← Book details Amrah Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 9

Sashe 6

Amrah Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakyar amrah ta bude bakinta tace "lalle Suhaima kin tabka babban kuskure tunda uwata ta haifane ba'a taba yimin hakaba, amma yau wai nice wata ta mareni har ta fitarmin da jini hmmmmm, nida koh kallon banxa mutum yamin sainaga bayansa amma wai ni *AMRAH MACIJIYA* 🐍 aka mara,

Suhaima najin haka jikinta yadau kyarma, wasu irin fitinannun tagwayen mari amrah ta wanka mata, Wanda suka yi sanadiyar fashewar hanci da bakinta nan take ta fadi kasa, nan amrah ta sake wanka mata wasu marukan a lokaci guda, wannan karon kam gaba daya dena ji Suhaima tayi, tana kuka tace dan Allah kiyi hkr, nasan na aikata kuskure amman wlh shairin shaidanne,

Rufemun baki amrah ta daka mata tsawa hade da girgijewa ta xama shirgegiyar macijiya 🐍,

Ai nan take Suhaima ta sumeeeee.

*Mascow*

Jalal kam kalaman amrah na karshe sune suka tsaya masa arai ya rasa ina kalaman ta suka dosa, sadeeq neh ya shigo yace, "haba buddy tun daxo muke jiranka fah amma kaxo nan kanata waya da girlfriend dinka, kuma kasan yaune xa'ayi wannan tiyatar, kuma inaji ajikina inshaa Allah xamuyi nasara"

Hakane nima inaji ajikina, muje suka fito suka shiga mota direct *Mascow International hospital* aka kaisu, suna xuwa babu bata lokaci suka shiga tiyatar,

💦Ni kuma nace all the best jalal 💦

*KANO*
AMRAH kan saida ta wahalarda suhaima sannan ta kyaleta, dakyar Suhaima ta iya Jan jikinta tanufi dakinta,

Ita kuma amrah gurin wayarta ta nufa tana xuwa ta dauki a barta ta haye kan gado tasa tafin hannunta ta shafe wayar nan danan tadawo sabuwa gal, ta tashi tasaka caji ta nufi bangaren su inna,

Tana xuwa ta xauna acan sukasha firarsu da inna,

Hajiya Sarah koh tana can tana neman yadda xata kawarda jalal, da taje gurin bokan hajiya nafeesa ce mata yayi "a gaskiya indai kinason kawarda jalal daga doron kasa toh fa saikin fitarda wannan yarinyar daga gidanki sbd indai tana cikin gidan toh fa bbu abunda xamu iyayi", toh amma boka meyasa kace haka,

Dariya ya kyalkyale da ita marar dadin ji sannan yace "ga wannan ki turarashi a cikin gidanki koh wane lungu da sako, xakisan dalilin da yasa nace saikin fitarda ita tukun" karba tayi tace ngd boka, ta fito ta dawo gida,

Tana xuwa tasaka mai aiki ta ibo mata garwashi Dan tayi turaren da boka ya bata,

Ita kuma amrah har ynx tana part dinsu inna,

Mommy kan dauko wannan turaren tayi ta bude ai da sauri ta rufe, tafarnuwace da k'ashi da kuma barkono aka hade gu daya aka nikesu,

Kunsan mee hmmmmm, wannan turaren idan amrah tajishi tohfa xata rikide ta xama macijiya kuma kunsan tana part din inna, kenan asirin amrah xai tonu koh yaya, ku biyoni kuji yadda xata kaya 💃💃💃💃💃

💫Rabeauty 💫
*please vote comment nd share*
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: 💫AMRAH MACIJIYA 🐍🐍🐍💫

By Rabeauty 🥰💫💫💫💫

(9)
Wani irin hankadashi tayi saida ya daki bango,

A fusace ya dako, Amma me ganin yayi amrah ta rikide ta xama shirgegiyar macijiya amma bagaba dayaba,

Daga samanta xuwa kugunta tananan a mutum dinta, amma daga kugunta xuwa kasan ta yaxama na maciji, gashin kanta ya mimmike tsaye ya koma macixai, idanunta sunkara xama green sosai hatta kwayar idonta da take fara toh itama ta koma green, kunnen ta yana fitarda wani hayaki, Wanda ya turnuke dakin baka iya ganin komai,

