Sashe 5
Awa 48 A Zirin Gaza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sauri "motar ku aka sawa wa bomb ko" ta tambaya tana kallona na gyada kai sauran mutanen da
suke cikin rumfar kowa yayi ta kansa
.
Ta shige gaba ina bunta muna gudu-gudu sauri sauri ta kurda can ta kurda nan . Da haka muka fice
daga kasuwar jami'an tsaro suna yiwa kasuwar tsinke , tafiya mai dan nisa ta kai mu wani dan gida
a cikin rukunin wasu jerin gidajen talakawa, duk unguwar larabawa ne acikinta idana kaga
bayahude toh babu shakka jami'an tsaro ne babu ja wai kare ga mutu a saura , sai da cikin unuguwar
babu jami'an tsaro a ciki sosai
.
Tayi sallama ta kwankwasa kodar wani karamin gida bayan yan mintina wata yarinya doguwa
budurwa mai matsakaicin kauri ta bude kofar, gashin kanta har kirjinta tana da fararen idanu kamar
madara a koko ga dogon karan hanci har baka , tana da siraran lebba da yalwar gashin gira
shekarunta zasu kai goma sha bakwai ko sha takwas , muna hada ido ta rufe kanta da mayafi.
.
[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
A hankali ta bude kofar ta karbi kayan zulaikha sannan ta kalleni tayi min barka da zuwa kuma ya
karbi jakata muka shiga dakin saukar baki, shine na farko da cikin gidan daga hannun dama ta bude
kofar tace na shiga na zauna a cikin akwai kujeru guda uku tsofaffi da dan karamin teburin shan
shayi, sai kananan kofuna na shan shayi a gefe guda na wani gadon katako tsoho.
.
Na zauna kenan yarinyar ta shigo da butar shayi ta daureye kofunan dake kan teburin ta zuba min
shayi ta fice tana tafiya cikin nutsuwa, sannan ta shigo da yayan itatuwa irir iri da ruwan sha ta
fita,shayin dana sha ya sana ji karfina ya dawo na kuma wartsake yayan itacen da sha sun gusar min
da yunwa
.
Ni dinne dai Shuraih 99% ke typing
.
Alokacin ne na nutsu sosai na shiga hayyacina na dauke takarda na tsara abubuwan daki daki,
wannan al'adace a gareni duk sanda zanfara wani aiki sai na zauna a tsanake na tsara komai dalla
dalla , saboda kashin bayan cin nasara a kowace irin harka ta duniya kota lahira shine kyakkyawan
tsari, da shiri mai inaganci ,
.
Domin kuwa duk wanda bai tsara al'amarunsa ba to kuwa ya dauki matakin ruda kansa.
.
Abu na farko shine lokacin dana ke da shi kankane ne ,kuma abin da yake gabana yana da yawa, ga
kuma wahala ba kamar yadda ba zata ba, yadda jami'an tsaro suke ta safa da marwa babu wani
yanci walwala, ga tashin hankali iri iri ga harsashi na yawo.
.
Akwai hatsarin na shiga neman yar uwar nagis kai tsaye don ban san matsayinta ba agun jami'an
tsaro ko taba cikin wadanda ake nema ruwa a jallo ,sannan jin cewa ina nemanta kuma na taso tun
daga sarrayebo, wannan zai bada haske ga jami'an tsaro su tasani a gaba don su halakamu gaba
daya,
.
Sannan kuma ban san waye jami'an tsaro waye da leken asiri ba, sannan na tuna da wanda muke
tafiya tare na tabbata dan leken asiri ne , nayi hamdala da Allah ya raba mu cikin sauki
.
Nagode nine dai Shuraih 99%
.
Babban abinda yake damuna nake son kuma sanin bakin zaren shine dalilin da falasdinawa suke
cikin wannan kunci da takura, koma meye harzukasu, suke dauki ba dadi da su haka, Na tsara
komai cikin dabara da yadda zan sami amsoshin wadannan tambayoyi ba tare da wani jami'in tsaro
ya sansano wani abu ba, kuma ba tare da mai bani labarin yasan cewa yana fadamini wani
muhimmin abu labari ba,
.
Zan lullube komai da sunan ni dan yawon bude ido ne da san jin tarihi ne wannan abu ne mai sauki
wajaen kwararren dan jarida musamman idan ya samu kansa cikin hatsari, Amma ba abu ne mai
sauki ba Izra'ila
.
Kuna tare ne dai da Shuraih 99%
.
Zulaikha ta shigo tare da wani saurayi da wannan yarinyar suka zauna"wannan yayana ne " tace
"sunansa Abduljalil shine wanta ita ana kiranta zakiyya shi yana karatu a jami'ar jaffa , ita daliba ce
a kwalejin yan mata ta jaffa
.
Bayan shirin yan mintuna sai na jeho musu tambaya cikin dabara "ko kun san labarin sarkin
Ramalla na karshe?"
Na zuba musu ido , wannan ne karo na farko dana fara aikin daya kawoni, ya kalleni sosai yasa
hannunsa a aljihun kirjinsa ya fito da kwalin taba ya kasta ashana sai zakiyya ta fice waje "ban san
labarinsa ba" ya gumtsu hayaki ya fesar "wani tsoho abokin babanmu yasan komai na labarin
falasdinu kafin a mamayeta da bayan an mamayeta da irin yake yaken da akayi tun kafin a haifemu,
duk sanda nake da wani aiki daya shafi tarihi shi nake ziyarta ya bayyana mini komai" ya dube ni ya
kalleni mahaifiyarsa " idan bazaka damu ba dana hada ka da shi mutum ne mai son bakon da yake
son sanin tarihinmu zai gamtsar da kai da duk wani bayani da kake bukata"
.
