← Book details Amrah Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 9

Sashe 2

Amrah Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

✨ TIGADAM✨
AMRAH kam iska tabi ta tare harira a bakin hanya, harira har xata gudu amrah tace "idan kika kuskura kika kara taku daya toh xan kasheki, ai kamar andasata a gurin ta tsaya, karasuwa amrah tayi kusa da ita sannan tace" meyasa kikeson ki fallasa sirrinah, meyasa kikeson ki gayawa gwaggo cewar ni macijiya ce, toh bari kiji wlh, wlh, wlh harira kika kuskura kika gayawa gwaggo koh kuma wani cewar ni macijiya ceh hmmmmm kinsan sauran, girgixa kai harira ta shiga yi hawaye na sauka akan fuskarta tace "amrah baxan xuba idobah ina kallo kici gaba da kashe mana mutane bah, hannuwanta ta hade guri daya alamar roko🙏sannan tace" Dan Allah amrah kidena kashe muna yan uwa, dan Allah na rokeki,
Tsaki amrah tayi tace "wlh harira duk Wanda ya shiga gonata wlh saina kasheshi Dan haka kidena wa
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: 💫AMRAH MACIJIYA 🐍🐍🐍💫

By Rabeauty 🥰💫💫💫💫💫

(3)
Hannunta tasa a cikin rafin ta ibo ruwa ta watsamata, a firgice ta farka tana ja da baya tana girgixa kanta hawaye na sauka akan fuskar ta cikin rabewar murya tafara mgn"da.. dan Allah am.. rah kiyimin rai kar.. ki kasheni, murmushi tayi sannan tace "hmmmmm harira kenan da inada niyar kasheki da tun ranar da kika fara ganin idanuwana da a ranar xan kasheki amman kuma baxan iyaba sbd yadda na daukeki kamar yar uwata tajini shiyasa baxan iya kasheki ba" ajiyar xuciya harira ta sauke sannan tace "kenan duk kashe kashen da akeyi a kauyen nan kece, kuma ke kika kashe malam abu? Eh nice kuma duk wanda kikaga na kashe toh yashiga gonata neh, kuma ni bana yafiya kuma bana mantuwa, kuma wannan abun daya faru inason yaxama sirri a tsakanin mu sbd koh gwaggo batasan cewa ni MACIJIYA ce bah"inshaa Allah ba Wanda xaiji toh amma wa'ennan da kika kashe yaza muyi dasu? Anan xamu barsu, ido 👀harira tafitar waje tana cewa "anan kuma amrah? Eh tashi mutafi, xata sake mgn amrah ta daka mata tsawa tare da tsareta da green eyes dinta, ai nan danan harira tahadi ye abunda tayi niyar fada, cikin kauyen suka nufa, AMRAH tashige gidansu itama harira tayi gida.
Washe gari da misalin karfe 4:00 mutane sunfara taruwa a fadar mai gari kuwa jiran maccido mai macixai yake ya kara so dansu wannan masifar tayi yawa.
AMRAH koh tuni ta fice daga gida lokacin gwaggo na bayi batama San da fitarta bah.
Farkon shigowa gari tanufa ta haye saman bushiya tana jiran isowar maccido mai macixai 🪱, aiko can ta hangoshi saman rakumin sa 🐫da wata katuwar leda da gani dai kasan magunguna neh a cikin ta.
Murmushin mugunta tayi sannan ta diro daga kan bishiyar ta tsaya bakin hanya, tun daga nesa ya hangeta, sanye take da kaya green har mayafin kanta green neh, yana isowa ya sauko daga kan rakumin sa, yanufi inda take yana cewa"ke yarinya me kikeyi anan gurin maimakon ace kina fadar mai gari".
Mayafin kanta ta yaye ai maccido nayin toxali da idanunta yagane macijiya ce, ai da sauri ya juya xai dauko kayan aikinsa amman ina harta xama shurgegiyar macijiya 🐍, xata kai mishi Sara sai kawai tagaya bace, kafin ta juyo taji anyan keta da takobi, ⚔️, kafin ta juyo kuma yasake bacewa, nantake ranta yakara baci, sai naga tana kara girma Wanda saida yakusa cika dajin, idanuwanta sunkara xama green sosai kwayar idonta tarinka fitarda wani haske, toh a cikin wannan hasken neh ta hangoshi ta bayan ta xai sake yankarta, ai a xafafe ta juyo takai masa wata irin Sara a wuya, nan take ya xube matacce a gurin dukda haka bata barshiba saida tayi masa jina jina, sbd bbu Wanda yataba Cin galaba a kanta saishi.
Rikidewa tayi ta dawo mutum, inda ya yanketa tasa Hannunta na dama ta shafe gurin, aiko ya dawo daidai kamar ba'a taba yankantaba.
💫💫💫💫
A fadar mai gari kuwa, kowa ya halarta shi kadai ake jira, ganin har 5:20 ta wuce yasa mai gari tura fadawansa su uku akan suje su dubo koh lfy.
Aiko suna xuwa suka tarar da gawarsa a bakin hanya, da gudu sukabar gurin, suna isa suka sanarda mai gari abunda suka gani, hmm lallai wannan shi ake kira tashin hankalinda ba'a sakawa rana, domin kowa ya shiga tashin hankali.
Harira najin haka, hankali tashe tabar gurin, gidansu amrah ta nufa tana xuwa kai tsaye tace "amrah meyasa kika kashe maccido?
Wani banxan kalloh tayi mata sannan tace" sbd ya shiga gonata "harira tace" haba amrah wai mekike son kixama, ke bakyayin wuyar kashe mutum, haba amrah kiji tsoron Allah, duk wannan abun da harira keyi kawai karfin haline, sbd a tsorace take da amrah.
Ran amrah ne yafara baci domin koh har fatarta ta fara sabulewa tana xama ta maciji, harira na ganin haka ta fita da gudu dan tasan idan ta tsaya toh fa saidai buxunta 🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️.

