← Book details Amrah Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 9

Sashe 4

Amrah Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

💫 Page 1💫
Kano state.
A wani kauye Wanda ake kira da tigadam, wata yarinya na hanga a bakin rafi xaune tana kallon ruwan rafin duka duka yarinyar baxata wuce shekaru goma sha biyarba,tashi tayi tana karewa gurin kallo, koh ina bishiyoyine koraye 🌳🌳masuban sha'awa, hanyar gida ta nufa kallo daya xakayiwa tafiyar ta kasan cewa wannan yarinyar ba cikakkiyar mutum bace sbd yanda take wata irin lankwasa, iskace tayaye mayafinda ta rufe fuskarta dashi,subhanallah, wannan irin kyau haka, yarinyar kyakkyawa ce kyan karshe idanuwanta Green ne gata fara kal yanda take da kyau xakasan cewa ba mutum bace,girgixa naga tafarayi Wanda ya matukar bani tsoro kafin kiftawar gira naga ta rikide ta xama shirgegiyar macijiya Green 🐍🐍🐍 sai sheki takeyi, cikin kauyen ta nufa tana kaiwa gurin wata kofa ta girgije ta xama mutum, da sallama ta shiga gidan, wata yar tsohowa dake bakin murhu tana ixa itace ta amsa, hade da fadin "wai ke AMRAH ba daman ayi miki fada saiki dau fushi ki wani fita dg gida kamar wata iska, waima daga gidan ubanwa kike? Karasuwa AMRAH tayi tana murmushi Wanda yakara fito da kyanta, tace" haba gwaggonah bafa fushi nayiba kawai dai fita nayi har kigama mitanki sannan na dawo"cikin kwantarda murya gwaggo tace "yar jikalle kinsan dai banason yimiki fada kece bakyayin mgn, dan Allah kikiyaye abunda xaisa na miki fada kinji, toh gwaggo inshaa Allah xan kiyaye, yawwa yar albarka, tashi tayi ta kara share gidan, ita kuma gwaggo tana kwashe abincin a cikin langa, ta xuba musu sauran a cikin kwano.
Bayan sungama Cin abincin saiga harira kawar AMRAH tabiyo mata su tafi islamiya, gaida gwaggo tayi sannan ta kalli AMRAH tana cewa "lalle AMRAH bakima shiryaba kuma kinsan yau malam abu ne xaiyi mana karatu kuma yace uku tayi mana cikin aji gashi ynx har 3:30 kuma nasan kafin mu isa hudu tayi kuma....... Xancenne ya makala sbd wani irin kallo da AMRAH tayi mata shiya hakana ka rasa xancen sbd tana balaaa'in tsoron idanun AMRAH shiyasa bata fiya kallon taba sbd idanunta green neh kuma kwayar idanunta farine ita harira har tunanin take anya AMRAH mutunce kowa, tashi amrah tayi ta shiga dakinsu batafi 5 minute bah ta fito cikin shirin islamiya, muntafi gwaggo, Allah yatsare gwaggo tace, Amin ta amsa hadi da Jan hannun harira suka fito suna isowa bakin soro ta dakko nikabinta ta saka sbd yadda idanuwanta suke, ba Wanda yataba ganin complete face dinta daga gwaggo sai harira, sbd duk Wanda yayi toxali da kwayar idanunta toh sunansa gawa, duk kauyen ba Wanda yataba ganin idanunta dg hancinta sai bakinta kawai mutane suka gani, suna isa malam abu ya tsakar dasu wai sunyi latti baxasu shiga ajinba, harira tashiga bashi hkr ita kuma amrah koh kallo be ishetaba abunda ya kara harxukashi kenan kuma yau yadau alwashin sai yaga fuskarta, harira kadai ta shiga aji ita kuma amrah yace tarage tsawonta a cikin rana, bayan yagama karatu ya fito ya nufu inda take ya shauda mata bulala koh gixau bata yiba ya kara shauda mata still bata mutsaba abun ya kara harxukashi yaci gaba da dukanta saida ya gaji Dan kashi ya kyaleta, ita kuma amrah idanunta sun kara rikidewa sun xama green sosai, hannu yasa ya taxge nikabinta da sauri yaja Baya sbd toxali da yayi da idanuwanta nan danan jikinsa yafara makarkata yama kasa mgn,ita kuma ta kafeshi da idanunta, da sauri yabar gurin, harira na karasowa ta kama hannunta suka nufi gida.
Bayan sallar isha'i amrah ta fice daga gidan gwaggo ma bata saniba, hanyar da tasan malam abu nabi ita ta nufa ta haye saman bushiya tana jiran isowarsa, aiko ba'a dadeba saigashi yabiyo da yar fitilarsa, aiko tayi sauri ta diro daga kan bushiyar rabin fuskarta rufeda Green din mayafi, yana isowa ya tsaya yana yadata da fitilarsa gabansane ya fadi dashi ya xata aljanace amman saiyafi fuska ya basar hadi da cewa "ke malama jayemin akan hanya tayi mishi banxa aiko yahau xaginta, amatsayinsa na malami amman yana xagi, can kuma yace waike wace irin dabbace, a harxuke tace" MACIJIYA 🐍"hade da yaye mayafin fuskarta, tashiga yin wata irin jijjiga nan take taxama shirgegiyar macijiya🐍 green sai sheki take, nan take malam abu yafara fitsari a wando, wata irin dariya ta sheka da ita sannan tace" malam abu kayi kuskuren dukana da kuma xaginta, a yau dinnan xan kasheka kuma ynx, kafin yayi mgn tayi sufa ta laulayeshi tashiga sararsa ta Ko ina ihu yake amman ita koh a jikinta saida ta tabbatar baya numfashi sannan ta kyalesa, a takaice dai ta kashe malam abu, anan tabar gawarsa tayi ficewarta xuwa gida.
AMRAH dai muguwace ta karshe amman bata fiya kisaba sai idan antabota, tohfa koh waye yatabota xata kashehe illa mutum biyu,Gwaggo da kuma harira".

