← Book details Abu Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 5 OF 5

Part din shi ya shiga ya mayar da kofan garam don ba mai kara bane kofan da kowa na gidan yaji sautin bugawan da yayi a lokacin.

Abu Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 655 min read

Oho god ya fada yana sasauta kwalan rigan shi sai zufa ke sharto mashi ta ko ina a jikin shi lokaci guda.
Zaune yakai ya mike kafa tare da dafe goshin shi ga wayan shi na kara ana kiran shi ya kasa dauka a lokacin.
Don yadda yake jin kansa na juya masa ya dade bai sha cocaine a rayuwan shi ba badon baidashi ba sai ranan yaji shi kawai yake son sha a lokacin.
Mikewa yayi ba tare daya tsaya kula wayan shi dake ruri ba a lokacin ya nufi inda yake aje kayan aikin shi ya dauko ya dawo tare da jawo dan table din dake gaban shi.
Ya zuba a gurguje ya fara shaka yana daga kai kamar kadangare kafin ya mike zuwa kitchen din dake part din ya nufi wurin fridge ya bude ya dauko kankara da cup ya saka tare da dauko kwalban giyan shi ya dawo ya zauna.
Bai daga ba sai da yayi tatil ko dagawa bai iya yi a wurin nan ya zube babu shirmen da baiyi ba a dakin shi kadai a cikin dakin.
Kamar zai buga yake jin kanshi a lokacin ya manta da inda yake balle maganan dake damun shi har safe mai gyaran gida ya shiga ya sameshi kaca kaca a dakin shine yazo ya kirani hankali tashe.
Ranan nayi kuka kamar Allah ya aiko ni karshe dai haka na daure na kamashi da kaina na kaishi bandaki na tubeshi haka kawai dabara yazo min in watsa mai ruwa masu sanyi a jikin shi .
Ruwan na sauka a jikin shi yayi firgigit tare da ajiyan zuciya wanan katon ma kukan baizo min ba juyawa nayi na fita daga bandakin.
Dakin nasa na fara gyarawa kafin na koma falo na gyaro na na saka kamshi a ko ina saboda amai da sauran najasan daya sake.
Na koma dakin zaune na sameshi da tawul daure a kugun shi ya zauna ya hade hannayen shi wuri daya tare da dukar da kanshi kasa kamar mai tunane.
Ina ganin shi haka a zaune nayi saurin juyawa zan fice dakin sunana naji ya ambata har lokacin mayer bata gama sake shi ba nake gani.
Kizo ki dauko min kaya na saka a jikina ya fada kanshi yana duke bai dago ba dan jin nayi kafin na juya na nufi wurin kayan nasa na bude.
Rasa wanda zan dauka nayi dayake nasan kayan nasa farare ya faye sakawa na dauko wani wando fari da riga shirt fara na kawo mai.
Under fa ya fada bayan na aje mai kayan a gefen shi na juya na dauko singlet da box dake jere a wurin.
Ina ajewa na fice dakin ban tsaya ba daki na koma na haye gado dama na shirya zan tafi school ne yanzu kuma na makara da zuwa school din.
Nayi kuka har na gaji kusan awa daya ya leko part din nawa ya sameni a kwance na kifa ciki yasan ba barci nakeyi ba a lokacin.
Yau ba zaki shiga school ba ke nan ya fada yana tsaye sai kamshi ke tashi daga jikin shi kamar bashi bane dazun a cikin najasa hakanan yanzu ko yasha wanka yana kamshi.
Ido na dago da sukai min ja dan kuka ya gani yayi kamar bai gani ba wani kallo na watsa mai ya juya da sauri ya fita daga dakin.
Nan ya barni kwance na dasa sabon kuka a fili tare da dinbin nadama da dana sani yafi dubu ina blaming din kaina da iyayyena.
Nayi sati bana yarda mu hadu dashi a gidan idan na dawo ina dakina ko wurin su fadila na daina shiga ga damuwa da yai min yawa.
Da ka ganni zaka gane hakan saboda ya nayina daya nuna hakan lokaci guda Fadila tayi tambayan duniya nace babu komai karatu ne kawai yai zafi ya sakani komawa hakan.
Kyaleni tayi ba don ta yarda ba bata kara tanka wanan maganan ba ta saka min ido amma a ranta tasan akwai abinda ke damuna dana koma hakan lokaci guda.
Tsakanina dashi kan kamar sarakai muka koma don shi baison mu hadu ni kuma ban son gani shi sam don na tsaneshi har kasan zuciyana a yanzu.
Ranan na manta da wayana a dakin fadila don haka wayan a can ya kwana dakin nasu tun da asuba kafin nayi sallah asuba na bude daki na fito don in buga masu su bude saboda maya zata turo min wano sako a wayan tunda dare nake jira.
Ina budan kofa mukai kicibis da wasu samari biyu suna fitowa daga part din yaya ko shigan su ma abin tsorone dan da gani su tantiran matasan kasan ne.
Wani irin kallo suka bimu dashi sai da tsoro ya kamani don ganin su wayan da ban dauko ba ke nan na koma daki da sauri na rufe wasu hawaye suna zuba a idona.
Sai zance nake kamar mahaukaciya a daki ni kadai da sauri na mike tsaye dan karamin jakkana dake aje tun zuwan mu kasan.
Kaya nashiga hadawa lokaci guda a gurguje na fito da dan troler dina zuwa part din su fadila na buga masu kofa suka bude.
Anty ku dauko kayan ku mu bar gidan nan tun kan gari ya waye muna a nan gidan kallon mamaki fadila ke min.
Saida na kai karshen magana take fadin kanki daya kuwa zainab ina kike nufin mu nufa da wanan safiyan haka yanzu.
Duk inda muka samu na bata amsa ina fadin ba zan zauna gidan wanan mai sabon Allah ba kuma.
Kiyi tunane zainab nan fa ba kasan mu bane muna a garin mutanene yanzu ina kike son mu tafi yanzu idan mun bar gidan nan.
Hannun halimatu na jawo tare da daukan akwatina ina faman ja muka fice a gidan tana tsaye tana kallon mu da mamaki a fuskanta.
Ganin da gaske mukeyi yasa ta nufi part din yaya jafar dake kwance shame shame saman gadon shi ko sallah safe baiyi ba ta shiga dana mashi door bell babu kakautawa lokaci guda.
Tsuki yaja yana mamakin waye wanan da safe haka yake damun sa dan nawan da yayi kafin ya bude kofar yasa har muka samu taxi muka shiga muka bar unguwan.
Yana budewa tana tsaye a cikin damuwa tace sir kazo ga madam can da sister ta zasu bar gidab nan sun dauki bag din kayan su sun fita.
What ya fada tare da kallon jikin shi daga shi sai bathrobe din dake jikin shi daya dauko yasa da zai fito kofan.
A hakan ya fito abinda bai taba yi ba tun kan ya fito yake fada da fadila don me bata fada mai ba da wuri ta bari muka fita daga gidan.
Babu kowa wajen gashi ba ranan aiki bane sai yan tsiraru mutane dake zirga zirga a unguwan.
Kai ya dafe da hannu daya tare da fadin shit yarinyar nan tana son caza min kai a garin nan how come zata bar gidan nan ya fada a fili.
Sai kuma ya juya wurin fadila ya hauta da fada don me zata bari har mu fita bata sanar mashi ba yanzu gashi mun doshi wani wajen da ba,a sani ba.
Nan ya barta ya juya cikin gidan a gurguje ya dauki key din mota da kanshi yai driving ya rasa inda zai tafi sai tafiya yake a unguwa yana dube dube ko zai ganmu.
Muko mai taxi ya tambaye mu wani wurin shakatawa da muke yawan zuwa nace ya kaimu lokacin ya ajemu na biyashi kudin shi.
Sai lokacin na fara wiki wiki da idanu na rasa abinda zanyi a lokacin abu na farko shine na fara tambayan ko halimatu zata ci wani abu don nasanta bata wasa da ciki ta ko kadan ita.
Wurin masu hada irin abincin su a bakin titi din nan naje aka hada mata taliya da tarkacen su don ita tana iya cin abinci su yanzu.
Wuri muka samu muka zauna taci saida ta koshi niko ina ta faman tunane a raina na inda zamu sai dabaran zuwa hotel ya fado min a raina.
Tana gamawa muka bar wurin don kallon da ake muna yayi yawa a lokacin munyi sa,a mun samu hotel mai dan saukin kudi muka kama bayan na nuna masu ID card dina na karatu.
Dakine mai dan gado da tv a ciki sai ban daki da sauran tarkace a cikin dakin wanka halimatu tayi ni kuma ina zaune ina faman tunane a raina.
Yaya ina zamu daga nan halimatu data gama shiri take tambayana nace gamu dai tukunna halimatu gida nake son mu tafi daga nan idan mun samu hanya.
Abin kurciya sai ta hau murnan jin wai gida zamu tafi tausayin kan mu ya kamani a hakan barci mai nauyi nayi sosai a lokacin daga ni har halimatu data kwanta a gefena tana danna laptop itama tayi barci.
Da wani irin matsakacin yunwa na falka ina neman abinda zanci a cikina lokacin fita nayi na nemo muna abincin na dawo dakin dashi .
Na samu halimatu falka a dakin tana wuri wuri da idanu sai gani na shigo ta sauke ajiyan zuciya tare da tambayan inda naje ?


ZAINAB IDRIS MAKAWAMASHA ALLAH ANOTHER FRIDAY AGAIN MAY ALMIGHTY ALLAH ACCEPT OUR IBADA FOR THIS FRIDAY ALLAHUMA AMIN, , , ,

YAR UWA TUNI GAREKI KI BIYA KI KARANTA WANAN LABARIN KARUWAN DA ZAKI SAMU A CIKI YAFI ABINDA ZAKI BADA YAWA UBANGIJI ALLAH YA TSARE MUNA ZURI,AN MU AMIN, , ,


Kwanan mu biyu a dan karamin hotel din ga wayana na kashe tun fitowan mu gidan wayan yake kashe ban kunna ba.
Haka yasa duk kokarin yaya wurin gano inda muke baiyi nasaran gane komai ba hankalin shi ya daga ga baki daya har yakai rahoton batan mu a wurin yansandan kasan.
Ban komai a dakin sai ibada da kuka sai kuma tunanen hanyan da zanbi mu tsare a kasan da bamu da kowa illa shi da ya kawo mu garin.
A kwana na ukune hakkurin halima ya kare ta matsa min sai mu fita tare sayen abincin kamar yadda na saba fita in sayo muna duk abinda take so a cikin dabara.
Yau kan ta tubure min akan tare zamu fita haka na daure muka fito har waje da ita muka sai abinda zamu saya muka koma ciki.
Saidai irin kallon da mutanen ke min yasa na dan tsargu don da farko na dauka don launin fatan mu daban da tasune yasa suke kallon mu haka.
Bayan na dawo dakin ina zaune ina kallon yadda halimatu take cin abincin ta hankali kwance kamar ba abinda ya dameta.
Wani tunane yazo min lokaci guda na mike na fara tattara kayan mu da sauri naja hannun halimatu muka fito key din su na mika masu don basu biyo mu kudi ba mune ma muka biyo na kwana biyu a wurin su.

Yana tsaye sai waya yake faman yi daya kashe wanan ya dauki wanan ya rike kunkurun shi da hannu daya.
Yayin da dukkan aninaiyan suit din jikin shi suke bude ta gama daka ganshi kasan hankalin shi a tashe yake sosai lokacin.
Waya ya shigo mai ya dan juya ya kalla rai bace tare da jan guntun tsuki yana kawar da kanshi gefe daya.
Bayan kiran ya katse wani ya sake shigowa ya daga a hasale muryan mace yaji tana fadin yaran da ake nema aka bada wanan layin.
Na gansu yanzu a hotel din green land akusa da child center na wanan birnin yace hold on ki kara fada min yadda bayanin shigan su yake.
Ta shiga mai kwatance tare da siffan mu da yanayin komai namu da sauri ya mike ya figi key din shi sai inda suke parking din mota ya shiga daya daga cikin motocin dake wurin.
Ganin haka security din shi suma suka bi bayan shi da sauri duk inda yabi suna biye dashi har zuwa green land motel dake gefen garin.
Inda muke takai da security din hotel din akan kin barin mu mu fita daga cikin hotel din da sukayi don kawai su tabbatar idan bamu bane ake nema.
Muna tsaye wiki wiki ya iso wurin a har gitse halimatu na ganin shi tun daga nesa take nunashi da hannu tana fadin lah ga yaya a cikin harshen hausa ta sheka da gudu ta fada jikin shi .
Shima rungumeta yayi a jikin shi na dan lokaci kafin ya dago kai ya kalleni ba tsoro ko kadan a fuskana illa kara daure fuska danayi kawai.
Mayar da hankalin shi yayi wurin ma,aikatan hotel din suna mashi bayanin tun zuwan mu da yadda suka gane mune ake nema a tv.
Godiya yai masu tare da basu abinda akai alkawarin ba wanda ya ganmu dayan security din ya duka zai dauki dan jakkan kayan dake gabana don har lokacin ban ko motsa a yadda nake zaune ba.
Wani tsawa na daka mai tare da fadin don't touch my bag ya dan dago daga inda yaya yake shikuma yace da mutumin ya dauka su tafi.
A daidai lokacin da yake takowa inda nake zaune ya tsaya a gabana na dan wani lokaci kafin yace kiyi hakkuri mu koma gida muyi magana a can yanzu idon mutane na a kan mu.
Na dago kai na dan kalli wanda suke wurin idanuwan su ko na akan mu suna dan magana kasa kasa.
Haka yasa na mike badon naso ba na fara takawa a hankali yana rike da hannun halimatu suka biyoni a baya.
Motan shi muka shiga saida mukai nisa da hotel batare da ya juyo ba ya fara magana yana fadin daga yau idan zaki kara irin wanan kada ki soma ki tafi da sadiya.
Don ba zaman ki takeyi a garin nan ba ni da kaina na karbota hannun iyayyen ta don haka baki da ikon aiwatar da wani abu a kanta yanzu.
Amma kada ka manta ita din yar uwatace bana wani ba idan ba don niba bazata zo nan kasan ba tare dakai.
Don haka ba zan barta ta zauna a gidan da fasadi yazama ruwan shan don sabon Allah ya zamo shine alkibilan ka ko yaushe.
Dan murmushi naji yayi bayan hakan bai kara furta komai ba har muka isa gidan mota na tsayawa na fito na barsu da halimatu a baya.
Ban bi takan kowa ba part dina na nufa yana rufe na dawo part din fadila sai ganina tayi kamar daga sama ina shiga gado na fada ina kuka.
Sunana ta kira da karfi zainab kece wai Allah mun godema ina kuka shiga haka a wanan kasan mai yawa kuma gashi ba kasan mu ba ?
Jin yadda nake gumjin kuka yasa ta bar tambayan da take min din don itama hankalin ta ya tashi a yadda ta ganni na shigo dakin.
Saiga halimatu tana jan dan troler din mu da gudu ta fada jikin fadila tace sadiya kun dawo wallahi tun tafiyan ku hankalin kows gidan nan a tashe yake.
Shi kanshi me gidan baya zama gida kullun cikin neman ku yake ko za aji labarin ku mundai godewa Allah tunda kun dawo lafiya ai.
Bari na kawo maku abinci kuci ta fada tana kokarin mikewa halimatu tace anty a koshe nake yanzu bazanci abinci ba.
Muryan shine daga kofa yake fadin ki taso an bude part din ki daga haka ya juya ya fice abinshi bai tsaya jiran komai ba.
Dafani fadila tayi tana fadin zainab kin ki ki saurareni ne ranan da baki tafi ba wallahi duk da tafiyan naku ya dagawa mijin ki hankali sosai .
Saidai kusa lefin tafiyan naku duk a kaina ya dora shi yaga laifina sosai dana bari kuka tafi nasan da a Nigeria muke babu abinda zai hana ya koreni tun ranan.
Zainab koma me yai maki mace da hakkuri aka santa bada saurin fushi ba don kinyi kankanta dayin yaji a shekarun nan naki.
Jin abinda ta fada yasa na dago kai nace amma banyi kankanta a wurin hisabi ba ko anty ?
Kina ganin yanzu idan na mutu Allah ba zai mun hisabi bane kwadayi ko son duniya yasa in zauna a gidan mai sabon Allah irin haka.
Yaya jafar ba irin mutanen da suke shirin tuba bane da sabon Allah da sukeyi a rayuwan su har sai yaushe yaya zai daina wanan halin ya tubawa Allah.
Kuka yaci karfina ta samu ta lalabani da ban baki da magana masu taushi har na tsagaita kukan da nakeyi din.
Ban bar fakin ba sai bayan sallah magariba na koma part dina nayi wanka na kwanta duk da nasan ba barci zanyi ba a lokacin.
Tun ina tunanen matakin da ya kamata in dauka har barci yai awon gaba dani a wurin ashe yazo yana kwankwasa kofan ban budeba a lokacin.
Washegari na kunna wayana da ya kwana yana caji a jone sako ya fara shigo min wanda duk kusan sakon maya ce tana tambayan rashin gani school kwana biyu.
Sai kuma sakon shi yaya da yake tambayan muna ina don Allah mu dawo gida idan sakon shi ya sameni.
Zamuyi magana in fada mashi damuwa na ba sai na bar gidan haka ba yana dai tsoratani ga barin gida da mukayi a wanan kasan haka.
Tsuki nayi bayan na gama karantawa na wurga wayan saman gado na mike zuwa wanka nafito na shirya tsab don fita school .
A falo muka hadu da fadila fuskana babu walwala na gaida ita ta amsa min a cikin fara daganin shirina ba sai an tambayi inda zani ba.
Hakan baisa ta kyaleni ba take tambayana bazan tsaya in karya bane nace banjin cin komai a yanzu ina kokarin fita falon.
Nakai kofa take min a dawo lafiya da farko banga driver dake kaini school ba har na nufi katafaren get din gidan naji ana mun horn a bayana na waiga.
Driver ne a cikin wata yar mota daganin motar taci kudi masu yawa kafin a mallaketa.
Madam ga motar da oga ya canza muna yanzu wancan satin aka kawo ta yace an tsaya service din tane.
Kamar bazan shiga ba son dan guntun tunanen danayi a zuciyana sai dai na bude na shiga muka fice gidan.
A school kan nasha kallo don photo na da yai yawo a garin ko ina ana cigiyan mu nida halimatu na.
Fuskewa nayi na shige class din mu nan ma dai ban tsira ba maya ce ta tareni a cikin fara,a da mutuntawa tazo ta rungumeni.
Dama wuri daya muke zama da ita nan muka zauna muna dan hira amma bata sako min zancen batana dataji ance munyi ba a garin.
Sai biyu muka fito break wurina samu nayi alwala da sallah kamar yadda na saba kebewa in yi sallah idan ina school.
Maya na zaune gefe tana karatu har na gama take cewa mu dan taka wurin cin abinci don ita yunwa takeji.
Mun zauna a wurun an bamu dan abincin su da akeci da tsunke na tasa nawa gaba ina tunane ban taba ba.
Dafani maya tayi na dago firgigit na kalleta abincin ta nuna min da ido alaman inci abincin mana.
Dan murmushi na kakaro a fuskana na fara cakulan abincin da dan tsunken dake hannu na kadan naci na ture plate din abincin daga gabana na dauki ruwa na kurba kadan.
Koda baki fada min ba nasan kina da damuwa a ranki wanda hakan ya shafi matsalan gidane ko ?
Kasa nayi da kaina don idona da suka cika min da hawaye lokaci guda ban sa amsan da zan bata ba a lokacin gashi banda abokin shawara bayan fadila.
Fadilan kuma yanzu na kara wayau ba komaine zan iya sheda mata daya shafi mijina ko banza kasan mu daya koda ba garin mu daya ba.
Don a tunane ban dauka da tasan wanan zancen na yaya ba ashe ita kar take daukana tana dai taka tsantasan ne don kada aikinta ya kubce mata.
How can i help you ?
Ta kara fada tana kallona na dago kai a hankali na kalle ta a lokacin har hawayen da nake tarewa sun fara zuba a idona ko.
Tisui ta miko min daga cikin jakkanta na karba na dan goge fuskana dashi a daidai lokacin ta mike tsaye tare da fadin time yayi na komawan mu last period.
Mikewan nayi muka jera zuwa ciki saidai babu wanda ya iya magana a cikin mu don kowa da irin tunanen da yakeyi a cikin ranshi.
Haka na koma kwana biyu bana son magana da kowa a gidan don gaskiya ina cikin damuwa sosai na tsorace da al,amarin yaya zuwa yanzu.
Wanka nafito ina tsaye a dakin ina tsane ruwan kaina da dan karamin towel da daura gaban zani a jikina .
Ranan babu inda zan tafi don satine kowa na gida yana hutu a ranan kamar daga sama sai ganin yaya nayi a dakin.
Kallo daya yai min ya kawar da kanshi da sauri na nufi wurin gado na daki hijjab dina na saka a jikina ya kai zaune yana dan tabe bakin shi alaman ko a jikina ni.
Dan shirune ya biyo dakin kafin naji muryan shi yana fadin wai ke meke damun ki haka kike rama?
Kinbi kin damu kanki kin sakawa zuciyar ki wani damuwa da bai shafeki ba haka ?
Zaka iya fadin haka idan kaga dama kuma hakan ba zai ban mamaki ba ko kadan duba ga yadda ka tara kai shedan nama fitsari ko wani lokaci.
Yau dan musulmi dakai yaya kake wanan fasadin a rayuwan ka kamar dan wasu arnaku da baisan addini ba da abinda Allah yace.
Wani kallo yai min a harzuke take idanuwan shi suka kade sukai wani irin ja jajir ban fasa fadan abinda zan fadi din ba duk da ganun hakan danayi.
Yaya yau yaya mami zataci danta na kwana da maza yan uwan shi mazan ma ba daya ba yaya har maza biyu a lokaci guda.
Wa,iyazu billahi ko dabbo bi yan a halal kitabi bazasu taba aikata hakan ba don sun san da Allah ya hanesu da hakan suna tsoron azaban da Allah ya tanadarwa mai wanan dabian.
Wani irin kallo yake min lokaci guda kamar ranan ya taba ganina a rayuwan shi ji nayi kawai ya dankeni iya karfi shi.
Sai dana dan sake karan wahala muryan shi naji yana fadin uban wa ya fada baki nazo dake nan ne don ki saka mi ido ga al,amarina.
Kin isheni kin dameni da fitina irin naki kada ki dauka don na saka maki ido kamar wani abu nake bukata a wurin ki.
Mace kike ni kuma mata ba ra,ayina bane na daukoki nan ne don rufi asirina in rufa maki ki rufa min asiri.
Idan kina da ra,yin yadda kikaga dama kofan hakan a bude yake maki zaki iya morewa rayuwan ki don yanzu nagane kin girma.
Irin naki ra,ayin ba zan iya daukan hakan bani don haka zan baki dama kiyi duk abinda zai kawo maki sauki da jin dadin rayuwan ki matakur ba zaki shigo min gida da wani ba.
Wa iyazu billahi na fada da karfi kafin inyi luuuu yaji na sake a jikin shi don tun lokacin daya fara magana idona ya fara rufewa a hankali.
Da karfi ta fara girgizani tare da kiran sunana a rude saidai ba alaman farkawa alokacin a rude ya nufi bandakin ya debo ruwa a wani dan roba yazo inda nake kwance saman gado kamar yadda ya barni ya dinga shafa min a fuska a hankali.
Wani iri ajiyan zuciya na sauke tare da bude idanuna a hankali ganin shi gaba na tsura mai ido kamar ban taba sanin shi ba a duniya.
A hankali na mayar da idona na rufe ya kira sunana a sanyayye da zainab har sau uku na sake bude idon da kyar na sauke a kanshi .
Ruwan ya sake shafa min a fuska har saman wuyana a hankali na sauke wani irin ajiyan zuciya na bude idon ina kallon shi.
Wani irin hawaye masu zafi suka dinga fito a idanuwana saboda zancen shi da suke min yawo a kwakwalwana a lokacin.
Mikewa nayi kokarin yi da sauri don gaba daya na tsorata dashi Allah ya ban sa,a na samu na jaye daga inda yake tsugunne .
Na fara ja da baya a hankali ina girgiza kai tare da fadin yaya dama kai ba musulmi bane ashe ?
Idon shi naga ya runtse don jin abindana fada yaya kai da bakin ka kake fadin hakan alhalin ina matarka na sunna.
Baka tuna ko yanzu ko anjima yau ko gobe Allah na iya karban rayuwan daya baka aro a kyauta ka koma gareshi.
Can kasan makoshin shi naji ya sake kiran suna da fadin ke baki san wasa bane a rayuwa ?
Na fadi hakane don ki saurara min ga abinda kike yawan fada min amma na fadi hakane bawai ina nufin hakan ba har zuciyana.
Dan Allah yaya na rokeka kayi hakkuri ka mayar dani gida wurin iyayyena tun kan rayuwana ya samu illa.
Nayi ma alkawari kamar yadda nasha fada ma ba zanyi wanan zancen da kowa ba a gidan mu.
Enough ya fada da karfi sai dan shiru ya kura min ido a hasale can yace ban aureki ko dauko ki nan dan mu rabu ba.
Na daukokine a bisa wani dalili nawa da ba lalaine ki sanshi ba a yanzu tunda naga kurciya na wahalal dake.
Abinda nake so dake idan zaki iya yanzu shine ki kawar da idanun ki ga al,amarina gaba daya.
Ki maida hankali ga karatun ki da kikeyi idan zaki iya kuma ki mun addu,a idan kin samu lokaci.
Idan kinyi hakan babu wanda zai ji mu dake har zuwa lokacin da komai zaizo ya daidaita zuwa lokacin kema kin idar da karatun ki .
Kinga kina da zabi idan zaki koma gida a lokacin sai ki koma amma yanzu ina rokon ki kwantar da hankalin ki ida nufi a tsanake.
Kaina kada a tsorace tare da hada hanayena wuri daya ina rokon shi da fadin na rokeka ko meye manufan ka yaya kada ka cuta ma rayuwan mu nida yar uwata.
Baiyi magana ba ya mike tsaye ya dan tsura min ido kafin ya sa kai ha fice daga dakin na dora hannuna a kai ina neman kuka a idona na rasa.
Jikina yai wani irin sanyi ga tsoro dake saukar min duk a lokaci guda haka na wuni sukku a gidan na kasa saka ko tufafi a jikina.
Jina shiru yasa fadila ta biyoni ta sameni dakin wani irin zazzabi ya rufeni a rude take tambaya abinda ke damuna sai kaduwa nake a cikin bargo.
Da sauri ta juya ta fita can sai gasu tare kasancewa ranan bai fita ko ina saida yamma yakan dan fita bai dadewa kuma yake dawowa gida.
Sai gasu tare dashi ya dan tataba min jiki yaji yadda jikin nawa ya gashe radau da zafi fita yayi sai gashi da magani ya hawo kan gado ya tayar dani ya bani maganin .
Banki sha ba don jina nake kamar zan mutu a lokacin ya dan dade rugume dani a jikin shi kafin barci ya dauke ni.
Nasan yayi hakan ne don ya kawar da hankalin fadila daga wani zargi don baiyi zaton tasan komai a game dashi ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWARAYUWA TANA FARUWA WUCE TAKE KAMAR BA AYI BA UBANGIJI ALLAH KA NUFE MU DA AIKATA ALHERI A KULLUN DA BIYAYYA TSAKKAKE A GAREKA ALLAHUMA AMIN, , , , ,

Sun gama duk wani shirin daya dace ga tafiyab su kamar yadda suka tsara abinsu gaba daya gidan zasu zo mai hutu wanan karon har yan matan mami da har yanzu suna lake da ita a gidan.
Ya jamal ne yace sai a rage yawa mami tace don me za a rage sun riga da sun sa rai ga tafiyan nan bayan hakama.
Shida ya dauki diyan talakawa zuwa can yana biya masu komai sai nasa da zamu dan je muyi sati biyu ko uku acan mu dawo zakace wai wani a rage yawa.
Barima in kira yar iskan yarinyar in sheda mata don kada muje tace zata yi muna halin su na yan talkawa da kuwa naci mutuncinta sosai wallahi.
A take ta fara kiran layina fitowa na daga class ke nan kira ya shigo min na dauko waya ganin mamine yasa na dauka da sauri na fara gaida ita.
Bata karba gaisuwa ba sai cewa da tayi ke ki bude kunnuwa ki kiji da kyau duk sanda na shirya zaki iya ganin mu gidan ku.
Zanzo inga irin iskancin da kikeyi don samun wuri a gidan shi don na kula yanzu gaba daya kuna kokarin jaye hankalin shi gareni da yan uwan shi.
Sai ke da iyayyeb ki kawai ya sani a yanzu zan zo zan sa ido na gani idan har hakan gaskiyane ba zan daga maki kafa ba wanan karon.
Zaki san ni maryam ba sa,an yin ki bane har uwayen ki dake kauye suna maki tafi har idon jafar ya rufe a kanki.
Daga inda nake ina sauraren ta na runtse idanuwana don iyayyena data sako a cikin zancen naji wasu irin hawaye sunzo min suna kokarin zuba a idona.
Da kyar na iya budan bakina na furta mami Allah ya baki Allah ya kawo ku lafiya naji ta kashe wayan.
Nabi wayan da kallo na girgiza kai tare da barin wurin na cin ma Maya a inda muke zama na zauna.
Kallon yanayi tayi taga ya sauya gaba daya take tambayana abinda ya sameni zan iya cewa ranan ne karo na farko dana fara ba Maya din labarina a takaice.
Ranan haka na dawo gida da bacin rai a tare dani ban fadawa kowa wanan zance ba haka na barshi a zuciyana ina dakon wahala.
Ba abinda yafi batawa mami rai kamar yadda akace karatuna har na kusa gamawa a yanzu don dan watanni ne ya rage muna mu karasa don haka take jin wani irin tsana tun lokacin da jamal ya fada mata hakan.
Ga karatun su baiwani ci gaba ba wanan lokacin dani a can na kusa kammala karatuna zuwa wanan lokacin na zama wata irin classic queen don daula da nake samu zakace yar wani basarake ne nidin.
Don gaba daya na tattara damuwana da tsoro na aje a wuri daya na fuskanci karatuna zuwa wanan lokacin .
Addu,a kan kullun muna kan yinsa ba fashi halimatu ma yanzu girma ya soma zo mata don haka na kara taka tsantsan tare da sa ido ga duk wani al,amarin ta.
Banda kawa kaf kasan bayan Maya duk da ba addinin mu daya ba hakan bai hanamu kawance ba don babu wanda ke tabo addinin wani a tsakanin mu.
Iya ka dai abu gudane idan lokacin ibada yayi zata rakani inyi ibadana ko ta tuna min is time for pray.
Inda nima hakan zan tuna mata da nata lokacin ibadan su idan ta shagala da karatu inda na kulla da yaya jafar yanzu.
Kawar da kai da nake ga al,amarin shi yanzu mun koma kamar wa da kanwar shi ga yawan alheri da kyautatawan da yake muna yanzu.
Don mota ko yaushe a cikin canza min shi yake da yayi yan watanni a gurina zanga ya sawo min wata an dauke wancan na farko.
Sutura ba,a maganan shi a wurin mu har fadila don yadda yake dan gayu dan kwalisa haka yayi kokari ya mayar damu muma da sutura tun bayan iya sakawa har yazu na iya irin kwaliyan su saidai ban yarda na kaucewa addinina ba da hakan.
Mun samu hutu muna zaune gida don bikin kirismeti da zasu yi a kasan ko mu da bamu addinin su an gyara muna gida yadda ya dace.
Amma saidai duk wanan abin baisa na daina jin tsanar shi da kyamarshi a raina ba sai dai ina kokarin ganin na nisance shi ga duk wani abinda zai kawo muna matsala ga hakan.
Falo muke zaune dukkanmu mu uku kallo mukeyi fadila da halimatu da yanzu bakina ya saba da sadiya kamar yadda kowa ke kiranta a gidan dole nima na kama kiranta da sadiya yanzu.
Sai fira suke tsakanin su da fadila yayin da hankalina ke ga karatun da nakeyi ga drinks da dan tsunken da nake zuka sai snack a gabana da nake dan hadawa ina ci.
Kofan aka turo alaman mutum ya shigo gidan a lokacin hakan baisa na dago kaina daga karatun ba sai da naji sallama muryoyin da ba zan taba mantawa dasu ba a rayuwana.
Muryan jalal da jamal ne don sune farkon shigowa gidan da sauri na dago kaina don jin muryan su da nayi mukai arba dasu na mike tsaye.
Ya jamal kune tafe na fada cikin farin cikin ganin su na nufi inda suken a lokacin aka turo kofan sai ga mutane na shigowa.
Tsaye nayi ina mamakin hakan a raina nace yanzu yaya yasan da zuwan su shine bai sanar min ba in san da hakan in shirya.
Mamice da hjy kusan na karshen shigowa gidan ganin hjy na manta da kowa don suna tsaye soror sai kallon mamaki suke min gaba dayan su a lokacin.
Sannun ku da zuwa nayi masu ina kokarin amsan jakkar hannun mami data rataya a kafadan ta kamar yadda ta nasaba amsa idan tadawo lokacin da nake gidan ta.
Fuska a daure tana yatsune fuska tace No ki barshi kawai sai banji dadin hakan da tayi min ba a gaban kowa don yan matan suna tsaye sun daskare a wuri daya sai kallon mamaki suke min.
Fadila har ta mike ta shiga kitchen ko ta hado masu abin tarbon baki ta kawo ta zube a gaban su bissimillah nayi masu wasu suka fara dauka .
Wasu kuma mamaki ya hanasu ai watar da komai suna zaune kawai sun zuba min ido tare da bin ko ina na gidan da kallo.
Na gaida mami ina masu anzo lafiya ta katseni da fadin yar mulki ashe kina gaida mutane ke nan ?
Dama tsiyan tallaka ya samu wuri ke nan sai yayi kokarin mallake komai ya dauka komai a banza akayi shi.
Haba iyami daga zuwa da wanan zaki tarbi yarki dashi ina shi arziki Allah kewa bawa shi.
Na dauka ai wanan zancen ya rigada ya wuce tun tuni a wurun ki don da rabo ya ratsa ai yanzu sun kai ga diya biyu a gidan nan rabon dai ne dake nesa ya kawo hakan.
Hjy da wanan ta daukeni uwa ai da ba hakan ba banga ranan da zan dauki zainab a matsayin sakuwana ba a zuciyata.
Maimakon inyi fushi irin da ko hawaye sai murmushi da na sake a fuskana kadan mami kiyi hakkuri ko na kira ba s dagawa yasa na daina kira yanzu.
Kowa shiru yayi yadda nake magana babu shayin komai ga hausan nawa zakace ma yare nakeyi a lokacin.
Komawa nayi saman kujera na zauna tare da harde kafafuna daya saman daya wanda bansan nayi hakan bani don sabo a yanzu.
Na dago kai a hankali na kalli inda su Aisha suke zaune dasu Rufaida nace kunzo lafiya ya hanya ?
Firgigit sukayi saida Aisha ta mike take fadin lafiya nuna muna dakin da zamu sauka don Allah ta fada tana nuna gajiya a tare da ita.
Sadiya take her to my room na fada sadiya ta mike da sauri tana fadin muje ita da kanta taja logued din ta zuwa dakin nawa.
Na juya wurin fadila nace a gyarawa mami dayan dakin part din can sai dayan na sauran sisters hjy zata zauna a dakin ta.
Nuriya kan ido ta zuba min mamaki ya hanata sauke numfashi ga yaran ta da alaman basu ganeni ba ma su.
Haka na fada ma Fadilan komai yadda zata kai kowa masaukin shi har nuriya da yaranta da mijinta.
Wai ina shi jafar din yaje ya mamud ke tambaya mami ta amsa da fadin nima shi nake son in tambaya ai yanzu.
Yana ciki na bata amsa kai tsaye shine baki fada mai zuwan mu ba muka kallo juna da fadila a daidai lokacin da mami din ta mike tana fada.
Wai zan rabata da danta da yan uwan shi dama burina ke nan inga kowa bai mameshi ba nasa ni dai har yanzu murmushi kawai nakewa fadan nata .
Duk da raina yana baci a yanzu yadda take kokarin tozartani a gaban yayan nata dake zaune.
Da ace mami tasan nima maraba nake nema da dan nata da bata tsaya bata baki ba haka don ni a yanzu godiya zan mata idan har ta rabani da danta.
Haba mami ya mamud ya fada baki sani ba ko tana da dalilin yin hakan amma yaya zainab zata hanaki ganin danki kuma ?
Kai mamud wai meyasa baku son ana zancen yarinyar nan ne haka wai ?
Yanzu har sai mun tabayeshi zata fada mai munzo koda a ce bamu bane muka zo gidannan
Ina part din nasa yake ta tambaya mami yana ciki baya son ana shiga mai part na fada maki ya jamal ke magana tare da nuna mata saman inda dakin shi yake.
A fusace mami ta nufi can din tayi sa,a kofan na bude ta tura ta shiga tana fada yadda ta samesu da yadda ya ganta a bazata ne yasa kowan su shiga rudani.
Shi dama a irin wanan lokacin da ake zaman gida yake samun lokacin sheke ayan shi yadda ranshi ke so a gidan.
Da baya baya mami ta fito daga falon a daidai lokacin na iso wurin don gudun abinda zai biyo baya a lokacin.
Ji tayi na rike ta ta baya nayi part dina da ita ba tare da kowa yasan meya ke faruwa a lokacin ba mami na biye dani har zuwa bakin gado na zaunar da ita kamar mutum mutumi.
A daidai lokacin Aisha ta fito daga wanka yanayin data ganmu ciki yasa taja ta tsaya daga kofan bayin tana kallon mu da mamaki.
Don yanzu ta barmu a falon mu fada gamu kuma tare a cikin wani yanayi ina ganin ta nace mami don Allah ki natsu kada hankalin saura ya tashi zan mamaki bayani daga baya .
Na mike tare da fita daga dakin da sauri na nufi part din nasa ina shiga yana zaune daga shi tawul a jikin shi daure a kugun shi.
Jin shigowana yasa ya dago kai gareni yana kallona nima kallon shi nakeyi tare da fadin kasan zasu yau yaya ka tsaya aikata wana fasadin ?
Kamar ya nasan zasu zo bake kika gaiyato su suzo dama ba ni na fada da mamaki a daidai lokacin da dayan katon gardin ya fito daga dakin da sauri yana gyara aninin rigan jikin shi.
Yana son fita daga dakin da hannu na nuna mashi ya koma ciki ya tsaya yana kallona da mamaki na juyo wurin ya jafar din ina fadin kowa na gidan nan yanzu don har ya mamud da Family shi suna tare.
What , ya fada da dan karfi nace sosai kuwa zan fita zan fada masu baka gida don mami ma yanzu haka tana dakina a cikin wani hali.
Shiru yayi har na gama bayani da zanyi na juya don barin wurin naji ya ambaci sunana a sanyaye da zainab .
Jin hakan yasa na tsaya cak may yasa kika bari mami tashigo part din nan ya tambaya yana dago kai.
Banda hujjan da zan dakatar da mami zuwa part din danta idan baka manta ba kuma kayi mi warning na daina shigo ma part din ka matukar bakai ka nemeni ba.
Don haka babu yadda zanyi in shigo ma don kai da kanka kayi warning dina akan ha, , , , ,
Koma su waye kice dasu gani saukowa kada kice masu komai tunda mami ta riga data ganni ko yanzun zanyi wanka in sauko.
Ban tsaya jiran abinda zai karasa fadi ba nasa kai na fice a dakin cike da takaicin shi a raina lokaci guda.
Dakina na koma don kowa na masaukin da aka bashi suna sauke gajiya ina shiga dakin na samu Aisha tsaye a kan mami data kasa magana tun fitana dakin.
Tsugunne nakai gefen gadon tare da dukar da kaina hawaye na zuba min a idanuwa tana kwance bata ko motsa a yadda take ba.
Jin sheshekan kukan nawa yayi yawa Aisha da take a rude take fadin mami wani abu ya farune da na shigo daki halan ?
Shiru ba amsa daga gurina har mami din da idonta kawai ta tsurawa kofan shigowa bata ko kfttasu don gaba daya ta fice cikin hayacin ta a lokacin.
Aisha dan fita ki bamu daki mami ta fada ba tare data iya dago kai ga yar nata ba Aishan ta fita tana dan waige da sauri.
Sai bayan fitan Aishan daga dakin muryan mami yazo min a kunnena tace zainab na amsa da na,am mami.
Wani irin rayuwa kukeyi gidan nan da mijin ki ne don yanzu na sameshi dana shiga a cikin wani hali.
Alama ya nuna kin san komai a kan hakan don yadda kika taroni daga baya zuwa dakin nan ya nuna min kin san abinda idona ya ganan min ke nan ?
Kai na dago cikin hawaye na dan kalleta sai kuka ya rinjayeni ganin hakan itama mami ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi.
Jin ana nocking din kofan yasa nayi saurin share hawayena na mike zuwa budan kofan hjy ce tare da ya mamud .
May ke faruwane da zuwan mu mami ya mamud ya fada a lokacin mami ta kara karfin kukan da takeyi din gwanin ban tausayi.
Kai kai haba mami wanan ai saiki dagawa mutane hankali mu dauka wani abu mumunane ya same ki daga zuwan mu ko kin samu wani sakone mara dadi daga gida ?
Haba dai wani sako iyami zata samu har ya daga mata hankali haka tana wanan irin kukan haka yanzu ?
Hajiya take fadin hakan tare da juyowa inda nake gurfane nima kukan nakeyi sosai a lokacin .
Wanan abin naku akwai daure kai wallahi ko dai wani abune ya samu shi jafarin bamu sani ba sai yanzu da zuwan mu zamu samu labari ?
Cikin karfin hali nace da ita lafiya yake hjy dama dai magana ce muka danyi da mami ya saka ta kuka don Allah kuce ta yafe muna zan bar yaya jafar din idan haka shine zai sa mu samu jituwa da mami dagani har yayan.
Jin abindana fada mami ta rage kukan da takeyi tana fadin zainab ni dama baki min komai ba zainab don dai rashin biyayyan da kukaki min ne ai tun farko nake wanan haukan daku.
Mami kiyi hakkuri ki yafe min ki roka min ya jafar ya sakeni in koma gida zaifi muna sauki.
Shout up zainab a kul na kara jin wanan zancen a bakin ki zan saba maki rai a wurin nan abinda ya riga ya wuce ya wuce ko ya mamud ya fada
Yau zainab da bakin ki zainab kike fadin hakan duk hakkurin da kikayi da wanan auren ai yanzu kun zama daya kike furta ya sakeki ?
Zata ce hakan dole hjy don jafar mutumin banza ne a yanzu na fahinci dalilin shi na zaben zainab dayayi a matsayin matan auren shi.
Wanda dacan hankalina bai kawo min haka ba sai yanzu dana fahinci waye jafar din don rayuwan jafar baida kyau hjy.
Jafar ya fita daban a cikin yayana da al,umman musulmai baki daya hjy zan iya fadin yau nayi dana sanin haihuwan jafar da cikina wallahi.
Wa,iyazu billahi mami don Allah ki bar fadin haka ko mai yai maki haka mai zafi kiyi hakkuri ki tausa zuciyar ki akan shi.
Idan kaga na yafewa jafar har mun shirya dashi ya daina wanan halin banzan da yakeyi a rayuwan shine zamuyi zaman da uwar shi.
Don haka yau ba sai gobe ba gaba dayan ku ku shirya mu bar masa gidan shi don banga amfanin zaman mu a gidan mai fasadi irin jafar ba.
Wa iyazu billahi iyami dan naki kike aiban tawa haka da bakin ki har kina kiranshi da mai fasadi wani irin aikin asha yake aikatawa mai muni haka.
Please mami don't tell her abinda idon ki ya gane maki don hjy bata da karfin zuciyar daukan wanan maganan a yanzu na fada da turanci.
Gaskiyane ya mamud ya fada shima a cikin harshen turanci sai hjy tace nasan dai ba zai wuce akidan nasara ba da yake yawan dauka kuma ko yaushe mukai waya ina masa huduba da hakan.
Jafar din ne ya turo kofa ya shigo da alama ya danji wani abu daga cikin zancen namu a dakin don kofan a rufe yake lokacin.
Yayi wankan shi fes ba zaka taba cewa shine ba mai mumunan halaiyan nan idon shi akan mahaifiyar su dake darzan kuka saman gadona.
Kafin ya mayar da kallon shi wurin hjy dake tsaye a kan yarta ni kuma ina rusunne a gefe ina hawaye.
Hannun ya mikawa ya jafar yana fadin so you surprise me zuwa haka babu sanarwa duka family baki daya.
Cikin dan basarwa ya mamud di yace dokan mami ne hakan ta hana kowa ya sanar daku zuwan mu saidai ku ganmu kwatsam.
Nayi dana sanin wanan zuwan yafi dubu dana san abinda kake aikatawa a kasan nan da ban taba taka kafana zuwa gidan ka jafar .
Dan murmushi yayi irin na masu karfin hali tare da fadinn haba mami me yai zafi haka kuma da bazaki zo gidana ba .
Ai ko baki zo don ni ba zakizo don yar ki nan ki ganta kiga inda take zaune tunda kin huce damu.
Shidai na gani sai dai kuma kai ja,iri da zuwan uwar taka ka bata mata rai haka me kayi haka da zafi har ka fice mata a raine lokaci guda ?
Dan murmushi kawai ya sake tare da kallon mamud yana fadin ina madam da yaran su ke ko har dasune tafiyan .
Kowa na nan ya mamud ya fada tare da fadin muje daga waje don mami ta huta ya soma tafiya yana fadin hakan.
Shi kuma ya mara mai baya muryan mamine ya dakatar dasu din da wani irin tsawa take fadin mamud na fada ma kafita ka samo inda zamu sauka gobe zamu bar kasan nan da yardan Allah.
Lokaci daya suka juyo gareta da mamaki suna kallon ta hjy ce ta katse su da fadin kekan tir iyami da wanan halin naki na rikau.
Don kawai danki ya bata maki rai zaki fadi haka gareshi idan kinyi hakan ma kanki kika bawa kunya ai.
Kada ki manta wanan tafiyan ba iya diyan ki kawai kikayi shi ba don haka ki shiga hankalin ki tun kan duniya ta saki a baki.
Ki fada muna laifin yaron nan kuki fitowa fili ku fada daga ke har matar tasa sai kwanaye kwanayen da kuke muna a yanzu.
Wanan maganan da hjy tayi yasa jikin mami sanyi amma kuma sai ta sake wani sabon kuka mai tayar da hankalin mutum .
Ya mamud din ne yajashi suka fice daga dakin suka sauko kasa nan ma babu kowa duk suna dakunan da aka saukesu suna mayar da fadi a game dani da kuma irin gidan da muke zaune.
Inda Aisha ke basu labarin ai basu ga kallo ba sai idan sun shiga dakina da nake zaune a ciki a nan zasu sha mamaki wai duk zee ce da wanan daulan haka.
Har suna hada baki wurin fadin ki bari don Allah nan ma din kadan ke nan ashe muka gani bisa ga nata din

ZAINAB IDRIS MAKAWAYA HAIYYU YA KAIYUMU BIN RAHAMATIKA YA ASTAGIS UBANGIJI KAI HASKE GA KABARIN DUK KAN MUSULMIN DA SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA ALBARKA KALMAN LA,ILLAH HA,ILALLA MOHAMMADAN RASULILLAH DA SUKA TABA FADA A RAYUWAN SU ALLAHUMA AMIN , , , , ,


Gidan yayi shiru lokaci guda baka jin motsin kowa a gidan sai na,orurin dake aiki kawai na gidan a lokacin.
Mami dake kwance ta mike a hankali zaune taji zaman bai mata dadi don zuciyar ta daya cushe wuri daya a lokacin.
Haka yasa ta saukowa daga saman gadon a hankali ta gyara hulan dake saye a kanta ta nufi kofan fita daga dakin.
Ba kowa falon don haka ta nufi wurin shan iska inda zaka iya tsayawa kaga duk wani abinda wajen gidan ke ciki daga inda kake tsaye.
Jamal ta hango tsaye shi kadai a cikin duhun yana tsaye ya harde hannayen shi guri daya yayin da kafafuwan shi ma suke a harde mashi.
Hankalin shi gaba daya ya mayar dashi gaban gidan jikin shi na jingine da dan bangon wurin yana tunane ga iskan sayi yana huro mashi a jiki.
Jin motsin mutum da yayi lokacin yasa shi dan juyowa inda yake jin tafiyan mutum din mami ya gani don ya sheda ta duk da akwai duhu a lokacin.
Hakan bai hanashi sheda mahaifiyar tasu ba da take tafe itama mami din ta sheda ko waye a wurin tsaye duk da duhun dake akwai din.
Mami baki barci ba ya fada cikin mamaki da tare da juyowa inda take yana fuskantar ta.
Jamal ban dauka zan kara barci da idanuna ba kuma a wanan halin da dan uwan ka ya jefa kanshi a ciki na rayuwa irin wanan.
Mami yanzu kin gani ke nan kema abinda na gani gareshi nake wanan fushin dashi .
Jamal na gani Allah ya nuna min da idona yau naga mugun gani da idanuwa ga dan dana haifa da cikina .
Sai wani irin kuka yazo mata lokaci guda jamal din yace mami ba kuka zakiyi ba don yanzu yaya addua da taimako yake so a garemu don yayi nisa a cikin wanan harkan ko yanzu.
Jamal dole inyi kuka yau jafar ne a cikin wanan halin haka jamal ina zan saka rayuwana dan dana haifa aka bar min amana shine ya zama haka a rayuwa.
Wanan kaddaran bawane, mami duk mai rai baya wuce kaddaran shi a rayu don haka zama ya kamata ayi asan hanyar da za a fitowa wanan maganan tunkan zancen nan yayi bosting kowa yasan hakan.
Sani kuma na yaushe jamal tunda matar tasa ta sani kila kuma yan uwanta nan da suke zaune suma duk sin sanda hakan ko ?
Kai haba mami zainab tana da matukar wayo bazata bar kowa yasan wanan zancen ba rufa min baki wani wayau can.
Zata dai iya yin hakan don ta kare kanta itama tunda take zaune dashi ai kila itama din yar hannun ce ke nan ai yanzu.
Ina mami baki san waye yarinyar nan zainab ba ashe har yanzu don koni danagani da idona kuma a kusan tare zance munga wanan abin amma bata yarda nasan da hakan ba .
Saida na fito mata da zancen da kaina ta yarda tayi min bayanin komai don haka nake ganin ko yanzu ba zata taba barin kowa yaji hakan ba a bangaren ta.
Jamal ke nan duk da kai yaron har yanzu baka tunane ko ita yanzu ya bata ta yasa bata yarda ta tona mashi asiri.
Shiru Jamal din yayi yana tunane kala kala a zuciyar shi kafin yaji muryan mami yaci gaba da fadin nima haka wanan tunanen yazo min .
Don yadda naga tana kokarin rufa mai asiri dole akwai wani abinda itama take boyewa nata don ko hjy dake dakin muna magana da mamud cewa tayi kada a bati taji komai don tsufa.
Sai wanan karewan da takeyi din ya tsaya min a zuciyana na fara zargin itama ta dade da lalacewa ta wanan fannin yanzu.
No mami kada kiyi zargin hakan a dai bincika a ji ai zata fadi gaskiya koma meye ba zata boye maku gaskiyan ba nake tsamani.
Kana wasa da wanan yarinyar jamal ya katse da fadin haba mami yanzu kuma meya saura na zargin zainab gareki.
Ga gaskiya tayi halinta baro baro za a tsaya zagin yar mutane damafa ya J yayi amfani da yarinyar nan zainab ne ya aureta bada yardan ta ba yabi ta wajen iyayyenta ya aureta.
Don kawai ya kawar da idon mutane a kasan ace yana da aure ai ba haka kawai yake zaune ba.
Don kada mutane damu a gano abunda yake aikatawa din wanan hikima yayi yaki yarda da auren hadin da kika so yi masa a baya.
Don yasan idan daga bangareki ne yarinyar ba zata taba yarda ta boye shi ba yadda zainab din ta boye shi na shekaru.
Idan ma cutane mami yanzun dai kingani yar mutane da aka baki amana aka cuta don mutuncin ki iyayyen ta suka gani tun farko suka yarda suka aura mai ita ba tare da wani kwankwanto ba can.
Kai jamal ni kake kokarin nuwa yaran nan kome ina dukkan ku ta dalilina kuka san yarinyar nan dai ?.
Koma meye zan zauna da ita ai in fahinci komai wallahi idan yarinyar nan tana da hannu cikin wanan matsalan gaba daya sai na sabawa rayuwan su.
Don me zai shiga daki haka da wanan katon suna wanan wasan banzan idan ba wani abu suke aikatawa ba hakan ?
Ok mami hakan yana da kyau ai ki bincika kiji komai don zaki gane mai gaskiya a cikin su yanzu ai idan kin bincika din.
Sai dai kuma mami ki sani danki fa abinda kika gani shine gaskiya abinda danki ke aikatawa a kasan nan don shi sam bai damu da diya mace ba a rayuwan shi.
Ga abu kin gani da idon ki mami zaki tsaya kina wani kwanaye kwanaye akan yar mutane ?
Yanzu dai ai abin cikin duhu ya fita fili Allah ya nuna maki wanan sirin da danki ke boyewa sheka da shekaru yanayi.
Ji kawai yayi mami ta fadi kasa a wurin somamiya da sauri ya nufi kanta yana kiran sunan ta cikin tashin hankali.
Gashi su biyu ne kawai a falon dabara ya fado mai na ya yayyafa mata ruwa ya nufi kitchen da sauri ya dauko goran ruwa mai sanyi ya dawo dashi inda take.
Ya yayyafa mata sai gata ta farfado lokaci guda sannu yake faman yi mata sai ta koma luuuu ta kara somewa kuma.
A daidai lokacin fadila ta fito don motsin da take ji tun dazun a gidan idon ta yai arba da mami kwance kasa somamiya .
Ga Jamal a kanta sai faman gurgizata yakeyi ihu ta yanka don tsoro lokaci guda muke bude kofofin gidan muna fitowa daga dakun nan mu.
Kai ranan munga tashin hankali asibiti suka nufa da ita kai tsaye dashi da yaya mamud sai jamal da jalal da suka bisu.
An barmu gida hankali tashe don bamu san halin da mami ke ciki ba a can don duk sun bar wayoyin su a gida tunda ba fitowan girma da arziki sukayi ba daga dakunan su.
Tambayan nasha shi wurin Aisha amsa daya nake bata shine nima ban san dalilin hakan ba nadai ga mami a wanan halin tun bayan shigan ta dakin yaya .
San nan na samu sa,ida a wirin su da tambayan da suke min hjy kan iya damuwa ta damu sosai da yar ta mami a halin data shiga.
Basu dawo gidan ba sai washe gari suke fadin anba mami gadome asibitin da aka kaita tana can kwamce tare da jalal da jamal.
Duk da hankali ya dan kwanta tunda sunce ba wani case bane sosai wai gajiya ne yai mata yawa na hanya.
Nikan a raina nasan ko meye umul,aba,isin hakan da takeyi naja bakina nayi shiru don kada wani ya farga ya gane nasan wani abu.
Gani da test a ranan Maya tana ta kirana dole haka na sance jiki na fice zuwa rubuta test din fadila kawai na fadawa inda zan tafi a lokacin.
Allah ya taimakeni ba a fara ba saura minti biyu za a fara na shigo ban dade ba aka fara test din muna fitowa nayi sallama da maya na tafi.
Na dawo na samu sun tafi asibitin duban mami sai fadilace kadai a gida sadiya bata riga data dawo gida ba daga makaranta don ni nayi saurin dawowa ranan.
Da kaina na shiga kitchen muka hada masu abinci tare da mai aikin daya data saura a gidan don sauran sun dauki hutun sun tafi gida.
Fadilace ke fadin rashin kyautawana da ban je asibiti duba mami ba nace da zuwana da rashin zuwa daya yake a wurina.
Don yanzu jira nake kawai ta ba danta umurnin ya sallameni mu koma gida don shi kawai nake jira yanzu.
Da sauri ta kalloni da mamaki tana fadin kada ki fadi haka zainab don nasan boss bazai taba sakin ki ba ai.
Saboda wasu dalilai nasa kina da rana da amfani a wurin shi sosai wanda ba kowane yasan da hakan ba.
Saki ya zama dole yanzu gareshi don lokaci yayi da zaiyi hakan na gaji da ganin laifina da mahaifiyar shi ke min ko yaushe.
Gara na bar mata danta a zauna lafiya ta aura mashi yar masu arzikin da take so ya zauna da ita.
Ina shima yasani ai zainab babu macen da zatayi wanan hakkurin da kikeyi a gidan nan yanzu.
Don haka ki daina ma wanan zancen zainab don haka ki shirya muje anjima mu dibo ta ko ran mijin naki bazaiyi dadi ba idan bakije ba ai.
Amma anty don ta katseni da fadin please zainab kada kice ba zaki ba din ko rashin zuwan ki a yanzu ai tasan da wani abu a kasa don abin zai iya damun kowa nan gaba.
Nace shike nan anty zan tafi da yamma idan Allah ya kaimu sai ki shirya idan sadiya ta dawo mu tafi dukkan mu.
Sun dawo gidan saidai ba wani damuwa a tare dasu don jikin mami din da sauki sosai sun dai kwantar da itace don ta samu hutu da natsu a can.
A falo suka zube wasu kuma suka shiga yin sallah masu rikon addini ke nan daga cikin su irin hjy tsohuwa da anty Na,ima sai Aisha data shiga itama don laluran ta ba laifi ta tsaya tayi sallah a dakin.
Don na shiga na sameta tana sallah amma su Nuriya dasu Rufaida suna falo ana hiran garin wanda a cikin hiran nasu suke sako habaici a ciki.
Dawowan Sadiya ba ta dade da shigowa ba a lokacin kowa na falo zaune har mazan suna cin abinci duk suka bita da kowa da abinda ke zuciyar shi .
Lokaci ne na mike zuwa daki na samu Aisha kwance tana waya nan daki na shiga ban tsaya ta kanta ba na fara watsa ruwa a jikina.
Nafito nake shiryawa don fitan da zamuyi zuwa duba hjy muryan Aisha ya daki dodon kunnena da farko tsuki mai karfi naji taja.
Hakan baisa na waigo inda take ba don zatona da wanda take wayan take tsukin sai naji muryan ta na fadin tsiyan banza ashe da gaske ake fadin dan talakka bai iya samun wuri ba dama.
To bari kiji wallahi zainab idan wani abu ya samu mahaifiyar mu wallahi ni da kaina zan dauki mataki akanki koda kuwa ya j zai halakani nima.
Na juyo ina fadin au dani kike zance ashe amma dai kafin ki halakani din zai fi kyau shi J din ki fara halakashi don shi musabbabin komai da mahaifiyar ku ke ciki.
Ni meye nawa a ciki don bani nakar zomo ba rataya akabani don haka kowa ya sakar mun mara nayi fitsari .
In laifine jeki gun dan uwanki ki tsure shi donni ba haifana kikayi ba da zaki sakani gaba zaki fada min rubish.
Tunda na juyo na fara magana Aisha ta tsura min ido tana kallona da mamaki karara a fuskanta har nakai karshen magana na juya ina daukan kaya da zan saka.
Can naji tace min lalai Aisha wuyan ki nan ya isa yanka zainab ni kike fadawa magana haka kai tsaye ?
Kamar ba zan bata amsa ba saida na dauko kayan na aje na dago ina fadin nafada maki indon wanan auren kaddaran na dan uwan kine harke kuke son takura min a rayuwa don Allah yanzu ba sai anjima ba kisa ya sakeni na koma gun iyayyena yafi min zama da wanan kaddaran.
Fadila ce ta turo kofan da sallama tana fadin madam we are ready ke muke jira ki taimaka ki fito min da takalma da jakka kayan nan.
Tace yes ma ta nufi inda nake aje su tana daukowa tsuki Aisha taja tana sauka a gadon ta nufi hanyar fita daga dakin.
Yadda ta fita yasa fadila gane akwai wani abu atsakanin mu lokacin ta kalloni bayan fitan Aisha din tana fadin meya faru kuma ?
Ba komai na bata amsa tare da rolling din dan kwali a kaina ina fadin muje ko tace ok muka fito na rufo kofa da key.
Muna saukowa duk idanuwan su a kaina don shigan da nayi ya girgizasu a wurin da alama kuma akwai maganan da sukayi akaina lokacin.
Zamu fita nace dasu don su basu gajiya da kallona ni har mamaki abin ke bani yasa ban nuna masu na tsargu da irin kallon da sukan min ba a yanzu.
Bin bayan mu Rufaida tayi da leke har lokacin dana bude mota muka shiga na fice gidan ta juyo tana fadin what ?
Wai kunsan kuwa yarinyar nan wani kafirin mota take ja haka da kanta a garin nan ya mamud ne daga inda yake zaune ya dago yana fadin ina ruwan ki ko jirgi a yanzu sai zainab taja wanan ba abin mamaki bane ai.
A mota nake ba fadila rabarin yadda mukayi da Aisha da amsan dana bata ni kuma .
Fadila tace kin min daidai wallahi don raga masu baida wani amfani ko kadan gara su san yanzu ke din ba sa,an su bace ai.
Mun isa asibitin ban wani sha wuyaba muka gane inda mami take muka shiga kamar yadda ka,idan shigan su yake a kasan.
Don sukan ba,a barsu sun shiga ba don sunyi yawa kuma ba time din duba mara lafiya bane lokacin.
Muna shiga muka samu jamal da jafar a zaune shiru a dakin mukai sallama bai dago kai ya kallemu ba yana dakilan wayan shi.
Jamal ne yayi muna sannu da zuwa muka kara gaidasu tare da yiwa mami sannu da jiki ta dan dago tana amsawa.
Abinci da muka zo dashine muka aje a gabanta nace mami ga abinci munzo maki dashi.
Godiya tayi muna sai lokacin jafar yayi magana yake fadin fadila ki taimaka mata ta tashi zuwa bandaki ta dan gyara.
No ta bari zan iya mami ta fada a karo nabiyu da tayi magana ke nan tun zuwan mu dakin da take kwance din.
Da kyat ta yun kura ta mike ta shiga bayin haka yasa dakin shiru babu mai magana a cikin mu har ta fito ta hau gadon da niyar kwantawa.
Abincin nake kokarin zubawa muryan mami ya dakatar dani tana fadin dakata zainab kada ki zuba don bazanci abincin gidan ku ba.
Wani irin kallon mamaki kowa na dakin yai mata lokaci guda sai fadilace mai karfin halin fadin mami kiyi hakkuri ki danci wani abu don Allah.
Jamal ta kalla inda yake tana fadin akwai kudin kasan nan a hannun ka ka sayo min abinda zanci a waje.
A sanyayye dan nata ya amsa mata yana fadin akwai mami amma da kici wanan din don gurin sayar da abincin yana da nisa sosai.
Jeka ka sayo min zan jiraka hakanan har ka dawo ta fada tana kawar da fuskanta daga kallon mu cikin dakewa.
Jamal na fita jafar din ya mike tare da fadin mami zan koma wurin aiki sai anjima zan dawo insha Allahu.
Ko motsi batayi ba balle yasa ran amsawa ga sallaman da yayi mata haka yasa kai ya fice daga dakin duk wanda ke wajen saida yaji wani abu a ransa lokacin.
Munyi shiru dukkan mu mami ke fadin kada ki damu zainab badon ke nayi haka ba wanan karon donshi mara hankali da tunane na aikata hakan don haka kada ki dauki wanan don ke nayi hakan dama.
Babu komai mami Allah ya shirya tsakanin ku na fada ina mikewa tsaye da sauri suka mike suma nace su jirani a waje ina zuwa.
Suna fita fadila ta rufo kofan hakan ya bani daman karasawa bakin gadon da mami din take kwance.
Ka nakai gurfane ina fadin mami kiyi hakkuri ki gafarce ni ban auri jafar don wani manufa da kuke fadi ba.
Asalima shi jafar di ne ya turasasa iyayyena ya aureni da wani manufa da yake dashi a zuciyar shi don cinma burin shi.
Kimarki da martaban ki hade irin kaunar da kika nuna min yasa iyayyena basu tsaya dogon bincike ba suka bayar dani ga danki.
Kuka ne yazo min na dakata na dan lokaci saida nayi mai isata naci gaba da fadin Alhamdullahi mami tunda yau kin gane waye jafar da abinda yake aikatawa na fasadi a doron kasa.
Don haka nake rokon ki a matsayin ki na uwa a gare mu mami ki tursasa jafar ya sakeni in koma wurin iyayyena tunda Allah bai nufa burin shi ya cika ba a kaina.


ZAINAB IDRIS MAKAWAALHAMDULLILAHI RABIL ALAMIN AR RAHAMANIN RAHIM, , , ,

YAR UWA WANAN NOVEL NA KUDINE DON GIRMAN ALLAH IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA DON KADA KI SHIGA HAKKIN WATA ALLAH YA BAMU CIKAWA DA IMANI AMIN, , , , , ,

Ido kawai mami ta zuba min har na gama na barke da kuka lokaci guda mai tsuma zuciya mami bata juyo ba.
Sai da ya jamal ya turo kofan ya shigo dakin da sauri ya karaso yana fadin subbahanallahi lfy haka zainab ?
Mami me ya farune take wanan kukan haka don Allah ko wani abin kuma ya jafar yai mata kafin ya fita.
Gata nan ai katambayeta kaji abinda takewa kukan don ni ban fahinci inda ta dosa ba don ni yanzu bashi ke gaba .
Zaune yakai yana fadin zainab me ya farune haka kike kuka don Allah ?
Ya jamal a taimakeni ya jafar ya sakeni in koma gidan mu don Allah na gaji da wanan auren wasan da mukeyi.
Kiyi hakkuri mami taji sauki za a kai ga wanan don kowa yasan yana cutawa rayuwan ki ai yanzu zee.
Sai dai ke din wani baiwane a cikin ahalin don zancen rabuwa da yaya yanzu bai taso a gareki ba zainab.
Kukane ya kubce min yasa nabar dakin da sauri don jin abinda jamal din ya fada game dani don ni yanzu banda wani buri dayafi naga ya sahale min wanan auren dake kaina in hutu da bakin cikin shi a zuciyana.
A mota fadilace take ta ban baki duk da bata san abinda ya faru ba amma haka tayi ta ban baki kan hakkuri.
Mun shigo gida yamma yayi a lokacin don haka kai tsaye kowa dakin sa ya nufa direct don yin sallah .
Koda na idar ban shigo ba ina part dina don yadda nake jin zuciyana a lokacin sai suka dauka hakan wani wullakancine kuma dana samu yanzu gare su.
Ban fito ba sai washegari don a ranan zamu rufe school zuwa hutun examas daya kawo jiki lokacin.
Na sauko na nufi falon suna zaune ana hira har hjy tafito a lokacin wurin ta na nufa nakai har kasa ina gaida ita da kwana take fadin.
Niko kawata wanan karon sam ban gane maki ba don bakya son shiga mutane yanzu sam ?
Zanyi magana naji muryan Nuriya na fadin kai hjy da wani abu kike ina zata shigo mutane a yanzu bayan tana ganin tafi aji da matsayi a yanzun.
Take annutin fuskan hjy ya sauya take fadin wanan wani irin magana kikeyi yar nan yarinyar nan idan ba wani abu ba me zaisa tayi hakan.
Ai munzo munga halinta a nan din ba hakan take ba ai yanzu ma din dai kila wani abin ne dai ya taso mata na uzuri.
Kara maimaita gaida ita nayi da kwana ta dan amsa da sauran hasalan a tare da ita nace zan leka makaranta in dawo.
Shi mijin naki fa ta tambaya tana kallona nace ya na ciki yana shiri shima zai fito yanzu don ni ina rigashi fita kullun.
Tace owoo Allah ya taimaka yasa a amfana ga abinda ake nema bayan ni dana amsa da amin babu mutum daya daya amsa mata wanan addu,an da tayi min.
Na juya inda suke a cikin jam,i ina ina kwanan ku ya bakunta ban jira amsan su ba nace na tafi sai na dawo.
Sai Na,ima ce tace tace min a dawo lafiya zee nace amin na leka dakin su Fadila na sallame su na fice gidan .
A waje na samu su yaya suna kallon gari daga dan wurin da suke nayi masu sallama na bude motana na tafi.
Na wuce ban dade ba jalal ya shiga ciki yana fadin ashe gaskiyan masu karin magana da sukace idan baka mutu ba ba debe tsammani a gareka.
Wai yau zee din mami ce take tuka motar da Nigeria sai dan wani dan kasuwa a lagos yake tukata wai yau ga zee a cikin shi tana ja.
Zee kan ai ta barmu da mamaki Na,ima ta fada sukan sauran shiru sukayi kamar basuji me ya fada ba a lokacin.
Hjy daga gefe tace Allah ke nan dare daya Allah kanyi bature dama abin haka yake wurin ubangiji ai.
Zaka ga dan mai kudi bai dace ba sai dan tallaka yazo shi ya bada mamaki baiwane na ubangiji hakan ai.
But Nuriya ta mike daga inda take zaune tana fadin muma din ai ba fin mu dai akayi ba dadin abin idan gidan miji sun kasa dakai ai iyayyen ka nada shi ko ?
Kaiya yar nan ai samun miji ga ya mace yafi na mahaifa don abin miji naka na kaima na iyayye kuma na sauran yan uwankane yanzu.
Har ta juyo kamar ta bada amsa sai kuma ta juya taci gaba da tafiya rai bace zuwa dakin da aka sauke su a ciki.
Yanzu kan zama gida ya kamani tare dasu dole na toshe kunnuwana akan irin maganganun da ake sake min a fakaice idan an zauna.
Ga mami an sallamo ta daga asibitin taki sake jiki da kowa a gidan tana daki ko yaushe ita kadai a ciki.
Ta fito da zancen komawa Nigeria hjy ta fatatake da fada don me take hakane tazo ne dama don ta dagawa yara hankali.
Don haka ba za a koma ba sai idan lokacin da suka diba din yayi hakan yasa mami din yin fushi da kowa a gidan babu ruwanta da kowa sai wanda ya shiga su dan gaisa sama sama kowa fushin ya same shi a gidan.
Ranan da suka cika sati daya a gidan suka shirya fita zuwa zagaya gari sun so mu tafi tare amma sai yaya yace na zauna suna sin ganina dama fadila da sadiya su rakasu.
Jin hakan da Nuriya tayi tace itama ta fasa fitan idan bada ni zasu fita ba nan kan ranan yaya yai mata jan ido akan lalai sai sun fita tunda da ita aka shirya fitan dama.
Badon taso ba ta shirya ta bisu suka fita bisa jagorancin jalal don jamal yaki shigowa gidan balle su leke mai.
Jin haka yasa na koma dakina ina zaman jiran tsamanin su basu dade da fita ba yaya jamal yazo ya kwankwasa min na bude.
Gaidashi nayi bayan ya amsa yake fadin kizo mami ke magana dake yanzu na amsa da to tare da komawa ciki na sako hijjabina na fito.
Ina shiga dakin ya mamud nagani a zaune yayi shiru kamar me tunane na gaidashi ya dan juyo yana amsa min.
Na gaida mami da jiki shiya nuna min wuri in zauna ban yarda na zauna saman kujeran da ya nuna min din ba.
Na samu wuri a kasa na zauna dan shiru ne kafin ya mamud ya kawar da shirun da fafmfin zainab tambayan ki muke son yi don Allah.
Kada ki fassara wanan abin da wani manufa ko ma,ana na daban ki tuna kema kamar mune kike a wurun mami.
Duk abinda yashafi dayan mu kamar ya shafeki ke ma don bayan kina diya a wurunta ga alaka na aurataya ya kara hadaki da mami din kuma a yanzu.
Don haka yarda da amana ya kara shiga a tsakanin mu ke nan ta ko ina yanzu don haka don Allah ki bamu amsa daudai abinda kika sani a game da mijin ki kada ki boye muna komai a game da rayuwan jafar a yanzu ?
Kaina gyada a hankali ba tare dana dago kai ba na kalli kowa daga cikin su yaci gaba da fadin don Allah zainab ki fada muna iya abinda kika sani akan jafar din dan zaman da kikayi nan dashi.
Don mun fahinci akwai sautin rayuwa wanda addini mu da al,ada bai amincewa ko wani dan musulmi dashi ba ya kasance yana aikata haka a rayuwan .
Ya jamal ya amsa da fadin kinga boye muna ko rufa mai asiri kamar kinfi kowa cutawa ne a hakan don asan ta inda za a fara taro wanan matsalan a tsanake.
Wani kuka ne yazo min ina kokarin dannewa saidai hakan bai yuyu ba gareni don saida hawayen ya zobo daga cikin idanuwana zuwa saman fuskana.
Kada kiyi kuka don Allah zainab don a wurin kine kawai zamu samu abinda muke son ji a yanzu kafin shi mu tunkare shi muji dalilin yin hakan garesh.
Nan ma dai shiru nayi masu don ban san mezan fara dashi ba a lokacin to tunda bata magana ai sai ku tambayeta muji don wanan ba abinda za a tsaya wani boye boye bane don mu fita daga zargin da zukatan mu ke ciki mami ta fada.
Hakane mami don na kula nima ba zata iya fadan komai yadda muke so ba a wirin ta ya gyara zama da kyau tare da fadin.
Zainab shin tunda kika auri jafar har zuwan ku nan akwai wani mu,a mulan aure dake shiga tsakani ku kamar yadda addini ya tanadar muna ?
Ma,ana yana kwanciyan aure dake yadda musulunci yace mata da miji suyi a tsakani ko kuma a, a wani hanya yake bi ya biya bukatanshi a gareki idan bukatan hakan ya taso a gare ku.
Kai na kara sadawa kasa don tambayan yai min nauyi da amsa hakan koda kuwa yaya jamal da yake kanin sane a wurin shi kadai.
Zainab ki fada mana mafita akeson a nema maku ga baki dayan ku do koba jafar kike aure ba yau hakan ke faruwa dole mu dage mu nema maki hakkin ki ga ko waye .
Don hakan yin shirun ki kamar kara dulmiyashi kike son yi ga aikata haramun a yanzu don baida kamarmu a fadin duniyan nan kaf da zasu tsaya akansa a yanzu.
Ki daure mun san wanan tambayan yana da nauyi ki fada muna kai tsaye amma kuma ya zama dole a gareki damu mu san gaskiya.
Kaina girgiza har lokacin kuka nakeyi da sauti a hankali mami tace kiyi magana mana kin tsaya kina girgiza kai kawai.
Mami kinsan sai anbi a hankali ba zata iya fadi kai tsaye yadda akeso ji ba sai dai a cikin fahinta za a gane komai jamal ya fada.
Kuna kwanciyan aure dai dashi ya mamud ya fada na sake girgiza kaina kamar yadda nayi da farko.
Wai kina nufin wani abu na aure bai taba shiga tsakanin ku ba tunda ya aure ki tun a can gida har zuwa nan ke nan ?
Na gyada kai innalillahi suka dauka dukan su mami kan kuka tasa saida suka bata baki suna fadin idan tayi haka ai ba za a gane komai ba karshe ma ya karta mu.
Ya juyo gareni ya sake fadin zainab ta yaya kuka zauna haka ba tare da wani ya san da wanan zancen ba kinsan kuwa kina cutuwa ?
Na girgiza kai yace wa iyazu billahi kuma ke baki taba masa maganan meya kawo haka ba don yanzu dai babu kurciya a tare dake ai ?
Sai lokacin na bude baki cikin muryan kuka ina fadin ban masa magana ba kan hakan saida nayi masa magana kan irin rayuwan da ya keyi a nan wanda bai dace ba.
Sai yace maki me ya mamud ya tambaya da sauri ya fada min kada in sa mashi ido ga duk abinda nagani yanayi idan ina son in tsira da mutunci na .
Kinsan yana mu,amula da maza yan uwan shi dan jim nayi nadan lokaci na kasa furta amsa ga wanan tambayan.
Muryan jamal ne yake fadin kinsan hakan ko baki sani ba na gyada kai alaman na sani kin dauki mataki a hakan ?
Nace yace shi mace bata ta burgeshi ba asalima asalima idan munga yayi hurda da mace eather yar uwar shi ko abokiyar aikin shi ko wani abin amma bada sunan so ba.
Wani irin kuka mai gumji mami tasa tana fadin na shiga uku jafar ya halakani jama,a ina zan saka kaina a duniyan nan ?
Tsakanina da jafar sai Allah , , , , a, a mami don Allah kada ki masa baki kuma ya kara lalacewa fiye da hakan Jamal ya fada a cikin damuwa.
Yana kuma sha har yanzu ko yaya mamud ya tambaya na gyada kai shiru ya biyo baya na dauka suna nazari ne kan zancen.
Ashe duk kuka suke a dakin sai da naji sheshekan kukan yaya mamud yasa na dan dago kai hakan yasa nima na kara sake sautin kukana sosai a lokacin.
Karshe dai ya mamud ne yace zainab koma dakin ki ko hakan ya wadatar damu kuma ba zamu nuna mashi munyi wanan zancen dake ba don gudun jefa ki a wani fitina kuma na daban .
Kaina gyada na mike jiki ba karfi cikin sanyin gwiwa na fice zuwa dakina a can na dasa wani sabon kuka saida lokacin sallah yayi na mike zuwa hin sallah.
Idarwa na yayi daidai da shigowan sadiya dakin tana fada min dawowan su nan ta zauna tana ban labari wanda ni a cikin zancen ta dain banhinci komai ba a lokacin.
Tare da sadiya muka kwana a dakina don yanzu Aisha tun ranan da muka samu matsala ta daina shiga dakin karshema daukan jskkar kayan ta tayi ta mayar dakin mami.
Zuwa safe ne jikin mami ya motsa aka kaita asibiti saidai ba a kwantar da ita ba magani kawai aka bata suka dawo gida.
Ashe a cikin daren suka zauna dashi tare da zayano mai laifin shi kaf yaso mussa masu saidai hakan bai samu ba.
Mami tace jafar ka cuce ni ka cuci rayuwana na na baya saidai ka sani ba zan bar zainab a gidan nan ba gaskiya tashi na tashin wanan yarinya.
Daga yau kuma jafar na sallame ka a cikin yayana tunda ka dauki turban shedan da ka yafa wa kanka ka zama abin kyama cikin mu.
Kai bamu kadai ba duk wani wanda ya sami wanan labarin dole ya kyamace ka a rayuwan shi.
Don haka bazan yarda ka cutawa yar mutane ba ka sallami yarinyar nan tunda ba aure a tsakanin ku tun kafin iyayyen ta suji su dauki mataki.
Sai lokacin da yaji mami ta kara maimaita zancenta kan tare dani zasu tafi ya dago kai ga idanuwan shi sunyi ja jajir don tashin hankali yace.
Mami akan me zan saki matana laifi daine nine na aikata ba ita kuma baiyi aune ba yaji saukan hannun mami a jikin shi.
Ya dago ta kara wanka mashi wani marin sai kuma ta kara fashewa da kuka tana fadin ka tashi ka bace min da gani .
Kuma dakata kaji daga yau sai yau idan ka kara nuna ka sanni ko wani nawa jafar muddin bakabar wanan halin ba sai na tsine ma.
Zaiyi magana mamud ya tare shi yace ka fice muna banza mara tunane da lissafi wawa kabi fudin duniya ka batawa zurian mu suna.
Ba mami dake duniya ba har daddy yana Allah wadai da samuwan ka a cikin zurian shi kayi gagawan tuba ga Allah tun kan ka wullakanta a duniya don karshen mai wanan dabi,an bai taba kyau tun a duniya.
Idan kana ganin kayiwa mutane wayau ne ai ba zakaiwa Allahn daya halice ka ba don yana nan madakata yana jiran kowa.
Dama manufar da kake fadin kana dashi ga auran yarinyar nan ke nan da muka kasa ganewa ashe abinda kake aikatawa ke nan a rayuwan ka.
Kana dan musulmai har ka iya mantawa da Allah zai iya daukan ranka akowani lokaci wata kila ma kana kan aikata wanan sabon ko kana shirin aikatawa Allah ya daukeka da wanan niyar.
In ma baka sani ba ka sani in ka mutu babu musulmin kwarai da zai halarci jana,izan ka wallahi.
Maganganun su kamar saukan garwashi yake jin shi a zuciyar shi saidai yadda yaga sun hau yau babu sauki a tare dasu .
Do bai taba zaton zata kwabe mashi da wuri haka ba shima sai gashi abu ya kwabe mai a lkkacin da bai shiryawa hakan ba.
Kalman mami gareshi da take ta nanata ta tsane shi ta tsaneshi ga baki daya tana kuma data sanin haihuwan shi datayi a yanzu.
Karshema tace datasan shi zata haifa da cikin shi ya bare bata haifeshi ba tun lokacin da wanan abin kunyan daya ja masu a duniya yanzu.
Lalai zainab yar albarkace don da watace da tuni an dade da jin wanan halin nasa gashi ta rufe ko su iyayyen shi bata fadawa wanan zancen ba tana zaune dakai a hakan.
Dole nema ka sallami yar mutane taje can tayi auren ta a cikin sallama idan ranshi yayi dubu ya baci a ranan don tashin hankalin da yake ciki.
Karshe ya mike ya fita daga dakin mami din ranshi bacd ya barsu ba don sun gama fada mai maganganh masu zafi ba.
Falo ya samu sisters din shi haka ya wuce su suna gaida shi bai karba masu ba ya fice daga gidan badon yasan inda ya dosa ba a lokacin.