💫Rabeauty 💫
*please vote, comment, nd share *
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: 💫AMRAH MACIJIYA 🐍🐍🐍💫

By Rabeauty 🥰💫💫💫💫

(5)
Da sauri amrah ta nufi gurin gwaggo tana girgixata tana cewa "Dan Allah gwaggo kitashi idan kika mutu ya xanyi, hannunta tasa a saman kirjin gwaggo ta rufe idonta, tana budewa wani haske green yafito daga idanta ya sauka kan kirjin gwaggo, wani dugun numfashi gwaggo taja, ajiyar xuciya amrah ta sauke, sannan tace gwaggo nah,
A hankali gwaggo ta fara bude ido da fuskar amrah tayi toxali ai da sauri ta tashi xaune tanaja da baya, da sauri amrah ta rike hannunta tace "gwaggo nah tsoro na kike?
Kai gwaggo ta girgixa tace" innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, magaji kaja mana masifa,
Amrah tace wace irin masifa babana ya jawo mana wadda ni bansaniba?
Hmmmmm FATIMA a yau xan sanar dake wanene mahaifinki.

💫💫💫💫💫💫
Tuna Baya.
Anyi wani jarumin mutum kuma sadauki Wanda duk kauyen nan bbu mai karfi irin nasa, har takai ga yana fada da mayu, aljannu da kuma macixai, sbd hakan neh yasa ake kiransa da magaji, mahaifiyarki kuma ta rasune a lokacinda xata haifeki.
Akwai wani shahararren maciji, mugu, Wanda ya addabi jama'ar wannan kauyen, ba halin mutum yafita sbd da xarar ka fita xai kashe ka, sunansa BAHUUL, ansha gwagwarmaya tsakanin sa da mahaifinki wato magaji, kafin yasamu nasarar kasheki, kafin ya mutu saida yace "hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh lallai magaji kayi namijin kokari gurin kasheni, toh amma inason kasa wannan a ranka SAINA DAWO DAUKAR FANSA, kuma akan 'yarka,
Yana gama fadar haka ya mutu, hankalinmu ya bala'eeeen tashi, haka muka rinka kula dake koh bandaki xan shiga bana barinki ke kadai saina jira mahaifinki ya dawo, haka dai mukata baki kariya, har kika shekara uku amma bamuga wani abu ya sameki bah, tun daga ranar muka share xancen BAHUUL, muka dauki xancensa a matsayin karya.
A wata assabar ranar da baxan mantaba, koda aka wayi gari bbu mahaifinki bbu labarinsa, hankalin kowa dake kauyen ya tashi matuka domin rashin magaji agaresu babbar matsalace, duk kauyen da yake kusa damu anduba amma ba'aga mahaifinki bah, har xuwa yau danake gaya miki wannan xance.
Hawaye amrah ta share sannan tace "gwaggo dama baba yana raye"eh FATIMA mahaifinki yana raye amma bansanarwa yanxubah, kuma nasan BAHUUL neh ya shiga jikinki domin ya dauki FANSA, amman dan Allah amrah tunda dai harkina da ikon juya kanki dan Allah kidaina kisa,wlh gwaggo bana sanin lokacinda nake yin kisa, nasan bayin kanki bane amrah amma Dan Allah kikara kokarta.... Bata karasa abinda xata ceba taga amrah ta tashi da sauri tana rike kanta, da sauri gwaggo ta tashi ta nufeta, AMRAH meya sameki, dagowa amrah tayi idanunta sunkara rinewa Dukda da farinda yake tsakiyar idonta yakoma green, tsoro neh ya kama gwaggo taja da baya,