💫Rabeauty 💫
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: 💫AMRAH MACIJIYA 🐍🐍🐍💫

By Rabeauty 🥰💫💫💫💫

(6)
💦Jalal kam yana gama duba patients dinsa ya nufi office dinsa Wanda yake dauke da sunansa Dr. JALALUDDEEN MUHAMMAD, ciki ya shiga ya xauna kansa ya dora saman table dinsa yakai akallah 6 minutes sannan yadago idanunsa sunyi jajir, agogo ya kallah yaga 5 saura minti 10, mukullin motar sa ya dauka yafito, yana fitowa wata nurse ta taso tana cewa "sir are u going?koh kallonta beyiba yace" yes am going and pls lock my office "yayi gaba abinsa har yakai gurin motar sa sadiq ya fito da alama shima ya tashi daga aikinsa neh, karasowa yayi yace" buddy kardai ace harka tashi "so kake na kwana anan koh ya, ya fada hade da bude motar sa ya shige, da sauri sadiq ya bude gidan gaba ya shiga yana cewa" yawwa ni mumaje ka ajiyeni a gida sbd yau bada motana naxuba, bece komai ba yaja motar yabar harabar asibitin💦

💫💫💫💫💫💫

TIGADAM
Gwaggo kam hankalinta ya matukar tashi sbd yanda taga amrah ta rikide lokaci guda duk ta bi ta nannade guri daya irin yadda maciji keyi, sallamar su megarine ya kara tayar mata da hankali, dan haryau bata manta abinda yace mataba "idan har amrah ta kasance macijiya toh xasu kasheta", ai da sauri ta nufi soron danta dakatar dasu amman kash sunriga sunshigo,
Suna shigo wa idanunsu ya sauka kam amrah wacce ixuwa yanzu fatarta ta fara sabulewa tana xama ta maciji, da sauri harira tayi kanta tana Kiran sunanta, tana xuwa tasa hannu ta dago da ita, wani irin wulli akayi da harira Wanda saida tayi sama sannan ta fado kasa, da sauri innah tayi kan 'yarta tana cewa,"subhanallah yau mexan gani, amrah lafiyarki kalau kow... ai bata karasaba taga amrah ta Mike tsaye idanunta sun kara rikidewa da sauri innah taja harira suka matsa daga gurin, wata irin girgixa amrah tafara nantake taxama wata irin shirgegiyar macijiya wadda tafi tada girma dan wannan kadan yarage ta cika tsakar gidan ai wasu tuni suka xube sumammi a gurin,
Wata irin dariya ta sheke da ita marar dadin sauraro sannan tace "hhhhh dama na gaya muku xan dawo daukar FANSA, ni BAHUUL bana yafiya kuma haka xalika bana mantuwa Dan haka yau kafin nabar kauyen nan saina kashe rabi daga cikinku sannan nashiga cikin gari nayi ta'asa son raina kuma bbu Wanda ya isa ya dakatar dani,