Najeeb kam tuni xawo da fitsari sun kubce masa Dukda Baya ganin ta sbd hayakin amma behanashi ja da bayaba yana cewa

"Dan Allah baiwar Allah kimin rai wlh bansan cewa keba mutum bace Dan Allah kiyi hkr, yana kaiwa karshe ya rushe da wani irin kuka, Wanda daka jishi xakasan na tsoro neh da firgici,

Hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh amrah ta kyalkyale da dariya marar dadin ji, dariyar da ta kara firgita Najeeb,

Sannan tace "kayi kuskure matuka tunda har kayi niyar rabani da budurcina, darajata, da kuma 'yancina, tunda nake a rayuwata ba' ataba yimin hakaba, kuma duk Wanda ya shiga gonata tohfa bana barinsa a doran kasa xan kashe shi, amma kai baxan kashe kaba sbd abu guda, shine JALALUDDEEN, kaci albarkacin sa, sbd kai kanen sane, wlh wlh wlh dabadan hakaba da saina kashe ka, kuma idan ka kuskura naji wannan xancen a bakin wani wlh xan manta da cewar kai jinin jalal neh na kashe ka,

Tana gama fadar haka hayakin dakin ya Washe ai da sauri Najeeb yabar dakin, yana xuwa room dinsa yasa key ya kulle kofarsa ya haye kan gado ya shige cikin blanket ya rufe kansa gaba daya jikinsa rawa yake.

Ita koh amrah kwanciya tayi akan gadonta daga kugunta xuwa sama ya rikide ya Ida xama na maciji, a haka tayi baccinta.

****************
Washe gari jalal kam yanata hada kayansa sbd xai tafi mascow gurin wani operation da xasuyi bama shi kadai xaijeba harda sadeeq da wasu doctors, gobe xasu tafi Abuja, saisu hau jirgin da xai kaisu mascow.

A bangaren amrah koh tana tashi daga bacci tayi wanka ta shirya cikin wata fitted gown ta material maroon wadda ta mugun yimata kyau ta kara fito da haskenta,

Fitowa tayi ta nufi part din jalal, a hanya ta hadu da Suhaima itama xataje gurinsa, taci adonta itama cikin wata riga ta yan kanti blue, wani irin banxan kallo Suhaima tayi mata, itakam batama bi ta kantaba,

Suhaima tariga amrah isa bakin kofar part dinsa tashiga yin knocking , itakam amrah tana isowa tabi ta gefenta ta bude kofar tana shiga ta banko kofar da karfi, da ace Suhaima bata matsaba da kofar ta daki fuskar ta, Suhaima kam ji tayi kamar ta buga ihu dan tsabar takaici,ace yarinya karama tana son taxamam mata jaraba juyawa tayi ta shiga motar ta tabar gidan.

AMRAH kam tana shiga direct ta haura sama inda dakinsa yake, tayi knocking, jalal kam da yake kan gado ya daura system dinsa akan cinyarsa yana wani aiki yaji ana knocking din kofarsa,

Dan kallon kofar yayi sannan yabada ixinin shigowa,

A hankali ta turo kofar bakinta dauke da sallama, amsawa yayi hade da kafeta da mayun idanunsa masu rikitarwa,

Karasowa tayi ta xauna bakin gadon ta gaisheshi, amsawa yayi still idanunsa yana kanta, dan kallonsa tayi da sauri ta sadda kanta kasa sbd ynx ba xata iya jure kallon sabah,

"kinyi kyau sosai" yace da ita, dagowa tayi tana murmushi tace "ngd" shiru suka yi for some minute sannan tace "yayana Dan Allah su nake mufita", xuwa ina? yace da ita, gurin shakatawa ta bashi amsa, OK jirani a falo ina xuwa, da sauri tace "toh" ta fita tana jin dadi, binta yayi da kallo, yana jin wani abu yana tsargar masa,

