← Book details Awa 48 A Zirin Gaza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 10

Sashe 9

Awa 48 A Zirin Gaza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hankada dan sandan dake gabana nayi tsalle gefe guda, bindigar na sauka akansa yayi kara kafin ya
fadi idonsa ya juya yif ya fadi kasa kamar itace
.
Ganin haka daya dan sandan yaja da baya ya fito da bindigarsa daga kugunsa a cikin rigarsa, kamar
na rumbacceshi ta irin salon da aka koya mini yadda ake kwace bindiga in an rutsa mutum,
.
Amma ganin bayana akwai soja da bidiga, naji gabobina sun tsaya cak kamar an zaren min laka,
sanyin karfen bindiga akeyata shi ya karyan lago Shuraih Usman inkiya 99%
.
"You are under arrest" sojan ya fada da kakkausar muryarsa, na daga hannuna sama "kayi amfani da
karfi akan jami'an tsaro" na bude baki zanyi magana sai naji kakat yana shirin harbi don haka na
tsaya kam bana ko motsi
.
A hankai suka bincike jakata suka dauken american express card dina da kudina sam dala dubu
ashirin dina na takardar dala dari dari acikin sin kinsu, suka dauki fasgo dina suka bincike kasar
jakar suka dauko sarkar wuya ta nagis, suka duba sosai "ancient atiquity" dan sandan ya mikawa
sojan, yadaga sosai precious jewellery of the middle age " ya saka a aljihunsa yasa dariya
.
Naji kamar an cire mani zuciyana koda nayi kokarin magana sai "zamu kashe ka yanzun nan" suka
sa dariya cikin kankanin lokaci nayi tunanin sarkarnan ita ta kawoni nan , sannan ga alkawarin dana
yi wa Nagis gashi nazo garinsu mintuna kadan ya rage na kaiga mai sarakar,
.
can na tana ai jiya ba yau bane ,yanzu ina da Shuraih Usman inkiya 99% horon soja na kuma kware
a fagen dabarun yaki naga kuma yaki nayi shi na shiga hatsari daban daban , don haka dole na
kwace sarkar nan ko da zan mutu kuwa, wannan shine abin da zanyiwa Nagis bayan ranta
.
Na saki jikina nakama rokonsu na marairaice har da hawayen karya, mai bindigar yana dan
waiwaya don duba wanda ya suma cikin hanzari na shammaceshi ni kai na nayi nayi mamakin irin
saurin danayi nasa hannuna na bige bindigar da karfi
.
Kafin dan sandan dayake gabana ya danna kuna man bindigarsa ne na dauke shi da kafata tayi sama
cikin sauri da azama na sunkuya kasa, yayin da sojan ya kawo harbi harsashi ya sami dan sandan
aka yayi tsalle ya fadi kasa tum
.
Nakai kasa Shuraih Usman inkiya 99%cikin sauri nayi kwabo na kwashe kafafunsa ya saki bindigar
ya zube da baya cikin sauri da azama nayi tsalle na hau ruwan cikinsa , muka kaure da kokawa
naiya kokawa don ni gwanin kokawane tun ina yaro
.
Ganin nayi biji biji da shi kuma bazai iya galaba da ni ba, ya zaro wuka a kugunsa ya kai min suka
nayi tsalle na goce gefe, ya sake kai mun wani wawan suka Allah ya kiyaye na sake gocewa
.
Ganin na daga shi sai ya tashi idonsa a rufe ya nufi bindigarsa ina share kafafunsa , ganin zaici da
baka dole ya saki wukar don ya ceci hakoransa daga zubewa ban san ya akayi ba sai naji ya kurma
ihu, wukarsa ta nutse a cikinsa jini na zuba hanji waje
.
Cikin sauri na kwashe kudina da sarkar da katuna na na harhada kayana cikin hanzari na rataye
jakata, ina ratayawa motar yan sanda ta gifta kwararon tana jiniya ban san lokacin dana daka wani
wawan tsalle ba na hau katangar rumfar kasuwar nayi sulu a bangon gini, Na dire waje na rarimi
jakata na kama cin gudu
.

