← Book details Awa 48 A Zirin Gaza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 10

Sashe 3

Awa 48 A Zirin Gaza Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Cikin hanzari na fisge fasgona daga hannunsa na buda wani shafin na nuna musu inda aka buga
mini iznin shiga kasar kuma na cire "tourist visit permit" na nuna musu a daidai wannan lokacin
wata mota jif patrol ta soja tayi birki a gabanmu akwai eriya doguwa a jikin motar
.
Wani manjo janar din soja ya dirgo kato ne mai katon ciki kamar tulu da walis a hannunsa fuskarsa
kamar an aiko masa da mala'ikan mutuwa a turbune babu wani annuri
Idanunsa irin na kyanwa kumatunsa kamar an sassaka, mai zagayyar fuska yana da saje da gemu
buyya wanda ya maida shi tamka dattijon biri
.
Kafafunsa shafta shafta kamar dirka, kafarsa daya tafi daya tsawo abinda yasa tilas yake tafiya irin
na kaguwa ya na dinkisawa a birkice
.
A kowane gefensa wasu matasa madaka kare suna biye da shi, kowane da karamar mashigan rike a
hannunsa sun gama shirin tsaf suna shirin bude wuta jiransa kawai suke yace ket su cika aiki.
Duk suna sanye da kayan soja mai rodi rodi , sauran kuma cikin motarsu suke suna masa rakiyta
duk sunyi shirin kota kwana , yana karisowa gurin sauran sojojin a sauran jami'an tsaro suka sara
masa sukayi cirko cirko wani kurtu ya fara masa bayani da yahudanci, ya dubi ne yayi musu
magana da amon sautin jemage
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne].
Nan take suka janye bindigoginsu daga saman sukayi sororo da su suna sauraransa cikin tsoro da
girmamawa kai kace mala'ika neshi .
Wannan girmama ta bani mamaki
.
Ya karen kallo tsaf ya karbi takarduna ya duba su a hankali cikin takama, kasaita da nuna isa ya
gama ya sake kallona yayi magana daga cikin motar sai naga wal hasken fitilar daukan hoto na
tabbata hoto na aka dauka , kawai sai naji sautin jemagen yana furta kalmomin turanci "be careful
don't do anything wrong like gathering information or tres-passing into security zone or any no go
area" yayi murmushin mugunta ya girgiza kansa "I will teach you a lesson that you will never forget
throughout your life "
Ya kalleni ya nuna ni da dan yatsansa cikin wani sauti mai tsoratarwa yace " kada ka tara ko ka
rubuta mummunan rahoto akan kasar izra'ila kada ka kuskura ka aika da labarai a ciki ko a wajen
izra'ila idan ka saba wannan ka'idodin yan yatsunka zasu baka amsa"
.
"I will cut this into pieces if you write mischief against us Mr goyim remember I am major dayin
robert" ya kalleni sosai ya kada kai ya juya yana dingisawa ya shige motarsa suka rankaya a guje
suka barni anan ina gumi ina yarfewa, sautin maganarsa yana kararawa acikin kwakkwalwata
.[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]
Mun karaso birnin telaviv da la'asar, yunwa da gajiya da zulmin major doyin yasa abun duniya ya
dameni
Na lura lallai nan ba wurrin da yan jarida suke da yanci bane , banayi binciken abubuwan da suke
raina .
Ko'ina jami'an tsaro da sojoji ne birjik kamar wani sansanin yaki, irin shingayen da na gani a hanya
tamkar wani filin daga ne daya fada hannun abokan gaba , irin yadda ake binciken mutane daga
inda suka fito da inda zasu da kuma abin daya fito da su sai ya tuna mini kasar afirka ta kudu
alokacin wariyar launin fata inda bakin mutum bashi da iznin zuwa wani gari sai da takardar izni
idan turawa sun amince da dalilin zuwansa a bashi kayadadden lokaci idan kuma lokaci yayi ya fice
ko ya yabawa aya zakinta
.
Direba ya dauke hanya yaki shiga dani cikin birnin ya zarce dani wani gari a bayan telaviv JAFFA
inda larabawa ne suke zaune a cikinsa
.

