← Book details Binta Yar Jagaliya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 8

Sashe 5

Binta Yar Jagaliya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"ɗazu na ƙafa muku sharaɗi kun bujere min to zaku rufe idanuwan ku har sai wani daran yayi sannan ku buɗe in kuka ƙus kura kuka buɗe to fa rundunar aljani gushshu zatayi sama daku sannan ki faɗawa labahani ƙar ya sake ya ƙara fita waje da sunan bara sai de yaji anyi sama dashi bashi ba dawowa,

"To mun gode ,

tuni suka rufe idon su suka fara laluban ƙofa ruge ruge suka shi ga yi ganin uwani ta bangaje IYA ba ta luraba yasa IYA ta fusgota ta dawo da ita baya tayi wuf ta futa gani take in ta ƙara second ɗaya rundunar aljani gushshu zata yi sama da su

Ganin iya ta futa yasa itama ta fita a guje har ta buge da garo É—akin uwani suka shiga suka cure gu É—aya hakama malam ya zuba ta gumi dan ko shakka babu yasan fatalwar gimbiya ce ta zo musu ba mala'ika ba duk abin da ake yana ji har da hana shi bara

duban mero yayi duk ta fita hayyacin ta sai surutai take allah ya rufawa saminu asiri da yau be ƙwana a idan nan ba

da ya ƙwana da dashi wannan rundunar gushshu zata haɗa domin ai ba zasu bar shi ba saboda kajin mutane da yana sakat a garin nan kullum cikin cin kaji yake suma harya sammu su

*WANNAN KENAN*

"wallahi momcy duk abin da zan ja hankalin sa ina yi amma wallahi a banza anya kuwa yana da lafiya?,

YUSRAH ki nutsu ki gano abin da baya so da wanda yake so shine fa amfanin zaman ki kenan a gidan wallahi na ƙwaɗayin dukiyar gidan alhaji ƙura kin san kaf ƙasar nan ba na biyun su a ƙuɗi da mulki ke ce wacce zata zamo silal dawamar mu a daula kinsan a kullum sai naji ɓakin cikin hajiya turai saboda mahaifin mu ya fi son ta shiyasa har ya bawa bilal auran ta lokacin da na gane haka wallahi har ƙwanciya nayi a asibiti ƙarshe sai ya haɗani aure da mahaifin ki wanda bashi da wata shahararriyar dukiya dan haka wallahi ko zan yawo tsirara sai na rusa hajiyan turai akomai

MOMCY yanzu wanne mataki zamu É—auka naji hajiyan turai tana cewa we waccan shegiyar yarinyar zata dawo gidan nan

ƙwafa tayi tace

"Uhmm zanyi maganin ta ,

MOMCY ya zanyi ya so ni duk abin da nake kamar baya gani fa

Dariya tayi tace

"YUSRAH yana kula da komai halin su ɗaya da mahaifinsa zai nuna miki kamar besan komai ba to kisam mummuƙe yake yana lura da komai sannan duk kan wani taƙun kowa yana sa mai ido amma zanje gun bokana Jibi,

"TO bye,

"Bye,

washe gari 🌅

cikin sauri yake komai saboda yau suna da taron jam'iya gashi sauran ƙwana sittin zaɓe wani satin za ai primary election za su yi tsare tsaran abubuwa geznar yasa blue black tayi mai kyau abinka da farar fata yasa black shoe ga rolex black a hannusa hula ya sa me tangaran gyara babbar rigar sa yayi ya sai ƙamshi yake zab gawa