ZAINAB IDRIS MAKAWALITTAFIN KUDINE DON ALLAH KI BIYA KAFIN KI KARANTA DA GUJEWA DAUKAN HAKKIN WANI, , , ,


Duk wanda ke gidan yasan akwai rikici a tsakanin sai dai ba wanda zaice ga dalilin daya faru a tsakanin su ba.
Sai hakan ya jefa kowa a cikin duhu akabar su da wasi wasin a zuciyar su don suna son sanin meke faruwa haka a gidan.
Sai dai sunfi karkata zuciyar su akan rashin kaunar da mami batayiwa auren mune ta tayar da wanan fitinan a tsakanin mu .
Har hakan ya jawo wani fitina da akeyi a lokacin wanda ya dagawa kowa hankali a cikin mu.
Nuriya har zancen ta tsare ya mamud dashi a dakin su ya hauta da fada yana fadin shi sam bai sam ma wani abu yana faruwa a gidan ba in ba data fadi hakan ba yanzu a gaban shi.
Bata gane komai ba dole ta bar zancen ga gulma kuma yana cinta akan sanin ko rikicin me akeyi a tsakanin su.
Gashi mami ta fada masu su shirya zasu koma gida tun lokacin tafiyan da suka debo baiyi ba na komawan su gida.

Da safene ina daki zaune wayana yai kara na dauka layin ya jafar ne ke kirana a take mamakin hakan ya kamani.
Saida naja aji na daga wayan da sallama a bakina naji muryan shi kasa kasa yana fadin kizo dakina ki sameni yanzu.
Ya kashe wayan nabi wayan da kallon mamaki a raina don mawuyacin abune zaisa ya nemeni a part din shi haka kai tsaye don ni har na saba da hakan.
Saida na dan dauki lokaci na mike na fito tare da rufo kofana na nufi part din nasa don ba nisa ke garemu sosai ba.
Dama kuma zamu bar wanan gidan mu koma wani unguwa dake can nisa da inda muke a yanzu .
Sanin hakan ranan yake waya a gaban mu muke jin yace wurin sabon gidan shi da zai koma da family din shi za a kai wanan dalilin yasa muka san zamu tashi a gidan.
Na dauka yana falon shi saidai ban sameshi a falon ba haka yasa na nufi dakin kwanan shi kai tsaye.
Saida na danyi nocking din kofan kafin in tura in shiga bawai zanji amsawan shi bane in har ya amsa din ma.
Can na hango tsaye a gaban widow dakin yana kallon haraban gidan na tako a hankali har zuwa inda yake tare da fadin gani yaya.
Ya juyo lokaci guda tare da dan kura min ido na dan lokaci kafin yace dani rufo kofa magana zamuyi dake.
Na juya zuwa kofan na rufo koda na juyo a lokacin ya dawo saman gado ya zauna wuri ya nuna min na samu a kusa dashi na dan zauna a cikin tsarguwa.
Zainab me kika fadawa mahaifiyata da yan uwana game dani ya fada ba tare da ya dago kai ba har lokacin kanshi na a duke ya harde hannayen shi biyu saman gwiwan kafan shi.
Da sauri na dan kallo shi don nima fuskana yana kallon kasan dakin dama a cikin mamaki karara a fuskana nake kallon shi.
Ya dago kai ya dan kalleni sai lokacin naga yadda idanuwan shi suka sauya sun rikede kamar ba nasa ba lokaci guda.
Nace mena fada masu ko sun fada ma na fada masu wani abu a game da kai zuwan su ?
Duk da nake yarinya ai nasan mutuncin kai na da kuma darajan aurena don haka bana cikin irin matan dake fallasa sirin gidan su.
Ido ya kura min kamar yana nazarina kafin ya sauke ajiyan zuciya yace idan bake kika fada masu ga yadda nake ba banyi zaton akwai wani wanda zai fadi hakan ba garesu.
Amma ai abinka ba a boye yake ba kowa ya sani idan ka boyewa wa mutane ai ba zaka boyewa Allah ba dole wata rana asan ko kai waye .
Saidai ranan ai mami ta shigo dakin kuma ta ganka tare da wanan abokin fasadin naka koka manta da hakan ne ?
Don ni ban san a yanayin data riskeka a ciki ba nadai ganta tayi baya acikin tashin hankali wanda hakan yai dadai da zuwana wurin na tareta zuwa dakina.
Bayan haka kuma ta wayi gari a cikin ciwon da har ta kwanta asibiti don haka ba ni zance da kawai na sani ke nan a gidan nan.
Humm kada ki mayar dani karamin yaro zainab idan baki fada masu ba abinda ke shiga tsakanina dake ba a matsayin mu na miji da mata yaya za ayi su san hakan su ?
Wanan ni ba matsala bane tunda zaman hakan bai dameni idan kana son jin komai ai zaka iya zuwa ka tuntubesu su fada ma wanda ya fada masu hakan.
Don ni ba a wurin mutum zan kai kukana ba sai wurin mahalicina don shine mai maganin kowa ba wani ba don haka meye amfanin fada masu komai.
Rashin kunyar nawa ai baikai in fada masu ga yadda muke zama dakai ba don na matsu ko me zaisa har in fadi hakan.
Na fahince ki zainab kina kokarin nuna min yanzu kinsan komai na dade da kula da hakan gareki don hakane kike son a rabaki dani yanzu ko ?
Idan anyi hakan an taimakeni ne yaya don ko ba a rabamu yanzu ba nan gaba dole a rabani dakai ai.
Kamar yadda nasan ka a dan musulmai a asali haka nima nake diyar musulmai a zahiri don haka ba zan zauna na yarda mu kone tare da kai ba tunda ka sani kake take sanin ka .
Tunda nakan fada mai magana ban taba gasa mai mai zafi irin wanan ba don haka hakkurin shi a ranan ya kai karshe dani.
A harzuke sai dana razana daya daka min wani tsawa ke enough kada ki daukeni mara hankali ko rashin wayau.
Naji mami na fadin zata wuce dake Nigeria bari kiji idan ma ke kika hada wanan zancen ki koma ki fada mata kin fasa tafiya don hakan zaifi maki sauki.
Don kafi ki tafi sai na halaki a kasan nan idan kin kafe akan zaki bisu ba tsoro duk da na tsorata da maganan nace.
Nasan zaka iya don imanin ka nada rauni ba Allah ka sani ba ai da baka kwana da dan uwanka namiji ba kabar , , ,
Marin daya daukeni dashi yasa naga wani irin duhu ya gitta min har na manta da abida zan fada lokacin.
Dafe wurin nayi na dan lokaci kafin na mike cikin karfin hali ina fadin ka mareni yaya ?
An mareki kada ki manta tun farko saidana fada maki auren mu na taimakon junane nida ke.
Don me yanzu zaki bijiro da wani zancen saki a baya ko kin dauka kinfi karfinane da kike min abinda kikaga dama ina kyaleki.
Akwai abinda nake duba nake raga maki sosai kada ki dauka hakan ba yana damuna bane don kawai banda abinda zanyi dake.
Wani kallo nayi mai wanda ban taba mai itin sa ba na raini na juya na fara tafiya don barin dakin.
Zaka san ka mareni don wanda bai sani ba yanzu zai sani bazan zauna da fasiki mai aikata fasadin mafi muni ba a duniya na fada dana kai kofan dakin.
Ya bini da kallo yana jin kansa kamar ya hade ranshi don wani irin takaicin da yake ji a zuciyar shi yana fadin.
Shi yarinyar nan zatayiwa tonon asiri irin haka duk ingata mata rayuwan danayi kada takai zuciyar ta ga hakan ?
Kafin wani lokaci wurin ya nuna alaman yatsun hannun shi don ya fito radau a fuskana abu ga farin mutum sai idanuwa na duk suka rikede sukai ja.
Kin fita nayi ina daki a kwance don ban gaida kowa na gidan ba da kwana a ranan haka yasa hjy aiko sadiya ta dubani ta same a wanan halin.
Komawa tayi ta fada mata ta samu kamar banda lafiyane ina kwance.
Sai ga hjy ta taso da kyar zuwa dakin take tambayan meya sameni ina kokarin boye mata take tambayana.
Wanan kamar shedan mari a fuskan ki nayi kasa da kaina ina hawaye jafiri ne ko shi yai maki wanan haka ?
A garin yaya haka ya faru ko uwar tasa tasa ya dokeki haka har tsanan yakai tasa dan ta gaba yai maki haka ?
Na samu na bude baki da kyar ina fadin hjy ki taimakeni ki rabani da ya jafar don ba cikkaken musulmi bane shi.
Innalillahi take fada tana taba hannayen ta a cikin mamaki kafin tace sallah ne baya cikawa ko azumine bayayi ?
Kaina girgiza mata a hankali ina maijin yadda zan bude bakina nayi maganan da ita a lokacin.
Saiga fadila ta turo kofan ta shigo dauke da abinci a hannun ta don tana da wanan dabi,an na kula dani idan ta fahinci bana cikin dadin rai.
Yanzu sadiya ke fada min bakya jin dadin jikin ki ta fada tana aje abincin tana kallona idon ta yi arba da shartin yatsun shi a fuskana .
Da sauri ta dago tana fadin subbahanallahi meya faru kuma haka madam wa yai maki wanan aikin haka ?
Wa zai mata banda mijinta mara tunane koma me tayima ai sai kayi hakkuri tunda baku kadai bane yanzu a gidan nan.
Wanan ai sai kabar mata abin fade idan yana dukanta bama kusa yanzu ma da muke nan akace ya duketa don bai san ciwon kansa ba.
Ina jafari ina dukan wanan yarinyar haka tunda ba karfin su daya ba wanan me zubin samudawa ina wanan yar zata dauki dukan shi haka ?
Hjy tunda nake zaune dasu a nan ko fada basa yi gaskiya a tsakanin su don zainab yarinya ce mai biyayya .
Yau daine hakan ya faru tsakanin su har abin yai muni to idan uwarshi tasa ya dukeki ai ya daki auren shi ke nan a gidan nan.
Jin haka na kara marairaicewa ina fadin don Allah hjy ki ceci rayuwana ban iya zama da yaya jafar a maysayin miji don ba dukiya nake aure ba.
Shiru sukayi suna kallo na kafin fadila tayi karfin halin fadin haba zainab ai addu,a bai bar komai ba ki dinga masa adduan nan dai da kika saba har Allah yasa ya daina wanan abubuwan da yakeyi din.
Amma zancen a rabaku wanan wani sabin tonon asirine a tsakanin ku zai taso maku har duniya ta jiku.
Bayan ana ganin ke din mai sa,a ce da kika samu miji da gidan hutu irin wanan kinga mutane basu gane halinda kike ciki ai.
Dakata yar nan kuna makana kun nuke ni ta baibai kun barni a duhu kai zancen ku yana nuna akwai mumunan zama a tsakanin auren nan da bamu sani ba.
Wallahi hjy a kwaishi kan sai dai tayi hakkuri data saba amma zainab tayi kankanta da irin wanan rayuwan haka da takeyi a gidan nan tunda da kurciyar ta.
Ace miji ba ruwan sa dakai ba zaya kalleka da sunan mata ba a idon sa saidai ayi ta labta ma kayan alatu kana hasaka gari ?
Tsohuwar ta gyara zama a rude tana fadin nikan kun barni a cikin duhu har yanzu don na kasa fahintar inda kuka dosa.
Sai ta mike tsaye wanan zancen bana kyalewa bane barin samu uwar nasa idan itace me sakashi cutawa yar nan haka a zaman su.
Duk kiran da fadila kewa hjy ta fice bata juyo ba gashi da kyat take tafiya yanzu ajiyan zuciya na sauke don nasan ko banza yanzu za ayita ta kare tunda har hjy taji wanan zancen duk da bataji duka ba ma.
Fadila ke fadin banso tsohuwar nan tafita haka a cikin fushi ba don yanzu komai zai iya faruwa har wa yan nan yaran su ji.
Dakin da mami ke ciki hjy ta dosa suka hade da ya jamal a kofa ta wuce shi tana fada haka kawai ka tasa yar mutane a gaba da duka .
Gara dai a kashe wanan auren kamar yadda iyami ke so tun farko kowa ma ya huta da wanan alkakan hakana.
Aure ba haihu bada ba jika amma fitinan shi har yau yaki karewa mutane a rayuwa gara akashe kowa ya huta.
Jin hakan yabi bayan ta zuwa dakin kusan a tare suka shiga mami na zaune ta jingina bayan ta da gado kafafuwan ta a mike da gani ba sai an tambaya ba tana cikin damuwa ko tashin hankali walau ciwo kuma.
Yau dai ayita ta kare a gidan nan ku sakarwa yar mutane mara ta huta mami ta dago kai da sauri tana fadin hjy kedawa kuma ?
Ni da dan nan naki jafari ya kama yar mutane da duka haka duk ya bata mata fuska da shartin yatsun shi ina yar nan ina daukan dukan bawan Allah nan.
Ko ya fara shaye shaye ni kan don sai magana take min bayani a dunkule mai nuna ABU A CIKIN DUHU SIRINE.
Mu muna mata kallon ta samu gida tana yadda ranta keso jiya jiyan nan na gama ji yaran nan wanda basu da aiki sai hassada da kyashi suna fadan haka da kunnuwana naji su sai gashi yau Allah ya nuna muna sirin dake boye.
To gara dai kisa ya sallami yar nan tunda abin ya kai ga duka haka tun muna nan ke nan inaga bama nan Allah kadai yasan ukuban da yake nuna mata tunda kin riga da kin masa huduban shedan ya dauka gara dai kowa ya huta da wanan auren itama ta kama gaban ta taje ta samu daidai da ita a can.
Saida ta kai aya ta dago kai don duban mami data kyaleta tana ta zuba haka sai taga mami din na hawaye mawuyacin abu ga mami din duk yadda ranta yakai ga baci kuwa.
Cikin muryan kuka mami ke fadin hjy jafar kasheni yake son yi ya huta a yanzu ina dana sanin ma haihuwan jafar a duniyan nan .
Hjy tayi tsaye sororo tana kallon mami din cikin mamaki don ganin yanayin ta dakuma abinda take fadi din don yadda tasan tana son dan nata fiye da duk yan uwan shi.
Haba mami ki daina fadan haka ki masa addua jamal ya fada daga bayan hjy inda yake tsaye a kofa ranshi bace.
Jamal dole in fada don jafar so yake ya konani a duniya bayan ya kona kansa saboda rudin duniya.
Fita yayi zuwa waje ashe ya mamud zai kira a waya ya kirashi ba a jima ba sai gashi yazo da saurin sa suka shigo tare.
Har lokacin mami kuka takeyi sosai itama hjy sai ta kama kuka duk da bata san abinda ya saka mami din kuka ba haka ?
Da sauri ya turo kofan ya shigo jamal na bayan shi ya maida kofan ya rufe don ma ginan su irin na kasan da wani bsijin wani da dole sauran mutanen gidan hankalin su ya dauku garesu.
Wai me kuma ya faru ni wanan abin gara mu koma gida zaifi mami fon wallahi hankalin kowa dai a tashe yake da wanan maganan.
Shi kanshi jafar din ai in kin kula baya cikin kwanciyan hankali duk tsiyat shi yanzu da yasan an gane me yakeyi ana nuna mai kyama.
Haka yasa ya tozarta ga baki daya baya cikin walwala duk da karfin halin shi kuwa wanan karon ya sare don bai zaci haka abin zaizo mai lokaci guda ba tunda ya maida mutane wawaye,
Yanzu ba wanan ba ya mamud zainab ya kama ya doka waya sani ko yayi shaye shayen nasa ne kuma ko ta kamashi yana harkan banza.
Sam ya manta da hjy tana dakin don idon shi ya rufe a lokacin yake faman dake maganan da ba a son taji din taji sai ji sukayi ta fadi saman gado Allah ya taimaka a zaune take lokacin.
Ihun kiran sunan ta da sukeyi yasa hankalin a gidan ya koma kansu da gudu aka nufo dakin mami din.
Gaba daya dakin suke shiga dan ihun da mami din keyi ina daki ban leko inda suke ba don hutun nasu ya zama muna tashin hankali ga baki dayan mu daga mu harsu a yanzu.
Ya mamud ya kira jafar a waya yana fadin kana inane kazo ga hjy ta some muna bata numfashi.
What hjy din meya same ta kuma yanzu muka gaisa da ita na fita to kazo dai yanzu ya fada ya kashe wayan.
Shike nan kun kashe min uwa kun huta saura ni ku kasheni mami ta fada a cikin kuka goran ruwa mai sanyi jalal ya dauko a fridge ya bulbula ma tsohuwan ta sauke ajiyan zuciya saidai bata bude ido ba.
Lokacin ne jafar ya shigo gidan a rude yana fadin ku dauko ta ga motab asibiti nan waje yanzu zasu karaso .
Yana kokarin daukan tsohuwan kakan tasu uwar ta daka mai tsawa da fadin kada ka taba min tsohuwa.
Tsayawa yayi cak bashi ba da wanan zancen ya daki zuciyar shi duk wanda ke wurin saida zancen ya taba mai zuciya.
Ya mamud ne ya matso ya sukuci tsohuwan dake kwance zuwa waje sauran suka mara mashi baya a cikin sanyi jiki.
Allah ya gyara daga Nuriya har yaran ta babu kowa a wurin lokacin suna part din su sun kulle don har yanzu bata bari yaran su sake jiki a cikin yan uwa.
Muna daki bamu san wainar da ake toyawa a gidan ba fadila tana ban hakkuri har muka koma hiran hjy da take nuna min kauna kamar ni din jinin tace.
Na,imace ta shigo part dina tana fadin hjy fa ba lafiya an tafi da ita salati muka saka fadila na fadin yanzu fa muke nan tare da ita.
Falon muka fito muka samesu zaune zugun zugun anan suke labarta muna dan abinda ya faru muna jimame tare da tamtaman hakan.
Allah ya taimaka ba a kwantar da ita ba bayan yan aune da sukai mata suka bata magani da sallama.
Bayan sun dawone kula da hjy ya dawo kaina nake kula da ita da komai dani da fadila yayin da shi kuma bai zama gidan sai dare sosai yake dawowa.
Ranan naji yaya mamud na fadawa hjy zasu koma Nigeria jibi jin hakan danayi yasa nima na fara shirya muna tafiya.
Fadila ta fahinci hakan ta sameshi ta fada mai don kada tayi laifi a wurin shi bai iya min magana ba don abinda ya faru mami ta kara daukan fushi dashi sosai da bai taba tsamani ba don ko ya gaida ita yakai bata karbawa yanzu ko gaban waye.
Don haka yaje ya samu yaya mamud don yai min magana ina daki zaune sai ga ya mamud din yazo nan dai yake ban hakkuri yana fadin.
Tunda yace da zaran na gama karatu zai zo damu Nageria don haka nayi hakkuri idona ya kawo hawaye nake fadin ya mamud kasan ya dai fada ne kawai .
Sau nawa yake zuwa gida bai je damu ba sai ya dawo muke sanin gida ya tafi ai dolen shi yazo gida don mami dake fushi dashi yace .
Muddin yana son albarka ya gama da duniyan nan lafiya dole yazo su shirya da mami din.
Dole ba don na yarda ba na bar zancen tafiyan muna kallo suka kwasa suka koma bayan ya cika yan uwan shi da abin arziki kaf da suka zo sai mami da jamal ne sukaki karban komai nasa.

ZAINAB IDRIS MAKAWALITTAFIN NAN NA KUDINE DON ALLAH KI BIYA MU FITA HAKKIN JUNA DANI DA KE YAR UWA, , , , ,

Gidan shiru kamar ba kowa tun bayan tafiyan su ashe mutum rahamane sosai don duk yadda nake dasu sai gashi na koma ina kewan su.
Ina dakina kwance don tafiyan dare sukayi ranan tunda muka dawo daga rakiyan su na shige daki ban kara lekowa waje ba har dayan rana.
Yunwa ya fitar dani na sauko nan ma babu kowa wurin a lokacin dakin su na nufa na tura na shiga.
Na hangosu saman gado kwance ba barci sukeyi ba sai dai sun kwanta shiru a lokacin ba wai hira sukeyi ba.
Sadiya tana kallo a wayana ita kuma fadila tana kwance ta kurawa rufin dakin ido tana tunane.
Kin tashi Fadila ta fada tana dagowa daga kwancen da take nake fadin eh dama ba barci nakeyi ba ina dai kwance ne.
Abinci fa ta tambayeni nace shina sauko ci zama nayi a dakin ta kawo min abincin na dan ci muna hira.
Itace ta sako zancen su tana tuna yadda hankali ya tashi da ciwon hjy kafin ta koma hiran yadda hankalin mami ya daga akan su koma gida alhalin basu gama kwanakin da zasuyi ba a nan.
Bandai yi magana ba sai murmushin da nakeyi kawai ina jin raina yana matukar baci sosai ga hiran da take min din a lokacin.
Nan dai na zauna a dakin har lokacin sallah yayi na mike na koma dakina bayan na idar da sallah kuma ba sake fitowa ba falon saida dare da zamuci abincin dare.
A takaice dai bamu hadu da yaya ba sai bayan kwana biyu da tafiyan su ranan ya samemu a falo zaune duk suka shiga mai sannu da zuwa.
Yanayin shi kawai na kalla nasan a buge yake yashawo maye don ko wurin hawa sama saida ya dan tsaya kadan kafin ya daure ya hau sama din.
Binshi nayi da kallo zuciyana tana wani irin tafasa kafin in mike zuwa part din na sameshi a yadda ya shigo din kwance shame shame saman kujera yana barci.
Saida na kare mai kallo na duka wurin kafan shi ina cire mai takalman dake kafan shi saye baiko tsaya ciresu ba.
Ya dan bude idanun shi a daidai lokacin dana fara cire mai takalman a kafan shi yana fadin wai meye hakane kin dameni fa yarinyar nan.
Kai na girgiza ina zare mai safan kafafuwan shi na mike dasu zuwa inda yake aje takalman daya saka kafin a goge mai a mayar.
Wanan ba aikina bane yana da mai gyaran dakuna a gidan yasa ban wani damu da inje in masa wani aiki ba a dakin nasa.
Na sake mai gudun AC din falon don yayi saurin farfadowa da wuri sanan na ja masa kofan na fita zuciyana na cike da tsanar sa.
Daki na na shiga ina tunanen zancen hjy a gareni da take fadin yar nan ki taimakawa mijin ki don Allah badon mu ba ko uwarshi dake nuna maki rashin kauna taimako zakiwa addini ki zauna dashi.
Zan samu lokaci mu zauna dashi kan matsalolin ku saidai hakan ba zai samu ba sai kin hada da hakkuri cikin al,amarin.
Hawaye ne yazo min dana tuna da wanan nauyin data dora min wanda ta rantse datun farko tasan da halin sa ba zata taba yarda ya aureni ba.
Yanzun kuma data sani din iya taimakon da zamuyi mai shine addua da saka ido ga wasu abubuwan da yake aikatawa koda yin hakan zai ja mana matsala a tsakanin mu.
Shine dalilin gwada hakan da nayi yanzu bayan na fahinci a buge ya shigo gidan ke nan don baida niyar daina hakan alama ya nuna.
Haka na kwana a cikin bakin ciki washegari inda na idar da sallah nan na kwanta sai barci don ban samu barci da dare ba saboda da tunane.
Haka ya shigo dakin ya sameno kwance kasa ina barci a takure ya dan dade tsaye yana kallona kafin ya juya zai fice daga dakin.
A lokacin na bude idanuna don nauyin mutum danaji a kaina tare da gyara kwanciyana shi nagani zai fita jin motsina yasa shi juyowa.
Baiyi magana ba ya sa kai ya fice dakin da sauri kamar wanda aka kora yayin da ya barni da mamakin abinda ya kawo shi dakin lokacin.
Saida naga fitan shi na mike da sauri na zauna ina dan dube dube a dakin banga komai ba na sauke ajiyan zuciya.
Wayana dake saman gadone ya dauki kara lokaci guda na mike zuwa inda wayan ke ruri na dauka bakon lamba daga Nigeria ake kirana dashi da mamaki nakai wayan a kunne na.
Muryan mami ne ya daki kunuwan nawa tana amsa sallaman da nayi saida na dan daga wayan daga kunne na a cikin mamaki.
Na mayar ina sauraren ta tana fadin mun sauka lafiya zainab nace Alhamdullahi mami ya gajiya ya sauran yan uwa da gajiya ta amsa a sake da lafiya lau zainab.
Ya kowa nan wurin ku kuna dai lafiya ko nace a cikin dan dari dari da ita lafiya muke to ki kara hannkuri don Allah zan kara kiran ki idan mun huta muyi magana a kan mijin naki kiji ko ?
Nace to mami nagode kiyi hakkuri kinji komai yai farko yana da iyaka insha Allahu ta fada a sanyaye na kara fadin na gode mami.
Bayan ta kashe nabi wayan da kallon mamaki ina rayawa a zuciyana yau ni mami kewa magana a tsigar lalashi haka ?
Nan ta barni da tunane barkatai a raina karshe na mike na shiga bandaki na watsa ma jikina ruwa cike da mamakin mami a zuciyana.
Don koda zata wuce wanan kalman ne muka rabu dashi na don Allah na kula na kara daure koma zai zo da sauki insha Allahu.
Ina zaune gaban mirrow nake wanan tunanen sai ga wasu hawaye masu dumi suna gangaro min a fuskana nasa gefen hannu na share a hankali.
Ina ayyanawa a raina cewa ni kuma nawa kaddaran ke nan auren dan luwadi mai bin jinsin shi ya gane me a hakan da yakeyi wai.
A take naji wani itin ysanarshi ya kara mamaye min zuciyana na mike zuwa wurin kayana ina dauka naji an shigo dakin.
Dan juyowa nayi shine ya shigo dakin a cikin shirin shi yayi wanka yasa tufafi a jikin shi yayi wani irin kyau da kamala zakace wani musulmine da tsoron Allah ya gama ratsashi.
Kallo daya nayi mai na kawar da kai daga kallon shi hakan bai hanashi karasowa inda nake tsaye ba.
Saida yazo gab dani ya ja ya tsaya yana fadin zuwa gobe ku shirya zamu bar gidan nan mu koma wani unguwa.
A raina nace at list ai zaka fada min da wuri don mu shirya amma ba haka kwatsam na inji wai gobe zamu bar wanan gidan zuwa wani wurin.
Saidai a fili ce mai nayi Allah ya kaimu kawai ya juya zai tafi sai kuma ya kara juyowa yana fadin uafin ku kawai da kuke so zaku dauka .
Naji na fada yasa kai ya bar min dakin na sauke ajiyan zuciya ina mai godewa Allah dayasa na rage kayana da yawa na tura gida.
Don hjy nabawa ta kai min gun innan mu don ita sakon zaifi saukin kaiwa a wurin don a kaduna take zaune.
Saida na gama shirina na fito falon zama nayi don inci abinci na samu irin girkin mu na yan Africane aka girka don girkin fadila daban yake da nasu idan tayi.
Zama nayi naci abincin sosai na turo ban kai ga dagawa ba fadila ta fito daga daki su tana fadin ashe kin fito yanzun nake zancen ki a raina ai ko kin tashi ?
Na tashi na bata amsa, sai ta dago kai ta dan saci kallon idanuwana da sukasha kuka tun a dare don tana saurin gane hakan idan har nayi kukan .
Zama tayi a gefena tana fadin kuka dai ya zama maki sana,a madam ya kamata zuwa yanzu kin saba da halin mijin na ki ai don shi bai dauki abinda yakeyi yanzu a bakin komai ba tunda yana cikin masu irin wanan dabi,an.
Da ace a gida Nigeria yakw rayuwan shi don dole yabar wani abin daga ciki saidai kash yanzu kan taro shi sai Allah gaskiya don yayi nisa sosai a cikin bata.
Ba yaya yasani kuka ba mamice mukai waya da ita da safen nan da sauri tace ba dai laifi kikai mata ba kuma na girgiza kai kawai tare da fadin hakkuri tabani kawai kanshi.
Anzo wurin ke nan ashe yanzu ta daina ganin laifin ki kan danta tunda ta gane gaskiya dama ai tasan gaskiya tunda ita ta haifi abinta.
Na mike tsaye don barin wajen ban son zancen yayi nisa kafin na juyo ina fadin yace gobe zamu bar gidan nan fa don haka mu shirya kayan mu a yau.
Gobe goben nan dai ta fada da mamaki nace haka ya fada dazun da zai fita tace ikon Allah shidai haka rayuwan shi take daban dana kowa .
Bahagon rayuwa dai ko dan wani abin da sani yakeyin shi don bai dauki mutane da muhinmanci ba a rayuwan.
Sadiya da aka fada mata sai murna da farin cikin komawa sabon wuri takeyi a fili da murrnan ta tacin min daki na rasa meke min dadi a lokacin.
Don Allah ya gani nasan wanan komawa gidan da zamuyi da biyu da uku zai canza wurin don wanan din ma da muke cikinsa ba laifi don in a Nigeria muke cikin sa sai ya zama gidan kwatance a gari.
Yayan mu ashe mu bar gidan nan cikin washe baki take tambayana haka na kallota ina fadin kinji dadin hakan ke nan ke ?
To ai abin murna ne ya samemu baki daya tana kaiwa kwance take wanan maganan nace eh abin murna kan ya samemu sadiya dake da maigidan ko ?
Don zamu koma can yayi bushashan da yake so yanzu idan nan na saka mai ido haka na damun shi.
Sam na manta da sadiya nake wanan maganan sai naji tace dani ba gidan sa bane yaya komai zaiyi yaje yai tayi balle ni banga wani abinda yakeyi ba ma.
Sadiya ki fice min daki tun kan ranki yakai ga baci yanzu na fada a hasale ina shirin sauke haushin daba nata ba a kanta kamar yadda uwa wani lokaci takan sauke haushi kan diyan ta idan ranta ya baci.
Falo ta koma ta zauna tana fushi har ya dawo ya sameta a wurin yanayin ta ya kalla kawai ya gane akwau abinda ke damun ta.
Ciki ciki ta gaidashi tana kawar da kai ya amsa har ya wuce ya dawo yana fadin sadiya yau ya akayine na ganki zaune ke kadai ?
Ba komai ta fada ciki ciki ya tako har inda take ya zauna kusa da ita ya sake fadin fada min mana yar kanwata waya taba min ke a gidan nan kuma ?
Yayan muce ta fada a sanyayye tana son yin kuka mai kikai mata kuma kukai fada ta sake fadan ba komai don kawai naji anty na fadin wai gobe zamu bar gidan nan shine shine ta kasa fada.
Shine me ya riko hannun ta yana tambaya shine tace wai ina murna don kawai zamu bar nan don na taya ka yin bushasha da kake so a can ?
Meye bushasha kuma ya tambaya da mamaki ta dago kai tana fadin nima ban sani ba haka dai ta fada ta koroni wai zata bata min rai.
Mikewa yayi ba tare dayayi magana ba zuwa part dina ya turo kofan ina zaune bakin gado na tsurawa kasa ido ina tunane.
Na rasa meye damuwan ki zainab duk yadda nake son mu rabu lafiya dake naga baki fatan hakan ke ?
Kai na dago ina mamakin dalilin wanan maganan yaci gaba da fadin meye bushasha a canza gida da har zaki zauna kina fadawa yarinya kamar sadiya wanan maganan ?
Ita ta fadama nace hakan nacene don bansan uban da takewa farin cikin don za ka canza gida ba ?
Idan ke baki farin ciki da hakan ki bari ita tayi don naga sadiyan tafiki wayau ma tunda ita yadda aka ajeta haka take bin abu.
Bazan taba bin karya da halaka ba saidai idan kasheni zakayi don ka fada dama zan saka kaina ga halaka idan nace sai nabi su mami ai.
Kai ya girgiza tare da fadin ni ban taba kashe ko dabba ba balle mutum idan ma haka kike tunane gareni.
Rashin inmani ai yana saka bawa yayi komai a rayuwan shi matukar ya fara kaucewa maliccinshi komai ma zai iya yi ai.
Shirme ke gareki zainab ina daukan ki yarinya da tasan kanta ga hakkuri da juriya ashe ba hakan kike ba ke ?
Zan iya jurewa a kan komai amma ba akai laifin da Allah zai tambayeni ba ranan hisabi wanda bani na aikata hakan ba kawai laifin wani ya shafeni.
Wani kallo yayi min na dan kasheshi da idon rashin kunya na dan lokaci kafin in dukar da kaina kasa .
Nasan da ace ba ya jafar bane nakewa wanan rashin kunyar haka da andade da jin mu da mai shi ko.
Amma sai inyi mamaki zan masa abinda bai dace ba saidai ya kalleni ya kyaleni hakana ya fice don a kullun muka hadu sai munyi fitina kan abu daya kuma yaki dainawa shi.
Yanzu kan tunda na kara dab shekaru na fahinci waye jafar din na daina tsoron shi sam a raina duk da ina dan dari darin shi ga wani abu idan bai shafi irin halaiyan rayuwan shi ba wani lokaci.
Yana fita na kuta don sadiya ta kaini iyaka yanzu banda daman yi mata fada sai tayi dalilin daya sani yaji yayi magana a kansa don hakane na shirya mata tsiya kan hakan.
Yan tufafina kawai na hada a cikin jakkunan tafiyana sai takardun karatuna dana dauka baya gasu ban dauki ko cibi ba a gidan kuma ?
Don nasan ko gida zan koma iya abinda zan bukata ke nan a yanzu don haka banba kaina wahala ba .
Sai dai da safe da yace idan akwai wani abinda zamu so zamu iya dauka don duk fitar dasu za,ayi don wani ne zai zauna a gidan na kasa dashi a wurin aikin su.
Nan na fahinci wanan sauyin gidan daga ma,aikatansu ya taso ke nan don haka na yanke shawaran kiran Maya da take kawata don na fahinci itama irin mune masu karamin karfi a kasan.
Kwatance nayi mata tazo gidan ta dauki duk abinda ranta keso tana murna ita kan da farin cikin hakan mota guda ta hada na kayan zuwa kauyen su da baida nisa da cikin garin sosai.
Sai da yamma yazo muka dauki hanya tafiya mai dan nisa da unguwar da muka baro din ya kaimu wani hatsabibin gida na zamani wanda kamar ba hannune ya gina shi ba.
Tsayawa fadin tsarin gidan bata lokacine don kowa yasan yadda chaina suka kwarai a wurin ginan su komai na zamani akwaishi a wanan gidan don ni abin har tsoro ya bani sosai.
Kamar yadda na zarga haka dinne ya faru don part din mu daban nasa daban a wanan gidan don haka zaici kareshi ba babbaka a wanan gidan.
Don ko kattai goma ya kawo ba zamu taba ganin su ba sai idan wani abu yakai mutum ya gani ga filin parking babba ga motoci a je a wurin.
Ga swimming pol mai kyau dashi ga wurin kiwon dabbobi can daga gefen gidan ganin haka sai kawai shima kanshi jafar din ban yarda da rayuwan shi ba gaba daya yanzu.
Har wani aiki yake masu yake samun wanan mahaukatan kudin haka a kasan mutane don ni in an barni zance wanan arzikin gaskiya da biyu.
Ban kara tsorata ba sai da muka shiga part din da yace shine namu ana saka muna kayan mu tsoro ya kara kamani sosai.
Haka muka kwana sabon gidan namu mai cike da abin aljabi a cikin sa wai matashi mai shekarun jafar ne mamalakin wanan katafaren gina irin haka.
Komai na gidan kan sai masha Allah ba a maganan wani bincike don fadan daya fi karfin ka sai ido don haka na raya dare ina kai kukana ga mahakicina Allah don neman tsari ga wanan gidan dashi kanshi mamalakin gidan a yanzu.
Da part din mu da nasa akwai katon falone gidan ne dayaji kayan alatu a tsakiya namu da nasa shima mai hawa biyu ne ginan saidai akwai bambaci sosai a tsakanin mu da wancan da muka baro.
Sannu sannu har muka fara sabawa da wanan gidan mai girma da ban tsoro duk da akwai tsaro sosai ba wani abin daga hankali a gidan.
Mu kanmu in ma cigaba ya samu ko wani daukaka mun sani don daula kan muna cikin sa sosai saidai hakan duk ragage ne a wurina.
Na daya da ace a gida muke cikin yan uwa hakan zai fi muna dadi don ko banza zaka taimakawa wanda ma baka da alaka dashi a can sabanin nan da kowa ta kasa yakeyi ba ruwan wani da wani don makwabtaka duk da unguwar da alama ba mabukata sam.
Sai na biyu wanda duk wannan daulan bai tsone min ido har in manta da addinina ba da al,adana na malam bahaushe don kullun zaka ganni saye da dan abinda zai rufe min tsiraicina wanda hakan ke min kariya ga duk narazana da iya shegen yan kasan da suke fama dashi.
Zan iyacewa Maya ce kadai wace nake hurda mai zurfi da ita don akwai yadda sosai a tsakanin koshi don mun karewa juna hakkin addinin mune tun farko wani bai shiga harkan addinin wani idan dan uwa na ibandan shi.
Maya kan da ace musulmace gaskiya da akwaita da rikon addini sosai sai dai kash ta kasance mai addinin suce na gargajiya ita.
A haka har hutu ya kare muka koma makaranta don ci gaba da darasin mu ba wani sokuni ko walwala a tare dani wanda yasa mayan ta kula da hakan.
Har yakai tana tambayana nake ce mata babu komai don ita a zaton ta ni ba matar aure bace saboda zata girme min sosai ga shekaru.
Ranan dai nake fada mata cewa nidin ai matar aure ce ta tsaya tana mamakin hakan don bata taba kowo hakan ba a fanta.
Take fadin babu wani alaman daya nuna ina da aure ai don komai nawa ya nuna still ni budurwace ai.
Da yake akwai yadda a tsakanin mu nan dai na dan bata labarina sama sama muka rabu tana cike da tunen halin da nake ciki din.
Na dawo gidane na tar da Fadila kuma a cikin tashin hankali wai danta daya mota ya bugeshi a hanyar zuwa makaranta ya rasu.
Ranan mun kwana cikin tashin hankali sosai a gidan don har ya jafar saida ya tausaya mata yana zaune a part din mu yana bata hakkuri.
Haka yasa tafiya zuwa Nugeria ya kama fadila din zata tafi ta barmu ke nan na dan wani lokaci kilama ra tafi ke nan ba zata dawo ba kuma.
Yanzu kam hankalina ya kara tashi sosai dason komawa gida dama itace mai debe muna kewa gashi itama din zata koma gida.
A cikin sati biyu ya gama mata shirin tafiya rana kan nayi kuka sosai ina ji dama ace nice zan tafi gida ba wani ba.
Baki ta fara bani tana fadin inyi hakkuri kada hakan yasa in sare in hakkura nagama karatuna kamar yadda yace tunda saura kadan ingama ai.
Don yanzu idan na koma gida ban karasa ba duk wahalan danayi ya tashi a banza amma a kalla in na kare karatun in ma rabuwa zamuyi ina da riban dana samu a wurin shi ai.
Tace nasan kina cutuwa da yawa zainab amma hakkuri baibar komai ba da rokon Allah nima nayi maki alkawarin zan dinga maki adduan akan wanan matsalan naku insha Allahu.
Da irin wanan ban bakin ta kwantar min da hankalina yasa aka kaita airport sai Nigeria ta barmu da halin mu a chaina mu kadai sai Allah.
Sam na manta da muyi wani zance da maya ranan muna hira take cewa dani tana son in samu lokaci in kai mata ziyara kauyen su don akwai abinda take son tataunawa dani a can amma fa idan na yarda.
Don tana son ta hadani da wasu kakanintane akan matsalana da mijina wanda tana son ta taimakeni a rayuwan ta itama kamar yadda nake taimakonta tun haduwan mu.
Shiru na danyi kafin ince ta bari in fadawa mijina zan kai mata ziyara tunda yasan muna tare da ita sosai a school.
Tace ba matsala idan naga hakan ba matsala zan iya fada mai niko hikimar yin hakan kada inzo in tafi bada sanin shi ba wani abu yaje can ya sameni bai sanda zuwana ba can.


ZAINAB IDRIS MAKAWALITTAFIN KUDINE YAR UWA DON ALLAH KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA PLEASE, , , , , , .

Duk da gakiyan data shana hanya hakan bai hanata shiryawa don zuwa garin zaria ba don da ba wani lalura a gabanta yadda tayi wanan tafiya da tana kwance a wanan lokacin tana hutawa.
Saidai wanan tafiyan yasha bambam da sauran tafiyan data sabayi a kullun don tafiyane na bashiri da ya risketa zuwa zaria din unguwar kusfa.
Gidan wani dadtijo data samu labarin shi a wurin sharan aikin sosai kamar yankar yuka don da wuya yayi aiki ba ai nasara ba akace.
Shine dalilin daya tayar da mami tazo kaduna cikin gagawa don hankalinta a tashe yake har wanan lokacin da tazo kaduna din.
Duk da mutanen da suka cika mata gida hakan bai hanata fita zuwa inda tayi niyar zuwa ba saidai wanan tafiyan daga ita sai yayan ta zasuyi shi bata yarda kowa ya bita cikin makarabanta ba don tafitane na shiri zasuyi kan abinda ya shafi rayuwanta da iyalin ta.
Haka ta fito tana ba mutane hakkuri uzuri ya kamata zata tafi unguwa sai ta dawo zata gansu kafin ta wuce.
Dole kowa ya hakkuru sai kalilan daga cikin danginta yan naci suka tsaya don akwai abinci da abin sha wadattace da aka girka don zuwan nasu.
Nan suka zauna a cikin radhin damuwa suna ci da sha da raha a tsakanin su masu kyashin juna kuma daga cikin su sunayi kamar yadda ake samun hakan a ko wani gidan mai akwai idan mutanen sa sun taru.
Tafiya sukayi na dan lokaci tsakanin kaduna da zaria sai gasu garin zaria din da bin kwatance har suka gano gidan malamin da dama yasan da zuwan su garin.
Basu tsaya wani bin layi ba don sha,anine na kudi akai masu iso suka shiga inda yake ganawa da mutanen sa.
Tare take da ya mamud sai jamal dasu kawai tayi wanan tafiyan don ko jalal da Aisha basu san abinda ke faruwa ba har wanan lokacin.
Bayan dan bayanin daya biyo baya yayi shiru kamar yana nazari a cikin ranshi yana kallon kasan da ke gaban shi zube a cikin wani katon katako.
Ga tasbaha a dayan hannun shi yana wani irin ja a cikin sauri yana kada kai suna gefe zaune sun kura ma abinda yakeyi idanu.
A sanyayye ya dago kai yana fadin lalai kunzo da babban al,amari mai wuyan sha,ani don gaskiya abinda nagani abune mai wuyan magancewa da sauri.
Saidai shi addua da sadaka baibar komai ba don duk yadda abu yake wanan suna rage karfin abu don ba abinda ya gagari ubangiji balle an hada da addu,a ga sadaka.
Musamman ke uwa kece ya kamata ki dage a wurin nemawa wanan yaron mafita daga fitutunun nan na duniya da suka taru sukai mai yawa a kanshi.
A yanzu mu maluma mun daina fadan sanadin abu don irin rigiman da abinda muka gani yake haifarwa daga baya.
Saidai wani hanzari ba gudu ba a wanan zancen ga wata yarinya dake tsaye fiye da kowa ga wanan zancen yar fara mara jiki sosai .
Don tafi kowa shiga damuwa da kuma yawaita yin addua a kullun kan wanan dan naki wanda a yanzu ma kiris take da samuwan warakan wanan al,amarin .
Saidai akwai dan tsaiko da wasi wasin yin hakan a zuciyar ta amma dai bari mu gani ya kara share kasan dake gaban shi yana dan wani tabe tabe a cikin kasan kafin ya nisa yace.
Bari dai mu gwada wanan dinbdon zan iya cewa ba tabbas a cikin lamarin yarinyar a yanzu don haka akwai yadda za ayi aike yaje gareshi..
Allah gafarta malam bamu dade da dawowa can kasan ba duk bamufi sati daya da dawo ba wurinsa yanzu.
Zaiyi wuya yanzu wani ya koma can din tunda har kasan chaina yake zaune tare da iyalin shi.
Tsohon yace na,am to idan har hakane yanzu sai dai aiyi aiki mai kama da aike a gurin shi zan baki addu,oi da zaki dinga yima safe da marance .
Zaifi kyau ace yasha wani abu daga cikin abinda zamu hada mai ya shiga cikin sa don ya ratsa jikin sa.
Ya mamud ya karbe da fadin malam zaizo nan kasan saidai ba lokaci amma munyi dashi zaizo ba dada dadewa ba in Allah ya yarda.
To duk lokacin da yazo din zaku iya kawo shi nan don akwai maganan da nake son muyi dashi ido da ido dashi.
Nan dai ya basu abinda zai basu suka fito suna godiya har lokacin ran mami ba dadi don ita tafi son ayi aikin gagawa wanda zai dakatar mata da dan nata daga aikata duk wani abin alfasha.
Ga tsohon kamar yana da magana a bakin shi don yace ba zai fada mata dalilin shigan dan nata wanan halin ba yayi mata magana ta baibai data kasa fahinta sai juya zancen take a cikin ranta har suka shigo garin kaduna.
Ta samu gidan nata a cike da mutane kamar yadda ta barsu kan ta tafi yanzu ma haka ta samu gidan saidai yau yan zuwa wurin nata sam basu ganewa hjyn tasu ba don fuskanta babu walwala.
Haka take amsa masu gaisuwan su tana wucewa don jin kanta takeyi kamar ba ita bace saboda damuwa da yayi mata yawa sosai a lokacin.
Saidai ganin anty Safiya tare da yar uwanta yasa ta dan ja ta tsaya tana fadin Safiya ina kika shige kwana biyu bamu haduwa ?
Jin hakan da gani da anty safiya tayi mami tayi mata magana cikin sakin fuska da hahaba a cikin mutane wanda rabon data samu ganin sakin fuskan mami wurin ta tun faruwan rikicin auren mu da jafar ta daina sake masu fuska haka yasa mijin ta cewa ai ba dole bane ta rabu da ita mana idan ta sauya mata.
Basu daddara ba yanzu ma suka zo yi mata sannu da zuwa don kawai wai tana gaba dasu suke mata biyayya a cewan su.
Don mami ta kasace mace ce mai yawan aikata alheri shiyasa ake yawan zuwa wurinta da zaran anji tana gari har wanda bata sani ba suna zuwa da koken su.
Har ta wuce kowa sai kuma ta juyo don ganin anty safiya da hannu ta nunata tana fadin ke wai kina kasan nan dama.
Ba anty safiya ba kowa dake wurin yayi makmakin hanka a yadda ta shigo bata kula kowa ba sai ganin anty din ta dan ja ta tsaya.
Ita ko anty safiya mamakine ya kamata sosai ganin yau yadda ta tsaya ta kulata a bainan jama,a sabani tun lokacin auren mu da ya jafar data tsani kowa nawa harda anty din data kawoni wurin ta.
Tana ganin itace sanadin komai a lokacin yasa ta rufe da ita gaba daya wullakanci iri iri sun sha shi wirin mami har suka gaji suka dauke kafansu a wurinta.
Yanzu dai di sunzo ne don cewa da akayi bata da lafiya tunda ta dawo chaina gashi kuma tazo garin kaduna sukace bari suzo su gaida ita kunsan abu ga maishi.
Da hannu ta yafutu ta tana ci gaba da tafiya da sauri anty din ta mike tabi bayan mami din suka shiga part din ta tare.
Safiya kin dauke kafan ki ko nazo garin nan yanzu baki zuwa ko wani abin ne ya faru tana zama take fadan hakan tare da cire gyalen data yafa a jikinta lokacin.
Anty safiya tace bawai hakana bane aiko ina zuwa wani lokaci dai bama ganin kine ko munzo.
Ok ta fada tana daukan wayan ta tace Ramatu akawo min abinci mana su mamud ma na part din shi akai masu nasu ta dago bayan ta aje wayan tana fadin.
Diyarki ce ko kanwar ki tana can yanzu idan kinganta ai ba zaki ganeta ba ma don gaba daya ta canza wallahi .
Ikon Allah suna dai lafiya anty ta fada tana gudun ta fadi wani magana tayi baranbarama a gaban mami din.
Mami ta amsa a kasalance lafiya kalau halan baku waya da itane yanzu ta fada tana dago ido don kallon anty din .
Ina ganin bata da layina nima haka don tunda suka tafi bamuyi waya ba gaskiya don yadda na falfale ta akan auren kamar yadda kika umurceni in mata din.
Kai ai komai ya wuce yanzu suna can zaune kalau abinsu sai karatun da takeyi tana gab da gamawa yanzu haka da munzo tare ai taga gida don sun dade basu zo gida ba, har kanwarta da suke tare a can.
Au da yarinyar ta tafi ashe gaskiya jafar yayi kokari sosai Allah dai ya saka da alherin sa don ba karamin kokari yayi ba yin hakan.
Aka toro kofan mai abinci ta shigo da abincin mama Ramatu na biye da ita a baya suka sauke abincin saman dan table din dake karamin falon.
Tare aka zuba masu da anty sai wani kallo mama Ramatu ke bin anty Safiya dashi duk da tagani bata damu da hakan ba.
Kowa yayi mamakin jin a ranan zasu koma ashe karfe nakwai na dare saida ta gana da wasu daga cikin jama,an wasu kuma aka basu hakuri sai gaba.

ANCHAU

Gidan namu yana nan har yau da fitinan shi kamar kullun duk da an raba shiya yanzu amma haka bai hana Lantana takowa har wurin inna yin fada .
Abban mu yayi warning dinta kan hakan bata daina ba ya kawo ido ya saka mata, dan gara ma yanzu don Sa,adatu na taka mata burki sosai idan tana gida.
Saidai duk da raba shiyan bai hana lantana saka ido ga shige da fice a sashen inna din ba don takan dawo barandanta ta zauna tana kallon abindake wakana a gidan .
Don yanzu inna nada katon fridge har biyu da take sana,a dashi kankara a wurinta ko wani lokaci mutum yazo zai samu dayan kuma ruwane da zobo mai sanyi da sukeyi dan kobon kashi na shigo masu .
Duk wanan aikin nasa ne da yakeyo masu aike a kai akai ba tare da sanina ba saidai inna ta fada min ko sa,adatu a waya nake sanin yayi masu aike wani ma banji sai daga baya acikin hira da mukeyi dasu a waya wani lokaci.
Motan su hjy ne ya tsaya a kofan gidan da sauri lantana tacewa karamin danta kai dan baba jeka kofan gida ka duba ko Abban kune yayi baki don naji mota ya tsaya a kofan gidan nan.
Yaron ya ruga da gudu zuwa dubawa ya dawo yana hakki yana fadin motace mai kyau mama wata tsohuwa ce a ciki tafito.
Ta mike da sauri tana fadin ina kuma muka samu tsohuwa mai mota kodai wani gidan suke nema sukazo nan din don bata sai sallaman hjy sukaji ta shigo tana tafiya da kyar don kafanta.
Kicibis sukayi da Lantana a kofa dake sabe da diyarta datake goyo don yaranta mata biyu yanzu data haifa bayan wancan da namiji din na farko data haifa.
Tana da namiji daya innan mu nada maza biyu yanzu itama saidai inna ta fara kiran auta kan wanda ta yaye din.
Tsaye tayi sororo tana kallon tsohuwar dake kwada sallama tana fadin gidan ne kuwa don gaba daya wurin ya sake mun ?
Asbe dake can tana jin tun lokacin da lantana ta tura yaron ta ta fito tana fadin maraban ku ku karaso daga ciki.
Lantana sai fadi take kina ta karaso kinsan wanda tazo nema kilafa ba gidan nan sukazo ba ai ko ba nan bane mutum ya shigo ka taresa ko ?
Hjy ta taka har zuwa cikin part din Asabe din suka gaisa bayan tayi mata taro na arziki saida hjy ta dan sha ruwan da Asabe ta kawo mata ta aje kwanon take fadin daga wurin su zainabu nake takwara na dake kasan wajen.
Asabe batayi saurin gane wa hjy ke nufi ba saida ta kara mata bayani da cewa yar gidan nan dake aure a Abuja nake nufi yanzu suna zaune a kasan waje ita da kanwarta uwarsu nake nema ?
A, a daga wurin su Abu kike ashe tana gyara zama tana tambaya kafin tace madalla da wanan zuwan naki kuwa ga gari ya dauka mun sayar da. Abune da kanwarta wa mai kudi.
Yanzun hakama basa raye an kashesu su biyun, ba kowa ya yayata hakan a garin nan ba nan ne Lantana duk tabi garin nan ta bata muna suna da wanan zancen saboda bakin kishinta na banza.
Zainabu kan tana raye karatune ya tsayar da ita yasa baku ganta ba kwanan nan muka dawo daga wurin su duk tace a gaishe ku.
Ai haihuwan diya mace ke nan babban arzikine a yanzu don aure ba inda baikai mace a duniyan nan sai kinyi kwana biyu a jirgi kafin kikai garin su.
Tana kokarin mikewa don kukan da taga Asabe ta fara take fadin kaini naga uwarsu bana son tafiyan dare shiyasa muka dako safiyan nan haka.
Asabe ta mike suka fito har lokacin lantana tana labe sai bakar magana takeyi dun kawo tsakar gida take fadin indai da kwadai da wullakanci .
Da anga bakin yan birni sai hankali ya gushewa mutum wurin kwadai kai kawai hjy ta girgiza duk Labarin lantana da nake yawan bata ba karya a cikin sa ko kadan don ta sheda hakan yanzu.
Sun shiga wurin inna sin samesu a falon su zaune ga dakin na kamshin turaren wutan kajiji da karo data saka don sanyin damana da akeyi.
Wanda yana cikin sirin mata da can baya wanda mata a yanzu suka daina amfani dashi don rashin sanin muhinmancin hakan .
Akwai wani sirin boye da ke akwai a cikin kajiji da karo wanda ba kowa yasan da wanan sirin ba sai matan da suka amsa sunan su ko a baya suke yawan amfani da wanan sirin a dakunan su.
Akwai haske da kwar jini ga kariya ga both uwa da yaranta wurin amfani da kajiji da garin karo da mata keyi a da can baya.
Don mace mai amfani da wanan gaskiya idan kin tambaya ba wani farmakin kishiya ko dangin miji ko makwabta da zai iya farma ki ko danki don akwa kariya sosai a wanan sirin .
A wurin miji kikan zama mowar mata do zaki zama zara a duk inda kika dosa balle ga mijin ki na sunna.
Hjy na shiga dakin ta dan sake murmushi tana girgiza kai don ganin inda na koyo tsabta da hakuri da sanin wasu sirika da take gani a wurina.
Sun zauna an gaisa sa,adatu ce ta fara tambayana take fadin muna lafiya satin nan daya wuce suka dawo daga wurin mu ai.
Nan dai ta shiga basu labarin mu da karatun da mukeyi a can chaina din a karshe tace a fita waje a shigo da sako na nan dana bayar akawo masu.
Lantana na ganin ana shigo da manyan kumshin kaya zuwa wurin innan mu sai zama ya gagareta ta shiga sintiri tana leken kayan da ake shiga dasu din har kumshi uku gasu dirka dirkan kumshi dasu.
Duk da inna bata sanda zuwan hjy ba hakan bai hana ta dan bata abin motsa baki ba gashi dan wake tayi da mai da yaji hjy ta sake taci sosai aka kaiwa driver da jikanta daya daya rakota nasu.
Bayan tafiyan hjy ne sa,adatu ta matsu a bude kayan suga abinda ke ciki dole dai saida inna ta bude suka shiga ihun ganin kayan.
Sun kira waya basu sameni ba ina school lokacin don ina kashe wayana idan zan shiga lectures bana shiga dashi a kunne.
Nan dai Abban mu ya dawo ya sakesu suna murnan sakon dana aiko masu din wanda tufafi ne sai zannuwan gado da sauran tarkacen mata.
Shima Abba har lantana sun samu nasu rabon don na rubuta sunan kowa a cikin sakon sai gashi lantana baki ya mutu a lokacin.
CHAINA

Zancen mu da maya ya tsaya min a rai don ina tsoro ban san abinda zanje inji ba ko ya kasance sha,anin su na tsafine.
Gashi ina ji daga chaina sai indiya a wurin tsafi ni kuma ban son inyi abinda zan kaucewa ubangijina gaskiya.
Itama a nata bangaren maya bata kara yi min maganan ba daya shafi wani zancena dashi tun wanan lokacin.
Inda shi kuma gogan yanzu ya samu saukin fitina tun bayan dawowan mu wanan gida akwai kofa ta bayan ko wani part ta baya yake yawan bi da mutanen sa tunda ba fasawa zaiyi ba ga halinshi.
Wanan ya kara kawo ko in kula ga zaman mu sai dai yana kokarin duk rana zai dan shigo sama sama ya duba lafiyan mu iyakan mu dashi ke nan yanzu.
Sai hakan ya kara kawo min kwanciyan hankali duk da rashin Fadila da mukayi mafi yawan lokaci zaman kadaici yakan dame mu don dama da tana nan da ita muke debe kewa ayi ta hira har wani lokaci.
Yanzu ko matan da muke tare dasu ba launin mu ba don haka ba ruwan mu dasu iyakan mu dasu sai gaisuwa idan mun hadu saidai akwasu da girmamawa sosai gaskiya.
Ga arzikin shi kamar ana zuba mai taki gaskiya ni har abin watarana yana ban tsoro idan ina tunane ni kadai.
Ga sadiya baki babu halin in zauna da ita muyi wani magana kamar yadda mukeyi da fadila don sai ince ma tafi daukan shi dan uwa yanzu bisa gani.
Shima yana yawan kulata sosai komai ya gani daya dace da ita zai sayo ya kawo mata shi ta dinga murna har nakanyi tunanen wa sadiya ta biyone a cikin iyayyen mu wai ?
Abin mamaki ranan safiyan asabar duk muna gida bamu fita ba har shi saidai ba lalai bane ai ya shigo wurin mu don mun saba da hakan dama.
Muna zaune falo zaman daki ya isheni ya dawo falon gidan dake tsakiya inda ya samemu ya zauna.
Da dan takardan daya shafi karatuna a hannu na dake nazari ya zauna a kusa da sadiya yana fadin yau dai sai ku shiya zamu tafi wani shakatawa tare daku.
Hakan da ya fada bausa na dago kaina ba tun bayan gaisuwan danayi masa daya shigo naci gaba da karatuna daya samu inayi.
Murna sosai sadiya keyi lokacin ganin ban dago kaina ba yasa shi fadin ina fatan kinji abindana fada ai ?
Ina da test ba zan samu zuwa ba itama din tace tana da pratical da zasuyi ai ranan mondaya na bashi amsa ina kallon shi.
Fitan da zamuyi din na dan lokaci zai hanaku yin test ko pratical don haka ku shirya karfe uku zamu bar gidan nan ya fada a dake yana mikewa.
Kallon mamaki na bi bayan shi dashi har ya shige part din shi Allah yasa ya kaimu irin wurun da mukaje ranan nan mu hau doki.
Muryan sadiyace ke fadin haka a gefena na juyo a cikin fushi ina fadin yanzu in mare bakin nan naki sakaran yarinya kawai.
Da sauri ta make a wuri daya don in akwai abindata tsana shine duka ganin haka na mike zuwa dakina na barta a wurin zaune.
Ina shiga dakin wayana yana kara da sauri na karasa na dauki wayan innan muce ke kirana nasan safiyace a wanan lokacin Nigeria .
Dauka nayi da sallama muryan Sa,adatune tana fadin inna na sameta ta dauka naji innan mu na bani wayan nan.
Mun gaisa take fadin saiga sako tsohuwan nan ta kawo muna ta shiga saka min albarka wasu hawayene suka zo min lokaci guda har inna ta gane kuka nakeyi.
A rude take fadin subbahanallahi meku ya faru dake ko baki da lafiya ne da kyar na iya budan bakina nace inna kalau nake.
Gida nake sin dawowa yanzu kuma yaki bari hakan don naso na biyo yan uwanshi da sukazo bai yarda ba.
Kanki daya kuwa naji inna ta fada keda ke aure inake ina bin wasu kuma kull na kara jin wanan zancen haka ranki zai baci sosai.
Kuka na sakawa inna cikin wayan ina fadin inna na gajine ya jafar ba abokin zama bane wallahi dabi,un shi da halaiyan shi sam ba na mutumin , , ,
Innace ta kashe layin bata tsaya ta karasa sauraren abinda zan fada ba a lokacin takaicin hakan yasa na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya.


ZAINAB IDRIS MAKAWALITTAFIN NAN NA KUDINE YAR UWA KI BIYA DON ALLAH KAFIN KI KARANTA DON SAUKE HAKKIN WANI A KANKI ALLAH YA BADA IKON BIYA, , , ,

Ba don na soba haka na shirya sai dai ba wani make-up danayi a fuskana riga kawai na zura a jikina na fito falon na samu har sun fita waje ko da uwar zumudi sadiya.
A mota na samesu zaune na bude baya da nufin shiga ba tare daya dago kai ya kallon in da nake ba yace dani.
Amma kinga ni zan tukaku ai da zaki shiga baya yafada yana gyara zaman shi cikin ko in kulla na dawo gaban motan na zauna na rufo kofan a hasale.
Don ni harga Allah wanan fitan haka kawai zuciyana naji baison fitan da zamuyi dashi a lokacin.
Juyowa yayi yadan kalloni ya girgiza kanshi don shigan nawa bai mai ba a lokacin sai kuma naji ya furzo iska daga bakin shi tare da shafo suman kanshi da hannu daya ya tayar da mota muka fice gidan.
Kida ya saka a motan kamar na yare bandai saurari mai ake fada ba balle na gane haka muke tafiyan har wurin wani taro don na gane hakan ne saboda motacin dana gani a wurin .
Saida ya tsayar da mota yake fadin zamu shiga wurin tarom nan ba zamu dade ba don abokinane ke bukin zagayowan haihuwan shi yau.
Kai na dan gyada ba tare da in kula dako ya kalloni ba muka fito daga cikin motan zuwa cikin inda ake taron .
Sune yan kasan birjit a wurin tun daga waje zaka gane hakan sadiya dake wani shige mai na finciko da karfi tayo baya duk da yajimu bai juyo ya kalle mu ba nace a hankali wallahi ki natsu ki kama kanki a wurin nan kin dai san kasan nan naman mutum sukeci.
Sai mu nemeki mu rasa a wirin sun daukeki sun yanka ba wani aiki bane a wurin su don haka kafana kafan ki idan kinji.
Na fadi hakane do yadda naga tana zumudin shiga ga wurin sam ban yarda dashi ba tun daga ganin irin mutanen dake wajen da nayi.
Take ido ya dawo a wurin mu nasan ba komai ya jawo hakan ba sai kasancewan mu bakaken fata kuma musulmai don abaya na saka sama na rufe kaina da gyalen shi shigar musulunci nayi kamar nasan hakan zai kasance idon ta ya jafar ne baiki na fito kamar sauran matan dake wurin suna shiga kamar tsirara dasu.
Tun a kofa aka fara bashi hannu wani irin gaisuwa da akeyi wurin zai daurewa mutum kai don in dane sai ince gaisuwan kasan ke nan a hakan .
Amma yanzu na fahinci komai ba wai dabi,an yan kasan bane wanan gaisuwan haka muke tafiya har zuwa inda taron yake duk wanda nayi katari ya gaida mu sai dai na dan dukar da kai yadda naga yan garin na gaisuwan su.
Idanuwa a kanmu sai kuskus da keyi kan shigowan mu din hannu philip ya miko wai mu gaisa na girgiza kai tare da mai gasuwan su na koma bayan yaya na labe sai ya bini da kallo.
Duk inda ya saka kafan shi muna biye dashi a baya har wani yazo ya jaye shi ina hangen su suna gaisawa da wasu da nake ganin kamar bakine suka zo saidai shigan su tantiran yan iskane ga sarka ga dankune duk sun saka a jikin su kamar mata.
Ganin hakan na kara shan jinin jikina ga sadiya tana makale a hannu na ban yarda na saketa ba.
Wani ne ke nufo mu a cikin murmushi har ya karaso inda muke ya miko min hannu yana fadin sunan shi Sam hannun nasa na kalla nace mai thanks kawai ina kokarin kawar da kai sai ji kawai nayi ya rungumoni a jikinshi.
Ban tsaya jiran komai ba na daga hannu na kwasheshi da mari kayauuu a fuska Allah ya ban sa,a na samu fuskanshi da kyau ya dafe wurin yana kallona.
Haka ya dawo da hankalin mutanen taron kan mu yana fadin pretty kika mareni do kinyi sa,a na kulaki kina mace ?
Sai zaran idanu nake a hasale nace dashi how dear torch me ina musulma zaka rungumeni haka kaiba mijina ba ba wani dan uwana ba ?
J dinnne ya karaso inda muke wanan maganan ya kalli mutumin yace me ke faruwa ne a nan ?
Ya dago idanun shi da sukai ja yana fadin don kawai ta burgeni nazo mata shine ta daga hannu ta mareni kawai yana murza wurin da alama marin ya shigeshi sosai.
J din yace kasani ai ita ba karuwa bane ko wata mai zaman kanta addinin mu kuma bai yarda dayin hakan ba don me zaka rungume ta ?
Just a hug nayi niyar mata don tana pretty girl ta burgeni kawai amma ban san hakan zai bata mata rai ba ai har ta mareni ?
Zuwan abokan shi su uku wurin ya hana J din bashi amsa don har ya dago idon shi jajaye da niyar fadin wani abu suka iso suna rungumar shi.
Tare da fadin mai zai sa kayi mata haka kaiko ai kaga shiganta kasan su musulmai ne basu yarda da hakan ba ai dakayi.
Yace naga J din kamar shi bai damu da addinin nasu ba don naga baya abinda sukeyi na dauka itama yar hannuce ya dauko .
Wani irin hawayen nadama ne suka zo min lokaci guda a idona a hankali na juya na fara tafiya da hannun sadiya dake makale da nawa har lokacin.
Fita mukayi daga cikin dakin da ake birthday din ba tare da nasan inda muka dosa ba a lokacin sai tafiya mukeyi babu ko waigawa.
Nake jiyo horn din mota a bayan mu sai sadiyane ta iya juyawa naji tace ga yaya nan a bayan mu da mota shi.
Hakan baisa na tsaya ba saida naji yace ina zaku tafine ana maki magana kina wucewa naja na tsaya .
Ya tsayar da motan yana fadin ku shiga mu koma gida sannan na taka na zagaya na shiga motan ba tare dana kalleshi ba muka fara tafiya bamu san yadda suka karasa a wurin taron ba .
Ga wayan shi nata ruri tun dauka daya dayayi ya duba bai kara duba mai kiran nasa ba lokacin sai tsukin da yakeyi kawai lokaci lokaci.
A wani babban shago ya tsaya tare da waigawa inda sadiya take zaune yake fadin ku fita kowa ya dauki duk abinda yake so a nan .
Shiru motan yayi ba wanda ya motsa a cikin mu ya kara fadin ku fita mu shiga nace daku ko bakuji bane ya fada a dake.
Bana son komai gida nake son zuwa kawai na bashi amsa ba tare da juyo inda yake ba sadiya fito mu shiga ciki.
Da sauri sadiyan ta girgiza kai tana fadin a, a yaya muje gida kawai nima ban son komai .
Kallon mamaki yayi mata kafin yace tsoro kike jine har yanzu sadiya ta gyada mai kai alaman eh.
Dama tunda bakiso fita ba nasan fitan ba zai muna dadi ba don kamar na tursasakine kika fito ai da sai ka barmu gida zaifi tunda ka fahinci hakan.
Na fada a hankali wasu hawaye na zo min a idona kai ya girgiza tare da bude motan yana fadin da zai fita ko ku fito ko kuma na mayar daku wurin taron nan don ba zaki hanani zama ba .
Kizo nan kuma ki tauye yar uwanki dani zabi ya saura gareki yanzu ya fada yana karasa fita daga cikin motan.
Dole na fito don ranan ji nake kamar duk zunubi a kaina ya kare don abinda dan arnen nan yayi mun a wurin.
Yana gaba muna biye dashi har muka hau lifter zuwa sama ya juyo yana fadin yau kan Sadiya ba zan tayaki zaben komai ba don fushi nake dake.
Kayi hakkuri ya jafar tsoro naji kada su kashemu a wurin kaga su arnaku ne duka wurin cewa da abinda na fada mata da zamu shiga wurin birthday din dazun shi ya tsorata ta ashe ta natsu badon Allah ba.
Balle taga abinda ya faru dani a wurin ya kara daga mata hankali take ganin kamar gaskiyane abinda na fada mata din.
Naji yace tsoron may kike ji kuma Sadiya ba gani ba ba abinda zai same ki ai muna tare kinji.
Mun shiga wurin ban dauki komai ba a shoprite din sai faman yawatawa da sadiya sukeyi karshe ma na dawo na samu wuri na zauna har suka gaji suka fito lokacin dare yayi sosai koda muka shigo gida.
Sallah nayi bayan nayi wanka nayi ta darazan jikina don ina jin kamar har lokacin indaya tabani wurin yatsunshi dun manne mun a kafada na.
Ko a school haka nake komai sukuku dani ba sakin jiki yasa har maya ta fahinci hakan gareni ina zaune cikin zurfin tunane .
Naji an dafa min kafada na nayi firgigit na zabura ina sauke ajiyan zuciya ta zauna gab dani tana fadin meke damuwan ki haka zee ?
Tun da safe ina hankale dake baki cikin hayacin ki ko kun kara hadewa da mutumin naki ne kuma har kike tunanen hakan ?
Kaina girgiza tare da dan dago kai ina fadin abinne ba dadi sister nan dai na labarta mata duk abinda ya faru dani a weekend din .
Dan guntun murmushi tayi tare da fadin matsalanki sai kinga native doctor din mu na gargajiya suke da herbal medicine dake kawo karshen wanan case din nasu da sauri harma a manta mutum yayi shi a baya indan an dace.
Amma yana da mata kai da zakubi don kada maganin ya baci amma nasan idan kinga kakata akwai yadda za ayi don wani dan uwan mu ya taba fadawa irin case din nan a baya yanzu kuma ya daina ko cigari baya kaunan gani balle giya.
Case din homosexual kuma sai dai idan kinje don na bata labarin ki tunkan kizo tana dakon ki a ko wani lokaci don ta tausaya maki sosai kan hakan.
Nagode maya da kullawan ki a kaina zanyi kokari na samu time da zamu tafi kauyen tare dake amma sai idan na shiryawa hakan zan fada maki.
Haka muka rabu na dawo gida da wanan maganan a raina ba abokin shawara fadila na kira da dare bayan mun gaisa na kwashe yadda mukayi da maya din na fada mata.
Saida ta nisa kafin tace zainab wanan damane sosai Allah ya baki kan hakan sai dai gaskiya akwai matsala ga hakan baki ganin idan aka samu akasin hakan abin zai iya dawowa kan ki ?
Kindan fa yadda kike da uwar mijin nan naki don haka nake shawarta ki da kidai kara tunane akan hakan gaskiya.
Anty ta yaya zan fara tunkaran mami da wanan zancen ai saita dauka ni din watace data iya irin wanan abubuwan tun a gida kamar yadda takan fada min cewa .
Nida iyayyena mun iya shige shige muna kammale mutum da dan sa tun kan mu shigo birni wanan zancen ba zan taba mantawa dashi ba a raina don ido da ido tasha fada min hakan.
Idan na tuna yana min zafi sosai wanan kalman yanzu kuma in fito mata da wanan zancen ai sai tace hakan gaskiyane dama.
To yanzu ke wani shawara kika yanke ga hakan don gaskiya kada wanan daman ya wuce ki yanzu zainab .
Don idan kika baro kasan baki gwada sa,an ki ba daga baya hakan zai dameki sosai kuma kinga abin nasa sai gaba gaba yakeyi yanzu.
Na sauke ajiyan zuciya tare da fadin zan kara tunane in gani abinda zai yuyu zan kiraki in fada maki abinda zuciyana ya yanke min kan zancen.
Dan tsuki nayi don wanan shawaran da fadila ta bani din din kamar ta famamin wani miki dake zuciyana ne lokacin.
Don sam ban kawo wanan tunanen ba da farko sai yanzu da ta fito min da zancen fadawa mami din nake tunanen hakan.
Kawai banda mafita saina share zancen a zuciyana naci gaba da abindake gaba na.
Kowa sai harkan gaban shi yakeyi don ba ganin shi nakeyi ba shima baya ganina sai idan zamu gaisa da safe bayan hakan sai kuma wata safiyan kuma idan yayi zamu gaisa.
Ranan ba school don haka na fito don nasha iska saman benen part din mu ina zaune a gurin wanda ba kowa ne zai sanda hakan ba.
Da takarda a hannuna wayana na gefe daya aje sai cup din drink's dana aje daga dayan gefen ina dan kurba kadan kadan.
Na dauki cup din drinks din na dan kurba kadan na aje kamar ance na dago kaina na kalli kasa sai na hango ya je suna fitowa da Taju daga cikin gidan.
Wani irin faduwa gabana yayi yaba da ras ras lokaci guda ban san lokacin dana mike tsaye ba ina mai furta innalillahi wa inna alaihim raju,un.
Allahuma Ajirni fi basibati wa,akalillif hairan min ha , .
Ina mai runtse idanuwa na kafin in bude in kara fadin La,illah ha illa anta subbahanaka inni kuntun minal zalumin har ban san lokacin da hannuna yakai saman cup din dana aje saman table din ba ya fado ya tarwatse a wurin.
Kai ya J ya dago daga inda yake tsaye yana kokarin shiga mota ya hangoni ina shigewa ciki hannuna yana dafe a bakina don kuka.
Sam shima baiji dadin hakan ba don bai kaunan in ganshi yana aikata wani aikin da bai dace ba shiyasa ma raba part din da akayi yanzu yai mashi dadi sosai don mun rage samun rikici dashi yanzu.
Motan ya fasa shiga ya juya zuwa cikin gida da sauri taju wanda ya riga ya shiga mota ya bishi da kallo kafin ya dago yana kallon saman benen part din mu baiga kowa ba.
Haka yasashi mamakin mai kuma ya mayar dashi cikin gidan a wanan lokacin bayan yasan inda zasu a yanzu yana da muhinmanci a garesu sosai.
Nikan ina shiga dakin na fada saman gado kife na fara rusa kuka mai tsuma zuciya naji an turo kofan da karfi an shigo dakin nawa.
Hakan baisa na dago don ganin wanda ya shigo min saima kamshin turaren shi mai mugun tashi daya ziyarci hancina a lokacin daya yasa na gane shine a dakin.
Zainab meke damun kine har zaki so halaka kanki da glass haka baki da hankaline kome ?
Ban dago ba sai kukan da nakeyi naji yaja wani irin uban tsuki yana tako zuwa inda nake kwance ina rusa kuka.
Jinayi kawai gaba daya ya ficikoni na kwanto a jikin shi lokaci guda nayi saurin kokarin jayewa ina fadi cikin muryan kuka.
Kada ka tabani don kai ba cikakken musulmi bane har abokan hurdan ka sun sanda hakan don sun fada a gaban ka suma.
Ni din ya nuna kamshi cikin mamaki yana kallona nace kai mana Allah ya kara min tsari da duk abinda kake nufi da daukoni dakayi zuwa wanan kasan na kafirai.
Idan har kana tunanen zaka iya juyani na koma kamar yadda kake fasiki ne Allah ba zai taba yarda kaga hakan ba a rayuwan ka, , ,
Wani irin mari yaso kaimun Allah ya taimakeni na kauce bai sameni ba na samu na kwace a jikin shi ina ja da baya baya.
Zainab ni kike kallon idona kina fada min haka ya fada kamar zaiyi kuka ba tsoro nace mene marabinka dasu yaya ?
Ai gara fasikin dake neman mata da kai yaya wanda ke fasadi da namiji dan uwan shi ta inda Allah mahalici mu ya hanemuyi koda matayen kuna aurene kuwa.
Amma kai don rashin tsoron Allah da karancin addini dake yawo akanka shine ka mayar abin tunkaho a gurin ka kamar ba zaka mutu ka koma ga mahalicin ka ba saboda rudin duniya dake damun ka.
Ya kara kaimu cafka a hasale na kara ja baya har na samu na sauka daga saman gadon muka fara zagayan dakin muna fadawa juna bakaken maganganu.
Ranan kan yayi mamakina matuka don idan wani ya bashi labarin hakan zai iya karyatawa don ban raga mai komai ba ban kuma ji tsoron shi ba.
Karshe nace dashi zan bugawa mami waya tazo ta daukeni don duk abinda ya sameni kaine na kuma riga da na fadawa iyayyena hakan da yan uwanka .
Don nasan gab kake daka kasheni a kasan nan don kawai kana ganin ina takura maka kan harkan ka.
Ido waje yake kallona yana nunani da yatsan shi yana kallona ido waje ya iya furta zainab ashe dama haka kike baki da hankali da wayau.
Ina maki komai da kike so ban ga na rageki da komai ba don kema ki amfana daga gareni tunda nasan kinyi hakkuri da ba kowa zai iya irin sa ba.
Ka daina idan ma kana mun ne don yaudara don ni na dade dagane manufan ka a hakan don ka auroni ne nan don ka kawar da idon mutane akanka ace duk zargin da ake fada akanka karyane tunda kana da mata tare dakai ko ?
Saida ya kalloni yace cikin girgiza kai tabbas hakane wanda ya fada maki hakan baiyi karya ba zainab .
Haka dinne ba wai ba amma sai na dauka zaben ki danayi ga hakan kamar ke din mai rufamin asirine ga wanan kaddaran da kowa ke gudu akansa .
Saidai ashe banyi tunane ba don ashe duk mata kalan ku daya da tsohuwa da babba duk daya kuke a wurin tunanen ku.
Ke kanki idan kinsan kanki ai abun kunyane ace mijin da kike aure yana hakan don ko ke bazaki tsira a bakunan mutanen da suka sanda hakan ba.
Kowa yasan tursasani kayi ka aureni don ko hjy da ace tasan hakan da farko bazata taba mara maka baya in zauna dakai ba zaman da baida amfani a garemu sai tarin zunubi ga Allah.
Ya sake girgiza kai ya kalleni zuwa lokacin idanuwann sun kade sunyi ja jajir niko ina tsaye daga kofa ina jiran naga yayo kaina in gudu.
Don a tsorace nake sosai dashi lokacin kiris ya rage na ruga da gudu da naga ya haruni din.
Shiru yayi ya koma ya zauna yana tunane sam ya manta da zancen wani taju na jiranshi a waje sai can ya dago ya kalleni yana fadin .
Babu wanda ya taba mi cin fuska irin wanan a gabana zainab yauni kike kira da kazami fasiki ido da ido.
Yo idan ba kazami kake ba me kake fada min sunan ka wanda ke wasa da gidan najasan da yafi ko ina wari a jikin mutum kaga aiko ka bata sosai wallahi kuma da kato namiji dan uwan ka fa.
Kina son ayi da kene din in gwada tir tir wallahi dakai ya jafar ka kuna baka tsoron kauri saidai irin ku karshen ku baya kyau don kun kama talala da yawa a duniya.