Gwaggo ce tayi kafin halin cewa "nicenan xan dakatar dake", wani irin kallo ta watsa mata sannan tace "ai wannan ba jikarki bace BAHUUL ne kuma me iya dakatar dani mutum dayane, MAGAJI kuma a ynx bayanan ni kadai nasan inda yake, kuma a inda yake bbu me iya ganinsa hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh ya bushe da wata irin dariya, mai gari ne yace" kai maxa ku kasheta "ai da sauri suka nufeta bakinta ta bude nan take wuta tafara fitowa, gwaggo na ganin haka tayi saurin Jan hannun harira da innah sukabar gidan, AMRAH koh saida ta kashe kusan mutum 20 sannan tabi iska tabar kauyen.
Tunda aka gayawa gwaggo amrah tabi iska tabar kauyen take ta kuka tana cewa "yanzu shikenan amrah ta tafi innalillahi wa'inna ilaihirraji'un wannan masifar dame tayi kama bbu MAGAJI ynx kuma bbu amrah wayyo Allah nah ta kara fashewa da kuka, innah mah kuka takeyi tana bawa gwaggo hkr, itadai harira komawa tayi kamar mutum mutumi sbd tafiyar kawarta kuma yar uwarta ya tabata sosae.
A bangaren amrah koh BAHUUL be tsaya da ita koh inaba sai a cikin garin Kano.

💫💫💫💫💫💫💫

Jalal kam yana sauke sadiq ya nufi hanyar gida gudu yakeyi da motar sbd har anyi sallar magriba so yake ya isa gida da wuri.
AMRAH koh tana bude idonta ta ganta awani gari, nan tashiga tuno abinda ya faru, kuka ta fashe dashi ta durkushe a gurin da take, wani Dan matashine ya nufi gurinta da sallama sannan yace "baiwar Allah me kikeyi anan ke kadai kuma gashi dare yanayi, da sauri amrah ta dago ta kalleshi sannan tace" bawan Allah da Allah ka taimaka mun da ruwa nasha wlh kishin ruwa nakeji, da sauri yace "toh bari na siyo miki jirana anan" kai ta daga mishi, juyawa yayi yatafi siyo mata ruwa, ajiyar xuciya ta sauke sbd ji tayi kamar ta sareshi tasha jini sbd yunwarda takeji shi yasa tace masa ruwa take so sbd yabar gurinta sbd muddin yaci gaba da tsayawa tohfa xata iya kashe shi, tashi tayi tafara tafiya batamasan inda take jefa kafar taba,
Jalal kuma tun daga nesa ya hangi yarinya yafara mata hon amma ita amrah bata nasan da ita akeba ji kake kuuuuuuuuuut anbugeta saida tayi sama sannan ta fado kasa sumammiya, da sauri jalal yafito ya nufu kanta jama'ah harsun fara taruwa, beyi wata wataba ya sureta da sauri ya ajeta danji yayi kamar ya dauki maciji, sake kallonta yayi sannan yakara surarta yasa ka abayan mota, shiga yayi ya nufi hanyar wata asibiti da take kusa da inda yake, dan idan yace ya koma aaibitinsu tohfa xata iya mutuwa💦💦
Hmmmmm lalle jalal ka daukowa kanka jaraba
🤣🤣🤣😜

💫 Rabeauty 💫
*please vote, comment, and share *
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: 💫AMRAH MACIJIYA 🐍🐍🐍💫

By Rabeauty 🥰💫💫💫💫

(8)
Inna lubabatu kam kama hannun amrah tayi suka nufi part dinsu.
Chapter 4 · 0% Book details