← Book details Binta Yar Jagaliya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 8

Sashe 8

Binta Yar Jagaliya Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Gaban makeƙen gidan suka tsaya sosai binta tayi mamakin arahar gidan tayi farinciki sosai sai ma da ta shiga taga an zuba komai yanzu jibi zata fara binkican mahaifinta kahu yayi murna da ganinta sai nan nan suke da ita shi da uwani zama tayi tana ƙarƙada ƙafa tace

"To yanzu kahu komai ya sauya Banda fita bara ,

toto nadena binta

Uwani

gyara zanin ta tayi tace

"Na'am binta,

Banda sana'a ina da kuÉ—in ciyar da ku

to bazan sake ba

kawata ni zan tafi

Okay muje in raka ki ko

Tashi tayi su ka fita

Tashi yayi shima ya dubi uwani yace

Ni zan fita in zaga gun yan uwa daula ta samu

To me gida sai kadawo

Dariya yayi yace

Rabon kiyimin wannan tarbar tun muna cin amarci

Ae yanzu komai ya huce

Babbar riga ya gyara ya fita tafiya ya fara wata ƙatuwar jeep ce ta tsaya baƙa wasu burɗadɗun mutane ne suka fito suka ce

Tsoho shiga

Ja da baya ya fara ji yayi ya jingina da wani garo juyowa yayi ashe mutum ne yace

"Lafiya ,

Ka yiwa kanka arziki ka shiga tambaya zaka amsa mana

Ba yarda ya iya yace

"To ba yarda ya iya ya bisu tafiya sukai mene sa tu kunna su ka je gidan gona duk bishiyo fitowa sukai suka tisa ƙeyarsa har wani har wani hadaddan floor wanda shi ake kira da aljannar duniya zama yayi a ƙasa suka fita suka jawo ƙofa

Hawaye ne ya fara zubomai ya gashi a fadar aljanu shi daman ya san ba zasu barshi ba tafiya yaji

Zabura yayi ganin mutumin da yake gani a poster

Murmushi ya sakar mai ya zauna yace

Bisimillah zauna cikin aminci

Murza idonsa yayi yace

Nan ma ya isa

Okay wata alfarma nake nema

Anya kuwa ni labahani ba mafarkin da nasa ba naka ba

Ido biyu kake zauna dan Allah

"To to zama yayi ,

Kai haƙuri na sa an dauko ka

Bakomai ka isane

Yauwa Nagode ina nemawa jikana auran yar wajanka ina fatan ba ai mata miji ba

Washe baki yayi me ragaje tayi goshi yace

"A'a ban mata ba Maryam a kwai ƙirkir wallahi tafi Binta komai,

ganin be gane wacce yake nufi ba ya danna wani majigi nan hotan Binta ya bayyana yace

"Wannan nake nufi,

Zaro ido yayi yace

"Binta tafi ƙarfina wallahi ga Maryam nan na baku ita nake da iko a kanta,

Kar ka damu aikai wakilinta ne zamu san yarda za a Kaita gidan a ɓoye sai dai ta farka ta ganta a gidan su zan kai ka Makka sannan zan baka ƙaton gida kai shiru da bakin ka

Zama ya gyara yace

"To to Ni wallahi yanzu a shirye nake na baku ita yanzu muje masallaci a daura,

Murmushi yayi yace

Angon baya ƙasar nan amma nine wakilinsa ga abokin sa zai zo a yau zan baka komai da nayi maka alƙawari za a dauki komai a nuna mata dan ya zama sheda.......✍🏻
Chapter 8 · 0% Book details