← Book details Awa 48 A Zirin Gaza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 10

Sashe 7

Awa 48 A Zirin Gaza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jirage na faduwa kasa suna ci da wuta , wasu kuwa a sama zasuyi bindiga su watse hayaki ya cika
sama kaman gajimare mizayal sam 6 yana harbo duk jirgin daya tashi sama sosai kamar kafa 40,000
a sama wanda yayi kasa kasa domin yin bomb akan tankoki zai ci karo da sam 3 ko sam 2 wanda
aka saita su don harbo jiragen da yake kasa kasa
Shuraih usman 99%
.
Tarun ayarin tankokin yakin da izra'ila ta turo a yakin sinai sun sha wuta sun yi dai dai suka watse a
cikin hamada suna cin wuta, saboda sun gamu da sabon makamin kone tanka, don haka tarun
tankoki sama da dari hudu basuyi komai ba
.
Illa zama kaskon suya yahudawa, tilas sojan suka fita daga tankokinsu suna jifa da makamansu da
hulunan kwanansu suna zubawa aguje suna ihu
Wasu sun bace a hamada wasu sun haukace wasu sun kurmance ko'ina takalma da hulunan da belt
da bindigogi kirar amurka zaka gani birjik
.
Sojan kasar siriya sun kai farmaki daga barin gabas takan tudun golan sun share sojojin izra'ila
acikin AWA 48 suka danna har wasu kauyuka sun kone gevel kibbuts da heamek.
.
Wayewar gari jiragen izra'ila sun kai hari kan garuruwan fararan hula sun kone gidaje da asibitoci
da makarantu sama da mutum 1000 sun mutu a rummaneh.
.
"Mummunan yakin atilare da tankokin yaki ya fara da misalin karfe biyu na yamma bayan da suka
sha kashi a shuraih Usman inkiya 99%
Hannun siriya, tankoki samfurin cneturions da patton suka dirkako zuwa tuddun golan nan suka yi
karo da tankokin siriya aka gwabza yakin tanka mafi muni da tsanani a tarihi
.
Hayaki da wuta ko'ina ga rugugin bom da manyan harsasai da inji tanka kawai zaisa kunnen mutum
ya kurmance, anyi kare jini biri jini ko'ina karekican konannun tankoki da gawarwakine suke yashe
kamar kasa
.
Can kuma jiragen saman amurka na phantom suka dinga ruwan boma bamai kamar ruwan sama
akan tankokin siriya sun yi lugudan wuta mai tsanani na lokaci mai tsawo,anyi daga sosai mutum da
kansa zai bude tankarsa ya fito ya ruga da gudu, sama wuta kasa wuta tsakiya masifar zafi
.
Kashe gari da taimakon jiragen yakin amurka da bayanan sirri na watan dan adam daga amurka,
izra'ila sunyi raga raga da tankokin siriya sun kuma lalata garkuwar makamai masu linzami da suka
hada jiragen izra'ila suka karya Shuraih Usman inkiya 99% rundunar sojan siriya suka sake kama
tuddan golan an sake fafatawa sosai akan golan sama da tankoki 1500 suka gwabza aka yi kazamin
yakin tanka a tarihi
.
Hakazalika wayewar gari a lardin suwiz sojan izra'ila sunyi nasarar karya sojan misira da suka
hauro cikin hamadar sinai, saboda sun kai tankoki masu yawa , sun kumayi nasarar lalata cibiyar
makamai masu linzami da suka hana jiragensu haurawa.
.
Wannan ya baiwa yahudawa damar raunaa ragowar tankokin da suke hamadar sinai ba tare da wata
kiryar mizayal ba , rashin sabbin tankoki da zasu ci gaba musu da raunatesu.
.
Rundunar sojan izra'ila sun keta garkuwan jiragen saman yaki ta yankin sinai sun lalata rumbunan
rokoki da mizayal da taimakon amurka da kayan yakinta da bayanan sirri na watan dan adaam, sun
lalata cibiyar bada umarni ta makamai masu linzami sam 6 sam 3. Amma haka bai faru ba sai da
amurka ta shiga kai tsaye
.

AMma dai kafin wuta a tsagaita larabawa sun kwato Shuraih Usman inkiya Shuraih 99%. Da dama
daga filayensu da izra'ila ta mamaye a yakin kwana shida 1967. Martabarmu ta dawo a idon duniya,
mu larabawa ba abin da muka tsana face ayi galaba da mu kuma a din ga kallonmu a mutanen
banza,
.
Abin dayasa muka samu nasara bai wuce cewa sojanmu sun samu kyakkyawan horo da ingattattun
kayan yaki na zamani irin wanda izra'ila take tinkaho da shi ba, kuma sojojinmu sun shiga fagen
daga da niyyar ko cin nasara ko su mutu, Amma ba su gudu kamar yadda sukayi a yakin kwana
shida ba, mun nuna wa izra'ila cewa mu ba kanwar lasa bane"
.
Matarsa ta shigo tare da wani mutum suka gaisa ni da abduljalil muka yi sallama da shi bayan nayi
masa godiya mai "nine zan gode maka da ka taho tundaga wata kasa don binciken yadda
rayuwarmu take da halin da muke ciki, ka nunan kana kaunarmu kwarai"
.
Ya saki hannuna nayi masa alkawarin zan dawo muci gaba da shira akan halin da aka jefa
falasdinawa a ciki
.
Har na juya zan tafi sai na tuna da maganar neman gidansu Nagiz nayi masa maganar sarkin ramalla
yace " sai na dawo ma ci gaba "tayaya zanje gidan " na tambayeshi
.
"An rushe gidan tuntuni don mu daina tunawa da shi, ba komai yanzu sai fili kawai, amma yana da
'ya'ya ya mike tsaye ya dauki Shuraih Usman 99% kwagirinsa ya rakoni kofar ya sunkuya kamar zai
sumbace ni " yana da diya sunan ta Nagis taana da kanwa Ikram dukkaninsu suna cikin kungiyar
hamas, bansan inda nagis take ba yanzu kada kaje nemansu
.
Ba mamaki jami'an tsaro su halakaka don kowacce ana nemanta ruwa ajallo"
Ya dafa ni kamar yana bani shawara sai ya fadi wasu kalmomi da sunan wani layi a cikin ramalla
yace na tambayi wani mutum na fada masa abin daya fada mini "zai taimaka maka kaga daya daga
cikinsu na gaya maka ne don na amince da kai maga alamar kai mujahidi ne"
.
Muka fito da abduljalil ya shiga mota zuwa gida ni na tafi cikin Ramalla
.
.
Anan zan tsaya sai mun hadu bayan kwana biyu
Nine naku akoda yaushe Shuraih Usman
Inkiya 99%
.
Abun dayasa kukaga bana post kullum kuma banayi da yawa shine
Nafi ga ne nayi post kadan mai amfani
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi Daurawa
Littafi na daya 1
Page 8
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
.
ZIRIN GAZA
--------------------Na shiga garin ramalla a wa daya bayan rabuwar mu da abduljalil kai tsaye na shige masallaci nayi
sallar azahar bayan sallama limamin masallacin ya mike yayiwa masallata wa'azi yana fadakar da su
abin da yake gabansu na fafatawa da yahudawa

