← Book details Amrah Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 9

Sashe 3

Amrah Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

(7)
Wata private hospital ya kaita da gaggawa aka karbeta wata nurse ce taxo saka mata drip da sauri amrah ta rike hannunta kumafa idanunta a rufe suke dakyar ta bude bakinta tace "karki yimin allura dan Allah" a tsorace nurse din ta kalleta saidai batace komaiba, treatment din ciwonta tayi sannan ta bata maganin bacci, nan take koh tayi bacci, fitowa tayi daga dakin ta nufi office din Dr. Kamal, a can ta tararda Dr. Jalal, tace "Dr ta samu bacci, OK u can go, yace da ita, fita tayi, Dr jalal yace" Dr ni xan wuce and pls take care of her, ya tashi ya fita, shima Dr kamal tashi yayi yabi Bayansa,
Dakinda aka kwantar da ita suka nufa, bakin gadon jalal ya tsaya yana kallon gashinta daya rufe mata fuska, har yasa hannu xai jaye gashin kuma ya fasa, ya juyo ya kalli Dr kamal yace Dr xan tafi na tahu da inna lubabatu dan ta kula da ita, toh shikenan Dr kamal yace, fita suka yi a tare, Dr kamal ya koma office dinshi, shi kuma ya nufi gorin motar sa.
Yana isa gida direct part din masu aiki ya nufa, ya gayawa inna lubabatu duk abinda ya faru, ai da sauri tace "toh bari na dakko mata kohda kayan tea neh idan ta farka sai tasha,nima nadan kimtsa, OK ni bari naje part dina nayi sallah dan koh magrib banyiba gashi har ankira isha'i, yana gama fadar haka ya fita daga part din.
Part dinsa ya nufa wanka yayi ya dauro alwallah yayi sallolinda ake binsa, yana gamawa ya fito, inna lubabatu yagani a bakin motar sa tana jiransa.
Yana isowa ya bude mata motar shiga tayi shima ya shiga yaja yabar gidan, Suhaima kam duk tana kallonsu wani irin tsaki taja ta koma ciki tana Kiran sunan aunty Sarah, aunty Sarah dake saukowa daga upstairs tace "lfy kike Kiran sunana haka kamar naci bashinki, kamar xatayi kuka tace" aunty yanxu fah naga ya dawo kuma ya sake fita tare da inna lubabatu, what hjy Sarah ta fada, hmm lalle inaganin karshen xaman ta a gidan nan yaxo har tayi matsayin da xata fita tare da jalal hmm, amma bari tadawo muji dalilin fitarsu tare.

*************
A harabar asibitin yayi parking agogon hannusa ya kalla karfe 9:00 yagani Dan karamin tsaki yaja, fitowa suka yi ya kaita har room dinda amrah take beko shigaba yajuya yayi tafiyarsa.
Inna lubabatu kam ajiye kayan da taxo dasu tayi, ta nufi gurin amrah dake bacci har ynx gashinta ta gyara mata da sauri taja da baya tana cewa "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" Dan kara lekowa tayi Dan ita wannan kyan na amrah ya bala'eeeen bata tsoro kyau sai kace aljana, kayan shimfidar ta ta dakko ta shimfuda tayi addu'o'i sannan ta kwanta bacci.
Jalal kam yana komawa part dinshi yasa key ya kulle Dan daxo yaga Suhaima kuma yanada tabbacin ta gayawa mommy kuma yasan xa'a iya aiko ta ta kira shi shiyasa ya kulle part dinsa.

***************
Washe gari hajiya nafeesa takawowa hajiya Sarah magani wai a saka masa a ruwa tohfa dayasha ruwan xai mutu.
Jalal kam koh aiki bejeba direct hospital ya nufa.

✨✨✨✨✨✨
Hospital.
A harabar asibitin yayi parking, direct dakin ya nufa, yana shiga inna lubabatu na fitowa daga toilet, gaisheta yayi sannan ya xauna yana cewa "wai har yanxu bata farkaba" eh wlh ni abun ma yafara bani tsoro, OK bari na kira nurse ya tashi xai fita kenan saiga nurse tashigo, kara sawa suka yi bakin gadon, a daidai wannan time din amrah ta fara bude idanunta, dishi dishi take ganinsu sai can ta rinka ganin su da kyau yunkurawa tayi xata tashi, da sauri nurse din ta taimaka mata ta tashi xaune, dan dagowa tayi ta kalli jalal Wanda shima ita yake kallo, kurawa juna ido suka yi, ita tana marvelled beauty dinsa, shikuma yana astonished eyes & beauty dinta, shiya fara janye idanunsa, sannan itama ta janye, ita kam nurse tunda taga idanun amrah tsoro ya kamata, kasa hkr tayi tace "baiwar Allah meya samu idonki, dan kallonta jalal yayi, wani kallo amrah ta jefe ta dashi Wanda yasa jikin nurse din fara rawa da sauri tace" Dr bari naje nakira maka Dr kamal"batama jira cewar saba tayi sauri ta fita.
Inna lubabatu ce ta matso kusa da ita tace "diyata na hada maki tea", kallon ta tayi tana tunanin menene kuma tea, kai ta daga alamar eh Dukda koh batasan menene tea bah, tashi inna lubabatu tayi ta nufi gurin da ta aje kayan tea tashiga hada mata.
Jalal kam ganin Dr beshigo bah yasa shi tashi ya nufi office dinsa yana kokarin shiga shikuma yana fitowa, yace "aa Dr jalal har kaxo, eh wlh nama Dan dade ai xuwa nayi a samu sallama pls, OK muje gurin ta tukunnah, suna shiga yayi daidai da gama shan tea dinta, karasawa Dr kamal yayi gurin ta yace" yam mata ya jikin, koh kallonsa bata yiba, balle yasa ran xata amsashi, dan tambayoyi yayi mata amma ba wanda ta bashi amsa da baki, saidai ta daga masa kai koh ta girgixa.
Juyowa yayi ya kalli jalal sannan yace "muje na Baku sallama, xaiyi magana kenan wayarsa ta fara ringing dubawa yayi (mommy) nagani a screen din wayar dan karamin tsaki yaja, ya juyo ya kalli inna lubabatu sannan yace" ki hada komai da komai kikai mota sbd ynx x
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: 💫AMRAH MACIJIYA 🐍🐍🐍🐍💫

By Rabeauty 🥰
💫💫💫💫💫💫💫
*In the name of Allah, the most beneficent, the most merciful.
*Seeking for guidance and protection of Allah as i am going to start ❤️
Ya Allah!!!
Guide my heart, and protect my hand to the end of this book, AMEEN.
Chapter 3 · 0% Book details