Shiryawa yayi cikin wata white gizna, yayi kyau matuka,

Falo ya nufa akan kujera ya same ta yace "mutafi koh", juyowa tayi ta kallesa tace "kai yayana kayi kyau sosai wlh kamar na saceka na tafi dakai" murmushi kawai yayi ya nufi kofa binsa tayi suka jera tanata yimai surutu,

Dan kallonta yayi sannan yace "haka xakije babu mayafi"

Hannunta ta dora kan goshinta tace "kash wlh ni nama manta ashe ban dauko mayafi bah"

Da sauri ta nufi part dinsu tana shiga ta dakko mayafinta ta fito, daidai lokacinneh mommy ta fito daga room dinta ta sakko kasa, kallon amrah tayi sannan tace "ke sai ina kuma"

Kallonta amrah tayi tace "fita xamuyi da yaya jalal"

Kan uba mommy ta fada "toh bbu inda xaki maxa woce ki gyaramin dakina"

Wani banxan kallo amrah tayi mata sannan tace "hmm bbu mahalu kinda ya isa ya hanani fita da yaya jalal Dan haka kinga tafiya ta" ta juya tana tafiya tana karkadawa mommy hips.

Tana Fitowa ta shiga gaban mota yaja sukabar gidan, direct gidan zoo ya nufa da ita,

Hmmmmm aiki jaaaa, toh kai jalal daka kaita gidan zoo toh idan taga yan uwanta macixai fah? Koh da yake babu ruwana Dan bani nace ka kaitaba eheee😏😏😏😏

💫Rabeauty 💫
*please vote, comment, and share *
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: 💫AMRAH MACIJIYA 🐍🐍🐍💫

By Rabeauty 🥰💫💫💫💫

(10)
Suna isa yayi parking suka nufi bangaren da namun daji suke, aiko ta dakko wayarta tayi ta musu vedio da pics,

Shidai saidai ya kalleta yayi murmushi, wani bangaren taga ya nufa, tace "yayana ina xakaje?

Bangaren macixai, ya bata amsarda, gaban tane yayi wani irin mummunan faduwa, tace" yayana dama kana son macixai?

"eh amrah ina matukar kaunar macixai, amma banason suxo kusa dani, dan kallonsa tayi xuciyarta na kara harbawa, karasawa suka yi gurin macixan,

Wani maciji baki kirin yana ganin amrah ya fara xillo yanason ya fito daga cikin kejin, jalal kam yadan tsorata ganin yadda macijin yakeyi,

Itakam amrah koh a jikinta sbd tasan cewa kohya fito bbu abunda ya isa yayi mata,

Jalal kam da sauri yaja amrah sukabar gurin, yawo suka yi sosai a cikin gidan zoo din basu bar gidan zoo ba saida akayi la'asar,

Shoprite ya kaita ya siya mata chocolates da biscuits dasu cake da dai sauransu, basu dawo gidaba sai around 6,

Jalal kam yana komawa part dinsa ya Ida hahhada kayansa dan gobe jirgin 9 xasubi ya kaisu Abuja daga can suhau na mascow ya kaisu, kuma ya yanke shawarar gayawa amrah cewa yana sonta, Dukda yasan ta mai yarinya amma baxai iya cutar kansaba xai gaya mata yana sonta, idan ya dawo ya gayawa daddy ya samu matar da xai aura, dan daya aure Suhaima ya gwammace ya xauna bbu aure.

**************
Washe gari sadeeq ya kira jalal yace masa kawai su hadu a airport,

Shiryawa yayi cikin sut dinsa baki wa'enda suka kara fito da kyansa da kuma haskensa, part din mommy ya nufa ya gaya mata xai wuce, Allah ya tsare kawai tace, a ranta koh cewa take "Allah yasa jirgin ya fado duka kumutu"hmmm ni kuma nace" Amin walaka tare dake😏😏😡😡

Jalal kam harya fito xai wuce sai kuma ya juyo ya kalli kofar dakin amrah, a xuciyarsa yake cewa "dama ta fito na ganta kafin na tafi", saida yadan bata lokaci amma amrah bata fitoba,

Juyawa yayi ta tafi, har yakai bakin kofar fita daga main falo yaji ance "yayanah" da wata irin murya ta shagwaba,
Chapter 6 · 0% Book details