← Book details Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 25

Sashe 22

Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon Inna yayi ya ga ta warware ta ƙara haske, ainihin haskenta na bafulatanar usuli ya fito, ta ƙara yin ƙiba sosai. Wani irin daɗi ne ya ziyarci zuciyar Anas saboda ya dawo ya iske ahalinsa a cikin walwala da kwanciyar hankali fiye da yadda ya tafi ya bar su.

Aisar ne yayi gyaran murya ya ce "Da fatan dai Anas an samu abin da aka fita nema?" Sunkuyar da kansa ƙasa yayi ya ce "Insha Allahu Baffa mun samu, yanzu mun gama karɓar horo, kuma kafin a gama hora mu ma, wajen sau biyar muna fita yaƙi kuma cikin ikon Allah duk muna cin nasara. Yanzu ma an ba mu hutu ne, na wata biyu kacal, idan mun koma zamu fita wani babban yaƙi wanda ba iya tawagar mune kaɗai za su je ba.

Murmushi Sa'ad yayi ya ce "Yanzu ɗana kenan ya zama babban soja" sunkuyar da kai Anas yayi yana murmushi ya ce "A'a Abba zamu zama dai" gaba ɗaya suka saka dariya. Sai a sannan Inna ta yi magana ta ce "Yanzu Anas kana nufin nan da wata biyu zaku koma wani yaƙin? E Inna idan mun huta mun koma zamu fita, girgiza kai Inna ta yi ta ce Allah ya ba da sa'a" gaba ɗaya suka amsa da amin.

A can gidan su kuwa yana isa Alhaji Abubakar ya gan shi, take ya shiga yi wa Allah godiya da dawo masa da ɗansa lafiya, domin tun bayan tafiyar Ammar aikin soja, ya daina barci mai daɗi abinci ma idan yana ci baya jin daɗinsa, kawai yana ci ne da kada ya zauna da yunwa. Rungume Ammar yayi a ƙirjinsa wani sassanyan farinciki yana ratsa zuciyarsa, ji yake kamar kada ya sake barin shi yayi nisa da shi.

Falo suka shiga Daddy ya ce "Ammar É—in ya je ya yi wanka, sannan ya dawo ya bashi labari" cike da ladabi Ammar ya ce "To Daddyna bari na shiga ciki, to Ammar É—ina kayi sauri domin ina nan ina jiranka."

Su Anas ana zaune sai faman hira ake sha, amma duk wannan hirar idanun Anas suna kan Basma, ya ƙura mata idanu, tun ba ta ankara yana kallonta ba har ta zo ta kula, gaba ɗaya sai ta ji ta takura tashi ta yi ta tafi part ɗinsu domin gaba ɗaya ta tsani wannan kallon da Anas yake binta da shi.

Kiran sallah aka fara yi a Masallacin unguwar, gaba ɗaya suka tashi suka shiga ciki suka ɗauro alwala suka nufi Masallaci. Su ma su Inna da Iya miƙewa suka yi, suka tafi domin su gabatar da tasu sallar.

Bayan sun dawo daga Masallacin, Aisar ya ce "Anas ya je yayi wanka ya kwanta ya huta, da safe sai suyi magana, tashi yayi ya nufi ɗakin da aka nuna masa nasa ne.......✍️

To be continue.....📝📝📝

*Hussaini Yusuf✍️*
[12/9, 4:38 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK*

*NA*
*HUSSAINI YUSUF*

*______________________________*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*______________________________*

*Page 47/48*

Bayan ya shiga cikin É—akin, sai ya ga komai tsaf-tsaf, komai na É—akin sabo ne har da air condition, ga wani tamfatsetsen gado a shimfiÉ—e a É—akin. A hankali ya zo ya buÉ—e haÉ—aÉ—É—iyar wardrobe É—in da ya gani a manne jikin bangon É—akin, kaya ya gani dai-dai shi, an shirya su tsaf cikin wardrobe É—in. rufe ta yayi ya dawo gefen gadon ya zauna, tunani ne kala-kala ya cika masa zuciya, to "A ina su Aisar suka samu kuÉ—i har suka gina irin wannan gida haka?" Shi kaÉ—ai yake yi wa kansa wannan tambayar, amma ba shi da amsarta dole sai wajen su Aisar É—in zai ji komai.

Ganin wankin hula yana niyyar kai shi dare, sai ya tashi ya nufi toilet ɗin da ya gani a cikin ɗakin. A hankali ya buɗe ya shiga, "Masha Allah" shine abin da ji ya faɗa, a hankali ya rufe ƙofar bathroom ɗin, sannan ya shiga yin wanka, wani daɗi ne yake ratsa jikinsa jin sa yake tamkar an yaye masa duk wata damuwarsa. Bayan ya gama wankan, sai ya ɗauki ɗaya daga cikin tawul ɗin da ya gani a cikin banɗakin ya ɗaura shi ya ɗauki wani kuma yana tsane ruwan jikinsa.

A jikin wani irin dressing mirror ya tsaya, wanda ban taɓa ganin irinsa ba a rayuwata. Kayan shafe-shafe ne sun fi gaban a ƙirga, ga perfumes nan wajen kala ashirin sai wanda ya ga damar zaɓa. Just vasselin ya shafa, sannan ya buɗe wardrobe ɗin ya ɗauko wata baƙar jallabiya ya sanyata a jikinsa. Wow! ba ƙaramin kyau Anas yayi ba a cikin rigar nan, zuwa yayi ya zauna a gefen gado ya shiga tunani, nan da nan tunaninta ya faɗo masa. Shi kaɗai ya rinƙa sakin murmushi, tamkar gonar auduga yadda ta haɗe ranta ba ƙaramin burge shi ta yi ba. A ransa ya saka kafin ya koma bakin aiki sai ya bayyana soyayyarsa a gareta, ko da baza ta amince da shi ba.