Wani irin raxanannen ihu amrah tasa Wanda gaba daya ya karade kauyen, faduwa tayi akasa tafara nannadewa yadda macixai keyi, amma fah bata koma macijiya bah.
Mutanen gari kam kowa yaji wannan ihun kuma sunji daga gidan gwaggo neh ihun yafito, shiyasa suka nufi gurin maigari, aka hadu aka nufi gidan gwaggo hardasu innah da harira, itadai harira gaba daya jikinta rawa kawai yake.

💫💫💫💫
KANO STATE.

💦JALAL kam yana fita ya shiga motarsa yabar gidan, wayarsa ce tafara ringing screen din nakallah ✨SADIQ ✨nagani arubuce, dauka yayi yasa a hands free daga can SADIQ yace "buddy ka iso" yes na iso ina hanyar xuwa office, daga can SADIQ yace "haba buddy daga dawowarka xata fito aiki kabari ka huta pls,dan karamin tsaki JALAL yaja yace" buddy kasan baxan iya xama a cikin wannan gidanba idan daddy bayanan, OK buddy saikaxo, ya kashe wayar yaci gaba da driving,
Wata babbar hospital ya nufa yayi parking, yana fitowa yam mata suka xuba masa eyes sunga dan handsome kyakkyawa balarabe sun saka mishi eyes, shikam koh ajikinsa danya saba da kallo, direct office din SADIQ yanufa, yana shiga ya samu guri ya xauna, wani hadadden guy neh ya fito daga wani daki farineh sosai amma bekai hasken JALAL bah amma fah dukansu sunaji da kyau, karasuwa yayi yaba shi hannu suka gaisa sannan ya xauna,
Yace "buddy wai har yanxu mommy bata dena nuna maka tsanaba, hmmmmm da farko dai tadena amma yau dana dawo inna lubabatu mai aikin mu take gayamin karnaci abincin da hajiya tayi sbd tasa guba, ido SADIQ yaxaro yace wai so take ta kashe ka, kamar yadda ta kashe ammi wai meyasa wasu basuda imani, idanun JALAL kam har sun fara canxa kala sbd bacin rai,
Tasowa SADIQ yayi ya dawo kusa dashi yadafa kafadarsa yace "buddy akwai mafita" da sauri JALAL ya kalleshi yace "wace mafita" Aure, what JALAL yafada, eh JALAL aure neh kawai mafita, hmmmmm gsky u re not serious sadiq nida bana kula yam mata ina xan samu wacce xan aura, kumafa mommy so take na auri suhaima, kuma muddin daddy yasan da wannan xancen tohfa bbu makawa saina aureta, gashi kuma wlh bana sonka kai koh ganinta banason yi,
Ka kwantar da hankalinka buddy, inshaa Allah kafin su yiwa daddy magana kasamu matar aure, hmmmmm kawai jalal yace tare da mikewa yace "bari na duba patients dina,
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: 💫AMRAH MACIJIYA 🐍🐍🐍💫

By Rabeauty 🥰💫💫💫💫
Chapter 2 · 0% Book details