ZAINAB IDRIS MAKAWAFATAN ALHERI GAREKU MAKARANTA WANAN NOVEL TARE DA FATAN SAKON DAKE CIKI NA ISA GAREKU YADDA YA KAMATA ALLAH YA TSARE MUNA ZURI,A AMIN.
LITTAFIN KUDINE DON ALLAH KI BIYA KAFIN KI KARANTA DON SAUKE NAUYI DA FATAN ZAKI FAHINCENI YAR UWA, , , ,

Fitan da basuyi ba ke nan ranan don zuwa wurin likitan su ya duba taju dake fama da lalura kwana biyu ke nan na wani katon kurji a duburan shi few days ke nan yana fama da wanan cutar.
Akwai wani magani da likitan su na musaman yake basu idan sun samu irin wanan matsalan bayan kwana biyu sai abin ya bace wurin ya koma normal.
Shine zai kaishi wurin likitan ya dubashi ya bashi yan taimakon da ake basu don kariya saboda shi taju kamar shine mace a wurin J din shi kuma ya J din yana zaman namiji a garesu haka yake wanan rayuwan kazantar dasu shekara da shekaru.
Wanda idan baiyi hakan ba da maza yan uwan shi ba baya jin dadin rayuwan shi sam .
Zai iya rantsewa bai taba jin sha,awan wata ya mace ba a rayuwan shi da sunan taraiya sai dai ya kalli ya mace da abokiyar shawara ko wani abu.
Haka yaso rayuwan shi ya kasance da zainab din don shi Allah yasa mai tausayin diya mace a rayuwan shi don hakane itama zainab din yake matukar tausaya mata sosai ga duk wani lamari nata.
Saidai kash bai samu zainab din maiyin biyayya a yadda yaso ta kasance mai saidai ya fahinci yarinyar addini ya ratsa zuciyar ta sosai irin masu ra,ayin rikau din nan ne da kudi baya rudasu ko wani abin.
Yanzu ma kalaman ta ya rudashi don yana son ta kwantar da hankalinta ta zauna suyi magana na fahinta don baison abinda zai kara tayarwa mahaifiyar su da hankali.
Shiyasa yake son ya bata lokaci ta sauko sunyi magana na tsanake yadda zata fahince shi ta dan jaye wanan furicin nata na fada a gida da tace tayi din don kafa shedan hakan din garesu.
Nan ya zauna shiru kanshi na duke a kasa ni kuma ina tsaye a firgice kofan dakin ina jiran tsamani.
Har na kai tsugune daga kofan na hade kaina da gwiwa na ina rusan kuka a tsanake cikin tashin hankali bamai sauti ba sosai.
Don hakane banji tasowan shi ba zuwa inda nake din sai jin shi nayi ya dafa min kafada na cikin murya mai taushi yake fadin zainab.
Kiwa Allah ki daina wanan kukan haka don Allah ke wai kuka baya isan kine ni dake cikin wanan jerabawan yanzu nace me idan ke kina kuka haka ?
Kada ki manta a gaban idon ki fa mami ta bar kasan nan tana fushi dani cikin bacin rai ta barmu fa ?
Amma kina ganin na kasa daina wanan abin da kuke ganin laifina a kanshi don sabo zainab ya kamata yanzu kifi kowa fahintar matsalana ai zainab.
Keda zaki zauna dani muyi shawaran mafita kan fushin da mami keyi dani shine kuma zaki kara hadani da ita kuma a yanzu.
Kaina na dago a cikin mamaki nace nice kuma zan hadaka da mami naku bai hadaku ba a yanzu.
Indon tanice kayi hakkuri don Allah ka taimakeni ka mayar damu gida yaya kada nima wanan abin ya shafeni don Allah ai muna dauka daya dakai.
Wani kallo yai min kafin ya hade yawu masu daci a bakin shi yana fadin cikin karfin hali don me za ai muna dauka daya dake kuma ?
Duk yana daurewa ne yaga hankalina ya kwanta kawai yasa shi tsayawa rarashina din da yakeyi a yanzu.
Wanan mutumin nefa ya kara dawowa gidan nan mutumin da tun ban sanshi ba nake ganun shi a mafarkina har yakai na waye dashi a idona.
Da irin barazanan son daukan raina da yake yaya don Allah ka tausaya min tunda har abin yakai mutanen naka yanzu raina suke nema kuma ka sani.
Yaya ka duba irin wullakacin da arnen nan yayi min a wuri dakaje damu ranan a gaban bainar jama,a .
Idan ba Allah ya gyara ba yaya me kasan zai faru a wurin damu wurin mashaya fa ka kaimu tsundun masu aikata masha,a da alfasha a bainan jama, a .
Har yai muna sauka daya da sauran matan dake wuri wanda har yau duk na rufe idona ina ganin wanan bakar ranan yana min gizo kamar yanzu ne yake kokarin rungumana.
Isanuwan shi ya runtse don jin zafin abin shima a cikin wani tsawa tare da daga hannu yake fadin enough zainab bana son kina tuno min da wanan abin don Allah.
Komai lalacewa na aiba zan taba son inga wani ya wullakata ku ba koda kuwa bana kusa daku zan dage sai inda karfina ya kare.
Kamata yayi ace kin tayani addu,a ba irin wanan masifan da kike mun ba koda yaushe instead ki jawoni a jiki sai bakar magana kike fada min ko yaushe.
Kina tunanen wanan halin da kikeyi yanzu shine zai sa nabar duk wani abinda nakeyi din.
Na dauka kurciyane ke sakaki hakan baki gane ni din mai so kine da gaskiya bawai don manufan da kike tunane ina dashi ba a kanki.
Nasan da farko bana aureki bane don so ko kauna amma a yadda iyayyen ki suka banke a cikin mutunci da girmamawa hakan yasa min kaunar ku na gaskiya a raina daga ke har kanwarki sadiya.
Jin abinda ya fada yasa ni sake hawaye wani na bin wani na kasa fadan komai a lokacin kinsan mace da raunin zuciya lokaci guda .
A take zancen shi ya kashe min zuciya na nadan dago kai na kalleshi shima kai ya gyada min alaman eh abinda ya fada har zuciyar shi ya fada min shi.
Na dukar da kai kasa sai ruwan hawaye nakeyi ya ciro hankaci daga cikin aljihun rigan shi ya miko min ban karba ba haka yasa ya fara goge min fuska da kanshi.
Kitayani addu,a na daina duk wani sabon Allah danakeyi yafi mun wanan yawan kukan da kikeyi a yanzu.
Duk wani addu,an da zan ma idan kayi da kanka Allah zaifi karba maka amma sai idan zuciyar ka da gangan jikin ka suna da tsarki Allah zai karbama addu,an ka tare dana mahaifiyar ka.
Yanzu ki tashi ki koma saman gado ki dan kwanta ko zaki samu barci natsuwa yazo maki tunda naga kin tsorata da ganin taju gidan nan tare dani.
Banyi magana ba na mike da zumar fita yake fadin ina kuma zaki haka falo zan koma in kwanta na basa amsa.
No kada ki fita haka ki tayarwa kanwaki da hankali don Allah ki zauna a nan nima ba inda zan tafi ai na fasa fitan yau.
Ance mutum rana gareshi sai gashi kan wanan dalilin mun wuni a dakin dashi duk da ba hira mukeyi ba kowa da abinda keci masa zuciya.
Dan gara shima yana kallon wayan shi lokaci lokaci yana shiga ciki nikan tunda na bashi baya ban juyo ba ina faman tunanen zuci.
Ranan taju kan ai mutuwa ne baiyi ba don ya gaji da jira har ya fito daga cikin motan lokaci lokaci yake kallon agogon hannun shi.
Ya dago ya kallo kofan gidan shiru baiga fitowan shi ba haka yasa shi yanke shawaran binsa ciki yaga halin da yake ciki din.
Nan ma ya samu part din a rufe kamar yadda ya rufe kafin su fito ga kuma ciwon nasa yana damun sa ranan sosai da zafi haka ya daure ya fita waje yana mai cizon yatsa don yasan yana wurina ke nan .
Ji yayi kamar ya bishi can part din namu sai dai yasan abinda zai iya fitowa bayan hakan saboda yasan irin alkawarin da yasha a kaina na, don kafin J din ya yarda ya dawo alaka dashi saida yai mai warning sosai a kaina kuma ya yarda zai kiyaye din.
Shine tunanen da yayi yasa bai nufi can part din mu da yake zaton J din na ciki ba a lokacin saidai daga inda yake zaune cikin furani yana dago kanshi lokaci lokaci yana kallon part din namu a fakaice.
Sallah da akayi naga baida niyar tashi yasa nayi magana dashi zaman shi a dakin nawa kamar an kafeshi dole a wurin .
Nake fadin azahar yayi fa tun dazun yaya lokacin yana dakilan wayan shi babu kakautawa ban san dai da wanda yake charting ba a wayan.
Dan kalloni yayi yana fadin OK kafin ya mike na zata fita zaiyi sai naga ya nufi hanyar ban dakina da nufin kewayawa a can don dauro alwala.
Da mamaki nabishi da kallo har ya shige don zan iya rantsewa da cewa tun zuwan mu gidan nan bai fi uku ko biyu ba daya taba shiga dakin kwanana a wanan gidan.
Sai gashi ya gane ina bandakina yake a dakin koda yake hakan ba abin mamaki bane don ginan mu da nasa iri dayane a gidan sai dan bambanci kadan daba a rasa ba kila.
Yana shiga yabi ban dakin da kallo yadda yake gyare tsab sai kamshi yakeyi haka ya sa ya sake jiki ya dauro alwalan shi ya fito ina zaune yace kiyi alwala muyi sallah yanzu.
Da dan mamaki na kalle shi don jin abinda ya fada a zuciya nace kadaiyi kai kadai wa zanbi sallah haka kana mashayi mai luwadi kuma ?
Yadda ya tsareni da ido yasa na mike na shiga da kyamkyami bandakin na dauro alwala nasame shi zaune bakin gado yana jiran fitowana.
Nayi mamakin jin yadda yake karatun sallah a tsanake yana bada hakkin ko wani aya yadda ya dace sai abin ya tsaya min a rai.
Nake mamaki har a fili mutum ya san kur,ani haka yake sakaci da daman shi ga wani can shi kimtsatsene a rayuwan shi amma Allah bai bashi ikon haddace alkur,ani maigirma ba a rayuwan shi.
Idarwan mu yayi daidai da rurin da wayana yakeyi ban dauka ba don adduan da nakeyi lokacin har kiran ya katse na farko.
Wani kira ya sake shigo min na dauka sunan maya na gani tana kirana ashe na dauka gaisuwa muka fara take fada min ai suna asibiti da mahaifiyar ta tun ranan Friday amma kila yau za a sallamesu.
Sannu nayi mata tare da tausayawa a yadda ta dan ban labarin rashin lafiyan mahaifiyar nata a wayan.
Duk yana jin mu tunda a kusa muke da juna lokacin har na kashe wayan na mike ina nade abin sallah don bana barin shi a wurin duk da ni kadaice a dakin nake amfani dashi.
Kawo mun abinci naci ya fada na sake kallon shi ina mamakin sauyin shi na dan lokaci guda tare da rashin fahintar shi kan hakan.
Ban taba shigo da abinci a part dina ba amma ranan sanadin shi saida ya saka na shigo dashi tare da kira mai sadiya muka zauna akaci tare , duk da ni a tsarge nake a cikin su don ban fahinci sallon yaudaran daya bullo min dashi din ba na zama min a daki yau.
Kiran dayan wayan da akayine yasa shi barin dakin ya fita yana waya sai lokacin sadiya ke fadin yau kan yaya ya bamu lokacin shi a gidan nan sosai .
Sau biyu ina lekowa zan shigo dakin nan sai na samu yana dakin a zaune na koma nace akwai dalilin zaman shi dakin ai tunda kika ganshi zaune yau.
Bansan ya suka kare da taju ba daya fita don dai ban kara ganin shi ba sai kashe gari da muka hadu zai fita office nima mun fito da shirin makaranta zamu fita.
Muka gaisa ya wuce muma muka fito na sauke Sadiya a nasu school din kafin in karasa makaranta.
Naso makara don traffic da ya tsayar damu saidai tunda na doso wurin maya bata a sit din mu na tuna da wayan mu na jiya da ita da take fada min zancen rashin lafiyan mahaifiyar ta.
Har aka tashi ban sake jikina ba saida na idar da sallah na kira maya din naji jikin maman ta?
Nan take fada min ai basu bar asibitin ba suna nan nake cewa gani zuwa insha Allahu ban tsaya school din ba na shiga mota na bar cikin school din .
Na fara zuwa don in dauko sadiya a can na dan bata lokaci wurin jiran sadiya din har muka samu an sallami su Maya daga asibitin sai banji dadin hakan ba sam.
Shiyasa washe gari na roki yaya ya barni na je kauyen na gaida maman nata don mutuncin dake tsakanina da ita.
Baiso barin mu ba don ya soma fada yana fadin meye nawana zuwa wani kauyen su na dan kara marairaicewa ina fadin.
Kayi hakuri yaya don mutuncin dake tsakanina da ita ba dadewa zamuyi ba idan munje na dago kai ina kallon shi sai cin abincin shi yake kamar bada shi nakeyi magana ba.
Idon dana zuba maine yasa shi dago kai ya dan kalleni yaci gaba da breakfast din shi a gurguje sai can ya dauko waya ya kira wani layi sukai magana.
Nan na fahinci driver ne zai kaimu kauyen da iyayyen mayan suke zaune din sai can ya dago yana fadin ki shirya wanda yasan wurin zai kaiku kada ku dade idan kunje banson kuna nisa da garin nan ba tare dani ba.
Insha Allahu zan kulla da kan mu har mu dawo lafiya na fada ya mike mukai mai a dawo lafiya bai amsa ba ya fita da tafiyan shi mai kama da sauri ko yaushe.
Tun fitan shi na fara shiri tare da tanadar dan abinda zamu kai masu a kauyen idan mun je.
Driver yazo muka dauki hanya ikon Allah ban taba zaton akwai masu talauci irin hakaba a wanan kasan .
Sai gashi naga abinda ban taba zato ba idona na ganan min irin yadda tallakawan su ke cikin wahala da yunwa.
Dama maya tana fada min irin yadda suke rayuwa don su basu yarda sa zamani ba sai gargajiya suka rike yasa basu faye samun cigaba a rayuwan su din.
Da wayan da mukeyi da maya har muka iso dan kauyen nasu wanda gidan su yake da dan nisa daga titin kauyen don suna cikin duwatsune su .
Maya tayi murnan ganin mu sosai don bata zaci hakan ba ta dauka kawai ina fully din tane b zuwa zanyi don duba mahaifiyar nata ba.
Mun shiga dan karamin gidan nasu mai ginan al,ajabi a wurin mu har dakin da mahaifiyar nata take kwance.
Mun dade a dakin kafin mu fito dan karamin falon su maya din mu zauna muna hira take fadin ai yakamata naje mu gaisa da kakannin ta da suka haifi mahaifiyar ta wace take bani labarin ta koda yaushe.
Dole na mike don mu taka zuwa gidan yaran suka fito suna kallon mu kamae dai yadda yaran kauye sukeyi idan sunga bako.
Dan gidane wanda bai kai wancen kyau ba da yan tsufin biyu suke rayuwa a cikin sa saidai akwai bambamci sosai dana su maya da muka baro a baya.
Tsohuwace sosai matar yadda maya ke ban labari sun dade kafin su samu mahaifiyar ta itama haka kafin a haifeta an dauki lokaci mai tsawo da auren mahaifan ta din.
Dalilin hakane wuri;yawon neman mahaifiyar maya din kakanin nata suka zama masu bada magani don shige shigen da sukeyi a dajin su don neman maganin haihuwa suka koyi wanan sana,an.
Tsohuwan nada kirki sosai bayan dan bayanin da maya tayi mata da yare game dani sai take min sannu da zuwa wurin hada hannayen ta biyu hakan yasa na gane me take nufi da hakan da takeyi din.
A duduke ta tashi ta dauko wani ganyen magani fresh ta fara dakawa a gabana kafin ta tace ta mikowa maya ta bani insha.
Saida nayi bissmillah na karbi ruwan ganyen na kurba baida bauri ko daci saidai kamshin itaciya da yakeyi na kurbe na mika mata cup din ina mata godiya da kai irin na kurame.
Dan murmushi ta sake a fuskan ta na tsufa kafin maya ta dauko wani zance sunayi sai ga fuskan tsohuwar ya sauya daga fara,an da takeyi lokaci guda.
Yaren su sukeyi kafin maya din ta juyo gareni tana fadin tshohuwar tace idan ina son zata taimaka min don ta yaba da hankalina sosai.
Na gyada kai alaman eh ba tare da wani tunane ba sai ga shi tsohuwan ta mike a duduke zuwa wani dan karamin kabat dake falon tsoho tana tono wani abu a cikin tarkacen ta cikin wani jakkar fata ta ciro abin.
Ta dawo ta zauna ta kalli maya ta fara mata bayani itama tana min da turanci ina fahintar ta dan abin bai kai wani abuba don dan garin maganine .
Sai wani abu kamar sayen ice yana wani kamshi tana bayani tare da nuna yadda zanyi yayin da niko gabana sai faduwa yakeyi don tsoro da fargaba.
Yadda tsohuwar ke bayani zaka gane wuth full confidence take akan abinda ta bani din nasa hannu bibiyu na karba da take miko mi gwiwa har kasa da alaman taji dadin hakan danayi sosai.
Dan kudin dana bata da zamu tafine yasa tsohuwar ta rungumeni a jikin ta tana dan taba bayana a hankali mukai mata sallama muka fito.
A hanyar komawa gidan su maya inda sadiya da driver suke jiran dawowana mu tafine take kara min bayanin akan maganin don bata fadi ainihin aikin da zaiyi ba a lokacin tadai ce nayi mai amfani dashi yasha ko sau dayane zanga amfanin shi.
Tare da fadin zan iya yiwa wani amfani dashi ma nan gaba idan naga yana cikin matsala irin na yaya din zan iya yi mai amfani dashi.
Maya ta matsa da nanata min kan inyi amfani dashi ko za a dace muka kara sallama da mahaufiyarta muka tafi.
Har muka zo gida ina faman tunane abu biyu na farko yanayin rayuwan su maya din a kauye sai kuma wanan maganin da tsohuwan ta bani yanzu yana a ciikin jakkar hannuna.
Mun dawo a gajiye na wurgar da jakkan saman gado ban daki na shiga don dauro alwala har wanka nayi don ban san a inda na zauna ba a gidan su maya din su basu sallah.


ZAINAB IDRIS MAKAWALITTAFIN NAN NA KUDINE DON ALLAH KI BIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA YAR UWA MU GUJI ABINDA ZAI KAIMU GA FADAWA HAKKIN WANI, , , , ,


Kwana biyu ina faman tunane a raina na yadda zan samu daman bashi wanan abin ya sha na rasa dabara yin hakan sai tunane nake a raina.
Kai karshe dai na barzancen har na fara mantawa da wani zancen magani can a kanshi don nazo nayi tunane uwarshi ma da ta haifeshi ta barshi a haka balle ni.
Iyaka dai na samu hanyar tsirewa daga gareshi da zaran na gama karatuna shike nan na fita wanan sarkekeniyar na auren shi ai.
Na sani sarai bai daina halin nan ba don babu abinda ya fasa daga cikin halaiyar nasa shiyasa na yiwa kaina alkawarin ko a gabana yake mugayen halinsa iyaka na ido sai kuma addua ga musulmi da zanyi tsakanina dashi.
Ashe abin ba haka bane idan ance miji abin yafi da nan duk da auren namu na wasan tamola ne ba kamar sauran auren da aka sani bane da farko.
Matsalan abin banda abokin shawara a rayuwana ga zurfin ciki dake damuna ko banza balle wanan din da ban yarda kowa yaji wanan zancen a gurina ba .
Ko abu yana damuna haka zai tsaya min a rai har lokacin da Allah zai gusar min da tunanena na manta da zancen ga baki daya .
Don ina da saurin mantuwa a rayuwana ban faye rike abu a raina na tsawon lokaci ba bai fita mun a raiba.
A bangaren mami kuma mu dai dan gaisawa yanzu a kai akai akala sau uku da ko sau biyu a sati zata kirani ta tambayeni muna lafiya dai ko ?
Idan na bata amsa zata sake tambayana yaya mijin naki zainab saidai nayi murmushi bazan bata amsa ba akan komai.
Zakaji tace kiyi hakkuri insha Allahu komai zai dawo daidai insha Allahu tare da kara kwantar min da hankalina.
Saidai duk yadda na iya daure da hakkuri saida yaya ya kaini kull har ya kawo muna matsala don yanzu kan kamar kara masa iskanci akeyi don dawowan taju gidan ya kara maidashi ruwa sosai.
Don yasan na sani yanzu ba zancen boyo a tsakanin mu a fili yake abinsa don ba mai kwaba masa yake gani.
Ranan na dawo school da wuri daga makaranta don haka kawai nake jin ba dadi a jikina muna fitowa darasin farko na shigo mutana na dawo gida don in dan kwanta.
Saboda ina jin kamar barcine ke damuna ko zazzabi ke son kamani a irin hakan kawai na yanke shawara in dawo gida.
Nayi mamakin ganin falon a bude don ban tsanmanin dawowan yaya gida a wanan lokacin daya dace ace yana wurin aikin sa.
Haka na bude falon cikin karfin hali na shiga har na rufo kofan na shigo kai tsaye tsakan falon na samesu kamar wasu karnuka suna romace a tsakanin su kamar wani miji da mata ko saurayi da budurwa.
Inna lillahi na fada da karfi ina sake yar hand bag dina dana sako tarkacena a cikkn sa.
Salatin danayi ne ya dawo dasu hankalinsu suka mike lokaci daya tare da sakin junan su ga maballan rigansu duk sun balle sun shagala da hakan.
Tashin hankali iya tashin hankali na shigeshi a ranan yadda gaba daya idona ya rufe na ke fadin stupid, idiot noses mazinata fasikai ku fice min a falo kafin na tona maku asiri a nan.
Ido rufe kamar gidana suke sheke ayan su din a ciki don yadda idona ya rufe da ganin su baro baro danayi a lokacin.
Wani kallon tsana taju din yai min don yadda yaga abokin fasadin nasa yayi laushi sosai yana fadin wai meye haka me ya dawo dake gida wanan lokacin ana karatu.
Ban iya magana ba don duhun da idona ya fara yi mun a lokacin na kara fadin ku fice min nan nace kada fushin ku ya shafeni a wurin Allah.
Ke ki natsu ki san abinda kike fadi mana da irin wanan kalaman naki ya mike da kyar yana mai gyara rigansa yake wanan maganan tare da nufo inda nake tsaye.
Na fara ja da dan baya kadan bai daina nufo inda nake ja da baya din ba naci karo da wani abu a bayana na fadi kafin in kai kasa na some don tsoro a wurin.
Da sauri ya karaso ya tareni na fada a jikin shi sai lokacin yaga ai a some nake ma ashe ya fara kiran sunana da karfi yana jijigani ban farfado ba.
Yasa ya juya inda taju din yake cikin daka tsawa dauko min ruwan sanyi a fridge mana da sauri baka ganin ta somane.
Haka taju din ya nufi kitchen da sauri ya dauko goran ruwan da har ya fara kankara ya kawo mashi bai tsaya kulawa ba kawai ya watsa min a jikina .
Na sauke wani ajiyan zuciya tare da dan bude idona kafin na mayar na rufe na kara sakewa lokaci guda kuma.
Ya subbanallah ya fada tare da dan jijigani yana kiran sunana a hankali kuma a rude ka barta zata farfado ai tunda ta falka taju ya fada.
Shout,up ya fada da karfi duk waya jawo hakan yanzu saida na fada ma ka bari zan dawo don jaraba ka manne min saida hakan ya faru.
Na fada ma yarinyar nan yar gargajiyace da rikon addini kayi duk wani taka tsatsan dasu don komai yanzu a cikin tako nakeyin shi don su.
Taju din yace I am sorry boss ban san zata dawo yanzu bane ni kuma ina son jinka a jikina wanan lokacin.
Yace yasa kayi min karyan baka da lafiya na bar aikina zuwa gida yanzu ga abinda ka jawo min yanzu wanan abu baka san iya inda zai tsaya ba .
Duk zancen da sukeyi ina jin su don na fara farfadowa lokacin zancen su yana shiga kunnena bandai bude idona kawai bane don ban son ganin su sam a rayuwa na.
Ji kawai nayi ya cicibene zuwa sama bai ajeni ba sai saman gadona ya shifideni ya juya wurin AC ya kunna tare da sake volume din AC din.
Ya dawo inda nakw yana dan murza min goshi tare da kiran sunana a hankali da zainab kina jina don Allah ki kwantar da hankalin ki mana ki natsu.
Don Allah ka fita yaya bana son ganin ka a rayuwana kai din shedan ya gama ma fitsari a zuciyar ka bama iya kanka ba.
Yaya a gidan ka ?
Gidan da iyalin ka suke zaune anan kake shimfida fasadi irin wanan kamar kai din ba musulmi ba haihuwan musulmai ?
Enough zainab ya isheki kin dai san koni waye don haka ki kyaleni yadda kika ganni a haka na fada maki.
Wayo ni Allah na na shiga ukku na lalace a rayuwana.
Ni zainab naga ta kaina ya Allah na tuba ka yafe min da wanan jerabawan dakake jarabbata na dashi idan laifi nayi ma ka jefoni a wanan rayuwan.
Tsuki yayi ya mike bai tsaya ba ya rufo kofan da karfi ya fice na kara kurma ihu kamar an tsikareni kuma na mike tsaye ina saukowa daga saman gadon.
Dan jakkana na dauko na nufi kofan fita nima da sauri sai dai ina zuwa bakin get din security din kofan ya rufo kofan da sauri yana min wani yare da ban sani ba.
Duk yadda naso fita daga gidan sun hana hakan dolw na koma cikin gidan rai bace ina hawaye.
Tashin hankali ranan na shige shi ga tunane kala kala da nakeyi a zuciyana sai can Sadiya ta fado min a rai don lokacin dawowan ta da yayi har ya wuce yasa na kara mikewa tsaye na nufi hanyar waje .
Ban kai ga fita daga falon ba sai ga sadiya din ta fito daga dakin tana fadin .
Yau yayan mu kin barni ina jiran ki saida ya jafar ya turo aka dauko ni a makaranta ya din yace driver ya fada min kina gida baki da lafiya wai .
Hannu na warewa sadiyan tare da fadin yar kanwata zo gareni don Allah ki rungumeni ko zanji dadi a rayuwana kada in mutu.
Da sauri ta karaso ta rugumeni din tare da fadin yayan mu meke damun ki baki da lafiyane ko wani abu ya sameki.
Saidana runtse idona ina jin dadin dumin ta a jikina kafin ince da ita ya jafar daine yake son kasheni Sadiya.
Kai ta dago tana zare jikinta daga nawa tana fadi a razane zai kasheki yayan mu me kikai masa nace nima ban sani ba Sadiya ya daice zai kasheni yau a garin nan.
Daga haka naja hannunta zuwa saman kujera wayan dake hannuna na fara neman lamban mami ina kiranta.
Kira biyu saiga mami ta daga wayan murya a raunane nake fadin mami na shiga uku yau a garin nan wallahi.
A rude mami ke fadin meya faru zainab ina jafar din yake ko wani abu ya sameshi take tambaya a rude.
Mami ba abinda ya sameshi kawai dai na kamshine yana abinda ba daidai shine yai min dukan tsiya ya ce zai kasheni ba zai barni da raiba tunda na saka mai ido da yawa.
Innalillahi shi jafar din baibar wanan dabi,an bane zainab ko kwayance ta fara tabashi yanzu har yake furta hakan ?
Sai kawai naji ta fashe da kuka nima kukan nakeyi na daukan hankali ina tausayawa kaina kan wanan rayuwan dana samu kaina a ciki.
Yayan mu mu gudu mana idan yaya a zama mugu kada ya dawo ya kashe ki din a gidan nan sadiya ta fada a tsorace don taji wayan mu da mami din.
Ni kuma na fadi hakan ne don labarin da Maya ta bani daya taba faruwa da wata inda take cewa zasu iya kashe mutum idan ya faye saka masu ido basu da yadda zasuyi dashi .
Sai kawai su kashe mutum su huta kuma ba ai masu komai idan an kwana biyu kigansu a gari suna yawon su.
Do suna da daurin gindi sosai a wurin manyan gwaunati da sauran jami,ai don haka ba ai masu komai ko an kamasu.
Jin hakan yasa nake tsoron hakan don nasan shima yaya din dole yana da wanan halin data fada min don bai rasa daurin gindi yadda naga yana shanawa a kasan son ransa.
Wanan dalilin yasa na fadawa mahaifiyar nasa haka don riga kafi a yadda na ganesa yau din kafin ya fita don zai iya aikata min komai tunda na gansa din yau ido da ido.
Sai gashi a rude ya dawo gidan tun kan ya hawo sama yake kwala min kira ina zaune sama ina jin yadda yake kwala min kiran a gigice muna tare da sadiya a dakina na tashi na rufe kofan da sauri a tsorace.
Don nasan sunyi waya da mami ke nan akan wayan da mukayi da ita dazun kan wanan zancen yasa ya dawo a hasale yake min wanan kiran na tashin hankali.
Muna jin lokacin da yakw dukan kofan a haukace muka rike junan mu a dakin a tsorace kamar zai shigo muna dakin ne, bayan a rufe dakin yake.
Har ya gaji da haukan sa ya tafi kilama dama a buge yake zo ya sauke haushi a kaina waya sanar mashi mudai muna ciki lokacin.
Haka muka kwana tsorace rai kuma bace damu don ko sadiya da take karama a tsorace ta kwana makake dani ranan.
Tunda safe na sake kiran manmi duk da nasan a lokacin sauran darene a can Nigeria ina kuka na tayar mata da hankali akan ta saka baki ya turo mu zuwa gida don na gama zama dashi ni.
Mami hankali tashe ta tayar da ya mamud tana fada mai abindake faruwa a waya duk da ban fito fili na fada masu gaskiyan maganan ba amma hankalinta yayi matukar tashi a lokacin.
Wanan wayan ne ya tayarwa kowa hankali tunda safe sai kiran shi akeyi aka daga mai hankali don mami ta fada mai har in ya yarda ya turoni nageria a haka asirin su ya gama tonuwa ke nan a kasan nan.
Tayi rantsuwa duk abinda ya sameni wallahi sai tayi sanadin da za a kashe shi shima kafin ya bata mata sunan zuria a duniya.
Yabi wayan da kallon mamaki bayan sun gama waya da mami yana mamakin yadda a shekaru na iya jefashi cikin wanan rikicin haka.
Don kalaman mami sunyi tsauri sosai a gareshi hankalin shi ya tashi sosai gashi ranan ya kori taju bai kwana dashi a dakin ba.
Don yana ganin duk shine ya jawo mashi wanan fitinan daya faru yana zaman shi a office din shi tajun ya daga mai hankali.
Yayin da shi kuma tajun ya kwana yana neman mafitan hanyan da zai ga ya raba tsakanina da jafar din gaba daya don tun haduwan mu da jafar din gaba daya komai ya jagule masa ba yadda abubuwa suke tafiya masu ba a baya.
Don yanzu jafar din ya canza kamar bashi bane mai yawan sha,awa a kansa a baya yanzu bai faye damuwa da hakan ba sai yaga dama tunda har yana iya koran sa a yanzu.
Shiyasa ya zama mai dole ya dauki mataki a kan zainab din da yakewa kallon karaman yarinya da farko sai fashi yarinya nason rabashi da farin cikin ga baki daya.
Matakin daya yanke a ransa shine yayi min silent kill ba tare da wani ya gane hakan ba har jafar amma ta yaya zaiyi hakan ba, a fahince shi ba.
Don idan ba raba yarinyar nan yayi da duniyan ga baki daya ba wanan karin kan yasan ba zai taba samun kan jafar din ba kuma.
Da ire iren wanan mafarkin ya kwana a ranshi har safe bai kai ga mafita ba yana falkawa wayan shi ya jawo yana neman layin jafar din saidai wayan yawan busy yayi yawa a ranan.
Shiko jafar daya gaji da tunane mikewa yayi ya shiga bandaki ya watsa ruwa tare da dauro alwala yazo ya tayar da sallah kafin ya fara samun natsuwa na zuwa mashi lokaci guda.
Saida ya shrya tsaf kafin ya fito part din namu ya nufa kai tsaye ya samu dakin har lokacin yana rufe bamu bude ba.
Mami ya kira itace ta sakamu mu bude kofan ya shigo don sadiyace ta bude mai kofan ta rabe a gefe a tsorace har ya shigo dakin yana mata kallon mamaki.
Kafin ya dago ya kalli inda nake zaune rakube saman sallaya a wurin danayi sallah har lokacin ban daga ba ina zaune.
Sadiya ya kara kallo yana fadin jeki kiyi wanka ki shirya na saukeki school tace to a tsorace ta fice daki da sauri zuwa abinda ya umurce ta yi din tana waigena a tsorace.
Sai take ganin kafin ta dawo dakin ya gama halakani ga kuma tsoro da biyyaya yasa ta barni dashi a dakin ta fita.
A hankali ya tako zuwa inda nake a dakin ya zo gab dani ya tsunguna a gabana ya kura min ido na dan lokaci.
Kafin ya furta a hankali zainab a zatona ke yar uwatace da zata iya rufa min asiri a duk irin halin da muka tsunci kan mu a cikin sa.
Sai gashi ke din ce a yanzu ke neman hadani fada da mahaifiyata da yan uwana har kina ikirarin zan kashe ki in rabaki da rayuwan ki.
Ban kawo ki kasan nan don na tozarta ki ba cin zarafin ki sai kawai don wani bukatana na daban wanda a baya na zata zaki iya daurewa da irin rayuwana.
Ashe abin ba haka bane ke a wurin ki tunane bai barni na gane irin ra,ayin ki na rikau da kike dashi ba a lokacin.
Ban taba zaton hakan ba a wurun ki don na dauka ke din ma a dan uwa na jini kike dauka na kamar yadda yasa na zaboki kan tayin mami na aure a kaina.
Nayi zaton idan na biyo ta wanan hanyar komai zaizo min da sauki a rayuwana ashe abin ba haka yake ba kece ma zaki min fiye da abinda na guda a gurin wata.
Don ke din na kula abin duniya gaba daya baya gaban ki kin nausa a wata duniyan na daban.
Ban iya cutar da wani ba zainab balle na fara a kanki a yanzu don haka ina rokom ki da kibar kiran mahaifiyana akan rikicin mu don Allah.
Banda ra,ayin rabuwa dake ko nan gaba balle wanan yasa na mayar dake Nigeria kamar yadda kike so nayi maku.
Idan zaki kwantar da hankalinki wuri daya saura kiris ki karasa karatun ki idan naga hankalin ki ya kwanta na kaiki gida kiga iyayyen ki idan kuma haka zamuci gaba da zama zaki tabbata a kasan nan baki je gida ba din zuwan ki a haka illa ne garemu baki daya.
Da sauri na dago kai ido tab da hawaye don ban so ma ganin sa na kalleshi ina son yi magana kuka ya rinjayi zuciyana har bakina bai iya buduwa a lokacin.


ZAINAB IDRIS MAKAWALITTAFIN NAN NA KUDINE DON ALLAH KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA NA FITAR DA HAKKI NA FADA MAKI YAR UWA ALLAH YASA MU DACE DA RAHAMAN SA AMIN.


Maza mutanen mu da irin hikimarsu ta maza badan yaso ba sai dole don yanzu shima yana dana sanin kakabowa kanshi aure daya yarda yayi don kawai ya farautawa mamin shi rai.
A yanzu yana dana sanin yin haka dayan san duk mata daya suke a wurin hali da bai yarda yayi wanan auren ba yake rayawa a ranshi.
Yarinyar daya dauka bagidajiya zai iya yaudaran ta da kudi da wasu kyalkyal din duniya duk da yana zube matasu kamar ba gobe amma tana son zame mashi ciwon idon rayuwa.
Sam bai taba zaton hakan ba da sauri ya dauka koda zan fahinci hakan sai bayan shekaru sun ja san nan zata iya fahintar rayuwan da sukeyi dashi a gidan.
Sai gashi a cikin yan shekaru ta nuna mashi halin mata a wurin wayau da hikima har ta iya hadashi da mahaifiyan shi haka.
Hadi na zargi da kake har mami na zubar da hawaye da bata taba irin saba tana ikirarin cewa zata sa a kashe shi shima duk inda ya shiga a duniyan nan.
Tabbas mami zata iya tunda ta furta hakan har in yayi gigin aikata hakan kan zainab din da kanwaera.
Shi ta yaya ma zai aikata hakan wai da har mami ta yarda da hakan da sauri don zainab din ta fada mata kawai zatayi amfani da wanan zancen.
Yana gama wanan tunanen ya dago kanshi dake duke ya kurama zainab din ido na dan lokaci .
Yarinyar ta rame sosai tayi wani hasken dake daukan ido tausayi ta bashi sosai don tana a tsorace ne ko damuwa har lokacin.
Baisan irin kalaman da zai mata amfani dashi ba a bakin shi ta yadda zata fahince shi a yanzu ta kwantar da hankalinta.
Don karyama ko yaudara bai taso ba gareshi yanzu tunda da idon ta ta ganshi bawai zato ba ko jiji da takeyi da farko.
Yanzu kan idanun ta ya gane mata koshi waye don haka babu sauran wani zancen dadin baki a kan hakan daya rage a bakin shi saidai hikima.
Muryan shi naji yana fadin wai yaushene zaku samu hutun makaranta ya fada yana kallo na ?
Jin abinda ya fadane yasa na dago kai da sauri don a zatona yana tambaya ne don ya mayar damu gida lokacin.
One month coming zamu samu saidai ita sadiya zata rigani samun hutu na fada mai a sanyayye don jikina da baida karfi sosai.
Ina son in kun samu hutu zamu tafi Dubai mu dan huta a can sai kunyi hutun naku can ga baki daya don nima zan dauki hutu a lokacin.
Fuska na bata ina kawar da kai daga kallon shi don jin abinda ya fada tunda ba gida zai kaimu ba a lokacin .
Ashe ya fahinci hakan danayi naji ya sake fada a daidai lokacin sadiya na fitowa daga daki yace ko Dubai din bai maki ba na kaiku America ko wani kasa kuyi hutun a can ?
Ni ba inda zan tafi na fadi hakan ina murgada baki kafin yace wani abu sadiya ta cabe da fadin yaya mune zamu tafi Dubai din ?
Eh sadiya a can nake son kuyi hutun ku wanan karon don ku dan ga garin tunda baku taba zuwa ba ko ?
Yayan mu shine bamu zuwa Dubai din don Allah karkice ba zamu can din ba ina son zuwa naga Dubai din nan da friends dina ke bada labarin sa.
Iyayyen su masu kudine idan kinji suna zance ke ko yar waye da zaki matsawa rayuwan ki zuwa can ?
Amma ai kanwan jafar ce ita din ko, ko anfada maki kani baya tunkaho da dukiyan wanshi ne ?
Wani kallo nayiwa sadiya din kafin nace tabi dai duniya a sannu irin haka ke kai mutum ga halaka karshe har mutum ya bar addinin sa ya fada sabon Allah.
Murmushi yayi tare da dan shafan gefen fuskan shi ya mike tare da fadin while sadiya saiki fara shiri ko ?
Don mukan Dubai zamu tafi mu huta ko ta daga kai tana satan kallona nidai nawa ido kawai na zuba masu ban iya furta komai ba garesu.
Haka muke samun kulawa daga gareshi a wanan lokacin don gaba daya yanzu ya sakawa duk wani motsi namu a gidan idanu idan yana gida.
Banda sakewa don kullun a cikin farga nake haka kuma yanzu nasakawa raina zaman dakin don falon da na riskesu a cikin sa suna fasadin su ya fita raina gaba daya.
Dana kalli daidai wurin dana gansu din a ranan sai naga kamar a lokacin ne suke aikata alfashan su .
Dakina ne ya koma min wurin zama muddin ina gidan saidai sadiya ta sameni a ciki muci abinci muyi hira ko kallo a nan.
Har wanan lokacin Maya bata tambayeni zancen magani ba nima ban tayar da zancen ba gareta don na manta da wanan zancen don abin yaya yayi nisa sosai.
Saima nake ganin ina wanan tsohuwar zata iya da taimakon kan haka al,amarin shi sai addu a kawai.
Ko banza sai nake ganin ai su din ba musulmai bane kuma ba Allah ma suka sani ba don haka ai abinsu ba zama dole a amsa masu ba a wurin Allah.
Kawai saina dinga addu,a da kyauta idan na biyo hanya naga marasa galihu saina tsaya na dan masu alheri.
Jerabawa ya sakamu a gaba hakan yasa ban ma da lokacin kowa a yanzu saina karatuna don ina son in fito da sakamako mai kyawo idan na gama.
Kwanan mu hudu da hutu muka daga zuwa Dubai inda mukaiwa dubai din saukan dare kafin mu kai hotel din da zamu sauka an fara kiraye kirayen sallah asuba.
Wani tsadden hotel ya sauke mu a kusa da ruwa muke duk da darene amma hakan bai hanamu gane kyau garin ba.
Dakin da aka saukemu shike kusa da nasa wurin dai sai kingani gwanin ban sha,a sallah nayi na haye gado sai barci ko abincin da yai odar akawo muna na karyawa ban tashi naci ba sai karfe daya na rana.
Sadiya bata dakin wanka na kara yi don naji dadin jikina bayan nafito na zauna ina gyara fuskana duk daba makeup nakayi ba a fuskana yau sai na samu kaina da shafa poweder kadan a fuskan nawa.
Gurin mayarwa ne naci karo da wanan maganin da kakan Maya ta bani don da wanan jakkar na tafi kauyen su maya din a ranan da naje can din.
Nayi mamaki kwarai dana ga wanan abin ashe ban cireshi a jakkar ba har nazo nan dashi uwar duniya.
Riga na mike na dauko na saka a jikina duk da bawasu kaya muka dauko ba don yaya ya hana hakan wanda zamu canza idan munyi wanka sai na jikin mu kadai muka dauko.
Kofan aka turo sadiyace a gaba yana binta a baya suna dauke da kaya niki niki a hannayen su haka yasani juyowa ina kallon su.
A saman gadon dakin suka zube kayan shi bai tsaya ba sannu kawai nayi mai ya juya ya fita bayan ya amsa min.
Baiko karasa fita daga dakin ba sadiya ke fada min yau yayan mu naga garin nan ashe haka wanan garin yake cike da musulmai ?
Ina kukaje na tsare ta da tambaya yayan mu ya shigo ya sameni zaune kina barci yace nazo muje unguwa.
Kada ki kara fita da kowa idan baki fada min ba na fada fuska daure Allah ya taimakeni tana matukar tsorona sosai don fada nakan mata idan tayi ba daidai ba.
Zama nayi na fara bude kayan suturu ne irin na mata yan duniya da suka amsa sunan su a ciki sai kuma na sadiya din leda daban ita sun kai kusan kala goma.
Ikon Allah na fada a fili a raina kuma rayawa nayi yanzu shi yaya bai gajiya da labto mana kaya haka ko a gida can chaina bazance ga yawan tufafina ba yanzu.
Sai kayan kwalama wanda ko ban tambaya ba na san saboda sadiyace ya sayo su haka kala kala.
Yunwa ne ya fara ziyarana sai lokacin na daga ido na hango abin karyawana saman table din cin abincin dake dakin mai kama da karamin palace.
Mikewa nayi zuwa kan table don na zauna tare da bude abincin irin cimarsu ne na larabawa aka shirya saman table din.
Dan kadan na tsakura na barshi don tafarnuwan da yai yawa a ciki duk da suma chaina suna cin tafarnu amma basu kai nan ci sosai ba.
Bayan karfe biyar shi ya shigo dakin da kansa yace muzo mu fita mu sha iska a waje munga kifaye suna wasa a ruwa wanda suka dauke min hankali sosai wurin kallo gwanin ban sha,awa;
Mun baza ido munyi kallo sosai ranan sai kusan magariba muka dawo cikin masaukin mu a gajiye.
Dadi kan muna shan shi zuwan mu dubai har yakai na kasa fahintar wanan daulan yadda yake kashe muna kudi don zuwa hutu kawai da mukayi a nan din.
Ban tashi sanin taju yana garin ba sai ranan da dare na fito daki kamar wace akacewa na fito wajen a cikin daren .
Na kama hanya zuwa waje don kawai iskan dake kadawa mai dadi a wajen dana shaka ta tagan dakin.
Kwatsam na gashi a gaba saida nayi wani irin kaduwa mai ban tsoro kafin na jawo karfin hali insa a rayuwana na dake na watsa mai harara kamar yadda shima yake min kallon rainin wayaun.
Shamlace man kaji kunya kato dakai kana bin karamin yaro kuna lalata dashi don taushewan kwakwalwa da batan basira.
In dai J ne insha Allahu sai ka zama abin kyama a gareshi nan gaba don ko kallon kare ba zai ma ba a duniyan nan indai akwai Allah na daga hannuna sama ina nuna saman alaman Allah na nan.
Na wuce shi ba tare da yai min magana ba naji mamakin hakan kwarai da yayi don sai murmushin mugunta ya sake kawai.
Ina tsaye rai a bace ina tunane wanan irun bala,in da yake tunkarana haka koda yaushe na jafar din.
Karama dani mai karancin shekaru a wanan halin haka ni yanzu ma na rasa abinda zanyi saidai kawai na barwa Allah lamarin sa.
Don abin ya wuce gaban mamaki sai la haula wala kuwati kawai za a ce ma lamarin nasa tunda har naga wanan katon kuma a nan.
Rasa abinda zanyi nayi a wurin na kunna wayana ina daukan hoton wurun don ya debe min kewa da bakin cikin dake cina a rai.
Don wanan karon nayi alkawarin bazan wa J din magana ba kan hakan saidai in bar abin a cikina kawai Allah yayi min maganin su da kanshi
Jimana naji an fada a bayana nayi saurin juyowa inga ko waye ke magana haka dani a wurin .
Taju ne tsaye ya saka hannayen shi a cikin aljihun wandon shi yace kada kiga kin fada min magana na kyaleki.
Yanzu dai nasan kin san ko wayw ni a gurin J din a tunane ki kina ganin har J din na iya rayuwa badani ba ?
Don haka yanzu ki ba kanki amsa a nan ya juya ya fara dan tafiya sai kuma ya juyo yace ku mata wawaye ne koda yake kwadayine ke damun ki keda iyayyen ki shiya kawo hakan.
Ya sake wani shu,umin murmushi a fuskan shi ya juya ya tafi ya barni tsaye a wurin ina binshi da kallo cike da kunan rai.
Har na dawo dakine ba tuna da wayana a kunne yake don ba kiran kowa nakeyi ba a nan tunda banda layin kasan a wayana.
Gado na fada sadiya na kwance tana kallon a system dina wanda aikinta ke nan sai sallah kawai ke tayar da ita lokacin.
Yaya kin fitane nace eh na sha iska ne a wajen bayan haka bamu kara magana ba don kwance nakai rigingine fuskana yana kallon saman dakin ina faman tunane.
Barci ya daukeni a hakan itama ashe tayi barci tabar sytem na aiki waya na kuma shima ya nuna a kunne yake don dan wutan da yake nunowa yana aki aiki.
Ya dawo ya shigo dakin don ganin wutan mu a kunne dayayi sai ya samu duk barci mukeyi a dakin dukan mu ga naurorin mu a kune a kusa damu.
Yayi niyar ya tayar damu daga barcin sai kuma ya barmu ya fara kashe system din dake wurun kan ta a yashe.
Bayan ya kashe system din ya mika hannu ya dauki wayana zai kashe ya ga video ne na dauka ya dan tsaya yana kallo.
Forwarding din shi yayi abin ya bashi mamaki don hotunan wajen hotel ne ya bayana yana magana sai dai baya jin me ake fada don ba kara.
Girgiza kai yayi yana murmushi ya dago ya kalleni ina kwance nayi barcina bansan inda nake ba ma a lokacin ya kashe wutan dakin ya fita.
Sai cikin dare na falka naga yadda muka kwanta tashi nayi da sauri na nufi kofan don in rufe sai na samu kofan a rufe ba key a wurin haka yasa na gane ta baya aka rufe mu.
Da tsoro na dawo cikin dakin ban kwanta ba abandaki na shiga nayi alwala nazo na tayar da sallah na dade a zaune ina addu,a da rokon Allah kan ya tsaremu ya karemu daga halaka.
Zancena da taju ne yake dawo min sabo saka sunan iyayyena da yayi yafi komai tsaya min a zuciyana.
A karshe wani dabara ya fado min a raina a hakan har aka kira sallan asuba na mike na gabatar sai lokacin na koma barci.
Da yake na sa abu a zuciyana sai banyi wani barcin sosai ba don kada yaya ya shigo ban sani ba.
Dakin ya shigo kuwa bayan mun gaisa dashine yanawa sadiya sherin wai ta fara zama yar lukuti tana dariya.
Yaya yau ina son shiga ruwan can don haka idan ka fita kada ka dade ka dawo mu shiga na fada kai tsaye ba tare da shakkan komai ba.
Bashi ba har sadiya tayi mamakin jin wanan maganan daya fito a bakina lokacin yace a cikin mamaki dama kin taba shiga ruwane ke nan ?
Ban taba ba yau dai nake son in fara na bashi amsa da hakan ya gyara tsayuwa yana fadin idan aiki ya barni zan dawo din Allah dawo dakai lafiya .
Yana fita na bishi da kallo tare da mamakin kaina nayin wanan karfin halin haka da nake son gwadawa a yanzu.
Tun lokacin na fara shiri na na fita har zuwa bakin shagunan dake layin hotel din na sayo wasu irin kaya masu matukar kyau ga tsada.
Kwalliya mai daukan hankali na tsarawa kaina don ban taba sanin na iya ba haka tun dan koyon da nayi zamanin zama da yan matan mami a gidan ta ina jin zancen su a wurin yin kwaliyan su zakaji suna gardama wanan yayi yawa wanan bai ji ba.
Kodana dauko rigan zan saka saida na runtse idanuwana kafin na bude na daure na saka kayan hakanan sai gani na koma kamar wace zata wurin fashion.
Ni kaina saida na gigiza dan ganina haka ba komai bane yasani hakan sai daukan irin shawarwarun fadila da yau nayi a zuciyana.
Don ina son in gwada in gwada sa,ata da hikimana na diya mace da fadila ke yawan fada min ko yaushe da takace.
Mu mata makamine gun da namiji komai taurin da namiji da cijewa ko gagara a duniya sai mace ta juya shi a wata tsigar nata wata rana.
Ta hanyar yaudarar ta ko kisa ko kuma kisisina da kutungwila irin na mata da maza basu taba gano hakan sai mace yar uwarta zata gane mai take shiryawa.
Wanan baiwa ne irin na mata da Allah ya halicci diya mace wanda su matan bayan addu,a wanan ne makami na biyu da suke amfani dashi a wajen mazanjen auren su ko hurda.
Ranan turare yasha kashi don duk wanda na gani har wanda ke cikin jakkana nayi amfani dashi a irin hakane na dauko wanda idan baki matan ba fadilace ta banshi da dadewa lokacin da zamu zo chaina tace ta karbo min nayi amfani dashi.
Uku da rabi na fara wanan shirin kafin karfe hudu don saida nayi sallah la,asar na zauna yin kwalliyan nawa na kammala komai daidai lokacin daya dace in kammala din.
A nasa bangaren kuwa yana tune da hakan yasa ya baro abin da yakeyi zuwa masaukin namu don shi ba mutum bane mai saba alkawari duk halin turawa shine akidar shi.
Don da hakan bai samuwa da bai mun alkawari ba tun farko dakin shi ya fara yadda zango yayi wanka ya shirya already yayi booking din wani haddaden jirgin hotel din da zamu shiga ruwan dashi.
Dakin ya turo wanda kamshi ne ta ko ina ya fara taron hancin shi ya fara raba ido a kan mu Allah ya taimake mu ina zaune saman gado ina zaman jiran tsamani ya shigo.
Duk da kusan wata biyun da suke shige idan ya kalleni gaban shi sai ya fadi ko yaji wani bakon yanayi a kaina yana ziyartan shi .
Wanda hakan yakan daukeshi don kawai yasaba da mune kwarai a yanzu yasa tausayine ko wani abu yakan ziyarci zuciyar a kaina don yasan badai feeling bane wanda maza kanji akan wata mace.
Shiya dauka hakan sabone kawai da tausayina da yake ji ayanzu ne don yasan bayai min daidai yasa yana jin wanan akaina idan ya kalleni wani lokacin.
Don saboda wani lokacin yakan zauna yana yin tunane mai zurfi kan matsalan namu tunda mami ta sakashi gaba yanzu don da kyat take daukan wayan shi koshi sai ya bi ta hanyar ya mamud yake samu su gaisa saboda Allah ya aza mai son mahaifiyarsu a ranshi.
Don hakane yakan zauna yana neman way out kan matsalan nasa da yake da wuya ya bari shima ya sani saboda yasha gwada barin ya kasa yin hakan.
Sai yanzune yasan ya fada tarko mai wuyan fita a cikin rayuwan shi wanda zaice kurciyane da zugin abokai sukai tasiri a ranshi a lokacin don kawai duniya ya fada halaka.
Gashi arziki da suna duk sun samu a duniya saidai shi gareshi a yanzu wanan duk banzane a wurin shi tunda har mahaifiyar shi da uwar cikin shi suna kyamarshi saboda halin shi.
Da wanan ya shigo dakin namu sai dai yau din muna hada ido dashi daga inda nake zaune nayi wani irin zama kamar wata Queen of manshion saman gadon.
Wanda nima dai haka kawai yanayin zaman yazo min bawai nayine da ganganba don kawai kada kayan jikina ya baci ne na zauna hakana.
Ras ras yaji a gaban shi wani abinda bai taba ji ko hangowa a gareni bane ya hango tare dani yau din daya shigo ya tsinkayeni hakan.


ZAINAB IDRIS MAKAWALITTAFIN NAN NA KUDINE YAR UWA KI BIYA KAFIN KI KARANTA A CIKIN SALAMA NA FITA HAKKIN KI NA FADA MAKI YAR UWA ALLAH YASA MU DACE DA RAHAMOMIN SA AMIN, , , ,


Ina zaune saman gado nayi zaman balance irin na goggagun mata yan duniya na wani harde kafa rabin cinyana duk a waje yake.
Na bude baki a hankali cikin wani yauki da yatsune ina fadin sannu da dawo tare da kawar da kai kamar shigowan shi ba dameni ba yadda na nuna.
Amsawa yayi da mamaki karara a fuskanshi yana kare min kallon irin shigan da nayi a lokacin don fitan da zamuyi din dashi.
Yayan mu na shirya muryan sadiya ya daki kunnuwan mu lokaci daya tana fitowa wani dan lungu dake dakin don dakin babbane an masa part part kamar kana cikin babban gida mai dakuna da yawa.
Mayar da hankalin shi yayi gareta har ta kara fitowa yake fadin Wa, Wooo wai wanan sadiyace kanwata dai dana sani ko idona ne ke mun gizo haka ?
Dan murmushin jin dadi ta sake a fuskanta ya mika mata hannu tazo gareshi yace kanwata kinyi kyau sosai wallahi .
Tace har na kai yayan mu yin kyau kuwa ya J har kin fita ya furta tare da jawota yana mata rada a kunnen ta kafin ta juyo ta kalleni a inda nake zaune bakin gado.
Idan kun gama gulman sai mu tafi na fada ina mikewa tsaye na dauko handbag dina dake gefen inda na zauna.
Ina gyara gyalen dana yafa saman hullar daya rufe min kaina da kyau ido ya kara bina dashi na turu baki ina fadin wanan kallon ai sai mutum ya kware haka.
Ina mamakin wanan kwalliyan ne haka don ban taba ganin kiyi irin sa ba duk da ruwa zamu shiga amma kika chaba ado haka dake ?
Nayi ne don daga ni sai kai sai Sadiya zamuyi tafiyan da ace wurin mutane da yawa zamu shiga bazanyi shi ba.
Hanya ya nuna min da hannu na kalli sadiya ina fadin shige mu tafi ta fara hanya na mara mata baya ya rufo dakin da makulli bayan mun fita.
Dan tafiya ne ya sadamu da wurin ina bin ko ina da kallo sai gamu bakin ruwa nidai har cikin raina dama ina son shiga ruwa koda bai kai haka yawa ba a rayuwa .
Sai gashi yau zan shiga ruwa irun wanan jiragene a wurin jere da juna muka tun kari wurin nomban da aka bashi.
Bamu sha wahala ba don jirgin yana da matakala kamar a tudu muke a wurin shiga cikin jirgin kuma a kwai komai kamar yadda muke ganin sun shiga a cikin film.
Bayan shigan mune kamar ance in daga ido sama ina dagawa na hango taju a tsaye saman bene yana kallon mu.
Dan murmushi na sake tare da daga mashi hannu alaman bye kafin na karasa shiga cikin jirgin ga baki daya a lokacin har jirgin ya soma tafiya damu ko.
A gaskiya masu kudi suna jin dadin su sosai a duniyan nan don idan ka dace da rahaman ubangiji gaskiya ka huta .
Allah yasa mu cika da imani na fada a raina kafin na kai zaune ina mayar da idona rufe ba komai ya sani haka sai tunawan da nayi da irin rayuwan da yaya yake ciki.
Ya haka kuma keda kikace jirgi kike son shiga kika rufe idanun ki yanzu kuma ?
Jin hakan da nayi yasani bude idanun nawa na sauke a kanshi yana zaune ya bude system ko har ya fara aiki a cikin sa yake wanan maganan.
Duniya nake tunane yaya na bashi amsa don nasha alwashin sakewa dashi yanzu a kan taju duk yadda zanyi sai naga na raba wanan alakan nasu koda kuwa yin hakan bazai sa yaya ya daina ba sai dai ya canza wani katon bashi ba.
Tunanen me kikeyi na duniya nace a daidai lokacin da nayi wani irin zama na yan barikin mata ina dora kafana daya saman daya.
Wanda yin hakan har ya baiyanar da rabin cinyana a waje wanda dama rigan nada tsaga har kasa idan mutum yayi irin hakan zai baiyana sosai a gani.
Duniya aljanan kafiri lahira kuma ta mai rabo duk wanan jin dadin naga iyakar shi duniya za a barshi ba a zuwa lahira dashi nagani.
Yaji maganan sosai har cikin ranshi sai dai bai kara magana ba yaci gaba da abinda yakeyi a cikin computer din shi ya kyaleni.
Tsawon wani lokaci wurin yana shiru jirgin sai tafiya yake damu a cikin ruwa hannu na mika na dauki dayan cup din dake saman table din dake tsakiyan mu ina tsiyayya ruwan enabi na fara kurbawa a hankali.
Yana sane da sabon halin dana tsiro dashi don yasan ba haka nake ba da rashin kunya sai dai yana bina yaga iya guduna kawai.
Daga inda nake zaune na kara daukan kofi na tsiyaya drinks din na mike a hankali zuwa gefen da yake zaune na zauna gab dashi ina mika mai abin sha.
Dan juyowa yayi ta miko min bakin shi da zuman wai in bashi don shi wanan ba komai bane a gareshi.
Don ko Aisha da take kanwarsa watarana ina gani itace ke basa a baki yana sha tun ina zagin su har na saba da ganin hakan na daina.
Tunawa da hakan da nayi banyi sanyi a gwiwa ba na mika masa ya kurba a hakan har ya shaye cup din.
Na aje na dan jiginu da jikin shi tare da daukan jaridan dake saman table din wanda aka aje don mu na fara karantawa.
Matane sexy girls gasu nan iri iri ko wace da irin nata shigan ciki computer ya rufe tare da fadin ki tashi mu leka waje kuga ruwa.
Don ita sadiya tana nata aikin kallo a cikin wayan ya dauke mata hankalin ta garemu tana jin hakan tayi saurin dago kanta tana son jin amsan da zan bashi.
Batare da yin magana ba na mike zaune shima mikewa yayi muka fita sosai muke jin dadin wanan fitan namu don sai da gari yai duhu muka dawo masaukin mu a cikin an,nashuwa.
Tun fitan shi dakin ko washe gari bamu kara jin duriyan shi ba saida yamma ya shigo muna ruwan saman da akeyi a garin ya dan dukeshi.
Don ni a lokacin har zuciyana ya fara wasi wasin din ko dai taju shima ya nuna fushin shi kan fitan mune yasa bai shigo dakin namu ba yau ya fita .
Tunda taju din da ire iren su sune kishiyoyina a yanzu wurin shi yasa na fara wanan tunanen haka sai gashi ya shigo dakin da yamma.
Gaidashi din dai mukayi yake tambayan sadiya ko zamu koma ruwa ne yau din ma Sadiya mu kwana a cikin ruwan.
Da sauri tace a,a yaya j bazan koma ba jiya ma banyi barci da dadi ba wallahi don da zaran na rufe idona ruwan nake gani saina bude.
Matsoraciya yace yana juyawa ya fita dakin yakan shigo da dare kafin mu kwanta sai gashi bai shigo dakin ba ranan.
Hakama washe gari bai lekomu ba sai wajajen karfe biyu aji wayan dakin na ringing na dauka.
Muryan shine a cikin wani irin yanayi yake fadin zainab sun kawo maku breakfast ki hado min ruwan zafi ?
Nace eh yace ok black tea kawai zaki hada min ki kawo min yau ban fita ba bana jin dadin jikina ne kadan.
Subbahanallahi nace hope dai da sauki yace ciwon kaine kawai ke damuna har nakai wurin kayan breakfast din sai wani tunane yazo min a rai.
Da sauri na koma na dauko wanan maganin ba tare da nabari sadiya ta kula da abinda nakeyi ba na nufi wurin da zan hada mai tea din da jakkata.
Na hada kamar yadda maya tayi min bayani na dauka na kai mai dakin da shine farkon shigana tun zuwan mu Dubai din duk da bamu da nisa dashi.
Yana kwance saman mamakeken gadon dakin jikin shi saye da dogon wando ash colour sai farar singlet daya saka a saman jiki ya kife cikin saman gadon yana kwance na shigo dakin.
A hankali na taka zuwa bakin gadon saida na kai zaune nake fadin ga ruwan tea din nan yaya na gado maka gaba sai faman faduwa yakeyi kamar nayi laifi za a kamani.
Dan dagowa yayi sai ya koma kwance yana tsuki kafin kuma ya dago da karfi ya tashi gaba daya yana fadin a daidai lokacin da nake mashi sannu, da jiki yace.
Ina ganin ruwan daya dan dukeni ne jiya yaja min ciwon kai dama jikina bai shiri da dukan ruwa ko kadan.
Kasha magani yace nasha don dashi nazo ban faye yarda da magani su nan ba shiyasa nake tafiya dashi duk inda zani.
Ya shiga ban daki ina ganin baki ta wanko ya fito har lokacin ina zaune a wurin dana zauna din ya dauki ruwan shayin yana kurbawa daga tsaye.
Dan kai na dago na saci kallon shi na dukar da kai shiru muke bayan ya gama kurban ruwan tea din ya aje cup .
Ganin hakan na mike na dauki cup din na fita dashi da zan fita nace Allah ya sauwa yake fadin ai barci zanyi na dan lokaci ko zan tashi inji saukin shi.
Nakoma daki da fargaba a ciki zuciya do dai kam na kada na bashi ya kuma sha saura in jiran hukuncin ubangijin mu yanzu kam a kan wanan lamarin.
A cikin wanan tunanen ne har barci ya daukeni ban sani ba barci sosai na samu nayi a lokacin a can cikin barci nake jin wayan dakin yana ringing alaman kira yana shigo min lokacin .
Da kyar na iya bude idanuwana da sukai nauyi saboda barcin na mike da kyat din kuma na jawo kan wayan dake gefen gadon.
Muryan yayane baya fita da ji yana cikin tsananin ciwo a lokacin yana fadin zainab kizo kada in mutu .
Gabana ya bada ras ras lokaci guda da sauri na sauko saman gadon ban tsaya jiran komai ba na nufi hanyar fita waje zuwa dakin nasa.
Ina shiga yana wani irin nishi da kakari kamar zai mutu ya dafe cikin shi da hannun shi daya yana mulmula a kasa.
Da sauri na karasa inda yake kwance saman ties din yana wanan gurjin kamar karimin yaro.
Gaba sai faduwa yakeyi don tsoro don ni su maya basu fada min zaiyi wanan wahalan ba haka.
Tsugunne nakai saman kamshi ina dan kiran sunan shi da yaya yaya me ya sameka haka ina fadi a rude tare da kai hannuna saman jiki shi ina taba shi.
Bai iya dago kai ba ba kuma magana sai kokarin nuna min cikin shi da yakeyi da hannun shi na kara rudewa sosai.
Magana yake son yi ya kasa haka yasa na mike a rude ina kuka zan fita daga dakin naji ya rike min hannu na a cikin nasa.
Na dawo inda yake din yana son kara yin magana yai wani irin yunkuri sai ga amai yazo mai lokaci guda wani irin bakin amai da ban taba ganin irin saba a duniya.
Amai yayi sosai a wurin na kara rudewa kamar rayuwan shi zai dauke a lokacin duk ya fita cikin yanayin sa lokaci guda har halittan shi ya dan sauyawa ganina.
Nishi yakeyi sama sama can ya samu magana yazo mai da karfi yana fadin dauko wayana ki kira a kaini asibiti don Allah kada in mutu.
Da sauri na mike na nufi wurin gadon dakin ina neman wayan nashi a karkashin filo naga wayan na dauko ina tambayan shi wani nomba zan kira.
Mai 00 karshe ya fadi yana mayar da kanshi a kasa da alama sayin yake so sosai a lokacin ya ban tausayi matuka.
Kamar jira suke a kirasa baifi minti biyu ba sai gasu dakin da gagawan su suka daukemu zuwa asibitin.
Likitoci sunyi aune aune a kan aman da yake yi din basu gane dalilin aman ba, yan magunguna suka bashi tare da karin ruwa muka dawo masaukin mu dashi.
Duk ya zabge lokaci daya yayi wani irin rama mara ma,ana a jikin shi ko don ban taba ganin wani a irin wanan halin bane oho ?
Aman bawai ya tsaya bane ga baki daya don yana yinsa lokaci lokaci idan ya taso mai da kyat mukaga safe ranan dashi don a dakin nasa na kwana.
Washegari ya dan tashi da dama amma duk jikin shi ya sake bai ko iya tafiya sai da kyat da bin bango yake iya zuwa ban daki ya kewaya.
Har na gane yana tsunguni ranan ya dawo ya kwanta ina zaune na zuba mai ido cikin tashin hankali da tsoron abinda zai biyo bayan hakan a kanshi.
Wayan shi dake gefe yayi kuka na dan kalleshi idon shi a rufe baida niyar budewa balle ya dauka.
Har kiran ya katse wani ya kara shigowa sai nakai hannu na dauka sunan mami na gani da sauri nayi recieve kada ya kare katsewa irin na dazun.
Jafar lafiya banji ka kira ba tun jiya ta fada mami bashi bane gashi kwance baida lafiya tun jiya din na bata amsa .
A rude tace meya sameshi kuma zainab injin dai ba abin bane ya fara bashi matsala har muryan ta yana sarkewa a lokacin don rudewa.
Mami daga ciwon kaine sai ya koma amai da tsugunni a yau din jiya dai aman yakeyi kawai.
Yanzu kuna ina ne wai ta tambaya, nace muna nan Dubai munzo hutu ne last week kunje asibiti ko nace jiyan munje sun bashi magani muka dawo.
Barin fadawa mamud ko zai iya tasowa yau yazo idan zai samu jirgi a lokacin naji ya dan yi magana na juyo gareshi yana fadin
Kice ta barshi zamu koma chaina ne inje asibiti can likitana ya ganni a can din ba sai yazo ba.
Na fadawa mami din abinda yace nan ta fara fada hankali tashe nayi shiru ina saurarenta tana fadin zai dauki ciwo tundaga Dubai har zuwa chaina nan babu likitocine da zasu dubashi ?
Nikan karshe wayan na kara mashi a kunnen shi yana jin fadan da mami din takeyi a wayan yace a karshe mami na riga nayi booking ko zai gani da zaran mun isa can din.
Yau zamu koma insha Allah anyi booking din jirgin tafiyan mu a yau din don likitan shi yasan matsalana.
Ba zainab din waya muyi magana ta fada ya miko min wayan tace zainab don Allah idan kun isa kinga abin bai tsaya ba ki kira mu ki fada muna halin da ake ciki .
Murya na rawa nace tau mami insha Allahu ki kula dashi sosai don Allah zainab nasan halin jafar da gardama kada ki daka ta nasa don Allah.
Ni yanzu idan mami tana min magana sai abin ya dinga ban mamaki balle yanzu da har mami din taji wai muna dubai da danta bansha zagi da sheri ba.
Wai har da danka min kula da dan nata a hannuna tana wani hadani da Allah can bayan ta gama min cin fuska a baya.
Don darajana da kima baikai na wace zata shiga cikin wanan daulan ba na danta iya abinda mami ke nufi dani ke nan ba wani abu ba.
Amma yanzu data ga dan nata yana da mugun tabo masu yawa da kyama a rayuwan shi shine take kokarin nuna min cewa tana sona a cikin ahalin ta a yanzu.
Idona na runtse wasu hawaye masu dumi suna zobo min meta fada maki daya sakaki kuka a yanzu muryan shine cikin sanyin murya yake min wanan tambayan.
Ban iya bashi amsa ba sai mikewa da nayi don barin dakin da sauri kada ki fita ki barni haka a cikin wanan halin da nake ya fada.
Ja nayi na tsaya wuri daya ban kara gusawa ba daga inda nake tsaye din yaci gaba da fadin banji ta fada maki wani abinda zai sakaki kuka haka har ki fushi ki fita ba ki barni ni kadai ina cikin wanan halin.
Don koma ta fada maki bazan yarda da hakan ba kema kin sani don haka ki dawo ki zauna har na dan kara jin karfin jikin nawa.
Zan je na fara shiri ne na bashi amsa ba tare dana juyo inda yake ba nake magana ina kokarin fita duk da ya hanani ina son kebewa inda zanyi kuka ma,ishina ba wanda zai hanani a yanzu.
Bina yayi da kallo har na bace mai da gani kafin ya sauke ajiyan zuciya yana runtse ido cikin takaici don shidai ya rasa meyasa ni kuka a cikin wanan maganan kuma ?
Ban iya zama dakin ba don halin dana barshi a ciki koda na koma na samu ya fito ban daki ya zauna a kofan don bai iya karasowa cikin dakin da kafafun shi a lokacin.
Nan kan hankalina ya tashi sosai don sai dana kamashi ya koma saman gado ya kwanta na shiga fadi a raina shike nan nine zanyi ajalin yaya ke nan ashe ?
Kofa aka buga don shigowa na mike na bude kofan wasu mutum biyu ne na sama a wurin tsaye suke tambayana shi na nuna masu ciki da hannu suka shiga.
Ashe likitane da wani abokin shi suka shigo basu fita ba saida aka daura mai ruwa da sauran magani sai gashi ya samu karfi har sallah naga yayi a tsaye bayan fitan su.
A lokacin hankalina ya fara dan kwantawa don ganin ya soma samun lafiya a jikin shi yanzu dama ni tsorona shine kada ya halaka a sanadiyar maganin da na zuba mai wani abu yazo ya same shi kuma.
Karfe takwas na dare muka bar cikin hotel din mun dan jira kafin jirgin ya tashi zuwa tara na dare muka bar kasan zuwa chaina.
Muna isa asibiti aka wuce dashi daga can duk gwaji likitan yace shi baiga courses din ciwon nasa ba sai dai idan wani abu yasha na daban da ya jawo mashi hakan.
Sai dai nan din sun kwatar dashi na kwana biyu kafin su sallamoshi ya dawo gida ya karasa jinya a gida kuma yana shan magani.
Bashi dake jinyar ba koni na rame sosai don ciwon nasa ya daga mi hankali amma yanzu da naga ya dawo normal na fara sake jikina nima.


