← Book details Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 25

Sashe 11

Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Take kuwa haƙorinsa yayo fitar burgu daga bakinsa, jini ya cika masa baki, amma haka bai sa Aisar ya ƙyale shi ba, ya hau shi da duka da bugu ya rinƙa tattaka ruwan cikinsa, tun yana ihu yana neman taimako, har ya daina motsi sannan Aisar ya ja shi cikin wata duhuwa ya wurgar da shi yayi tafiyarsa abinsa.....

Babu wanda ya ga lokacin da yayi masa wannan abin domin hanyar ba mutane ne suke binta sosai ba, shi yasa tun lokacin da ya fara dukansa babu wanda ya zo wajen ballantana ya cece shi daga wajen Aisar É—in.....

Sauri kawai Aisar yake domin ya isa gidan Iya, zuciyarsa fes ya ɗauki fansa akan wanda ya haɗa shi da ƴan garin, ko kaɗan bai yi nadamar abinda ya aikata ba domin ya tsani munafiki, tsana ba ta wasa ba, da wannan tunanin ya ƙaraso gidan Iya, shiga yayi ya gaishe su bai jira sun amsa ba yace " Iya kuyi sauri ku haɗa kayanku yanzun nan domin so nake mu bar garin nan kafin wani abun ya faru da mu.....

Tambayar shi abinda ya faru Iya ta yi, cike da zaƙuwa yace "Iya yanzu ba mu da lokaci, ku dai kawai ku shirya mu tafi, idan mun samu nutsuwa zan faɗa muku komai....

Nan take kuwa suka hau shiri, dama ba wasu kayane masu yawa da su ba, nan da nan suka gama shirinsu suka biyo bayan Aisar suka fice daga gidan....

Gidan Aisar suka nufa, akan hanÆ´arsu ta komawa ne suka haÉ—u da wani abokin Aisar a firgice ya dubi Aisar yace "Yawwa Aisar dama neman ka nake yi ruwa a jallo, kuyi sauri ku bar garin nan domin naga matasa yaran ÆŠanliti sai wasa makamansu suke yi wai me garine da mahaifin matarka Rahila suka turo su, su hallakaka du É—auki matarka su tafi da ita, ba ka ga shirin da suke yi ba, wallahi so suke su kashe ka a cewarsu kai É—anta'adda ne....

Fashewa da kuka Iya da Inna suka yi, shi kuwa Aisar ransa ne ya ɓaci matuƙa, ba don yana son ya tseratar da rayuwar su Iya ba, da sai ya tsaya ya koyawa me gari da sauran mutanen garin hankali.

Cikin sauri ya ke tafiya su Iya suna bin shi a baya, su Nisreen da Safna ma, su har gudu-gudu sauri-sauri suke yi, hannuwansu sarƙe da na juna, addu'a yake yi a cikin ransa Allah yasa ba su je gidansa ba.

********
Farkawa yayi daga dogon suman da shafe awa ɗaya yana yi, ganin shi yayi a cikin ciyawa a kwance, an jefar da shi kamar mushe da sauri ya tashi zaune, nan take ya rinƙa tuno abinda ya faru tsakaninsa da Aisar, shafa bakinsa yayi yaji jini, hawayen baƙinciki ne ya zubo masa kamar an tsikare shi ya miƙe tsaye ya kurma wani uban ihu.

Ihuuuuuuuu! Aisar gani nan bisa kan ka, falfalawa yayi da gudun tsiya cikin garin domin ya je ya shirya yaransa su yi wa Aisar kisan wulaƙanci......

To be continue............
Comment and share

Hussain Yusuf
[12/9, 4:36 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK*

*NA*
*HUSSAIN YUSUF*

*______________________________*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

*_______________________________*
*Page 25/26*

Shi kuwa Aisar yana zuwa gida ya tarar har Rahila ta gama haɗa musu kayansu, ita da Anas suna tsaye suna jiransa. Yana shigowa ya gansu, yace su zo sai su biya ta gidan su Iya su tafi, lokacin wani abokinsa ya shigo gidan a firgice. Ya dubi Aisar yace "Alhamdulillahi Aisar dama kai nake nema, kuyi sauri ku bar garin nan tun kafin a hallaka ku," kallon shi Aisar yayi yace "me yake faruwa ne, a firgice yace "wallahi Aisar ga su can a fadar me gari sai faman wasa makamansu suke yi wai za su zo su yaƙe ka tun da kai ɗanta'adda ne, don haka kuyi sauri ku fita daga garin nan, tun kafin su zo su iske ka suyi maka wata illar." Aisar nunawa yayi ko a jikinsa, Rahila da Anas kuwa ban da kuka babu abinda suke yi, kallon abokin nasa Aisar yayi yace "Mu'az zan baka amana idan har baza ka ci mini ba, cike da tausayawa Mu'az yace "Aisar bani duk amanar da zaka ba ni insha Allah zan riƙe maka ita hannu biyu."

"Alhamdulillah" shine abin da Aisar yace sannan ya dubi Mu'az yace ga dabbobi na nan, don Allah ka ɗauke su ka mayar da su gidanka ka cigaba da kula min da su, har lokacin da zan buƙace su, idan kuma baza ka iya kula min da su ba, to ka kai min su kasuwa, idan na koma inda za ni sai muyi waya.