ɗauki brief case ya ɗanna remote ya kashe komai na ɓangaran sa cikin nutsuwa yake taka stairs case wayar shi ce tayi ƙara alamun shigowar message be biya ta ƙai ba ya nufi shashin hajiyan turai duk inda yabi sai sojojin nan sun gaishe da shi amsa musu yake cikin sakin fuska

a bakin ƙofar hajiyan turai ya tarar da sam driver sa sam yace

"good morning sir ,

morning sam

ɗur ƙusawa yayi ya amshi brie case ɗin sa

miƙa mai yayi

Cikin hausar sa mara fita yace

"sir ga sabuwar jaridar c.n trues ,

cak ya tsaya be juyo ba yace

innaje office zan duba ta

"sir is very important ,

juyowa yayi ya amsa shafin farko yaga picture ɗin shi anyi rubutu da manyan baƙi

*SHIN KO KUN SAN DALILIN DA YANA ƊAN TAKARAR SHUGABAN ƘASA AZZAM BILAL ƘURA YIN AURE* ✍🏻

*Binta yar jagaliya*

*Oum yasmeen yar mutan yakasai*

Zubawa rubutun ido yayi yawa me shirin gano wani abu wato in kana so ka san asalinka shiga siyasa rintsai don sa yayi a hankali bakin sa ke furta

*HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKIL*

ba abin da ya ɗaga mai hankali sai we ana zargin sa da yana hurɗa da karuwa shi yasa yaƙi aure ringing ɗin wayar shine ya dawo da shi hayyacin sa da sauri ya ɗauka ganin mahimmancin kira yasa dole ya ɗaga yayi shiru

AZZAM kana dawo wa daga taron jam'iya ka biyo jirgi ka tawo akwai matsala duk da alhmdllh nayi maganin matsalal

to kawe yace mai sukai sallama kai tsaye shiga ciki yayi domin gaishe da hajiya turai sai wanda ya karan ce shi zai gane cewa yana cikin fushi sosai fuskar sa har ja tayi abinka da farin mutum cije leɓansa na ƙasa yayi a rasa da me za ahaɗa shi sai da zina rumtsai ido yayi tambas siyasa mugun wasa ne in baka da juriya ka shigeta sai a haukata ka ba abin da ya tsana ya ƙƴamace shi irin zina dai dai ta kansa yayi yayi sallama

cikin fara'a ta am samai yace

"lafiya azzam naga yanayin ka ya sauya wannan fa jaridar da ka duƙunƙune ta me ke faruwa?,

risina wa yayi ya ƙaƙalu murmushin dole yace

"hajiya bakomai barka da safiya kin tashi lafiya,

ajjiye chokalin hannuta tayi ta dauki tissue ta goge bakin ta ta miƙe cikin nutsuwa take takowa inda yake tace

"Azzam ni na haifeka dan haka kome zakai ka ɓoyemin abin da ke zuciyar ka ni me iya karantar shine ta idonka ko fuskar ka azzam kai ka ɗe muka haifa duk da haka mun baka tarbiya ta gari mun hane ka da yin ƙarya me yasa yanzu xaka fara alhalin fusƙar ka ta nuna ? ,

ƙasa yayi da idanuwan sa jikin sa yayi sanyi ya miƙo mata jaridar amsa tayi ta sami gu ta zauna ga banta ne ya waɗi tayi shiru na wasu sakanni kana tace

"ɗaukaka bata zuwarwa mutum ta cikin sauke dukƙan wata nasara tana zuwa da ƙalubale ba kowa ne zai yarda da wannan zancan ƙazafi ne duk wanda yayi maka nasan ubangiji ba zai barsa ba ɗana ƙar ka sa komai a ranka Allah yayi albarka ya dafa maka ,

sosai nasiyar mahaifiyarsa ta shige sa tambas duk wanda yayi sa'ar uwa ta gari ya dace yace

"hajiya zan tafi taron jam'iya sannan zanje kura baffa na nemana,

okay Allah ya tsare

"ameen yau muzamfar zai dawo na barmai komai na kasuwanci na kafin komai ya dai dai ta,

"To allah ya rufa asiri ya buÉ—a,

"Ameen ya allah,

miƙewa yayi zai tashi yaji ance

yaya ina ƙwana

be juyoba ciki ciki ya amsa yayi gaba abinsa

haɗiye wani yahu me ɗaci tayi tayi zaman daɓaro a ƙasa kai kace yar borice zuciyar ta tayi wani irin baƙi dan ma Allah ya temake ta hajiya turai ta shiga ɗakin ta sallamar ramlat taji da sauri ta ɗago kai tana jifanta da wata iriyar harara