ZAINAB IDRIS MAKAWALITTAFIN KUDINE YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DON SAUKE HAKKIN WANI A KANKI, , ,


Alhamdullahi zan iya cewa don jikin yaya yayi sauki sosai kuma ina bashi kulawan daya dace sosai a matsayina na sunan matar shi.
Yar uwan shi kuma mafi kusa dashi a yanzu haka yasa na zage sosai wurin kula dashi din don shima a iya yin shi gaskiya yana nasa kokarin damu tankar yan uwansa na jini.
Don haka naba kaina shawara dama kuma kinsan mace ga rauni da sanyi hali a wurin namiji nima hakan ne yaci don shi kanshi saida yayi mamakin yadda nake bashi kulan a lokacin.
Ba tare da wani jin komai ba tsakani da Allah nake masa komai yadda ya kamata don shi kanshi ya fahinci hakan.
Safiyane yau na shirya cikin wani riga ja na daure kaina da ribon mai ja shima da farin duwatsu.
Dan gyale ja na dora saman kaina sai dai bawai rufe kai din nayi ba sosai sai kamshi da jikina keyi a lokacin .
Dakin na part din shi na nufa don gaida shi da kwana akwance na hango shi ya kurawa silling din dakin ido kamar mai tunane.
Kamar yadda na saba idan ni nazo gaidashi da kwana bashi ya sameni a zaune part dina ba.
Jin motsina baisa ya motsa a yadda na riskeshi ba har nakai bakin gadon na gurfa gwiwa bibiyu ina fadin yaya ina kwana ya karfin jikin kuma ?
Zainab na dago kai na kallo shi sai kuma naga ya danyi gajeren murmushi ya kawar da kanshi daga inda yake kallo.
Haka sai yasani tsarguwa da yadda yai min din ina a yadda nake ban motsa ba nayi shiru shima hakan baiko amsa min gaisuwan da nayi masa ba na safen dana
saba zuwa part din in gaida shi don da sadiya mukan zo gaidashi din ranan kuma ni daya nazo.
Sai can nace dashi a hada ruwan wankane ka watsa yanzu na fada ina kallon shi don jin amsan da zan bashi.
Ki hada nima ina son inyi wanka yau in dan fita tunda naji sauki sosai mikewa nayi zuwa ban dakin na hada mai ruwa kamar yadda yake son yi dashi tun ranan farko daya fada min yadda zan hada mai din.
Na hado ruwan na dawo na fada mai zan bar part din tunda ba wai wani hira mai tsawone irin na mata da miji a tsakanin mu ba dama.
Muryan shi ke fadin sai ki fitar min da tufafin da zan saka idan na fito tunda yanzu naga zaki fara aikin ki na mata a gareni.
Wani irin juyowa nayi ina kallon shi a cikin mamaki a fuskana don jin abinda ya fada din gareni.
Ba matsayin mata ya saka nake maka wanan ba a matsayi kanwa a gareka da kuma Allah nake maka komai don ka cancanci hakan a gareni .
Ina fadan hakan na sa kai na fice daga dakin don jin da nayi yace fita zaiyi a lokacin da ba haka ba idan na shigo bana fita haka zan zauna a wurin shi.
Duk da ba wani magana mai tsawo ko hira a tsakanin mu saidai kowa yayi sha,anin gaban shi a dakin ko ina tunane ko taba waya wanda hakan yakan daukeni wani lokaci mai tsawo a wurin shi.
Wanda bai sani ba sai ya dauka wani hiran arzikine ko wani abin miji da mata ya tsayar damu a cikin dakin lokacin.
Alhamdullahi gaskiya don jikin nasa yayi sauki sosai saidai da alama har yanzu baya jin karfin jikin nasa ko kadan.
Karfin hali irin na mazane kawai yakeyi yana fita don kada ya zauna don da mace ce nasan har lokacin nan tana kwance tana fama da jikin ta.
Saidai wani abin dana dan kula dashi a yanzu shine irin kallon da yaya yakan min wani lokaci kallo ne mai tare da ma,ana iri daban daban.
Na kasa fahintar dalilin hakan da yake min wani lokaci idan zamu hada ido dashi zaiyi saurin kawar da idon shi gareni.
Gashi a yanzu ya dora min nauyin hada mai ruwan wankan shi duk safiya duk da komai a hade yake amma dole sai naje na hada mai zai tashi yayi.
Haka cin abincin sa dole ina wurin har ya gama zamu tashi duk da ba wani hira tsakanin mu a lokacin.
Ga mami da ke kira yanzu kamar ta bude ido ta ganta a kasan takeji don zata kira akalla sau uku a rana tana jin halin da muke ciki a nan.
Wanda wanan kiran har ya soma samin zarginta kan dan nata watay ita duk abinda yakeyi ma bata ganin laifin shi ashe ga hakan don yadda naga ta damu da halin da yake a yanzu.
Har take fadin idan azumi yazo zasu shigo su ganshi su danyi azumi tare damu suna jiran Aisha ta karasa karatun tane aiyi bukin yayye su yasa basu zo a yanzu ba.
Tabdi ba zuwan mami din ba sai irin takura min da sukeyi idan sun zo da fanin laifina ko kyashin da baya boyuwa a fuskokin su.
Shiko cewa yayi yana farin cikin da zuwan su indai zasu zo din suyi azumin a tare damu zaiji dadin hakan..
A raina nace tunda kai da uwarka baku da matsala duk tudun laifin ka bata ganin hakan gareka sai ma so da take nuna maka zallah ai kace kana farin ciki da hakan .
Muryan shine ke fadi yana kallona yace zainab na san kema zaki fini jin dadin hakan tunda yanzu naga naku da mami din yanzo daya har tana maki sako a boye ko ?
Ban sani ba don wani aiki sai mami na sani da sauri na dago kai na kalleshi tare da fadi cikin mamaki sako kuma ?
Daga wurin mami yaushe mami tayi min sako dana zo kasan nan idan ma har mami zata aiko min wani abu ai ta hannun ka abin zai fito.
Hakane fa kuma ya fada yana murmushi yana batun mikewa tsaye na sake fadin sai dai idan ka manta baka ban sakon ba yana hannun ka ?
Banjin yana a hannu na gaskiya sai dai idan na manta nima nake ganin kamar ke ra aikowa anywhere forget it ba damuwa.
Bayan shi nabi da kallo har ya fice kafin in tabe baki ina mayar da kaina ga kujeran da nake zaune tare da lumshe idanuwa na nadan lokaci.
Tunda mami ta furta zata zo yake shirin zuwan su din duk da bai fads ba nasan abinda yasa ake wasu yan gyare gyare a gidan wanda ya dace.
Dare ne naga bai shigo ba yasa na shiga part din shi tunda nasan yana gidan bai fitan nan da yakeyi a baya yanzu ya daina tunda yayi ciwo baya yawan fita koda rana da ya dawo office yana gida sai kuma gobe idan ya fita.
Wando ne da riga tie a jikina baki rigar kuma yellow mai dan fadi wuyan shi ma da fadi sosai.
Sai dai rigan ya dan sauka ya rufe min mazauna na rabi kayan sun matukar karban jikina sosai sun dane min jiki da kyau.
A falon shi na saneshi zaune da kwalba da cup a gaban shi ya zauna ya mike kafafun shi saman karamin table din dake gabab shi .
Yayin da dukkan maballeyan riganshi suke bude mashi duk chest din shi a waje ya dafe kanshi da hannun shi daya kamar mai barci.
A hankali na tako zuwa inda yake zaune ganin kamar yana barci yasa dana kare mai kallo nake batun juyawa na bar dakin.
Ina zaki kin shigo kuma zaki fita yana sauke hannun shi data dafe goshin shi yake fadin hakan .
Kallon kwalban da cup nayi na turo baki kafin nace naga kamar yau dakin yafi karfin shigana ai don naga kamar ka gama warkewa yanzu.
Dan murmushi yayi yana gyara zama tare da fadin zoki zauna a nan mu sha tare don na yau din tare zamu sha dake ai.
Wa ni na fada har ina nuna kaina da hannuna nace Allah ya tsare ya kareni don ni na zabi na Allah da wanan na nuna da bakina inda kwalban yake.
Kanshi ya dan mayar ga makarin kujeran ya lumshe idanun shi a hankali yace yana taba wurin da yake zaune ta gefe zo zauna a nan nace maki ko ?
Kallin shi nayi kamar in tafi nake ji sai kuma wata zuciya tace min naga iya gudun shi ga hakan sai na tako na zauna kamar yadda yace min din.
Na zauna a dan takure ban sake jikina ba da zaman ya dago yana zuba abin a cikin kofi ya miko min yana fadin karba ki dan sha.
Wani kallo nayi mai ina kawar da kaina gefe daya nake fadin har abin yakai can yaya ka koya min shan wanan haramiyan abin ?
Dauki kwalban ki karanta idan na cutarwane na baki yana komawa yadda na sameshi da farko saman kujeran.
Ban karba sai mikewan da nayi na fice part din ga baki daya raina a bace ina tunanen irin halin yaya da abin haram ba komai bane a gareshi shi ?.
Har ni yakecewa yau wai nasha giya a tare dashi don kawai ya mayar dani yarinya ko me ?
Ko wawiya ya daukeni ko bakyauya har yanzu ban san komai ba kan hakan har yake kokarin juyani ga halaka.
Ranan banyi barci ba sai na daman sanin sa da nayi ga baki daya ina jin wani irin tsanar shi yana karuwa a zuciyana lokaci guda.
Washe gari ma kin shiga nayi wuri shi don karya shigo mi part sai naki bude ko ina da safe na lafe a dakina kawai.
Don ranan bamu zuwa makaranta daga ni har sadiya muna gida a kwance abin mu shidai ne mai fita baya dadewa koshi a irin wanan ranan.
Ganin bamu bude kofan mu ba yasa shi fita bai ganmu ba sai text da yayi min a waya dan guntu da cewa nina fita sai na dawo.
Na tabe baki ina jefa da wayan saman gado don haushi tare da fadin dan iskan mutum kawai ka fara bata kanwar ka kafin ka bata ni mana
Daya dawo din ma bai nememu ba part din shi ya nufa ya rage kayan jikin shi ya shiga ban daki ya watsa ruwa a jikin shi don yaji sanyi..
Sai bayan da yayi sallah isha,i ne ya fito zuwa part din ya samemu zaune a falon mu muna kallo sadiya ce ta fara gaidashi da dawowa.
Sadiya yau ba assignmemt din ke nan kika tsaya kallo a nan tace yaya ba test saidai zamu fara exam bada dadewa ba.
Ya kai zaune tare da kallon inda nake yana fadin ya zainab kuna lafiya dai ko yau banji duriyan ki ba gidan nan.
Baki na turo gaba ina fadin lafiya nake bagani ba yanzu a zaune au har yanzu fushi kikeyi kan wanan maganan ?
Dan dagowa nayi tare da kallon shi watau shi baima dauki hakan komai ba ke nan har yana tambayana yanzu.
Amma ke zaki iya bani abu insha ba tare dana sani ba koda abin zai wahalal dani a rayuwana idan nasha in dai bukatan ki zai biya ban damu da hakan ba ?
Wani kallo nayi mai na mamaki sai na dukar da kaina kasa kafin na dago nace nasan ko na baka ba wanda zai cutar dakai bane sai dai ya taimaki rayuwan ka ai.
Umm,humm haka kike tunane ko a naki zaton ban tunanen komai don nasan daidai nake ga abinda nayi balle ma banyi ba din sai abin da zuciyar ka ya baka kan hakan.
Mikewa yayi tsaye ya fara tafiya ina kule dashi a dan kwanakin nan idan yana tafiya wani lokaci sai ya dafe gefen cikin shi da hannu daya yakan iya tafiya da kyau.
Bin shi nayi da kallo har ya fice kodana juyo sadiya ta mayar da hankalinta gareni tana kallona.
Da sauri ta duka kamar bani take kallo ba nabi lafiyan kujera na kwanta ina tunane a raina kardai ace yaya ya fahinci na saka mai magani a dubai ?
Idan ko hakane na shugo uku ashe nawa ya sameni ke nan dashi tunda gashi ya fara sake min magana a fakaice kan hakan.
Kamar maya tasan halinda muke ciki sai gashi washe gari ta fito min da zancen tana tambayana ko nayi amfani da wanan maganin kamar yadda akace nayi din.
Ajiyan zuciya na sauke kafin na fara bata labarin abinda ya faru sai kawai naga tana tafawa tare da fadin ki godewa wanda kike bautawa da yasha wanan abin zee.
Don na yarda da aikin kakata hundred pacent kan wanan da wuya ya kara kallon wani abin da zaisha har ya fita hankalin shi.
Shi dayan fa kikai ga amfani dashi ta tambayeni nace ai lokaci guda duk na hada nayi amfani dashi tace Budah da cewan wai abin bautan su.
Baki tsoron hakan zai iya tabashi don karfi ke ga maganin sosai ashe da gaske da ake fadin ku bakaken fata kuna da karfin hali sosai haka.
Tsoro naji wani tunane yazo min dana tuna da yana yawan dafe gefen cikin a yanzu saidai ban san dalilin da yasa yake hakan ba da yake yi ?
A maraice na bata labari irin yadda yakeyi a yanzu tun bayan ciwon da yayi na fita hayacin shi a Dubai.
Dan tunane ta tsaya tayi kafin tace ina ganin sai mun koma wurin kaka muji ko akwai wani abinda yasa yake hakan.
Zamu iya zuwa yanzu na tambayeta don na riga da na tsorace a yadda ta nuna min illan abinda nayi lokaci daya ba daidai bane.
Dan duban lokaci tayi da dan tunane tace zamu iya don zamu iya zuwa mu dawo lojacin tashi ma baiyi ba a yanzu.
Mota muka shiga tafiya mai dan tsawo ya kaimu kauyen nasu dake da dan nisa da cikin garin mun samu kakan a waje tana shanya wasu ganyayyaki tayi muna taro na arziki.
Mun zauna an gagaisa ne maya ta kora mata bayani kamar yadda na fada mata tana mamulan baki irin nasu na tsofi take fadin .
Kinyi aikin yarinta yarinya amma yanzu shan maganin yakai kamar sati nawa a jikin shi na dan yi tunane tare da dago kai na bata amsa baikai wata daya ba ina gani.
Duduke ta mike zuwa cikin dan gidan ta ta dan dade ciki ta fito da wani abu kamar kankara da wasu dai maganin kala biyu a hannun ta ta miko min.
Karba nayi da hannu bibiyu cikin girmamawa take fadin ki masa amfani da wanan zai daina jin abinda yake ji din da yardan mai duka.
Don su basu yarda su ambaci Allah ba don basu san shi ba basu bauta mashi na karba ina istigifar ni dai bukatana kada ya halaka a sanadiya na shine fatana ban yarda da abin bautan ta ba tunda na fada tarko ko.
Mun dawo yamma yayi sosai don haka ina sauke maya gida na nufo don nasan yanzu sadiya tana gida zai turo a dauke ta .
A falon gidan gaba daya na samesu zaune tare dashi suna zaune shi yana waya ita kuma tana kallon tv na shigo a gajiye.
Da sauri sadiya ta taso tana rungumeni tare da fadin I miss you sister tun safe na shafo kanta dake bude ina fadin bakya ji baki son saka hula a kanki sadiya.
Na nufi inda yake zaune yana waya amma hankalin shi yana gareni tunda na shigo yana waya da hannu ya yafuto ni nazo dan hugging dinsa nayi ina fadin miss you.
Ya dan rungumoni na dago zan juya muryan shine ke tambayana me kika jeyi sea side yau da mamaki na dago ina kallon shi.
Na yadda har yasan inda naje na wayance da fadin munje duba wani projects ne a can bakin ruwan yaya baki kirani zaki tafi can ba saida na gani.
Da wasu course mate dina muka tafi ban san zamu dade a can haka ba na dauka zamu dawo da wuri na bashi amsa yace take time next time.
Bana son kuna zuwa nisa a garin nan don akwaisu da nuna wariyan fata wani lokaci kada wani abu ya samu mutum.
Nace insha Allahu a raina kuma sai mamaki nakeyi yadda yau kawai har ya gane na tafi wani wuri na daban ba cikin school ba.
Na dai samu na shige ciki don duk na gaji don na dan watsa ruwa don wani irun yunwa nake ji sosai a lokacin saboda banda ruwa ban iya cin komai a waje ko ruwan sai shanshi ya kama dole zan sha idan na fita.
Don kasan kafirai ne ba zan yarda ko bread din su inci ko snacks din su ba don amfani da man alade ba komai bane a wurin su su yasa nake kiyayye hakan.
Duk da yunwan da nake ji saida na rama sallolin dake kaina har isha,i saida nayi kafin na fito na nemi abincin da zanci.
Shine ya shigo ina zaune ya saka wani jallabiya blue a jikin shi tafiyan shi kawai zaka gane cikin karfin hali yake a yanzu duk ya rame ya zube har duhu ya danyi.
Zama ma da kyat ya kai zaune na dago kai na dan kalle shi cikin tausayi tare da sada kaina a kasa ina ci gaba da cin abinci don ba a dining na zauna ba.
Jin abincin ya fita min rai nayi tunda naga yanayin da yake ciki din zuciyana naji ba dadi lokaci guda.
Ban san lokacin da bakina ya furta mashi baka da lafiya har yanzu yaya don yanayin ka ya nuna hakan na fada ina ture abincin a gabana.
Hannu ya mika ya jawo plate din zuwa gaban shi ya dan diba ya fara ci ba tare da yayi magana ba saida yayi kamar cibi uku ya koma ya kwantar da jikin shi saman kujera yana dafe goshin shi yace.
Ban san meke damuna ba zainab kwata kwata na rasa gane kaina ga baki daya bana jin dadin komai a yanzu tunda ciwon nan ya kamani wallahi.
Komai gaba daya ya fice min a rai haka bakina bana son ko kadan in saka abu a cikina sai naji shi kamar wuta na saka indan naci.
Kaje asibiti na tambaya da sauri naje sunyi gwaje gwaje sunce basuga komai a tare dani ba har yanzu.
Innalillahi nace ko mami zamu fadawa ta san halin da ake ciki da sauri yace No kada ki fada mata tunda zasu zo ai ki barshi ki dai tayani da addua kawai shinafi bukata a yanzu.
Rabin addua na a kan kane ne ko yaushe yaya sai dai idan banyi sallah ba aiko na gode da wanan taimakon ke alherice zainab a gareni na sani ke sakon Allah ce zuwa wurina yanzu na gane hakan.
Dago kai nayi na kalle shi yace kwarai nasan da hakan ba yau ba zainab ke din kin kasance a yadda banyi tsamani ba.
Da farko wani sashe na zuciyana yakan min tambaya a kanki amma yanzu ta haska min matsayin ku a gareni daga ke har sadiya .
Ban kara gaskanta zuciyana ba sai wanan lokacin da na kwanta ciwo na samu taimakon da ban taba zato ba a wurin ku.
Zanma ce ke don kece mai komai da yadda hankalin ku ya tashi a kan hakan ya nuna min matsayin dan uwa ko mace a kusa da kai a yanzu.


ZAINAB IDRIS MAKAWALITTAFIN KUDINE KI BIYA KI KARANTA YAR UWA DON GUJEWA FADAWA HAKKIN WANI NA SAUKE NAUYI NA FADA ALLAH YA BADA IKON TSAREWA ALLAHUMA AMIN.


Bayan mun dan gama zaman da zamuyine ya samu ya mike da kyar muna mai sannu da jikin yana dafe da cikin nasa ta gefe haka ya bar falon ya tafi.
Na sauke ajiyan zuciya bayan fitan shi daga part din ina mikewa tsaye kallon sadiya nayi ina fadin shige ki kwanta dare yayi yanzu.
Ta mike ba don taso ba ta shige tana turo baki gaba na kashe wutan falon na shige ciki don in kwanta saboda gajiyan dana debo a ranan.
Saidai kodana kwanta barci ya gagareni sai faman tunanen abinda ya wakana a falon tsakanin mikewa nayi zaune don kwancin ya gagare ni a lokacin.
Tabsa yaya yana ji jiki don iyanzu yakai ga fadi da bakin shi ga alaman hakan kuma ina gani shawara na fara yi a zuciyana na yadda zan bashi wanan abin da tsohuwar ta kara bani yasha a yanzu.
Abinda ban sani ba shine ashe yana can daki yana mukurkusa shi kadai yayi amai tun yana iya tashi yaje yayi har tashin ya gagareshi.
Da kyat ya iya daga waya ya kirani muryan shi kawai ya isa ya sanar ma da halin da yake ciki a rude na mike dagani sai rigan barci zuwa dakin nasa a rude.
Kai ba dadi a yadda na same shi a kwance kaca kaca a cikin amai dan ihu na saka a cikin gigicewa yayi saurin bude idanun shi ya sauke su a kaina yana fadin.
Kada kiyi kuka zainab nasan nina jawa kaina wanan kila giyan da nake sha ne yake min haka a yanzu .
Ka bari in baka wani magani da nake dashi kila zai taimaka ma kafin mu kira muje asibiti dan murmushin karfin hali ya sake a fuskan shi.
Haka yasa na juya da sauri na nufi dakin na tsaban rudewa ma baisa naga maganin da farko ba sai na dauka nayar dashi ne wurin sauri.
Baki yar ba zuciyana ya bani hakan na tsaya nema a tsanake na ganshi can kasan jakkana dana jefa.
Da sauri na dauki na nufi kitchen din mu na hada na kai mashi baiki sha ba da taimakona ya mike ya shanye ga baki daya ya koma ya kwanta.
Kallon gadon daya baci nayi cikin dabara da hikima na gyara ko ina cikin ikon Allah sai gashi ya mike wai zai kewaya shine na samu daman gyara ko ina yadda nake so.
Da alama ya samu sauki sosai don har ruwa ya watsa a jikin shi kafin ya fito don yaji dadin jikin nasa daya sake mai.
Nina taimka mai ya saka tufafi a jikin shi can kuma ya yunkura kamar zai kara amai da ban san lokacin dana tallaboshi ba sa sauri.
Yana ta kokarin kakarun aman bai samu fitowa ba ya koma ya kwanta sai barci ganin haka na dauki wayan shi na nemi layin mami na kurata.
Tana dauka take fadin jafar ya akayine ya jikin da sauki ko nace a dan maraice mami bashi bane nine gashi kwance yau jikin ba dadi sosai.
Innalillahi tace a rude yanzu kuna asibiti ne ko gida muke mami idan na masa maganan asibiti baya son zuwa ne.
Ke wata irin yarinyace da har yanzu baki waye ba zainab idan kin masa magana baiji ba baki kaisa ko ki fadawa abokan sa suzo su kai shi mana.
Ban san abokan sa ba mami kuma yakan ce dani ai yaje asibitin idan na matsa mashi din.
Zainab idan kika bar min da ya halaka a kasan mutane ba zan yafe maki ba wallahi.
Mamaki da rudewa ne ya kamani lokaci guda na rasa amsan da zan bata sai kawai na kashe wayan gaba daya na aje a gefen shi don kunnuwa ba zaici gaba da iya sauraren wanan matar ba a yanzu.
Juyawa nayi inda yake kwance na dan kalleshi barci yakeyi har lokacin nima na dan kwanta a gefen har barci ya dauke ni ban sani ba a wurin.
Washe gari abin mamaki ko daya tashi sai naga ya mike da kansa saidai rashin karfin jikin da baida shi a lokacin.
Ya dan dade a cikin ban dakin kafin ya fito ya tayar da sallah a tsaye nan nasan yaji saukin jikin sosai mamaki karfin magani irin nasu nakeyi a raina.
Ya dade zaune yana addu,a kafin ya mike ya koma ya kwanta saman gadon ya koma barci ranan dai ban fita ba don yanayin da yake ciki din.
Yakai wani lokaci mai tsawo yana barci kafin ya tashi yana neman abinci yaci ya sake yin wanka ya fito a lokacin ya kunna wayan shi dake kashe.
Kamar jira ake ya kunna kira ya kama shigo mai wanda kiran daga nan chaina ne abokai da wuri aiki suke kiran shi.
Ban fada mai komai kan zancen wayana da mami ba saida ta kira shi da kanta tana fada wai haka kawai don keta na barshi gida ina kallon zai halaka ban kira a kaishi asibiti ba.
Haba haba mami yarinyar nan fa tayi kokari sosai a kaina kuma ko yanzu tana ciki yin sa ne.
Kaima ai kana kokari akan su don me ita bazatayi ba har tana fada min wai kana gidane a kwance.
Haba mami zainab bata cancanci wanan kalamin ba a gurin ki don nasani ta tare shi da fadin ta yata zata biyewa rashin hankalin ka ta barka a gida.
Ko dai meye ai mami zainab mata tace tasan zafina tasan ciwona don haka yarinyar nan tayi duk yadda akeso fa bai yarda uwar tayi wani magana ba kuma.
Suka dan dai taba hira akan ciwon nasa tana tambayan shi ainihin abinda ke damun shi tare da kara nuna mai bakin cikin ta kan halaiyan da yake yi wanda take zaton shi yaja mai wanan ciwon haka a yanzu.
Har dare yana duban yanayina ko zan nuna wani bacin rai kan abinda mami din ta fada mai nayi mata baiga alaman hakan a wurina ba shima sai ya share zancen baice dani komai ba.
Da dare na shigo na gaidashi tare da bashi abinci ban fita ba saida ya gama na mike zan bar dakin naji ya ambaci sunana da fadin .
Zainab haka yasa na juyo da sauri baiyi magana ba yasa na dan kara matsowa inda yake ban dai zauna ba amma na tsaya a cikin ladabi yake fadin.
A lokacin daya lumshe ido idon shi a rufe zainab me kika bani nasha jiya ne naji sauki haka da sauri ?
Magani oh wanan maganin ya dade a wurina dama dashi nazo tun daga gida na waraka ne kan cututuka ko wani iri na bashi amsa.
Ya bude ido yana kallona kamar me nazarin wani abu ya ce dama kina dashi tare dake baki bani nasha ba nake ta wanan wahalan haka naji dadin magani sosai ina shan sa kamar an zare mi ciwon naji lokaci guda.
Ban taba amfani dashi ba na fada ina juya don na matsu in bar wurin a lokacin kada ya kureni har ya gane ba gaskiya na fada mai ba.
Kwana biyu kwatsam su mami suka diro garin shi kanshi bai san da zuwan su ba ban nuna mata komai ba don tun lokacin da mukai wayan nan da ita wani abu bai kara shiga tsakanin mu ba kuma koda wayane.
Don sai naga kamar kwata kwata dai mami bata yi danine a rayuwan ta don banga laifin da za a dora min kan mutum mai shekaru kamar ya j ace wai nice zan matsa mai ya kula da kansa bayan shine ya kawo mu kasan ai.
Nan muka shiga dawai niya da su kamar ba komai a zuciyana sai dai a gaskiya na barwa kaina duk wani abu da nake shiryawa a yanzu game da kowan su gidan.
Lafiya kalau zan shiya masu abinci idan masu aiki sun gama ba zan fita ba sai na gama dasu don wanan tafiyan ba irin wancan bane da sukazo da yawan su .
Wanan daga mami sai samarinta biyu da Aisha kawai suka zo part daya aka bar masu don hakane ba wani takura a tsakanin mu yanzu.
A yadda mami take matukar son diyan ta wanda a yanzu na kara gane hakan sosai yadda duk da ya J yaji sauki a yanzu.
Amma hakan bai sa wai mami ta nuna wai ita jinyar jafar din takeyi ba a fili tana nuna tafi kowa sanin zafin dan ta da sanin abinda yake damun shi .
Wanda banyi tunanen cewa jafar din zai fada mata ba don da zai iya fadiawa wani nasan nice ta farko da zai fadawa hakan.
Kawar da ido da kai ga komai yasa mami din bata samu wani kafan yi min wani rashin mutunci ba don haka muka zauna lafiya da kowa a cikin har azumi yazo suna kasan tare damu.
Ranan a na zaune da safe samarin basa ciki suna waje sai shi da mami da Aisha ne sai ni da na shigo gaida mami din da safe zan fita zuwa school.
Baki fita ba ke nan har yanzu kina gidan nan ya fada yana zaune a kasa kusa da kafan mami din abinda ban taba ganin yayi ba tun zuwan mu kasan zama a kasa.
Karatun ai ba wai ta saka a ranta bane nake ganin mami ta fada ya dan gyara zama yana fadin ai mami zainab ta saka karatun nan a ranta sosai kuwa.
Zainab din zaka ban labarin halinta a yanzu kuma jafar don ta zama matar ka komai ko ta canza ne ban sani ba ?
Sorry ma na mance kin fini sanin halinta ai tana nan har yanzu da sanyin halin nan nata ai sai mami din taja wani tsuki tana kawar da kai.
Aisha tace ya j ai yanzu ba zaiso a fadi wani kalma a kan zee ba koda tayi laifin ma balle yana ganin batayi ba .
Aisha ke nan ki bar ganin mami da zainab suna abin su na uwa da yarta kice zaki saka baki tsakanin su har yanzu sai Allah ni zan baki labarin hakan.
Ni dai ina zaune a inda nake ban ce da kowa kala ba a cikin su naji yaci gaba da fadin a daidai lokacin dana mike tsaye yana cewa.
Har sako fa mami zata aiko dashi tun daga can ba zan san da hakan ba sai idan tunanena ya bani haka.
Sako kuma naji mami ta fada da dan mamaki ni dai fita nayi ban karasa jin zancen su ba.
Sai bayab na dawo ne na shiga gaida ita ta tsareni tana tambayana da fadin zainab jafar ya gaya min kece kika bashi magabin da yai sanadin barin shan giyar sa ko ?
Na dago kai da mamaki tace ya fada min komai don shi a nasa zaton ko nice na aiko da abinda kika bashi din har yaji sha ya fice masa a rai ina tsaye ne a lokacin sai nakai zaune.
Kafin ta kara fadan wani abu jalal ya shigo dakin yana fadin mami garin nan yana da dadin azumi sosai don basu da zafi irin namu can Nigeria gaskiya.
Jekiki huta zamuyi maganan daga baya mami ta fada don ganin jalal din ya kai zaune a lokacin .
Ya dago ya kalleni yana fadin dama magana ake irin na uwa da yarta nima dai ina ganin irin auren ya j zanyi mami in samu mata kamar zainab din ki don bana son mace irin Nuriya gaskiya.
Fita nayi daga dakin ina dan murmushi don abinda ya jalal di ya fada saidai zuciyana cike da zargin maganan mami yake alokacin
Bata kara min maganan ba nima haka banwa ko J din maganan ba saida akai azumi ashirin suka tattaro suka dawo Nigeria.
Munyi sallah lafiya wanan sallah har idi muka tafi wanda hakan bai taba faruwa damu ba tun zuwan mu a gida zamu dai zauna .
Sai dai mu kalla yadda ake bukukuwan sallah a kasashen duniya wanda mu nan cikin gida muke babu wani celebration da mukeyi.
Sai gashi a wanan shekaran tun da daren muka bar gidan mu muka kwana a wani hotel a cikin wani unguwa ashe a can ne masallacin su yake da suke sallah a garin.
Bayan an sauko ne motocin mu suna jiran mu muka dawo namu gidan wanan kan mun san ayi sallah don yadda yaya ya nuna muna har kwana biyu muna shagalin da murna da kai ziyara a gidajen yan uwa musulmai dake kusa don suna da musulmai tsararu a cikin kasan sosai ashe.
Hutun sallah ba yawa ga ma,aikata don haka sati daya mukayi ana shagalin muka koma makaranta don ci gaba da karatun mu.
Yaya kan a bangaren shi jiki yayi sauki sosai don bai wanan dafan cikin da yake yawan yi a baya yanzu.
Gashi yayi wani kyau raman da yayi don zafin ciwo a baya duk yanzu yana shigewa ba a ganin wanan sosai a jikin shi don dan cikowan da yakeyi yanzu ba wannan kaman.
Sai dai ina yawan tuna halaiyan mami na nuna kiri kiri son danta akan komai da take min don na lura nami ba ganin laifin dan nata takeyi ba asalima tana kokarin dora komai ne a kaina a ganina.
Don ko dan zaman da mukayi dasu anan duk da da farko taso nuna hakan a fili amma daga baya sai naga kuma ta canza ta daina nuna min wani abu.
Nima sai na dauka a hakan nake nuna ba komai a raina don haka kowa ya aje a ranshi da ba komai din dai.
Ganin yadda yanzu yaya ya koma wani silent bai son hayani duk da dama can din shi din ba mai hayaniya bane sosai amma dai sai na yanzu din yayi yawa sosai.
Don zai iya zama a wuri duk abunda zamuyi ba zai ko daga kai ya kalli mutum ba balle mu saka ran zaiyi magana kan kiriniyar mu har ya gaji da zaman shi ya tashi a wurin zuwa part din shi.
Gama sadiya da har rawa da marming zata dinga yi koda yana zaune don ba karamin sabawa sukayi ba dashi sosai a yanzu.
Wanda tun ina zargi a kan hakan har yakai na debe komai a raina nima mai dan girman bai damu dani ba balle ita da keda sha uku yanzu cif a duniya.
Yau ma kamar kullun ya dawo wirin aiki da yanzu mun saba dashi idan ma ya dora dan dakiku a kai mun sani zamu fara fadin yau yaya bai dawo in time ba.
Shiko da ya dawo baya zuwa part din shi kamar yadda yakeyi a baya nan wurin mu zai shigo direct mu gaisa ya dan zauna damu na lokaci kafin ya shige part din shi sai kuma bayan sallah isha,i zai fito aci abincin dare a tare tun bayan zuwan su mami wanan ya zama muna dabi,a a gidan yanzu.
Zaune nake na tasa laptop a gaba ina aiki ban san shigowan shi part din namu ba don itama sadiya ta shiga ciki dauko littafin da take assigment kan shi.
Muryan shi ne daya duka bayan kujeran dana zauna na mike kafa ina aiki a cikin system din na shagala ga karanta abinda nake sercheing a computer din.
Naji muryan kamar daga sama yana fadin wanan ai da wuyan fanhinta da kin bi ta cikin Google direct zaifi ki fahinta ai.
Ganin yadda na dan kadu ne yasa ya dan shafo kaina yana fadin kin cika tsoro da yawa duk security din dake gidan nan amma kike tsoro haka zainab ?
Ban ji fitowan ka bane yaya sai muryan ka danaji a kaina yasa na tsorata da hakan.
Zagayowa yayi ta gabana ya zauna yana fadin when last kukayi waya da mami tun bayan komawan su gidane wai ?
Da sallah ma ai munyi waya sau biyu dasu na bashi amsa ina dagowa daga duken da nake ina kallon shi don jin dalili tambayan nasa.
But tace dani mana yanzu kin daina kiran ta duk da na fada mata kin fara exam a yanzu baki da lokacin komai saidai tayi fada cewa exam ai ba zai hana ki kirasu ba .
Zan kira na bashi amsa ina tagumi don nasan wani abin ke shirin tasowa kuma a kan wanan maganan da mami din tayi yanzu.


ZAINAB IDRIS MAKAWABARKAN MU DA SHIGA WANAN WATAN MAI ALBARKA YAN UWA UBANGIJI ALLAH YA SADA MU DA ALHERIN DAKE CIKIN WANAN WATAN ALLAHUMA AMIN, , , ,

LITTAFIN KUDINE YAR UWA KADA KI MANTA DA HAKKAN DON KAUCEWA SHIGA HAKKIN WANI, , , ,


Akwana a tashi ba wuya a wurin Allah yau gashi har na kamala karatuna a ta fannin fasahar kimiya a kasan chaina inda na fito da sakamoko mai kyau wanda yaya jafar ya nuna jin dadin hakan a fili har ya kasa boye farin cikin shi ga hakan.
Yayin da sadiya take matakin yar gaba da primary a shekara na biyu zata shiga na uku a yanzu daidai lokacin dani na kare nawa karatun .
Har lokacin muna matsayin kannesa ne ga ya J da muke zaune a gidan shi wanda kuma ta dalilin shi muka samu wanan matakin na ci gaba da muka samu a rayuwan mu.
Eh ba zance ya j ya daina duk wasu mugayen halaiyan sa dana san su a baya yana yi ba don a yanzu in ma har yana yine saidai in a boye yake wanan rayuwan do banga hakan a gare shi ba gaskiya.
Asalima a yanzu ga baki daya ya koma kamar ba ya J din da muka sani a baya bane don ga baki daya ya canza gaba daya .
Ya koma wani irin mutum mai taushi da tausayi ga ibada da kula a tare dashi ga natsuwa da kamala da kullun yake kara sauka masa.
Banga wani shirin da yaya yakeyi don zuwan mu gida ba asalima ni yanzu da zaman gida kawai nakeyi yasa wanan damuwan yake damuna a raina har karshe na kasa boye hakan a zuciyana.
Yau tun safe na tashi da wanan damuwan a raina gashi ni kadai ne a gida haka zan wuni daga kallo sai in shiga interneat ina searching shine kawai aikina.
Ina zaune a babban falon mu tv na aiki saidai ba kallon nakeyi ba hankalina yana gun computer na dake gabana ina hada wani kimiyan da nake tunanen hadawa danaga ana tallan shi ko ina a kasan.
Pretty me kikeyi haka ya fada a bayana na dan dago kai na kalleshi tare da dan sake murmushi a fuskana ina fadin yau ka dawo da wuri haka yaya ?
Na dawo ne don nasan ke kadai ce zaune a gida yanzu yasa naga ya dace ba dawo ba dubaki ashe ma na manta kina da abokin hira gashi a gaban ki.
Wanan bai rage min komai yaya sai kewan gida da yanzu yake damuna sosai ina son zuwa gida na ga Inna ta da yan uwana yaya .
Wani kallo yayi min daga inda ya zagayo ya zauna a gefena gida a yanzu baki ganin yin hakan zai taba karatun sadiya ?
Ai ba don karatun ta muke nan ba na fada a dan hasale OK tunda ke kin karasa naki zaki fadi haka ko ?
Ba hakana bane yaya gani nayi kayi alkwarin hakan a baya don Allah yaya ka kaimu gida mu duba su yanzu kusan shekara biyar ke nan muke nema rabin mu da gida fa.
Ba yanzu ba zainab gaskiya don so nake kici gaba da karatun ki a cikin shekaran nan in Allah ya yarda.
Ba zan tsaya karatu ba a nan gida zan koma karatun ya isheni haka yaya nima fa haifana akayi zanso na samu ladan da ko wani da ke samu ga hakan.
Bai min magana ba sai mikewan da yayi lokaci guda ba tare da yai min magana ba ya fice a falon na bi shi da kallon mamaki.
Wanan dan maganan ya jawo muna dan tashin hankali a tsakanin mu har yakai munyi dan kwanaki baya kula wani harkana a gidan yana shan kamshi dani.
Ban shiga harkan shi ba duk da hakan yana damuna sosai don sai yanzu na san ashe ba karamin sabone tsakanin mu a yanzu.
Tun ina daurewa har ya kai na kasa hakan ina shawara kan na same shi na bashi hakkuri sai dai nakan tambayi kaina idan naje ince masa me ?
Ban san ya ake abi sallon ba miji hakkuri ba indan irin haka ya faru a tsakanin su balle mu dake zama irun na wacin gadi da juna kinga hakan ashe zai min wuyan fahinta don nawa kaddaran auren yana daban dana sauran mata gaskiya.
Don haka ban kara gigin wanan shawaran a raina ba don haka na kawo ido na zuba mai kawai na bisa a hakan kowa yana harkan gaban shi a tsakanin mu.
Ina kallo sai dai ya dan shigo yai magana da sadiya ba zai dade ba ko ya zauna zai fita sai kuma gobe.
Saidai hakan ni bai hana in ya shigo da safe na gaidashi ba ya amsa min a dakile gashi ba inda zan kaishi kara inji sanyi .
Wurin mamine nasan ko nakai goya masa baya zata yi kan hakan karshe ma ta kara min wani zafin da yafi wanda nake ciki a yanzu din.
Don kanshi ko me ya gani ranan muna zaune falo da dare da sadiyan ba wani hira mukeyi ba sai rage dare a tsakanin mu ya shigo.
Ga hasken kwan falon na wuta ya haska mu tar ina zauna a cikin wani riga mai shara shara a jikina rigan baida hannu sune irin kayan dana sakawa a kasan don yana sauka min har kasa .
Gasu su ba jallabiya bane ba kuma abaya ba haka suke kamar kayan yan brazil da sukafi amfani dashi wurin wani bukukuwan su na shahara.
Sai dai ni da ba bukin nake zuwa ba a gida nakan saka abina ko shi ba don kwaliya ba don dai kawai ina dasune da yawa nake amfani haka dasu.
Kayan suna min kyau sosai a jikina idan na saka saidai ba wanan a raina nidai zan saka kawai don ba wanda zan burge ga hakan idan ma nayi ne don shi din ba wai burgeshi zanyi ko jan ra,ayin shi ba a kaina.
Sadiya yau kuna wani show ne a nan banda labari ya meka gani ta fada tana dagowa daga kwancen da take tayi rub da ciki saman kujera.
Gani nayi dai yau kunyi wani kyau daku ko zamu fitane ku ga gari ko kada wanan kwalliyan haka ya tafi a banza.
Ba a banza bane yaya tunda ka gani har ka yaba ai idan mace tayi kwalliya a mijin ta tayi akace .
Daga inda nake zaunw na watsa wa sadiyan wani kallo mai harara don abinda ta fada din nake fadin.
Miji sadiya yaushe nayi auren har zan wa mijin kwaliya ya gani dani da wance bata da aure babu bambanci a tsakanin mu a gun wasu daine nake matar aure kamar su inna da sauran yan garin mu.
Maimakon yai fushi da abinda na fada sai gashi ya wasance yana fadin sadiya kin yarda dav zancen nan nata wai ?
Gaskiyane yaya duba ga har yanzu bata haihu ba tana da wanan hujjan don burin su inna a kullun tayi waya damu zanji tana tambaya wai har yanzu shiru babu labarin haihuwa gareta ?
Killa shiyasa ta fadi hakan yanzu duba ga sauran yan kauyen mu sa,annin auren ta ai duk suna da haihuwa biyu ko ukku wasun su ?
Sadiya naso ace kin girma a gaban su inna da wanan wayau naki bazai dauki garin naku ba mema sunan kauyen naku ?
Lah yaya har ka manta da sunan garin namu niko ko barci na tashi akace min meye sunan garun mu zan ce Anchau da gudu.
Yau hausa suke a tsakanin su sosai don bai faye mata magana a cikin yaren hausa ba nice dai koda yaushe hausa nake mata a tsakanin mu don kada mu manta da yaren mu mu koma gida ai muna dariya wata rana.
Idan ba haka ba sai ince da yanzu sai turanci da yaren yan garin da take ji a yanzu don saurin daukan yare dake ga yaro ko ni ba a barni a baya ba wurun daukan yaren su don ina jin wasu masu saukin dauka a yanzu duk da ban mu,amula da kowa sosai kamar maya da yanzu naje gidan su yafi a kirga don kaina .
Gashi duk zuwa kakan maya din sai ta hada min maganin irin nasu ta ban wanda ban san irin amfanin su ba a gareni ina dai karba ina sha don sanin ba masu cuta min bane.
A zancen da yakeyi da sadiya din kuwa raina yakai kololuwar baci a lokacin dashi don fadin wai ya manta da sunan garin mu a cewan shi yanzu.
Ba abin mamaki bane don ka manta da sunan mahaifan mu ai yanzu tunda ka biya bukatan da kake dashi akan mu.
Murmushi ya sake tare da fadin ai ban isa in manta dasu ba a rayuwana sunan garin kawai na manta kuma sadiya nake tambaya ta fada min ba wani ba.
Ai gata nan sai ta fada ma da bakin ta kafin ma na rufe baki sadiya tace dashi ANCHAU ne sunan garin mu yaya.
Gaskiya sunan garin akwai dadi sosai kuma gashi garine da ya tara manyan yan boko da suka san kansu a tahirin kaduna kaf.
Yanzun ma ga wasu karin an samu harda yan scientic a cikin su mata masu kera fasaha da kansu don wanan matar tawa nan gaba .
Sai lokacin na gane zolaya yazo dashi akaina na neman jin bakina kawai yasa ya fadi haka akan garin mu.
Nace gara dani nasan asalin garin mu wasu ko kauyen su basu san hanyar shi ba har yanzu sai kame kamen garin wasu sukeyi da sunan nasu.
Sadiya ke kinji akwai wanda zaice bai san asalin garin su ba ko ga suna idan ba karya ba.
To idan nan sani din a tafi mana in ba tsoro ba na fada ina kwashe kafafuwana ina dorawa saman kujera tare da kawar da kai a gare su.
To zamu gani idan mun je Nigeria idan wani zai nuna min hanyar asalin garin mu lokacin da nake zuwa ke kina ina ?.
Zamu gani idan an tafin ai in ba burgan aiki ake muna ba a nan don banga alaman an sanda yan kauyen ba sai yan birni.
Wai yaushe zamu tafi gidane yaya sadiya ta tambaye shi da saurin don jin yace idan mun tafi Nigeria zai kaimu garin nasu.
Zamu tafi idan ki samu hutu sadiya har in yayi daidai da lokacin banda aiki sosai zamu tafi.
Ko yanzu dai ba wani amsa mai karfi na fada a raina ina dan tunane kafin naji sun buge da hiran gida shi da sadiya din fitan da basuyi ba ke nan a ranan sai washe gari muka samu fita dashi ya kaimu yawo cikin gari tare da yin sayyaya mai yawa muka dawo gida dashi a cikin farin ciki iyakar abinda ke tsakanin mu ke nan dashi ko yaushe.
Da irin wanan har muka shirya fada ya kare a tsakanin mu a yanzu mun koma daidai a tsakanin mu yakan shigo mu dan taba hira da yakan yi kamar na dole wani lokaci.
Wani lokaci zanyi zargin bai daina komai ba a cikin halaiyar shi don ba wani canji da nake gani dake nuna ya daina din.
Abinda ban sani ba shine abune mai wuya ashe koda mutum ya daina wasu halaiyar shi ya dawo daidai lokaci guda kamar yadda nake tunane ni.
Abin ba haka yake ba don shima yaya din yana fama da kansa ne sosai boye hakan yakeyi kada mu fahinta da hakan.
Haka zai ta fama da ciwon ciki wanda bai san kanshi ba sai da kyar zai samu ya lafa mai ko kuma wani kumfa mai kauri ya dinga fita mai a baki zai wuni yana fama da wanan laluran yana faman shaye shayen abinda zai lafa mai da ciwon .
Ranan ya fita wurin aiki sai gashi zuwa karfe daya sai gashi ya dawo ina dakina kwance ina barci .
Dakin shi ya nufa a gigice ya fada saman gado a yadda ya shigo din ko takalman kafan shi bai cire ba don zafin ciwo.
Kamar a mafalki nake jin wayana yana ringing da kyat na bude idona na kai ga wayan na dauka muryan shi babu dadi yake fadin.
Wanan maganin da kika taba bani nake son ki bani yanzu idan akwashi a wurin ki har yanzu ?
Kana ina yanzu yace part dina kwance banda lafiya tun daren jiya da kyat na samu na fita yau dama.
Maganin na dauka na jika kamar yadda tace na nufi wurun shi wani irin juyi na sameshi yana yi shi kadai a dakin da sauri na karasa inda yake din ina mashi sannu.
Ya tashi da kyat yana karban maganin ya kafa kan shi saida ya shanye ya cire baki sa yana miko min cup din daya sha maganin.
Zaune nakai gefen shi tare da kura mashi idanu na dan lokaci sannu a hankali na fara ganin yana karya zufa a goshin shi sai barci.
A cikin dabara na cire mai takakman kafan shi sai ya bude idanu shi ya sauke a kaina tare da fadin nayi barci ne ko ?
Wai da takalman zan cire ma ko zaka ji dadin barcin nan wurin ne yake yawan damuna sosai sai yayi kamar ya bari kwana biyu kuma sai naji ya motsa min ba dadi wallahi ya fada yana bata fuskan shi.
Da zaka daure ka sha maganin na yan kwanaki mu gani ko Allah zai sa a dace a hakan zan sha ya fada a dan maraice yana lumshe idanun shi a haka barci ya daukeshi yana sake ajiyan zuciya kamar karamin yaro.
Tagumi nayi ina tunane ni kadai a dakin sai bin ko ina na dakin nakeyi da kallo amma a can kasan zuciyana sai tunanen kada fa wanan abin ya halaka wanan mutumin ta dalili na.
Don yanzu kan na yarda da cewa maganin kakar maya ce ke bashi wanan matsalan haka yake hanashi sukuni da sakashi yawan ciwon mara da ciki da yake complain ko yaushe .
Lalai idan haka din ne kuwa ya zama dole in koma wurin kakar maya in mata bayanin komai dake faruwa kan abinda ta bani na bashi din yasha .
Don ni har yanzu ba wai naga wani canji bane a gurin shi banda wanan matsalan dake taso mashi na yawan ciwon mara din.
Gashi har shi kanshi ya fara zargin hakan don wanan zancen daya taba fada min a gaban mami din ya nuna yasan na bashi wani abu yasha da yake zargin hakan.
Kwana biyu yana shan wanan dan abin mai kama da kankara da nake jika masa yasha yana kuma dada kara samun sauki don idan ya sha sai wani irin zufa ne zai dinga karyo mashi a duk kafofin jikin shi lokavi guda sai ya tube yana neman sanyi a jikin shi.
Haka yakanyi duk tsawon kwanakin nan da yake shan wanan maganin dan hakane ma baya sha yanzu sai da dare idan zai kwanta.
Na gama bashi maganin na juya zan fitane naji yana fadinn wai zainab waya baki wanan maganin da kike bani ne ?
Na tambayeki ranan baki ban amsa gamsashiya har nake zaton ko mami ce ta aiko maki dashi ki bani tace bata san zancen ba ?
Dan shiru nayi kafin na dago kai nace mai na fada ma dashi nazo garin nan dama ina dashi a wurina nakan yi amfani dashi idan cikina yana ciwo.
A zaton ki zan yarda da wanan maganan da kike fada ne ko kin mata farkon zuwan mu kasan nan kiyi ciwo mara saida aka kaiki asibiti ?
Baka yarda ba ke nan dani ai da kada kasha tunda zuciyar ka yana baka zan iya cutama ne da maganin .
Ban ce hakan ba amma kin san dalilin da yasa kike min amfani dashi wanda yasa nake zargin hakan a kanki sai yanzu na kara tabbatar da hakan.
Kada ki dauke ni karamin yaro da baisan abinda yakeyi ba zainab na kallo shi da sauri don jin abinda ya fada yace eh.
Na dade da sanin komai shiya har da farko nake zargin ko mami ce ta baki kiyi min amfani dashi ashe tunanena bai bani daidai ba.
Kece don kanki kika ga daman yi min amfani dashi ai da saiki fada min tun a Dubai da kika fara saka min nasha wahala kamar zan mutu.
Kin ko san kwana na kawai ke gaba a wanan lokacin dan da zan iya mutuwa a wanan lokacin.
Hawaye ne yazo min masu dumi kan maganan da yake fada min din na kasa furta komai sai hawayen da nake zubarwa kawai.
Babu abinda zan iya fada tunda har ya gano hakan a yanzu nace dashi don kawai yana wanan halin na bashi magani ya daina ko don ina son shi nayi masa hakan bai sani ba tunda gashi yana fadi da bakin sa ya san na bashi wanan maganin kan wani dalili nayi hakan zan bashi amsa.


ZAINAB IDRIS MAKAWAYA ALLAH KA SADAMU DA RAHAMOMIN DAKE CIKIN WANNAN WATAN MAI ALBARKA KASA MUNA CIKIN YANTTATUN BAYIN KA KA HANE MU DA AIKATA HARAMUN KOMAI KANKANTASHI KA BAMU IKON BAUTA MAKA BAUTA MAI TSARKI A GAREKA YA ALLAH.
YAN UWA BARKAN MU DA SHAN RUWA YA ALLAJ KA NUNA MUNA KARSHEN SA LAFIYA ALLAHUMAN AMIN, , , ,


INA MAKI TUNI DA MU GUJI SHIGA HAKKIN WANI DON ALLAH KI BIYA KAFIN KI KARANTA YAR UWA.


Haka na koma part dina a sabule ban tsaya bashi amsa ba sai juyawa da nayi na fita daga dakin zuciyana cike da zargin kaina ga abinda na aikata din ba tare da tunanen abinda zai je ya dawo a kaina ba.
Na dade a zaune ina wanan tunanen kafin na koma tuna abinda ya fada na nayi nasaran raba shi da giya da homosexual a yanzu wanda ban tabbatar da hakan ba duk daya fadi hakan da bakin shi.
Saidai zan iya cewa hakan don ganin yadda yake kashe lokacin a gida kuma tare damu ba ba irin zama tare da katan banzan da muka zo kasan muka samu suna baibaye dashi kamar jela.
Sun hanamu sakewa ko dogin motsi dashi a lokacin ko kaunan fitowa ba muyi mu gansu suma din hakane kiri kiri suke nuna rashin kaunan mu a fili basa boye hakan ko kadan a zuciyar su.
Yanzu ko sai ince kamar hakan ya zama tarihi a gare mu don tun dawowan mu daga Dubai ban kara ganin wanan taju din daya saka yar kara a tsakanin mu .
Na cewa dani dashi aga wanda zai karbe J din ni dai nasan ban fadawa kowa wanan zancen ba amma kuma gashi tun wanan ranan dana gansa tsaye zamu shiga ruwa har wanan ranan ban kara jin duriyan shi ba ko a gari.
Mikewa nayi na kewaya don fitsarin daya cika min mara din tsoro don a nawa wautan sai nake ganin yanzu babu yarda ko aminta a tsakani na da yaya din kan wanan zancen.
Na fito Sadiya tana shigowa dakin kin gama assigment din ke nan na fada eh na dauka kina part din ya j ne ai nazo na dauki wayan ki ne na duba tana fadin hakan ta nufi wurin da wayan ke caji a socket.
Gado ta fada tana fadin wanan gamen din nake son yau na karasa ko zan ci ina last stege din sa a yanzu ta fada tana gyara kwanciya.
Kokarin dauko kaya da zan saka na kwanciya nakeyi don haka ban tsaya nabi ta kanta ba sai dana gama na hau gadon ina fadin.
Wai ni wanan taju din yaron yaya ne ya fado min a rai yau wanan dan iskan mai baki kamar yayi wanka da kwata ?
Ni sam bai min ba wanan mutumin haka kawai nake jin tsanar sa don kallon banzan da yakewa mutane idan ya ganka da yaya J.
Ke sadiya harke yakewa hakan na zata aini kadai yakewa kallon raini haka ranan ai ban fada maki bane saida ya j yace ya fice masa a mota da suka daukoni.
Ki bari don Allah na fasa cikin mamaki wallahi anty kawai yacewa driver yaja mota ban gama shiga ba don shi yaya yana aiki a sytem a lokacin.
Mugu azzalumi wanan ma yafi mami bakin ciki da zaman mu da yaya na fada a dan hasale ni a dole an taba min kanwata .
Ranan kan taju yasha zagi a gun mu har Nabil saida muka tuno dashi mukayi masa nasa wasalin kafin na kai kwance don shirin barci .
Nan barci ya daukeni na barta tana game a wayan don haka take bata lokaci wurin buga gamen da ya fito zata shiga ta iya do rashin aikin yi da bamu dashi.
Washe gari naso na share sai dai hakan bai yuyu ba don shi da kanshi ya shigo wurin mu da zai fita ya gaisa damu a cikin sakin fuska bai nuna komai ba a ranshi.
Sai dai wani halin da ban san dalilin shi ba a yanzu da yaya yake tsiro min dashi shine yawan son taba min jiki isan muna tare.
Zai kama hannuna ko yayi hugging dina kamar yadda dabi,un yan kasan yake ko kuma ina zaune zai dan lakatar min kumatuna da hannun shi.
Da farko ina daukan hakan ga dan shakuwan dake tsakanin mune a yanzu yasa yake yawan min hakan.
Sai dai yanzu dalilin wanan maganan daya fada a daren jiyan yasa na fara zargin hakan da wani abu na daban da yake ji a hakan.
Don dacan ko kallo ban isa a wurin shi ba balle yayi gigin taba wani part na jikina da nake daukan hakan da kyama ko tsanan mata da yakeyi ne ya jawo hakan da yake nuna min.
A yanzu ma dalilin wanan tunanen shine bai fita daga falon ba saida ya dan rungumeni na sai ya dawo in kula da kaina don sadiya a nan ta barshi ta tafi don tunda na gama nawa karatun ya hutar dani da fitan safe saidai driver ya kaita ya kuma dauko ta idan ta tashi daga school din.
Haka ya fita ya barni da wanan tunanen tare da kamshin turaren shi a jikina wanda yakan dafe min a jiki kamar nice na shafa zan wuni ina jin kamshin a tare dani yana saukar min da wani irin feeling a jikina.
Na dade kwance a katon falon gidan wanda yaji kayan alatu iri iri na zamani sai babu ne kawai babu garemu a gidan.
Can nayi mika na gyara kwamciyana ina lumshe idanuna tare da wani tunane kafin na sake dan murmushi a fuskana don tunawa da zancen fadila da nayi a lokacin.
Da take fadin ke din fa mace ce da ko wani na miji zai kyala ido a kanki ya kasa kawar da idanun shi a kanki .
Balle mijin kin nan da yake yaro mai yayi da zamani ga kudi ga ilimi ga kyau ga tsare gida dole ko wace mace zata so ta mallakeshi idan ta samu wanan daman a wurin shi don haka ki kara kama jiki ki kwato mutuncin kina ya mace a wurin mijin nan naki.
Wanan sayi da tayi basar da kanki da kuke yi ba zai kaiku ko ina ba nan gaba zaku dawo kuna ganin laifin junane a tsakanin ku ga banza.
Wanda kema kina da laifin a wurun hubbasa hakan gareku a yanzu koda yana kyamar mata a rayuwan shi ke ki daure ga hakan ki bishi a yadda yake har komai ya daidaita a tsakanin ku nan gaba.
Haba fadila ina hakan zai yuyu ga mutumin da bakinsa ya fada bai san dadin dake ga ya mace ba da wasu mazan suke fadi.
Ta yaya zan iya mu,amula da mutumin da yake kallon mace kamar namiji a wurin shi bai dauki fadan ma,aikin Allah da wani muhinmanci ba ?
Mutumin da ya zabi ya butulcewa ubangijin shi ta munanan hanyoyin da Allah ya fadi irin azaban daya tanadarwa masu irin wanan halaiyan tun a nan duniya kuma ya karanta yasan da hakan.
Amma ya take sani saboda rudin duniya kawai da abokai sai naji wani irin tsana da kyamar shi yana sauk mn a zuciyana.
Hawaye ne ya gangaro min daga idona zuwa fuskana nake kokarin sharewa don takaici da jin zafin halaiyar yaya din a yanzu wanda nasan ba ko wace mace ne zata gane hakan ba don irin daulan da muke ciki a gidan kullun sai macen da irin haka ya sama na kaddaran rayuwa.
Abin akwai ciwo akwai takaici don koda nayi rantsuwa yafi dubu ba kowane zai yarda cewa bai taba aikata haka dani ba duk tsawon dadewan mu dashi na zaman aure da nakeyi a gidan shi.
Mutane ba zasu taba yardan cewa wani abu maka mancin wasan aure bai taba shiga tsakanina da yaya ba tunda ina zaune a gidan shi har tsawon wanan lokacin.
Allah na tuba ka yafe min idan har zamana da yaya laifine a wurin ka na fada ina mikewa zaune don kwanciyan ba zai min ba a lokacin.
Allah ya gani idan da a yanzu ne yadda nake din nan na kara wayau ba zan zauna da yaya koda na wata daya bane a gidan shi yana wanan halaiyar na Allah waddai da tsinuwa a wurin Allah.
Tambayan kaina nayi ni yanzu yaya zanyi da rayuwana don nasan komai boyo dole mutanen Nigeria su san wanan magana wata rana.
Kukane tazo min sosai lokaci guda ina fadin ya Allah ka yafe min in har zama cikin wanan gida mai zunubi laifine a gare mu baki daya.
Kuka nayi sosai har yanayi na ya canza ga baki alaman na wuni ina kuka ya baiyana a gareni wanda hakan ya saukar min da zazzabi.
Inda Allah ya taimakeni sadiya ce ta rigashi dawowa gidan shigowan ta yasa na dan tashi ta hada min tea ina zaune ina sha dukunkune sai gashi ya shigo dakin .
Da alama ko part din shi bai shiga ba a lokacin ganin yadda ya sameni ne yasa yasan babu lafiya a tare dani ga kuma muryana daya dan sauya a lokacin.
Lafiya meya sameki pretty na ganki a haka nace zazzabine kuma nasha magani ya sauka min a cikin wani yanayi ina kawar da kai nake wanan maganan dashi.
Takowa ya karasa yi har zuwa inda nake zaune yakai hannun shi zuwa jikina yana dan tabawa babu zafi jikin naki ya fada.
Ina runtse ido don tabanin da yayi din sadiya ce ta bashi amsa da fadin jikin yayi sanyi yanzu data dan sha tea din nan amma a kwance rijib na sameta dana shigo.
Ina zuwa ya fada yana ficewa dakin sai da ya dauki yan dakiku sai gashi ya shigo dakin wanan lokacin ya sauya kayan jikin shi zuwa wasu yadi masu taushi na kasan chaina.
Irin wanan kayan sukan mashi kyau sosai idan ya saka saidai bai damu da saka irin su ba shi ko su din farare ne kal dasu da wani dan less a kasan rigan da sai mutum ya duba sosai zai gane hakan.
Idan ya saka kayan musulunci yakan burgeni har bai isata kallo a ranan sai gashi yau din daya saka ko kadan bai burgeni ba sai ma kawar da kai da nakeyi daga kallon shi din tunda yai sallama ya shigo dakin.
Tashi muje asibiti ya fada yana shigowa dakin na kawar da kai ina fadin naji sauki ba sai naje asibiti ba .
No ban yarda da wanan ba tashi maza muje kiga likita nasan bakya ciwo a wasan dadi don hakan muje a dubaki.
Ban so ba ba kuma yadda zanyi dashi dole na mike hijjab na dauko yau na saka muka fita yana biye dani a baya yaiwa sadiya sai mun dawo.
Mun danyi tafiya kadan yake fadin meya sakaki kuka har kika jawa kanki ciwo haka lokaci guda ?
Kamar yadda bai kalleni ba nima hakan ban kallo shi ba sai bin motan danayi na kara narkewa a hankali ina lumshe idona.
Tambayan ki nakeyi zainab ya fada wanan karon yana dan kallona nima kallo shi nayi ina fadin kawai dai haka kukan yazo min.
Maganan tafiya Nigeria ke nan ya sakaki kuka haka ko har kina kokarin jawa kanki ciwo a yanzu ?
Shiru nayi kawai ba amsa don bansan abinda zan fada ba ya sakani kukan don ta dalilin shine hakan ya faru har nayi kuka.
Bai kara magana ba sai ma gudun daya karawa motan sai gamu wani asibitin dabana gwaunati ba nan dai yaga likita sai gashi an shiga dani ciki an dan min tambayoyi kamar mayu suma din sun gane hakan ya faru ne ta sanadiyar kukan da nayi yaja min hakan.
Likitan bai dauka ni matar aure bace koshi ya fada mai nidin sister shi ce oho har yake fadin ko dai nayi kuka akan saurayina ne ?
Yaja min zazzabi da ciwon kai na dan lokaci don jikina bai nuna wani abu yana shirin samuna ba da har kaina zai min ciwo.
Magani da sauran tarkace suka bani muka fito don ba zancen allura don wanan ciwon kawai da suka gani a lokacin baikai ai mun allura ba.
Bai dauki hanyar gida ba sai ya nufi wani wuri da suke sayar da kayan kwalama na sayin yayi leda biyu ya dawo muka dawo gida har lokacin bai kara min maganan komai ba saida zan fita cikin motan yake fadin.
Ki tabbatar da kin sha maganin nan yanzu don kada ciwon ya zama maki babba a jiki nan gaba.
Falo na zauna don sadiya tana falon shima da ya shigo nan ya zube ledojin dake hannun shi ya nufi kitchen da kanshi ya dauko min goran ruwa mara sanyi ya kawo min tare da fadin.
Karbi nan ya duka ya bude ledan maganin ya balla min ya miko na karba nasha don dole badan naso ba.
Na koma na kwanta saman kujeran yake fadin sadiya bude ledan nan ki dauka kusha ta taso da sauri tana budewa abinda ta gani a cikin ledan yasata murna tana fadin wai yaya ashe a kwai wanan a kasan nan ?
Ranan naga wanan taju din dashi yana sha mugu ya shanye bai bani ba kina son shine ashe ya fada yana dago grif fruit din ya balla tare da fadin ki wanko mana sai musha.
Amma Taju baya kasan nan ne yanzu na fada ba tare dana kallo shi ba yi yayi kamar baiji abinda na fada ba a lokacin sai da sadiya ta dawo ta aje fruit din ya kara tsunka ya kai a bakin shi ya tauna yake fadin kefa ba zaki sha bane kin tsaya kina tambayan wanda bai shafe ki ba ?
Ya shafe ni tunda yana tare dakai a gidan nan kaga ya shafeni idan akwai kara ai .
Ba mamaki tunda ke dashi kun dauki junan ku da kishi har kunawa juna barazana a kaina ko ?
Ni din na fada da mamaki yace karya zan maki bakuyi hakan bane dashi a dubai na nuna maki hakan a wayan ki ?
Sai yanzu ma na gaskanta abinda ya tunzuraki har kika zuba min maganin da kike ganin zai hanani wani halaka dasu a yanzu.
Idan ma na zuba kanshi ai ba laifi nayi ba tunda kaima ka fada yanzu da bakin ka cewa shi din kishiyatace a wurin ka kaga ko zanyi komai a kan ya barka har abada idan zan samu daman yin hakan ai ba laifi bane.
Zaki ba kanki wahala a kan hakan don kowa da kalar rayuwan shi abinda wani ke so bashi wani ke so ba ai.
Koda ace Allah ya halasta hakan akan mutum zai ki bin umurnin Allah na fada ba tare da na dago ba saidai zancen ya saka sadiya a cikin tamtama don bata san dalilin da yasa muke wanan maganan ba.
Dama nasan meya sakaki wanan damuwan har kikai kukan daya ja maki ciwon kai kina son ki bawa kanki wahala akan hakan.
Yaya ka daina ba kanka wahala da tunanen zan iya zubama abinda zai cutar dakai don ban san kowa ba a kasan nan da zan shiga na samo wani abu.
Nasan wanan shine kuma abinda ke daure min kai har yanzu kan hakan zuciyana ta kasa gaskanta min gaskiyan wanan zargin da nake yi.
Zargin yayan mu kakeyi yaya sadiya ta fada a cikin mamaki ba zarginta nakeyi ba sadiya idan ma tayi hakan tayi nasara kan abinda ta aikata din.
Ya mike tare da daukan ledan shi fuskanshi a daure ya nufi part din shi na dade ban dago ba bayan tafiyan shi sai sadiya take fadin akan me yake maki wanan zargin yaya ?
Gashi kinji ya fada wai nice silar barin Taju gidan nan wanda bansan kan abinda yake magana ba ?
Gara daya bar gidan nan wallahi don ni wanan mutumin bai mun ba sam ya faye fadin rai da jin haushin mutane wallahi.
Duk da dare ne a lokacin bai hana ni shiga part din yaya ba a lokacin nayi mamakin ganin kofan a bude bai rufe ba.
Har na wuce falon banji motsin shi ba kamar mai sanda nake tafiya zuwa bed room din shi sai kamshi ke tashi ta ko ina a part din.
Kasa na hango shi zaune saman ties din dakin ya aje kwalba da cup a gaban shi sai kankara daga gefen shi da alama kamar sallah ya idar ya zauna a wurin.
Da sauri na juya zan bar dakin naji muryan shi yana fadin karaso mana ki shigo ina kuma zaki bayan kin shigo ?
Kamar zan tafi sai kuma na juyo na karaso inda yake zaune din kallo daya nayi mai na kawar da idon ina fadin.
Nazo muyi magana akan wanan zancen da kake fada min ko yaushe saidai kuma gashi ko a yanzu din hakan na nuna baka bar komai ba da kake yi a baya.
Ya dago kai yana fadin da kikaga me a yanzu ina kin ban maganine din na daina sha da sha,awan maza yan uwana da Allah ya doro min ?
Allah bai doro maka hakan ba kai ka biyewa shedan ya dora ma wanan halin don da abin kwarai ne da sauran yan uwan ka sunyi hakan.
Na gane akwai raini mai yawa yanzu tsakanina dake zainab zaki iya fada min maganan da duk yazo maki a baki ba tare da kinji shakkar fada min hakan ba.
Daga inda nake tsaye na kalleshi nake fadin ba zan taba son na kasance cikin irin matan nan ba a rayuwana saida yin hakan ya zama min dole a yanzu don sanin kokai waye a gareni.
Nafi kowa kusanci gareka yanzu a duniyan nan kasancewa ta wace muke kwana muke tashi a rufi guda ma,ana a gida daya .
Murmushi naga yadan yi kamar yadda yakeyi idan baison magana yanzu yaya sallah ka idar amma ka tasa giya a gaban ka kana sha fa ?
Zainab wai me kika daukeni ne halan ina don na daina shan giya kika ban maganin da ki kaki amsa hakan cewa don shi kika ban har yanzu.
To don me kuma zaki dawo kina zargin har yanzu ina shan giya a rayuwana giya a yanzu ko sunan sa bana son ji a rayuwana.
Yasa a kullun nake maki korafi kan abinda na kasa bari don kaina sai gashi ke kinyi nasaran rabani da wanan dabi,an a cikin sauki.
Kina zaton yawan tambayan da nake maki kamar da wani manufa nake maki hakan No ina tambayan kine don nasan ainihin inda kika samu wanan makarin a cikin sauki.
Yadda yake min magana a lokacin zaka fahinci akwai abubuwa a zuciyar shi da suke damun shi don ba yadda nazo muyi maganan kan irin yadda ya sani a gaba da wanan zancen har hakan yake damuna ba sosai.
Wanan idan ba giyar bace meye yaya kana ikirari a kullan yanzu ka daina sha ka daina sha kamar ruwa yadda ka saba kwankwada ko me ke nan haka ke nufi yanzu ?
Ya dago idanun shi da suka sauya kalla don abinda nake fadi yace ko zan boyewa kowa halin da nake ciki ba zan taba boye maki ba ke don nasan kona boye zaki san gaskiya.
Ya dago kwalban yana fadin karbi ki duba idan giya nake sha don zuciyar ki ya huta zargina kullun.
Wani iri naji kunyane ko tausayi ban sani ba yana fadin ni yanzu kunyar kaina nake ji a wurin kowa idan baki sani ba ma yau ki sani giya dai kan na daina shan sa har abada ta dalilin ki zainab.YAN UWA MUSULMAI BARKAN MU DA SHAN RUWA UBANGIJI ALLAH KA YANTA MU CIKIN YANTATTUN WANAN WATAN MAI ALBARKA AMIN YA ALLAHU.
ALLAH KA KARFAFA MUNA ZUKATUN MU MU ZAMO MASU KASKANTAR DA KAI A GARE KA AMIN YA ALLAHU, , , , ,

LITTAFIN KUDINE YAR UWA DON SAYA SAIKI KIRA WANAN LAYIN 08036959257 KO 09026931792 DARI UKUNE KAWAI KUDIN SA ALLAH YA BADA IKON BIYA YAR UWA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DA YARDAN UBANGIJI, , , ,


Rayuwa haka ya kasan ce ba tabbas a tsakani da yaya akan cewa ya daina duk wani halaiya nasa mara kyau a yanzu.
Ni dai tunda yace yace ya daina na dauka din ya daina ko ya rage don ba yarda nayi da hakan har kasan zuciyana ba.
Sai dai ba wanan zancen a tsakanin mu ban sani ba ashe yaya yana nan yana shirin tafiyan mu zuwa Nigeria a asrince.
Don daga gyaran gidan da zamu zauna har suturo da duk wani abinda zamuci ko amfani dashi an gama hada komai a can Nigeria din ya tura wasu daga nan wasu kuma an saye a wani kasan an tura can Nigeria din.
Ko mami bata san da wanan shirin nasa ba balle wani dan uwansa ya sani dama dai jamal ne wanda nasu yazo daya da jafar din .
Yanzu ko sun raba gari a tsakanin su do ma mahaifiyar su na tsaye a kansu ne yasa basu kai inda ba,a so ba a tsakanin su din.
Don shi jamal din ga baki daya ya tsani jafar gaba daya a rayuwan shi ya tsani duk wani abinda ma ya fito daga hannun jafar din.
Tun yana iya boye hakan a zuciyar shi har yakai mami ta kai ga fahintar hakan duk abinda ya fito daga jafar din shi jamal baya amsa baya ko kallon abin.
Ranan a gaban kowa mami ke masa fadan hakan sam ta manta da cewa sauran yaran basu san halin da dan uwan nasu ke ciki ba a lokacin.
Take fadin Jamal ina kula da take taken ka kan dan uwanka kana nuna kyama da tsana akan komai nasa.
Duk halin da jafar ke ciki a yau ko ma ya zama abin kyama ne a gun wasu banyi tsammanin ku zaku iya guje masa ba ai.
Tsit sukayi falon kowa na kallon su kafin shi jamal din yace mami nifa ba tsanan shi nayi ba ina dai koyi ga abinda sunna ya koyar da mune ga masu wanan halin kawai.
Hali wani hali kuma kega ya J da har zai fadi haka mami kawai kila hassada ya jamal ya fara a kan dan uwan shi .
Amma meye matsalan da har zai fadwa dan uwan shi haka ni dai a gareni banga wani abin kushewa gun ya j din ba sai dai wanan bakauyiyar yarinyar da yake aure kawai wace bata san kanta ba balle na wasu .
I realy totally hate dis zainab yanzu wallahi ji irin dukiyar da shegiya ke ciki amma bata san yadda zata juyashi ba dan gidadancin dake damun yar iska.
Wani kallo jamal din ya watsa mata tare da fadin dan Allah gafara can ki rufawa mutane baki gada na balla ki a wurin nan.
Tunda bakya son ta ba sai ki kasheta ba ko ki fitar da ita cikin daulan da kike kyashin zaman ta din a yanzu.
Zainab da kike gani tafiki hankali da wayau sau dubu dan ita tasan ya kamata ba wai daula ko arzikin shi ke gaban ta ba ita.
A,a,a ke Aisha ki kyale bakin ki fa akan zainab don bata taba laifi a gaban bros tun asali kin sani .
Ta sani mana tunda yafi son ta sama ga dan uwan shi tunda ta iya makirci har ta gaji a rayuwa har yana wani son ririta ta yanzu a gaban kowa.
Mikewa yayi tsaye don fita daga falon yana fadin gaskiyane dai baki so mami amma yarinyar nan ai bata cancanci irin wanan ba a wurin ku yanzu tunda kunsan zaman da takeyi dashi itama.
Sakarai kawai mara hankali zanga yaushe zakayi hankali ka daina wanan halin wai kai mai ra,ayin rikau hakan.
Fita yayi bai juyo ba yana fita jalal ke fadin mami wai me ya J yakeyi ne da kullun jamal ke nuna baya son shi haka ?
Kyale mara hankali da baisan me yakeyi ba dan kawai dan uwanka na wani hali mara kyau zaka nuna masa tsana haka ?
Ni dana haifeshi ince me yanzu don yanzu dani duniya zatayi kwatancen shi idan an tashi fada ai.
Wani irin kallo yaran kewa uwar cikin rashin fahintar inda maganan nasu ya dosa a lokacin kafin Aisha tace wai mami nafa kula kamar akwai wani hali da ya J din keyi wanda ba a son mu sani.
Wata kila dai mata yake nema ko tunda naji jamal na fadin ko zainab na hakkuri dashi ai.
No kai ina ba dai ya J ba kan akan mata don da munga alaman hakan tuni a gareshi ba wanan bane mami basa son muji daine nake gani.
Dan Allah ku rufa min baki koma me yakeyi ku tayashi addu,a Allah yasa ya daina ta fada a cikin bacin rai tana kawar da kai a garesu baki daya.
Ranan wanan zancen da yaran sukayi ya hana mami din shakat a rayuwan ta dashi ta kwanta can dare kamar yadda ta saba tashi a cikin dare tayi nafila hakama ranan ta tashi tana mika kukan ta ga Allah.
Tun tana yi a cikin zuciyar ta har yakai ta fashe da kuka a fili tana rokanwa dan nata sauki a wurin Allah.
Tare da kaskantar da kanta ga Allah ta daga hannayen ta sama duka biyu tana hawaye tana addu,a tare da mika kukanta a kaskance wurin ubangiji.

