← Book details Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 25

Sashe 16

Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da jin haushi Anas ya daka musu tsawa, a firgice suka juyo suna niyyar guduwa, don ba karamin tsorata suka yi ba. Kallonsu yayi yace "wato ku saboda rashin hankali, ina can bakin gate ina ta faman jiranku amma shine za ku zo nan wajen ku hau cirar wani mangwaro ko?"

Yanzu ma na san Abba yana can yana jiranmu, tsuru-tsuru suka yi da ido, gaba dayansu sun sunkuyar da kansu ƙasa. Kallonsu malamin yayi yace "ku kuwa me yasa kuka aikata haka? na ga ba'a zuwa nan wajen sai a lokacin break muke bari a zo" me yasa ba ku zo da break ba sai da aka tashi? ga shi duk kun bi kun dagawa ɗan'uwanku hankali.

To daga yau idan na ƙara ganin wani anan bayan an tashi sai na zane shi, ku mu je ku fita dag...... hangota yayi a ɓoye a bayan wata bishiyar gwanda, sai faman leƙo su take yi, haka ne ya hana shi furta abinda yake shirin faɗa.

Nunawa yayi kamar bai ganta ba, ya dubi su Basma yace "naga ku baƙine anan makarantar waye ya kawo ku nan wajen tun da dai baku san shi ba ?" zazzare ido suka fara yi wannan ta kalli wannan an rasa wanda zai ba wa malam ɗin amsa a cikinsu.

Murmushi malam yayi kai tsaye ya nufi wajen bishiyar gwandar da ya hangota a bayanta, tana tsaye jikinta ban da rawa babu abinda yake yi, daga bayan gwandar ya tsaya ya miƙa hannu ya kamo hannunta. Firgita tayi ta saki wata ƙara! nan take ta saki kuka tana roƙon malam ya saketa.

"Don Allah Uncle Jamil ka yi haƙuri ba zan ƙara ba, na tuba na bi Allah na bika, kayi min rai ba zan ƙara ba" dariya ta so ba shi amma sai ya sha kunu, a ransa yake cewa "Bilkisu kenan sai fitinar tsiya, amma akwai ɗan banzan raki, kamar wacce za'a yanka".
Daka mata tsawa yayi yace "indai ba ta yi shiru ba sai ya zaneta" ɗif kamar ɗaukewar ruwan sama ta daina ihun da take yi, duban su Nasreen Uncle Jamil yayi yace "wannan ce ta kawo ku nan wajen ko?" da sauri Nasreen tace "E ita ce tace mana idan muka zo zata cira mana mang..... shiru tayi sakamakon hararar da Anas ya aika mata, sosai ta tsorata don bata taɓa ganin Anas a cikin ɓacin rai kamar yau ba.

Kallon Anas Uncle Jamil yayi yace "me yasa zaka hanata faɗar abin da yake bakinta?" rai a ɓace Anas yace "Uncle mu zamu tafi don na san yanzu Abbanmu yana can yana ta aikin jiranmu" duban Bilkisu Uncle Jamil yayi yace "maza ki tsugunna ki bai wa yayansu hakuri na ɓata masa lokaci da wahalar da shi ɗin da kika yi".

Zuwa tayi gaban Anas ta durƙusa, da sauri Anas ya dubi Uncle Jamil yace "ni ai na hakura kuma ba ita ce tayi min laifi ba, ka ga wadanda suka yi min laifi" ya faɗa yana nuna su Safna da hannu. Bai tsaya jin wani abun da Uncle Jamil zai ce ba ya ja hannun ƴan'uwan na shi suka fice daga cikin garden ɗin.

Shi kuwa Uncle Jamil kallon Bilkisu yayi yace "ke Bilkisu me yasa ba ki da hankali ne" haka kawai zaki jawo yara cikin school garden bayan an tashi daga makaranta ko? don kuyi ta'adinku son ranku da safe sai a nemi wanda yayi a rasa, alhali kuma ke ce me janyo yara kuna yi ko? duk ta'adin da ake yi ashe kece ki ke kawo yara kuna yi ana É—orawa masu gadi akan ba sa kula ko? to yau asirinki ya tonu gobe zaki ci ubanki kuwa a cikin makarantar nan, don a kanki sai na haÉ—a assembly na zane ki a gaban É—alibai.

Da sauri ta kama ƙafafunsa tana kuka tana cewa "don Allah malam ka yi haƙuri daga yau ba zan ƙara ba" murmushi yayi yace " ke dai ki bari gobe kiyi bayani a gaban sauran student, ga shi nan saboda fitinarki kullum ba kya cigaba a makarantar nan, ƙannan ƙannanki sun zo sun tafi sun bar ki saboda tsabar rashin ƙokarinki. An kai ki ajin yara sai kiyi ta saka su suna aikata laifi, kina zare kan ki ko? da sauri ta girgiza mai kai tace "wallahi malam bana saka su" murmushi yayi yace to me yasa da na shigo kika ɓuya a bayan bishiya? wato so kike sai na fita sannan ki fito ki gudu ko? to tun daga ƙofa na hango ki a ciki.....

Su Anas suna fita suka ci karo da Sa'ad yana ta faman neman su, kallonsu Sa'ad yayi yace "ina kuka tsaya ne ina ta nemanku? tun É—azu na zo nan É—aukarku amma har É—aliban suka gama fita ban gan ku ba lafiya?" murmushi Anas yayi yace "idan mun je gida zan faÉ—a maka Abba mu tafi kawai".

