← Book details Awa 48 A Zirin Gaza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 10

Sashe 2

Awa 48 A Zirin Gaza Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Toh anan zan dakata Tambayata anan shine
MAI NE NE SUNAN MARUBUCIN LITTAFINNAN
.
AWANI SHEKARA YA WALLAFA WANNAN LITTAFI
Bazan ga masu cika bakin cewa wai su suna karanta tsoffin littatafan hausa
Daga naku shuraih 99%
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi Daurawa
Littafi na daya 1
Page 2
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]
Lokacin daya juya na naji yayi tsaki yace "we don't know who give you this pucking visas....."
Na dan tsaya don naji karashen maganar jami'in tsaron ya rike kafada ya hankadani gaba "you are
not welcome here"
Turanci irin na amurka
.
Hankalina ya tashi gaba daya yayin da muka fito muka shiga dakin da akayi min bin cikie na zauna
ina jiransu su tattaro min kayana .
Raina ya gama baci matuka ainun don ba irin wulakancin da ban gani ba wajen binciken nan
tambaya kamar wanda aka kama da laifin kisan kai
.
Aka garomin fasgo din akan tebur ya fado kan cinyata na yunkura na dauki jakata , don haushi ko
budawa banyi ba na saka a ljihu, na figi jakata na saba a kafada nayi waje fuskata a daure rai na
abace
.inajin takun sahun mutun yana biye dan yana kokarin kwantar min da hankali wai ba sun yi min
hakan don wulakanci ko kin bako bane sunyi ne don matakan tsaro
.[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]
Ni dai ko sauraransa ban yi ba da haka ya rakoni har tsakiyar filin jirgin saman abin dauya dameni
kawai in rabu da wadannan yan wulakancin in dawo sayarebo wajen kausar ko hankalinta ya
kwanta ni kuma inji sanyi a raina saboda ganin masoyiyata
.
Mutumin yayi min rakia zuwa kofar wani jirgin saman "swiss air" ina kokarin mika "boarding pass"
dina na shige jirgin sai naji an rike min hannu ta baya , na juya a hankali na dube shi tsaf, dogo ne
fatar jikinsa jajaja alamar ya zauna a kasa mai zafi ,
.

Idonsa kanana masu launin toka toka , gashin kansa ruwan gitsawa yana da gashin baki ba gemu
.[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]
Ya mika mini hannu nine mr Ros ina son ganinka a ofis dina
Wannan kalaman sun bata mini rai kwarai sai naji kamar ya kwaro min ruwan zafi, cikin sauri na
nuna masa bodin pas "bana bukatar ganawa da kowa ba kun koreni ba na jefa masa maganar cikin
gadara
.
Alokaci guda nayi kokarin shigewa ya rikeni gam " haryanzu kana cikin kasar izra'ila don haka dole
ka mutunta dokokin karsa, ka biyoni kada kaji komai"
.
Naso nayi gardama koda na lura jami'an tsaro suna yimin muzurai kuma na san cewa ban shiga
cikin jirgin ba dana shiga to nabar izra'ila kenan, ina cikin inuwar swizland" dole subarni ganin haka
dole na rufawa kaina asiri na bishi duk jama'a suna kallona sun kuma san cewa da walakin goro
amiya wannan shima ba karamin wulakanci bane , ace cikin dubbai an tasa ka gaba kamar barawo
kowa na kallonka
.
mintina biyar a tsakanin ya miko min takardar iznin yawon bude ido a izra'ila amma banda wasu
wurare daya kira "security zone" na duba takardun na ga babu iznin zama a telaviv da kewayanta
sannan kuma an rubuta baro baro kada na shige kwana uku a kasar
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne].
Na nutsu sosai wata tambaya tazo min me yasa yanzu aka bani izini bayan angama wulakantani an
galabaitar dani an koreni kuma meyasa aka bani izni bayan da an mini cikakken bincike an gano ni
hatsari ne ga tsaron izra'ila har an koreni don a huta da kaya sannan kuma a kirayoni a bani iznin ba
wani kace na ce , lai lai da sake wai mai kaza ya tashi da kai, don haka nace dole nayi taka tsantsan
da mutanen nan sai maganar shugaban hizbulla a sarayebo ta fado min "zasu iya binka su halaka
ka"
**************************************
Rana ta raba sama gari ya dauki zafi sosai na duba agogona na ga shabiyu da rabi na rana , na shafe
a sama da awa biyar kenan a filin jirgin saman ana yimin tambayoyi da binciken bin kwakwaf
.
Na fito harabar filin jirgin tare da dan rakiyata inda jama'a suke zirga zirga a wajen akwai wajen
ajiye motoci masu zuwa filin jirgin.
Akwai kuma wajen ajiye motocin haya da bas bas na alfarma sunyi layi , sai ka fadi inda zaka kuyi
tsada da direba
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne].
Kai tsaye ko kuma kaje ofis dinsu idan kana da kudi da yawa ka cashe musu kudinsu su baka direna
ya kai ka duk inda kake son zuwa iya tsahon zaman ka a kasar, idan kuma kai sananne ka iya hayar
motar har iya zamanka.
.
Na dauki hayar mota ajin masu kudi duk kuwa da cewa ba matsala bane a guna amma ina da wani
abu araina
.
Muna shige shigen karge na jami'an tsaron filin jirgin sama na faa fahimtar halin kuncin da
falasdinawa suke ciki.
.
Duk ina da naga ana aikin kaskanci ko aikin wahala idan na tambayi direna sai yace falasdinawa ne.
Ina son tambayar dalilin daya sa falasdinawa ne kawai suke aikin kaskanci sai naji gabana ya fadi
Ras. Don haka na kanne nace na bincika da kaina
.
Yayin da yake shigowa yakin cikin birnin telaviv lokacin na kuma ga wani abu daban wato taruwan
jami'an tsaro da sojoji dauke da makamai kamar ana yaki, motocin yan sandan tarzoma suna zirga