Haka yace "to Aisar ni dai na karɓi wannan amanar taka hannu biyu," saboda haka yanzu zan kunce su na mayar da su gidana zan cigaba da kula maka da su insha Allah har zuwa lokacin da zaka buƙace su daga hannuna, godiya sosai Aisar yayi wa Mu'@z sannan ya ja hannun Anas da Rahila suka fita daga gidan suka nufi gidan su Iya.

Suna zuwa suka tarar su ma har sun gama haÉ—a kayansu, nan da nan suka fito suka bi wata siririyar hanÆ´a, wacce zata sada su da bakin titi.
Tafiyar minti talatin suka yi sai ga su, a bakin titi kasancewar titin motoci basa binsa sosai, sai faman jiran mota suke yi ta zo amma shiru har suka shafe awa guda suna jiran mota amma babu wacce ta zo zata wuce, sai wata guda É—aya ita ma kaya ne ta É—ebo saboda haka babu damar shigarta.

A cikin garin kuwa zugar ƴan'daba ne hannunsu riƙe da mugayen makamai, sun nufo gidan su Aisar sai faman wasa kansu suke yi, suna zuwa suka daki ƙyauren gidan da sandunan hannunsa nan take kuwa ƙyauren ya kakkarye, suka kutsa kansu cikin gidan, suna shiga suka tarar babu kowa, sai da suka lalube kowanne ɗaki na cikin gidan, amma ko motsin su Aisar basu ji ba.
Saboda haka suka fito suka nufi gidan Iya, nan ma dai ba su tarar da kowa ba, ba su tsaya wani ɓata lokaci ba, suka nufi bakin titi don su riski Aisar ɗin a can.
Har yanzu shiru babu motar da ta zo wuce wa, har sun ga ji da tsaiwa su Iya sun tsugunna, daga tsugunne Inna ta hango zugar ƴandaba sun nufo inda suke hannuwansu riƙe da makama. A firgice ta muƙe tsaye ta nunowa Iya su, Aisar ma yana waigowa idanunsa suka yi tozali da su, a firgice yace "su Iya su tashi su bar wajen.
Har sun tashi za su gudu, sai suka hango wata mota ƙirar golf ta nufo inda suke, tun daga nesa Aisar ya rinƙa ɗaga wa motar hannu, su kuma ƴan'daban koda suka hango motar tana niyyar tsayawa domin ta ɗauki su Aisar, sai suka rinƙa gudu domin su tarar da su kafin su hau motar.
Me motar yana zuwa dai-dai su Aisar sai ya ja burki ya tsaya, ya dubi su Aisar yace "Ina zaku je ne?" Cike da zaƙuwa Aisar yace "cikin Jalingo zaka kai mu" murmushi me motar yayi yace gaskiya kuna da sa'a, dama can na nufa yanzu kuyi sauri ku shigo.

Da sauri Aisar ya buɗe motar, sai da ya tabbatar kowa ya shiga. Sannan shi ma ya shiga gaba, me motar kuwa ya ja suka tafi, ƴan'daban kuwa dai-dai lokacin da motar ta tashi suka ƙaraso wajen, wasu daga cikinsu suka ɗauki duwatsu, suka rinƙa jifan motar, amma ko kusa da motar jifan bai kai ba, na gaba yayi gaba na baya........Gudu sosai direban yake yi da su Aisar, kallon Aisar yayi yace "daga Jalingo ina kuma zaku nufa?" Murmushi Aisar ya saki yace "za mu nemi motar Kano ne, don na ji an ce can ɗin yafi daɗin zama shi yasa na ɗebo iyalina zamu koma can da zama."
Murmushi direban ya saki yace "gaskiya ne ka iya zaɓan wajen da zaka koma, don Kano indai ka tashi ka nema to insha Allahu zaka samu, yanzu a nawa zan kai ku can Kano ɗin, saboda nima haifaffen Kano ne, yanzu da ka ganni a Taraba, wasu fasinjoji na kawo, shine na shigo nan yankin Mambila domin na wasa idanuna, sai kuma Allah ya haɗa ni da ku, ka ga yanzu na huta zuwa tasha in jira lodi.
Shi ma Aisar ɗan murmusawa yayi yace "Yanzu kenan kana nufin har can Kanon zaka kai mu?" Gyaɗa masa kai direban yayi kafin yace "ƙwarai da gaske ma kuwa, don yanzu ma can na nufa da ku.

Hamdala Aisar yayi, sannan yace "to direba kana ganin a kamar nawa zaka kai mu can Kano ɗin?" Ko kallon Aisar ɗin bai yi ba, yace "ni ko nawa ku ka bani Allah yasa musu albarka" dubu biyar Aisar ya miƙa masa, karɓa yayi har da godiya.

Ana kiraye-kirayen sallar magriba su Aisar suka iso Kano, ba su san inda za su nufa ba, saboda haka direban da ya ga haka, sai ya ji tausayinsu kai tsaye ya yace bari ya kai su gidansa, da safe sai ya nemo musu inda za su zauna.Godiya sosai Aisar da su Iya suka yi masa, saboda halin kirkin da ya nuna musu, a unguwar Darmanawa gidansa yake, saboda kai tsaye can ya nufa da su.Lokacin da suka isa, sai ya tsayar da motar a ƙofar wani gida, ɗan madaidaici, sannan ya fito su ma gaba ɗayansu suka fito daga cikin motar.
Chapter 11 · 0% Book details