Mayafi ramlat ta cire tayi É—amara tace

"wallahi kinsan ni bana ɗauƙar raini ko ? dan wallahi yanzun nan zanyi ƙasa ƙasa da ke banza ƙaruwa ,

cikin zafin nama yusrah ta É—aga hannu zata mare ta haseena ta tare tace

"ƙarya a kai miki ai yusrah baki ga komai ba sai ance miki yau an daura aure na da yaya azzam ,

Ramlat da zuciyarta ta kawo har huya ta É—auki takalmin ta ta bugawa haseena abaki tana huci tace

"wallahi kaf cikin ku ni ya azzam ya dace ya aura saboda ni daga dangin ubansa nake kufa yan karan ƙaɗa miya banza ye kawe,

dariya yusrah tayi ta tafa hannaye ta rangaÉ—a buÉ—a tace

"anayi muna jin daÉ—i ku gama haukan ku ni zan aure shi,

sosai bakin haseena ya fashe yana zub da jini dafewa tayi ta zuba uwar ƙara da sauri hajiya turai ta fito tace

"lafiya haseena ramlat yusrah me ya same ki haseena ?"

yusrah tayi carab tace

"faɗa sukai ita da ramlat ta sami gu ta zauna ta kurɓi lemo ta sa earpon a kunnanta tana bin waƙa,

hmmm ni ba zuwanku gidan nan shine matsalata ba aa faɗa kuke ace har yanzu baku girma ba ko wacce a cikin ku da tayi aure da tuni da ƴa'ƴanta wallahi yanzu nan zan ƙira azzam yayi maganin ku nasan beyi nisa ba

Haseena tace

hajiya ɗan allah kiyi haƙuri insha Allah ba zamu ƙara ba

Ramlat kuwa sai hura hanci take domin tare suka tashi da azzam ya bata shekara ukku saboda shi taƙi yin aure yanzu haka tana aiki a asibitin kura ta ɗauki hutu ta tawo nan gu ta samu ta zauna tace

hajiya ki haƙuri insha allah ba zamu ƙara ba yaran nan ne basu da kunya

hajiya turai tace

yusrah ki basu mukullan ɗakuna su zaɓa wannan barin ku gu ɗaya a kwai matsala

wani uban murmushi ta saki me cike da ma'anoni tace

"To hajiya ,

miƙewa tayi ta tashi domin wallahi ba zasu zauna a ɓamgaran nan ba in da ake kai baƙi zata kai su ba har gori sukai mata ba

wannan kenan garin kura

fitowa tayi ta zabga wata uwar hamma ɗakin kahu labahani ta kalla tuni wata dariya ta kubɓuce mata ta dinyi harda ruƙe ciki ganin saminu ya shigo yana waka tayi sauri ta haɗe ranta tace

"ke saminu zo ka siyomin indomi da ƙwai,

washe baki yayi domin yasan in ta aike shi tana yi mai hasafi abin hannunta be rufe mata ido ba yace

"to anty binta gani ,

ɗaki ta shiga ta miƙo mai ATM card ɗinta tace

"kai ma ka siyi ta 500 sauran ka daÉ—e ,

anty binta bazan dade ba allah isa kar in sami lahi

Banza tayi mai ta sami gu ta xauna tana yar waka aguje kahu labahani ya fito riƙe da ciki da alama bayi zaishi ga ɗaga murya tayi tace

"kahu lafiya kake tafiya a ɗur ƙushe?,

wani to tuƙuƙin bakin ciki ne ya zomai huya yace

"Binta ƙar de duk abin da akai ki ce baki jiba ?,

Zaro manyan idanuwanta tayi tace

Kahu ban sani ba me akai
Chapter 5 · 0% Book details