Shuraih 99% ke cewa
.
Nayi murna da jin haka don haka nace " muje na ganshi mana yanzu "ya dubeni yayi murmuishi
"Ba a nan garin yake ba sai gobe zan kaika wajensa a nablus ne " na duba agogona naga lokacin da
nake dashi bashi da yawa "ina son ganinsa yau don sauri nake akwai wani uzuri da nake da shi"
Ya kada kafadarsa " banda hali zuwa nablus a yau , ina son zuwa jami'an ina da jarabawa kuma
kafin agama dare yayi, kasan nan ba'abari ayi tafiya da daddare daga wani gari zuwa wani garin ,
karfe shida zuwa bakwai na dare dole kowa ya koma garin da yake da zama ko ya fuskanci tuhuma
.
Shigewar zakiyya da farantin abinci ta ajiye a agabana tafice " zan biyo ka jami'ar nace masa bayan
da yayi mini bismillah
.
Jami'ar jaffa tana daya daga jami'ar da larabawa suka gina suke gudanar da ita da harkokinta, akwai
falasdinawa da yawa suna karatu wasu kuma suna koyarwa,
Haka zalika akwai yahudawa har ma da turawa dalibai da malamai
.
Hukumar yahudawa ce ke lura da tsara tsaren makarantan da manhaja da ake amfani da ita , tana da
shashen karatu mai zurfi akan ilimin kimiyya da aikin likita, tarihin da aikin injiniya
.
Abduljalil yana koyan aikin likita yana da sekara ta biyu muna shiga ya shiga aji bayan ya kaini
dakin karati, ina shiga na dukufa binciken littatafai, da kasidun tarihi daban daban akan kasar
izra'ila amm banga abin da nake son gani ba , labarai ne wanda ko agida najeriya na iya samu, sai
dan abin da ba a rasa ba,
.
Wanda ya karamin haske akan binciken dana ke son yi
Kuna dai tare ne da shuraih 99%
.
Bayan ya gama yazo muka fita zuwa gida a tahowar mu mun shafe kasa da mintuna goma sha
biyar , amma akan hanyar komowa mun shafe sama da mintuna arba'in saboda cunkoson da jerin
gwanon abun hawa "me ya kawo wannan Jerin gwanon" na tambayeshi "abduljalil yace "larabawa
da yawa suna aikin leburanci a da sauran aikin karfi a tel-aviv da saura garuruwa na yahudawa da
suka mamayee in sun kwana a gidajensu da sassafee kuma su sake neman iznin shiga garuruwan
domin neman abun da zasu ci, wannan yasa duk safiyar Allah da kuma La'asar hanyoyi suke cika
makil da abin hawa saboda kowa yana kokarin zuwa gida kar lokacin fara tare mutanee yayi
.
Nayi shiru kawai ina kallon jama'a a cikin dogayen motocin bas da sauran ababan hawa makare da
mutane ,
.
Yauwa anan zan tsaya na dan huta sai mun hadu a page 6
.
Dan Allah ku saka ni acikin Addu'anku
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi Daurawa
Littafi na daya 1
Page 6
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
[Shuraih 99% nake cewa daku]
.
Toh jama'a sai daikuyi hakuri don kuwa fallayen littafin sun babbale, a saboda hakanne zamu danyi
tsallake ,
.
Amurka da sauran kasashen turai sun tara musu dimbin makaman yaki na zamani wasu ma ba'a taba
jarabasu ba sai a lokacin, yahudawa suna da cikakkiyar masanaiya game da duk wani motsi da
sojojin larabawa sukeyi , domin suna samun bayanan sirri kai tsaye daga ma'aikatar tsaro ta amurka
kada ka manta kuma shugabannin wasu kasashen labarawa munafikaine
.
"Wannan nasarar ta basu daman waftar kasashen larabawa, don haka min sake fafatawa da su
ashekarar 1967, wannan shine yakin kwana shida, kwanan bakin ciki"
Abuja'afar yayi shiru banyi wani kokarin tambayarsa ba don na lura fuskarsa ta sauya idanunsa sun
kada sun yi jawur don haka na lura abin daya ke son fada ne yake masa ciwo matuka zuwa can sai
hawaye ya dinga tsattsafowa daga idanunsa yana bin kumatunsa a hankali
.
Ni dinne dai shuraih 99%
.
Cikin murya mai rauni tana rawa cike da sauti mai ban tausayi ya labarta mini labarin yakin kwana
shida " yakin kwana shida yakine yakine da larabawa ba zasu taba mantawa da shi ba har abada,
domin kuwa mun tozarta acikin kwana shida mun kaskanta mun ga wulakanci , munyi asaran
filayen mu, an kashe mana mata da yaya iyalai masu yawa bazasu sake gaini juna ba.
.
Domin iyalai da yawa an watsasu acikin duniya suna yi gudun hijra cikin kaskanci da yawa sun
halaka matayenmu da yawa sun ga wulakancin da basu taba zata ba domin kuwa an yiwa da
damansu fyade,
.
Yi tunani a ranka cewa matar da bata taba fita waje ba ko kuma wacce wani namiji bai taba ganin
fuskarta ba , balle kirjinta, rana daya ta samu kanta cikin fasikai sui mata tsirara suna lalata da ita a
gaban ya yanta ko danginta , sannan a yasar da ita a filin Allah bako sutura,