Zaune nake ina bitan kur,anina da yanzu na koma gare shi sosai fiye da komai da nakeyi don ina son na kara saukewa duk da banda wanda zai karani a lokacin.
Sadiya ta fito daga dakinta tana saye a cikin dan wando pink daya tsaya mata iya gwaiwan kafanta sai yan aninaiya biyu da akaiwa wandon ado dashi sama rigace fara mai shaka shaka da rigan ta fito dashi a jikin ta.
Zama tayi kusa dani tana kokarin lalaban wayana dake gefena ajiye sai lokacin na dago kai na kalleta na tsayar da karatun da nake ina fadin .
Amma dai kinga abinda nake zaki zo min kai babu hula ko dan kwali ki zauna a kusa dani haka ?
Ba zama zanyi ba ai waya nake son dauka dama ta fada a cikin harshen turancin da yanzu dashi take iya magana ko a gida sosai.
Kallon ta nayi mai kama da harara ina kawar da kaina gefe ta gane may nake nufi yasa ta juya ta koma dakin.
Naci gaba da abinda nakeyi ban tsaya bin ta kanta ba sai can ta fito saye da hula a kanta ta zauna nisa dani tana kumbure kumbure na fita batun ta.
Shine ya shigo part din saye da farar jallabiya zakace balarabe ne shi din yadda rigan ya karbi jikin shi kusa dani ya zauna daya shigo .
Sai dai hankalin shi yana gun sadiya yake fadin Sady ya na ganki a haka kamar an bata maki rai ko ?
Shafawa nayi tare da dago kai ina fadin fushin banza takeyi tunda bata son a fada mata gaskiya don tana kokarin kwasan dabi,an nasara ta dorawa kanta yanzu niko ba yarda zanyi da hakan ba.
Me tayi ya fada yana kallon sadiya din ai gatanan ta fada da bakin ta ina mikewa don dauko mai ruwa don nasan ko ban dauko ba zai tambaya idan zai tsshi.
Ina zaki ya tambayeni ruwa zan dauko ma a fridge na fada naci gaba da tafiya na dan dade a kicin din don adduan dana tsaya yi a cikin ruwan ba wani addu,a bane sai fatiha dana tsiri karanta mai kafa goma sha daya a ruwan wanda kafin nasa nakan karanta na aje mai ya danyi sanyi daya tambaya na dauko mai shi.
Sai ranan na manta ban karanta masa ba har ya shigo part din namu haka yasa na dan tsaya ina karantawa har na bata lokaci a karamin kitchen din namu na part din.
Wai ke zainab tunda yarinyar nan tana son waya don me baki bata wayan can dana ce ki bata ba tun farko.
Tiren Ruwan da cup na aje a gaban shi cikin ladabi ina kokarin budewa yace min barshi sai na tashi zansha a cikin muryan shin nan me kamar na rowa ga mutum idan bashi yaso magana ba.
Wayar tana inane tunda kin hana mata naki ya sake maimaitawa nace tana nan aje wanan ma ai ya ishe mu amfani banda mutanen gida wa muke kira dashi.
Naki ma ai wani za a saya tunda ba zaki gida da wayar data sha hannu ba sai ki bata ta ci gaba da gamen dinta a zauna lafiya ko gimbiyar game ?
Sai lokacin tayi murmushi a fuskanta jin abinda ya fada din yace to koke fa sadiya kin zauna kin hade rai haka kamar wata matar soja can dake ?
Ni da naga sa,adatu hade fuskanta ai baiban tsoro na fada ina zama a inda na tashi muryan shine ya sake fadin akwai wani abinda kuke son sayane zaku tafi dashi gida duk da dai ba dadewa zamuyi ba zamu dawo ?
Don hutun nasu na tambaya baida yawa kwarai akace wanan karon saboda sadiya sai mu dawo da wuri yaya nikan sai na gama koda zan dawo na bashi amsa.
Tunda kece mai shirya tafiyan ya fada a dan hasale amma yaya kasan dai mun dade rabo mu da gida ai na fada ina kallom shi.
To idan hakane sai a fasa tafiyan in hakan bai maki ba wata daya na yanke zamuyi a can zuwa lokacin nasan kin gama dai abinda ya kaiki ai.
Duk da naji dadin zancen a raina amma a fili cewa nayi wata daya kuma yaya ina laifin dai wata biyu zuwa uku haka ?
Karatun nata fa wai zainab bana son wasa da abinda ya shafi karatun ku ga baki daya kema na saya maki form da mun dawo zaki koma karatu ne nan gaba.
Ko hakan bai maki bane zaki tsaya batawa kanki lokaci zanso ace kin hada karatun ki kaf a nan kafin mu tattara mu koma Nigeria gaba daya da zama can don hakan nake planning nan gaba don mami ta fara fadin mu koma gida hakana.
Mami tana da gaskiya yaya zama acan kusa da yan uwa zaifi ma tana ganin ka a kusa da ita hankali zaifi kwanciya ai balle ni wa yanan abokan naka yaya basu min ba sam.
Zainab yaushe kika san abokaina da har kika san basuyi maki ba ya tambaya da mamaki yana kallona .
Nasan su tunda sune mahalakan ka a yanzu na fada a hankali sai naji ya sake dan murmushi kawai yana kada kai .
Can yace zainab da kinfi haka bansan inda wayau ki zai tsaya min ba don kallon da nake maki kin wuce haka a wurina.
Abi ma dariya ya bani na kai bayana saman kujera ina dan murmusawa tare da fadin ni di kuma yaya sadiya karya na fada matar da take zaune a gida take fadin abokaina.
Yanzu da nayi magana yayan mu laifina zata gani yaya ta fada tana nokewa ga maganan ruwan dake gaban sa ya bude ya zuba a cup din tare da dan kurba a hankali yana kada kai kafin yace ina ganin ranan Friday mai zuwa muna Nigeria.
Don haka idan akwai abinda kowan ku keso sai ya fada ko ku fita ku sayo da kanku zaifi min sauki saidai bana son kaya masu nauyi da yawa kin sani ga tafiya.
Duk iya abinda zan rika yaya tufafine ko dan wani abin amfanin mu na bashi amsa ina cikin farin ciki da jin zamu wuce gida dabai fi an kwanaki ba a lokacin ashe .
Tu wanan ranan sosai muke busy yawon fita sayayya duk ban san cewa ya riga da yai muna sayayyan da ban taba zato ba don wanan tafiyan.
Kafin ranan duk mun gama wani shiri na tafiyan mu inda nikan shiri nakeyi sosai na barin kasan gaba daya a raina don haka duk wani abunda zan tuna nayi dana sani bukatan shi a can na tanada don komawa dashi gida duk ya yaya yace baya son muyi tarkacen kaya da yawa ga tafiyan.
Ranan daya bukaci mu fitar a tafi da kayan airport yasha mamakina sosai don bai iya boye bacin ranshi a zuciyar shi ba don ganin yawan kayan da yayi dana fitar.
Haka ya daure akai muna packed din shi zuwa airport inda kayan da alaman zasu rigamu isa ga nawa tunanen.
Shiri sosai mukayi daga gyaran jiki zuwa duk wani abinda ya kamata ace munyi don ban yarda na bar kasan ba saida naje har kauyen su maya mukai sallama da ita da iyayyen ta kan na tafi na tafi ke nan ba zamu sake haduwa da suba idan na tafi.
Kamar yadda duk wani sabo yake udan za a rabu haka muka rabu da maya da yan uwan ta kakarta bata barni haka ba saida ta ban wasu abunuwa datace na zanka amfani dasu har yayana nan gaba muka rabu cikin kewa da juna ina kuka maya ma tanayi.
Washe gari da daren ranan muka bar kasan chaina zuwa Nigeria sai dai naji haushin tsayawan mu a kasan Dubai da muka kanceqa da yayi wani aiki ya taso mashi a can da zai tsaya ya dan yi.
Ba laifi mun tsaya a Dubai mun kuma sha dadi sosai duk da shikan baida lokacin mu kullun sai dare yake dawowa masaukin da muka sauka wani lokacin ma kafin ya dawo zai samu munyi barci ko.
Wasa wasa kwanan mu biyar a dubai din wanda ni dai nayisu ba a cikkn dadin rai bane do na matsu na bufe ido na ganni a kasata Nigeria a lokacin.
Shiko hakan ko a jikin shi don ba abinda ya dameshi a zamanu din sai ranan da yake fadin gobe zamu bar kasan ya danga walwalana kadan.
Alhamdullahi mun sauka Nigeria da dare amma ta kano ba kamar ta Abuja ba kamar yadda ya tsara muna.
Nasan maganan hauka zanyi idan nace ya barmu mu fara zuwa gida don gamu a kano don yafi muna kusa da gida a lokacin.
Amma nasan zuciyana hauka take ban don ba zai taba yarda da hakan ba sai idan mun danganta da wurin mami da yanzu zaman ta ya koma garin Abujane kamcankan duk da an sauke su a lokacin.
Don lokacin har waya tayo min kan wai ban kirata na mata jajen saukan su a mulki ba ta fada don takanas ta kirani a waya ta balbaleni ni dai sai hakkurin dana bata kawai a lokacin.
Duk da an sauke su bata kwaso ta dawo kadana da zama ba sai suka zauna can ga baki daya tunda dama gidan su na kansu suke zaune a cikin sa yanzu ba na gwaunati ba.
Duk wani gyaran gidan da aka kara yi yaya J ne ya kara gyara masu shi suke zaune a cikin sa yanzu.
Karfe goman safe duk muna Abuja ba zance ga unguwar da muke shiga ba don garin gaba daya ya kara sauya min ga dan sanin danayi mai a baya.
Duk da rudewan sauyawan wurin hakan bai hanani gane ba wancan gidan da muka zauna a farkon aurena dashi bane kafin mu wuce zuwa chaina.
Wanan gidan na yanzu yaci uban wancan sosai ga fasali da keruwa komai na gidan sabone ba sai an fadawa mutum haka ba.
Motocine a haraban gidan gasunan birjit a cikin rigunan su rurufe sai shuke shuke da zai tarbe ka.
Tun saukan mu kano ya sauya layin wayan shi naga ya aje wancan wayan da mukai tafiya dashi haka kuma ya miko min nima waya sabuwa a kwalin ta kiran samsung full ita kuma sadiya iphone karama mai kyau da su.
Zakace duk biyun ba zaka gane bambancin su ba don kyau godiya nayi a fili a zuciyana kuma fadi nake kyautan karshe ke nan tsakanina dakai baka sani ba.
Don yanzu sai lalabashi kawai nakeyi in samu naga mun sauka ya mika mu gida lokacin zan tayar da balli na a garesu.
Don duk wani rudi da abin duniya da yake min yanzu ni bashine a gabana ba kaina kawai nake son na kwata a garesu naga na fita hannun shi baki alaikum ba tare da duniya ta zargi komai a hakan ba.
Kinga gidan ki na abuja ke nan da fatan tsarin ginan yayi maki kyau sosai ya fada kamar mai rada a lokacin.
Don naga kina da sha,awan ruwa wancan kuma babu swimming poll a cikin sa yasa na fadada wanan din aka gyara makushi sosai.
Dan murmushi yake na sake tare da fadin gidan yayi kyau sosai wallahi ballw ni yar tallaka ina ni ina wani zabem gida mai kyau gareni.
Bana son kina kiran kanki da hakan don yanzu a matata kike a idon kowa don haka wanan kallaman ya fita a bakin ki.
Donke din matar jafar kankia ce ba yar anchau ne ko meye sunan garin naku ba na manta ya fada yana kawar da kanshi don motar data tsaya gab da kofan shiga gidan.
Innalillahi zakace wasu basu tunanen lahira idan suna hada duniyan su kamar ba zasu barshi ba don tsarin gidan kamar ba gobe.
Haka muka fito muna bin gidan da kallon mamaki zuwa cikin gidan saidai duk hakan bai hanani addua a bakina duk da na rude da ganin wanan gidan haka.
Sai tambayan kaina nake wai ya jafar ne mai mahaukacin kudin nan haka kamar wani mai shekaru a duniyan nan daya tara kudi irin haka.
Oyyoyo da uwar dakina muryan fadilace ya daki kunnena lokaci guda sun fito tare da wasu daga cikin gidan.
You again muryan sadiya ta fada da dan karfi ta nufi wurin ta da gudu don murnan ganin ta a lokacin.
A hankali nake takowa cikin dan murmushi zuwa gareta ta hadamu ta rugume ga baki daya kafin sauran mata su shiga gaida mu suna muna sannu da zuwa cikin nuna kulawa a gare mu.
Na dago ina fadin mun sameku lafiya suka amsa a cikin fara,a da murna kamar sun taba sani mu da farko.
Shine ke waya da bansan wanda yake wayan dashi ba a bayan mu yake fadin mun iso a kawo mai abinda yace azo dashi din.
A raina nace giya ke nan ko wani katon tun da naji ya fadi hakan yayin da matan suka shiga gaidashi da zuwa da sauran yan aikin gidan.
Muna shiga wani katon hoton mu da muka dauka a chaina dashi ranan sallah ne ya tareni don nasha kwaliya a photon zakace ko balarabiyace ta asili yadda na fito a photon.
Da murmushi na sake tare da tambayan kaina yaushe har ya yi wanan aikin haka kai yaya ya iya duk wani abinda zai kawar da zargi a zukatan mutane shikan .
Ai wanan photon sai a dauka ni din matarshice ta gaskiya yadda photon ya karbi falom kamar kai magana damu mu amsa ma a fili.
A falo muka zauna aka shiga gaisawa da masu aiki sai kuma wasu biyu da ban sani ba na dai ga suna zirga zirga a gidan kamar yan uwan shi.
Kafin shi ya fara mikewa a daidai lokacin da Fadila ke fadin ai maza a kara gyara table din abincin don muna da gajiya kafim mu shige ciki mu huta.
No saidai su nikan zan shiga na watsa ruwa ya bada amsa yana kallon agogon hannun shi kafin ya juyo yana fadin mami bata san da zuwan mu na fa nasan zaku kwasa da ita karshe.
Da nayi laifin me tunda tasan bani bace mai tafiyan a raina kuma fadi nayi saidai tayi da wanda ta gani don ni goben nan zan bar gidan nan idan ma ba kasani ba ka sani.
Don a kage nake ko zuwa abujan duk bat da saune kawai nayi mai kada mu raba hali tun a hanya shiko sai wani nuna jiji damu da yakeyi a gaban kowa yadda kasan auren gaskiya muke a tsakani mu dashi.


ZAINAB IDRIS MAKAWAYA ALLAH KASA MUNA CIKIN YANTTATUN BAYIN KA UBANGIJI KA KARBA MUNA IBADUN MU KA GAFARTAWA DUKKAN MAGABATAN MU KA BAMU CIKAWA DA IMANI A ZUKATAN MU ALLAHUMA AMIN, , , , ,


LITTAFIN NAN NA KUDINE YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA AKANKI BA YAR UWA, , , ,

DON SAMUN LITTAFIN NAN ZAKI KIRA 08036959257 KO 09026931792 DARI UKU NE KACAL KUDIN SHI, , ,


Dakin namu nabi da kallo komai ansaka na jin dadin rayuwa dan Adam a dakin kamar ba gobe a wurin bawa.
Wanka na shiga na fito na samu an shigo mun da kayana dana zo dashi ranan na bude wardrobe da niyar aje jakkar kayan gaba daya ba tare dana zazzage kayan ba don idan zan tafi gida dauka kawai zanyi na tafi dashi.
Saidai abinda nagani a cikin wardrobe din shi ya girgizani lokaci guda don kayane ciki shake nau,i nau,i na mata irin namu na kasan Africa.
Wanan ko a wata dayan da yace zamuyi mu koma yaushe zan saka su a jikina duk a cikin wata dayan balle su kare.
Don sun kai kala hamsin ko fiye da hakan a cikin wardrobe din idan ma basufi hakan ba ga lissafin.
Nan na karewa kayan kallo ina sauke ajiyan zuciya kasa daukan ko daya daga cikin kayan wardrobe din na zari guda a cikin jakkana na saka na koma bakin gado na zauna ina tunanen wanan halin na yaya J.
Na kasa fassara wanan halin na yaya J gaskiya don wani sahu zan saka shi a yanzu shin zan iya kiransa da mai yawan alheri ko kuma mai iya yaudara ne ?
Don wanan halin nasa idan ba wani akasi ba sai mace tace ta dace da miji gaskiya don irin halaiyar nan nasa.
Salaman sadiya dakin yasa na dago kai ina kallon ta fuskanta da fara,a take tafe tana fadin wai yayan mu kinga yadda aka cika min wardrone da kaya.
Nuna mata nawa nayi da hannu ina fadin duba can ki gani sadiya wanan ai haukane ko ?
Ta nufi wurin wardrobe din tana fadin a,a yayan mu zamu saka mu ji dadi wallahi gaskiya yaya j mutum ne yasan harkan arziki sosai wallahi.
Tana budewa taci gaba da fadin da har ina kallon ina karawa g wanda muka sayo a can da zamu zo ashe ga wanda yaci uban wanan din a nan.
Wani irin ihu ta sake lokacin data bude wardrobe taga kayan shine ta sake wanan ihun a firgice tana taba kayan da ta gani din a ciki .
Yaushe duk zaki saka wanan kayan haka masu yawa yayan mu, gasu nan dai na bata amsa ina mikewa take fadin zan saka sau uku ko biyu a wuni nikan duk sai na saka su a jikina kafin mu koma.
Ta gama daddaga kayan ta juyo da nufin ganina a inda ta barni zaune bana wurin ina tsaye bakin mirrow dina ina kallon kayan shafen dake wurin.
Wani dan turare ne ya dauki hankalina na mika hannu na dauko ina karanta sunan shi sunan da larabci aka rubata shi aswad.
Jin hannun sadiya nayi a kafadana tana fadin wai amma yana da kyau sosai nace sadiya meye baida kyau a wurin nan.
Mun gama kallo muka koma kan waya zube muke saman gadon tana danne danne a wayan nikan barci ne ya fara daukana a wurin.
Fadila ta shigo dauke da tire da sauran tarkace tana fadin na dauka kunyi barci don gajiya kasan nan akwai nisa sosai da nan duk ka sauka sai ka yi hutun gajiya wallahi.
Bude idona nayi da suke a lumshe ina fadin saukin abin mun dan huta a Dubai kafin mu karaso nan din shine saukin mu ai.
Zama tayi daga gefe tana fadin ya bayan rabon mu ni kuma ina fadin ya jikin mama da sauki ko ?
Mama ta samu sauki sosai kafin na iso na samu baban yaran nan ya kaita asibiti an kula da ita nace kin fada min a waya yanzu dai jikin da sauki ko ?
Tace da sauki sosai uwar dakina ya wajen ku da alama abubuwa a yanzu kamar sun kamkama don alama ya nuna hakan.
Gaba dayan ku kunyi wani irin kyau kun kara haske kamar mutum ya sace ku wallahi nikan gaskiya da badon na san kuba sai nace baku bane gaskiya.
Dan murmushi na sake kafin nace kai anty ke nan wanan zuzutawan haka tace gaskiya na fada ance alaman kwanciyan hankali yana ga mai kiba .
Don wallahi kun sauya sosai a yadda na san ku don haka abubuwa a yanzu suna tafiya da sauki ga alama.
Bandai fadi komai ba sai murmushin da nakeyi sadiya ce ke fadin bayan ki kan ai munji dadin yaya fiye ma da yadda kika barmu anty.
Ke kan akace ko shekara nawa kayi baka ga mutum ba kada ka tambayi halinsa don hali na nan bai canza ba sadiya har yanzu.
Sadiya kan ai sai abinda ya karu na bata amsa ina mikewa tare da bude fruits salad din da ta shigo muna dashi na fara zubawa a hankali.
Naga kamar kun kasa cin abincin nace bari na hada maku wanan din ku dan ji nauyi yayane zaiso shan wanan din a yanzu don naga baici abincin sosai ba shi.
Mun zuba mai sadai bamu da halin shiga part din shi a yanzu sai dai idan ya fito barin gama na kai masa na bata amsa ta bini da kallo saidai ban san me haka ke nufi ba.
Kadan nasha na mike muka fito tare a dakin ina karewa gidan kallo a tsanake babban gidane kan wanan gidan sai dai part din mu yana kallon juna da nasa a sama amma akwai wani irin falo babba a rsakanin mu dashi.
Na karbi kayan da ta dauko a hannu ta na nufi part din data nuna min nasa sai dana kwankwasa na tura kofan na shiga dan karamin falone na wuce sai dakin kwanan shi ko ina yana kamshi a part din
Yana kwance saman gado ga sytem din shi a gefen kanshi bude sai dai ba aiki yake a ciki ba da alama yana aikin barci ya dauke shi.
Ganin halin da yake ciki yasa nayi shawaran juyawa kada in tayar dashi daga barcin sai dai hakan baikai ga samuwa ba naji ya motsa yana fadin.
Meke sa idan kin shigo kin samu ina kwance kike saurin juyawa ki fitane kin dauka zanyi barci mai nauyin da har za a shigo min ban sani ba ?
Banson in tayar da kaine daga barci don naga kamar ka samu barci a yanzu idon shi ya bude gaba daya ya sauke a kaina yana fadin.
Na dauka kina zaton ko zaki samu ina abinda baki kaunan ganin inayi ne yasa zaki koma don kin ganin a kwance.
Wanan yanzu ai ba damuwa na bane yaya tsakanin ka da mahalicin ka Allah ne wanan ka daina ko kayi wanan ya saura gareka kuma ?
Haka zaki fada yanzu ko ya fada yana kallon cikin idanuna sai ban yarda mun hada ido dashi ba na aje mai tiren a saman dan karamin table din dakin da yake kala daya da gadon nasa ina jawo table din zuwa gaban shi.
Don na kawar da zancen nace ga wanan ko zaka sha don naga bakaci abincin ba sosai dazun.
Naci mana ya fada yana mikewa kinsan bana cin irin wanan abincin kada ya saka jikina budewa sosai.
Da jikin ka zai budewa ai daya dade da budewa yaya don ruwan kwalban da kake durawa cikin ka sosai.
Zainab bana son jin wanan zancen a bakin ki don sanin kankine a yanzu na daina wanan harkan don haka bana son a tayar min da wanan zancen kuma .
Kayi hakkuri idan hakan dana fada laifine na barka lafiya na fada ina kokarin ficewa dakin yake fadin bakiji ba ko ?
Na juyo ina dan kallon shi yake fadin zuwa dare zamu fita zuwa gidan mami mu gaidasu idan zaku iya fita a yau din ko kuma a barshi da safe sai mu tafi.
Zaifi kyau yau din mu tafi na bashi amsa daga inda nake na rungume hannayena a jikina eh hakan zaifi don mamud ya fada mata muna garin tun safe.
Tayi fadan hakan ke nan na tambaya badan na shiryawa hakan ba fadan me zatayi tunda mun shigo kasan ko ?
Zo ki zauna ya fada yana gyara zaman shi da kyau tare da fadin idan bake ba wata mace ce zata shigo wurin mijinta aga ta fita haka da sauri.
Ai sai a dauka akwai rashin jittuwa a tsakanin mune kila kinkoga hakan ba zanji dadin shi ba daga zuwan mu ki bada mu haka ?
Yaya ke nan ka dauka ba,a san zaman da mukeyi da kai bane a hakan kana dauka kowane zaka iya wasa da hankalin shi a hakan.
Sai dai idan kin fadawa wani wanda ban debe tsamani fadilace ko zaki iya fadawa ban taba ki kamar sauran maza.
Wani kallo na watsa mashi da sauri tare da fadin kada ka daukeni yarinya kamar da bansan kaina ba har yanzu.
Ko a da can ban fada mat komai game da zaman mu da kai ba balle yanzu da hankalina ya kara zo min na fahinci me kake nufi dani.
Me nake nufi dake zainab ya fada a daidai lokacin da yakai cibin mix fruits din a bakin shi tare da bissimila a fili na dan kalleshi.
Don a kwaishi da wanan akidar na fadan bissimila ga duk abinda zaikai a bakin shi ko wani lokaci idan zaici abu.
Niko nasan kin kara girma a yanzu zainab don nasan kin fara kiyasta wasu abubuwa a tare dake .
Ban fara kiyasta komai ba saidai a yanzu din zan fara mutukar wanan halaiyar naka munana suna tare dakai yaya don ba zan zauna da wanda ke sabon Allah a fili ba haka gaskiya.
Da nai maki me a cikin zaman namu dan dama ina zargin hakan a gareki tuntuni saidai ki sani ba kowa zaki fadawa wanan zancen a yanzu ba ya yarda da zancen da zaki fada.
Saboda basu gani a jikina ba kome yasa ka fadi hakan ai jikin shike nuna kana cikin wani hali keko naki bai nuna hakan ba.
Shine hikimar ka a kaina banda wani hikima ko basira a yanzu da da can baya wanda yafi in ganki cikin farin ciki kamar haka ?
Da alama dai dadin zancen yake yana kuma bugun cikina da wayaun manyan yaji wani shiri nake a kansa yanzu da mukazo gida.
Farin ciki a haka yaya farin ciki zuciya tana cike da damuwa da tashin hankali akan mutum kullun ?
Zainab meye matsalan ki a yanzu dani kallo shi nayi da mamaki kamar zanyi magana sai kuma naja bakina nayi shiru ina kallon shi ban iya furta kai din kaine matsalata ba a yanzu kamar yadda na bashi amsa a zuciyana da hakan.
Bakinane yai subul da baka nace ina ko naga matsala dakai kana da irin su Taju dake debe maka kewa duk lokacin da bukatan hakan ya taso maka.
Na sani zainab nasani banda wanan din da kike ganin shine matsalan ki a yanzu dani baki da sauran matsalan komai bayan wanan.
Koshi din ai zaki iya idan kina so sai ki gwada ki gani ko zakici nasara a kaina har ki samu yadda kike so din.
Ka dauka yaya ina da feeling a kanka ne kamar yadda baka da wanan feeling din a kaina haka nima haka kwata kwata ban taba jin wani feeling akan kaba irin wanan.
Take naga annurin fuskanshi ya canza lokaci guda yace kina nufin baki da feeling kamar sauran mata akan mijin ki ?
Miji miji fa kace yaya ko yau bakin ka ya mantane har ka furta hakan a gabana bayan zaman kanwar ka nake ga idon kowa.
Haka dai kika fada zainab wanan zancen ai ya dade da wuce ko ga idon kowa don wayau ki yafi nawa yawa zainab.
Banda wayau bayan hakanndin haka ka tsawa zamana da kai yanzu kuma lokaci yayi da hakan zai kawo karshe na fada ina barin dakin.
Dakina koma raina na min zafi don wanan maganan da mukayi a yanzu watau yaya daukan jarababba yake min ko me ?.
Shiko na fita na barshi da tunane na a zuciya don abinda yake zargine ke shirin faruwa wanan yarinyar gab take da daukan wani mataki a kansa yanzu.
Me zanwa zainab na wake kaina kada ta kasa hakkuri ta fasa abinda ke tsakanin mu ne?
Wata zuciya tace mai baka saba da wanan halin nata bane a baya babu abinda zatayi duk hakan barazanane kawai na mata ka riga da ka gama da ita ko don babu inda ka ragota a yanzu kan wurin zamantakewa ya fada.
Sai kawai ya shafe zancen da basarwa don yasan haka dinne ba wani abinda zanyu inma zanyi din nice dai a kasa bashi ba.
Don babu mai yarda da duk wani abinda zan fada a yanzu don za a dauka sherine kawai na mata a hakan.
Hannun shi yakai ya shafo gaban shi da kusan wata da watani ke nan yake fama da wanan matsalan yaji shi a lankwas kamar kullun.
Hannun ya mayar a fuskan shi yana shafowa a hankali shi yanzun ma ba zaice ga ta inda matsalan ya fara mashi ba.
Don dai yasan cewa da farko bayan maganin dana basa a Dubai yana tare da lafiyan shi na mazakuta sai daga bayane ya fara fuskantar wanan matsalan da yake ji a yanzu tare dashi.
Gashi ya kasa fadawa kowa bayan likitan shi da yagani kan wanan zancen a chaina ya kuma dubashi yace lafiya komai nasa yake.
To a ina wanan matsalan ya taso masa shi dai ba zaice zainab din bane da wanan matsalan sai kawai yake danganta kansa da kawai don yanzu baijin sha,awan ko wani irin jinsi don jin dadin rayuwan shi ya kawo masa hakan.
Da kyat ya mike ya shiga bathroom don ya watsawa jikin shi ruwa sai dai har ya fito zuciyar shi yana cike da tunane kala kala daya kasa fahinta.
Nikan sallah nayi sai a lokacin na samu barci ya daukeni sosai don na samu barci har lokacin sallah la,asar ya wuce ni sosai.
Bayan na samu na tashi da kyat na shiga bandaki na dauro alwala nayi sallah ban fito ba dakin na zauna ina dan dube dube a cikin wayata sabuwa daya saya min.
Sosai nake jin dadin wayan don komao na wayan yana da kyau sosai kafin hankalina ya dauko ga tunane ba abinda yazo min a rai sai zancen zuwa gidan mami daya ce zamuyi da yammanan nake tunanen yadda mami din zata karbe ni .
Dukda mun shirya sama sama a yanzu da ita sai dai ina tsoron halin dan adam tunda har yanzu bawai na kwanta mata a rai bane.
Koma meye wanan karon kam nasan ba zan yarda daduk wani rainin wayau kowa ba a kaina don ga kura mai laifi basu gani saini da banci ban sha za a dinga dora laifi a kaina ?
Sadiya na tuna tun fitana dazun ban kara ganin ta ba hakan yasa na mike zuwa dakin da take tana ciki da waya tana faman yin game hankalinta ya dauku a wayan.
Jin motsina yasata dago kai tana kallona tare da fadin ashe kin tashi yayan mu na shiga dazun na samu kina barci.
Ke wai me yasa bakya jin magana sadiya wanan yasa nake hanaki rike waya don sai ya canza maki akidar ki ga baki daya wallahi.
Ina fara magana tayi saurin lkashe wayan tana ajewa gefen filonta da sauri zaune nakai cikin bacin rai ina fadin kinga akan wayan nan zamu samu matsala babba dake don akan wanan hali zan mayar dake na dauko binta mu zauna tare don ita ban taba jin tayi wani abin rashin ji ba .
Ina kokarin yi mata wanan nasihan ne don gujewa gurbacewan rayuwan ta nan gaba a kan waya duba ga yadda naga daga shi har kannen sa basu da lokacin kowa akan wanan nauran a rayuwan su don zai iya zama dakai na tsawon awan ni ba tare da yai magana dakai ba hankalinshi naga waya yana tabawa kawai.
Duba ga hakan nake tsoron kada ta tashi da wanan akidar nan gaba ya zame mata hitina a rayuwa gashi mu ba diyan wasu a tarihin mu.
Idan na fara irin wanan fadan taka natsu sosai ta daina duk wani abinda takeyi ko yanzuma din da nake magana hakane ya kasance a tsakanin mu.
Kuma ina son ki saurareni da kyau kiji duk wani tambayan da fadila ko wani zai maki akan rayuwan mu kada ki yarda inji ance ga abinda kika fada don idan naji da Inna zan hadaki wanan karon.
Bazan fada mata komai duk tambayan da zatayi min idan kinyi hakan kin kyautawa kanki na bata amsa ina mikewa don barin dakin.
Shiru tayi tana bin lafiyan filo ta kwanta tana kallona har fice dakin ta sauke ajiyan zuciya tare da fadi ta rasa meya sa nake yawan tsanan ta mata hakane ?
Daki na koma har lokacin banjin dadi a kasan zuciyana kawai naji na tsani komai sai bacin rai dake kara min yawa nakeji .
Duk a kan dan maganan da mukayi da yaya J a ranan kawai nake jin raina yana wanan bacin da yake min.
Allah ya taimaka har tara na dare ya wuce banji yace mu fito zuwa gidan mami din ba daya fada zamu shiga da dare.
Hakan yasa na fara shirin kwamciya kafin Fadila tayi min sallama ta shigo dakin tana fadin taga fitan mijina a cikin daren nan ko lafiya ya fita a wanan lokacin.
Tabbas tunane na ya fara zama min gaskiya akan fadila shiyasa yanzu nake taka tsantsan da ita wani lokaci.
Don na fara zargin wani abu akanta da yanzu wayau na da hankalina suka fara kawo min haske akanshi don yawan tambayayin da take min lokaci lokaci koda a wayane kuwa idan muna wayan.
Har yakai hankalina da tunanena sun fara hasko min wasu abu a kanta ko yanzun ma tambayan data jefo min ya kara rikitani tana fadin.
Ko dai mijin naki bai bar wanan harkan bane har yanzu a cikin mamaki na juyo ina fadin harka wani harka ke nan fa ?
Sai kuma ta rasa abinda zata fada min kan hakan tace wai irin dai halaiyar nan da yakeyi a baya.
Ance mutum mai yawan murmushi baka fahintar bacin ranshi lokaci guda sai dai ya jefaka a cikin kwankwanto da zargin kanka kaida yakewa wanan murmushin a lokacin.
Hakan ne ya faru da fadila dani sai kuma ta fara dan kame kame tana fadin a yanzu kan ai komai ya wuce da alama akwai fahinta a tsakanin ku a yanzu.
Dama babu ne na tambaye ta cikin alaman mamaki a fuskana naci gaba da fadin ban taba fada dashi ko wani rashin yarda wanda ya shafi ni dashi har wani ya sani na bata amsa.
Tare da karewa da fadin bana shiga harkan shi hakan ya kara jawo mana zaman lafiya a tsakanin mu wanda ko wace mace ke fata da mijinta.
Itama din kallon mamaki ta bini dashi lokaci guda tana dan murmushi a fuskanta nima hakan nakeyi.


YA HAIYYU YA KAIYUMU YA ALLAH KA KARBI IBADUN MU KASA MUNA CIKIN YAN TATTUN BAYIN KA A WANAN WATAN MAI RAHAMA DA DAUKAKA ALLAHUMA AMIN, , , ,

LITTAFIN KUDINE KI BIYA DARI UKU KI KARANTA YAR UWA DON ALLAH KI GUJEWA SHIGA HAKKIN WANI YAR UWA KAN ABIN DUNIYA, , , ,

Na san mai karatu zakiyi mamaki jin abinda na fada akan fadila hakan kuma ya samo asaline tun ranan dana fara gane waye fadila a gurin mu.
Ranan kishin ruwa kawai ya tayar dani a cikin dare na fito don neman ruwan da zan sha a lokacin.
Banyi amfani da ko wani irin haske ba don nasan inda ruwan yake sauri kuma ya hanani tsaya na dauki ko wayana in haska.
Har na dauko ruwan zan fito naga kamar gittawan mutum a falon namu karami.
Naji tsoro iya tsorata nayi shi don haka na samu wuri na lafe a bayan kofan kitchen din muryan fadila naji tana waya a hankali.
Tana fadin wallahi duk dabaran da zanyi in gane wani abu a gareta nayi shi har yanzu ban gane komai ba a wurin ta .
Don yarinyar akwaita da shegen wayau tsiya don wayau ta yafi karfin shekarunta sosai wallahi.
Na saka ido sosai don in fahinci wani abu a gurin shi na kasa fahintar hakan duk da janta danayi a jiki sosai abu daya na sani shine.
Yana shan cocaine din amma baya harkan sayarwa don aikin sa a nan yana jawo mai babban riba da samu fiye da zaton me zaton hakan.
Shiru tayi tana sauraren me ake fada mata a wayan kafin tace zan saka ido kafin tafiyana yazo sosai zan kara gano wani abu a hakan.
Kara lafewa nayi sosai inda nake boye ina mamakin ta a raina kafin naji tayi sallama da maishi tana kashe wayan ta dan haska ko ina ta koma daki.
Sai dana dan dade ban fito daga inda nake boye ba kafin na fito na koma daki cikin tunanen wacece fadila din ?
Haba abin mamaki ne ace mace wayayya kamar fadila tana aiki irin wanan haka sai dai mutum ya duba ga irin yanayin da kasan mu ke ciki na rashin aikin yi zaisa mutum yayi duk wani aikin daya samu don dogaro dakai.
Tun wanan ranan na kara tsorata sadiya a kanta ta kuma tsorata duk tambayan da tayi mata takan zo ta fada min da amsan da ta bata a lokacin.
Sai gashi bayan kwana biyu tana fada muna gida zata wai mahaifiyar tace ba lafiya a lokacin.
Yanzu yana da wuya kayi saurin yarda da mutum farat daya irin haka Allah ya taimakeni ga zurfin cikina.
Nidin na kasance irin mutanen ne da basu da yawan sake magana ga kowa idan hakan ba ya kama dole bane.
Idan zan tuna duk hiran mu ko sakewan da zanyi sai dai ita din ta kasance mai ban shawara ko tayi magana akan abinda tagani da idon ta tana bugun cikina.
Kinji dalilin daya sa yanzu nake ja baya da zancen fadila din duk da bansan dalilin kasancewar ta a cikin mu ba har wanan lokacin.
Bamu hadu da yaya J ba sai washe gari misalin sha biyun rana da nake ganin fitowan shi ke nan daga barci.
A falo ya same mu na gaji da kwanci na fito muna zaune da sadiya fadila ta bar wurin zuwa kitchen duba masu aiki a can.
A daidai lokacin tana dawowa yake fadin pretty ya kike na dan dago kai na kalle shi tare da fadi cikin wani yanayi lafiya ya gajiya ?
Akwaishi wallahi sai yanzu na tashi ki bani abinci na danci zan fitane yanzu ya fada yana zama a gefena kaina dago kafin inyi magana ta juya zuwa wurin da za, a shirya mashi abincin kamar yadda ta saba yi.
Yadda muke zaune zaka dauka mu din wasu ma,aurata masoyan juna a lokacin don ya zauna ya dan kwanto min a jikina .
Fadin an hada table da tayi yasa na rigashi mikewa na nufi dinning din ina duba abincin ya biyoni a baya.
Zama yayi na fara zuba mai abincin bayan na gama na samu wuri na zauna a gefen shi zakace zaman arziki mukeyi dashi a lokacin yadda muke nunawa.
Yana ci muna dan hira har lokacin daya kare ya goge bakin shi ya mike ya danyi hugging dina yana fadin sai na dawo.
A dawo lafiya nayi masa na mike na bar wurin cin abincin nan koma inda na tashi ba da farko dakina na nufa.
Ina shiga daki take cewa sadiya da alama dai yanzu sun daidaita tsakanin su ko take tambayan sadiya din ?
Dama ba daidaitane a tsakanin su anty ta tambayi fadila din cikin mamaki sanin halin sadiya yasa ta basar da zancen itama sadiyace data shigo take fada min yadda sukayin.
Bani da wani buri a yanzu illa inji ya kawo zancem zuwan mu gida wurin iyayyen mu duk da ko gidan mami ma da yake garin bamu je ba suma basu leko inda muken ba har yau kwanan mu biyu da zuwa kasan.
Tunane nayi dan ganin dacewan hakan ya dawo da yamma nake fadin yaushe ne zamu gidan mami mu gaida su din duk da nasan kai ka tafi ko kun gaisa ko.
Ko yau ina can tunda na fita muna tare dasu idan kun huta sai mu tafi lokacin da kuka shirya hakan ya bani amsa.
An jima zamu idan Allah ya kaimu na fada ina shirin barin dakin naji yace sai ki fitar da tsaraban da zaku kai masu idan zaku tafi.
A cikin mamaki nace ba wani tsara dama dai turarene sai wasu jewels dana sayo da zamu zo na fada ina kallon shi.
Tsara yana dayan dakin nan sai ki duba kiga abin daya dace ku kai masu a ciki da duk wani wanda ya dace aba shi tsaraban.
Ba mamaki don sanin halin sa nace angode kawai na fita zuwa dakin don duba kayan suna daure har lokacin ba a bude su ba.
Don haka ban san ko meye a cikin kayan ba na juya na fita na koma daki da niyar fara shirya fitan da zamuyi din.
Ban fadawa kowa zancen fitan ba ko sadiya don gudun ta fadawa wani hakan sai bayan sallah magariba nace taje ta shirya inji yaya zamu fita.
Ta juya da murna ta fita nima na zauna ina idar da isha,i na shirya wanan dakin na koma na samu an bude kayan a lokacin na shiga duba ina zaba.
Kayane irin na tsaraban mata da maza sai wasu abubuwan da ban sani ba na dai dauki wanda zan dauka na fito.
Shiyasa aka kwasa zuwa cikin mota da zamu fita da muka fito na rufo kofan da key din dana gani a wurin na zare key din har kofan da zai sada mutum da part din mu da nasa sai da na rufo na jefa key din a jakkata.
Wani iska ne mai dadi ya daki jikina har hanci mai dadi muka tako a hankali zuwa wurin motan dan shi a baya muka barshi bai fito ba.
A hankali motar ke tafiya muryan sadiyane ke fadin anty tace bata san zamu fita ba wai.
Baki fada mata zaku fita bane ya tambayeni daga gefena nace ban fadawa kowa ba ya sake fadin har fadilan ?
Ban fada mata ba don ta canza yanzu a sanin da nayi mata a baya ke sai yanzu kika san da hakan ya tambayeni ?
Na juyo na dan kalleshi yake fadin na sani ita din yar sandan ciki ce bincike takeyi a kaina sai dai tana dauka ban sani bane .
Sai dai ya akayi ke kika san hakan ya tambaye ni cikin son jin amsa nace zuciyana ne ya bani hakan ban fada mai komai dana sani game da ita ba.
Amma kina da abin mamaki zainab yadda har kika gano hakan da sauri da kanki game da fadila din ?
Idan ina zaune da mutum tsakani da Allah nake zama dashi shiyasa Allah ke nuna min ko waye maishi da sauri haka ban taba zama da wani mutum da wani manufa saidai kai ka da muke zaune ka munafunceni.YA HAIYYU YA KAIYUMU YA ALLAH KA KARBI IBADUN MU KASA MUNA CIKIN YAN TATTUN BAYIN KA A WANAN WATAN MAI RAHAMA DA DAUKAKA ALLAHUMA AMIN, , , ,

LITTAFIN KUDINE KI BIYA DARI UKU KI KARANTA YAR UWA DON ALLAH KI GUJEWA SHIGA HAKKIN WANI YAR UWA KAN ABIN DUNIYA, , , ,

Na san mai karatu zakiyi mamaki jin abinda na fada akan fadila hakan kuma ya samo asaline tun ranan dana fara gane waye fadila a gurin mu.
Ranan kishin ruwa kawai ya tayar dani a cikin dare na fito don neman ruwan da zan sha a lokacin.
Banyi amfani da ko wani irin haske ba don nasan inda ruwan yake sauri kuma ya hanani tsaya na dauki ko wayana in haska.
Har na dauko ruwan zan fito naga kamar gittawan mutum a falon namu karami.
Naji tsoro iya tsorata nayi shi don haka na samu wuri na lafe a bayan kofan kitchen din muryan fadila naji tana waya a hankali.
Tana fadin wallahi duk dabaran da zanyi in gane wani abu a gareta nayi shi har yanzu ban gane komai ba a wurin ta .
Don yarinyar akwaita da shegen wayau tsiya don wayau ta yafi karfin shekarunta sosai wallahi.
Na saka ido sosai don in fahinci wani abu a gurin shi na kasa fahintar hakan duk da janta danayi a jiki sosai abu daya na sani shine.
Yana shan cocaine din amma baya harkan sayarwa don aikin sa a nan yana jawo mai babban riba da samu fiye da zaton me zaton hakan.
Shiru tayi tana sauraren me ake fada mata a wayan kafin tace zan saka ido kafin tafiyana yazo sosai zan kara gano wani abu a hakan.
Kara lafewa nayi sosai inda nake boye ina mamakin ta a raina kafin naji tayi sallama da maishi tana kashe wayan ta dan haska ko ina ta koma daki.
Sai dana dan dade ban fito daga inda nake boye ba kafin na fito na koma daki cikin tunanen wacece fadila din ?
Haba abin mamaki ne ace mace wayayya kamar fadila tana aiki irin wanan haka sai dai mutum ya duba ga irin yanayin da kasan mu ke ciki na rashin aikin yi zaisa mutum yayi duk wani aikin daya samu don dogaro dakai.
Tun wanan ranan na kara tsorata sadiya a kanta ta kuma tsorata duk tambayan da tayi mata takan zo ta fada min da amsan da ta bata a lokacin.
Sai gashi bayan kwana biyu tana fada muna gida zata wai mahaifiyar tace ba lafiya a lokacin.
Yanzu yana da wuya kayi saurin yarda da mutum farat daya irin haka Allah ya taimakeni ga zurfin cikina.
Nidin na kasance irin mutanen ne da basu da yawan sake magana ga kowa idan hakan ba ya kama dole bane.
Idan zan tuna duk hiran mu ko sakewan da zanyi sai dai ita din ta kasance mai ban shawara ko tayi magana akan abinda tagani da idon ta tana bugun cikina.
Kinji dalilin daya sa yanzu nake ja baya da zancen fadila din duk da bansan dalilin kasancewar ta a cikin mu ba har wanan lokacin.
Bamu hadu da yaya J ba sai washe gari misalin sha biyun rana da nake ganin fitowan shi ke nan daga barci.
A falo ya same mu na gaji da kwanci na fito muna zaune da sadiya fadila ta bar wurin zuwa kitchen duba masu aiki a can.
A daidai lokacin tana dawowa yake fadin pretty ya kike na dan dago kai na kalle shi tare da fadi cikin wani yanayi lafiya ya gajiya ?
Akwaishi wallahi sai yanzu na tashi ki bani abinci na danci zan fitane yanzu ya fada yana zama a gefena kaina dago kafin inyi magana ta juya zuwa wurin da za, a shirya mashi abincin kamar yadda ta saba yi.
Yadda muke zaune zaka dauka mu din wasu ma,aurata masoyan juna a lokacin don ya zauna ya dan kwanto min a jikina .
Fadin an hada table da tayi yasa na rigashi mikewa na nufi dinning din ina duba abincin ya biyoni a baya.
Zama yayi na fara zuba mai abincin bayan na gama na samu wuri na zauna a gefen shi zakace zaman arziki mukeyi dashi a lokacin yadda muke nunawa.
Yana ci muna dan hira har lokacin daya kare ya goge bakin shi ya mike ya danyi hugging dina yana fadin sai na dawo.
A dawo lafiya nayi masa na mike na bar wurin cin abincin nan koma inda na tashi ba da farko dakina na nufa.
Ina shiga daki take cewa sadiya da alama dai yanzu sun daidaita tsakanin su ko take tambayan sadiya din ?
Dama ba daidaitane a tsakanin su anty ta tambayi fadila din cikin mamaki sanin halin sadiya yasa ta basar da zancen itama sadiyace data shigo take fada min yadda sukayin.
Bani da wani buri a yanzu illa inji ya kawo zancem zuwan mu gida wurin iyayyen mu duk da ko gidan mami ma da yake garin bamu je ba suma basu leko inda muken ba har yau kwanan mu biyu da zuwa kasan.
Tunane nayi dan ganin dacewan hakan ya dawo da yamma nake fadin yaushe ne zamu gidan mami mu gaida su din duk da nasan kai ka tafi ko kun gaisa ko.
Ko yau ina can tunda na fita muna tare dasu idan kun huta sai mu tafi lokacin da kuka shirya hakan ya bani amsa.
An jima zamu idan Allah ya kaimu na fada ina shirin barin dakin naji yace sai ki fitar da tsaraban da zaku kai masu idan zaku tafi.
A cikin mamaki nace ba wani tsara dama dai turarene sai wasu jewels dana sayo da zamu zo na fada ina kallon shi.
Tsara yana dayan dakin nan sai ki duba kiga abin daya dace ku kai masu a ciki da duk wani wanda ya dace aba shi tsaraban.
Ba mamaki don sanin halin sa nace angode kawai na fita zuwa dakin don duba kayan suna daure har lokacin ba a bude su ba.
Don haka ban san ko meye a cikin kayan ba na juya na fita na koma daki da niyar fara shirya fitan da zamuyi din.
Ban fadawa kowa zancen fitan ba ko sadiya don gudun ta fadawa wani hakan sai bayan sallah magariba nace taje ta shirya inji yaya zamu fita.
Ta juya da murna ta fita nima na zauna ina idar da isha,i na shirya wanan dakin na koma na samu an bude kayan a lokacin na shiga duba ina zaba.
Kayane irin na tsaraban mata da maza sai wasu abubuwan da ban sani ba na dai dauki wanda zan dauka na fito.
Shiyasa aka kwasa zuwa cikin mota da zamu fita da muka fito na rufo kofan da key din dana gani a wurin na zare key din har kofan da zai sada mutum da part din mu da nasa sai da na rufo na jefa key din a jakkata.
Wani iska ne mai dadi ya daki jikina har hanci mai dadi muka tako a hankali zuwa wurin motan dan shi a baya muka barshi bai fito ba.
A hankali motar ke tafiya muryan sadiyane ke fadin anty tace bata san zamu fita ba wai.
Baki fada mata zaku fita bane ya tambayeni daga gefena nace ban fadawa kowa ba ya sake fadin har fadilan ?
Ban fada mata ba don ta canza yanzu a sanin da nayi mata a baya ke sai yanzu kika san da hakan ya tambayeni ?
Na juyo na dan kalleshi yake fadin na sani ita din yar sandan ciki ce bincike takeyi a kaina sai dai tana dauka ban sani bane .
Sai dai ya akayi ke kika san hakan ya tambaye ni cikin son jin amsa nace zuciyana ne ya bani hakan ban fada mai komai dana sani game da ita ba.
Amma kina da abin mamaki zainab yadda har kika gano hakan da sauri da kanki game da fadila din ?
Idan ina zaune da mutum tsakani da Allah nake zama dashi shiyasa Allah ke nuna min ko waye maishi da sauri haka ban taba zama da wani mutum da wani manufa saidai kai da muke zaune ka munafunceni.
Oh really ?
Ya fada kanshi na duke yana duban wani takardan dake hannun shi hankalina na mayar ga titi da muke tafiya.
Har motan ya sha kwanan da zai sada mu da gidan mami din dake wani katon unguwa mai gine gine masu kyau da daukan hankali.
Gaba daya sai gidan ya canzawa sanin danayi mai a baya saida muka fito ne a cikin mota na tabbatar da ba wancan gidan bane da muka zauna dasu a baya.
Allah ya gani ban shiga gidan da wani manufa a zuciyana ba lpkacin sai gashi muna shiga komai ya canza a lokaci daya.
Da farko mun shiga da sallama mun jero tare da yaya sai sadiya dake dan bayan mu kadan tana biye damu a bayan mu.
Ko kaine wa dole mu baka sha,awa yadda muka shigo gidan a lokacin gaba dayan su suna falon mami din a zaune har Nuriya da yaran ta kamar wani abu sukeyi a lokacin.
Jalal kan ya amsa muna sallama da nuna murshin da ganin mu yana fadin a, a mutanen chaina ne yau a gidan namu haka ?
Sai ya jamal daya dago cikin mamaki yana fadin a, a zainab kuma kun zone ashe sannun ku da zuwa a cikin fara,a.
Ya jalal mun sameku lafiya na fada tun a tsaye kafin na juya wurin ya jamal ina fadin ya jamal ya gida ya aiki ?
Zainab ai sai mutum ya dauka kema yar chaina din ce ko yar wani nahiyar larabawa yadda kika koma din nan inji ya mamud ya fada cikin yar fara,a.
A daidai lokacin dana zube gaban mami itama sadiya ta zube kamar yadda taga na zube din muna gaida mami.
Sai ji nayi ya jafar shima ya zube a kusa dani yana fadin kamar yadda na fada mami ina wuni mun samuku lafiya.
Duk suka kwashe da dariya banda mami data daure fuska tana fadin kai yanzu bakaji kunya ba ace kuna kasan nan tun shekaran jiya amma sai yanzu matar ka zata shigo gidan gaishe mu ?
Haba mami kin san suna tare da gajiya nine nace ta bari su huta sai na kawo su na kuma fada maki ai a waya.
Kaina yana sade a kasa koda take wanan maganan can na dago na dan kalli inda yan matan gidan da ya mamud da matar shi suke zaune nace yaya mun same ku lafiya anty ya gida ya yara ?
Kafin nace kuma anty mun sameku lafiya ya gida ya aiki da karatu duk a lokaci guda na jera masu gaisuwan a tare.
Sai ya mamud ne da anty Na,ima suka amsa mun da fara,a suna fadin munzo lafiya ya can ni sai lokacin ma nasan ashe Nuriya matar ya mamud ta kara haihuwa ashe .
Don na ganta da yarinya karama dauke a jikin ta da alaman har an yayye yarinyar ma a lokacin .
Muryan mami naji tana fadin sarauta dai da jin kai irin na samun wuri har zainab ce yau za a ce wai tana hutun gajiya irin haka a rayuwan ta.
Da sauri na juyo na dan kalli mami din kafin naji ya jalal yace haba mami sai kace ita din ba mutum bane naga ke idan mun dawo har karin ruwa ake maki fa.
Gasu dai gwanin ban sha,awa kamar ace da yara suke tafe shine abin zaifi burge mutane ai ba a tafi uwar duniya a dawo haka babu ko kwai ba.
Nuriya ta fada tana wani irin dariyan shu,umanci a fuskanta wanan kuma sai idan da Allah kike jayayya don shine mai bada haihuwa lokacin da yaso kuma a inda yaga dama.
Zainab tashi muje ya J ya fada yana mikewa fuskan shi a daure da sauri ya mamud yace ku tafi ina yanzu kuna shigowa zaku tafi kuma.
Dole mu tafi don ba zan lamunci cin fuska irin haka ga iyalina ba ga kowa duk wanda yace zai taba min mata kamar ni ya taba don haka ba zan dauki wanan ba.
Kayiwa matan ka iyaka kan sake zancen daya shafeni idan ma haihuwan takewa zainab gori dashi ai ba zainab bane mai laifi don nine raggon namijin dana kasa bata cikin ta haifa.
Falon yayi tsit a lokacin kamar babu kowa a cikin sa sai Nuriyan ne tayi karfin halin fadin yo ni ai da wasa kuma naga dacewan hakan na fada don yaci ace yanzu kun fara aje iyali ai.
Kai wanan halin baiyi ba wallahi kamar kuna jirace da yarinyar nan tazo ku gasa mata magana haka.
Duk da dai mami ke kika fara bada hanyar yin hakan sai dai ku sani a yanzu kuna falon kaf banda mami babu wace ta kama kafar zainanb ko mijin da komai da har zaku tare ta da wanan zancen haka.
Kema mai haihuwan aiba rawa ko kida kikayi gaban Allah ba ya baki su da kika tareta da wanan zancen mara dadin ji jamal ya fada yana jan tsuki ya bar falon a fusace.
Nuriya ke nan yanzu dai kinji idan ma dama kina jiran inxo ki gasa min wanan maganan ne haka daga shigowa na kamar kina jirace dani.
Na fada a daidai lokacin dana mike tsaye sadiya ma ta mike tana manne dani kamar taga abin tsoro a falon.
Gaskiya haka baiyi ba Nuriya at,list ai kya bari ta huta kafin ma ki fadi abinda ke ranki ai Aisha ta fada.
Ballwma ko an raina dan tsuntsu ba acin shi da gashi don anyi sake dan zaki ya girma ko gaskiyar jamal ne Nuriya zainab dai ba abin yarwa bane yanzu don muje ta muna goma na arziki gaba dayan mu nan Na,ima ta fada tana mikewa.
Saida safe mami na fada ina bin bayan ya j din daya fara tafiya a lokacin kafin na juyo ina fadin ga tsaraba nan mami da muka zo dashi ayi hakkuri dashi ba yawa.
Na sa kai nabi bayan shi ins jin ya mamud na fadin kin gani mami saida nace kada kiyi wanan zancen a gaban su tunda ya fadi uzurin shi kika yi a gaban wanan mara hankali da tunane.


ZAINAB IDRIS MAKAWAZAINAB IDRIS MAKAWAYAN UWA DA FATAN MUN WUNI LAFIYA YA IBADA ALLAH YA BAMU KARFI DA LAFIYAN BAUTA MASHI BAUTA TSAKAKAKE A RAYUWAN MU ALLAHUMA AMIN


LITTAFIN KUDINE YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DA SAUKIN FAHINTA BA TARE DA DAUKAN HAKKIN KOWA BA A KANKI, , , ,
DON KIRA 08036959257 KO 09026931792 ACCOUNT 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK, , ,

Babu wanda yai magana da dan uwa tun fitowan mu cikin gidan mami din sai tafiya yake damu a guje a haka har muka karasa bakinn wani plaza ya juyo inda sadiya take yana fadin ya sadiya mu tsaya a sai wani abune a nan ?
Da sauri ta girgiza kai tare da yaya muje gida kwai hakan ya nuna itama din a tsorace take a lokacin da abinda ya faru.
Ya mike zuwa hanyar gidan namu horn ya danna saiga masu get sun bude da sauri don sheda horn din motan da sukayi.
Motan na tsaya nayi saurin fita daga motan na dauka shima fita zaiyi a lokacin saidai muna fita sai naga ya juya ya fita daga gidan.
Muna shiga falon fadilace ta tare tana muna sannu da dawowa na amsa take fadin ai ta dauka zamu dade ashe yanzu zamu dawo.
Eh na bata amsa dashi don ina ganinta zancen ta da mukayi ya fado min a rai lokaci guda ina ganin ta na tuna wai ashe ita din yar sandan ciki ce take zaman leken asiri a gidan mu to akan me na tambayi kaina ?
Maimakon na zauna a falo kamar yadda muka saba nake fadin bari kawai na rage kayan jikina sai na nufi hayar dakin inda sadiya ma take biye dani bata zauna ba a falon itama.
Mun wuce munbar fadila da mamakin mu a fili kafin ta sauya tunanen ta da cewa wata kila gidan mami muka je aka bata muna rai a can.
Tsoranta nake ji yanzu sadiya ta fada a bayana yasa na juyo ina fadin tsoron wa ke nan anty mana naji yaya yace ita din yar sandace wai .
To kinga kada ki soma yin wani abinda zata gane kin san komai a wurin ta tunda har mun gane ta sai mu bita da hakan shike nan.
Wa zata kama a gidan nan anty da take zaune a nan nima tunanen da nakeyi ke nan sadiya saidai nasan don yaya take wanan aikin a nan mukan meye ruwan mu a ciki tunda bamuyiwa kowa laifi ba .
In ma har mamice ta turota nasan ba zata taba kamani da laifin komai ba tunda banyi ba insha Allahu.
A dakin muka kwana tare da kanwata da barci ya daukemu bamu ma sanda hakan ba tun muna hiran abinda ya faru a gidan mami har mukai shiru muka fara barci.
A cikin dare na falka a dan tsorace na tuna ban rufe kofa ba lokacin bayan na rufene na shiga bandaki na dauro alwala ba abinda nake tunane sai kalamin Nuriya wanda nasan dani take wanan maganan .
Ba komai yasa haka ba sai hangen nesa da take min tana ganin kanar duk dadin duniya da daula ya kare a gareni yanzu.
Wanda ita bata san ABU CIKIN DUHU SIRINE BA ba ko wani dadi yakan daure a dadin da take zato ba ba tare da kalubalin rayuwa a bawa ba.
Hawayen takaici da bakin ciki suka fara zubo min masu zafi daga idanuwana a daidai lokacin da wani tunane ya ziyarci zuciyana na mike lokaci guda na fara ibada sai bayan na dauki lokaci na shafa tare da waigawa inda naji motsin sadiya ina kallon ta sai barcinta take a tsanake hankali kwance nace kin huta baki da damuwa sadiya.
Washe gari tun bayan idar da sallah mu da asubah sadiya ta koma dakinta ta kwanta nasan tayi gudune don kada ince ta tsaya muyi tulawan safe da mukanyi wani lokaci idan ta kwana dakina da safe.
Nima din ranan ban iya tabuka komai ba gado na koma na kwanta tare da dunkulewa wuri daya a haka barci ya daukeni kuma.

Tun daren jiyan ya kasa tsayar da tunanen shi wuri daya har zuwa wayewan garin da bai samu sukuni a tare dashi ba.
A gaskiya ya jefa yarinyar nan a cikin wani hali yasan shikan da badon Allah yai mai zabin mata irin zainab ba a rayuwan shi da yanzu kila ya auri mata sun fi a kirga yana sakin su don halin shi.
Shidai yasan bai iya tsinanawa mace komai na abinda ya shafi jin dadin aurataiya har ya kai ga an samu ciki don tara zuria.
Sam irim wanan tunanen baizo mashi a raiba da farko sam ya manta babu wani babban buri ga dan Afirca kamar ya ga ya tara iyali a karshen rayuwan shi.
Yau sai gashi tun ba,aje ko ina a gaban shi an fara suka na da zance mafi tayar da hankalin wanda ake fadawa hakan.
Nuriya why zaki shigo cikin lamarina haka da gagawa ki bata min tsarin komai da nake shiryawa a kan mu.
Yasan wanan zancen ba waiba zai iya jawo masu matsala a tsakanin shi shida zainab din komai hakkurin ta kuwa.
Don komai hakkurin ka akai ma gori akan haihuwa kuma laifin ba naka bane dole ranka ya baci ga hakan.
Balle shidin da zainab da ba wani irin wanan mu,amulan a tsakanin su da har zai kai ga tunanen haihuwa nan gaba.
Idon shi ya lumshe a hankali yana sauke ajiyan zuciya don numfashin shi da yake ji yana harde mai lokaci guda daga inda yake kwance saman gadon dakin nasa.
A hankali ya fara tunu abubuwan da suka faru dashi tun farko har ya tsunci kanshi cikin wanan harkan duk da ba zai iya cewa ga dalilin fara hakan ba gareshi.
Da idan akwai wanda ya tsani wanan halaiyar a bayan shi yake sai gashi dumu dumu yau a cikin wanan harkan daya tsana din yana yi.
Wani irin nauyi yaji zuciyar shi na mashi lokaci guda da har bai iya sauke numfashi ya sauka mai yadda ya dace.
Da kyat ya dago daga kwancen yana dafe da zuciyar shi ya kai zaune har lokacin hannun shi na saman chest din shi kafin ya samu ya sauke numfashi da karfi yana runtse idanun shi .
Ya dade zaune a hakan kafin ya mike cikin rashin jin dadin komai a lokacin ya nufi hanyar fita daga dakin nasa.
Direct part dina ya nufa kai tsaye ya tura kofan dakin ya jishi a bude duk da safiyane sosai a lokacin yayi mamakin ganin kofana a bude.
Kai tsaye yasa kai ya shiga babu kowa a falon ya nufi uwar dakin da yake tunanen ina ciki a lokacin.
Can ya hangoni kwance tsakiyan gado na dunkule a wuri daya ina barci kamar a wahalce nake yadda na kwanta din.
Ya dan dade tsaye yana kallona yasan dalilin maganan jiyane daya faru a gidan mami din ne ya kawo min rashin barci a daren jiyan.
Kamar zai fita sai kuma kawai ya nufi gadon ya hawo a hankali har zuwa inda nake kwance din ya kwanta ya rungumeni a jikin shi.
Ga mamakin shi sai yaga na gyara kwanciya ina kara shigewa cikin jikin nasa duk a ciki barcin da nakeyi nayi hakan .
Shima ajiyan zuciya ya sauke a nasa bangaren yana jin tausayin kanmu a karo na farko da nadama a rayuwan shi.
Ga kamshin bodyspray din da nake amfani dashi yana shiga mai hancin tare da saukar mai da wani irin yanayi a zuciyar shi da ba zaice ga irin abinda yake ji ba lokacin sai kara rungumeni a jikin shi dayayi a hakan.
Mun kai wani lokaci yana shakan kamashin man gashin da nake amfani dashi wanda har yakai ga daukan hannun shi a hankali ya cusa a tsakiyan gashin kaina dake kwance lub yasha gyara yadda na kamashi wuri daya da zan kwanta tunda ba kitso muke samun yi ba.
Can a cikin barcina nake ji nauyin mutum a jikina sai nake gani kamar mafalkin haka nakeyi kafi hakan ya fara hanani barci don wasan da yakeyi a kaina din.
A tsorace na bude idona tare da dan zabura a firgice a cikin razana ina kokarin yin ihu don tsoro .
Sai nake gani abin kamar a mafalki don bude idanun da sukai min nauyi don barci da nake ji a lokacin ga kuma mutum a tare dani da ban kawo cewa shine ba sam a raina.
Common relax zainab its me jafar kin faye tsoro da yawa now jin hakan bai hanani yunkurin kwance kaina daga gareshi ba a cikin tsoro.
Sai kara rikoni da yayi a jikin nasa babu yadda zanyi in kwace kaina a lokacin don irin rikon da yai min din.
Meye haka yaya zaka shigo min daki ina barci har ka hau min gado ka rike ni kuma ?
Baiyi magana ba sai dan murmushin da naji ya sake da baikai ciki ba dayayi a lokacin.
Kafin can inji yace zainab zuciyana kamar zai fashe nakejin sa na kasa rike kaina da kaina ina neman inda zan raba naji sanyi ne a rayuwana.
Ba tare da na juyo ba don babu daman hakan saboda irin rikon da yai min ba daman na kaucewa hakan.
Amma a cikin karfin hali irin namu na mata nace mai babu sanyi ko sauki a tare dani yaya don babu abinda zan ma a hakan ka sani.
Nima din da ka sani da baka nufoni ba don a hakan yadda kake ka sameni a yanzu don ba kai kadai ke cikin bacin rai ba yau.
Na sani zainab ya fada kamar wani karami yaro dashi yana kara cusa kanshi a kaina yadda muke kwancen.
A cikin wanan yanayin fadila ta fado dakin ta samemu ta koma baya da sauri tana dafe kirjin ta do abinda idon ta ya gane mata a lokacin.
Wanan wani irin mutum ne da ba,a gane gaban sa sai da ina gab da hada komai dana samu gareshi yanzu kuma zai canza min lissafi ?
Idab na bada shedan shi din guy ne bai aikata wani abu da matar shi fa yanzun ga idona kai haba ashe malam biri yai kama da mutum na kasa gane gaskiyar yarinyar nan tun farko.
Ashe akwai abinda ke wakana a tsakanin sune wani lokaci yasa take kin fada mi komai idan na tuntube ta da zancen nasa.
A dakin kuma shiru ne ya biyo baya kamar ba zai yi magana ba sai can yace a naki ganin ke nan zainab ?
Amma at list ko wanan rikon da nayi maki naji sanyi a raina ba kamar yadda na shigo dakin da kumci ba a zuciyana da farko ba.
Da karfin gaske na kwace kaina a jikin shi jin abunda ya fada din ina fadin duk wani jin dadi ko walwala ka haramtashi a zukatan mu yaya.
Yau sanadin ka har ake daukan laifin da banawa ba ana dora mi duk da bansan yadda ubangiji ya halicceni ba tun farko ko ni din mai haihuwace ko akasin hakan .
Amma a yanzu kam laifin hakan yana wurin ka yaya don dama na dade ina tsoron wanan ranan duba ga yadda mutanen mu suke nan akan aure.
Tareni yayi da fadin na fiki sanin duk wanan matsalan yana tafe muna komai dadin dadewa watarana za a samu wanda zai muna wanan korafin na haihuwa a tsakanin duba ga yadda muka dauki shekaru a tare dake.
Amma sam banyi tsamani hakan zai fito daga bangarena ba sai dai daga gun yan uwan ki nafi zaton hakan.
Zainab nasan kinyi hakkuri ga komai game da zama dani a hakan don banda abinda zan iya saka maki dashi a rayuwana da zan maki na ga na saka maki ga hakkurin ki.
Nima din a yanzu nakan yi nadaman hakan saidai ba kowa bane zai yadda da hakan sanin ni ko waye ke tare dake kuma kikai hakkuri kika zauna dani hakana.
Duk da nasan Nuriya ta yi wanan zancen tana daukan kece mai laifin rashin haihuwan a tsakanin mu duba ga irin rayuwan da kike ciki a gidana.
Wanda nasan zafi da kishi irin naku na mata yasa ta fada muna wanan maganan haka a gaban kowa don dai kawai taga ta bata maki rayuwan ki.
Saidai da tasan abinda kalamin nata zai jawo a gareta da bata furta hakan da nufin tozarci a gareki ba don ba iya ita wanan kalaman zai shafa har mijin ta da kowa a yanzu hakan zai shafa.
Kara matsawa nayi dan nisa dashi a cikin murmushi nace kaiyya idan kai hakan ga yaya mamud baka kyauta ba kuwa .
Don baka da dan uwa mafi soyuwa a gareka bayan shi da jamal duk da ban zauna dasu ba munyi wanan zancen amma naga damuwa karara a tare dasu kan sanin ko kai waye da sukayi.
Shiru yayi gashi yana son bani hakkuri saidai ya rasa kalman da zaiyi amfani dashi wurin bani hakkuri a bakin shi don shi a nasa ganin tsaya a bata lokaci wurin ba mace hakkuri wani abune can na daban .
Gyara kwanciya naga yayi ya mike saman gadon tare da lumshe idanuwan shi sai hakan da yayi min a daki ya zama min wani bakon al,amari kuma tunda ban saba ganin hakan ba ni.
Sai mukai shiru na dan lokaci kowa da abinda yake tunane a ransa sai da na jefo mai tambayan da baiso ne ya bude idanun sa lokaci guda da nace.
Yaushe ne zamu gida muga su inna na tambaya cikin kallon shi inji amsan da zai bani lokacin sai cewa yayi dani sai idan kun kara hutawa zan shiryawa zuwan ku din.
Ba wani hutu don ba aikin komai nakeyi ba ko wani abu a nan yanzu don haka gida muke son zuwa mu ganesu.
Zaku tafi amma ba yanzu ba ya fada yana kara gyara kwanciya vikin dan kara lafewa saman gadon kamar mai shirin yin barci a dakin.
Iya kuluwa na kulu da jin amsan daya bani a lokacin don haka ban ko iya bude baki na ce dashi wani abu ba sai faman tunane da nakeyi a can kasan zuciyana wanda na kasa tsayar da zance guda kan hakan.
A hankali nake ji saukan numfashin sa dake nuna min ya samu barci ne a hakan na sauka saman gado a hankali zuwa bandaki don i kewa ya daga nan na tsaya yin wanka.
Har na fito yana a inda na barshi a kwance yana barci bai tashi ba balle in sa ran fitan shi daga dakin nawa sai abin nasa yake ban mamaki.
Haka na daure na karasa bakin mirrow ina shafa mai a jikkina da sauran al,adun mu na mata idan munyi wanka.
Kamar ance in daga kai yana kwance ya lafe a inda yake din ya kura min ido yana kallona nayi sauri kawar da kai daga hada idon da mukayi dashi da sauri.
Mikewa nayi zuwa wardrobe dina na bude sai lokacin nace dashi an lodawa mutum kaya haka kamar wanda zaiyi wani abu dasu ba sakawa ba.
Idan basuyi maki ba sai ki kyautar ya fada yana juyawa daga barin da yake kwance din nace har yaushe zamuyi amfani da wanan kaya haka wai ?
Har na gama na shirya a boboye duk yana dakin banu abinda nake ji sai haushi da takaici nasa na yadda ya zauna min a dakin da bansan dalilin hakan ba.
Bai fita dakin ba nima kamar an dasani a dakin haka muka zauna sai wuraren sha biyun rana ya bar dakin ya nufi part din shi.
Nima daki na gyara duk da wata tazo wai itace mai gyara amma ban yarda da hakan ba dana tashi kafin tazo na gyara dakina tsab balle yanzu da nake jin tsoron duk wanda ke gidan tare damu zaune sai nake masu bugu daya gaba dayan su ma aikatan gidan.
Ban fito ba saida sadiya ta shigo dakin tana fadin yayan mu kun tashi ke nan dazun nazo zan shiga anty ke fada min yaya yana ciki kwance.
Fadila fa na fada da mamaki tace eh ita ke fada mi hakan sai na koma barci yanzu na tashi yunwa nake ji sosai tana shafan ciki ta.
Ina mamakin fadila a raina nace ke nan bakici abinci ba kema tun dazun jin hakan yasa na mike muka fito falon tare ganin fadila dake mazurai yasa nace barin duba yaya ya fito mu karya na nufi part din nasa.
Na samu yayi wanka har ya saka tufafi a jikin shi a cikin daure nake fadin wai sadiya bataci abinci ba tun dazun tana jiran mu fadila ke fada mata kana dakina.
Bakiji lokacin da ta shigo dakin bane muna kwance ya fada na zaro ido waje a cikin mamaki yace eh ai hakan yayi kyau don zata shiga duhu kan abinda take hadawa yanxu.
Haka dai muka fito suka shiga gaidashi yana amsawa cikin basarwa har ya zauna yana fadin kanwata ya akayi baki ci abinci ba kika tsaya jiran mu ?
Haka dai muka zauna duk abin yana daurewa fadila kai don ta kasa fasara matsayin da yaya j yake ciki a yanzu don bayanin data tara nata yanzu ya bayar da ita kuma.
Wayan shi ne ya shiga kuka alaman kira na shigo mashi a lokacin ya basar kamar bai ga kiran ba haka yasa na duba ya mamud ne na dan dube shi sai ya dauki wayan ba don yaso ba sun gaisa yake tambayan shi naji yace bana gida na fita tunda safe.
Haka yasa na dago ido ina kallon shi vikin mamaki don da alama abinda ya fadi yake shiri sikatawa don laifin daba nasu ba ya shafi kowa a yanzu ke nan.
To meye laifin su ma akan wanan maganan dashi ya jawa kanshi hakan kome aka fada ai naga shiya jawa kansa dai hakam.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


HASBUNALLAHU WANI IMAL, WAKIL YA HAIYU YA KAIYUMU BIN RAHAMATIKA YA ASTAGIS , , , ,


LITTAFIN NAN NA KUDINE YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DA SAUKIN FAHINTA BA TARE DA DAUKAN HAKKIN KOWA BA A KAN KI YAR UWA, , , , ,
DON KIRA 08036959257 KO 09026931792 ACCOUNT ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK, , , , , , ,


Kwana biyar rabon mu da gidan mami har ranan ya J bai leka gidan ba tun mami na boye zafin hakan da take ji har ya kai ranan ta zauna a falo suna magana da yaranta ta sako zancen rashin zuwan shi gidan da baiyi ba.
Kowa yai shiru a falon sai jamal ne ya bata amsa ba tare da ya dago kaiba yake fadin mami ya zaizo kuna masu cin fuska irin haka ko waye ma ai dole yaji zafin hakan.
Shike nan kada a fadi gaskiya don kawai ya dauki yarinyar tafi kowa ko me zaice tayi laifi kada a fada.
Harni zainab zata ce saita huta zata zo gaidani da ace matsiyatan mahaifan ta ne garin nan har zata kwana uku bata gansu ba ?
Haba haba mami wanan abin fa ke batawa ya j rai daku ko ya iyayyen zee suke ai yanzu an zama daya dasu mami jalal ya fada.
Ji wani maganan banza da wa suka zama daya wa yan nan kaskantattun mutanen Aisha ta fada tana wani kauda kai.
Ke ni kike fadawa maganan banza haka ku mi shiru mami ta fasa a hasale tana zarewa kowan su idanu lokaci guda.
A daidai lokacin ya mamud ya shigo falon ganin yadda ya samesu kowa ranshi a bace yake fadi tun kan ya zauna.
Ba wanda ya bashi amsa sai ya juya wurin mami yana fadin mami mai ya faru kuma na ganku rai a bace ?
Barsu da batun banza kasan su jamal da jalal kamar wa yanda yarinyar nan zainab ta asirice su basu son ayi zancen ta ko kadan.
Zancen me kuma mami ina dai anyi wanan zancen ya tafi waya tayar da maganan kuma yanzu ?
Nice na tayar kan zancen rashin zuwan shi gidan nan yau kwana biyar ke nan da yin wanan zancen bai leko ba.
Zaizo mana mami abinda akai masu ne ba a kyauta ba idan ke kin fada masu ita wanan mara hankalin ina ruwanta da rashin haihuwan su har yanzu ?
Ko ita din da take haihuwan yaushe ta iya kula da yaran da har take fadawa wani bai haihu ba ?
Ta samu wurine a wurin mami don taga mami ta saka yar mutane a gaba akan danta yasa itama ta fadi hakana jalal ya fada .
Ya salam yaran nan me kuke son mayar dani ne yanzu bari kuje dukkan ku rayukan ku zai baci dani wallahi kan wanan zancen.
Kiyi hakkuri mami ya mamud ya fada yana kaiwa zaune kafin yace barin gwada kiran jafar din yanzu muji in lafiya yake don na kirashi yake ce min yana wani aikine.
Ya kira shi saidai bai dauki wayan ba har ya katse ya kara kiranshi wayan ya nuna yana busy.
Yace kin gani duk na kira busy yake saka min harni fushin ya shafeni ke nan ya fada yana kallon uwar tasu.
Yayi fushi mana indai don kan yarinyar nan ne zainab mai shegen bakin wayau su na yan kauye yarinya kwarkwar da shegen bakin wayau zanyi maganin ta ai don ba zan yarda ya kara barin kasan nan ba tare da kara aure ba.
Da sauri duk wanda ke falon ya dago kai yana kallon ta don jin abinda ta fada din .
Kai haba mami kada ki soma wanan abin don zai zama tonun asiri a garemu baki daya tunda kinga ko zainab din dai hakkuri takeyi dashi ai.
Hakkurin me mamud kune baku gane wanan yarinyar ba tun farko ni yanzu na dawo daga rakiyan ta ai.
Tunda na gane me take hadawa kan dan uwan ku idan da baida amfani a gareta zata zauna dashi tsawon wanan shekarun hakane ?
Tunda ta kasa shawo kanshi ai gara a auro wace zata zama silar barin komai nasa zaifi ta fada tana kawar da kai gefe daya a hasale.
Wanan shawaran naki baiyi ba mami sam wallahi don ya j din ba zai taba yarda da hakan bama wallahi .
Ke dai ki barshi a yadda ya zabawa kanshi illa dai a tayashi da addua shine abin yi a yanzu don wallahi tonawa kai asiri kawai za ayi ga hakan.
Ya mamud na shiru jamal ya dauka yace kai mami ina kika samu wanan shawaran kuma yanzu ?
Ya fada yana kallon ta yace kindai san waye ya jafar ai kin kuma san haiinsa idan zainab ta zauna ta rufa maku asiri duniya bata jiku ba wanan da zaki aura masa itace zata zama silar tona maku asiri a duniya .
Wai kanshine farau wanan halin idan na kara masa aure ai ita yarinyar da zan aura masa ba wata bace ta daban a cikin yan uwa zan aura masa wace ta waye ta san kanta har ta taimaka masa ya daina wanan halin da ake masa zaton yana yi.
Au mami yanzu baki yarda yana komai ba ke nan ya jamal ya tambaya cikin mamakin jin abinda mahaifiyar tasu ta fada.
Idan ma yanayi sai ka dauki laspeaker kayi shela zai fi ma sauki idan da har na yarda da zancen ku yanxu ban yarda da hakan ba.
Lalai mami akwai abinda ke damun ki ya mamud ya fada tare da fadin ke da kanki ba wani ya fada maki wanan abinba duk da mun san da haka amma ke kika gani fa da idanuwan ki.
Nayi da kai na gansa a wani halin a lokacin ko wani ya fada ma hakan cewa yaga yana aikata wanan abin .
In ma har zargi ake masa a bari ya kara auren sai mu tabbatar da hakan daga bakin wata ba a bakin wanan yar sherin yarinyar ba zainab.
Duk shiru sukayi sai can Aisha da har lokacin bata sanda zancen ba tace wai ma har me yake aikatawa haka mai muni da ake ta wanan zancen wai ?
Iyaka dai zainab tace yana neman mata ko ba a nema ita aka nemeta ne wai da ake wani tarewa kada a kara masa aure .
Waya gane me take samu ina gidan su da yan uwanta kawai take aikawa inba wanan karon data kawo muna wanan tsaraban ba haka ?
Ya jamal daya mike ya watsa mata wani irin harara daga inda yake kafin ya juya ya fice falon suka bishi da kallo cikin mamaki.