Kamar an tsikare shi ya tashi ya fita daga ɗakin, kai tsaye ɗakin Inna ya nufa. Tarar da ita yayi ta idar da sallah tana shirin kwanciya, ganin Anas ya shigo sai ta fasa kwanciyar ta zauna a gefen gado, shi kuma Anas ya zauna a ƙasa. Cike da ladabi ya sake gaisheta, ita ma da nuna kulawa irin ta uwa ta amsa masa gaisuwar tana mai shafa kansa tana sakin wani tattausan murmushi. Shi ma ban da sakin murmushin babu abin da yake yi, domin babu abin da ya fi so a duniya fiye da ya ga mahaifiyarsa a cikin walwala da farinciki.

Ƙasa-ƙasa yayi da muryarsa ya ce "Inna wai a ina ku ka samu kuɗin da har kuka gina wannan katafaren gidan?" Dariya Inna ta yi ta ce "Ka kwantar da hankalinka ba Baffanka ya ce da safe zai sanar da kai komai ba? To ka jira safiyar mana idan Allah ya kai mu." Ba ta jira abin da zai ce ba ta cigaba da magana "Ni kuwa Anas akwai maganar da nake son mu yi ni da kai, dama ina son a kirawo min kai kafin ka kwanta. Amma sai na yi tunanin ka gaji, sai na bar ka ka huta, idan Allah ya so da safe muyi maganar, amma tun da ga shi ka shigo shikenan sai muyi maganar ta mu.

Gyara zama Anas yayi ya ce "Ina sauraronki Inna" murmushi ta yi ta ce "Ta so ka dawo nan kusa da ni sai ka fi fahimtata" tashi yayi ya koma kusa da ita ya zauna yana mai fuskantarta. "Tun bayan da ka tafi neman aikin soja, Alhaji Abubakar yake ta yi min aike wai yana son ya aure ni domin yana da yaƙinin zan iya riƙe masa Ammar na kula masa da shi. Na bashi taimakon da duk wata uwa take bai wa ɗanta, kuma ya ce idan na aure shi sai na haɗa da ku da Ammar ɗin na riƙe ku, ni na zama tamkar mahaifiyar Ammar da ta rasu tun yana yaro. Shi kuma ya zama tamkar mahaifinku da kuka rasa.

Kullum idan ya aiko min haka nake faɗa masa, sai ka dawo na yi shawara da kai, tun da hankalinka ya kai a saurare ka a ji ra'ayinka a cikin wannan magana. Shiru Anas yayi ya ɗaga kansa sama yana tunani, sai da Inna ta dafa shi, kamar an soka masa allura ya dawo hayyacinsa. Duban Inna yayi ya ce "Inna a iyakar sani na ba mu daɗe da rasa Baffa ba, muka samu madadinsa" da sauri Inna ta gyaɗa kai alamar gamsuwa da maganar Anas cigaba yayi da ce wa "Baffa Aisar shi ya zamar mana kamar Baffanmu da muka rasa, akanmu ya rabu da garinsu, akanmu aka ci masa mutunci aka nemi ya mayar da mu inda ya tsinto mu ko kuma ya bar garin, amma ya zaɓi barin garin akan ya mayar da mu inda ya same mu." Ban da hawaye da yake zuba a idanun Inna babu abin da take, domin ta tuno irin wahalar da suka sha kafin su baro ƙauyen nan da yake yankin Mambila a can Jahar Taraba.

Muryar Anas ce ta doki dodon kunnenta, in da yake ce wa "Inna ni a gani na babu wani uba da zamu samu bayan Baffanmu fiye da Baffa Aisar" shiru Inna ta yi tana nazarin maganar Anas tabbas gaskiya ya faɗa ita bata taɓa yin wannan tunanin ba ma, nan take ta shiga mamakin kaifin hankali gami da hangen nesa irin na Anas. Cigaba yayi da ce wa "Inna ke kin sani da a ce Baffa Aisar yana da damar kai ni makarantar horon sojoji, ba zai taɓa barin Abban Ammar ya kai ni ba, da kansa zai so ya kaini." Da sauri Inna ta girgiza kai alamar gamsuwa har yanzu ta kasa magana saboda a baya duk ba ta yi wannan tunanin ba, sai yanzu da Anas ya ankarar da ita sannan ta gane irin halaccin da Aisar yayi musu a rayuwa.

"Haka Inna idan muka duba Daddin Ammar yayi mana halacci a rayuwa, da bai kamata mu watsa masa ƙasa a ido ba" ita dai Inna ta yi shiru tana sauraren ɗan nata ta kasa furta ko da kalma ɗaya "Don haka Inna ni na amince ki auri Daddin Ammar, amma ke kaɗai zaki koma wajensa mu muna tare da Baffa Aisar, tun da shine ubanmu na ainihi bayan Baffanmu da ya mutu. Amma kafin ki sanar da shi ki fara faɗa wa Baffa Aisar mu ji shi kuma abin da zai ce akai" murmushi Inna ta yi ta ce "Haƙiƙa na daɗe ina nazari akan maganar auren nan amma ban taɓa yin kwatankwacin wannan tunanin da kayi yanzu ba."
Chapter 22 · 0% Book details