallahi kamar ke kikayi kanki".
Guntun murmushi tayi tace "aa ba ni nayi kaina ba, Allah ne yayi ni"
Yak'e Hudu yayi, ya san Yesmin da datso magana dole sai yayi taka tsantsan.
Yace "wai Dr Yas nayi ta kiranki baki dauka, ba kuma kya calling back, kuma na san kina ganin Missed call".

Bata tanka shi ba, ta ciro wayarta tace "wai har yanzu baka gama ba? To ina jiranka a ciki please". Ta saka wayar cikin jakka tace "Uncle Hud, wallahi ina ganin missed calls dinka, attimes ma akan idona kake kira, but attimes kawai am not in the mood to pick your call kagane? Don na san usual surutanka zaka min, kuma ni banda energy din jinsu over and again kagane?".

Kafin Hudu yace wani abu, ya shigo, babu wani abu sabo a jikinshi amma sosai ya ma K'amshi kyau. 
Tuni ta mik'e tsaye har ya tako har gabanta, kallon kallo suke wa juna, Hudu na zaune ya gama k'ullewa ya kalli wannan ya kalli wannan.
Gira Zaid ya daga mata yace "Ya Da Kallon?".

Murmushi ta sakar mai tace "Sosai kayi Kyau Zaiduna".
Kafin Zaid yayi magana Hudu ya fincike Zaid ya mayar dashi gefe ya sha gaban K'amshi yana huci yace;
"Yanzu ke Yesmin ta kan wannan Dan Makahon mara gata kike min wulakanci? Ta kanshi kike k'in saurarana?".

Zaid yace "kai so kake na maka mugun bugu ko? Ka manta bugun tsiyan da na maka ko".
Hannu K'amshi ta daga mai tace "kash Zaid, rabu dashi, ba girmanka bane magana da Agola, akwai rashin gata da ya wuce agolanci? Yana kasan kafar yayarshi yana fadanci kamar wani marok'i sai abunda ta dauka ta bashi, kamarshi yazo yayi katokato, cima zaune, ba cis ba as, duk randa babanka ya rabu da yayrshi ba baida sauran gata, bai da amfanin komai, kar ka sake ranka ya baci ta kan wannan cima zaune, barin kira Dalo, don Outing dinnan da ita zamu".

Wuce su tayi duka, shi ko Zaid kashe ma Hudu ido yayi tare da rufa ma K'amshi baya.
Wani Ihun bakinciki Hudu ya sake ba wanda ya kallo inda yake suka shige dakin Dalo a tare.
K'amshi tace "Hajiya Sadiya tashi muje Yau outing zamuje"
Ido ta zaro tace "ina zaku?"
K'amshi ta dagota daga kwancen da take tace "dake zamu ko ma ina zamuje".
Dalo ta sake ware idonta tace "ni ina zanje? Baba ya hanani  fita fa".
K'amshi tace "come on my friend get up and dress up".
Dalo tace "Aunty Yasmin ki rufa min Asiri donAllah, wallahi Baba yace kar na sake na taba fita, ya Zaid gaya mata donAllah".
Zaid ya murza idonshi da murmushi a fuskarshi yace "Ai fa Dalo Yesmin ba zata ji ji ba, tunda tace da ke zaaje da ke zaaje din, sai ta san yanda zatayi da baba in ya kama mu, ki tashi dai kafin ya dawo muje mu dawo".
Dalo tace "in suka gaya mishi fa?"
K'amshi tace "i know how to shut them up, trust me".

Numfashi Dalo ta ja ta sake a hankali kafin ta bude Wardrobe ta ciro wani doguwar rigar da Mancy ta aiko mata dashi, gudun magana ne ya sa bata taba sakawa ba, Zaid yace "zan jiraku a waje" ya fita.
Sai da ta shirya suka fita tare gaban Hudu wanda yana ganin fitowar Dalo ya dauko waya don shaida ma yayarshi.

Zaid a gaba Dalo a baya Yesmin a  seat din driver suka fita daga Gidan.
Wayar Dalo ke ringing ko da ta duba Aunty shafa ce, sai da hanjin cikinta suka kada, ba kasafai Aunty shafa ke kiranta ba, in har ta kirata to ita Aunty shafa ta fita kuka tana so Dalo ta mata wani abu sai ta kirata.
A daddare tace "donAllah ku maidani Gida bana son problem, ga Aunty shafa na kirana".
Yesmin ta cigaba da tuk'inta tace "answer and put the phone on speaker".
Bin umurnin Yesmin tayi ta kawo mata wayar daidai gemunta.

Muryan Aunty Shafa ya karade Motar "Ke Sadiya Gidan Uban wa kika tafi harda sa sabbin kaya, karuwancin  da kika saba zaki ko?".
K'amshi tace "Wai ya Aunty Shafa? Dalo na tare dani, ko akwai matsala ne?"
Da sauri ta sauta murya tace "kingane Yesmin Babanta ne be so tana fita a gidan".
Yesmin tace "to muna tare ba wani wuri zataje ba".
Yesmin ta ma Dalo alamu da ta katse kiran.
Zaid na gaban Mota bece musu komai ba, ya san akwai wani abu da Yesmin ta sani wanda Shafa take tsoron a sani shiysa take daga mata tana kuma bari tana takata amma ko so daya be taba son sanin ko meye ba, abu daya ya sani shine ya yarda da Yesmin dari bida dari.

