← Book details Awa 48 A Zirin Gaza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 10

Sashe 4

Awa 48 A Zirin Gaza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nayi sallama a kofar rumfar wata balarabiya sanye da dogon siket har kasa ta sanya riga mai dogon
hannu ta yafa mayafi kato ya rufe tun daga kanta zuwa kaurinta tana fara'a ta tareni "ahlan
wasahlan" tayi min nuni dana shigo ciki"marhababika ya akhi"
Ta nuna min kujera na zauna ina shiga kanshin yayan itatuwa suka bigi hancina sha'awa ta
motsa ,kanshin ni'ima na kayayyakin marmari ya kaure rumfar
.[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]
Cikin fara'a ta tambayeni sunana da kasar dana fito na gaya mata ni dan najeriya ne sai kawai cikin
sauri ta bani ruwan sha ta jinjina min "nayi farin ciki da ganinka saboda dan uwana yana kasuwanci
acan " ta fada cikin larabci
.
Sannan ta dauko jakar saye syae ta cika mini da kayan marmari ina kokarin ciro kudi na biyata ta
riken hannu tace "kyauta na baka dan uwa na, saboda ina son musulmin Nageriya "
Na gode mata na gaigaisa da sauran mutanen da ke rumfar na fito kofar rumfar ta biyoni "ina ne
masaukinka kwana nawa zaka yi " na bude baki zan bata amsa kenan sai wata kara mai karfi da
fashewa ta abku, wuta da hayaki a lokaci guda suka watsu cikin sauri na saki ledar da ke hannunsa
na watsar da jakata na rumbace ta muka zube a kasa , nayi haka don gudun kada tararratsin bomb ya
same ta
.
TOH FA DAN JARIDA YA FADA HATSARI
Daga shuraih usman
Inkiya shuraih 99%
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi Daurawa
Littafi na daya 1
Page 4
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
Daga kowacce kusurwar kasuwar sai mutane ne ke runtumawa a guje , daga nan kuma sai harbi da
bindigogi masu sarrafa kansu ya biyo baya abin da yakara yamutsa gun kasuwar ta yamutse ,
.
Hayaki ya turnuke sama kura ta tashi hargowa ta cika ko'ina mutane da gudu suna tsallake
rumfunansu ko rufe su basu yi ba wasu sunyi karfin hali sun tsaya rufe kofofinsu
.
Cikin sauri na samu naja jiki na rakube a jikin gyaren rumfar ita ma tayo ciki, cikin sauri muka rufe
kofar ta matse matsen kofar na samu wata yar kafa data bani daman kallon abun da yake faruwa
acikin kasuwar
.
Matasar dana gani suna kaiwa da komowa a cikin kasuwar rike da bindigogi suna harbin mutane na
tabbata falasdinawa suke harbewa
.
Cikin mintina biyar kasuwar ta yaye ba kowa sai jami'an tsaron yahudu suna zirga zirga wasu a kasa
wasu acikin landorobobi
.
Suka shiga kama wanda aka harbe suna jefawa acikin motocinsu wasu kuma suna bin falasdinawa
da gudu suna kamasu izan sunyi gardama sai su harbesu wasu kuma suna kofofin rumfunansu suna
kamo mutanen da suke ciki wannan yasa na gane dalilin dayasa wasu suke guduwa daga
rumfunansu
.

Matan ta mike ta janye katakon da ake leken waje nan da nan ta rude ganin suna ta jifgar mutanen
da suka kama , na lura da inda motarmu ta tsaya ba komai sai karikiceta dai-dai da direbanmu cikin
jini, hannunsa ya cire idonsa ya fita sai kafarsa ce take dan motsawa ganin wannan ya tayar min da
hankali sosai bansan lokacin dana fara kyarma ba zufa na keto mani , "wai da ban fito sayen lemo
ba da yanzu bani " nace a raina
.
Motar asibiti tazo tana jiniya tazo ta kwashe gawarwakin mutane ban san kowane bane , akwai
wasu mutum hudu da suka rasa sassan jikinsu motar janwai motocin da bomb yayi kaca kaca da su .
.
Ko mintina goma sha biyar ba ai ba an kwashe gawarwakin an janye mushen motocin an wanke
jinin . Wama ya nuna cewa lallai yahudawa sun shirya da irin wannan ranar sosai kuma basa son
kowa yasan irin barnar da suke
[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
.
Ina shirin cewa ta bude kofar ganin kura ta lafa sai naji hayaniya da kawar mutane sai na hango
mutumin da muka shigo mota tare ya shiga motar jami'an tsaro ya tafi da fari nayi mamaki amma
dana tuna akasar yahudawa nake ko ince kasar da su ka kwace da karfin tsiya banyi wani mamaki
ba
.
Alokacin da motar shiga-ba-biya take shirin ficewa daga kasuwar a lokacin hayaniyar jama'a ta
karaso cikin kasuwar wasu matasa a guje suna kabbara suna jifansu da duwatsu suna tunkararsu,
.
Batare da ko bindiga ba kowani kwakkwaran makami ba , ganin haka ban sana lokacin dana
wangame kofar ba na fito don na kashe kwarkwatar idona ba
.
Rannan naga ikon Allah matasan falasdinawa suka taho gadan gadan ba wani tsoro ko fargaba a
guje a daya barin soja da yan sandan izra'ila cikin sauri suka dinga dirgowa daga cikin motocinsu
wsu suka durkusa wasu suka sunkuya wasu kuwa suna harbi suna gudu da haka suka tarbi
falasdinawa masu jefa da duwatsu kamar soja yayi karo da abokin gabarsa soja afilin daga [shuraih
usman inkiya shuraih 99% ke magana]
,
Mamaki da al'ajabi ya kamani ,ina mamakin yaya soja da muggan bindigogi zai harbi farar hula da
bashi da makami, alokaci guda kuma ina al'ajabin yadda akayi mutum ba komai a hannunsa ya
tunkari mai bindiga ,
.
Aka ja daga daya barin karar bindiga daga daya barin kuma kabbara gurin ya kaure
.an shafe sama da mintina ashirin ana dauki ba dadi falasdinawa suyi kora soja da bindiga kaga ya
ruga da gudu har yana fadiwa, in anjima kuma kaga falasdinawa suna gudu abin kamar al'mara ,
.
An harbi falasdinawa da yawa an jikkata wasu wani abu daya bani mamaki shine duk wanda aka
harba yana faduwa na bayansa zai zo da gudu ya daukeshi
[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
.
Sannan kuma wani nan take zai maye gurinsa, don haka babu wata gawa ko masu rauni da sojan
yahudawa suka kama
.
Ana cikin haka sai wasu falasdinawa suka hau saman rumfunan suna kabbara , suna jifansu da
duwatsu wasu kuma suka biyo ta bayansu ganin za'a yi musu kofar rago sai suka jefar da wadanda
aka kama suka tsere a guje n nan da nan kasuwar ta rude da kabbara da sowar falasdinawa suka
mamayeta
.