.
"Dole ne mu sauke nauyin daya hau kanmu dole mu kwato kanmu daga kan gin bautar 'yan kaka
gida , falasdinu ta falasdinawa ce kuma masallacin kudus na musulmi ne"
.
Kabbara mai karfi tama sallata ta katse shi da aka lafa yaci gaba "duk musulmin duniya ya
haukansu suyi yaki don yantar da masallacin daga hadarin da yake ciki,
.
To amma mune makwabtan masallacin don haka mune zamu fara nuna kin yardarmu , da
bijirewarmu sannan muyi tawaye , mu yi fito na fito mu fafata, mu hautsina da yahudawa don mu
nuna wa sauran musulmin hanya"
.
Aka sake kabbara mai karfi har sau uku, da haka yayi bayani na zaburar da matasan dake cikin
masallacin ya kuma kare da "Allah ya tsinewa masu danne hakkin mutane, ALLAH YA TSINE
WA 'YAN TA'ADDA" masallacin ya kaure da kabbara yayin da ya ce "ALLAH YA TSINE WA
IZRA'ILA, ALLAH YA TSINEWA AMURKA"
(Nima shuraih 99% nace Allah ya tsinewa yahudu, jama'a kuyi comment da Allah ya tsine masu)
.
Cikin dabara wasu matasa suka sashi a tsakiyarsu suka fice da shi daga masallacin suna kabbara
suna daga hannuwa, wannan lamarin ya farkar dani samun wani kuzari a ruhina, duk da labarin
yakin da abuja'afar ya bani wanda yasa jikina yayi sanyi bakin ciki kuma ya rufeni wannan bayanan
da kuma kumaji da kuzarin da ruhin gwargwarmayar dana gani tare da matasan Ramalla ya bani
kwarin guiwa da farin ciki a raina, domin naga alamun daukan fansa a tare da matasan
.
Kai tsaye na tafi inda akayi min kwatance bayan na gama nazarin gurin a taswirar matafiyata dana
saya na nablus, na sauka daga bus na yi tattaki mai dan nisa , kwatsam sai (shuraih usman inkiya
99% bazan taba daina fadin Allah ya tsinewa Izra'ila ba ) jikina ya bani kamar ana bina cikin
hanzari na waiwaya naga wani mutum dogo dan tsattsama yana sauri yasa bakaken kaya da hula
hana sallah.
.
Ina ganin sa gabana ya fadi na sassauta tafiyata na saurara ya cimmini ya dan bangajeni ya shige
.
Ganin haka sai na koma baya ina isa bakin hanya wata motar limousine mai kofa shida , gilashin
motar bakine yana daukar ido ta tsaya a gabana a hankali, ganin ta tare hanya sai na kauce zan gifta
sai naji wata murya kamar na taba jinta amma na manta inda na taba jinta , nayi kamar ban jiba sai
na sake ji " may I give you a lift "
.
Muryar mace matashiya mai taushi lokacin na tabbata na taba jin muryar, don haka na waiwaya
sosai na sunkuya don inga mai maganar, ban iya ganin ta ba, sai gabana ya fadi ras, don haka ban
amince na shiga ba naci gaba da tafiyata
.(Shuraih Usman inkiya 99%
Na fara tafiya amma ban san inda zan nufa ba ganin ina kokarin ciro taswira daga aljihuna sai motar
tayo gaba ta cimmin "can I help you" har zance a'a sai kofar motar ta bude wata yarinya ta fito
sanye da siket iya cinya da tabarau baki a idonta tasa takalmi mai tsini rigarta shara shara wacce ta
bayyana dukkan surinta kusan mamanta a waje suke, hannun ta akwai agogon gwal
.
Ta tsaya a gabana tana kanshin turare kana ganinta kaga ba Amurkiya, hakika na san cewa akwai
inda na taba ganinta amma saboda halin da nake ciki na kasa gane ta
"Kai bakone anan ko" tace dani na dubeta
"Ni dan yawon bude idone " ina gama fada mata nayi kokarin tafiya tayi murmushi
"Ina kake son zuwa ne in kaika "ta duben tayi dariya "kana jin tsorone" jin haka na gaya mata inda
zani
.
Chapter 7 · 0% Book details