Dana nemi dalili yace wai ba bashi iznin kaini cikin birnin tel-aviv ba "doka ta hana shiga da bako
sai da izni na musamman"
.
dana ji haka nace ya kaini otal mai saukin kudi ba wai don babu kudi isassu ne aguna ba , ina da
kudi masu yawa wanda na samu daga wajen kaosar dalar amurka cinkus a jakata kuma duk binciken
da akayimin ba wanda ya damu da kudina ina dauke da "america express card" don gudun sata ko
shiga halin kaka ni kayi naso zama a otal mau saukin kudine don na samu cudanya da talakawa da
sauran mutanen da ake samun labarai barkatai a gunsu
.
Sabo da yar gogayyar dana samu a aikin jarida , na lura mutane masu kudi ko fada aji basu cika
fadar labaran rayuwansu ba, ko abinda jama'a suke da sha'awa akansa na halin zamantakewa ko
halin musgunawa daga hukuma , su kullum suna boye labaransu suna kuma kaffa kaffa da abinda
zasu fada a ko'ina suke, sannan kuma hukuma bata cika musguna musu ba, don haka basa sukarta ,
Bihasali ma ra'ayinsu shine ra'ayin hukuma amma ta zama cikin talakwa kuma larabawa zai kai ni
na samu na kai ga bin da na zo nema ba tare da katsalandan din jami'an tsaro ba
Matsala ta itace wannan dan rakiyar dole nasan yadda nayi na yarda shi cikin dabara
.[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]
Tafiyar kamar mil shida daga tel-aviv muka yi kwana zuwa dan gari mai girma da ake kira jaffa,
abubuwan danagani sun bani mamaki kwarai , gidajen larabwa falasdinawa wasu sun rushe wasu
kuwa sun dade da zama kango, wasu kuma ga suna ,rabi a rushe rabo a tsaye , babu wani gyara
kamar wani sansanin bayi ,
Jami'an tsaro da suke safa da marwa sun maida garin kamar garin da aka fafatawani yaki
.
Abinda zaka fara fahimta shien talauci yayiwa mutanen farin kanta na tambayi direba dalilin da
gidajen wasu suke a rushe "basu da iznin gyara gidaje" ya fada mini
.
Wannan amsar ta bani mamaki mutum da gidansa wai sai ya sami iznin gyarasa, zan sake tambayar
naga dan rakiyata yana kallona sai kawai na kanne dana tuna da maganar mr doyin , muna dada
ratsa garin jami'an tsaro suna kara yawa suna tsaida abin hawa suna bincikawa suna buda kaya
sannan su caje mutum tsaf
.
Da kayi wata gardama sai su kama mutum su garkame shi acikin wata shiga ba biya.
Wannan abubuwan din bani mamaki da tsoro da haushi alokaci guda, domin wannan babu wata
maraba da mai mutane fursononi a garinsu ko daurin talala mai kamar sake
.[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]
Mun isa babbar kasuwar garin karfe biyu da rabi na yamma munje don nayi saye saye sannan ya
wuce dani gidan saukar baki
Tun kafin na fito daga motar naga matan larabawa suna saye da sayarwa cikin fara'a wasu suna sai
da kayan marmari da yayan itace .
.
Alokacin guda kuma wani abu ya bata mini rai matasa sanye da wandon kaki rin na soja da fara
singileti sanye da wata hula yar karama mai kama da yar madina shudaye mai ratsin fari suna rike
da mashigan suna bi layi layi , rumfa rumfa kamar duba gari kasancewar su agun sun mai da
kasuwar kamar kurkuku
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne].
Can na hango wata katuwar rumfan sai da kayan mar mari iri iri kamar su tuffa lemon tsami dana
zaki kala kala, akwai dabino da inibi kala kala da sauran yayan itatuwa ,yawuna ya guda don haka
na dauko jakata na rataya na doshi rumfar "ina kuma zaka" direban ya tambayeni " zan sayo kayan
marmari a wancan rumfar" na maida masau
.
Chapter 3 · 0% Book details