zirga ko'ina rike da bindigogi da rediyon walis a kugunsu suna lura da kowa suna muzurai kai kace
jiya jiya ne akaci garin da yaki.
.
Gaba daya yanayin garin ya sauya ya koma irin yanayin filin daga , a gaskiya har yasa tunanin tuzla
ya fado mini arai, naji na kasa jurea har zuciyata ta fara bugawa da karfi, na dubi wanda yake
gefena wanda shine dan rakiyata "tourist guide " na kalleshi sosai "wannan jami'an tsaron haka
lafiya kuwa?" Na tambayeshi tun daya shigo baice komai ba sai a lokacin
"Sune dakarun zaman lafiya" ya dauke kansa yana kallon waje a daidai lokacin wata mota ta gifta
mu na lura da ita ganin yadda ya kalleta, sabuwa ce mutum biyu ne acikinta daya yana magana ta
rediyon walis dake cikin motar babu fallen rubutun lamba, bayanta kuma wata ta shigemu an rubuta
"first class citizen" dan kasa mai daraja ta daya. Ba a jima ba kuma wata ta shige da lambar "third
class" da fari dai banyi niyyar tambaya ba saboda yadda naga na kusa dani yana kallona amma cikin
dabara sai na jeho tambayar"mai daraja ta daya" meye kuma haka ya dubeni zaiyi magana sai
mukayi burki a shigen jami'an tsaro
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne].
A gabanu jerin gwanon motoci suna tafiya a hankali zuwa kofar shingen sojoji da yan danda wasu
dauke da bindigogi suna muzurai, wasu kuwa suna rike da na'urorin bincike irinsu na'urar sansanar
bomb data binciken bindiga wasu kuma suna takardun mutane sunayensu da kuma gurin da zaus da
lambar motar da matsayin mai motar wato bako ne ko dan gida ne, shi din ma wacce daraja yake da
ita kuma wanne jinsi ne bayahude ne ko balarabe "kai wadannan mutane da rashin yarda suke"
bansan lokacin da wannan furucin ya fito daga bakina ba sai dai nayi sa'a da harshen hausa nayi shi
.
Mutumin dake kusa dani ya kura mini ido ya kalleni sosai, adai dai lokacin kuma motarmu cikin
sanda ta kai ga kofar shingen wani soja rike da bindigarsa kirar amurka m16 ya iso cikin sauri ya
sunkuya tun kafin yayi magana direban ya bashi takardunsa sukayi magana, ga alama dai sun saba
da shi na lura lokacin daya mika takardunsa sinyi musanyar alama ta cikin dabara cikin na lura da
su ta wutsiyar idona
.
Wani ya karaso dauke da wani dogon karfe mai fadi daga karshen sa kamar shebur ya karasashe a
karkashin motar sannan ya umarcemu mu fito ya kara mana na'urar binciken bindiga, ya bukaci
fasgo dina na mika masa ya buda ya dubeni sama da kasa
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne].
Yayi magana sojoji cikin sauri suka baibayeni kafin kace kwabo har wani ya doramin bindiga a
wuya , sunyi mamaki da suka ga ko gezau banyi ba ni mamaki kawai suke bani ba tsoro ba,
Na dubesu daidai cikin natsuwa "ka keta dokar kasar izra'ila "wata murya ta fada a bayana nayi
kokari na waiwaya don yin tozali da mai maganai suka hanani motsawa "what is the hell with you"
na fada cikin fushi "you are deported" murya ta mayar mini duk jami'an tsaro dake wajen suka juyo
guri na cikin sauri suna jiran cika aiki kamar kare ya hango muzuru
.
Toh anan zan tsaya don na gaji
Sai mun hadu ranar friday
Daga shuraih Usman
Inkiya shuraih 99%
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi Daurawa
Littafi na daya 1
Page 3
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]
Chapter 2 · 0% Book details