Girgiza kai kawai Sa'ad yayi sannan ya wuce gaba suka bi shi a baya.

A hanya Anas ya bayyanawa Sa'ad dalilin da yasa suka daɗe, bai ɓoye masa kkomai ba amma maimakon ransa ya ɓaci, sai ya saki murmushi yace "yarinta ce insha Allah za su daina" a haka dai da suka koma gida, Sa'ad tara su yayi ya musu faɗa sosai, ya nuna musu ɓacin ransa akan haka.

Kuma yace "daga yau idan an tashi su za su rinƙa jiran Anas a ƙofar gate" Rahila da Husna ma sun yi musu faɗa sosai daga baya dai da nasiha suka gama yi musu faɗan.

Washe gari ko da suka je makarantar, ƙin kula Bilkisu suka yi, sai faman shishshige musu take yi amma ko kallonta ba su yi ba ballantana ta saka ran za su kulata. Sosai suka mayar da hankali akan abinda ya kawo su makarantar, sai ga shi cikin ikon Allah sun fara fahimtar abubuwan sosai.

******************************
A kwana a tashi babu wuya a wajen Allah, yau Anas ya kammala secondary school, yayin da su Safna suke Js.s two. Akwai wani abokin Anas da suka haÉ—u a makarantar, shi ma ra'ayinsa irin na Anas ne, ma'ana shi ma soja yake son zama, zuwa yayi ya sanar da Daddyn shi a samo masa admission a makarantar horar da sojoji ta Kaduna, kuma yace tare da Anas yake son a samo musu.

Saboda Daddy ya san ko wanene Anas a wajen Ammar bai ɓata masa wani lokaci ba yace zai samo musu tare, kuma ya je ya shaidawa Anas ɗin shine zai ɗauki nauyin karatun na shi,har su kammala kuma ya ɗauki alƙawarin shine zai tsaya musu har sai sun zama manƴan sojoji a ƙasar nan.

Ai da gudu Ammar ya fita daga gidansu ya nufi gidan su Anas domin ya shaida masa wannan albishir ɗin, yana zuwa ya tarar da Anas a ƙofar gida, ya zuba tagumi hannu biyu kallonshi Ammar yayi cike da zumuɗi yace da shi......

Anas albishirinka da sauri ya É—ago ya kalli Ammar din don sai lokacin ma ya san da zuwan shi, sake maimaitawa Ammar yayi yace "Anas albishirinka" da sauri Anas yace goro...........

To be continue........
Comment and share

_*Hussaini Yusuf*_
07069475482.
[12/9, 4:37 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK*

*NA*
*HUSSAINI YUSUF*

*______________________________*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*______________________________*

*Page 37/38*

*Z* ama Ammar yayi yace "to bani goron sai na faɗa maka" murmushi Anas yayi yace "idan kuma albishir ɗin bai yi min daɗi ba fa?" "ai wannan albishir ɗin da zan yi maka ba'a taɓa yi maka irin shi ba" kallon shi Anas yayi yace "don Allah kayi sauri ka faɗa mini indai yayi min daɗi ni na san kyautar da zan yi maka".

Murmushi kawai Ammar yayi yace "Anas ka godewa Allah domin burinka yana gab da cika, Daddy na yace tare da kai zai nemo mana admission a makarantar horon sojoji ta Kaduna" a zabure Anas ya miƙe tsaye yana yi wa Ammar kallon tuhuma, zama yayi ya kalli Ammar ɗin yace "ta yaya Daddyn ka ya san ni da har zai samo min admission?".

Murmushi Ammar yayi yace "Anas kenan ai kullum idan na zauna da Daddy na babu labarin da nake ba shi face naka" da haka har ya san ka a baki amma bai taɓa ganinka ba, kuma nace kaine kake taimaka mini a makaranta, sosai kana da kirki.

Haka ne yasa duk lokacin da na yabe ka, sai Daddy ma ya yabe ka, kuma na ce masa burinmu ni da kai iri É—aya ne, ma'ana ni da kai duk sojoji muke son mu zama.

Da yace min zai nemo mini admission na shiga makarantar horon sojoji, sai na dage nace tare da kai za'a nemo mana, idan kuwa ba haka ba na fasa yin sojan gaba É—aya.

Dole Daddy ya haƙura zai nemo mana a tare ka ga sai mu wuce ko? har hawaye sai da Anas ya zubar don murna. Duban Ammar yayi yace "Ammar tashi ka raka ni na je na yiwa Daddynka godiya."

Da sauri Ammar ya dakatar da shi ya ce "Yanzu Daddy na baya gida, sai dai ka bari a ƙarshen satin nan yake zaman gida, da kaina zan zo na raka ka wajen shi ka yi masa godiyar, yanzu ni dai ka bani goron albishir ɗin da ka ce zaka ba ni." Murmushi Anas yayi yace "jira ni anan ina zuwa" sannan ya shige cikin gidan, kai tsaye ɗakinsa ya nufa, dube-dube yake ta yi ya rasa me zai ɗauko ya kawo wa Ammar ɗin, saboda ya matuƙar burge shi ba kadan ba.
Chapter 16 · 0% Book details