Matsanancin gudu kamar raina zai fita ya kaini cikin wani lungu inda palasdinawa suke karfina ya
kare na yanke jiki na fadi, cikin murya mai taushi akayo mini sallama wasu hannuwa suka ci cira ni
zaune na bude ido na duhu ya fara yi "ina ne wajen saukar baki"
.
Na fada ina haki, wani ya karbi jakata yabani dabino, wani kuma ya kuma ya mika mani jaka cike
da tuffa da inibi da lemon zaki
.
YOH KAGA MUSULMAN DUNIYA KENAN
.
Anan zan tsaya maci gaba a page 10
Nidinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99% mamallakin shafin hausaebooks da
Keffians News Teller ke cewa
ALMAU'TU LIL IZRA'ILA
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi daurawa
Littafi na daya 1
Page 10
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
.
Mun isa wani gida wasu matasa rike da bindigogi masu sarrafa kansu suka kewayeni, sun rufe fuska
da makayuwa idonsu kawai ake gani, a kusurwar gidan akwai wasu dauke da "rocket propelled
launcher"
.
Kowanne yana rike da madubin kawo nisa kusa ,muna isa daya ya dirgo yasa sauko yana bani
mamaki, kuma ya tuna min da yadda yan hamas suke dirga yabani hannu muka gaisa
.
"Na hango yadda kayi da la'annun can ka birgeni ko ka taba yaki ne" ya saki hannuna na bashi
labarin zuwana da kuma gaskiyar cewa ni dan jarida ne"
Muka shiga wani dan ofis a kuryar gidan ya saka aka kawo min ruwan sha "nine aba yusuf
mataimakin shugaban Hamas reshem zirin gaza da kewayenta, jin haka murna ta rufeni sosai , don
wannan shine mutumin da Abuja'afar yace na nema a zirin gaza Shuraih Usman inkiya 99%
.
Naji kamar nazo gida , nayiwaa Allah godiya daya saukaka min abubuwana haka , amma duk da
haka ban saki jiki da suba don gani nake kamar basu bane
.
Wayewar gari da sanyin safiya unguwar jeninta cike da matasa birjik , na fita daga layinmu na ktsa
cikin jami'an tsaro cikin tsoro, na isa wani dan banki da ake canjin kudi na dade ina bin layi,
.
Ina gaf da zuwa kanta suka samu umarnin tsaida harkokin banki kai tsaye,dana nemi dalili matar da
take kanta tace "sabon tashin hankali ya barke a zirin gaza yanzu ba shiga ba fita an rufe ko'ina"
.
Gabana ya fadi Allah yasa dai ba abin da ya sameni a sarayebo bane za'a maimaita ba nace araina
"waya bada umarnin " na tambayeta
"Peoples committee" tace dani sai na gane kwamitin jama'a na palasdinawa na ya bada wannan
umarnin ba gwamnatin izra'ila bace
.
Kamar yaddaa na fara fashintar abubuwan tun daga jiya a wajen Abu yusuf Shuraih Usman inkiya
shuraih 99% ke typing

.
Jama'ar cikin gari suka harzuka suka hau kan titi suna zangar zangar lumana na fice daga harabar
bankin ina tafiya ina waige waige, na shiga wani shagon sai da shayi don na karya, kuma naji
tsegumi
.
Na fara shan shayin kenan sai naji kabbara ta kaure akan titi, motocin yan sanda suna kawa da
jiniya daban daban cikin sauri na kurbe shayin na fito na tsaya a bakin titi don na kashe kwarkwatar
idona
.
Matasa mata da maza , yara da manya dauke da kwalaye an rubuta tsinuwa da la'anta ga mamayar
yahudawa, wasu anyi rubutun ayoyin jihad, wasu kalmar shahada aka rubuta
.
Suna tafe suna kabbara suna tsinuwa yahudawa da gwamnatinsu, sahun gaba ya kunshi matasa
majiya karfi da kuma wasu yara kanana cikin jan kaya, matasan suna sanye da bakaken kaya dun
suna rawa irin ta soja na gabansu ya rike wata jar tuta an rubuta INTIFADA,
Shuraih Usman inkiya 99%
.
Gefensa matasa suna zarya suyi gaba suyi baya cikin azama da kumari a bayansu wasu suna dauke
da tutar palasdinu da kwalayen da suke kira ayi tawaye, wasu an yi kalmomin masu daraja da ayoyi
masu tsarki
.
Suna tafiya cikin jin karfi suna buga takalmansu a kasa da karfi kasa tana rawa bayansu wasu
matasa sunyi shiga mai ban sha'awa suna jan tutar izra'ila a kasa wani na dauke da kwali a bayansu
an rubuta death to izra'ila
.
Haka suka ringa shigewa kungiya kungiya sahu sahu cikin tsari gwanin ban sha'awa, nan da nan jiki
na ya dau tsima kamar an yimini allurar karfin jiki
.
Kawai ina tsaye sai naji kafata tana tsima kamar an kada mini gangi, koda wani ayarin cike da
matasa majiya karfi yan bana bakwai wanda suke sanye da bakin wando da farar riga da jajayen
kyalle a goshinsu , suna waka suna rawar soja suna zarya suyi gaba da gudu su dawo baya Shuraih
Usman inkiya 99% suna fadin;
.
Shahada maganin mutuwa
Allah bamu shahada
Allah a gaza mana
Allah karya yahudu
Allah karya amurka!!!
.
Wannan wakar na sha jin yan hizbullah suna rera ta alokacin dana ke bosniya, ban san lokacin dana
amsa musu ba, ban yi aune ba sai na tsinci kai na a tsakiyar yan zanga zanga cikin yan mintuna sai
na ganni a sahun gaba
.
Ina rawa ina waka ina juyi ina buga kafata a titi, kamar ba ni ba duk hatsarin da nake ciki na manta
cewa bafa a kasarmu nake ba, na mance kasar izra'ila nake, na manta a bin daya faru jiya atsakanina
da jami'an tsaronsu, bana shakka kuma ana nemana, dadin dadawa kuma lokacin da aka kayade min
saura kadan kuma yana cika akan dole na fice ko su shiga farautata,
.
Amma gaskiya duk wanda ya saba shiga rawar sojoji ko zanga zanga ta fito na fito yasan cewa duk
wani hatsari ko tsoro bacewa suke yayin da kaga ayarin masu zanga zanga na ficewa tya gabanka,
komai mantawa zakayi dashi har sai ka shiga sannan hankalinka zai kwanta,
.
Chapter 9 · 0% Book details