Yana zaune dan falon dake part din shi saidai wanan karon ba komai yake yi ba zama yayi kamar mai tunanen wani abu a zuciyan shi.
Kafin wayan shi dake gefe ya dauki kara ya kalli wayan saida ba sunan mai kiran nasa wanda hakan ya bashi mamaki waye zai kirashi da bakon lanba ne ?
Ya raya a ranshi yayan shi mamud ne ya canza layi don kin daga mai kira da yakeyi a kwanan kin nan.
Ya dai daure ya daga kiran ba tare da yin magana ba muryan jalal yaji a wayan yana gaidashi ya amsa yake fadin bros kwana biyu gashi har yau mami tana zancen ka.
Ya J rashin zuwan ka yasa mami tana shirin karayi ma aure don ta dauka laifin zainab ne hakan .
Wani murmushi ya sake a fuskan shi yana fadin aure fa jalal ita mami din ta fadi hakan yace wallahi yau take fadin hakan a gaban kowa dake falon .
Nan dai ya kwashe komai ya fada mai a cikin bacin rai har yana fadin ni bansan meyasa mami take kin zainab dinka ba yaya ga Nuriya da take mata iskanci amma bata ganin hakan.
Kada ka damu jalal ta dai fadi hakan ne kawai amma tasan ai banda ra,ayin mata biyu a rayuwana.
Bai tsaya jin ta kanin nasa dake fadin kada ka bari ta san ni na fadama don tayi warning din mu kada wanda ya sanar ma da hakan.
Ya kashe wayan ya mike tsaye cikin hasala zuwa dakin shi don ya watsawa jikin shi ruwa kafin nan ya fito.
Ya fito ya samu miscal har uku a ciki hardana jalal din daya kara kiranshi sai na ya mamud bai kira kowa a cikin su ba don yasan zance dayane dai suke kiranshi a kai.
Fitowan shi yayi daidai da shigowan ya mamud gidan muna gaisawa sai gashi taro na musanman aka hadawa yaya din a babban falon gidan da akayi don karban baki maza.
Sun gaisa yake tambayan shi ko lafiya kwana biyu bai shigo ba yake fadin lafiya kalau yake yana hutu ne a gida kawai.
Kana ganin rashin shigan ka gida wurin mami hakan da kayi shine mafita a gareka yanzu.
Dan murmushi ya sake tare da fadin mamud ya kake son nayi da mami meye laifin yarinyar nan zainab mamud ?
Idan mami bata godewa zainab ba ba kuwa zata hattare ta ba haka tana kokarin maida mun mata abin tsana a gareta.
Shima mamud din dan murmushi ya sake ma dan uwan nasa yana fadin duk mun san da hakan mun fadawa mami din komai.
Amma ta nuna ba hakan ba ni yanzu hukuncin da take son dauka a kanku don kawai maganan wanan mara hankalin Nuriya da mami ta hau shine matsalan dake shirin kunno muna kai a yanzu.
Wani matsala ke nan ya tambaya kamar bai san komai ba a kai sai mamud din ya dan dukar da kai kasa yana fadi a sanyaye mun dai fada mata zatayi kuskure idan tayi hakan don zai shafi gaba dayan mu gaskiya.
Duk zancen da sukeyi a kunnen fadila sukeyin shi kafin J din yace dashi ku barta duk wance zata aura min taje ta aura zata gane true colour dina lokacin.
Dan kallon fargaban jin abinda ya fada da fadila tayi mai yasa shi fadin fadila live dis place please.
Da sauri ta mike daga zuba ruwan juice din da takewa ya mamud ta koma ciki da sauri cike da biyayya a gareshi don bin umurnin shi.
Hakan baisa ya je gun mami din ba saida aka dauki kwanaki ya tafi bai wani tsaya ba suna gaisawa ya juya ya fito fuska a daure.
Nikan a lokacin ba abinda nakeyi sai sha hakkuri don mu samu ya sallameni zuwa gida gashi a bangaren fadila gulman abinda taji yana cin ta don a gaskiya duk da tana aiki akan shi ne hakan bai hanata sona a cikin ranta ba duk da ta kulla da ina ja baya da zancen ta a yanzu don ba kamar da muke ba sai mu zauna ba wani zance mai tsawo kamar yadda muka saba a baya da ita.
Satin mu biyu da zuwa Nigeria sai ga wayan sa,adatu take fadin ai gata ta hanya zuwa wurun mu inna ta aiko ta ta duba lafiyan mu.
Sam banji dadin hakan ba duk da hakan yana cikin karamawan iyayye a gare mu don asan mu din muna da gata yin hakan kamar al,adane na malam ba haushe.
Don inna tayi tayi da Abba a samu wanda zaizo ya dubamu da saukan mu amma sai Abba din ya hau fada kan hakan dole inna taja bakin ta tayi shiru.
Shine karshe suka yanke shawara a daki da yaranta kan sa,adatu ce zata zo Abuja ta dubamu da dan tsaraban da inna din ta hada muna kamar su dambun nama datayi mai yawa sai man shanu da kwai da dubula.
Duk a gidan malam mijin mai zube inna ta bada kudi aka hada komai a can da tare zasu zo da maizube din sai aka tashi ranan da zasu zo din wani a cikin yan uwan maizube din ya fadi ya rasu da asuba.
Shine dalilin da sa,adatu ta biyo hanya ita kadai duk da bata taba zuwa Abuja ko wani wuri mai nisa irin hakan ba sai wanan ranan.
Jin haka yasa na bugawa yaya waya ina sheda mai zancen zuwan sa,adatu din dake hanya tafe shima yayi mamakin hakan yake tambaya tana ina yanzu nace tace sun kusa shigowa gari don motan safe ta biyo zuwa Abuja din.
Bai dawo gidan ba sai tare da ita sukaje tssha aka dauko ta niki niki da robobi tsaraban da tazo muna dashi din.
Munyi murnan ganin juna da yar uwan mu har mun manta da duk wanda ke wajen a lokacin yadda muka makalewa juna don daukin ganin .
Sai cewa ya j yayi kuyi a hankali kada ku kayar min da matana don Allah duk aka kwashe da dariya a wurin yadda mukeyi saida ya ba kowa sha,awa don hakan na nuna akwai shakuwa da kaunan juna a gare mu.
Daki muka shiga bayan gama murna sai mamakin yadda muka canza take yi har ta kasa boye hakan.
Fadilace ta kawo mata abinci har dakin don gaskiya ina gani kokarinta wuri kaskantar da kai da takeyi don aikin ta wurin boye ko ita waye gare mu ta nuna aikin da ya kawota garemu shine takeyi a gidan.
Yau dai naga sa,adatun nan da nake yawan jin labarin ta gun ku ta fada tana aje turen abincin a gaban mu nace ga anty fadila sa,adatu.
Ta juyo tana fadin ayo itace ashe gaskiya yayan mu tana yawan ban labarin ki anty sannu da dawainiya an gode fa.
Ni kaina naji dadin hakan da sa,adatun ta fadawa anty din sai na karbe da fadin wallahi sa,adatu ko ya j yana fadin banda kamar anty a rayuwana shi kanshi yafi yarda da ita sama da kowa a rayuwan shi.
Yana daukan ta tankar yar uwa a garemu yanzu don ya wuce zaman aiki a tsakanin mu sai zumunci da rufawa juna asiri a yanzu don shi yanzu bai san abinda zai saka mata dashi ba.
Wani irin yanayi ta nuna a fuskanta lokacin da nake fadin hakan ta dan sake dariyan yake kawai tana dagawa a sanyayye ta bar gurin.
Tana fita na bita da kallo a fakaice kafin muryan sa,adatu ya dawo dani daga kallon fadila din tana fadin .
Anty wanan gidan naku kamar a turai mutum yake ni ai ban gama kallo ba don kawai kada na bar abin kunya na shigo.
Ki gama mu fita sadiya ta fada da take kwance rub da ciki tana jagulan wayan sa,adatu din dake hannun ta tana dubawa.
Munyi hira sosai ranan a daki muka wuni sai bayan la,asar yaya Jafar ya shigo dakin ya same mu zaune mun baje tana muna hiran Asabe da Lantana na fafatawan da ake tsakanin su yanzu.
Sai dariya muke kwasa ina kwance a gurin dana sallame sallah ita kuma sa,adatu tana saman rogh din dake tsakiyan dakin sadiya na saman gado kwance.
Gaida shi sa,adatun keyi ya amsa tare da karasa shigowa dakin ya nufi bakin gado ya zauna yana tambayan ta mutanen gida ?
Tace duk suna gaida shi su inna sunce ai masu godiya kafin su hadu na alherin daya aika masu shekaran jiya dashi .
Dago kai nayi da sauri na dan kalleshi bai nuna komai ba yi yayi kamar bai ganni ba ma na kallon da nake masa.
Yanzu karatun ki yayi nisa ko ya tambaye ta tace insha Allah muna two hundred level ke nan yace ashe kun fara nisa sosai .
To ya zancen ku da baba yanzu dai ya amince ki karasa karatun naki kafin zancen auren naki ko mu tsaya mu sha buki kafim mu koma ne ?
Ya tambayeta a cikin zolaya tace Abba ai case ne wallahi ni ba do kai ba yaya ai ba zai yarda naci gaba da karatuna ba a yadda ya dage din nan .
Yanzu ko shiru baya zancen ma sam idan ba nayi masa wani laifi ba kuma a kan lantana ce dake zugashi zakaji yace yar abu kaza aure zan maki in huta ai.
Ya kwashe da dariya zakace ba ya j bane ya sake haka a gabanta yana kwasan dariya nice na katse su da fadin ga sako nan inna ta aiko ma dashi ina nuna masa kayan da tazo dasu din.
Abinka da wanda bai saba da hakan ba ya dago kai yana fadin wanan meye haka da yawa aka aiko muna kuma ?
Sadiya ce ta sauko saman gadon da take ta fara bude mai roban dake cike da dambun nama kafin ta koma gana kwai dana man shanu .
Yake fadin kai wanan duk namune haka amma inna tayi dawainiya da yawa gaskiya.
Ai kaima kana dawai niya dasu sosai har su rasa bakin godiya sa,adatu ta fada yake tambayan sadiya cikin basarwa wanan din da kika bude da farko meye shi sady ?
Tace barin debo ma kaci kaji dambu ne na nama aka soya yace a hakan na tuna mami idan tazo ana kawo muna shi muci muna US.
Ta debo mai a lokaci nace sai a dibarwa su mami a kai masu don wanan dai yayi muna yawa kan a nan.
Bai ban amsa ba sai diba da yayi ya fara ci wanda hakannda yayi yai muna dadi sai godiya yake daids ya danci sosai muna hiran mu da sa,adatu bai ce komai ya mike yana fadin zaki kwana biyu a nan ke nan ko ?
Eh to kwana biyu din innan mu tace nayi na koma kada Abban mu yayi fada idan na dade yace ba zai yi fada ba ai a wuri mu kike ba wani wuri ba.
Mu yaushe zamu tafi ina tare zamu koma da ita idan zamu tafi na tambaya yayi kamar bai ji me nake fadi ba yasa kai ya fita.
Wai mu ba zamu gida bane yayan mu sadiya ta tambaye ni nace sadiya ban san me yake nufi da tafiyan mu ba har yanzu sai ja muna rai yake yi.
Kai wai meye a zuwa gidan da kuka matsa dayine ina dai dole ku tafi kafin ku koma ai .
Ki bari kawai sa,adatu bafa komai muke mashi a nan din ba kawai kuntatawa iri na mazane kawai.
Anty a gaskiya kinyi dacen mijin aure ga hankali ga natsuwa gashi da son yan uwanki kamar nasa kowa yana fadin hakan gaskiya ki godewa Allah da wanan rufin asirin da yai maki ke kan.
Wani iri naji a raina sa,adatu ke nan ke fadin haka ina ga iyayyen mu da ya riga ya saye nasan akwai aiki a gabana kan abinda nake kokarin shiryawa nan gaba ke nan.
Don su ba zasu gane ABU A CIKIN DUHU SIRI NE BA ni kadai nasan irin rayuwan da nake yi da ya jafar din don ko sadiya dake zaune damu nasan kirkin shi zata fada a gida idan hakan ya taso .


ZAINAB IDRIS MAKAWAZAINAB IDRIS MAKAWAALLAH YA SADA MU DA RAHAMOMIN SA YASA MUNA CIKIN YAN TANTUN BAYIN SA YA NUFEMU DA AIKATA ALHERI A RAYUWAN MU AMIN, , , , , ,

LITTAFIN KUDINE YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKI SALAMA DA AMINCEWA DON ALLAH DON KIRA 08036959257 KO 09026931792 ACOUNT 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK, , , , ,


Washegari mun tashi lafiya tare da kannena dashi mukai breakfast a cikin raha yana zolayan su har muka gama.
Ya mike zai tashi nake cewa dashi zancen tsaraban da za a kaiwa su mami din sa,adatu tace dayani sai naje na gaida mami tunda ba dadewa zanyi a nan ba idan za,a kai masu.
Allah ya gani banda niyar zuwa gidan mami kuma kan abinda sukai mun a ranan yasa na tsani sake zuwa da niyar gaida mami din gidan ta kuma.
Duk da nasan hakan abune mai wuya a wuri amma ba yadda na iya dole na amsa da hakan na dakyau sai naga ya dan kalleni a falaice baidai yi magana ba ya barmu a wurin.
Kamar yadda muka tsara hakan muka shirya da yamma bayan sallah la,asar don fita zuwa gidan mami din a karo na biyu da zuwan mu garin duk da nasan akwai kalubalin da ba za,a rasa ba ga zuwan namu gidan dake jiran mu.
Tunda a yanzu na gane dai ba zan taba haske a wurin mami ba don ta nuna min hakan a zahiri bata dai kaunana a yanzu sam.
Amma don kada kanwar tawa ta gane akwai wani abu a tsakanin mu da mami din yasa na daure don na kaita ta gaida mami din wanda ita take ganin hakan girmamawa ne a wurin ta.
Driver ne ya kaimu a cikin wani haddaden jeep dake fake a gidan tun zuwan mu nake ganin motan a jiye sai gashi yau da moka fito naga itace zamu fita da ita wanda hakan umurnine daga maigidan nasan.
Dukkan mu ukun mun gama haduwa wurin tara kwalliya da kure adaka inji bahaushiya wuri kwalliya muka dauki hanya har da fadila a wanan tafiyan sai da tayi mamakin jin cewa ta shirya zamu fita tare da ita.

Zaune take dakinta tana waya da yar uwanta dake fada mata hjyn su jikin ta ya dan motsa a ranan amma sun kaita asibiti taji sauki a lokacin tana dai kwance.
Bayan sun gama magana ne da yar uwan take tambayan mami din da cewa ashe jafar tare yazo da matar shi kasan wanan karon dazun nake jin haka da suke waya da yaya a falon hjy.
Dan wani basarwa mami tayi kafin tace tare sukazo ai yar rainin wayau yarinya da take ganin yanzu daidai take da kowa tunda ya maida ita wani abu a idon duniya.
A dama haka zata gani yanzu ai yaya tunda ta samu tsuntsu daga sama gasshe a hannun ta ba dole ta dauka tafi kowa ba.
Wai ki duba yarinyar nan saida ta kwana kusan biyar a kasan nan kuma a garin nan fa wai kafin zainab tazo gaidani .
Da sauri mama Ramatu din tace ita zainab din lalai yanzu wuyan ta ya isa yanka ke nan inda uwarta ce a garin zata iya hakkuri har kwanakin bata zo ta ganta ba.
Shina fadi nima Ramatu har yaran nan da basu san ciwon kansu ba suke ganin laifina kan hakan don nayi magana Nuriya kuma take fadin .
Ai bata burge ba tunda basu zo ganin mu da kama hannu ba da zasu zo shine fa wai jafar din har da daukan fushi dani don hakan.
Shi jafar din ta tambaya da mamaki tare da fadin kai yaro kamar wanda aka shanye da asiri kan yarnan wanan abubuwan da yakeyi akanta ?
Barni da mara mutunci zanyi magani su daga shi har ita don ba zai bar kasan nan ba sai da auren wata matar wanan karon .
Ta san cewa ban haifa mata dan ita kadai ba don su juya shi yadda suke so ita da iyayyen nata da yakewa bauta.
Wai yaya kina ganin zai yarda da hakan yanzu dama can bai yarda ba balle yanzu din kuma ya yarda ?
Zan tsaya sauraren shine Ramatu ai wanan karon umurni kawai zan bashi bawai rarashi ba daga shi har ita ai basu fi karfina ba Ramatu.
Zan zauna ne in saka masu ido tsawon wanan shekarun ba haihuwa ko batan wata tare dasu sai bakin kazafi da sheri da suke kokarin kulawa yaro ko yaushe shiko idon shi ya rufe baya ganin hakan ko kadan ?
Ai gara kan a gwada don shi bai sanin dadin hakan sai idan anyi zai gane gata akai masa da yin auren.
Shidai nagani Ramatu amma yaran nan da yake kansu daya duk basu ban goyon bayan hakan ba ai ni zan tsaya bin ta kansune halan.
Aisha ce ta shigo dakin a fusace tana fadin nifa mami ban ganewa wanan mai aikin naki ba fa duk akace tayi min gyaran daki sai wani abina ya bace a dakina.
Wayan ta katse tana kallon yar nata kafin tace wai bata daina wanan halin ba har yanzu kawai wanan karon idan zargina ya zamo gaskiya zan koreta ne don na gaji da zanbar yan aiki a gidan nan.
Kwanaki ina fada maku daga cire agogo in shaga ban daki sama ko kasa na nemeshi ban gashi ba a gidan nan.
Wazai dauka mami banda ita mudai tun barin mu da zee wallahi bamu kara samun yar aikin kwarai ba a gidan nan abu kamar da sa hannu a hakan.
Ita ma din aka sani ko hakan take wanan mai iya kilibibin tsiya da takom saka wa zai sani idan ma tanayin hakan ?
Kai haba mami gaskiya bata taba hakan ba ida ba dai wanan case na yaya j da ita ai zainab mutunce a wanan lokacin.
Tsuki mami din taja tana mikewa ta fito daga dakin tana kwalawa mai aikin kira da tantano tantano hat tana sarkewa wurin daga murya.
Matar ta fito da sauri tana amsawa da akala zatayi haihuwa bakwai ko shidda da haihuwa don dai ta dan manyanta kadan.
Tana fadin gani hjy mami ba tsaya jiran komai ba take fadin wai saunawa zanyi warning dinki kan taba muna kayane idan bamu baki ba.
Ni hjy mai kuma akace na dauka yanzu karya za ai maki muna tare da wasu a gidan nan bayan ke da za ace sune suke daukan muna kaya.
Wallahi sunma tallahi ban daukar maku komai ba hjy ta fada a cikin wani yanayi na bacin rai da rudewa lokaci guda.
A wanan lokacin mukayi sallama muka shigo gidan duk abinda suke fadi a kunnen mu wanda shigowan mu bai hana matar cigaba da magana ba tana fadin.
Hjy mezai sa na dauki abinda ba nawa ba idan ba a banba sai dai idan ba a duba bane da kyau.
Ban duba ba na nema banga dankune dana cire ba na aje saman side drower dina yanzu kuma na nema kaf dakin ban gani ba.
Da mamaki muka karaso tsakiyan falon inda suke matar tace nikan ban dauki dan kunne ba wallahi kuma ban maga yan kunne a wurin ba gaskiya.
Don Allah rufawa mutane baki mutanen banza duk haka kuke sai an yarda daku kwana biyu ku yaudari mutum mami ta fada a cikin takaici.
Wanda nasan gugan zana ce akai muna gaba daya lokaci guda harni dana shigo da yan uwana a gidan lokacin yasa mami fadin hakan don ta sokeni kawai.
Sallama na kara yi don kawai su bar zancen tunda mun shigo muzanci bada kyau a yadda sukewa matan .
Aisha ce ta amsa tana fadin kune a gidan sannun ku da zuwa tana yar sake yake a fuskanta muka karaso mami na fadin.
Ni dai ban taba dace da yan aikin kwarai ba a gidan nan kowa ka yarda dashi sai ya ha,ince ka a karshe ya nuna ma halin yan duniya.
Ta sake fadi a fusace jeki wallahi kifoto mata da dankunen ta kafin na hadaki da security ranki ya baci.
Ta juya zuwa wurin kujera ta zauna muma zama mukayi saman kujerum muna gaida ita .
A cikin mamaki ta dago kai tana amsawa tare da mamakin hakan don bata iya boye mamakin taba na zaman da mukayi akan kujera tana zaune sama itama a lokacin muke gaida ita.
Wanda ta dauki hakan a raini ne sosai a wurin ta, don kamar zaman tsara da tsara ne mukayi da ita a falon a ganin mami din.
Saidai ta daure ta amsa muna da kyat tana wani jan kamshi a tare da ita a daidai lokacin da wani yaron gidan yake shigo da roban da fadila tayi siling din kayan tsaraban Sa,adatu da tazo dashi.
Can ta juyo tana kallon shi tare da fadin wanan fa daga ina haka kuma tana kallon shi tana son karin bayani kan kayan da taga ana shigowa dashi falon.
fadila ke fadin hjy tsarabane da akazo dashi daga anchau shine aka kawo maki.
Inane haka kuma ta fada a wullakance tana dan bata fuska , a cikin dan murmushi fadilan tace mahaifan uwar dakin mu zainab ga kanwata nan da tazo jiya tazo dashi.
Ta dago ido ta dan kalli sa,adatu da mamaki ya fara kasheta a zaune tana fadin owo tazone ashe ?
Babu ko ya mutanen gida sai cewa tayi lafiya dai tazo ko wani abu tazo yi nan din da tazo tare da tsure mu da idanuwan ta tana karewa sa,adatun da mukai matukar kama da ita sai dai hanci da dan dogon fuska da haske kadan dana darata dashi wanda hakan yasa na fita kyau a gani da kuma wayewa shine kawai bambamcin mu.
Kai tsaye wanan karon na bata amsa da fadin duba mu tazo tayi taga saukan mu ta duba lafiyan mu.
Sai ta kawar da kai gefe can Aisha tace meye a cikin roban tana kallona ki duba ki gani mana da idanun ki na fada cikin dakewa.
Mami tayi saurin dago kai tana kallona don jin abinda na fadawa yar nata kai tsaye ta kasa danne zuciyar ta tace koma meye ai ba abinda baki taba gani bane da zai dameki har kina tambaya.
Wayana yai kara daga cikin jakka na sa hannu na dauko sunan ya j na gani a screem din wayan na dauka yake fadin kuna ina nace gidan mami.
Badai matsalan komai ya fada da sauri na ce a wayence babu don kada a gane tambayan da yai min din a lokacin sauran yan matan suka fito dakunan su.
Da yanzu dai ina ganin zaman su ya dawo Abuja ne suma bayan gama karatun su saidai ba wace tayi aure har yanzu a cikin su.
Rufaida ke fadin ba tare data kulamu ba ko tayi muna sannu da shigowa take cewa mami naji kina fada da wanan matar mai shegen baki.
Bari Rufaida macutan mutane ne yan aikin nan dukkan su ka basu amana sai sun yaudare ka maha,inta sai mutum.ya kwaso talaucin shi daga kawai yazo ya sameka da abinka yace zai cuceka har gida.
Af mami ai kin saba da halin su dama wahala ke koro su ai suzo birni aiki kome suka gani sai su dauka a banza ka sameshi kai wasu har su so hada kansu da yan gida su nuna sun fi mutane a karshe.
Dan murmushi na sake kadan ina fadin wanan kuma in kinga haka dama can mutum ba wullakntace bane da baiwan sa yazo .
Wasu ba sunan aikin suke zuwa ba cin arzikine sai kiga sun fi masu gidan iya shege don kawai haye daga sama ba a san kan arzikin ba.
Ai abin ke dai daga Allah ne da yake tsarawa kowa rayuwan shi yadda yaso mu zamu koma mami dama na kawo sa,adatune ta gaida ke.
Ban jira me mami zata fada ba na mike tare da kallon inda su Aisha suke ina fadin mun barku lafiya mun tafi.
Idan mijim ki na gida zan shigo don ina son ganin sa ki fada mai ban ko tsaya ta kanta ba na karasa gaban mami tare dan dukawa ina sallaman ta muka fita.
Shiru motan ba wanda yai magana a cikin mu kowa da irin tunanen da yakeyi a lokaci a zuciyar shi.
Mami kamar bata son ganin mu gidan ta kullun mukazo sai ta dinga daure fuska tana nuna bata son ganin mu.
Babu yadda zatayi ai dole ta ganku tunda danta ya dauko ku gidan shi bai kuma gaza da ku ba a rayuwan shi .
Don haka tayi a banza tunda bata sadai ya sake ki sai dai tace zata kara mashi aure don ki don kawai ta bata maki rai don kiyayya.
Aure kuma aishi yaya din ba zai yarda ba sai dai idan yana ra,ayin hakan dama zai yarda da shawaran nata sa,adatu ta fada .
Nidai ina jinsu ban tanka masu ba ina tunanen wanan maganan da fadila ta fada yanzu don tabbas hakan zai iya faruwa ba wai bs.
Gashi a bakin fadila nake jin zancen don nasanta nasan halin ta idan ta fadi magana kamar ta auna ne kafin ta fada.
Mun tsaya wani shago don sayen yan abubuwan motsa baki da zamu gida dashi har lokacin banda walwala a tare dani har muka koma gida.
Zaune muke a falona muna hira ya shigo da waya a hannun shi yana yi shiru mukayi don shigowan nasa ga waya da yakeyi.
Yana fadin yanzu dai me ya kawo wanan zancen nasan zainab nasan abinda zata iya mami don haka ban yarda da wanan zancen ba.
Na fada maku ban son irin wanan zancen akan yarinyar nan matatace fa zainab don haka yan uwanta nada daman zuwa dubata duk lokacin da sukaga dama.
A hasale yake magana don ranshi daya baci kan abinda mami din ta fada mashi ya karasa zancen da fadin bana son irin hakan .
Wanan dalilin yasa bana son zuwan su nan din tun farko don bana son irin abinda naga anayi din nan gaskiya.
Shiru yayi yana sauraren su kafin muga ya kashe wayan ya tura a aljihun rigan shi ta gaba ya juyo yana fadin meya faru ne da kuka je gaida mami dazun.
Nima da mamaki nace wani abin kuma akace munyi da mukaje ya ja tsuki tare da fadin yanzu mami ta kirani tana fadin wai naja maki kunne kan abinda taga kina son yi mata yanzu.
Ni din bana fatan ranan da zanwa wani babba rashin kunya ko wani abinda bai dace ba don nasan darajan iyayyena da manya na tun kan nakai haka.
Nasan neman bakine kawai sukeyi kan hakan yasa na dauki matakin da ya dace a yanzu kan hakan.
Indai nice su bar bata lokacin su ai na fada ina kawar da kaina gefe don raina da yake a bace.
Ya juya ya fita sai lokacin Sa,adatu ke fadin amma matar nan bata da hali ashe har me akayi bayan sune suke gasa muna magana ba a kula su ba.
Ni yau da nice da sun san suna sake min magana don wallahi ba zan kyale suba su dinga daukana kaskantata koda yaushe bayan Allah ya daukakani a cikin su su nuna min bakin ciki.
Haka kawai zasu azawa mutum tsana da kiyayya don kawai hassada da bakin ciki irin na dan adam me suka rasa a rayuwan su da zasu kyashe da baiwan da Allah yai maki yanzu.
Da nace daku kada mu tafi ai zaku ga kamar banson zuwan kune gidan amma yanzu da kuka gane wa idon ku komai ko na fada nan gaba zaku yarda dani.
Ai itama tana da yara mata a gaban ta bata san inda Allah zai jefa rayuwan su ba nan gaba shi tallaka ba abin rainawa bane sam a duniya.
Ranan sa,adatu tayi fada har ta gaji ta kyale don kanta nidai ba wanan ne a gabana ba don inda sabo na saba da halin mami da yaranta tun kan na auri danta a baya.
Fadila ko cewa tayi idan bata so ai sai ta dawo da tsaraban karshen kiyayya ke nan ai da zata nuna min sa,adatu tace shine ai.
Sai na dauka zasu dawo da tsaraban da muka kai na sa,adatu din sai gashi naji shiru banga an dawo dashi ba har tsawon kwanaki shima bai kara zancen ba.
Sai dai bai kara zancen mami din ko wani na gidan su ba a gaban mu sai mazan ne kan shigo su dubamu jefi jefi zamu gaisa a cikin mutunci dasu.
Nakan yi mamaki sosai yadda mami wai ta manta da komai na halin yaya take kokarin daukan laifi ta dora min koda yaushe sam bata kokarin maganan kan zancen halaiyar nasa balle a san mafita a kan dan nata.
A kan wanan tunanen na tsaya a zuciyana cewa duk ranan da wani zance ya kara hada mu zan fito fili in fada mata hakan don tasan dan da take min kyashin zama dashi fa ba cikakken namiji yake kamar kowa ba.
Sai dai me kuma a bangaren shi yaya Jafar din gaskiya yanzu yana jefa min wasi wasin akan shi ko da yaushe.
Don a gaskiya yana tsayuwan sosai akaina kan yadda mami din take kokarin nuna min zai tsaya ko a gaban kowa ya nuna shi bai yarda da hakan ba sam wanan ya kawo saukin wasu halaiyan da mami din ta dauko nuna min.
Wasa wasa saida sa,adatu ta shafe sati da kwanaki a wurin mu kafin ya shirya zancen zuwa gidan mu a lokacin.
Nayi mamakin irin tsaraban daya shiryawa tafiyan mu din da zan kaiwa iyayyena da yan uwa a gida.
Ga kuma kudi daya ban don kawai wanan tafiyan da har na rasa me zanyi dasu idan naje gida din don yawan su.
Lalai ka bar wanda yafika da wayaushi da hikima a kanka don sai Allah zai iya kwato ka gareshi gaskiya .
Don nikan yaya Jafar ya nuna min ya fini hikima da wayau tare da sanin duniya a yadda yake nuna min kamar babu gobe a kan mu wurin kulawa.
Saidai hakan bai hanani matawa da irin zaman da mukeyi dashi ba duk da yana rudina da abin duniyan da yake gani zai iya matar dani ga komai dake tsakanin din dashi na basajan da yakeyi wa mutane dani.
Wanda ya samu hakan ne ta dalilin hakkurina da zurfi ciki da Allah yai min wanda sam ban nunawa mutane sai idan kana da kula sosai zaka iya gane hakan.
Don ko zuwan sa,adatu wuri mu ban yarda ta fahinci irin rayuwan da mukeyi dashi din ba don yawan shakuwan dake tsakanin mu dashi zaka dauka wani zamane najin dadi akeyi tunda ba a daki daya nake kwana dasu ba.
Muka dauki hanyan garin mu a safiyan tafiyan cike da dauki da ka,idan zamuyi sati daya a gida mu dawo Abuja lokacin.
Na dauki duk wani abinda nake bukata har takarduna da bazan iya bari su a yanzu ba a matsayin riban da naci a zama gidan yaya jafar din danayi dashi.
Tafiyan mota masu lafiya karfe biyu da yan kai muna cikin gidan mu da mukai masu zuwan bazata a ranan do ba wanda yasan da zuwan mu a ranan sak ganin mu sukayi kawai ana muna sannu da zuwa.

HASBUNALLAHU WANI IMAL WAKEEL YA HAIYYU YA KAIYUMU BINRAHAMATIKA YA ASTAGIS, , , ,
BARKAN MU DA SHAN RUWA UBANGIJI ALLAH YA KARBA MUNA IBADUN MU YASA MUNA CIKIN YANTTANTUN BAYIN SA YA SADA MU DA RAHAMOMIN SA YA GAFARATAWA MAGABATAN MU YASA MU GAMA DA DUNIYA YA TSARE MUNA ZURI,AN MU DAGA FITUNTUNUN DUNIYA ALLAHUMA AMIN, , , ,

Yan uwa nayi rashin kanwar mahaifiyata hjy hazeena Ahmed dake aure a garin zuru matar Ahmed jolly provose na yauri.
Allah ya karbi ranta bayan gajeren jinya datayi anshan ruwa lafiya da ita ranan asabar ciwon kai da ulcer yayi sanadiyan barin ta duniya a ranan ta rasu tabar yara biyu a duniya da fatan zakuyi mata addu,a irin na addinin musulcin nagode.

Ba wanda yasan da zuwan mu ranan sai gani mu akayi mota ta tsaya da baki a kofan gidan mu idon mutane dake shawagi a lokacin ya dawo gare mu.
Sai ganin Sa,adatu data fito farko daga motan ya dawo da hankalin su sanin cewa bakin gidan mune wanan.
Saida na dan dade ban fito a motar ba ina daukan jakkata da sauram kayan dana rike a hannuna kafin na zuru kafata farare da suka canza dan samun daula a yanzu waje.
Kafin gaba daya na fito daga cikin motan nida sadiya kusan lokaci guda muka fito daga motan kallo ya koma garemu nan kowa ke fadin albarkacin bakin shi a kan mu.
Don wasu na tambayan ina sa,adatu ta samo turawa wasu na fadin yartane da yar uwanta da akace suna turai zaune an sayar dasu ga wani mai kudi sai kudi yake turowa iyayyen su ba a san ko suna raye ba daga cikin irin maganganun da Lantana ke yadawa a garin game damu.
Na juya ina magana da driver kafin na juyo na fuskanci shagon tsoho baba iro wanda na bari ds kaya cike a ciki a baya inda mafi yawan mazan unguwan mu ke zama da can amma yanzu banga kayan ba .
Ba kuma jama,a da yawa a wurin basu fi su biyar zaune wurin ba a ranan na dan daga masu hannu tare da fadin baba iro mun sameku lafiya ?
Da sauri suke amsa min tare da fadin cewan wani a cikin su kungaji aina fada maku itace don bata da girman kai kaf a cikin su.
Nidai na shige ina jin su ban tsaya kula su ba don maganan da suke fadi a lokacin game damu din.
Sa,adatu ce a gaba muna bayan ta muka shiga da sallama Lantana na wanki a part din ta ta dago kai don ganin wanda ya shigo don sai ka shiga ta cikin tsohon part din mu zaka shiga kofan da zai sadaka dana innan mu a yanzu tunda basu bude kofan su na baya da aikai masi Abban mu ya hana hakan duk cikin dokan lantana a lokacin.
Wanda ba don komai tayi hakan ba sai don duk wanda zai shigo wurin inna mu tana gani da kuma abinda za a shigo gidan dashi din.
Sa,adatu bata tsaya bin ta nata ba duk da ta dago tana muna kalon mamakin data kasa boyeshi a lokacin a fuskanta don zaka gane a rude take da gani mu din.
Wurinta na nufa da yar fara,a a fuskana ina fadin anty Lantana mun sameku lafiya tunda ita ta kasa magana sai idon data waro a bude a lokacin.
Can kamar a firgice take fadin ai Abu kune tafe ashe sannun ku da zuwa a yadda ta tareni wanan karon naji mamaki matuka tankar ba Lantana bace.
Na duka ina daukan yarta dake zaune tana kuka ga yarinyar ko wanka safe ba ai mata ba sai tsamin dauda da ke fita a jikin ta .
Uwar ke fadin kada ta bata maki kaya Abu fitina take ji dashi halinta ke nan kukan banza ko yaushe.
Bayan na dauki yarinyar na juyo ina fadin mun sameku lafiya ya bayan rabo cikin kame kame har lokacin take fadin ahe zaku zo yau bankoji ana fada ba.
Nace ba wanda yasan da zuwan mu a yau din shiyasa ina Asabe da cewa kakan mu tana wurin ta ta ban amsa sai bina da kallon mamaki da takeyi.
Ihun kanne da suka fito daga part din innan mune ya dauke muna hankali duk suka zo suka kankame muna a jiki nida sadiya dake makale dani duk inda na saka kafata.
Lah yaya kika dauki wanan mai dattin haka ta bata maki jiki kanwata ta fada a cikin gatse don lantana taji haushi.
An dauke ta din ai ita ba irin ku bace da kuke raba daya biyu a gidan nan an dai ji din a ajeta kada ta bata mata jiki.
Ban tsaya ta kansu ba don zasu iya rikidiwa a wurin nake gani don haka na nufi part din asabe kakan mu ina tambayan su hanyan part din.
A wurin asabe din sun tsaya suna wagala tsohuwar da tsokana wai mu din bakin turawane mun zo muyi mata alluran riga kafin tsufa ne.
Ita kuma ta yarda da maganan su ta shiga yin bare bare ban taba riga kafi ba tun zamanin shagari da akai muna lamba a hannu ina lafiya sai yanzu za a zo min wani allura can.
Asabe wai baki gani ni bane Abuce fa na fada ina kallon ta ina murmushi tace tana kallo a cikin mamaki.
Abu dai Abun dana sani sai kawai ta fashe da kuka tana fadin hakan ta rungumeni tana fadin.
Abu ashe zan ganki kafin na mutu Allah na godema da ka nuna min yaran nan sun dawo garemu lafiya.
Ana ta fadin mun sayar daku ga mutumin da bamu sani ba don munga kudi ya rude mu sai gashi mutumin arziki da alherin sa yana ta turo muna da abin arziki a gidan nan kai da kai.
Sai da muka dan dade a part din na asabe tana faman bamu dariya kafi mu taso zuwa part din innan mu har lokacin yaran lantana suna biye damu a baya har lokacin.
Asamau kanwata ta juyo cikin hattara tana fadin ku kuma ina zaku haka kuna wani bin mu a baya ?
Da sauri na juyo ina fadin haba asma,u ki daina hattaran su haka mana jin muryan Lantana mukayi daga bayan mu tana dauke da ruwan pure water da ta sayo muna tana fadin.
Haka suke masu ai komai bakin cikin ku kuwa sai kun gansu a cikin gidan nan wa yanda sukai gadon mugun abu a zuciya.
Duk da zancen nata ya dakeni a zuciya don nasan gun innan mu take nufin sun gado bakin halin ta manta da nata halin ita garesu.
Ko taga yadda na danyi da fuskane sai cewa tayi ga ruwa mai sanyi kusha na juya wurin asamu din ina fadin karba an gode anty lantana.
A waje na samu innan mu bakin baranda tana jiran shigowan mu da sauri na karasa jikin inna din sai hawaye suka zubo min lokaci guda don murna.
Sa,adatu na shiga part din mu take fadin inna bani makulin kofan nan na baya a bude a shigo da kaya ta mika mata a daidai lokacin ne aka fara shigo da kayan da muka zu dashi din na tsaraba da ya sayo muna.
Yayin da lantana ta koma ta kasa ta tsare a kofanta taga an shigo da abinda muka zowa inna dashi gidan zuwan mu.
Drivers din basu tsaya ba kamar yadda ya umurce su da sun sauke mu su juyo da mota daya zasu bar daya a gurina a nan don zirga zirgan mu a garin.
Haka yasa suna gama sauke kayan sukai muna sallama duk da nasan ya sallamesu hakan bai hana na kara masu alheri ba da zasu tafi.
Falon na inna ya hargitse da hayaniya lokaci guda kowa sai fadin albarkacin bakin sa yakeyi a lokacin kan mu.
Gyaran muryan da Abba yayi yasa kowa natsuwa a falon nan aka shiga gaida shi da dawowa gida yana amsawa sadiya ce ta taso ta rungume shi.
Farin cikin Abba bai boyu ba ga ganin yadda muka sauya gaba dayan mu yake fadin wai sadiya ce wanan ko yar gidan gwaunan jahan nan ?
Duk aka kwashe da dariya a falon sai lokacin na fito daga cikin daki ina fadin Abba sannu da dawowa ya washe baki don gani na yana fadin a, a Abu kune haka tafe ?
Yaya shi maigidan naki da mahaifiyar shi tare da yan uwan shi shine tambayan Abba a gareni cikin nuna jin dadi da rikon da suke min a can.
Allah sarki ABU CIKIN DUHU SIRRINE yanzu shi Abba yana tunanen zaman mutunci muke dasu a baki daya har nayi wanannsauyin da yake gani a tare dani a yanzu.
Muryan Abban ne yake saka masu albarka kan kokarin da sukeyi damu a can hakan yana fadin wa yan nan mutanen sai godiya kawai Asiya.
Da cewan innan mu ya fadi sunan ta kai tsaye don jin dadin abinda idon shi ya gane mashi bai san na badinin dake a boye ba a lokacin.
An dan taba hira kafin ya mike don fita yana fadin bari je a nemo abinda za ai masu kafin yamma yayi ya fita.
Har kwana biyu ina gida iyakata na fito daga part din mu zuwa wurin Asabe da lantana mu gaisa in dawo dakin mu bazan kara fita ba sai kuma washe gari.
A rana ta uku da zuwan mune na shirya zuwa gidan su maizube don mu gaida su tunda mun saba sosai yanzu dan zaman mu da ita a abuja kafin mu koma chaina akwai shakuwa sosai a tsakanin mu da ita yanzu don lokaci lokaci muna waya dasu.
Don idan nabi ta mutanen dake shigowa ba zan fita zuwa ko ina ba garin nan don tsaraban da ina ta zauna ta rabawa mutane unguwa da yan uwa yasa suke shigowa gaishe mu.
Cikin wani dinkin yan mali na shdda marron colour dinkin har gwiwa yakai min ga farin lace da akai mai kwaliya dashi duk jikin kayan.
Duk da ba dadin daura zanin nake ji a yanzu ba haka dai na daure na daura don sanin gidan da zan tafi wurin malam ne mu gaisa amma da abinda zai kaini kuma a kasan zuciyana.
Mun fito a cikin shiri na tsaya da inna muna magana take fadin idan mun fito mu gangara mu gaida wasu yan uwanta nace to inna.
Ni da sa,adatu ne a gaban motan tana nuna min wasu sabbin gina har na dauki hanyar da zai kaimu gidan malam din.
Muk tsaya a kofan gidan malam din da mota na bude muka fito suka kwaso kayan muka shiga ciki.
Farko munci karo da kishiyar su wace itace amarya a gidan tana ganin mu take fadin shike nan ma yaya ga wace zamu gaidawa anjima tazo har gida.
Nan suka fara fitowa suna muna sannu da zuwa muna amsawa kafin mu zube a dakin maizube ana sabom gaisawa da yaushe rabo ?
Munyi hira sosai dasu kafin kafin su watse suh bar daki ya rage sai mu da ita take tambayana ya bayan rabo ?
Na danyi murmushi kafin nace wallahi maizube sai alheri saidai har yanzu muna nan kamar yadda kika sani.
Ta dafe kirji tana fadin ban fahince ki ba zainab kina nufin har yanzu ba wani abu a tsakanin ku dashi ko me ?
Kallon sa,adatu dake zaune nayi sai na kawar da kai da sauri ta gyara zancen ta da fadin har yanzu ace ba shiri dake da yan uwan shi haka ?
Sa,adatu ta cabe da fadin wallahi maizube nima shedane kan hakan dan zuwan nan da nayi kwana biyu sai dana sheda hakan.
Nan ta shiga ba maizube labarin abinda ya faru tsakanin mu da mami a gidan ta ranan tace ikon Allah wanan matar da karfin hali take ashe.
Zamani na abinda dan ka ya kwaso har idan baida illa akaima sai ka ruguma da hannu biyu tunda ba Allah ya hana hakan ba.
Saidai idan da illa ga abin zaka nuna kinsa gareshi har sai ya gane abinda kake nufi da hakan.
Amma wanan kamar tana jayayya da ikon Allahne hakan shiyasa nake son na bar masu gidan har danta na fada a sanyayye ina dukar da kai kasa duk suka kaleni.
Ki bar mata danta anty ai sai taji dadin hakan tayi nasara ke nan a kanki wallahi ke suka samu sukewa hakan da nice da duk sun gane kuren su har wa yan nan yan matan gidan nata masu yiwa mutane kallon raini din.
Amma kice zaki bar mata danta dama ai haka take so ita ki barshi din tunda dama ba zaman ku a tare take so ba dashi.
Tana fadin hakan ta mike tsaye tare da fadin ni barin kewaya kinji fitsari ya cika min mara tun dazun wallahi ta fita daga dakin.
Maizube ta kalleni tana fadin amma yanzu kun daidaita da mijin naki a tsakanin ku nan ma kaina iya kada mata alaman a,a takaice na dan fada mata abinda zan iya don ta fahinceni.
Hankalin maizube yai matukar tashi a lokacin sai maimaita cewa takai har wanan lokacin kana zaune da mutum kamar dutse ba abinda ke gudana a tsakanin ku haka ?
Gaskiya wanan ba abinda za a kyaleki bane zainabu don a gaskiya kina cutuwa da yawa sai dai dole ki san yadda zaki bulowa mutane da maganan a yanzu.
Maizube wanan ba wani abu bane illa ranshi daya fita ga mata sai yan uwan shi maza yake bi shine matsalanshi kawai.
Jam jam wa,iyazu billahi wanan abin da muke ji dauri a jakkar magori shine ya kawo garemu yanzu ?
Shigowan sa,adatu dakin yasa mukai shiru kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi cikin mu a lokacin.
Anty muje kinsan ba nan kawai zamu tsaya ba gashi malam bai dawo gida ba har yanzu.
Zan dawo na yini a nan na fada ina mikewa don nasan maizube din zata fahinci mai nake nufi da hakan dana fada ai.
Mukai masu sallama muka fito daga gidan zuwa gidajen da inna ta umurce mu da mu tafi idan mun fito gidan malam din har gidan mahaifiyar Lantana nasa muka je mukai mata alheri bayan mun gaida ita sa,adatu ta cika fam dani kan zuwan mu gidan.
Sai bayan la,asar muka dawo gida a gajiye mun samu wai anyi fada da innan mu da anty lantana wai an fake da zuwan mu Abban mu yana shiga lungun inna ko wani lokaci yanzu.
Wanan maganan shi ya kawo fitina har suka kaure da fada a tsakanin su don kishiya bata raina abin fada kullun.
Ana hakane muka shigo gidan a daidai lokacin da Lantana ke fadin mijin yae taki dake yankan kai yana turo maku kudin jini kuna kashewa keda ubansu.
Muka karasa shigowa muka samu ko wace na tsaye cirko cirko rayukan su a bace sunyi shiru don ganin mu.
Kamar ba zan tanka masu ba har na dan wuce na juyo ina fadin haba innan hakan ba girman ki bane yanzu ai shi kadai na fada na shige part din inna abina.
Saidai ina tunanen a raina wanan maganan ke nan ina ga sun san gaskiyan ko waye mijina a gaba me Lantana zata fadawa innan mu ke nan ?
Dakuwan da muka dawo dashi daga gidan wata yar uwan inna na bude ina rabawa kannen mu kan na fara ci na dibarwa yayan lantana nasu akai masu.
Nan sa,adatu ta hau fada ba za a basu ba ai yanzu muna ji ta gama zagin innan mu da mijina tana masa kazafin da ba shi ba a tsakar gida.
Nace naki ne ko nawa sa,adatu duk me tayi don kanta ai itama ta haifa kuma zasu girma ai taji idan da dadi abinda takeyi din.
Inna ta shigo nake mata maganan don Allah ta bar biyewa haukan lantana suna zama daya haka a gaban mu.
Dama shi me son fada maka magana yakan jaka fadane ya samu kafan fada ma magana a cikin fada din.
Yar nan bar wanan matar mara hali ko yaushe ita burin ta shine taga ba, a zauna lafiya ba a gidan nan.
Nan dai na bawa innan mu hakkuri aka bar zancen kowa ranshi ba dadi ga abinda ya faru din ranan.
Sai bayan kwana biyu ina kuryan dakin inna kwance da dare bayan kowa yayi barci inna ta sameni ta zauna a bakin gado inda nake kwance.
Na dago da sauri ganin ta shigo ta zauna a wanan lokacin nasan magana ya kawo ta wurina ke nan.
Yar baba meye damuwan ki da har kika kasa fada min kike shiti yankewa kanki hukuncin da bai dace ba badon sa,adatu taji kudirin ki ba kan hakan.
Wani abu ta fada maki nayi inna na tambaya cikin mamaki don na manta da munyi wanan zancen a gabanta.
Hukuncin da kike shirin dauka don kawai mahaifiyar mutymin nan bata kaunarki da danta har yanzu.
Wani dan murmushi na sake a fuskana kafin na fara silalo da hawayen takaici na dago kai na kalli inna cikin karfin hali na toshe bakina ina fadin .
Inna ba don mahaifiyar shi nake son rabuwa dashi ba don akidarshi ce daya kaucewa addini nake son barin shi.
Wani ka)on mamaki inna tayi min kafin tace dani kin ko san abinda kike fada yar nan mutum kamili kamar wanan zakiwa sheri don kawai bakya son shi ko me zaki mai wanan kazafin ?
Kallon ina nayi nan dan lokaci kafin na girgiza kai ina hade wani kololon bakin ciki daya tokare min makogorona dama nasan za a rina idan na fito masu da wanan zancen ai.

YA ALLAH ALLAH KA JIKAN MAGABATAN MU KA GAFARTA MASU KURAKUREN SU KASA ALJANNAN MAKOMAR MUSULMAI YASA ALJANNA MAKUMAR WANDA YA FURTA KAMAL LA,ILLAH HA,ILLAH MOHAMMADAN RASULULILAH, , , , , , ,


YAN UWA MUSULMAI YA SHAGALGULAN SALLAH DA BANKWANA DA RAMADANA DA FATAN RAMADAN DIN BANA YAZO DA KARA MUNA IMANI A ZUKATAN MU AMIN, , , ,


Ganin da inna tayi na kasa magana sai hawaye ke zuba a fuskana sai kuma ta shiga damuwa lokaci guda ta rude.
Hankalinta ya tashi ta koma fadin ki rufa muna asiri ki rufa min idan da wani abu ki fada min mu san inda zamu bullo ma ko meye matsalan ki da mijin ki yar nan ?
Da kyar na iya budan bakina da yai min nauyi ina fadin inna da matsala a cikin auren mu babba sai dai idan kince na koma mu zauna a hakan zan koma don ke .
Menene matsalan dake akwai tsakanin ki dashi inna ta sake tambaya tana kallona don son jin mezan fada.
Bakina yai nauyi da abinda zan fadawa innan sai kawai naja filo na mayar da kaina tare da sake wani irin kuka lokaci guda mai ban tausayi.
In don matsalan kice da uwar mijin ki wanan ba kanki bane farau ai naji muryan innan na fadi,don da wayau ki kinga irin zaman da mukayi da kakar ku a gidan nan.
Yanzu fa da nayi hakkuri komai ya wuce sai abinda ba,a rasa ba tunda yanzu ta gane gaskiya ita da kanta.
Cikin kukan da nake nayi karfin halin fadi inna matsala ba irin taki bace tawa matsalan daban yake dana ko wace mace inna.
Subbahanallahi wanan maganan babba ke nan ta fada sai kuma tayi shiru na wani dan lokaci can naji ta mike zata bar dakin .
Ta kai kofa ta juyo tana fadin kiyi tunane kafin ki san abinda zaki fadawa mahaifin ku don kin san shi kin san halin sa ta fita.
Ban daina kuka ba sai ma karawa da nayi kan wanda nakeyi da farko don nasan za a rina kan hakan.
Don ba kowane zai yarda da abinda zan fada ba gashi ma ban fada din ba a fahinceni asan akwai matsala akan hakan dana ce.
Haka na kwana ranan tare da dinbin tunane a raina ina nemawa kaina mafita da naga zai dace dani.
Washe gari koda muka tashi inna ta dauki zafi dani sosai ko gaisuwan da nayi mata da kyar ta iya amsa min shi ba cikin dadin rai ba.
Ganin haka yasa nima na nisance ta na koma kuryan daki ban zauna a falo ba yadda muka saba gaba dayan mu.
Kanne na sai shigowa dakin suke suna tambaya ko lafiya nake na zauna a dakin har tsawon kwana biyu muna haka da inna ba wani sakewa a tsakanin mu ni da ita.
Ranan na uku na shirya nake fadin zan je naga maizube tayi min sai mun dawo wanan tafiyan ban yarda na tafi da kowa ba sai karamar kanwa daya dana dauka muka fita tare da ita.
Nayi sa,a na samu malam a gida muka gaisa da matan shi maizube tayi min jegora zuwa wurin malam din.
Ya tareni sosai yana saka min albarka tare da kara ban hakkuri irin na manya kafin maizube tace dashi barin baku wuri ku gana ayi yaushe rabo ko ta fada cikin hikima .
Nace ba sai kin fita ba ai tunda kin san komai tun farko kamar dai yadda kika barmu har yanzu hakan muke dashi.
Ta amsa da fadin eh malam gaskiya kamar yadda dai na fara fada mane zaman nasu ba dadi sai hakkuri.
Ga kuma fannin uwar mijin nata shima dai babu dadi har yanzun din don kiyayyan nata da ita yana nan bai gushe ba.
Nan malam din ya danyi murmushi yana fadin halin ku mata sai ku wallahi mace ko tayi shekaru kamar me bata taba canza halinta na mata.
Ita bata san ke din alheri bace a garesu ke maizube na fada na kara fada maki tun farkon auren yarinyar nan ita din alheri ne a cikin su.
Duk sanda zanyi istihara akan matsalan su ni haske nake gani a lamarin nan banga wani abin aibu ba a cikin auren ta da yaron nan .
Sai dai dan matsala na rayuwa da ba a rasa ba can da ake samu gun ko wasu maurata da suke tare na rayuwa.
Dakin yayi tsit babu mai motsi a tsakanin mu sai can na gyara zama ina sharce zufan dake zubo min a goshina lokaci guda jin abinda malam din ya fada.
A raina ina fadin ta yaya malam zai fadi hakan har in ance malamai suna ganin abinda ke faruwa ga mutum .
Ni tayaya malam zai kira min wani alheri bayan halin da nake ciki muryan malam din ne ya dawo dani daga tunanen dana tafi yana fadin.
Maizube ki bamu wuri in kara ganawa da ita akwai abinda nake son ji a bakin ta don naga akwai nauyi a tare da ita har yanzu.
Take maizube ta mike don bin umurnin mijin nata tana fadin nima dai haka naga yafi don matsalan kawar tawa babba ne don gaskiya malam sai anyi bicike sosai ga matsalan nan.
Ace mace na zaune gidan miji har tsawon wanan shekarun yana kallon ta photo malam ba ko wace mace bace zata iya wanan hakkurin haka.
Hannu malam din ya dagawa mai zube din alaman ya isa tare da fadin ke kuma yanzu zaki zama babban banza ko makin ki yabe ta kan hakan sai kuma ki tunzura ta.
Malam abinne keda daure kai wallahi koma meye Allah na maganin sa ai tana kokari tunda har takai haka dashi yanzu riban ta ya rage ta girba da yarda ubangiji ya fada yana daukan tasbahan dake aje a gefen shi.
Maizube ta sa kai ta fita tana fadin Allah yasa haka malam muma ai hakan muke fata wallahi.
Ki daure kinji malam ya fada bayan fitan maizube dakin yana fadin koma meye matsalan da yarda Allah saukin shi na zuwa.
Kinyi kaifin basiran zama hakan ansani an takura da yawa idan hakan gaskiyane sai na tare shi da fadin.
Malam ba zan mashi kazafi ba ko kadan kalar rayuwan shi shi daban ne dana sauran mutane don da bakin shi yasha fada min shida mace sai zaman mutunci da yan uwan taka a tsakanin su.
Malam ya kada kai nace kuma ko acan da muke ya sha ya fada a gabana da cewa nidin kanwarshi ce ta jini.
Jam malam ya fada da sauri a cikin mamaki kafin yaci gaba da fadin dole akwai abinda ke damun shi a rayuwa daya kawo hakan.
Malam ba wani abu bane illa masifan daya fada rayuwan shi a ciki na bashi amsa daga inda nake zaune a gefen shi.
Ya dago kai tare da tambayana ko kin san duk wani halaiya nasa zuwa yanzu bana son ki boye min komai da kika sani game dashi .
Ki dauka nan kamar yadda zaki sake da iyayyen ki ki bani amsan komai a bayane ta yadda zamu san mafita akan lamarin.
Dan dukar dakai nayi na dan wani lokaci kafin na dago na fara fadawa malam din komai dana sani a game dashi.
Har maganin dana amso mashi a wurin kakan maya da yadda mukayi dashi a lokacin har abinda ya fada min zuwan mu nan ban boyewa malam din komai ba na fada mai.
Sai dai kafin in gama fada mai idanuna sun cika da hawaye a lokacin haka na karasa a cikin kuka da bacin rai.
Shiko malam babu abinda yake fadi sai wa,iyazu billahi har na kai karshe yana girgiza kai cikin mamakin abinda nake fada mai.
Dan shirune ya biyo a dakin kafin inji muryan shi yana fadin Allah kai muna tsari da sherin zamanin nan.
Sai dai ko akwai wanda kika fadawa a cikin yan uwan ki ko iyayyen ki wanan zancen da kika zo ?
Kaina girgiza mai kafin na iya budan bakina da kyat nace dashi a, a malam ko kanwata da muke tare a can bata san da zancen nan ba.
Kin kyauta kwarai da kina karaman na har kika iya rikewa mijin ki siri irin wanan nace to amma malam.
Sai dai yan uwan haihuwan shi da mahaifiyar shi sun sani suma din banice na fada masu ba halin yau da gobe ne yasa suka gane hakan.
Amma mahaifiyar suce nake ganin bata yarda da zancen ba duk da taga makamancin hakan tare dashi amma laifina take gani na ma danta sheri.
Malam ya tare da fadin mata ke nan ga gaskiya sai su baude soboda son zuciya da diya da Allah ya dora masu.
Babu uwar da zata yarda da sherin danta idan bata gani da idon ta ba saidai dan wani haka kuke mata wurin son kai.
Ita yanzu ba abin ta gode maki bane a irin kokarin da kikayiwa rayuwan su da badon Allah ya taimaka kin hadu da wanan kawar data taimaka maki ba wa yasan inda abin zai tsaya mai tunda masiface wanan Allah ya jerabi rayuwan shi dashi.
Nayi shiru shima din dai shirun yayi har na dan wani lokaci kafin na dago kai ina fadin ni yanzu malam so nake kawai a rabani dashi ba zan iya wanan zaman dashi ba.
Da sauri ya dago kai ya tsura min ido kafin ya sake murmushi yana fadin kayya yaro dai yarone ashe ?
Ke abu baki tashi rabuwa dashi ba sai yanzu da tafiya ta kawo ga gangara a tsakanin ku kada ki zoje ladan ki wurin gajin hakkuri irin na dan adam.
Ai tunda kika ji ya fada da bakin shi ya daina haka din ne ya daina sai dai yanzu mu nemo mafita ga zancen kawai.
Yanzu abinda nake so dake ki ban kwana biyu nayi ustihara naga inda bakin zaren yake don mu san daga inda zamu fara aiki a kai.
Ina fatan dai kina da sauran kwanaki kafin ki koma ko ya tambaya yana kallona don jin abinda zan fada.
Sai dana gyara nace dashi malam akwai don kwana goma ya ban nayi a nan yau muna da kwana shidda da zuwa garin nan.
Yace masha Allah kafin sauran kwanakin su cika mun san dan abinda za a gwada a gani ko Allah zaisa mu dace da hakan .
Amma ba zan ce dake komai ba a yanzu sai idan mun duba mun gani duk abinda ya dace sai ayi sai ki matsa da addu,a a naki bangaren don addu,an ki yana da tasiri a gareshi sosai.
Mun dan dade yana min yan nasihohi su na manya kafin in fito in masu sallama na dawo gida.
A gidan kuma bayan barina gida inna da sa,adatu sun tasa sadiya a gaba suna mata tambaya.
Sai fasin take bamu da matsalan komai da yaya din nan take kara basu labarin irin rayuwan da mukeyi a can har zuwa lokacin dana dawo gida .
Gaida inna nayi na shige dakina kai tsaye ban tsaya a falon da suke zaune ba don ban jin dadin yanayina a lokacin.
Sa,adatuce ta dauko abincin ta shigo dashi dakin ta samu na ina rage kayan jikina don zafin daya dameni tunda na faita.
Ga abincin ki anty ta fada na dan kallo ta ina fadin nagode zan kewaya nayi alwala kafin naci don naga lokacin azahar ya gabato.
Kodana idar da sallah ban tsaya bin ta abinci ba na koma saman gado na lafe ina faman tunanen zancen mu da malam da muka fara.
Har inna ta shigo ta sameni a hakan take fadin au abincin ma da aka kawo maki bakici ke nan ko ?
Na dan dago a yadda nake kwance nace zanci anjima inna ta juya tana neman abinda zata dauka a dakin daya shigo da ita.
Zata fita take fadin ya zancen ku na zuwa fambeguwa da kuyi wurin yar inna dake aure a can .
Sai lokacin nadan dago da kyau ina fadin zamu tafi inna akwai abinda nake jira na karba ne zuwa jibi sai mu tafi.
Daga hakan tasa kai ta fice a dakin bata kara magana ba wanan zancen da mukayi da inna ne zuciyar ta ya bata taje wurin malam din koshi yasan irin matsalan da nake fuskanta tunda na kasa fada mata ita.
Da yamma naji tana sallaman mu cewa ta unguwa wanda tun zuwa mu banga ta fita ba sai wanan ranan.
Sai dai duk da hakan ban kawo komai a rai
na ba kan hakan sai ta dawo da mukai mata nan kanne suka sameni a dakin muna hira duk da ba dadin hiran nake ji ba a lokacin.
Taje wurin malam din sun gaisa take fada masa damuwan ta a kaina tare da yadda mukayi da ita din.
Malam din yace koda baki zo ba a yau ni zan aika kizo ai don yarki na cikin gagarumin matsalan rayuwa da ko ke din nan mahaifiyar ta ba lalai bane ki iya daukan hakan.
Sai dai ki godewa Allah da ya baki ya irin wanan a rayuwan ki don ita di abin alfaharine ga kowa idan ya samu yaro irin hakan.
A matsayin ki na uwa a gareta ke ya dace ta fadawa wanan damuwan nata ki san irin matsalan da yarki ke ciki na rayuwa.
Amma sai kika kasa yin hakan gareta kikai aikin jahilci baki tsaya kin san damuwar yar ki a gidan auren ta ba.
Yau da ace ba yarki bane dakeda zurfin ciki da tunane wanan zancen ya fita a garin nan ke kanki da fita waje ya gagareki koda rdarene kuwa.
Gaban inna dake faduwa ya kara bugawa sosai don jin abinda kanin mahaifin nata ya fada a kaina.
Ta dago kai a cikin tsoro tana fadin malam ban san abin yakai girman haka ba na dauka irin shirmen yaran yanzu ne kawai take son ta aikata.
Koma shirmene Asiya ai sai ki saurareta kafin ki balbale ta da fada ki kara tayar mata da hankali haka.
Idan ma baki sani a yanzu yarinyar nan Abu tana bukatan taimakon mu akan rayuwan da takeyi a gidan mijin ta din matsalan ba karami matsala bane a yadda kike tunane.
Na shiga ukku inna ta fada tana kyarma tare da fadin meye matsalan da yai girma haka malam ?
Kin ga ki kwantar da hankalin ki insha Allahu Allah zai muna mafita ga wanan zancen nan inna ta fara kyarma tana magiya ga malam din ya dan fada mata wani abu do hankalin ta ya tashi sosai.
Na fada maki ki kwantar da hankalin ki ya zama dole ai ki san wani abin don ki taya ta da addu,a don ba zamu kyale yarinya ba ta zauna haka har tsawon shekarun nan babu abinda ya taba shiga tsakanin ta da miji na aure.
Innalillahi wa inna alaihim raji,un malan matsalan da yar nan ke ciki ke nan ban sani ba kadan dai kikaji Asiya daga abubuwan dake gudana.
Saidai abinda nike so dake wanan maganan yanzu ya tsaya iyamu don ko mahaifin ta ban son yaji wanan zancen yanzu sai in har abin ya gagare mu.
To ya zama dole ya sani a lokacin don ba zamu yarda yarinya ta koma tana zama haka ba shekaru kurewa shigewa suke ga bawa.
Malam nagode Allah ya bar zumunci inna ta fada dolene muyi maki Asiya don kema baki yarda mu ba ai, ko banza ai dole muyi maki tunda muna raye daku.
Haka inna tayi sallama da malam din cikin tashin hankali ta dawo gida yanayin ta kawai zaka kalla ka san cewa tana cikin tashin hankali.
Kallon juna mukayi nida sa,adatu sai sa,adatu din ta tashi ta bita zuwa cikin dakin sukai kus kus naga itama ta fito a cikin damuwa a fuskanta sai dai ta zauna ta dan wayen ce kawai.
Tun wanan ranan inna ta koma rarashi na tana jana a jiki dama akwai akidar yar farko da takan nuna min wani lokaci don sunfi shakuwa da sa,adatu gaskiya sama da ni.
A cikin hikima da dabara takan sameni a daki mu danyi hira tana dan jefo min zancen zaman mu wani nakan bata amsa wani ko na yi shiru kawai don amsan bai faduwa.
Da haka har inna ta fahinci wani abu take dan ban hakkuri na daure in kara hakkuri don haka zama ya gada wani lokaci mata da hakkuri aka san su dama.
A raina nakance wani hakkuri ba inna nawa kan yafi gaban yin hakkurin da kike nufi nayi.

ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA DA FATAN MUN WUNI LAFIYA ALLAH YA SADA MU DA AHERIN SA AMIN YA ALLAHU, , , ,

YAR UWA KADA KI MANTA NOVEL DIN KUDINE KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA, , , ,

Sannu a hankali har inna ta fahinci irin zaman da nakeyi da ya jafar tun bayan auren mu dashi ba abinda ya taba shiga tsakanin mu har zuwa wanan lokacin.
Kalman hakkuri kawai da ban baki yake fita daga bakin ta na kara hakkuri na dan lokaci kamar yadda malam ya fada.
Na kancewa inna naji kawai amma amma a zuciyana ba haka abin yake ba din ni ba zancen gyara nake so a tsakani mu ba illa iyaka dai naga na barshi har abada.
Kwana biyu ya cika a haka na shirya zuwa gidan malam din kamar yadda mukai alkawari dashi zanzo bayan gama binciken shi.
Inda na samu ni yake jira na iso daman zai tafi wani unguwa shi bayan mun gaisa da iyalin malam din mun dan taba raha kamar yadda muka saba da iyalinshi idan mun shigo a matsayin su na matan kakan mu din.
Na nufi wurin malam din ni kadai nabar kanne dana zo dasu tare dasu maizube suna hira a tsakar gida.
Muka gaisa dashi yake tambayana lafiyan inna nace suna can lafiya ya dan dade yaja dan dube dube yana jawo ledoji a cikin kayan shi.
Kafin ya dago kai yana fadin kamar yadda na fada maki zanyi istihara kafin nace wani abu sai idan na bincika naga abinda ke nan.
To a gaskiya nayi din kuma naga akwai matsalan da duk kika fada ba karya a cikin sa ko kadan.
Ya dago kai ya kalleni na dukar da kaina a cikin damu a lokacin da yake fadin sai dai abinda nake so dake yanzu na farko ki kwantar da hankalin ki .
Komai yana bukatan natsu a cikin sa dolene mu bishi a sannu kafin mu kai ga nasara ga abinda muke nema.
Bai fada maki karya ba kamar yadda yace maki ya daina ya daina wanan harkan din saidai kawai matsalan da karfin maganin nan da tsohuwar nan tabaki da yaso yai mai yawa a jikin shi saboda abin ya bugeshi sosai.
Ki godewa Allah yar nan da Allah ya taimakeki ya hau dake kan masu bibiyan ki da sheri akan mijin naki.
Mafarkin ki da kikeyi a baya ya baiyana a gareni yanzu na fahinci dalilin mafarkin naki akan wanda kike yawan gani ya shiga tsakanin ki da mijin ki a cikin mafalkin ki.
Ba wani bane illa wanan harkan da sukeyi ne Allah ke son ya baina muna tun baya ba a gane hakan ba sai yanzu da lokacin da baiyanan yazo muna.
Don haka ya zama dole ki daure ki kara jajircewa akan wanda kikeyi tun farko kada su ga kasawan ki ga hakan.
Babban kokarin da zamuyi shine muga mun shawo kan matsalolin nasa a baki daya har in son samune ya rabu da abokan harkan nasa har abada.
Saidai gaskiya wanan tsohuwar data baki magani tasan kanta a wirin aiki don tasan magani sosai.
Don mawuyacin abune mutum ya iya daina wanan dabi,an haka kai tsaye ba tare da ansha wani wahala sosai ba dashi.
Don abin nasa ya hade masa da yawa akwai sa hannun makiya dana muggan abokai a cikin lamarin shi .
Shi yasa abubuwan suka taru sukai mai yawa a lokaci guda don Allah yayi yaron nada karfin arziki mai yawa a rayuwan shi dan ba haka akaso ya kasance ba.
So akayi ga baki daya ya lalace a rayuwan shi tun farko an haska anga cigaban shi dana sauran yan uwan shi akwai rinjaye mai tazara a tsakanin shin da duk wani na family din su baki daya tun wanan lokacin aka jefa masa wani rayuwa na daban a cikin lamarin shi don ba haka mai sakon yaso ya kasance ba.
Kuma an basa abin yacine tunda kurciyan shi na yarinta akaso ya soma lalacewa don mahaifinsa yana tsaye da lamarin yanyan sane abin bai samu tasiri sosai a jikin saba wanan lokacin sai bayan mutuwan mahaifin nasa ne abubuwan suka fara aiki a jikinsa yanzu.
Gareku iyayyen zamani kalubali ne wanan zancen a gareku mu kula da wa yanda muke mu,amula dasu a rayuwan mu don wasu a fuskane kawai soyayyan su garemu.
Baikai ciki ba yadda kike zaton kekaki bazaki iya cutawa dan wani ba wani nacan ya kyashewa naki yana kai masu hari a fakaice sai mu yawaita addua gun yayayen mu don nema masu kariya daga shedanun mutane kamar yadda malam ya fada mahaifin su jafar yana tsaye ga addua a gun yayan shi.
Shine dalilin dayasa abubuwan jafar din sukai sanyi basu samu aiki a gareshi yadda maishi yaso ya gani ba.
Ga kuma abokai dake canza rayuwan yaro lokaci guda ya zama dole garemu wanan zamanin musan dawa diyan mu suke mu,amula a kullun don kawaicewa fadawa halakan zamanin Allah ya tsare ya kare muna zuri,a amin.
Har malam ya gama bayanin sa jikina ya mutu a lokacin ina tunanen waye zai jefosa haka da mugun abu don ya koma hakan.
Don masu kishiya nake jin iri wanan kalamin na faruwa a tsakanin su idan a hadu da mai raunin imani.
To amma gashi ita mami bata da kishiyan kuma hakan ya sameta ga zurian ta yanzu.
Muryan malam ne ya dawo dani ga tunanen da nakeyi da yake fadin kinga akwai aiki babba a nan don sai mun wareware kulin zamu san aikin mu na kyau akansa.
Na gyada kai kawai alaman eh malam don jikina ni lokacin ya gama mutuwa da zancen daya fada min din.
Zaki iya turarara wanan hayakin ta yadda zai kai ga hancin sa ya shaka na kwana uku malam ya tambayeni.
Na dago da kai da sauri a dan razane don sanin kwanan wasan don wancan karon da kakar maya ta ban magani yadda muka kwashe dashi.
Malam bai tsaya jin ta bakina ba don ya fahinci irin tunanen da nakeyi a lokacin sai cewa yayi dani zaki iya mana sai kace ke din ba mace bane.
Yana fadan hakan yake miko min maganin dake kulle a cikin wani dan kyale ja na karba kafin ya juya yana dauko wani a haka dai duk yai min bayanin ko wani maganin da amfanin sa gareshi.
Nabar gidan malam a hanya wayan ya jafar ya shigo min na dauka da kyar bayan mun gaisa yake fada min yaso shigowa satin nan don mu dawo amma yafiya ya kamashi zai fita ba zai dade ba zai dawo sai yazo ya dauke mu mu dawo.
Jin hakan take wani tunane yazo min a zuciyana don na gama yanke shawara a kansa ko yanzu.
Do duk abinda zanyi karshe nice mai laifi a wurin mami ba zata ga hakan ba sai laufin da zata dora min da banji ban gani ba.
Haka na dawo zuciyana cike da zargi iri iri a lokacin don ni abin har tsoro ya fara ban don mutum ba abin yarda bane ashe haka.
Don ko waye lalai na jikin sune don yadda mami take kafa kafa da yayan ta nake gani ashe hakan bashi ya dace tayi kawai ba a rayuwan ta a kan yayanta.
Don bayan sa ido irin wanan da takeyi ya zama dole kuma uwa ta dage da addu,a da neman tsari gun yayayen ta ashe .
Koda ta hanyar yawan yin sadaka ko alheri da sunan yayanta Allah ya tsare mata su don sherin zamani.
Amma da yake ita mami yanzu irin rayuwan turawa ne gareta duk ta mance da wanan a rayuwanta batayi sadaka ba zuwa garesu don hakan balle wani neman taimako gun malamai a kansu don abin yanzu saida hakan .
Saidai kada mutum ya zure don gudun fadawa ga halakan ubangiji don yadda da irin abubuwan nan gaba daya yana juya kan mutum ya manta da Allah watarana.
Sai mu kula mu dinga sadaka da sunan yayayen mu da yawaita alheri ga marayuwa da masu karamin karfin shine mafita.
Washegari kawai na tashi ina fadawa inna zan tafi fambeguwa tayi mamakin hakan saidai bata hana mu zuwa ba sai ta fadawa Abban mu shima ya yarda.
Da sa,adatu da sadiya mukai tafiyan inda Allah ya taimakeni shine mun tafi washe gari sai ga waya ana neman su sa,a datu makaranta nace su tafi tare da sadiya don naga bata sake jiki ba.
Suna tafiya nima na tsiri tafiya kan zanje na duba wata kawata na dawo kafin su dawo haka na samu hanya na balle ba wanda yasan inda na nufa.
Ni kaina ban san inda zan nufa ba na juyo zuwa kaduna kawai gidan wata kawata da mukai yayin zuwa makaranta a tare lokacin can dabaran zuwa ya fado min don su din gidan sune na kansu bana wani ba.
Ban sha wani wahala ba sosai wurin gane gidan saidai itace da farko bata gane ni ba saida nayi mata kwatance da kyau tace ta ganoni ta rungumeni.
Mun zauna ana yaushe rabo a nan take ban labarin ai mahaifin su ya rasu bayan rabuwan mu bada dadewa ba.
Na tausaya masu sosai don ni kaina naga sauyi sosai a gidan maganane kawai ban yi ba tun shigowana.
Gidan da yake da yawan arziki ga yan aiki da jama, a amma yanzu shiru babu kowa tun wajen gidan shara da tulin ganyen bishiya zasu tareka a waje shiyasa da farko harna zata ko ba kowa a gidan ne yanzu.
Mun kai wani lokaci muna hira kafi mu ci abinci mu kwanta barci na kashe wayana gaba daya tun shigowana garin kaduna na jefa a jakana.

Ya jafar ya kira layin nawa yafi a kirga da safe zuwa rana don hakane ya nemi layin Abban mu yake tambayana.
Abban yake fadin bata fadama zasu ziyara nan fambeguwa wurin yan uwan mahaifiyarsu ba yace ok kila ta fada min na mantane ya kashe wayan bayan sunyi sallama da Abban yace masa bari ya samo lamban da za a samemu dashi a can.
Abba ya shigo gida ranshi a bace yana wa innan mu fada kan zuwana wuri mijina bai sani ba gashi yanzu ya bugo waya yana tambayana.
Itama inna hankalin ta ya tashi nan ta buga waya sai dai wayan baya shiga hankalin inna ya tashi take tambayan sadiya ko ba service a garin tace sun baro services a can lafiya kafin su dawo.
Hankalin innan mu ya kara tashi gashi yarta di ba waya ke gareta ba balle su kira nata layin suji ko lafiya nake.
Har dare inna na kokarin kiran layina shiru babu layin hankalinta kuma yaki kwanci da hakan har sadiya ta dawo daga zari,a ta samesu a hakana itama ta gwada layin nawa bai shiga.
Sai cewa ake layin yana kashe idan sun kira sadiya dake gefe tace aiko anty mu bata kashe wayan ta haka idan dai ba wani matsala ne ya faru da wayan ba.
Har washe gari basu sameni ba haka yasa sa,adatu fita ta samo layin wata yar garin data sani ta kira akan taje gidan ta duba in lafiya nake ta fada min na kunna wayana ya jafar nason magana dani.
Basu akace wa kawar babu wata bakuwa a gidan wace suka zo duk sun wuce koda ta kira sa,adatu dare yayi lokacin don haka saidaf safe sa,adatu ta sameta take fadin abinda aka fada mata.
Sai hankalin su ya tashi sosai nan inna hankalin ta ya kawo cewa akwai matsala ta bangarena ke nan lalai wanan abin da nayi yana da alaka da zance da yaya jafar di nan hankalin ta ya kara tashi sosai.
Sai gashi ya jafar din ya kara kiran Abban sun gaisa yake tambaya ko na dawo dan layina baya shiga ana fadin layin yana rufe har lokacin.
Mamaki ya kama Abba yake fadin bata kira kaba ke nan danace su sanar mata bayan sunyi sallama ne Abban ya shigo gida ya hau inna da fada ta inda yake shiga banan yake fita ba.
Dole washe gari sa,adatu tayi asubancin zuwa fambeguwa da kanta ta duboni ko taji inda nace dasu zan tafi daga can don hankali su ya kwanta.
Saidai tana zuwa din kamar ta karo tashin hankalime gare su don ta dawo da labarin ba wanda yasan inda na tafi sai innan mu ta fashe da kuka.
Dole ba yadda za ayi aka fadawa Abban mu komai shima nan hankalin shi ya tashi ya fara fada inna cewa komai ya sameni itace don itace ta kirkiro da surfan aje gun yan uwanta ai.
Daba haka ba ai da ina gida asirin su rufe yanzun me zasu fadawa mijina cewa nayi tafiya na bata ba a san inda nake ba ko me ?
Daga shi sai inna da yan uwana ake kumbiya kumbiyan maganan a tsakanin su har karshe dai saida Asabe ta san da zancen itama hankalin ta ya tashi sosai.
Inna taje gidan malam tana kuka take zayana masa komai malam din yai murmushi tare da fadin nasan za a rina don yarku na cikin wani hali wallahi.
Sai dai kada ku damu sosai za a san abin da akayi ta dawo gida lafiya kada abin ya kai ko ina amma hankalin ta ne ya tashi sosai da mijin nata har mahaifiyar shi.
Nan dai malam di yace za ayi rokon Allah duk inda na shige na dawo gida lafiya ba tare da wani abu ya faru dani ba insha Allahu.
Abba kan ya saka inna a gaba har ya kai inna itama ta hasa ta mayar mashi da amsa a cikin zafin rai ta fadin shin malam kana ganin laifina a nan.
Kai tunda yarka tazo garin nan ka taba zama da ita ta fada ma halin da take ciki a gidan auren ta daudai da rana daya malam a gidan nan.
Abba yace owwoo yanzu kika fito mi a mutum sak watau duk abinda yar nan tayi da sanin kine Asiya boye min kawai kikeyi dama ?
Tace wallahi bada sanina bane malam don babu uwar da zata koyawa yarta mugun abu haka tabar dakin mijin ta da mutane suke hangen tana a cikin daula ne ita.
Saidai mu iyayyen mun kayi sakaci wani lokaci har abu ya girma ba tare da mun maida hankalin da halin da yaro ke ciki ba sai abu ya lalace.
Shike nan Asiya kin sai komai dai da yarinyar nan tayi ke nan to wallahi bari kuji baku isa ku kunyatani ba a idon jama,a.
Duk inda taje koma wani iya shege take ji dashi a zuciyar ta zata dawo nan ta sameni sai ta koma gidan mijin ta bata mai dani mutumin banza a garin nan ta tona min asiri ko watau kunga Allah ya rufa min asiri ta tsatson ku ?
Kaiya kaiyya ina ta fada har sau biyu kafin tace shine matsalan malam bahaushe wallahi kaji na fada ma yarinya tana cikin matsala watau kai ko a jikin ka malam don kawai dan abim duniyan da kake samu daga wanan mutumin ko ?
Ya rufe maka ido ba zaka dawo da hankalin ka wuri daya ka natsu kaji ko meye matsalan yar taka ba da miji nata kadai kawai burin ka ta dawo ta koma koma meye ta karata can dashi ko ?
To ban yarda yata ta halaka a haka ba don kawai kana kwasayin abin duniya kai yanzu idanuwan ka sun rufe ba zaka nemawa yarka manufa ba.
Nan Abba shima ya taso kamar zai daki inna a ranan kan wanan maganan har yana fadin idan ta kuskura ta kashe aure na da ya jafar a bakin auren su ke nan itama.
Ran inna ya baci matuka tana mayar mashi da martani har yakai saida su sa,adatu suka ja inna zuwa daki sannan Abban ya fita .
A waje ya hadu da lantana dake labe tana saurare ta rasa gane zancen da akeyi da farko amma ta dan tsuntsunci wasu daga cikin maganan inda ta fahinci akwai matsala ke nan ga aurena dama tana neman sanadin da zata katse duka jin dadin daulan data hangomu a cikin sa ni da innan mu da kowa a dakin mu da wanan bakin cikin take kwana take tashi dashi a kullun.
Abban mu yana fita gidan malam ya nufa don ya kai karan inna a can ya sa ai masa iso a wurin malam din nan ya samu wuri a waje ya tsaya yana cika yana batsewa har malam din ya fito ya sameshi a wurin.
Bayan sun gaisa ne ya koro magana ya fadawa malam din komai saida malam din ya gama jin Abba ya nisa tare da fadin.
Bello ka ban mamaki matuka duk da matar ka ta baka haske a cikin zancen auren yarka zuciya ya hana ka gane hakan ?
Malam wani matsala take kira wa yarinyan nam fisabililah duk wanda yaga yar nan yasan tana a cikin daula ai.
Malam ya katse shi da fadin kaiya amma bakai tunane ba bello a nan ka yanzu barin fito maka baro baro ka sani yar ka na cikin matsalan aure a rayuwa ta a gidan mijin ta don haka ka daina wanan kumfan bakin da kake yi a yanzu.
Kamata yayi ka natsu a sama ma yarinya mafita ga rayuwan ta ayi abinda zai kawo zaman lafiya garesu da kwanciyan hankali .
Don babu auren da za ayi tsaon wata daya ko biyu zuwa uku ace babu wani abinda ya taba shiga tsakanin mata da miji irin na aureta a tsakanin har wanan lokacin.
Bale yarka dake neman shekara shidda yanzu a gidan mijin ta ya kake ganin wanan abin zai kasance komai hakkurin yar ka kuwa ?
Jikin Abban mu yayi sanyi wani zufa ya fara keto mai lokaci guda ya kara gyara zama yana cire hulan kanshi.
Kafin ya nisa yana fadin yanzun malam kana ganin hakan yana yuyuwa a tsakanin su kadafa yarinyar nan taiwa mutumin nan sheri kuma kan hakan ?
Malam yace malam Bello ke nan ka godewa Allah daya baka ya kamar wanan yar mai hakkuri da sanin ya kamata do sauran zancen ba zai fadu ba.
Abba yace wa iyazu billahi ban samu zama da ita ba gaskiya malam ban san da wanan zancen ba sam wallahi.
Ya dan dade suna tautanawa da Abban kafin suyi sallama da juna ya nufo gida gwiwan da sanyi sai tunane yake a ransa.
Yana hanya bai karasa gida ba kiran ya j din ya shigo mai haka ya bar wayan har kiran ya katse don ko ya dauka baisan amsan da zai bashi ba a lokacin.

ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH YAN UWA DAFA MUN WUNI LAFIYA ALLAH YA GAFARTA MUNA KURA KUREN MU AMIN.

LITTAFIN KUDINE YAR UWA DON ALLAH IDAN BAKI BIYA BA KADA MU SHIGA HAKKIN JUNA PLEASE, , , ,


Ina kwance ina barci dakin da muke kwana nida kawata nake jin suna kus kus kus da mahaifiyanta a waje.
Matar na fadin yanzu yaya zamuyi da bakuwan nan gashi gidan nan haka muke babu abinda zamu dafa balle ai mata abin karyawa.
Wani irin tausayin sune ya kamani lokaci guda na tuno sanin da nai masu a baya can da irin daulan da suke a cikin sa.
Lafewa nayi kamar ina kan barcin har lokacin sai ta shigo ta zauna a bakin gado bayana tayi zugun tana tunane.
Nima tunanen nake a raina bandai rasa komai a gidan mijina ba na rayuwan duniya sai kwanciyan hankali kawai dana rasa a tare dani.
Wanda ko wace mace ke burin tayi aure ta kai gareshi watau ko wani gida da mutum yake ganin ana rayuwa da nasu kalan kalubalin rayuwa da suke fuskanta.
Sai can na motsa kamar a lokacin na falka daga barcin take fadi daga bayana a sanyaye zainab kin tashi nace eh besty na mun tashi lafiya ya gajiyan dawainiya ?
Tayi dan murmushi tana fadin haba dai wani dawainiya kuma besty kinfi haka a gareni ai kin sani.
Gaakiya ta fada don lokacin gaskiya ta tsare min komai a makarantar da muke zuwa din don ko yanzu ban nuna mata ni din wata tsiya bace saidai ta gane hakan kawai a wurin yanayina.
Mikewa nayi daga saman gadon na kewaya bandaki bayan na fitone na dawo na zauna a bakin gadon.
Jakkar hannu na na dauka daga inda yake aje a kasa na dauko kudi masu yawa a ciki ba tare da nasan ko nawa bane na mikawa Nafisa din ina fadin.
Kiba umma wanan kudin banyi tsaraba da zanzo ba don ina tamtama koba zan sameku har yanzu a gidan nan ba.
Kallon mamaki tayi min tana zatgin ko naji shawaran su da mahaifiyar tane da sukayi na tare da fadin don Allah ki bata kice tayi hakkuri dashi ba yawa.
Haka ta fita cike da mamakina a ranta na irin kudin dana debo mata din ko a ina na samesu haka sai sheki sukeyi a hannun ta.
Uwar ba irin makwadaitan matan nan bane don haka ta taso yar nata a gaba zuwa dakin nata tana fadin ke yar nan wanan kudi haka masu yawa ?
Ta samu na idar da sallah nafila ina addua na dago kai ina fadin wallahi umma ba komai ban samu yo maki tsaraba bane shi yasa.
Umma tace ba zan karbi kudin nan ba don gudun fadawa ga halaka kin gani nan na tsaya a matsayin da Allah ya zaunar dani da diyana a gidan nan.
Don tun lokacin da mahaifin su ya kwanta dama yan uwan shi da abokan aikin shi suka wawashe abinda ya bari sai gidan nan da mota daya muka tsira dashi nake tsorin duk wani abin haram da zai fado a hannun mu.
Lah umma don Allah kada kimin mumunan zato a gareni ina nan a yadda kuka sanni har yanzu ba canzawa nayi ba umma.
Ina da aurena a kaina tunkafin na karasa karatuna igiyan aure ya hau kaina muna kasan chaina ne zaune da mijina tun wanan lokacin .
Sai naga sun kalli juna ina da yarta tana fadin haba nikan na sani zainab don kamanin ki da yanayin ki kawai mutum zai kalla ya gane ke din bata wasa bace yanzu nayi murmushi da jin hakan.
Kafin na dago kai ina fadin umma dan matsala muka samu da mijina nazo nan na karasa ina hawaye.
Subbahanallahi umma ta fada don jin abindana fada na zancen mijina take fadin keko yar nan Allah ya rufa maki asiri da gani me zai kaiki wanan kasadan kuma ?.
Umma ba wanda zai taba gane irin rayuwan da nakeyi a gidan sa nayi haka don kawai ya gyara wasu halaye nasa da ban so.
Mijin naki dan gari nan ne ko wani kasa yake umma ta tambaya na gyada kai alaman eh tare da fadin gidan danayi aiki ne a baya can garin nan.
Nafisa ce ta dafe kirji tana fadin dan minister kike nufin kin aure ba dai last done din nan dake zaune a chaina ba ?
Ta fada tana kallona don son jin amsan da za bata a lokacin na gyada mata kai a hankali alaman eh shi nake nufi.
Sai naga ta wani rungumoni a jikinta tana fadin kawata kice kece mai sa,an da kikayi dace da wanan hadaden guy din da ake maganan sa dama .
Wai ya auri wata yar kauye da ba ajinsa ba shiyasa bukin sa ba wanda yasan anyi a kasan nan don ba kowa yasan da zancen auren sa ba.
Kinga diyata yanzu hankalina ya fara kwanciya da zancen ki bari naje a hada maku abin karyawa na dawo mu zauna mu san abinda ake ciki.
Don ba zai yuyu na barki haka gida ba a san inda kike ba hankalinsu yana a tashe yanzu duk inda suke na rashin sanin inda kike.
Umma daga wurin yayan maman mu na wuto nan amma baki kyauta ba yar nan a
zaton ki ba zasu san baki can gurin ta ba yanzu ?
Nayi shiru tare da dukar da kaina kasa na dan wani lokaci har umman ta gama min fada mai kama da nasiha ta fita daga dakin.
Nafisa tace dani kiyi hakkuri besty kowa hakkuri yake a gidan shi ba zaki gane bane nafisa na fada ina share hawayen dake zuba a idona.
Duk da haka ki godewa Allah daya baki irin mijin da ko wace mace take fatan samu a rayuwan ta nidai jinta nake kawai don na kula su mutane basu san abu cikin duhu sirine ba.
Ka bar mutum inda ka ganshi kawai kada kayi amfani da zahirin shi don baka san zuciyar shi ba can abinda ke cikin rayuwan shi da zai baiyana ba zaka kara kallon shi sau biyu ba.
Har mahaifiyarta ta kawo muna abin karywa tana kan bakin ta kafin ta juye zancen da ban labarin irin halin da suka shiga a baya.da yadda yan uwan su suka cuce su.
Wanka nayi na sauya kayan jikina na saka dogon riga wanan karon tare da yafa gyalen shi a kaina a lokacin Nafisa ta gama gyara dakin nata.
Kwana na biyu a gidan su Nafisa yayin da can gida aka tsanan ta nemana ta ko ina dole ya jafar ya sanda bana gida kuma ba a san inda na nufa ba.
Tambayan dayane kowa keyi duk da ba kowa yasan da zancen batan nawa ba shine dama akwai wani abu a tsakanin mune dashi na rashin zaman lafiya ?
Hjy ya fara nufa da zancen batan nawa daya shigo kasan kaduna ya nufo direct ya samu hjy da zancen take tambayan shi ko akwai wani abu a tsakanin mu na sabani daya hadamu ?
Yace shidai a nasa sani baisan da zancen ba don lafiya muka rabu kuma muna waya dashi lafiya babu komai daya hadamu dashi.
Anya jafari ka canza halin ka kuwa a kan yarinyar nan dana san ku dashi a baya hjy ta jefo mashi tambayan ?
Yace a lokacin da yake cire hular dake saye a kanshi hjy wani haline nawa zainab bata sani ba da zaisa ta bata haka wa mutane.
Duk wani kyautatawan daya dace nasan inawa zainab shi hjy a daidai lokacin ne hjy ta dakatar dashi da fadi kai tsaya kada ka mayar damu mutanen banza.
Nasan halin yarinyar nan haka kawai ba zata saka kafa tabar gida ba haka kai tsaye ba tare da wani abuna faruwa a tsakani ku ba.
Saida ya gogo zufa a goshin shi kafin yace hjy me take so bayan irin kulawan da nake bata a gidana ?
Wai kai kuwa kasan me ake nufi da kalman aure a addinance ko a rayuwan malam bahaushe dole akwai wani abinda kakewa yarinyar nan wanda ba daide ba .
Kasa fadan komai yayi ga hjyn don kalamin ta ya dawo dashi hanya lokaci guda yasa ya fara zargin kansa da kansa kan hakan.
Amma hjy duk da nasan na auri zainab ne don rufin asirina ina iya baki kokari na wurin ganin na kyautata mata ta hanyar inganta rayuwan ta don ci gaban ta kada ta zauna hakana.
Hjy tace bn fahince ka ba dan nan wani irin rufin asirine kake magana a kanshi kullun haka duk zancen auren ka da yarinyar nan ya taso ?
Wanan matsalana ne dani da ita ba lalaine kowa ya san da shi ba ya bata amsa kai tsaye a cikin ko in kula irin na akidan yan turai.
Ta fara tafa hannayen ta wuri daya tana salati kafin tace dole ni nasan da akwai abinda kake boyewa mutane kan auren ka da yarinyar nan tun farko.
Shike nan idan na auri mace don wani bukatana hjy sai jama, a sun gama jin dalilina shine matsalana da kasan nan wallahi ya fada a dan hasale.
Itama hjy a cikin hasala take fadin duk yadda akayi baka da gaskiya akan zancen nan tunda yarinyar nan har hakkurin ta ya kare a kanka,
Hakkurin me hjy illa iyaka tace bana kwana da ita nasan wanan shine damuwan ta a yanzu kawai.
Innalillahi hjy ta fada a cikin rawan jiki tana kallon shi shima din kallon ta yakeyi cikin halin ko in kula kafi cikin karfin hali hjy ta iya budan bakin ta tace dashi.
Ka dauka kawai ka rasa auren ka jafari har in wanan zancen daka fada ya tabbata hakan gaskiyane ?
Kafin ta juya tana fadin kai me ya sameka da har baka kwana da matar ka tana yarinya karama ka barta a hakan.
Kako san nauyin abinda ka aikata a addini gareka ko so kake yar mutane ta fada ga halaka idan hakkurin ta ya kare ?
Hakkurin me hjy zai kare ga zainab karamar yarinya da ita har yaushe wanan abin zai dameta a yanzu don namiji baya tabata ya fada with full comfidence babu wani damuwa a tare dashi.
Hjy bata san lokacin data fashe da kuka ba tana fadin ya tashi ya fita yaje can ya samu uwarshi su san yadda zasu gyara wanan zancen da kansu.
Ganin da gaske hjy keyi yasa ya koma lalashin ta yana fadib bana son mami ta san wanan zancen don kinsan tsakanin su da zainab din dama.
Shine dalilin dayasa na nufo nan wurin ki don ki ban shawaran da zau dace kafin a farga da hakan kowa yasan zancen batan nata don nasan da manufa tayi hakan gareni.
Hjy kan bata tsaya sauraran shi ba sai salatin da take sakewa tana fadin boyar Allah an hada kai dani an cuta maki a cikin rashin sani wallahi.
Don wanan kan ba musulunci a zuciyar shi sam don duk dabi,un kafirai ne a zuciyar ka karara wallahi.
Ya dade zaune a wurin shiru kafin ya mike ya bar falon tsohuwar ba tare da yi mata sallama ranshi a bace kai tsaye kauyen mu ya nufa.
A can ma bai sha da dadi ba a gurin Abba sai dai godiyan shi ga Allah shine iya abinda na fadawa iyayyena ke nan ga yadda ya fahinta.
Hakkuri ya basu akan zai gyara insha Allahu shidai burin shi shine ansan inda nake muyi ido biyu dashi kawai yasan zan amin in koma.
Don bai dauki wanan matsalan dana gabatar a gaban iyayyena wani babban matsala ba can don shi a ganin sa aini mutane zasu zaga kan hakan.
Abuja ya nufa da yamman nan kai tsaye gidan mami ya nufa bai boye mata komai ba game da rashin ganina da ba, a yi ba.
Sai cewa mami tayi idan ma na tafine in tafi mana ba sai a aura mashi wata ba a cikin gata dama ba yarda tayi da kasancewan mu tare ba ita.
Don dan tallaka bai iya samun wuri ba duk gatan da ake muna nida iyayyena bamu gani ba muna neman mu tonawa mutane asiri a gari.
Ya mamud yace asha mami bai kamata ki fadi haka ba wallahi duk hakkurin da yarinyar nan tayi ba a gane mata ba har ake fadin haka gareta.
Hakkuri hakkurin me wani riba ya samu ga auren ta dama banda barnab suna ni hakan yafi mun nono fari wallahi.
Sai ji tayi ya jafar na fadin mami bafa bana son zainab bane ina son matana don haka ki daina fadan wanan kalamin a gareta.
Ana neman hanyar da zata dawo gidana kina kokarin sako wani sabon matsala kuma yanzu ni sam bazan taba yarda da hakan da kike son yi mun ba.
Ka rufa min baki mara hankali kawai me kake tsunta gun wanan yarinyar ne wai a rayuwan ka ?
Mami ba zaki fadi hakan ga zainab ba yarinyar da tayi min tsaye kan duk wani al,amarin da wani ya kasa min har ta samu na daina wasu abubuwan a rayuwana.
Ka daina fadan wanan shirmen jafar a gaba har me zainab zata iya ma wanan bagidajiyar yarinyar mara hankali da wayau.
Mami ke kike ganin hakan ga yarinyar da tayi min tsaye da addua ga komai har na daina harkan da kowa yake tsana na dashi.
Idan baki sani ba ki sani mami zainab ce sillar daina shangiya da har kan guy da nakeyi a baya.
Wani irin zabura mami tayi tana kallon shi tarre da dafe kirjin ta tana fadin wai dama da gaskiya kana wanan harkan jafar.
Ya kalli mahaifiyar nasa ido da ido yace kwarai kuwa mami kuma a haka yarinyar nan ta zauna dani hakana.
Wa kike tunanen zan zauna da ita tsawon wanan shekarun ina kallon ta ba tare da duniya taji mu ba.
Don haka ni bani da kamar zainab a rayuwana banda wance tafi min ita mutunci a idona so ki daina bata yarinyar mutane haka idan ma laifine ni nayi ba ita ba kuma tayi hakkuri ta zauna dani hakana.
Shot up mami ta fada a hasale cikin wani irin tsawa da bata taba yiwa kowa ba a cikin su.
Don baka da kunya jafar kake fadan wanan maganan haka kai tsaye kasan girman laifin da kayi a wurin Allah ?
Hukuncin kissa ne fa ya hau a kan ka har zaka zauna kana fadawa mutane wanan maganan haka ?
Kai idan ka san ciwon kanka ashe har zaka tsaya kana wanan maganan a yanzu ita yarinyar da kake magana a kanta kana wani neman kareta a gaban mu ai kwadiyine ya zaunar da ita har tsawon wanan shekarun bata damu ba sai yanzu ?
Don kudi ya rufe mata ido ita da iyayyen nata yasa basu ga laifin ka a farko sai yanzu zata zo tana wani neman mafita a yanzu ?
Mami laifine don ta zauna dani a hakan ashe haka din laifine gareta a wurin ki na dauka ai babu kamar zainab a gurin ki yanzu.
Yarinyar data kwatoni a cikin halakan dake kanki kika kasa kwatoni a cikin sa sai ido da aka zuba min ina kara shiga cikin halaka.
Badon zainab ba da ban san iya inda rayuwa zai fada ga halaka ba da ke kanki ba zaki so a kirani da dan ki ba mami.
Saidai haduwana da zainab shiya kawo min sauyawan rayuwa har na koma kamar ko wani mutum a yau.
Daga tsaye yake wanan maganan sai da yayi tako kamar biyu ya tsaya yana fadin na fada maki a nemo man matana idan ba haka ba nima ku rasani kamar yadda zainab ta bata.
Daga hakan ya sa kai ya fita kowa ya bishi da ido kafin mami ta fashe da wani irin kukan bakin ciki daya tokare mata makoshi a lokacin.
Suma yan uwan nasa kukan sukeyi don gaba daya ya basu mamaki ya kuma zarewa sanin da sukai mai a baya.
Yau ya koma kamar ba jafar di da suka sani ba idanuwan shi ga maganganun daya fada masu tsauri da nauyin fada shiko baiji nauyi ko kunyan idanuwan su ba yada ya fita abin shi.
Gidan shi ya nufa kai tsaye duk da darene bai hana ya samu yan gidan wasu na aiyukan su ba a lokacin.
Gaidashi sukeyi yana amsawa da kyat har ya shige part din shi kowa ya ganshi a lokacin yasan yana cikin bacin rai sosai.
Wanka ya fada ya dade tsaye a bayin ruwa kawai ke sauka masa a jiki ya dafa hannun shi a bango ba abinda yakeyi sai aikin tunane.
A iya tunanen shi ya rasa me yayiwa zainab din ta dauki wanan matakin a garesu don bai taba zaton hakan ba a yanzu a wurin ta.
Tayi hakkuri ta zauna dashima a lokacin da yake cikin ganuwan shakiyancin shi balle yanzu da bata ganin komai a tare dashi.
Menene bukatan zainab a yanzune ya tambayi kansa can ya runtse idanun shi na dan lokaci kafin ya kai hannun shi ya shafo gaban shi yaji a yadda yake mai duk tsawon watanin nan.
Wani iska ya furzu a bakin shi kafin yayi wani tunane ya zabura da sauri ya kai hannun shi ya kashe ruwan dake zuba mai a jikin sa yana sauke ajiyan zuciya.
Ya fito ya shirya a gurguje ya nufo falon shi ya samu fadila na kwashe kayan abincin da suka jera mai don tasan tunda yakai wanan lokacin ba zai ci abincin ba.
Sam bata san da fitowan shi ba a lokacin sai muryan shi da taji a bayan ta yana fadin Fadila wani shiri kukayi da zainab akan tafiyan ta ?
A dan tsorace fadila ta juyo tana rawan jiki tare da fadin sir ban fahince ka ba yayi mata wani irin kallo mai kama da tsana kafin yace me kika fada mata ranan a kaina.
Jikin fadila ya fara rawa ta mayar da kayan data dauka a hannu ta tana fadin sir ban fada mata komai ba believe me ba muyi wani magana a kan ka ba tunda tazo.
Kin tabbatar baki fada mata zancen da kikaji ranan munayi da dan uwana ba a falon nan ya tambaya cikin tsare ta da idanun shi.
Da sauri fadilan tace believe me ban fada mata komai a kan wanan zancen ta yaya ma zan fada mata wanan maganan idan har ina kaunan ta da farin ciki ?
Idan har na binciko na gane da hannun ki a cikin tafiyan nan nata duk hukuncin dana yanke a kanki ke kika jawa kan ki kowa kike kuwa bai dameni ba don kina yar sandan ciki.
Wani irin faduwan gabane ya ziyarci zuciyar fadila lokaci guda hankalinta yai mungun tashi ya juya ya barta a wurin tsaye cikin farga ba da tsoron .
Na sanin ashe ita din yar sandace yasan aikin da takeyi a gidan sa ke nan amma kuma bai koreta ba ga hakan.
Haka yasa ta kai zaune saman kujeran dinning din tana tunane to idan shi ya sani ita zainab fa tasan da wanan zancen ke nan ko me ?

ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH YAN UWA MUSULMAI DA FATAN MUN WUNI LAFIYA ALLAH YASA AMIN .
UBANGIJI ALLAH YA KARAWA ANNABI DARAJA DA DAUKAKA A DUNIYA ALLAHUMA AMIN.

YAR UWA LITTAFIN KUDINE WANAN DON ALLAH KI BIYA KAFIN KI KARANTA DON GUDUN FADAWA HAKKIN WANI NAGODE ALLAH YA BAMU IKON KIYAYYEWA AMIN.


Na fatar da komai na jakkan hannuna ina nema brosh dina sabo gurin hakane na manta da kayan saman gado ciki har da wayana.
Wandatun zuwa kaduna gidan su Nafisa ban taba fitar dashi wani ya gani ba sai wanan ranan dana fitar din garin sauri in shiga bayi kuma na manta dasu saman gadon.
Nafisa ta shigo dakin dauke da abin karyawan data hada muna don yau umma ta tashi bata ji dadin jikin ta hawan jinin ta ya tashi mata.
Shine dalilin zuwan nafisa kitchen tunda safe ta shirya muna abin karyawa don yayanta dake zaune a yola can kauyen su tun bayan rasuwan mahaifin su da abubuwa suka sake ya koma can yana dan buga buga irin na tallaka yana samo masu abinda zasuci a gidan.
Ganin wayana saman gado ta dauka tana mamakin irin girman sa bayan ta gama dubawane ta ga dacewan ta saka min shi a caji.
Ta dauka ta saka bata gane kan wayan ba don haka ta kunna ta gani ko ya kawo ya dauki cajin a daidai wanan lokacin kuma kiran sa,adatu dake faman gwada layina a koda yaushe kiranta ya shigo a lokacin.
Ina ban daki naji kukan wayana ai a zabure na dago da sauri na watsa ruwa na fito daga ban dakin ina mamaki.
Itama Nafisan ta tsorata da hakan don bata taba zaton kira zai shigo min a wanan lokacin ba haka.
Kallon juna mukayi lokacin dana fito bayin da mamaki karara a fuskana a cikin daburcewa take fadin waina saka maki cajine kada ya dauke sai kuma ga kira ya shigo lokaci guda.
Ai da kin sani baki kunna ba da zaki saka min canjin na fada ina karasowa inda wayan ke ringing don ganin wanda ke kirana a lokacin.
Sunan Sa,adatu nagani a wayan naki dauka har kiran ya katse ina kokarin kashewa ne kira ya jafar ya shigo na kashe wayan.
Shikan a nasa bangaren kiran ya nuna mai a kaduna nake don haka ya sake wani irin murmushi a fuskan shi lokaci guda .
Saidai tambayan kanshi yayi kaduna ina nake zaune ke nan ya tambayi kan shi lokaci guda don a iya sanin sa bai taba jin nace ina da wasu a garin kaduna ba ai.
Nan gidan anty Sa,ansu ya fado mashi a rai don idan ba zai manta ba ai na taba fada mai itace ta kawoni gidan mami aiki daga Anchau.
Kai ina ya fada anya a sanin da yaiwa gwaggo sa, a zata iya ajeni a gidan ta ba tare data tuntubi gida ba.
Don shi bala,in ganin mutuncin anty sa, a yake gani ko yaushe don tun suna kanana ya fahinci hakan matar tana son su tsakani da Allah sabanin sauran yan uwan su da akan samu tsegumi a tsakanin su kullun.
Wani tunane yayi ya danna kiran ya mamud yake tambayan shi ko yana da numban gwaggo sa, asu dake kaduna.
Ya mamud yake fadin wallahi baida layin ta sai dai idan zai nema mashine ya turo mai yace hakan yayi kyau ya kashe waya don baison wani dogon magana a yanzu.
Ya mamud ya kira wani dan uwan su a kaduna shine ya turo masu layin gwaggo sa,a din a lokacin sai dai abinka da yan uwan zamani shi maishi yana tunanen wani alheri zasuyiwa anty sa,a din a lokacin.
Can gidan mu kuma ihu sa,adatu tayi tana fadi wallahi inna layin yayan mu ya shiga saidai bata dauka ba har ya katse.
Inna tace ta sake gwadawa amma wayan yana a kashe baya shiga kuma yanzu don dole suka aje wayan suna tunanen ina na shiga haka na boye ne.
Yayin da anty Fadila ita kuma ta tsure sosai ga abinda ya fada mata din ta kwana tana tunane tana fadin ashe mutanen nan sun san me nakeyi a gidan su amma basu taba nuna min hakan ba.
Ko wanan ne dalilin da yasa yanzu bana gane komai a wurin zainab din ga baki daya ta sauya min ba kamar da da take fada min komai ba.
Wai to ta yaya har haka ya farune bayi sakacin da suka fahinci ko ni eaye mai kuma nazo yi a gida a matsayin yar aiki yanzu ?
Ban nunaww Nafisa komai a fili sai dai a zuciyana gaskiya ban so hakan ba don sanin waye ya jafar game da computer da nayi zai iya tracing dina a haka har ya gano inda nake.
Ina zaune a dakin bayan fitan nafisa sai ga umma da bata jin dadi ta shigo dakin daganin yanayin ta kasan a cikin karfin hali ta kawo kanta dakin na nafisa.
Ina ganin ta na dan daga ina sannu umma ya karfin jikin ko zamu tafi asibitin ne dai na fada a cikin kulawa gareta.
Murmushi umna ta dan sake tana kawai zaune gefen gado inda nake muna mata sannu kafin tace dani ai ko haka nagode yar nan.
Yanzu yayan ku ya shigo min da magani masu kyau da tsada wai zainab ce ta bada kudi ya sayo min su na gode Allah ya karawa arziki albarka .
Nace amin a kasan makoshina take fadin ai na dade ban sha irin su ba don rashin kudi gashi yanzu har Allah ya taimakeni na samu na mike ciwon bai kaini kwance ba.
Nake fadin ayyah sannu umma Allah dai ya baki lafiya tace amin kamin dan shiru ya biyo dakin can ta dago kai tana fadin.
Zainab dama gurin ki nazo yanzu kawarki ta sameni a daki tana fada mi karanbanin da tayi maki ai.
Kallom inda nafisan take tsaye a cikin damuwa nayi kafin nace umma me kuma ta fada maki tayi min ina kallon Nafisa din ido cikim ido.
Nafisan ke fadin wallahi banji dadin hakan bane besty shiyasa naje na fadawa umma ta baki hakkuri.
Kai haba besty kika tayar da umma kan wanan maganan shiriritan tana fama da kanta haka don Allah ki daina hakan mana.
Bashi ba zainab wallahi Allah yaga niyata dama naso nace dake ki kira mahaifiyar ki don ta san kina nan wuri mu ko hankalita zai kwanta ga hakan.
Da sauri na dago kai na kalli gefen da umma din take zaune tace eh zainab mahaifiya ba wasa bace.
Yanzu Allah kadai yasan irin yadda take ji a ranta na rashin ganin ki din nan kwana biyu da ba,a yi ba ga kuma mahaifin ku nasan ba zai kyaleta ba kan hakan don su maza a kullun mune da laifi akan yayan mu ai.
Duk da bansan me ya hadaki da mijin ki ba zainab alama dai kuma ya nuna min krce da gaskiya don haka ki natsu kiyi tunanen irin halin da mahaifiyar ki da yan uwan ki zasu shiga na rashin sanin inda kike a yanzu.
Hawayene ya fara zuba min a idanuwana lokaci guda don jin me umma din ta fada nima kaina da wanan tunanen nake kwana nake tashi a kullun tunda na barsu din.
Nasan inna zata shiga wani hali kan hakan haka kuma Abba zai dauki laifi ya dorawa inna duka ita daya alhali bata san da wanan zancen ba.
Da kyar na iya budan bakina don hawayen dayai min yawa nace Umma idan ba haka nayi ba ba zasu daukan man mataki ga halinda nake ciki ba ko kadan umma.
Tace na sani zainab nasan halin maza sai su cutama su koma baya suna kyautatawa iyayyen ka ko wani na tare dakai na kut da kut don kawai su batar da laifin su gareshi.
Don haka ba tare da dogon bincike ba zainab kiyi hakkuri ki ban lamban mahaifiyar ki nida kaina zan kira i mata bayanin kina hannuna don haka ta kwwntar da hankalinta ta.
Jin hakan na dago kaina da idanuwa da suke tab da hawaye na kalli umma din mace kamila natsatsa ta kada min kai alaman inyi hakkuri don Allah in karbi tayin ta din nace shike nan umma.
Kallon inda wayan nawa nayi kafin in kai gareshi har nafisa ta matso tana daukan wayan ta miko min na karba layin umma din na nema na mikawa nafisa wayan don ba zan iya karanto mata ba a lokacin.
Kira daya sai gashi inna ta dauki wayan kamar tana jirace da kiran dama ta dauka da sallama umma ta karba kamar sun san juna dama sai bayan gama gausuwan ne umma ke fadin nasan dai baki san wace ke magana ba inna ta amsa da eh ko altine ce ta damau, ?
Umma tace lala ba ita bace bakuwace na kiraki ne a kan yarki dake hannu na a yanzu da sauri umma tace gunki take boyar Allah ?
Tace eh nan tazo wurina sanadiyar diyata da sukai karatu tare shekarun baya daya wuce na kirane don hankalinki ya kwanta tana nan tare damu zaune.
Cikin sanyin murya irin na inna take fadin hankali kan ya tashi matuka don kowa na ganin nasan inda take zaune boyewa kawai nayi.
Musanman mahaifin du da yake ganin da sanina ta bar gida nasan komai kan matakin data dauka din saboda Allah hjy za ace .
Yau shekaru shidda da yan kai da auren yarinyar nan haka take zaune a gidan mutumin nan ashe kamar photo ?
Ba wani abinda ya taba shiga tsakanin su na aure har wanan lokacin kokai nan da girman ka ai ba zaka yarda da hakan ba ko ?
Subbahanallahi innalillahibwa inna alaihin raji,un umma ke fadi a bakin ta tana fadin ai kinga kuwa bata fada muna komai ba wallahi tunda tazo garin nan nima ban matsa mata kan sai ta fada min ba din.
Jam ko a shari,ance kan ai ba aure matukar ba an gyara ba gaskiya don hakkurin diya mace a wanan kalilan ne duk da a zahiri mun fisu hakkurin hakan.
Nan dai inna ta koro mata da zancen komai kamar dama jira take ta samu wani wanda zata amayewa damuntane kan hakan.
Da gani kuma ranta abace yake matuka sun kwasa da Abban mu a kaina dama kuma hakan nake gudu na gudu daga gaban su don kaucewa fitina ashe ban fita ba.
Karshe dai umma ta mika min wayan don inna taji muryana ko zataji sanyi a ranta na karbi wayan a hannun umma muka fara gaisawa da inna din a sanyayye.
Tace in kwantar da hankalina tunda gidan mutunci nake yanzu kuma hankalinsu su ya kwanta tunda sun san inda nake ai.
Har zuwa lokacin da za,a zauna da mijina idan ya bada hujjan shi na dalilin hakan a tsakani mu don malam yace zasu zauna dashi .
Kamar inna na gani a lokacin na gyada kai ina fadin ni inna bana son a wani zauna kawai malam ya raba aure na dashi kwata kwata na tsane shi inna.
Da sauri umma ta karbi wayan tana fadin ki kyaleta don Allah zaki kwantar da hankali ki nuna kema har yanzu baki san inda takw ba .
Inna tayi mata godiya tana karawa suka kashe wayan umma ta kalloni tana fadin yar nan haka kikai fama a gidan wanan mutumin ?
Na dukar da kaina kasa take fadin dole dayan biyu ko kece kikai masa wani abu ko kuma baida lafiya a jikin sa idan bashi ba ta yaya namiji zai zauna da mace kamar ki yana kallonta haka.
A raina nace umma kudai baku san komai ba ke nan a daije ga hakan ga hujjan dana kawo maku din.
Gaba daya ya rikice da neman na don sunyi waya da anty sa,a da yaya mamud ya samo layinta ya kawo mai ya nuna ko mun iso wurin ta don munce zamu zo idan mun shigo kaduna ?
Take fadin ayyah ashe mun shigone wallahi bata ji ba ko ga wani cewa munzo nigeria ai suka dai gaisa ya kashe wayan bayan ya fahinci ba can nake ba.
Mamaki ya kara kamashi lokaci guda ya gyara zama ta hanyar mimike kafafun shi ya dora hannun shi saman goshin shi yana murza a hankali.
Ya mamud dake gefen shi zaune ne ke fadin bata je can ba ke nan ko ya bude idanuwan shi da sukai masa ja jajajir ya sauke ga dan uwan nasa yana fadin wai bata can .
Amma dai tabbas nasan tana cikin garin kaduna tunda wayana ya nuna min hakan nasan tana garin comfarm.
Jafar duk laifin kane tun farko har hakan ya faru ya mamud yana kallon dan uwan nasa tare da gyara zaman shi yaci gaba da fadin.
A iya sani da kai ban taba zaton wanan halaiyar a gareka ba sai gashi daga sama mun tsunceka a cikin wanan harkan why jafar why zaka zabi wanan mumunan akidar ?
Hummh ya fada a yadda yaken zaune bai cire hannun shi a saman goshin ba yadda yaken da farko sai can ya cire ya kalli dan uwan nasa da idanuwan shi da suka kada suka kara rinewa ya sauke kan mamud din.
Mamud nima bansan dalilin fadawa wanan harkan ba gaskiya na dai tashi na tsunci kaina a cikin sa dumu dumu nima ba zance ma ga dalilin hakan ba yanzu.
Nayi iya kokarina don kaucewa hakan sai dai Allah bai karba min ba har hakan yakai ga yanzu da kowa yake kokarin sani .
Don nasan dole zainab zata fadawa iyayayyen ta wanan maganan tunda yanzu rabuwa take son yi dani ta ko wani hanya ?
Kai sam zainab ba atayi hakan ba da zatati aida ta fada muna muna tun zuwan mu chaina Jamal daine ya fara fada muna hakan koshi sai da mami ta matsa mai ne ya fada min ni kadai ba tare da mami a wurin ba.
Jamal ke nan dan uwana ya gaji ya fada ma balle zainab da aure ne ya hadani da ita don me kake tunanen ba zata fadawa iyayyen ta halaiyana ba ita ?
Kai ya mamud din ya girgiza yace kai ai ka godewa Allah daya taimakeka ya hadaka da mace kamar zainab don da ace watace ko irin su Nuriya da tuni ta dade da tona min asiri duk da bamu kasan nan kuwa.
A wanan lokacin ya mamud ya farga da wani yanayi da dan uwan nasa ya fara shiga a lokacin don bai farga da wuri ba da hakan.
Sunan shi ya fara kira a hankali kafin wani tari ya fara sarkeshi yana dafe kirjin shi da yake jin yai masa nauyi da tauri lokaci daya.
Da sauri ya mamud din ya mike zuwa wurin jafar din tare da riko dan uwan nasa yana kiran sunan shi hankali tashe da kyat ya samu ya dago kai ya amsa mashi.
Tun yaushe ne baka da lafiya haka ya tambaye shi dan murmushi ya sake a fuskan shi na karfin hali kafin ya kalli mamud din yana fadin kada ka damu da wanan.
Da zainab tana nan itace idan ya taso min takan ban wani magani data amsa min a can.
Wani iri mamud din yaji a ranshi da dan uwan nasa yai wanan maganan ya mike tsaye yana fadin abinda nake fadawa mami ke nan game da yarinyar nan tabi bayan ta asan abinda ake ciki tana fadin wai dama can bata dace dakai ba.
Gara ku rabu ta nema maka wata can daban daidai da kai mami ta manta cewa kowa na fada mata zainab alherice a gareka amma ta kasa fahintar hakan don kawai tana ganin girma da kimar iyayye ta baikai bane ta aure ka kome oho ?
Yau ma akan case din ku saida suka kwasa da jamal don kawai ya fada mata gaskiya kan hakan ta haushi da fada sai da ya fita ya kyaleta.
Dan murmushi ya sake kafin ya kai kallon shi ga wayan dake kiran layin shi har kiran ya katse bai daga ba ya mamud dai ido ya zuba mai a lokacin.
Kafin yace dashi shi zai koma office anjima idan ya tashi zai lekoshi yaji ya ake ciki sai jafar din yace dashi ba sai ka dawo ba ka huta kawai.
Yana fadan hakan ya mayar da idanun shi ya lumshe yana jin takon tafiyan dan uwan nasa har ya fita daga gidan.
Kiran wayan ne ya kara shigo mashi ya bude ido yana kallon bakom lamban dake kiran shi din kafin ya daga da sallama a cikin harshen turanci.
Sai yaji anyi mai sallama a musulunce ji muryan maishi ba yaro bane dadditijo ne kuma mai kamala shima ya amsa mai a mutunce.
Malam yace nasan ba lalai bane ka sanni amma zaka iya jin sunana a bakin matar ka zainab ?
Jin ya ambaci zainab din yasa ya gyara zaman shi da kyau yana saurare dattijon a lokacin malam yaci gaba da fadin.
Kan zancen matar ja nake son ka samu lokaci kazo mu zauna a kai kafin mutane su farga da halin da ake ciki tsakani ku.
Cikin karfin hali jafar din yace saidai malam ban fahinci ko dawa nake magana ba a yanzu a takaice kai waye gun matata ?
Dan murmushi malam yayi kafin yace da jafar din nasan haka nine kakar matarka zainab mijin maizube data zauna a wurin ku a farkon auren ku nan Abuja.
Ga mamakin malam din sai yaji ya gyara murya a cikin ladabi yana fadin a malam ne na gane yanzu ya kwana biyu ya jama, a ?
Malam ya amsa da fadin alhamdullahi tare da katse zancen da fadin idan ka samu lokaci ka shigo akwai zancen da nake son muyi ni da kai idan kazo.
Yayi wa jafar din sallama ba tare da bashi daman fadin komai gareshi ba kuma shima sallaman ya mayar mai suka kashe wayan .
Wayan yabi da kallo yana tunane me malam keson su tatauna a tsakanin su shi da shi ko zainab din dai ta fada masu komai ne yake son ganin shi ke nan ?
Ko kuma duk wanan neman da ake mata dama tana gidan malam ne iyayyen ta basu dan da hakan ba ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAWAalliya:
ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI DA FATAN MUN WUNI LAFIYA ALLAH YA SADA MU DA ALHERIN SA AMIN
LITTAFIN KUDINE KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DA AMINCI YAFI.

Irin samakon da yayi ne ya ba malam mamaki matuka har ya kasa boye hakan a zuciyan shi yakewa ya jafar din ba, daya fito yana fadin.
Kai ka dauka zan sace ma matar takane kayo min wanan samakon hakan a gida ya fada yana dan dariya tare da mikawa jafar din hannu kafin ya juya wurin kanwata da ta rako ya jafar din gidan malam din yana fadin kece yar rakiya ko kika nuna mai gidana.
A cikin dan kunya ya jafar yake fadin malam an tashi lafiya ya kwanan iyali ya amsa da lafiya tare da fadin mu karasa ciki ko malam jafar ya fada yana nuna mai kofan shiga zauren nasa kai tsaye.
Bayan sun zauna suka kara gaisuwa da malam din kafin malam ya fara magana yana fadin ka kyauta da ka amsa kirana da gagawa don mu samu mukai karshen zancen ba tare da kowa yasan meke gudana ba a tsakanin ku.
Don ko yanzu an fara sake zancen a gari saidai wasu basu yarda da hakan ba gaskiya kaga ko a kai karshen abin zai fi.
Gaskiyane malam ya fada cikin dan kunya da dukar da kanshi kasa malam yaci gaba da fadin gaskiya sam baji dadin hakan daya kasance a tsakanin ku ba tun farko.
Ya sake dukar da kanshi kasa don kunya da nauyin malam din da yake ji har cikin ranshi a lokacin.
Nasan fashewan wanan zancen yanzu a gare ka babban nauyi ne da kunya ace dan musulmi ke aikata wanan sabon a doron kasa hakan .
Dan adam yakan manta da irin azaban da Allah ya tahadar mashi tun a nan duniya kafin aje ga lahira ya koma a makomar da Allah ya tanadar masa.
Duk wani jin dadi sabo da bawa zai aikata a cikin sabon shi na dan lokaci ne don yanzu duniyan rayuwan cikin sa kalilan ne.
Ka godewa Allah daya hadaka da wanan yarinyar mai zuciya irin na manya da sanin ya kamata da dogaro ga ubangiji.
Yau da ace watace ba zainab bace na tabbatar da wanan rikicin sai yafi hakan a gareku ya dan dago kai a lokacin tare da fadin gaskiyane malam.
Nasan zainab yarinyace mai karanci da kara agareni wanan yasa nake jin ba zan iya rabuwa da duk wani abinda zatai min ba na tozarci.
Baza a kai ga hakan ba da yardan Allah don yanzu haka zainab tasan abinda kai da iyayyen ka baku sani ba a zancen nan naku.
Ya dago kai da sauri ya kallo malam, malam din yace eh haka zancen yake don abinda bincike na ya nuna min mun tatauna shi da ita nan ranan .
A yadda nasan zainab da tausayi da karamci a rayuwan ta zata duba ma kan hakan sai dai da yake shi dan Adam ajizine ba a yanke mai hukunci ga abinda zuciyar shi ke nasa mai don haka ban san dalilin zainab na aikata hakan da tayi ba a yanzu.
A sanina nasan zainab tayi hakan ne bisa wani dalili nata da ba lalaine mu iyayyenta mu san hakan ba tunda har ta iya boye ma iyayyen ta sirin dake tsakanin ka da ita don har gobe basu san mai kake aikatawa yarsu ba na asha.
Ya dago kai ya kalli malam malam din yace kwarai ko wanan hujan da suka rike ninan na fada masu hakan don kawai a fitar da wani tuhuma ko zargi a tsakanin ku.
Kuma na tabbatar da zainab ba zata taba fada masu sirin nan ba don kawai kare mutuncin ka a idanun su.
Dukar da kanshi yayi yana hawaye don jin abinda malam din ya fada kafin malam din yace na kirakane nan kafin kazo da iyayyen ka a zauna ya kamata in ganka mu zauna a tsara komai a mutunce.
Malam dai bai boye mai ba duk yadda mukayi dashi ya fadawa jafar din komai har makarin daya ba zainab ta bashi sai daya fada mai.
Cikin mamaki jafar din ke tambaya malam kana ganin jifana wani yayi da wanan mumunan akidar yace kwarai kuwa.
Bakai akaso ya shafa ba mahaifinka akai wa da farko sai abin ya dawo gareka kai din anyima naka don duk inda zasu su duba kan iyalin shi farko sunan kane zai haska.
Wanan dalilin yasa suka juyo a kanka suka saki kowa da komai a cikin iyayyen ka don ganin taurarin ka sunfi na iyayyen naka haskawa nan gaba.
Allah ya kawo saukin abin ta sanadiyar zainab data dauki mataki akan ka da wuri wanda ba kowa ne zai iya tsayawa yai maka hakan ba kai tsaye.
Yanzu duk mu manta da wana

n mafita shine abin nema a gareka ya zama dole gareka ka tsaya kasha magani sosai ka dawo mutum kamar kowa.
Tare da kuma neman tsari don kasan mai neman naka na gidan kune ba fasa jifan ka zasu yi ba tunda sun dauki niyar hakan a zuciyar su sai sunga bayan iyalin ku kaf.
Sun dauki lokaci suna tataunawa da malam din kan matsalan nasa da kuma irin matakin da zai dauka don zaman mu ya dore dashi nan gaba.
Nan dai yayiwa malam sallama tare da ajemai alheri amma malam din yaki amsa ko daya daga cikin abinda ya bashi din.
Karshe jafar din yace ai masa sadaka dashi a inda ya dace da niyar Allah ya rabashi da abinda ke damun sa a rayuwan shi.
Nan dai ya kama hanyar airport bai ko leka gidan mami din ba don gaba daya yaji gidan nasu da yan uwan shi sun fita ranshi a lokaci daya.
Sai tunane yake ko mai yaiwa wani da zai masa wanan karen aikin hakan na zancen abokan sa kuma zai yi kokari ya nisanta kanshi dasu in Allah ya yarda.
Ya iso Abuja a gajiye don gaba daya wani irin zazzabine ya rufe shi lokaci guda jan jin wanan maganan da yayi daga bakin malam din mai nauyi haka da kunya.
Dakin shi ya shige ya kwanta ya rufe kanshi kwanan shi biyu bai leko waje ba ya mamud yana zuwa neman shi ace yana ciki bai fito ba .
Ga kuma wayoyin shi duk a rufe lokacin hakan ya tayar da hankalin mamud din zuwa na karshe da yayine ya dawo gida hankali tashi ya samu mami data dau zafi dasu baki daya kan zancen dan uwan nasa don sun mara masa baya kan maganan yana fadawa mami din.
Itama hankalinta ne ya tashi sosai ta mike ba bata lokaci zuwa gidan jafar din da yaranta gaba daya suka tafi hankalinsu a tashi dukan su.
Sunyi dukan kofan da kyar ya taso ya iya budan kofan a lokacin har mami taba da shawaran a balla kofan aga halinda yake ciki a cikin dakin.
Sai gashi ya bude masu da kyar duk ya rame ya fita hayacin sa yayi wani irin baki lokaci guda mami na shiga tana gani yadda dan nata ya koma ta hau fada tana fadin.
Wanan yarinyar ta zama min masifa a rayuwa yanzu a kan wan yar kake kokarin halaka kanka jafar da sauri ya mamud din yace haba mami ba lokacin wanan zancen bane ai .
A samu a ceto rayuwan sa tukun kafin a fadi wani maganan da za, aimai yanzu don yadda ya koma din nan ya kamata yaga likita gaskiya.
No ku barshi ba sai naga likita ba ai na samu sauki sosai ya fada yana gyara zama saman kujeran da ya hau din.
Mami da sai binshi da wani irin kallo takeyi tana mamakin wai jafar ne ke son halaka kan shi akan mace haka ?
Tambayan da jafar din ya jefo matane yasa kowa ya kadu a falon don cewa yayi mami ko zaki tuna ina karami gidan da mukaje akan ban abinci naci har ya zama min matsala a lokacin ?
Abinci a kasan nan ko a can US din ta tambaye shi yace a nan dai mami don ance nayi ciwo sosai a lokacin kan cin wanan abincin da nayi ?
Wanan kuma wani zance ke nan yaushe mami zata iya tuna hakan abinda ya dade dayi ba yanzu ba .
No ni zan tuna jafar ya fada don har ni nayi ciwo a lokacin ai gidan uncle musane mana mahaifin Rufaida daddy yaje damu ranan anty ta bamu abincin daddy bai ci ba yace mu muci tun a gidan mukai ta amai.
Kwarai kuwa ta fada ainayi fada da daddy ku a lokacin kan hakan tunda ba sabawa da irin abincin nan kukayi ba da yasa kukuci.
Ido jafar din ya lumshe na dan lokaci kamar yana tunane kafin ya bude su ya sauke ga yan uwan nasa a daidai lokacin mami ta jefo masa wani tambaya da cewa .
Mai ya faru kake tambaya yanzu babu komai ya bata amsa yana kawar da kanshi gefe daya kowa falon yai shiru yana nasa tunanen a zuciyar shi.
Ita kanta mami abinda ya farune a wanan lokacin yake dawo mata a rai gaban tane ya fadi ta kura dan nata ido a lokacin ne likitan da suka kira don ya duba shi ya shigo dakin.
Bayan yan aune aune yake fadin ya kamata ka huta don jinin ka gab yake da ya hau a wanan lokacin ya kamata ka fitar komai a ranka yanzu don samawa kanka lafiya.
Dan murmushi ya sakewa likitan ba tare daya furta masa komai ba yans gyara kwanciyar da yayi a lokacin.

Kwance nake ringingine ina tunane umma ta shigo dakin ta sameni a hakan take f

adin tun kan ta karaso yata kin fara kewan gida ko ?
Jin hakan da nayi yasa na dago kai da sauri ina dan murmushi tare da fadin kai umma ina dai tuna wani abune daya daure min kai umma.
Nan na bata labarin abinda malam ya fada min ranan na kare da fadin umma shi nake tunane wa zai masa wanan aikin haka a cikin yan uwan nasu ?
Kai duniya ai in fada maki yata haka duniyan nan ta koma yanzu wallahi sam mutane basu da imani a zukatan su yanzu ko kadan.
Wanda bakai tsamanin ko tunanen zai iya cuta maka ba shine zai cutama din don haka ne akeso a kullun mutum ya mayar da hankalinsa sosai kan iyalin shi.
Zakiga mutum ya nuna maki so da kauna kamar ya hadeki a ransa don kauna amma shine zai koma baya yai maka sheri bari ma in maki na mahaukaci yan ciki daya ma a zamani nan sai su cutawa junan su fa.
In har hakan da kakan ki ya fada maki gaskiyane bai kamata yanzu a ce kin bar mijin ki a cikin wanan halin da yake ba a yanzu kinzo nan kin zauna haka zainab .
Saura kiris ki cin ma nasaran ki sai dai kuma shedan ya rudeki yayi maki huduban tsiya da kika bi kina kokarin goge ladan ki kan hakan.
Zainab ba zan cuta dake ba ko kadan yadda na dauki nafisa a gareni yanzu haka nake jin ki a zuciyana.
Don ke din yarinyace mai hankaki da sanin ya kamata don haka hakkuri zakiyi na mayar dake gun iyayyen ki ayita ya kare a tsakanin ku dasu da mijin naki.
Don zama da boyon ki a nan yanzu baida wani fa,ida a gareki zainab hakkuri ya kamata kiyi da mijin ki koda kin koma gida kici gaba da daurewan da kikeyi da farko a kansa kina masa addu,a .
In Allah ya yarda ubangiji ba zai bar wahalan ki ya tafi a banza ba zainab Allah yaga zuciyar ki da niyar ki a kanshi.
Shima kuma din nasan ya sani abu daine idan ka riga daka saba shi a rayuwan ka yana da wuyan bari ko kuma ki masa uzuri wata kila wani lalurane yake damun rayuwan shi har ya kasa kaiwa gareki zainab Allah masani.
Hawaye nake yi duk da nasan gaskiya umma take fada min duk a cikin zancem nata ya zama dole di inyi biyayya gun umma in koma gidan mu gaban iyayyena ayita ta kare din kamar yadda umman tace din.
Bakina na bude da kyar nace umma ba wai wanan zaman da mukeyi dashi bane matsala a gareni sai yadda mahaifiyar shi har yanzu ta kasa gane hakan a nata bangaren .
Take tsanana ni da iyayyena kan zamana da dan nata wanan shi ya saka bana kaunar komawa gidan shi a yanzu.
Ina ruwan ki da ita zainab ina tana gidan ta kina naki sai kun hadu ko kunje zata ganki kuma duk abinda zata fada shi ba zai taba daukan hakan ba tunda yasan hakkurin da kikeyi dashi ai.
Shike nan umma zan koma koda baizo din ba zan nuna masu nidin diyace idan Allah ya yarda da sauri umma ta riko min hannu tana saka min albarka ina amsawa a kasan zuciyana .
Haka nafisa data fita zuwa kasuwa ta dawo ta samemu da umman tana ban baki itama ta zauna sunayi tare a gaskiya nafisa da mahaifiyar ta mutanen arziki ne matuka.
Don yayan tane yayi kokarin neman mota don nasi yana ajiyene a gidan kamar photo kawai baya aikin komai suna kallon shi.
Motar abokin shi ya dauko mukai tafiyan dashi samako mukayi muka bar kaduna dan lokaci kadan muna anchau.
Sai ganin mu akayi kamar daga sama don ba wanda yasan da zuwan mu a wanan ranan.
Wanan dawowan yayiwa innan mu dadi sosai don nan take ta nuna cewa ai dama ba wani wuri na tafi ba gidan yan uwan ta naje ganin su .
Wanda hakan baiwa Lantana da tabi makwabta tana fada masu ai yaji nayi na gudu ba,a san inda na tafi ba .
Sai gashi na dawo gida a cikin salama sai hakan kuma yai mata zafi a ranta har ta kasa boye bacin ranta.
Taro na sosai su umma suka samu daga innan mu da yan uwana inda suke nuna su din yan uwan innane ga mutanen gidan mu din.
A nan suka wuni don umma basu tafi ba sai data gana da Abban mu suka dan tatauna kan matsalan mu Abba yace zasu zauna dashi ai suji dalili hakan daga bakin shi.
Malam kuma godiya yayiwa umma sosai bisa irin kokarin da tayi na dawo dani gida a cikin salama ba tare da rayuka sunkai ga baci ba.
Don Abbana shi kan bai boye yana goyon bayan jafar ba har lokacin don

nunawa yayi na koma naci gaba da hakurin da nakeyi da mijina.
Tunda hakan sirin mune baki daya dani dashi yanzu ai tunda bai rageni da komai ba bayan wanan matsalan kuma yace yana neman maganin hakan don kawo karshen matsalan dake damun shi din.
Kafin su umma su tafine kuma sai ga Abban ya canza shawara ya samu su umma a falon inna yana fadin ni hjy naga tunda yarinyar nan ganin mu dai tazo yi dama .
Ya kamata ta shirya ta koma dakinta kawai tunda dama lafiya suka rabu da mijin ta ai yin hakan kamar zai kara muna girmane a idon sa.
Da sauri inna tace a, a, a dai tsaya har yazo din aji ta bakin sa zaifi da sauri umma da ta fahinci hakan zai iya kawo masu matsala a tsakanin su tace hakan zaifi gaskiya.
Don haka basu bar garin ba aka saka ranan komawa na muna daki muna jinsu lokacin mutuwace kawai banyi ba don ta kaicin abinda abba din yayi min.
Shike nan ni nasan yanzu banda baki a wurin mami don wanan zai jawo min abin fada sosai a wurin su .
An aje umma zata dawo su rakani har abujan idan ranan yayi ita da maizube zamu tafi haka aka aje zancen komawan nawa.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAWAASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI FATAN ALHERI A GAREKU KO YAUSHE ALLAH YA BAMU IKON BAUTA MASA AMIN, , ,


LITTAFIN KUDINE KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA YAR UWA ALLAH YA BADA IKON SAUKE NAUYI AMIN, , , , ,


Duk wani motsi da yunkuri da naso yi don daukarwa kaina fansa kan wanan halin na ya jafar iyayyena sun hanani motsawa .
Daga mai fadin yin hakan kamar tozarcine ai a gareshi sai mai fadin may ya ragani dashi da zan gujeshi ko don yadda ya dauki dawainiyar karatuna dana kanwata ai zan hakkura na zauna in rufa mai asiri ba tare da wani ya jimu ba.
Magana dayace ya karya min gwiwana shine maganan innan mu da tayi min tana fadin ki kara basa dama kiyi hakkuri ki koma ko Allah zaisa ya gyara nan gaba.
Idan kinga bai gyara halinsa ba kinga kina iya daukan mataki a lokacin ke nan don gaskiya ba zanso ace ki rabu da wanan bawan Allah ba ko dan kiyi sanadin kubutoshi daga halakan da yake ciki a yanzu ma.
Haka kuma mahaifiyar shi data sa ido taga karshen zaman ku dashi ko dan haka ba zan so ace kinbar shi a yanzu ba a daidai lokacin da yafi bukatan ki a kusa dashi ke nan yanzu .
Sai gashi kina kokarin goge ladan da ya kusa zama rabon ki a wurin Allah don ba karamin jahadi kike kokarin yi ba tunda har Allah ya fara kwatoshi daga halaka ta dalilin ki a yanzu.
Wanan kalaman na inba ne suka kashe min jikina sosai har na dinga zubar da hawaye don tausayin kaina da sauran yan uwan da suka samu kansu a irin halin da nake ciki a lokacin nan .
Ba wanda yasan irin yadda zuciyar ka yake ji a irin wanan zaman da mutum keyi da mai iri halin nan sai ma mutane ko sun sani din suyi kokarin dora maka laifi don kawai kayi kara na dan lokaci guda.
Don wata ko na sati daya ba zata iya daukan hakkurin da kai kakeyi a gidan auren irin wanan ba .
Irin yadda inna ta nuna min yasa na tattara komai na barwa Allah zan koma nayi hakkuri don abubuwa biyu zuwa uku don kwadayin na zama silar shiruwan shi.
Na biyu kuma don farin cikin iyayyen da naga komawan nawa suke bukata kawai gidan yaya jafar a yanzu.
Sai kuma uwa uba don mami da yan matanta da inna da umma suka nusar dani yadda komawan nawa gidan ya jafar din zai zafafa masu rai idan na koma don su burin sune suga nabar shi ga baki daya .
Sai kuma irin su Lantana yan bayan fage a garin mu dake da yawa wurin saka ido suga nabar gidan jafar din a samu abinfada a karshe.
Ire iren tunanen da nakeyi ke nan a raina har na amince da zuciyana zan koma gidan na rugumi hakkuri a zuciyana.
Ana gobe zan koma bayan magariba mukaji sallaman malam mijin maizube a kofa innan mu zan iya cewa a iya wayau na wanan ne karo na farko da malam din ya tako har gidan mu.
Bayan gausuwa da dan barkwancin da akayine ya bukaci kowa ya barmu a falon dani dashi a lokacin a haka suka fice suka barmu dani dashi sai dan shiru ya biyo baya bayan fitan kowa falon kafin ya kira sunana a lokacin.
Na dago kai na amsa a dan kunyace ya fara fadin duk da nasan sherin shedan ne daya rudeki har kika kai ga aikata hakan don kina ganin mu bamu damu da damuwan ki ba ko wani abu haka ?
Sai dai zainab ina son ki sani shi hakkuri bai taba faduwa kasa banza a rayuwan bawa duk mai hakkuri mawadaci ne watarana.
Don haka zainab ki koma dakin ki ki kara hakkuri na dan lokaci muga abinda Allah zai maki sakaiya dashi ga hakan.
Don yanzu insha Allahu kina kiris ne da ki cinye jerabawan ki fa Allah ya dora maki a gidan shi na kirashi yazo munyi magana dashi ta fahinta.
Jin hakan yasa na dago kai da sauri na kalleshi kafin in mayar da kan ina mamakin hakan .
Malam yace kwarai na kirashi ba tare da kowa ya san da hakan ba kuma yazo mun zauna munyi magana dashi ta fahinta ya fada min komai yadda ya daxe na kuma fahinci inda matsalan yake yanzu.
Basa wani a nan gidan yasan da zuwan shi ba garin nan ko a gidan nan naku bani tsamanin wani yasan da zuwan shi din.
Don haka yanzu sai kin kara jajircewa kan wanda kikeyi a baya zainab nasan kina kokari sosai amma ki kara a kan wanda kikeyi a baya.
Insha Allahu muna sa ran abunuwan zasu zo da sauki don mawuyacin abune mutum ya shiga wani kungiya su barshi ya fita a ckkin shi salin alin ba tare da wani tangarda ba.
Balle shi din da suke ganin kamar samun shi a cikin su wani babban kamu sukayi a hakan yanzu kuma yace zai fice cikin su ba tare da ansha wahala ba.
Jin hakan na dan dago kai a tsorace na kalli malam yace kwarai nasan ke baki san da wanan zancen ba ai burin ki kawai shine kiga ya bar aikata abubuwan da yakeyi ko ?
Kamar yadda mahaifiyar shi da yan uwan shi duk basu san da wanan zancen ba suma a wuri su.
Ba abin mamaki bane a wanan zamanin idan kaga mutum yana wandakan shi ka dauka ya samu damane kawai a banza kabar mutum kawai a yadda ka ganshi don bakasan zuciyar shi ba.
Tsorone ya kara kamani lokaci guda amma sai malam din ya kara wayar min da kai yadda zan fahinta.
A karshen maganan nasa ne na gane wa yan nan abokan nasa na chaina shi dasu kamar wani gungiya suke cikin sa da yasa ya jafar din kara fadawa a cikin halaka.
Ga kuma nan gida mai binshi da sheri da son ganin komawa bayan shi a kullun sun masa aiki tun yana karami da iyayyen shi basu farga da hakan ba.
Malam din yaci gaba da fadin don haka yanzu aikine ja a wurun ki ko kun koma din ba zaki zauna hakan ba ki kara komawa wuri wanan matar koda abinda zata kara baki a hakan .
Duk da nasan insha Allahu har in kinyi aiki da wa yan nan abubuwan da muka hada mai abubuwan zasu zo da sauki sosai kema kanki sai kinsha na tsarin jikin ki din zasu iya waiwayan ki a ko wani lokacin kan hakan.
Ya miko min wani dan ruwa daga cikin aljihun babban rigan jikin shi yace karbi wanan ki shanye duk yanzu.
Da yardab ubangiji saidai ta Allah ba nasu ba don wanan makaru ne sosai majarabi ne kwarai na sani.
Ina hawaye na karba da hannu biyu na bude dan goran nayi bissimillah na kafa kai na shanye kamar yadda yace inyi din.
Ya kara miko min wasu kulli da zanyi wanka da hayaki tare da wasu addu ,a da aka rubuta min zan dinga yu safe da yamma don tsari.
Da wanan tunane na zancen mu da malam na kwana a raina ina faman tunane a raina watau a zamanin nan ko wani gida da kalan nasu matsalan ke nan na rayuwa.
Zama haka kai sakw bayayi ke nan sai mutum ya hada da neman tsari a wurin Allah da yawaita sadaka da kyautatawa gun mabukata shine zaman lafiya ga bawa.
Washe gari karfe goma na safe muka bar garin mu cike da bacin ran rabuwa da gida da zamu sakeyi na tsawon wani lokaci kuma don ban sa rau yaya zai kara bari nazo gida kuma ba nan maza.

Wasa wasa har abu yakai ga karawa yaya jafar ruwa don rshin karfin jikin shi da bayayi a wanan lokacin dole mami ta tsareshi saida aka kara mai ruwa don ya dan samu karfi.
Duk suna falo gaba dayan su sun sakashi a tsakiya sai ya dan ci abincin da mami tazo dashi don ta fahinci rashin cin abincin sa a yanzu.
Mami na fadin kawai zaka halaka kan ka kan wata yarinya can da bata damu dakai ba kana kokarin jefa kanka a cikin halaka haka.
Kai haba mami na fada maki bafa wani wuri ta tafi ba tana gidan yar uwan maman suce ashe a kaduna .
Nayi mamakin ma rashin dawowan su jiya da basuyi ba don kwanakin dana bata ya cika jiya ya fada yana bata fuskan shi.
Kaiya yanzu kuma hakan suka tsarama cewa zata dawo din bayan ka gama fadin ta bata har kana batun yiwa mutane hauka.
Mami ai dole ya damu rashin jin ta a waya da baiyi ba na kwanaki kin san yadda kasan nan ya koma fa a yanzu ya mamud ya fada daga gefen shi.
Tama bata din mana Aisha ta fada waya damu da ita idan ta bata tunda ita bata san ciwon kanta ba ta tashi taje wuri ba tare da fadawa mutane ba.
A cikin wani murya yake fadin AISHA ya kalleta kawai ya kawar da kanshi tare da gyara kwanciyan shi saman kujera.
Kai haba Aisha wanan wani irin maganane haka kuma ku kullun baku son gaskiya wallahi Na,ima ta fada tana kawar da kanta gefe.
Kaji kuma Na,ima da wani zance ai gaskiya aka fada rufaida tace kawai ta tayawa mutane da hankalin a banza.
Do kawai taga kamar yanzu din daya take da kowa har zata tafi wuri haka ta share mutane don kawai ta dagawa mutane hankali ta karasa kasa kasa don tasan kwanan wasan.
Nifa ku bar wani kame kame a gaban shi mami ta fada idan ma zata tafi ne ta tafi din aini har na fara murna tafiyan ta sai ga mamud na fada min wai rudun jafar ne taje wurin yar uwar maman sune ashe.

A daidai wanan lokacin suka ganmu kwatsam a bazata daga ni sai sadiya da hjy umma muka shigo don a dakatar da zuwan mu da maizube don kada su dauka wani abinne hakan.
Ashe ko hakan yai muna daidai do yadda muka samesu gaba dayan su a gidan zaune a falo lokacin.
Da wani irin mamaki suke kallon sadiya dake shigowa gidan jaye da dan troler kayan ta kai tsaye.
Da sauri ya dan dago daga kwancen yana fadin sadiya kune tafe ashe ina yayar taki take duk wanda suke zaune a falon suka kalli juna lokaci daya.
Sadiya tana fadin gasu shigowa suna baya tare da gwaggo data rako su da zamu dawo a daidai lokacin muka shigo ni da umma da Nafisa.
Basu ba duk mun dan kadu muma da ganin su sai dai mun dake mun shigo kamar babu komai a rayukan mu lokacin.
Nayi wani haske fayau dani don dan raman danayi a lokacin saidai hakan kuma bai hana kyauna ya kara fitowa fili ba sosai a lokacin.
Gaba dayan su idanuwan su ya koma a kanmu sai Na,imace da su ya jalal ke muna sannu da zuwa don mami ta ma kasa magana a lokacin .
Saboda bata yarda da abinda suka fada ba ta dauka shirine kawai don su batar mata da hankali suka shirya hakan.
Muna amsawa ya dago shima don ganin mu tare da umma yana mata sannu da zuwa dole yana kallon gefen shi su Aisha da sauran sukai saurin mikewa suka bamu wuri muka zauna.
Gaisuwa aka fara a tsakani su da umma bayan mun zauna din kafin umma tace ashe kuma bayan tafiyan yar nan jikin maigidan nata ya kiya haka ?
Ya mamud ya saurin fadin eh wallahi da zazzabi ya dawo kasan da yai tafiya kuma sai gashi ya kira layin ita zainab baya shiga gida kuma sunce basu sameta ba a lokacin ya dada tayar mai da hankali.
Kai ai zainab bata bata a kasan nan in ba wani ikon Allah ba hikiman ta dai na yarinyane zakaje wuri ba ka fadawa mijin ka ba ya sani don hakane ma da akace ya bugo bata nan .
Yasa nace ai sai muzo tare nida taje wurina in bashi hakkuri kan hakan da tayi kasan yaran yanzu basu daukan irin wanan da muhinmanci su.
Kai haha mama aida baki taso ba ko ita dayan ma ta dawo ai yasan gida taje gashi an dade ba ahadu ba dole ta dan zaga ta gaida ku ai.
Hakane amma zuwan zai sakashi jin dadin hakan don yasan an mutuntashi kaga gaba sai ya bata bakin zuwa ko ina ta duba mu ko ?
Shi dai yana gefe sai dan murmushi yakewa umma din ba tare da yayi magana ba a lokacin .
Kallon tsab mami takewa umma tunda ta fara magana sam batayi kama da irin yan uwana da take daukan sune gareni ba kawai.
Don umma dai in ba don da duniya ya basu baya ba a yanzu tana cikin matan da a zamanin baya suke fada a kaduna aji.
Ya jafar ya dan kalleni cikin kulawa yana fadin ki shiga dasu ciki su huta ko kuna da gajiyan tafiya a yanzu zaka dauka wani zancen soyayya mukeyi dashi a lokacin duk suka zubo muna ido duk da basu jin me yake fadi.
Ganin hakan na mike tsam daga inda nake zaune ina fadin Nafisa mu shiga daga ciki ina daukan jakkar umma dake gefen ta aje inda ta zauna.
Duk suka bimu da kallo bayan mun mike din don basu so hakan ba a rayukan su gaskiya jin karin bayanin da umma din tayi masu don kwana uku na kara ga kwanakin daya bamu din muyi a gida ke nan.
Wanan ita din wacece mami ta tambaya bayan mun shige ciki yan aikin gidan kuma suna shigo da kayan mu a cikin gidan har lokacin zuwa dakunanan mu .
Ai ba lalai bane ya san yan uwanta duka duba ga yadda aikai auren su din kinga ba wai ansan yan uwan zainab din bane duka.
Bata daiyi kama da yan kauyen nan ba ita kila a wani birni take zaune Aisha ta fada.
Amma kema dai kina da yan uwa a kauye ko don ba kowane zaune a birni ba ina su hjy dasu mama Ramatu duk a kauye suke zaune.
Jamal ke fadin hakan ba tare daya dago kanshi ba daga latsan wayan da yake yi tun zaman shi a falon bai furta komai ba tunzuwan su sai yanzu.
Mami tace cikin tsawa zaka fara ko tun dazu nake kule daku kuna kokarin hana yarinyar nan shan ruwa ya fada mata.
Bata da kunyane mami ana magana sai ta dinga saka baki a maganan wataga ya saka baki a cikin zancen cikin mu ?
A daki kan muna shiga umma tana zama take fadin ikon Allah gaskiya dai tayi halinta don wanan matar bata iya boye bakin cikin ta ba sam.
Haka muke umma na fada ina kokarin cire lafayan dake jikina daga sama ina juyawa Nafisa ke fadin aini umma ban ko tsaya kallon su ba ni mamakin gidan nan nakeyi kamar ba a cikin kasan nan ba.
Ita da tasan kanta ai kinga wanan bai rudeta ba ko umma ta fada ai idan ranka ya baci ko ka hango abinda ba daidai ba har kana da zuciyar kwarai abin duniya baya rufe ma ido sam.
Hakane umma don mai daki shiyasan inda ruwa ke masa yoyo akace ita da ke zaune cikon su tasan irin rayuwan da take yi a nan.
Sallaman Fadilace ya katse muna zancen mu ta shigo da dan fara,a a fuskanta kadan tana fadin ina baya tun zuwan mutanen gidan su oga sai yanzu ake fada min kin dawo ashe.
Nan dai ta juya tana gaisawa dasu umma tare da tambayan lafiyan su inna tana tambayan sadiya sai gata ta shigo dakin tana fadin.
Anty wai yaya yace ga bakon mu ya shigo shima a kawo masa abinci da abin sha a falo.
Sai dai ganin anty fadila yasa ta dakatar da maganan da takeyi ta makaleta don murna a lokacin nake fadin bakin falin sun tafine ko suna nan.
Tace babu kowa yanzu a falon ina ga sun tafine don basu falo sai fadila ke fadin ai sun tafi yanzu ina shigowa dakin nan.
Nikan wanka na shiga don hakan ya zama min kamar dabi,a na yanzu ance zama da madaukin kanwa don haka shima yaya din yake da tsabta dole nima na iya hakan.
Abinci lafiyayye Fadila da a yanzu nake ganin sauyi a wurin ta suka gabatar muna tare da sauran yan aikin dake shigowa muna gaisawa dasu a lokacin.