Wannan shine abu na farko daya bani mamaki a saukata a cikin falasdinu . Na kirata falasdinu
saboda shine sunan halal ba izra'ila ba kamar yadda yahudawa yan kaka gida suke kiranta
.[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
Tambayar da nake yiwa kaina kuma na rasa amsar ta shine wane abu ne ya ingiza mutum ba
makami ya kori mai bindiga har ya gudu yana faduwa yana barin bindigarsa
.
Me ya baiwa falasdinawa karfin guiwa har suka fuskanci yahudawa rike da bindigogi duk da sun
san cewa harbesu zasuyi ga kuma sheda agansu sunga an kashe da damansu,
.
Sannan kuma wane daliline yasa mutum yana gani an harbe dan uwansa zai tsallake gawarsa ya
shige gaba ya kuma tabbata shima harbeshi za'ayi sannan kuma me yasa suke dauke gawan wanda
aka harbe
.
Wannan tambayoyin da wasu irin kamar son jin dalilin da ko'ina aka saka jami'an tsaro suna gadin
dauka cin garin kamar anci garin da yaki kuma na ajin tsoron kwace shi koda wane lokaci, me yasa
aka tsaurara matakan tsaro bayan kuwa su falasdinawa ba su da makamai da zasu iya yaki da
yahudawa,
.
Kai kona kare kai basu dashi sannan wata kuma me yasa duk matakan tsaron nan ba su hana
falasdinawa yunkuri da yin bore a kasuwa ba ?
.[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
Hakika wadannan tambayoyi ne da suke bukaar amsa wanda duk wani dan jarida mai kishin aikinsa
zai so ya gane bakin zaren abin da na kuduri niyya kennan duk kuwa da cewa ba neman labari na zo
ba , na zo ne neman yar uwar NAGIS don na bata sarkar wuyanta to amma yaya za ace ni HADI
dana shiga cikin runtsi a bosniya lokacin da ban san komai ba a dabarun yaki, yaki ta rutsa da ni na
fito lafiya cikin ikon Alla
.
Sannan ga wata dama ta samu ta aikin jarida na hakika na kiyin wani abu sam-sam ba zan iya
hakuri ba idan kuwa na hakura ban bincika na , to ba sunana hadi hantsi leka gidan kowa ba, neman
labari ya zame mini jini da tsoka don haka naji ba zan iya barin wannan damar rubuta halin kunci da
kuntatawa da yan uwana musulmin falasdinu suke ciki ba.
.
Wannan shiya sauya mini makasudin tafiyata, shu'urin aikin jarida ya motsa sai dai kuma na san
cewa nan fa ba a maraba da yan jarida domin yahudawa sun san tasirin yada labarin abun da suke
aikatawa, don haka basa yiwa yan jarida da suke aiki bil hakki da wasa , saboda basa son duniya taji
labarin irin danne hakkin dan adam din da sukeyi .
.
Kawai sai na gabana ya fadi ras dana tuna da gargadin mr. Doyin
.
Har kullum dai nine Shuraih Usman
Inkiya shuraih 99%
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi Daurawa
Littafi na daya 1
Page 5
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
Na bude kofa zani wajen da aka fafata matar nan ta riken hannu " kai bako ne kada kaje su kamaka
bari in rufe muje gida in saukeka" ta fada mini sunanta "ismi zulaikha" ta fara hada kayanta cikin
Chapter 4 · 0% Book details