Chimex Shawarma ta nufa dasu, su ka bada order aka gasa musu guda biyar duk chicken and sausage ta biya kafin suka je Havillah Ice Cream.
Anan suka ci Shawarman bayan ta siya musu icecream.
Fira sukayi su uku cike da kaunar Juna, sukayi pictures kafin suka koma mota, yawo kawai sukai tayi a Garin Katsina, Girman Yesmin ya k'aru a idon Zaid, don ya dade be ga Dalo cikin farinciki irin na yau ba, sai da ta tsaya a Dadin Kowa ta siya ma Dalo Chocolates kafin suka koma Gida gab da Maghrib.

A kusan tare suka isa Gidan da Baba. Ganin Sadiya da Zaid a tare ya sa zuciyarshi nauyi, Yesmin tace "Ina wuni Daddy" ya amsa da murmushi "lafiya lau Yesmin yaushe aka zo?"
Tace "dazun da safe na zo, na zo muku weekends" yace "ayyah mungode sosai ina sukayi posting dinki bayan service?" Tace "General hospital na Kankia" "Allah ya taimaka" yana kallon Zaid da ya dauke kai ita kuma Dalo ta na jiran saukan fada ko duka a daddare, be ce musu komai ba, gaba yayi zuciyarshi na mai nauyi, yaranshi.. ya Allah".

Yesmin ta kallesu duka tace "muje ko?".
Tayi gaba suka bi bayanta.
Suna hanyar parlo sukaji muryan shafa'atu na cewa "Alhaji kaga Sadiya tun dazun ta fita, har yanzu ba ta dawo ba".
Nan da nan fuskar baba ya chanza " Ina Sadiyar, ba zata huta ba sai ta jawo min magana cikin Gidan nan ko? To kafin ta kasheni ni sai na kasheta".
Tuni Dalo ta koma bayan Yayanta a tsorace, shima Zaid ya tsorata da sudden change din baban, yanzu fa ya gansu, ya san tare suke, amma be ce komai ba, amma matarshi tayi magana duk ya koma wani zararre, matar nan ta maida masu mahaifi kamar wani toy.

Yesmin ta kallesu tace "Relax, ba abunda zai faru" parlorn ta k'arasa shiga ta wurga ma Aunty Shafa'atubwani mugun harara mai ma'anoni da yawa. Hajia Shafa ta dan tsorata tace "Laah kaga Alhaji na manta, ashe Sadiya da Yesmin suka fita, na ma manta, kar ka damu". Kamar wani pagal ya washe hak'ora yace "au haba dai? To to to ashe suna tare da Yesmin, ai ba damuwa, barin shiga daki" yayi haba Hajia shafa tayi saurin rufa mai baya don bata shirya haduwa da Yesmin ba.

Sai da suka kai Dalo har daki kafin suka fito a tare.
Hudu da Annah suna tsaye a Parlo.
Don Zaid ya k'ular da Hudu don ya san yana son Yesmin yace "Yesmin ayi rigegen zuwa dakina" da daria tayi saurin fita ya rikota ta fizge hannun ta arta a guje shima ya bita a gujen, bakinciki kamar ya kashe Hudu.

Yanzu shi ke gaba tana biye dashi a baya sukayi BQ.
Ita kuma ta fito daga dakinsu da Plates a hannu ta ga wata na bin Zaid suna gudu suna daria.
Zuciar Labiba ya halba.
Chak Zaid ya tsaya yana kallonta yanda itama take kallonshi, hakan yasa Yesmin chogewa itama don kallon abunda yake kallon.

Budurwa ce ta gani tsaye daga chan bangaren tana kallonsu, daga inda take ta hango fushi a idon yarinyar da bata wuce 18 ba, kallon Zaid tayi ta ga hankalinshi kacokam na gun yarinyar da wani expression a fuskarshi da ta kasa gane ko menene.
Yarinyar ta ga ta share wani abu a idonta kamar hawaye, ta wuce kitchen sauri sauri gudu gudu, a kan idonsu ta sake dawowa a guje ta fada daki.

Wani jijiya Yesmin ta hango a kan Zaid duk ya damu.
Jiki a sanyaye tace "Zaid who is She?"
Murya chan k'asa yace "Noone".
Kafin tace wani abu tuni yayi gaba ya wuce dakinshi tare da barinta tsaye.
Gidansu Labiba Yesmin ta kalla kafin ta tsaya wani nazari kafin ta shiga dakin Zaid ta ganshi kwance rigingine duk yanayinshi ya chanza.
Murmushi tayi tace "Yau ko ka tashi ka min Fira ko na je shagon Eskaley na zuk'i world".
Dariya ya fashe tare da mik'ewa yana fadin "Me zanyi in babu ke k'amshi?".

#1love
#DM
#anatare
#FWASonSo
#nagode

Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉
Chapter 10 · 0% Book details