ZAINAB IDRIS MAKAWAASSALAMU ALAIKUM WAHAMATULLAH YAN UWA MUSULMAI BARKAN MU DA WANAN LOKACIN ALLAH YA SADAMU DA ALHERUN SA AMIN, , , , ,

YAR UWA BA DAMUWA BANE TUNINE HAKAN KADA KI MANTA KI SHIGA HAKKIN WANI IDAN BAKI BIYA BA DON ALLAH KI BIYA KI KARANTA, , , , ,

Mutunci da daraja bako ranan sun ganshi a gidan wurin mu don har sai da suka gaji daci don kansu daki na daban aka kai ko wani su.
Amma karshe a dakin umma da aka sauke ta a nan muka taru gaba dayan mu dakin wurin ta ana hira inda a karshe hiran ya koma na daulan duniya da sauran su.
Muna cikin hira misalin hudu da rabi ne yaya ya shigo dakin don gaida umma da gajiyan hanya gaba daya dakin kowa ya shiga kama kanshi a lokacin.
Nayi mamakin ganin wai ya jafar ya iya ladabi gun sarakan shi irin na malam ba haushe ashe don har kasa yakai yana gaida ita abinda ban taba gani ba a wurin shi ko dan bamu taba hadewa a gaban iyayyena bane dashi oho ?
Umma ta amsa itama a cikin dan kunya take kara yi mashi nasiha kan zama da iyali sai hakkuri don mu mata haka muke kaman yara wurin tunane.
Ya daga yana godiya ya fita daga dakin kafin umma ta juyo tana fadin ke ko yan nan kije gunshi tunda muka iso gaein nan kuwa ?
Kasa nayi da kaina lokacin data fadi hakan don ban tafi ba kuma ba zanyi karyan hakan ba gaskiya.
Assha zainab baki kyauta ba gaskiya kema kina da naki matsalan ke nan a nan don ba aiwa maza hakan ai kome ko ke tsakanin ki dashi.
Ya kamata ace kinje kun gaisa ba wanan da kukayi ba a bainan jamma,a dashi kinga a hakane zaku samu fahintar juna a tsakanin ku har ku warware matsalan dake akwai ba tare da kun shirya hakan ba.
Ya zama dole ki dinga bashi hakkin shi a naki bangaren bawai ki biye masa ki dinga share shi ba haka ban san lokacin dana bude baki ina fadin ummz bawai ban zuwa bane.
Shi din ne yayi warning dina tun farkon auren mu kan hakan ya kance shi mace bata gaban shi asalima shida mace sai dai mutunci da zaman yan uwantaka a tsakanin su.
Badake matarsa ba kan ko ya fadi hakan don kece mace mafi kusanci yanzu a duniyan nan gareshi kinfi ko uwarshi kusanci a wurin shi.
Hakama kinfi duk wata yar uwa tasa mafi kusanci a yanzu gareshi kefa mace ce zainab kina da hanyoyin da zaki sauya duk wani akidar shi wanda bai maki ba a cikin ruwan sanyi.
Na marairaice murya ina fadin umma yaya zanyi nikan yace baya son mace a kusa dashi ko dakinsa dokar shiga yasa min a lokacin idan bashi ya bukaci naje nayi wani abuba bana shiga part din shi sam.
Ikon Allah sai kace wanda baya hurda da mata su nake jin haka a garesu Nafisa ta fada a bayana inda take zaune.
Wanan wani irin maganane Nafisa ko kin manta shi din tashin American ne wai bakin akidarsune kawai ya kwasa a zuciyar shi na rashin daukan abu da muhinmaci .
Ki bar wanda bai tashi a cikin al,adan malam bahaushe ba kawai don shi hakan da yakeyi ba komai ya daukeshi ba a wurin shi.
Gyara ya zama dole yanzu gareki ba wai rashin kunya bane yasa nake fadan hakan gaskiyan maganan a nan kema kina da naki laifi zainab.
Dolene ya zamo makwancin ku daya dashi koda hakan ba zai kasance kullun ba haka kuma duk wani bukatan shi ko laluran gida ya zamo kece mai masa shi.
Kyautatawa fa yana daga cikin abinda namiji yafi so a rayuwan shi koda kuwa yarone kankani yana son hakan gareshi.
Wanka ki zamato kece mai tayar dashi kafin ya tashi kin hada mai ruwa ya shiga kin tsaya dakin ki gyara kafin ya fito kin feshe dakin da kanshi kin fitar mai da kayan da zai saka a ranan.
Ya fara shiri idan akwai lokaci ki tsaya har ya shirya kafin ki fita zuwa hada masa dinning da already kin gama abincin kafin ki tayar dashi daga barcin don gudun makara.
Kina zaune kin tsare shi har ya gama ki rakashi idan fita zaiyi kina masa fatan alheri da addu,an kariya a gareshi har ya fice gidan .
Zainan ki fada min cikin wa yan nan halaiyar wani kikewa miji ki a ciki na dukar da kaina kasa tace kin gani .
Inda ake fara samun matsala ke nan a wurin mu, mu mata ana fadin ni mijina bayai min kaza baya min kaza.
Kinga a nan ai matsalan na mace ce don itace tayi sakaci da hakan ba zance ki matsa dole sai ya kwana dake ba a,a.
Wanan kawai idan kin tsare ya isa shi kanshi yaji kunyar kanshi da kanshi yasan abinda yake maki bai dace ba ya gyara wasu daga cikin halin da yake nuna maki din.
Kwanciya a kullun kusa da miji wani sirine da Allah ya boye hakan a zukatan ma,aurata wanda su kadai suka san feeling din hakan.
Amma dake dashi kuna zaune haka a cikin jahilci kowa na ganin laifin wani alhalin dukkan kune masu laifin gaba dayan ku.
Din haka ya zama dole ki gyara kema a naki bangaren a gani ko za a samu nasara a wanan bangaren.
Don Allah zainab kiyiwa Allah kema kiji tsoron Allah ki gyara kada kiyi tsamanin Allah ba zai iya kamaki da laifin wanan sakacin ba.
Irin wanan har sai mutum ya shiga wani hali ma dan uwa shi bai sanda hakan ba sai azo ana ganin laifi mutum daya.
Hawaye nakeyi kawai zuwa yanzu nasiha sosai umma ta zaunar dani tayi min sosai a karshe tace in tashi in tafi gurin mijina mu gaisa.
Hakana mike ba don naso ba na nufi hanyar fita daga dakin gwiwa duk sunyi sanyi sai faman sake saken yadda zamuyi arba dashi nakeyi bayan abinda na aikata masa din nagudu .
Daki na shiga na dan kara gyara jikina kafin na fito zuwa kasa babu kowa a falon sai na,uran wuta dake aiki a lokacin.
Dan fita nayi na hango su can a gaban gidan zaune su ukku saman fararen kujerun roba dashi da ya Uzaifa da mukazo tare sai wani da ban san kowaye shi din ba tare dasu lokacin.
Gabana ne ya fadi naji tsoron hakan don ban amice da imanin shi ba har lokacin nan don tsoro nake jin kasancewar su tare da wani namiji dan uwana ko wani musulmi a yanzu.
Wata zuciyane tazo min da magana tana fada min haba ya zai aikata hakan kan dan uwan ki komai abinsa ai yasan kunya.
Tunanen hakan yasa na danji sanyi a raina na juya ba koma part dina ba tare dana je inda suke din zaune ba suna shan iska din.
Zama nayi a daki ni kadai ina tunane ta yaya zan fara tunkaran yaya din kamar yadda umma ta umurceni dayi yanzu.
Kawar da kunya da nauyi zanyi in sameshi kai tsaye cikin dakewa don haka ya zama dole in koyi yin hakan in jeraba in gani ko zan samu sauki a hakan .
Kafin na koma tunane su mami kuma ta wani hanya zan bulo masu a yanzu don dai na kawar da irin tsana da bakin cikin da suke gwada min a fili.
Shawaran umma dai din zan bi da tace in nuna ban ma san sunayi ba in dinga wayen cewa kawai idan sun min abu in daina nuna damuwana a kai.
In nuna masu hakan bai dameni bani da dansu nake zaune bada su ba hakan zai kara jefasu cikin shakku da fargabana.
A haka ina faman tunane har lokacin sallah magariba yayi na mike na gabatar da alwala na tayar da sallah.
Ban fito dakin ba sai da nayi sallah insha,i na yi wanka na fito daga dakin dakin umma na fara shiga na gaida ita inda na samu an kawo masu abincin dare.
Ban wani tsaya ba don tana zaune har lokacin tana lazumi na fita bayan mun gaisa kai tsaye part din shi na nufa .
Gabana sai faduwa yakeyi haka na daure na shiga dakin baya falo na nufi kuryan dakin ban hango shi ba ma nan nabi dakin da kallo na dan lokaci yana gyare tsab kafin in juya zan fice daga dakin naji ance dani.
Ki karaso mana zaki koma kuma nayi mamakin daga ina yake magana sai gashi ya juyo saman kujeran dake kallon window dakin nasa irin sofa din nan mai laushi yana kwance sama da tasbaha a hannun shi yana ja.
Saida na dan kadu kafin in samu courage din fadin dama ba wani abu nazo yi ba zuwa nayi na gaishe ka da wuni naji ya jikin naka kuma ?
Ina magana ina karasowa inda yake zaune din gefen kafan shi na samu na zauna ya dan ja kafan nasa kadan yana fadin.
Naji sauki dama ba wani ciwo bane ai kinsan halin mami da rudewa ciwon kaine dole ta saka saida akai min karin ruwa jiya.
Tafika damuwane da jikin ka don kai baka dauki hakan serious ba shiya sa su inna suna gaida kai sunce ace sun gode.
Ni zan gode masu ai da suka dawo min dake lafiya aina dauka zaki dawo tare da Asabe ne ta kwana muna biyu nan ?
Asabe kuma na tambaya a cikin mamaki yace eh ai yanzu irin su kin san hutu suke so da kulawa kullun naga tsohuwan tana ban tausayi wallahi.
Ni kan ka rufa min asiri na dauko asabe gidan nan ace kuma na cika gida da yan uwana haka sa,adatu ma tazo da sunan kwana biyu hakan ya zama abin magana.
Shiru yayi na dan lokaci bai ban amsa ba sai can yace amma nan dai gidanane ko ba gidan wani ba kuma yan uwan matane suka zo muna ai.
To idan kana son tazo sai ka aika a dauko ta zaifi tunda yanzu ban zo da ita ba yace zan dauko su din ai ita da hjy su kwana muna biyu kafin tafiyan mu.
Na kawar da zancen da fadin abinci fa yace tea na umurce su su hado min kafin in kwanta karfe tara na dare.
Ba sai sun kawo ba tunda na dawo wanan aikinane yanzu ai na fada ina mikewa tare da fadin wani nau,i za a hada ma yace black tea na jinger.
Na juya yake fadin bakya son hutu yanzu ke nan nace ai wanan aikin lada zanyi don nayiwa dan uwana dawainiya.
Na fita ya bini da kallo kamar wace ya fara gani a ranan ko yana kallon wani abu a jikina.
Kai tsaye kitchen na nufa a karo na farko inda na samu yan aikin suna gyaran kitchen din cikin girmamawa suka shiga gaidani .
Na amsa ina fadin ruwa nake son hadawa oga shayi da sauri namijin ya taso yana fadin dama oga yace a hada mai zuwa nine akai masa.
Ka barshi akwai hadin da zanyi mai na fada tare da juyawa zuwa dakina dauko abinda nakeson zubawa tunda Allah ya ban sa,an wanan ranan ke nan a kanshi duk da malam ya fada min ba matsala wurin hada mai din.
Kamshi sosai na zuba sai ganyen shayin daya biyo baya ina tsaye har ruwan ya tafasa sosai kafin na juye na tace shi, na mayar a cikin flask..
Dakina na nufa da flask din wanka nayi na zauna tsab na gyara jikina na kawo hijab na saka na shiga wurin umma na samesu suna hira nake fadin idan akwai abinda suke so a tambayi fadila za a kawo masu.
Na fito na kara gyaran jikina tsab da turaruruka a cikin hikima na shafa wani da malam ya bani dan mitsitsi dashi a jikina kamar yadda yace a ko wani sako na jikina din.
Na gama na sanya wani rigan baci mai silk mai dan hannu pink clour da dan filawa a gaban rigan sai dan wandon shi iya gwiwa da dan tsaga a gefen kasan wandon.
A haka na dauki kayan shayin zuwa part din shi na samu ya fito daga wanka yana saka jallabiya a jikin shi na aje kayan bayan nayi sallama ya amsa min .
Ina ajewa wayan shi na kara ya dauka kai tsaye saman gadon shi na nufa na zauna ina hangoshi daga inda yake tsaye bakin seif din shi yana amsa wayan .
A hankali na kwashi kafana dake zube na haye gadon da kyau gabana sai faduwa yakeyi don ban san abinda zai iya biyowa bayan hakan danayi mai ba.
A yadda nasan ya tsanin hakan a baya in ba lokacin da baida lafiya ba har ya nemi taimakona a ranan bayan hakan ban taba yin gigin kawo kaina wurin shi ba haka.
Idona na mayar na lumahe na fara jero addua a bakina ban masan wanda zan karanta ba ina dai yin duk wanda yazo min a lokacin ne.
A haka yana karba wayoyin dake faman shigo mai a tsaye har ya hada tea din yana sha duk a tsaye din kafin ya koma bakin window dakin ya zuge ya mayar da hankalinshi waje.
Idona na mayar na rufe wani tunane yazo min nasan a lokacin ji yake kamar yayi ihun ganina haka saman gadon shi ya san da manufa nayi mai hakan.
Saidai a yanzu babu yadda zaiyi tunda yasan neman magana nake wurin shi kawai don yin hakan.
A daidai lokaci cikin wanan tunanen ne barci ya soma satana don akwai gajiya a tare dani na tafiyan da mukayi a mota ranan .
Kamar a mafalki nake jin muryab shi yana fadin zainab a nan zaki kwana ne ki tashi kafin barci ya dauke ki mana.
Maimakon in tashi kamar yadda yace sai na gyara kwanciyana da kyau na fita batun shi dama nasan za a rina ga yin hakan.
Saida ya dan dade tsaye a kaina yana kallona kamar yana nazarina kafin inji ya taka zuwa dayan bangaren gadon ya hau a hankali kamar mai tsoro ya da kwanta rabin kafafuwan shi a kasa.
Kamar an zabureshi naji ya mike zaune na dan lokaci can kuma ya koma ya kwanta tare da daukan dayan hannun shi ya dora saman fuskanshi.
A haka har barci ya dauke mu kowa da irin tunanen da yake a ranshi a lokacin nikan cike nake da tsoro da mamaki shi a lokacin.
Tabbas malam yayi gaskiya don wanan abin nasa bana kai sake bane irin yadda naga yanayi a lokacin don kawai na zo inda yake a ranan na kwanta a kusa dashi yake nuna wasu irin halaiya na daban.
Da a yan shekarun baya da suka wuce ne ina tsoron shi sosai gaskiya ba zan iya kwanciya a dakin ba ganin yadda yakeyi din nan.
Amma a yanzu dana dan kara shekaru a tare dashi abubuwan nasa sun daina firgitani haka kai tsaye.
Can a cikin barci nake jin kamar ana kokawa dashi na bude idona da sauri don gani meke faruwa dashi.
Barcin shi yakeyi amma kuma kamar a wahalce yake a cikin barcin nasa sai dai yana faman juyi kamar yana faman fada da wani a lokacin.
Allah ya taimakeni dabaran yin addu,a yazo min tun ina addua har na fara karatun kur,ani da karfi a fili.
Sannu a hankali naga ya fara sakewa numfashin shi yana dawowa normal can ya sauke ajiyan zuciya kafin ya juya yana gyara kwanciyan shi.
Tsoron kan naji shi a ranan gaskiya barci kuma ya kaurace min a idona gaskiya sai addua da tunane nakeyi lokaci guda.
Kafin asuba barci ya dan daukeni sai dai abin mamaki har mukai sallah ya koma min kamar bashi bane yayi wanan abin a cikin dare sai gashi ya koma normal dinshi.
Nikan sai ya barni cike da tunane a raina sai faman satan kallon shi da nakeyi har na fice daga dakin na koma dakina .
Da kyat na samu nayi wanka don barcin da nakeji a lokacin riga na saka na fada saman gadon sai barci haka ya jawo ban samu fitowa da wuri ba ranan sai wajajen sha dayan rana na falka.
Saidana shirya ne na fito don gaida umma sai na samu sun shirya wai dama ni suke jira un fito muyi sallama su zasu tafi.
Da mamaki nake kallon umma tare da tambayan umma wani abu ya faru ne kuma take fadi cikin mamaki itama .
Zainab mun dawo dake dakin ki lafiya kuma alhamdullahi ba, a samu matsalan komai ba a gun mijin ki to me kuma zamu tsaya yi yanzu ?
Ai sai ya zama muna rashin hankali ko gamu har mu uku da yaran nan ai sai mijin naki ya daukemu mutanen banza kuma.
Kedai ki daure kiyi duk abindana fada maki a naki bangaren da yardan Allah koma meye Allah zai sama maki mafita a nan.
Umma zanyi kamar yadda kikace dani insha Allahu amma zancen tafiyan ku yau don Allah a fasa har zuwa gobe ko jibi sai ku tafi.
Sam umma din bata yarda ba a karshe saina roketa su dakata har ya fito suyi sallama dashi don Allah bata soba dole dai ta yarda da hakan.
Hira mukeyi niko sai tunanen abubuwa nakeyi a raina akan halin danaga yaya a ciki a daren jiya din nakeyi.
Na tambayi kaina koshi yasa malam yake fada min sai na kara dagewa da addua da neman tsari nima a jikina ?
Kuma har yake fadin yanzu kabar mutum a yadda kasan shi don bakasan ciki zuciyar shi ba ke nan ya tabbata dai yaya yana cikin wani kungiya kenan dai na asiri ko ?
Sai misalin sha biyu ya shigo dakin suka gaisa nan umma ke fada mai zasu tafi dama shi suke jira ya shigo suyi sallama dashi su tafi.
Bai boye mamakin hakan ba yake fadin haba mama aikwa bari zuwa jibi dai sai ku tafi din idan an shirya tafiyan naku ko ?
Kai haba munzo munyi yadda ya dace tsayawan me kuma zamuyi a yanzu ko hakan ma mun gode kwarai da mutantamun da akayi.
Ina gefe babu abinda nakeyi sai satan kallon shi ina zargin shi a raina tare da fadin watau shi dai ya tara abu goma da goma ke nan a rayuwan shi.
Kai zama cikin kafirai baiyi ba wallahi don komai kama kanka idan ba Allah ya kareka ba sai ka bace hanya ke nan.


ZAINAB IDRIS MAKAWAASSALAMU ALAIKUM YA YAN UWA MUSULMAI UBANGIJI ALLAH YA BAMU WUNI LAFIYA AMIN YA ALLAH KA SADAMU DA RAHAMOMIN KA KA KAREMU DAGA DUK WANI ABIN KI ALLAHUMA AMIN, , , ,

YAR UWA KADA KI MANTA DA LITTAFIN KUDINE KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DA AMIN BA TARE DA DAUKAN HAKKIN KOWA BA A KANKI, , , , , ,


Kamar yadda ya roki umma hakan ne yafaru don sun dage tafiyan nasu sai washe gari da safe zasu tafi din.
Ina dakina kiran wayan shi ya shigo min na dauka yake fadin in sameshi a falon shi na sama.
Banyi nawa ba ga hakan na sameshi shi kadai zaune ya tasa computer a gaban shi yana aiki ga cup din ruwan a gefen shi da yake sha.
Idona na akanshi bayan nayi sallama ya amsa min ba tare daya dago kan shi ba har na karaso inda yake zaune din idona yana akanshi.
Alokacin na kula da jikin shi daya tashi kamar yayi fada da wani yajin mai ciwo a haka nagaida shi da aiki na samu wuri na zauna daga gefenshi sai lokacin ya dago kai ya kalleni yana fadin.
Gobe din zasu tafi ko nace eh baka basu hakkuri su dage tafiyan nasu ba dazun yace hakan zaifi kyau ai ga kudi nan ki dauka a basu dubu dari uku.
Wanan kuma ku fita idan zaki iya ko kuma ki hadasu da fadila taje ta rakasu su sai tsaraba dashi.
Na dago kai a cikin mamaki nake fadin an ko gode wallahi amma dai ban tsamani zasu iya kashe wanan kudin duka saidai su gyara motan su da ya uzaifa ke neman kudi dashi ya lalace.
Jin haka yasa ya dago kai da sauri ya kalleni saina dan tsargu da kallon da yai min din naci gaba da fadin .
Ina nufin tunda mahaifin su Nafisa ya rasu yan uwan shi da abokan shi suka kwashe abinda ya bar masu suke cikin halin wahala motan daya da aka bar masune yaya uzaifa ke dan haya suna samun abinci yanzu kuma motar ta baci sun shiga wani hali ko abinci yana masu wuya a yanzu.
Zainab ke mai kikai msu akan hakan na dago kai da mamaki ina kallon shi don jin abinda ya fada din yace eh a matsayin ki na wace tafisu zarafi a yanzu wani taimako ya kamata ace kinyi masu.
Nan ma dai shiru nayi ganin ya tsureni da idanun shi yasa nayi karfin halin fadin ni me zan masu kuwa nadai taimaka masu dana abinci a lokacin da nake gidan su.
Nafisa kawatace ba yar uwata ta jini ba a makarantan da mami ta sakani a kaduna kafin mu dawo abuja muka hadu da ita ta taimaka min sosai a lokacin.
Tun wanan lokacin take a raina don bazan iya mantawa da karancin da taimin ba a lokacin shine dalilina nazuwa gidan su a yanzu na nemeta.
Ko a yanzun ma sun min karcin da ko wani dan uwana ba zai iya min haka ba don umma ta nuna tankar nice nafisa a wurinta ta sakani a hanyar daya dace kuma.
Nasan da hakan ko baki fada ba don ba zai yuyu matana ta tafi surun da banyi bincike a kanshi ba in kyale ta.
Na bincika nasan komai a kai don haka nake tambayan ki ai ya kamata ire iren su dake cikin wani hali kuma kina tare dasu in dinga sani don a taimaka masu ga rayuwa.
Ba wai ki shiru a kyale mutum a cikin wahala ba haka irin su ba zan san da halin da suke ciki na bukatan taimako ba ai ga kuma suna a cikin bukatan suna kuma cikin makusantan mu a yanzu.
Irin wanan alheri nakan so inyi shi saidai rashin sanin wa zan tunkara da hakan tunda bawai kusantan mu irun su sukayi ba.
Bayan hakan ma ai banda wani lokaci a yanzu da zan san hakan har insan wani na cikin irin wanan halin.
Yanzu ki basu wanan din ki bar ni zangana dashi yaron a waje inji abinda za a taimaka mashi dashi kafin su tafi.
Da wanan ya duka yaci gaba da aikin da yakeyi a cikin laptop dinshi kawai bai sake magana ba kuma bayan wanan din.
Kara dago kaina nayi idona ya sauka akan wuyan shi daya fi yin miki da yawa yana nuna kokawa yayi da wani ko wasu.
Sai abin ya ban mamaki sosai don a iya sanina dashi dai bansan shi da fada ba ko daga murya saidai idan ranshi ya baci bai iya nunawa mutum hakan ba a lokacin da ranshi ya bacin .
Har na mike ban bar tunane ba akan jin ciwon nasa sai faman tunanen inda ya samu miki hakan a jikin shi.
Dakin da umma din take na koma suna zaune nima na samu wuri na zauna a gefen ta tare da aje mata sunjin kudin duka a gefen ta.
Ta dago kai da sauri tana fadin na meye wanan kuma nace umma shi yace abaku kowa dari dari har yaya uzaifa.
Wanan kuma wai ku shirya fadila ta rakaku kasuwa ku sayo tsaraba dashi na bata amsa duk suka kalloni kafin su juya kuma su kalli juna ita da yarta.
Kai umma ta fara girgizawa kafin tace dani haba zainab ai wanan ya zama lalura kuma mu da mukazo neman lada za, a bamu wanan kudi haka ?
Don haka dauki kudin nan ki mayar mashi kice mun gode don Allah da zumunci muka kawo masa ke badon wani abin hannun shi ba.
Da sauri na tare da fadin a, a umma ko na mayar masa ba zai karba ba fada zai min kan hakan ko yanzu saida yayi min fada sosai kan zancen motan ya uzaifa dana fada mai ta baci.
Kai ta dago ta kalli Nafisa dake daga gefe zaune itama Nafisa din da sauri tace wallahi umma bada wani manufa na fada mata motan yaya din ya baci ba a cikin hirane har muka dauko zancen lalacewar motar tashi.
Yanzun dai na fahince ku so kuke ko mayar dani tsohuwar banza a cikin ku, ku bata min ladana da kimana a idon mijin ki ko ?
Wallahi umma ba yadda kike tunane zancen yake ba sam ban roke shi akan hakan ba sai don kawai ya tambayani zancen uzaifa nake dan fada mai abindana sani game dashi kawai .
Shine yake fada don me ban fada mai tun jiya ba yasan da hakan sai yanzu nake fada mashi zancen .
Amma wallahi ba rokon shi nayi ba akan hakan na dan marairaice mata ta bini da kallo kafin tayi ajiyan zuciya tana kawar da kai gefe daya.
Dakin yayi tsit a tsakani mu kafin ta dago tana fadin gaskiya hakan bai mun dadi ba wanan ai sai yaga kamar roko mukazo yi dama gunsa.
Umma yadda fa kike zato sam ba haka abin yake ba Allah sam umma ban rokeshi ba ko kadan yadda na fada maki haka zancen yake.
Idon ta ta kara saukewa kan kudin dana aje din a gabanta tace wanan kudin a gaskiya yayi yawa zainab don haka ki raba biyu ki mayar mai da rabi.
Murmushi nayi na mike tsaye tare da fadin Nafisa nasan umma ba zata fita ba ki shirya mu fita anjima karfe hudu.
Ina fadin haka na koma dakina don indan huta saidai tunane ya hanani hakan don a gaskiya zancen lamarin yaya ya fara daure min kai yanzu kuma.
Tunanen irin fada da naga yanayi a cikin mafalkine ya dawo min a raina zubur na mike daga kwancen da nake tare da wani irin tsoro da ya ziyarci zuciyana a lokacin.
Cikin kaduwa na mika hannuna inda wayana yake aje na fara neman layin malam kakana don in kirshi nayi sa, a wayan yana shiga don shi yace duk abinda na gani wanda ya fara daure min kai na kirashi don asan abin yi.
Bayan mun gaisa ne yake tambayan ya muka isa nace lafiya kalau ya sake tambaya to ya muka kwashe nace baiyi wani magana a kai ba har yanzu malam.
Saidai gaskiya naga wani abinda ya daure min kai dashine nan na koro mashi komai duk yadda abubuwan da yayi a barcin sa.
Sai da na gama fada mai komai ya danyi shiru kafin yace dani dama na fada maki sai kin jajirce don iri abubuwan da zaki gani a yanzu .
Don ko ke idan sun fahinci wani abu zasu iya juyowa gareki su farmakeki insha Allahu har in kin dage da addua ba zasu taba galaba a kanki ba da yardan ubangiji.
Dasu yake fada a mafalkin don ga zahiri kin gani da idon ki idan zaki tuna a baya irin yawan mafalkin da kika dingayi a lokacin yanzu shine ya fara baiyana maki a fili zakiga zahiri saidai irin kallon da kike ganin mutumin na maki yanzu din kece zaki masa da yardan Allah.
Mun kai wani lokaci da malan din yana min bayani kafin muyi sallama dashi ina masa godiya.
Ajiyan zuciya na sauke tare da lumshe idanuwana lokaci guda abubuwan da nasha gani a cikin mafalkina a baya ke dawo min a raina.
Dakin su umma kuma ina fita sadiyama dake kwance gefe ta daga tana fadin zanje in kwanta umma tunda ance za, a fita anjima.
Sadiya na fita dakin Nafisa ta kalli umma din tana fadin umma hakan da ki kaiwa zainab baiyi ba sai ta dauka kamar da wani abu ai.
Dole inyi fada Nafisa don na rasa abinda zan fada kan hakan iya gaskiyana ke nan don a yanzu kusan daya na daukeku a wurina don yarinyar nada hankali sosai wallahi.
Ita din a yanzu wani haskene ubanguji ya kawo muna a rayuwan mu a yanzu ban san kalman da zanwa yarinyar nan godiya dashi ba a yanzu.
Don ko wanan kudin kawai ya isa ya taimakawa uzaifa a halin yanzu na yarda alheri danko ne baya faduwa kasa banza.
Kin taimaka mata a baya yanzun kuma itace take taimakon ki a yanzu da abinda yafi wanda ke kika taimake ta din.
Umma a lokacin fa ba ma wani abu bane nake taimaka mata dashi sai dan abincin tara na da muke ci tare kuma in saya muna wani abu muci tare.
Don haka kawai yanayin ta yake ban tausayi yasa naja ta a jiki muna yawo tare ko ina tare zaka ganmu har dai sukazo suka koma abuja da zama ga baki daya.
Alheri Nafisa kona kwayan dabino ne sai ya rikede wata rana ya zama maka kamar girman zinari.
Haka muka fita da yamma ina a cikin damuwa har umma na tambaya ko dan abinda tayi min ne na koma haka kuma ?
Dan murmshi nayi tare da fadin umma ai ba afushi da zancen ku don kome kuka fada idan mutum ya kwatar da hankalin shi mai amfanine a garemu.
Abubuwane dai kawai suke ban mamaki dan dawowan nan namu umma a game da yaya jafar din yanzu.
Ina dai ba wanda zai iya illanta muna ke bane yar nan umma ta fada a dan razane.
A, a umma lamarin fa dai ya shafe shi ne ni bai shafeni ba tace to Allah ya sauwaka daga haka kowa yai shiru a motan.
Mun zaga sun sayo abinda suke so sai dai ba sosai ba don a karshe duk abinda suka nuna suna so basu saya ba nakan saya nace ya ban sha,awa nima.
Mun dawo a gaji lokacin magariba ya yi mun samu ana sallah magariba bamu tsatsaya ba muma muka gabatar da sallah kafin mu shirya masu kayan su a wuri daya.
Yau ma kamar ince yaya jafar yafi shan wuya a cikin barcin ko ince mafalkin shi don dambe sosai yayi a mafalkin nashi da kuma surutu da banjin abinda yake fada har saida na tayar dashi daga barcin nasa.
Yana falkwa da kyat ya fara fadin bani ruwa in sha zainab ki taimaka min da ruwa sai kuma zufa da yake karyo mashi a lokaci guda ya jiki sharkaf duk da sanyin AC dake akwai a dakin lokacin.
A cijin gigita na falka na nufi inda goran ruwa yake na dauko mashi ya kafa kai zuka daya ya zuke ruwan goran duka kamar wani mai cutar masha ruwa.
Ni dai ina tsaye gefe na rugume hannaye ina kallon shi a cikin mamaki na rasa abinda zanyi mai a lokacin .
Kamar an tuna min na shiga karanta mashi Amanal rasulu har zuwa karshe kafin naga ya koma ya kwanta lankwasa saman gadon yana sauke numfashi guda guda ya dafe goshin shi da hannun shi.
Ranan kan naji tsoro kwarai da wanan abin dayayi a gabana gashi kuma na dauki alkawarin duk wani abinda ya sake faruwa dashi ba zan sake kiran mami in fada mata ba .
Tunda tace kazafi nake son na kullawa danta don kawai in bata mata sunan zuri,anta a duniya nake fadin haka .
Shiru ne ya biyu dakin na dan lokaci ina tsaye a kanshi na kura mai ido kafin inga ya sauke wani ajiyan zuciya ya gyara hannun shi dake saman goshin shi da alama kanshi ke masa ciwo sosai a lokacin.
Hannuna nakai a hankali saman kafada shi jin hakan yasa ya sauke hannun nasa da sauri ya kallo inda nake tsaye ya sauke idon shi akaina.
Meke damun ka hakane yaya ko baka da lafiya ne baka fadawa kowa ba matsalan dake damun ka kada yai ma yawa a hakan.
Murmushin karfin hali naga yayi tare da dan jan jikin shi ya koma baya yana fadin koma ki kwanta abinki ba abunda ke damuna mafalkine kawai nayi.
Ka dinga addua idan zaka kwanta zaifi akasari idan mutum ya kwanta ba tare da addu,a ba hakan ne yake faruwa dashi.
Nagode ya fada tare da juyawa kamar wanda baison ganina a lokacin don haka na gane na zama mai karfe kafa a yanzu ke nan.
Juyawa nayi side din da nake kwance da farko na koma na kwanta ina karanto muna addua a fili ta yarda har yake iya jin abinda nake karantawa.
Haka dai muke kwance ba wanda ya iya komawa barci a lokacin ganin shirun yai yawa na mike na shiga bandaki na dauro alwala na fara gabatar da Nafila.
Ko me ya gani yakai kusan rabin awa naga shima din ya mike ya nufi ban dakin ya dan dade a ciki kafin ya fito daga ciki da alama alwala yayi shima yazo ya fara sallah.
Saida akai kiran sallah muna zaune shiya fara mikewa ya sake dauro alwala kafin nima nabi bayan shi .
Ina idarwa ban tsaya gaidashi ba na mike zuwa dakina na kwanta don barcin da nake ji sosai a lokacin.
Barci ne mai nauyi ya daukeni can cikin barcin nake jin ana ja min kafa hakan yasa na bude idanuwana da kyar don ganin mai tayar dani din.
Da kyar na iya bude idona shine tsaye a kaina yana saye cikin kaya irin na motsa jiki kamar bashi bane ya wahala a daren jiya din haka ?
Ki tashi kada kisa su makara rana ya soma yi ya fada yana tsaye a kaina zan tashi na fada ina gyara kwanciyana don barcin bai sakeni ba.
Ya kara fadin zaki tashi ne fa don sun shirya nake ganin tun dazun haka yasa dole na mike ina mamakin shi a raina har lokacin kamar bashi ba .
Mota nan waje da zasu tafi dashi munyi magana da yaron zai kawo min takardun shi in duba inda ya kamata a sashi ya fara aiki.
Da sauri na mike zaune don jin abinda ya fada nace a cikin mamaki mota yaya eh ya tafi dashi ya fara amfani dashi.
Ganin na tashi yasa shi ya juya ya fita daga dakin nabi bayan shi da kallon mamaki ga mutum har mutum a fili amma ya samu rauni ga imanin shi.
Yanzu wa zan fadawa wanan maganan ya yarda dani a yadda muka kwana dashi a daren jiya a wahalce dashi har a yarda da abinda na fada yadda ya mike haka da safe.
Gashi gari ya waye ya mike tangararam kamar wani abu bai faru dashi ba haka a daren jiya din don haka yanzu dai ya tabbata a zuciyana shi din yana wani kungiya ke nan na asiri ko wani abu na boye da mutane basu sani ba ?
Wanka na shiga na fito na shirya tsab kafin inje dakin umma din na samu har sun karya fitowan mu kawai suke jira a lokacin.
A, a wai har kun shirya kome na fada ina kallon nafisa dake zaune a cikin shirin ta .
Tace fitowan ki kawai muke jira mu da yanzu munyi nisa kinsan yau umma nada ganin likitan ta ai.
Gaskiyane na fada ina kawai tsugune kasa don gaida umma din a cikin ladabi da biyayya ta amsa min da dan fara,anta a fuska don jin dadi.
Ita a zaton umma din abubuwa sun fara kamkama a tsakani da yaya yanzu don haka takw ganin hikimar ta yayi na cusani a gareshi datasa inyi don dole.
Saidai da ace a lokacin umma tasan kusantan shi da nakeyi yana sashi shiga cikin ukuba a kullun na kwanta a kusa dashi da bata umurceni da yin hakan ba a lokacin.
Don wanan zuwan da nake daki shi ina kwana a kusa dashi da nakeyi ashe yana cikin dokan su yin hakan garesu su kusanci mace ko numfashin mace a makwanci daya su da mace dokane a gare su
Wa, iyazu billahi asirin ma kanshi wahalane kawai a cikin sa ga dan mami na cikin fitina da masifa daya jefa kanshi.
Amma ita mami din mulki da giyan duniya ya hana mami ta kwantar da hankalinta ta fahinci komai a lokacin.
Bayan mun gaisane nake fadin umma yace in fada maki mota na nan da zakuyi tafiya dashi ga makulin motar yace abawa yaya uzaifa ita nasa ne yabashi.
Yar nan me kike fada kuma bayan wanan alherin da kuka cika mu dashi a baya sai kawai ta fashe da kuka lokaci guda.
Dakin yai shiru haka ya sakamu muma dake dakin a lokacin sake hawayen daga idanuwan mu sai umma ta bude baki kamar zatayi magana sai kuma ta kara fashewa da kuka mai ban tausayi.
Fadilace da a yanzu take wani ja da baya damu bata sakewa tun dawowan mu na kula da hakan a gareta ta shigo dakin don ta fada muna yaya Uzaifa yaja falon yana jiran fitowa su umma.
Ta samemu a cikin wanan halin na kuka ba maiwa wani magana taja ta tsaya tana kallon mu a cikin mamaki.
Kafin ta bude baki tace haba hjy koma mene ai bai kamata ke ki sare masu gwiwa ba don kukan ki dole ya sakasu a wani hali haka.
Yar nan dole in kuka wanan alheri haka kamar kaika haifi mutum banda baki godiya kukan nan kawai zan iyayi a yanzu.
Mama kiyi hakkuri don Allah haihuwane mai akbarka kukayi shi ya jawo maku wanan yanzu.
Da ace kun haifi wata ba zainab dake da sanin ya kamata ba da duk wanan alheri baku sameshi ba hakkurin ta da dauriya ne ya jawo mata hakan.
Hakane yar nan dadin haihuwa mai albarka ke nan gun iyayye duk wata uwa tsakanin ta da danta tun yana ciki shine adduan samun mai albarka dama.
Haka dai ta samu ta lalashi umma har suka fara shirin tafiya a falo suka tsaya jira shi ya fito suyi ban kwana dashi.
Sai gashi ya fito a cikin shirin shi na bakaken suith a jikin shi yana cikin ujula yana sauri ganin su yasa yaja ya tsaya suka gaisa.
Nan umma ta shiga mashi godiya bai tsaya ba yace haba ba komai umma na fadawa uzaifa ya dawo wani sati ya sameni nan kafin mu koma.
Kai Alhaji dawainiyar yayi yawa ba mu kadai bane wanan irin alherin haka ubangiji Allah ya saka da alheri kuma ya baku masu rama maku nan gaba ya hadaku da zuri,a masu albarka aka amsa da amin nikan a cikin zuciya na amasa hakan.

Yan uwa ina mika sakon ta,aziyana a gun yan uwan da sukai rashi a cikin satin nan ubangiji Allah ya gafartawa musulmi yakai hasken rahama a kabarin su amin ya gafartawa duk wani musulmi daya kwanta daman shi Allahuma amin.

ZAINAB IDRIS MAKAWAJUMMA,AT MUBARAK YAN UWA MUSULMI UBANGIJI ALLAH YA SADA MU DA ALHERIN DAKE CIKIN WANAN RANAN ALLAHUMA AMIN.
YAR UWA LITTAFIN KUDINE KI BIYA KI KARANTA VIKIN SALAMA DON KARUWAN KANKI DA KANKI YAR UWA, , ,

Kamar yadda maya tayi min alkawarin kirana karfe takwas na dare ina daki zaune saman sallaya ta kira layina din.
Na dauka muka gaisa take fadin yanzu haka tana gidan kakarta don yadda tajini a dazun bata ji dadin haka ba.
Da yake video call mukeyi da ita ta nuna min fuskan kakar nata a screen din wayan ta tsohuwar take murmushi ba yaren su nake ji ba don haka na daga mata hannu alaman gaisuwa a gareta .
Bayan mun gaisa din takewa maya yare mayan ta kalloni tana fadin wai me ye damuwana a yanzu ido na dan lumshe kafin na sauke ajiyan zuciya na fara ba maya din bayani ita kuma tanawa tsohuwar kamar yadda nake fada mata.
Daga ta bata fuska sai ta dan kada kai tsohuwar keyi don jin bayanin da nakewa maya din.
Saida na gama ta fara magana tana dan tafiya a duduke zuwa wurin da take aje maganin ta ta dauko ta juya tanawa maya magana.
Maganin naga maya ta amsa a hannun ta tana nuno min tare da fadin wai ki duba irin wanan maganin ta baki irin sa kwanaki.
Shi zaki dauko kiyi amfani dashi a yanzu ta bude maganin tare da nuna min shi sosai a screen din wayan ta nace nagane.
Ta sake fadin zaki jika mai a ruwa har sau uku daga nan ki bar bashi sai tsohuwar ta katse ta da bayanin da takeyi din ta fara magana tana nuna mata wani farin garin magani dake hannunta.
Nan dai sukayi min bayanin komai na yadda zanyi amfani da magugunan data bani a kwanaki da na tafi masu sallama zamu dawo Nigeria.
Don ni na barsu kenan a nufina bazan sake komawa kasan chaina din ba kuma a yadda na yanke a zuciyana.
Bayan mun gama wayan ne dasu ba nufi wardrobe dina ina binciken inda na aje maganin da tsohuwar ta bani din.
Suna ajiye kamar yadda na ajesu daya bayan daya na duba ko wani na dauko na dawo bakin gado na zauna ina kallon maganin.
Can kasan zuciyana nace Allah kaga nufi a kan hakan banyi don na raina ma yin ka ba ya Allah ka gafarceni akan hakan idan na saba maka .
Kasa wanan karon iyakar wahalance ga hakan kasa mu dace da nasarorin ka ya Allah na fada ina shafa hannuna a fuskana.
Tashi nayi daga inda nake zaune din na nufi inda wasu cup suke ajiye na dauko tare da goran ruwa na zauna a inda na tashi din.
Ruwan na fara zubawa a kofin na daga tare da karanta fatiha kafa bakwai a cikin sa don ance kome ke damun ka fatiha na maganin sa da yardan ubangiji.
Na kawo garin farin maganin na dan zuba a cikin sa kadan na fara karkadawa kafin in daga in kai bakina da bissimillah.
Na gama duk yadda ta fada min din inyi bayan na kamallah na koma na kwanta saman gadona ina mayar da numfashina a hankali.
Ina nan kwance ido a rufe naji an turo kofan dakin an shigo na bude idona a hankali sadiyace ta shigo tana fadin anty kin kwantane da wuri haka yau.
Zan tashi yanzu na bata amsa ina mikewa tare da fadin kin ci abincine tace min bata ciba muje yanzu muci na fada a daidai lokacin dana sauko saman gadon.
Mun zauna falon ke nan ya shigo fuska a daure nice na fara mashi sannu da zuwa wanda hakan ya bashi mamaki don ya dauka a yadda muka rabu da rana ina cike dashi a ranan.
Haka yasa yaje gidan mami ya zauna abinsa ya yini a can bai dawo ba sai wanan lokacin daya shigo gidan.
Duk da hakan bai tsaya a falon ba ya nufi part din shi kai tsaye bayan ya dan tsaya yana amsawa sadiya gaisuwa tare da tambayan ta tana lafiya ?
Baifi yan mintuna a tsakani ba na mike tsam ina fadin sadiya ina zuwa na nufi part din nasa nima.
Na sameshi tsaye a tsakar dakin yana cire rigan jikin shi na karaso inda yake ina fadin yau ina ka shiga har wanan lokacin ?
Ina gidan mami ya bani amsa kai tsaye a yadda yake amsa min din naji ba dadi gaskiya saidai na hade hakan a raina na kara takowa har inda yake ina fadin .
Suna lafiya ya yaran ya mamud basu zo badai gidan nan har na tambaye shi don rasa na fadi a lokacin .
Kema kinsan uwarsu ba zata bari suzo gidan nan ba din har yanzu fushi takeyi dani bata zuwa ko naje gidan.
Ikon Allah me yai zafi haka a tsakanin ku ta dauki fushi dakai haka hummm kawai yace yana kokarin wuceni ya shiga bayi.
Ya kai kofan bayin duk a cikin daurewa nake fadin mu jirakane ka fito muci abinci na tambayeshi don karfin hali don kawai in nuna mai yanzu ba haka zancen yake ba a guna.
Naci abinci gidan mami a koshe nake ya fada yana shigewa bayin kai tsaye nabi bayan shi da kallo.
Kafin ajiyan zuciya ina mai jin zafi a raina tare da tunane nabar dakin nasa watau mu mata a zalunce mu kuma mu koma bi da biyayya garesu Allah sarki diya mace ubangiji Allah kaiwa mata rahama albarkacin Annabi Mohammadu sallalahu alaihin wasallam.
Falo na dawo na zauna a dinning muka fara cin abincin da aka shirya na dare don mu a gida.
Mun gama hira muka danyi kafin kowan mu ya mike zuwa part di shi har lokacin banga ya leko mu ba .
Haka yasa na gane cewa bazai fito di ba ke nan yake nufi ina shiga daki na fada bandaki nayi wanka na fito na shirya tsam kafin in saka rigan barci na dauki abinda kakan maya tace min in shafa bukata kawai ko bai shafa bashi yaji kakshin shi dab a hancin shi dai kawai ko hakan ya wadatar.
Sosai na mulke jikina da maganin nabi da dan turare a sama saboda kar kamshin maganin ya tashi sosai.
Na dan dade a zaune ina tunanen hanyar da zabibsakon ya isa a hancin shi duk da nasan abune mawuyaci yin hakan garemu a yanzu.
Can dai na daure na mike na dauki hijab din sallah na na dora saman jikina kamar yadda na saba yi idan zan shiga part din.
Bakina tab da addua kamar kullun na nufi part din nasa kofan yana bude har lokacin na shiga jna rufo kofan a hankali nasaka key narufo kofan.
Kwance na hango shi rigingine ya na saye da jallabiya a jikin shi ya dora hannu a fuskan shi kafaduwab shi suna a harde yana dan kada su a hankali.
Duk da nasan ba barci yakeyi ba a lokacin hakan bai hanani tafiya a hankali ba motsi ba na karaso har baki gadon da yake kwance din sama.
hankali nakai zaune saman gadon har lokacin ina kan adduan da nakeyi a lokacin na gama na tofa tare da shafawa a jikina nayi bissimillah na hau gadon da kyau tare da dan jawo jikina zuw inda yake kwance duk da ban taba masa hakan ba sai wanan ranan.
Kaina nakai saman kirjin na dora lokaci guda yayi wani irin zabura yana fadin kanki daya kuwa zainab ?
Sau nawa nake fada maki idan har bukatan hakan ya taso min da kaina zan nemeki da hakan.
Ikon Allah na fada a raina kafin a fili ince dashi ban kwanta a nan don wani feeling ko wani abuba na kwantane kawai don in dan samu sauki a zuciyana a wurin dan uwana don kawai naji dumin wani ajikina.
Ba tare da yai magana ba ya kai hannun shi da zuman bambareni a jikin shi na kara lafewa kamar da gaske a jikin nasa.
Da karfi ya fincikoni zuwa gefeb shi ya juya yana wani irin mayar da numfashin sa da dan sauri kafin can inga ya mike zuwa ban dakin.
Shiru shiru bai fito ba sai zuwa can ya fito da alaman ruwa a jikin shi yayi wanka ke nan a lokacin don kawai na dan taba shi din ya watsa ma jikin shi ruwa a lokacin.
A hankali na mayar da idona na lumshi jin bai hawo gadon ba a lokacin yasa na bude idona yana tsaye gaban mirrow yana faman goge jikin shi.
Tabdi jam ashe abin bana wasa bane na fada a raina ina kara gyara kwanciya har barci ya daukeni ban sani ba lokacin.
Kodana falko a cikin dare na hangoshi can saman kujera kwance kuma har lokacin baiyi barci ba idanun shi biyu da waya a hannu shi.
Tashi nayi zuwa bandaki na dauro alwala kamar yadda na saba yi a kullun don Nafilan dare.
Sai zuwa can ya shiga ban dakin nan ma dai irin abinda yake ji yaji a ban dakin ga kanshi yayi wani irin daure mashi lokaci guda haka dai yaja kafan har ya fito.
Yau ba mafalkin asalima tsorone kawai daya ziyarci zuciyar shi haka kawai yake jin kamar tsoro yake ji saidai baisan na meye ba a lokacin.
Saida yai sallah raka,a hudu ya dan samu saukin abinda yake ji a zuciyar shi muna wurin har akai kiran sallah asuba .
Nayi sallah kamar kullun nabar dakin zuwa dakina sai dai abin mamaki ba kamar yadda ya saba tashi a cikin kuzarin shi ya tashi ba a yau.
Gashi nan so wick dashi bai son magana da kowa a ranan karshe ma ya kwanta yana barcin rana abinda bai taba yi ba ke nan a sanina dashi .
Koda kuwa baida lafiya baya barci da rana saidai ya rufe idon shi kawai na dan lokaci ya bude .
Allah ka tsare muna rayuwan mu daga fadawa a cikin halaka saboda duniya ko neman wani abu makamancin hakan.
Duk da irin halin da nakw ganin shi baisa na fasa shafa wanab magani ba insha kuma a nasa bangaren kuma sam ya rasa gane lafiyan jikin shi sam.
Shidai yasan cewa lafiyan shi kalau baya jin ciwon jikin shi tako ina amma kuma yawan kasala da damuwa ya hanashi sukuni ko kadan.
Ban dada ba ban kara ba a yadda aka ban lokaci da zanyi amfani da magani in bari daga nan kuma aka sake dorani kan wani da zan fara.
Nikan garin ceton wani naga ta kaina yar uwa sai dai abinda zance yanzu gaskiya kamar yadda malam ya fada min ne naga sauki sosai ga harkokin ya jafar a yanzu.
Ranan ya shigo da rana yake fadin in shirya zamu Samunaka mu duba hjy bata jin dadin jikin ta su mami sun tafi mu zuwa yamma jirgin mu zai tashi.
A rude na dago ina fadin subbahanallahi har ciwon yayi serious hakane sosai yace ance sosai ne ciwon suna can dai sun tafi su dubo.
Ya na fadin haka ya juya ya fita daga dakin nan ya barni ina jimame akan tsohuwar har wani lokaci kafin in mike in fara shirin tafiya .
Bayan sallah la,asar ya shigo yana fadin ba zamu tafi din ba mami tace mu dakata zasu zo da ita nan Abuja yau din nan.
Sai naji hankalina ya kara tashi sosai ba abinda nakeji sai rashi zuwa ganin ta da banyi ba gani har kaduna amma ban samu leka wurinta ba har na dawo.
Tunda ya fita bai dawo ba ranan har dare sosai haka yasa nasan yana can wurin su hjyn ke nan a lokacin nasan sun iso da ita Abujan kenan tunda yakai wanan lokacin haka a waje.
Har na gama komai na shiriya zuwa dakin shi na kwanta ni kadai a dakin ina addu,in dana iya a bakina.
Barci ne ya daukeni na dan lokaci sai gashi ina mafalkin wasu mutane masu bakaken kaya duk jikin su sun saka hulunan kayan saman kawunan su.
Wanda duk yazo ya wuni a inda nake tsaye ina kallon su din cikin mamakin me ya kawo ni nan kuma su din su waye ?
Fuskan dayan abokain shi philis na gani na gane a lokacin ya daga hannu kamar yana warning dina Allah ya taimakeni na furta Au,zubikalamati min sheri min halak .Lah illa ha in,llah anta subahanaka inni kuntun minal zalumin ya wani yanka ihu duk sauran suka kallo mu sai na juya da sauri nabar wurin.
A daidai lokacin kuma na falka daga barcin sai wani irin zufa dake fita a jikina don wahala na mike zaune a firgice ina bin dakin da kallo a tsorace.
A daidai lokacin kuma kiran wayan jafar din ya shigo wayata saida na dan zabura don tsoron da nake ciki a lokacin.
Na kai hannu da kyar na dauki wayan yana fadin kina inane haka nace dakin ka na kwanta ki koma dakin ki yanzu har in dawo ya fada a cikin comand ya kashe wayan.
Wayan nabi da kallo tare da kallon lokaci karfe biyu na dare da wasu yan mintina a lokacin.
Na mike da sauri zuwa dakina banko rufo kofan dakin da kyau ba wurin sauri don ba karamin tsorata nayi ba a lokacin gaskiya.
Ban kwanta ba na shiga ban daki na dauro alwala na tayar da sallah na dade zaune ina karatun kur,ani naji dawowan shi gidan uku da darabi koda ya shigo.
Dakina ya fara shigowa tun daga kofa yake jin kira,a na har ya karaso tsakiyan dakin inda nake zaune yana fadin.
Mesaya kikaje dakina ke kadai a wanan lokacin na dan dago kai na kalleshi na mayar naci gaba da abinda nakeyi shima ya juya ya fice a dakin da saurin shi.
Kafin asuba wani irin zazzabi mai karfi ya rufeni lokaci daya haka nayi sallah a dadafe na koma saman gado na kwanta.
Rufe nake ina nishi da kyar sadiyace ta shigo ta sameni a wanan halin hankalinta ya tashi sosai ta juya da sauri zuwa part din shi ta fada mai halinda nake ciki.
Tare suka dawo dashi yana tambayan ya nake ji nace zazzabine kawai nakeji a lokacin ya fita sai gashi da magani ya kawo min nasha yana zaune har ya dan fada min.
Sai lokacin nake tambayan shi jikim haji yace taji sauki daya barsu jiya da dare yanzu zai koma yaga jikin nata kuma.
Wani asibiti take na tambaya a cikin karfin hali ya fada min tare da fadin kada kice zaki a wanan halin ki bari sai kinji sauki ya fita.
Bayan fitan shi zazzabin ya taso min sosai na ce sadiya ta ban ruwa na karanta fatiha a ciki nasha sai barci ya dan daukeni a lokacin.
Mafalki marasa kyau na dinga yi a wahalce dai nayi barci sosai a lokacin koda na tashi na dan samu sauki har nayi wanka.
Na fito na shirya don zuwa duba hjy don tana raina a lokacin sosai mu uku muka tafi da sadiya da fadila zuwa duban ta sai abinci da kayan marmari da muka saye a hanya don mu kai mata.
Kusan kowa na asibitin a lokacin don bayan sallah la,asarne lokacin mun shiga mun gaisa dasu tana kwance an daura mata ruwa ana kara mata.
Mama Ramatu ke fadin dazun mijin ki ke fada muna baki da lafiya ai nace naji sauki ne na taso gashi a lokacin wani zazzabi nakeji da sanyi a jikina.
Mami dake gefe zaune tace ya dai fadane kawai don ya kareta wani zazzabi kika gani a nan don Allah.
Kai haba yayan mu kika sani ko alherine ya samemu ake wanan zazzabin yanzu haka ai wasu haka suke laulayin cikin su dama.
Dakin yai shiru ba wanda yai magana a lokacin mamice ta sake fadin ai bata da niyar baku jika ta zauna suna jin dadi idan suka hadu da fushina watarana maganin su zanyi ai.
Da yafi mami tunda ita bata iya haihuwa ai hara a kawo wace zata haihu muna Aisha ta fada fadila ta karba da fadin Allah ne bai kawo ba hjy komai dan lokacine ai.
Wanan kina min shishigi da yawa mami ta fada abin mamaki a lokacin hjy akaji muryanta tana fadin iyami ko bayan raina kikasa jafari sakin yarinyar nan ban yafe maki ba.
Dakin yayi tsit ana sauraren hjy kafin Aisha tace dama na fada maku ai ji wanan tsohuwar da kowa ya rude a kanta tun jiya batayi magana ba yanzu take fadin haka.
Sai aka kwashe da dariya hjyn da take kwance take fadi cikin karfin hali zo nan kiji kawata inji dumin ki kusa dani tana kokarin mika hannun da ake mata karin ruwa dashi gareni.
Kai hjy da zainab sai Allah a tsakanin ku Na,ima ta fada tana fadin to mu din da baki damu da jin dumin mu ba sai mu tafi tunda zuwan mu baida amfani a wurin ki.
Ni dai na taka zuwa bakin gadon na riko hannun tsohuwar ta rike gam tana fadin zauna a nan kinji ko suna so ko basu so kin shigo cikin mu ke nan.
Muna zaune a haka sunawa junan su sheri suke fadin albarkacin bakin su kan hjy mazan suka shigo ya jafar yana ganin mu a dakin yake fadin.
Zainab kin iya tasowa ne yanzu naje gida bakwacen ake fada min kunzo asibiti ya mamud ne ke min sannu da jiki yana gaida ni har su jamal din kasa nayi su lokaci guda akaga na sunkuya kawai dama ni kadai nasan yadda nake ji a lokacin karfin haline kawai nakeyi a hakan.
Tsale daya ya jafar yayi ya kai gareni ya rungumoni na some a lokacin ban sab inda nake ba kuma sai hankalin su ya fara tashi.
Da sun dauka pretending nakeyi a lokacin har mami tana jan tsuki jamal ya fita da sauri ya kira likita yazo dashi dakin likitan ya duba yake fadin dama bata da lafiya ne haka har jinin jikin ta yana batun konewa duka.
Lokaci daya mami ta mike tsaye cikin furgicin jin abinda likita ya fada a game dani yana kiran nurse da sauri yana fadin a shirya daki a kaini ciki nan hankalin kowa ya tashi kuma.
Mami da kanta ta rikeni har dakin da aka kwantar dani duk bansan wainar da ake toyawa ba a lokacin sadiya kan kuka ta saka masu tana ihu ganin halin da nake ciki.


ZAINAB IDRIS MAKASSALAMU ALAIKUM WARAHAMUTULLAH YAN UWA FATAN ALHERI A GAREMU BAKI DAYA ALLAH YA SADAMU DA ALHERUN SA AMIN, , ,

LITTAFIN KUFINE KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA YAR UWA DON GUJEWA SHIGA HAKKIN WANI, , , , ,

Naga maki da al,ajabu a cikin yan kwanakin nan don ranan dasu umma suka tafi ranan munyi barci a tsaye a dakin don ni kaina tsoro aka fara bani ina tsaye da kiran Allah.
Saidai abinda ke ban mamaki a yanzu shine a lokaci yaya zai koma kamar bashi ba amma in gari ya waye sai ya dawo min mutum daidai kamar bashi bane muka kwana a raye yana min saddabarun a cikin dare.
Sai gashi gari ya waye ya koma kamar bashi ba da zarah biyar tayi daidai lokacin da za,a fara kiran sallah ya fara samun sauki lokacin gari ya fara wayewa ke nan.
Ina kula da hakan tun fara kwanana a dakin shi a daidai wanan lokacin ne yake samun natsuwa ya koma normal kamar kowa.
Kamar kullun dakina na nufa ina idar da sallah ban tsaya jiran wani abu ba na haye gado sai barci a ranan nayi barci sosai.
Don ban tashi ba sai after one na rana koshi nasan don sabo da lokacin sallah ne duk inda musulmi yake da zaran wanan lokacin yayi zai fara ji a jikin shi.
Wanka na fada kodana fito time din yayi har ya gwauta a gurguje na tayar da sallah din don makaran da nayi.
Ina zaune ina shafa mao a gaban mirrow dakina ya shigo dakin a cikin madubi muka hada ido dashi nayi saurin dukar da kaina a kasa.
Kin tashi ke nan ai na zata har yanzu din barci kikeyi baki tashi ba da zance dake kada ki kwana a dakin sai ki dauki hakab da wani manifa a zuciyar ki.
Ko yanzu din da idona ya gane min gaskiya bashi zaisa in fasa kwana a dakin ba komai shedancin mutum dai ai Allah ya fishi.
Gaskiyane amma kuma Allah baice ki kusanci abinda zai iya ja maki illa ba ai zuwana biyu dakin nan kina ta barci baki tashi ba.
Idan har zan samu barcin da rana inyi na daren ba damuwa bane matukar addua akan hakan zai muna tasiri ai.
OK ina maki fatan alheri ga hakan na ce amin kamar a fusace ya sake dan murmushi ya juya zai fita daga dakin sai kuma yaja ya dakata yana fadin.
Zan so tunda kin fara fahintar hakan kiyi nisa dani kamar yadda na umurce ki dayi tun farko kada ki jefa kanki ga halaka.
Ban fahinta ba nace a cikin mamaki na juyo da sauri ina kallon shi kafin in ce dashi.
Ke nan hakan na nufi in barka har abada ko me don magana kayi min a dunkule wanda na kasa fassara ma,anan shi yanzu ?
Da zaki dauki shawaran da zan baki zaifi maki sauki a rayuwan ki ki zauna kamar yadda na umurce ki da nisantana tun farko.
Saida na sake wani irin laulausan murmushi a fuskana na mike tsaye na fuskan ce shi a lokacin saboda tsaban rudewa na manta da daura gaba nake tsaye a gaban shi don yadda nake ji nace.
A yanzu idan har zanyi hakan dayan biyune zai biyo baya kodai na nisance ka har abada ko kuma kai din da kanka ka rubuta min takarda shedan ka sakeni in koma wurin iyayyena da zama.
Shima murmushin ya mayar min kamar yadda nayi masa da farko yace kina ban mamaki a yanzu da wanan taurin kan naki zainab.
Idan wani ya fada min ke din zaki iya hakan a baya zan iya mussanta masa hakan akan bai fahince ki bane ya fadi hakan.
Zaka iya fadan komai saidai amsan bukatana nake saurare a yanzu don hakan nima ya isheni don ban san a matsayin da nake a zuciyar ka ba har yanzu.
Zaki iya fadan komai a yanzu zainab mutukar ba zaki daukeni a matsayin makiyin ki ba dai yana fadin haka ya juya ya fice rai bace.
Na bishi da kallo ban san lokacin da wani irin kuka yanzo min ba lokaci guda don takaici bakin gado na koma na zauna ina hawaye ni kaidai.
Sai faman tunane da nakeyi na yadda mutane su a wajen su suke min kallon wace ta dace da mijin aure .
Basu san cewa ABU A CIKIN DUHU SIRINE BA da ace zan zauna in fada wa wata irin rayuwan tashin hankalin da nake ciki tun shigana gidan sa da mata da yawa sun gane ba daula ne arzkin da mace ke cikin shine zamana jin dadin aure ba a yanzu.
Eh nasan da yawa kan sun dace amma akwai irin mu da ke cikin jarabtan aure ta hanyoyi daban daban a duniyan nan.
Sai dai muce ubangji Allah ya kawo muna dauki ya fitar damu da ma wa yanda basu shiga ba amma yana zane a kundin kaddaran rayuwan su sauki.
Na gaji da kukana ni kadai na kuma ba kaina hakkuri na mike na saka dogon riga haka kawai naji zuciyana yana son kiran maya a ranan.
Duk da zuwana Nigeria na kirata sau biyu mun gaisa take fada min cewa ta samu aiki a wani karamin company yanzu ta fara aiki a nan.
Saida kiran ya kusa katsewa ta daga tana fadin inyi hakkuri bata kusan da wayan ne a lokacin.
Mun gaisa nake tambayan ta aikin ta da iyayyen ta ta amsa da kowa lafiya aiki kuma tana nan tanayi saidai wurin bai mata ba idan ta samu wani zata canza.
Nake dan bata hakkuri akan tayi hakkuri dashi for now don ta rage zaman banza hakana tace hakane.
Ya kuke ina mijin ki da sady nace suna lafiya ta kara jefo min tambayan dake cina a raina tace muryan ki ya nuna min cewa kinyi kuka yau zeey ?
Dan murmushi na sauke har tana iya jina a lokacin naji tace why zeey why da zaki zauna kina kuka akan abu daya kullun.
Nasan dai a kan halin sane kike kukan naki ko zee nace a cikin muryan kuka maya kasheni yake son yi kawai nan dai na fara kora mata labarin komai da ya faru zuwan mu gida.
A karshe ta ban hakkuri tana fadin in bari idan taje gida zata kirani muyi magana yanzu tana wurin aikintane.
Mukai sallama da ita na kashe wayan ina ajiyan zuciya na mike na nufi hanyar fita daga dakin dakin sadiya na fara lekawa bata cikin dakin .
Na nufi falo kai tsaye don nasan tunda ban ganta a dakin ba tana falo ke nan a nan na sameta zaune tana kallon wani film.
Kallon ta nayi watau sadiya dai sai gyara Allah ranan da wanan daulan ya subce muna muka koma gida da zama.
Don duk dabi,un ta na diyan masu kudine ita ba zakace gidan mu ta taso ba a lokacin saboda irin rayuwan da na hango a gareta.
Har na karaso kusa da ita bata sani ba jin takon mutum ta juyo da sauri tana fadin lah anty ashe kin tashi na shiga daki kinata barci.
Remote na duka na dauka saman table na kashe tv ina fadin tashi kije kiyi sallah kada in saba maki yanzu na fada rai bace.
Ganin ba wasa a fuskana don wani lokaci mukanyi wasa har da kokawa a tsakanin mu idan mun bushi iska a tsakanin mu.
Wanan karon kan babu wanan sakin fuskan a gareni don haka ta mike tsam tana turo baki ta bar falon.
A hankali na juyo bayan na gama binta da harara ina sake ajiyan zuciya na kai zaune dan table din dake kofan na jawo na dora kafana .
Ko zanji dadin zama a hakan ta hanyar mike kafafuwana saman dan stole din na dora hannuna saman fuskana .
Ina zaune shiru ban motsa ba ban kuma kunna tv ba don komai bana jin dadin shi a lokacin sai wani tunane yazo min.
Tambayan kaina nayi wani makusamcin shi zan fadawa damuwana ne da zai duba min wanan zancen
Amsa naba kaina da fadin ya mamud shi ya cancanci in fadawa don yasan halin da dan uwan shi yake ciki a yanzu.
Na dawo naba kaina amsa da kaina da fadin in kuma na fada mai ai kamar na tonawa kaina asirine kuma.
Hujja dai iyayyena suke so a gareni ko yanzun kuma ina da babban hujan da zan basu ai akanshi.
Zancen mu da innan mu ya fado min a rai da take fadin nayi hakkuri na zauna dashi ko dan mahaifiyar shi da basu sona dashi ya nace min.
Da wanan bakin nacin ai gara shima ya kini din zaifi min dadi na bawa kaina amsa ni kadai muryan fadilace ya katseni tana fadin .
Ashe kin tashi lafiya dai kike ko nayi mayawa da mayanni don mu gaisa kina kwance.
Hannuna na sauke ina fadin lafiya kalau nake take fadin an wuni lafiya abinci har yayi sanyi baki karya ba.
Barci ne ban samu sosai ba a dareb jiya yasakani wanan barcin dan ruwan zafi zan kurba ya isheni koshi hanjina nake son ya bude.
Ta juya da sauri bata jima ba sai gata da kayan shayi ta hado min ita da kanta ta hada min komai nace nagode har ta juya zata wuce nake fadin.
Ya yaran ki kin samu lekasu kuwa jin haka yasa ta juyo tana fadin ko gafarceni don Allah nasan kinsan komai a kaina don oga ya fada min maganan daya girgizani a ranan.
Na dago da sauri ina tambayan ta akan mefa don bansan abinda kike magana a kaiba yanzu ?
Kai ta dukar kasa sai naji wani iri naci gaba da fadin indai akan matsalan mune ki barshi kawai dani don yanzu ba da bane nasan ciwon kaina a yanzu.
A hankali ta dawo inda nake tana zama take fadin zan fada maki magana daya zainab ko ki yarda ko kada ki yarda Allah ya sheda har cikin raina gaskiya daya nake fada maki.
Sai tayi shiru kafin tace dani duk yadda kike ganin munin halim mijin ki zainab ki hakkuri ki zauna dashi hakana da halinsa.
Duk da nasan a yanzu ba lalai bane ki yarda da zancen da zan fada maki din don kin san koni waye a wuri ku yanzu tynda mijin ki ya sani ya kuma fada min yasan zamanan aikin da nakeyi gidan nan tare daku.
Jin hakan na dago kai na dan kalleta da mamaki don jin abinda ta fada din a lokacin a raina nace ke nan ya jafar ya sanar da ita mun san zaman da takeyi a tare damu ke nan.
Tace haka ba zai hana ni zama daku tsakani da Allah ba zainab don ni musulmace kamar ku ba zan taba bada shedan karya akan abinda banga makamancin shi a wurin ku ba gaskiya.
Nazo nan aikine bisa zargin da akewa mijin naki da yin fasa kwari da sauran abubuwa na rayuwa don gani shi da da mahaukacin kudin da kasa suke zargin shi dashi.
Sai dai zamana din don bincike a cikin ku zainab na gano mijin ki tsayayyen mutum ne wanda ya tsaya da kafan shi wurin nema ya kuma dage da aikin shi kuma da kafafun shi yana neman na kasa ba kamar yadda ake tuhumar shi din ba.
Yawan kyautatawan ku gareni yasa ni kaina na fara zargin hakan kafin in binciko komai na gane gaskiya .
Yanzu nazo maki nan ne a matsayin yar uwa kuma aminiya kamar yadda kika rikeni a baya a matsayin yar uwa kuma aminiya saidai yanzun da kika san koni din wacece ba ki dauke hakan ba ayanzu sai dai duk da hakan.
Zanso kiyi hakkuri ki kuma kara hakkuri ki zauna da Jafar har abada a rayuwan ki don shine kawai yanzu mafita a gareki da rufin asirin ki.
Zainab abinda baki sani ba shine kina fita gidan jafar kema kanki mutane zasu kyamace ki idan kowa yasan irin rayuwan da kika guda a gareshi har ki barshi.
Sai zargi ya fara yawo a zukatan mutane a kanki cewa ta yaya kika zauna dashi na tsawon wanan shekurun a cikin wanan halin nasa ?
Kaina dago da sauri na kalle ta tare da zuba mata ido don jin abinda ta fada zai iya faru game dani nan gaba idan nace zan bar gidan shi tace eh haka zancen yake gaskiya a wurin mutane.
Shi mutum dan tara ne bai cika goma ba kowa da kike gani yana da nasa kalar jerabawan rayuwa da Allah ke dora mashi sai idan Allah na son kane .
Karshe sai ya yaye maka wanan jerabawan ta hanyar sauki da lumana Allah ya jefoki a rayuwan mijin kine do ki taimaka masa kuma kina taimakawan ba laifi.
Don ba ko wace mace bace zata zauna tayi hakkurin shekaru kamar yadda kikayi zainab don koni din da nake magana ba lalai bane na iya hakan.
Nasan jafar yana da rauni duk da baki fada min ba nasan komai don kin san aikin mu bawai kawai saka ido bane ga binciken da mukeyi akan mutum ba kawai mu leki asirin aikin daya kawo mu wurin mutum mu barshi.
A, a komai daya shafeka sai mun gane a lokaci guda a irin hakane na gano mijin ki ba mai sha,awan mata bane shi a rayuwan shi.
Zaman turai da kuma miyagun abokai ya bata rayuwan mijin naki da kuma asiri irin namu na bakaken mutane ya bata rayuwan shi duk da hali irin na kyautatawa nasa.
Sai da ya samu akasi a rayuwa yana wanan aikin da ko wani addini da al,ada bai yarda da irin wanan fasadin ba a doron kasa.
Ki godewa Allah daya nufi mijin ki da samun rayun shi a yanzu ga daina wasu halaiya nasa masu muni da yakeyi a baya can .
Duk da mahaifiyar shi ce ya dace tayi hakan amma ta kasa tsayawa ta duba rayuwan dan nata sai shirme da zugan mutane da ke rudin hankalin ta.
Hakkuri gareki zainab shine mafita a yanzu don ki girbi wahalan ki da hannun ki idan kinyi sake kinaji kina gani sai watace zata zo daga baya taci gajiyan wanan hakkurin naki a gaba.
Nasani zainab mahaifiyar mijin ki na kokarin shirya yi mai aure don a ganin ta ke din baki cancanci zama da danta ba haka matsayin ki dana iyayyen ki baikai na yadda take son matan diyan ta su kasance ba.
Na dago kai da sauri na dan kalleta again tace yes zainab wlh bawai hjy mami bata son ki bane a, a wanan ne kawai ya kawo maku rashin jittuwa a tsakanin ku da ita .
A gabana gidan nan kwanaki dan uwan mijin ki yazo da wanan zancen gidan nan yana fadawa mijiki abinda mahaifiyar tasu take kulla mai wai zata aura mai wata a dole don kare martaban shi.
Sai dai amsan da ya bayar a lokacin shi ya wadatar dani a lokacin na kara sanin kina da tasiri matuka a zuciyar shi.
Sai gashi daga baya kuma kina neman ki bada wanan kafan a garesu suyi yadda suke so a kanki.
Don duk da sanin halin danta da tayi kin san ance uwa bata taba ganin laifin danta kome akace ya aikata zataga sheri ake masa don tarbiyan data bashi ita kadai tasan halin shi.
Wanan matsalan ke damun wasu uwaye a yanzu da basu tsayawa su natsu su san yanzu da zamani komai ke tafiya a yanzu.
Duk da nasan sheri shedan ne da har ya rudeki kike ganin bari gidan nan shine mafita a gare ki da har zaki iya gudu ki bar dakin ki wata tazo ta gaje daga baya.
Kada kiyi mamakin yadda nasan hakan duba da irin shakuwan dake tsakanina dake a baya yakai har mijin ki yake zargin nasan wani abu a game da tafiyan naki .
Shine ranan ya titsiyeni a nan falon yake min warning kan na fada mai inda kika shiga a kasan nan kika boye ?
A lokacin gaskiya hankalina ya tashi sosai da jin haka da nasan zaki aikata hakan da na baki shawaran karki soma yin hakan a yanzu.
Inda na kara tsorata da zancen sai nake ganin suna yawan shigowa gidan nan akai akai na gane hakan da takeyi na son cusa mashi wani manufane na daban a lokacin.
Sai gashi Allah ya gyara kin dawo kwatsam a lokacin da kowa bai tsamaci hakan ba da zaki dawo a kan lokaci ba tare dana waje sun fahinci komai ba.
Ko suma na gidan kansu ya daure da ganin kin dawo salin alin duk da akarshe hjy mami cewa tayi kwadayine ya dawo dake gidan nan ai.
Ido na lumshe dama nasan zata fadi hakan a kaina koda banji haka a bakin fadila ba din nasan abinda mami zata fada ke nan kan dawowa na din a lokacin.
Ta dan motso kadan daga inda take zaune takai kai hannun ta saman gwiwana ta dafa haka yasani bude idanuna dana runtse a lokaci guda don takaicin kalami mami a gareni da nake ji a lokacin har kasan raina.
Hakkuri zakiyi zainab kowa da irin tasa kaddaran a rayuwa wata kila Allah ya jefoki a cikin sune don ki zamo masu haske a nan gaba ita bata sani ba ta tsaya tana hauka a yanzu.
Ki nuna komai bai dameki ba zainab kibar nuna bacin ranki haka a fili don ko zaman da kikayi nan na fahinci abinda ke damun ki ke nan yasa kikaji ina maki wanan bayanin haka a yanzu.
Nasha fada maki ke di mace ce zainab kin kuma nunawa duniya ke mace ce don kinyi amfani da iliminki na mata gashi yau har kin kai ga taka nasara akan shi kin rabashi da wasu halaiya masu muni a rayuwan shi.
Koya sani a yanzu ko bai sani ba shi da duk wani nasa dole a karshe zasu san hakan da cewa ke din ce haske a garesu kinyi namiji kokari sosai kiris ya rage ki kai ga in ma nasara ki akan komai da yardan ubangiji.
Tana fadin haka ta mike tare da fadin ni zan tafi don yan kwanaki ya rage min a gidan nan zamana ya kusa karewa daku tynda na gama hada abinda nazo samu a wurin ku din.
Sai dai ina fatan zaki bi shawaran dana baki din kiyi amfani dashi don Allah kada ki bari kowa yasan zaman da kikeyi a gidan nan yanzu a bar ABU A CIKIN DUHU YA ZAMA SIRIN KA KAI KADAI.
Tana fadin haka ta juya zata tafi da kyar na iya budan bakina nace mata nagode anty bayan hakan ban kara furta komai ba akanshi.
Hanyar kitchen ta nufa na bita da kallo a inda nake zaune ina mamakin wasu zantuka da tai min yanzu din a karshe.
Tabbas ABU A CIKIN DUHU din ne kuwa zama a gidan yaya jafar din don mutane na min kallon jin dadi da samun duniya a gidan shi yanzu.
Ni kuma ina zaman hakkuri da danne zuciya akan tayuwan wani don duk wanan hangen da mutane suke min bashine a gabana ba yanzu.
Zakaji duk wani na tare dani zai ga kamar don abinda mami din take min ne nake son barin gidan a lokacin har iyayyena da suke ganin wanan ne ya tayar min da hankali har nake son yiwa jafar din sheri akan wai baya kwana dani.
Kwana dani ba shine a gabana ba mutane sun ki su gane hakan a gareni maganan fadila din ne don ya zama dole inyi hakkuri in bar zancen a raina koda hakan shine ajalina a gidan nasa.


ZAINAB IDRIS MAKAWAAWAFATAN ALHERI GARE KU DUKKA MASOYANA NAGAISHE TARE DA FATAN NASARA GA DUKKAN AL,AMURAN KU NA YAU DA KULLUN, , ,

KISAYA YAR UWA KI KARANTA A CIKIN LAMUNA KADA KIJI KYASHIN BIYAN DARI UKU DON KARUWAN DA ZAKI SAMU A CIKI YAFI KARFIN HAKAN ALLAH YASA MU GANE HAKAN AMIN, , , ,


A rude suke sama kaina saida likita ya zo ya rokesu dasu fice a dakin su dubani suka fara fita daya bayan daya tare da tarin tambayoyi a zukatan su.
A bangaren ya jafar sai fuci yake yana fitar da iska a baki da hanci don takaici irin yadda yake ji a zuciyan shi lokacin don yasan abinda ke damuna a lokacin.
A bangaren mami kuma ita a nata zaton tunane takeyi kodai jafar din ya samu lafiyan da har na samu ciki a yanzu ne .
Hakama yan uwanshi da suka san da zancen suke zargi suma sai dai ya jamal ne da hankalin shi bai kwanta ba sam don zargin bai dauke shi da muhinmanci ba sam.
A karshe fita yaya jafar din yayi zuwa bayan don yai waya a kuma daidai lokacin Aisha taji tausayin sadiyana dake ta rusan kuka ta jata zuwa bayan.
Da farko bata dauka shi bane yana fadin na fada maku tun farko kada ku taba min yarinyar nan kuma kun sani.
Ta dan dago daga inda take zaune ta hango shi din daine ke magana a waya a hasale saidai bata san da wanda yake wayan ba a lokacin .
Yaci gaba da fadin duk wanda ya tabi lafiyan ta na rantse maku gaba daya dangin shi sai naga bayan su haka yai ta fadin maganganu kafin ya juya ya bar wurin bayab ya kashe wayan nasa.
Jinkin kanwar tasa Aisha har wani irin bari yake a lokacin ta mike tsam tare da jan hannun sadiya suka bar wurin ta hanyar canza hanya.
Kasa zama tayi asibitin take cewa mami ita zata koma gida a lokacin mami tayi mamakin hakan kuma ga yar nata a rude yanayin ta ya canza lokaci guda sai ta dauki hakan ga tsorone kawai yasata hakan yadda ta ga nayi a gaban su.
Har ta fara tafiya ta juyo tana fadin mami kema zanso kizo muje gida akwai abinda nake so zan fada maki .
Aisha kanki daya kuwa ya zan bar asibitu muna cikin wanan halin haka ai saiki sa a zageni idan na wuce.
Haka Aishan ta tafi tabar sadiya tare da fadila a asibitin hankalin kowa a tashe lokacin likita yayi iya binciken shi baigano ciwon komai da yaja min konewan jini ba haka lokaci guda .
Dole wai sai an kara min jini akace a lokacin yace aje a dibi nasa mami tace kai har yaushe ka tashi a ciwo a dai duba na sayarwa a gani.
Kai sam mami ba za,, a kara mata jinin sayarwa ba gaskiya ya fada daga inda yake tsaye cikin tashin hankali kafafuwan shi a harde ya dora hannayen shi saman weast din shi duka biyu.
Jamal yace a je a dibi nawa ai zan iyabawa kowa jini na mami ta kalleshi ta rasa abinda zata fada dole ta kyalesu kawai suka tafi.
A can ma jafar din yaki yarda sai nasa aka diba aka kara min mami tayi fadan hakan sosai don ta nuna mashi bacin rai akan haka har tana fadin idan shi baisan ciwon kanshi bane yake neman kashe kanshi saboda mace su sun dani
Likitan da ya shigone yasa su fita ya fara kara min jinin a jikina sai lokacin na dan farfado har ina gane inda nake ina bin mutane da kallo.
Har dare sosai su mami basu je gida ba sai sha biyu saura na dare suka sauketa a gida don tunda Aisha ta tafi da motan driver bai dawo ba.
Ga mamakin mami ta zata Aisha ta dade da barci a lokacin sai ta iske su a falo zaune suna kallo da yan uwanta.
Tana ganin mami ta mike suka shiga daki tare a gurguje mami tana sauri tana cire kaya a jikin ta zata shiga bayi.
Aishs tace mami ya jikin zainab din da sauki ko tace tana shigewa ban dakin da sauki zainab zaki tambaya banda hjy.
Mami na fada maki da magana wlh kin ki ki saurareni tun dazun wallahi mami akwai matsala akan ciwon zainab din nan.
Ja mami tayi ta tsaya tana fadin wai ban gane ba me kike nufine da magana sai ta kalli kofan dake bude ta mike ta rufo kofan kamar wani zai ji abinda take fadi a lokacin.
Ta zauna ta kurawa mami dake tsaye kofan bayi ido fadi mana ina sauraren ki mami tace ga mamakin mami sai taji yar nata na fadin mami kizo kusa don Allah kiji kada wani yaji mu a waje.
Ikon Allah Aisha meke damuwan ki hakane yau bayan kin rufe kofa wa kike tunanen zaiji kine wai yanzu.
Me kike son fada min har jikin ki ke kyar ma hakane wai tace mami is something serious daya shafe ki wallahi.
Jin haka mami din ta karaso gaban ta yana faduwa don gani yadda yar nata ta tsoroce a lokacin.
Zama tayi a gefen yar nata tana fadin ki fada min gani nazo kusa dake Aisha sai Aishan ta dago kai ta kalli mami din gaban mami ya kara faduwa ganin idanun yar nata tab da hawaye lokaci guda gaba daya hankalin ta ya tashi
Mami ko kinsan ya j yana cikin kungiyan asiri kuwa what mami ta fada da karfi kafin ta fara girgiza kai tana fadin No No No Aisha kin san abinda bakin ki ke fada game da dan uwanki kuwa ?
Kai Aisha ta fara dagawa kafin tace a cikin kuka mami na sani ba zanwa ya J sheri ba ko da kuwa ba dan uwana bane shi.
Wallahi mami ciwon nan na zainab da sanin ya j wallahi ke Aisha mami ta fada da dan karfi ki san abinda kike fada kada in saba maki yanzu a wurun nan.
Wallahi mami naji abinda yake fada a waya da kunnuwana da banji wanan bakin abinba bazan taba fadin hakan ba mami.
Nan ta fara bata labarin yadda abin ya faru har zuwan shi yana waya da abinda taji ya fada a wurin lokacin game da zainab din.
Innalillahi mami kawai ke fadi kafin kuma tazo ta fashe da kuka tana fadin jafar sai kuma ta girgiza kai a cikin takaici.
Can ta juyo kamar tababa tana fadin bayan kanwar zainab din ke dawa ke wurin mu kadai ne ta bata amsa.
Ita kanwar zainab din fa taji abinda yake fada tace ban tsamani taji don kukan da takeyi a lokacin saboda shi najata zuwa bayan wurin filawowi.
Innalillahi Aisha jafar ya kasheni idan wanan maganan gaskiya don ko mu ba zai bari ba wata rana.
Wallahi mami najine ya fada exactly abinda naji na fada maki mami ban kara masa ba ni yanzu tsoron da nake ji shine kada su kashe ta a sanadiyar shi fa.
Ki bar wanan zancen Aisha zanga mamud mu tatauna a kai zuwa safe don yanzu nasan ya shiga gida ko tunda ya saukeni.
Mami a nan zan kwana tsoro nakeji wallahi ba zan iya kwana dakina ba yau ta fada a cikin dan shagwaba.
Mami bata tsaya ba ta wuce zuwa ban dakin da tayi niya kai tsaye zuciyar ta cike da tunanen dan nata.
Har ta fito bata bar jin abinda take ji ba a lokacin don haka ta samu wuri takai kwance Aisha na gefe kwance taji mami din ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Haka yasa ta mike zaune tana fadin mami ki bar kuka please kada ki jawa kanki matsala don Allah addua ya kama ayi masa yanzu please.
Aisha jafar yana son ya kasheni me yar mutane tayi masa yake son bada jinin ta a sh haka ?
Mami ni godiyana ga Allah daba zarah bace yake aure haka ya faru da kinsan iyayyen ta ba zasu taba yarda da hakan ba sam.
Tunanen da nakeyi ke nan yanzu Aisha da ace itace a gidan nasa yau ina zan sa kaina a kasan nan inji dadi.
Yanzu ne na kara tabbatar da kalami da ya keyi idan nayi mai maganan aure sai yace zainab ce daidai dashi ya aura.
Ashe abinda yaron nan yake nufi ke nan ban fahinta ba har hjy tsohuwa ta rigani fahintar manufar sa din .
Haka suka kwana sai kusan asuba mami din ta tashi ta fara nafila ana fitowa sallah ta kira wayan mamud tana neman shi idan ya tashi.
Hankalin ya mamud ya tashi yana zaton ko hjy ko nice wani abu ya faru damu.
Ya amsa da fadin mami gani zuwa yanzu Nuriya dake gefen shi ta dago da sauri tana fadin lafiya dai ko yace ban sani ba sai na tafi.
Kodai zainab din ce ta cika ta tambaye shi tana kure shi da ido don jin amsan da zai bata a lokacin yace itace damuwan ki a duniya dama ?
Kai ba a maganan arziki dakai dama ta fada tana kawar da kai gefe cikin jan tsuki da jin haushi shi a lokacin.
Rigan shi dake gefe ya dauka ya zura ya fice dakin da sauri zuwa part din mami din hankalin shi a tashe.
Yana shiga part din mami din ya nufa babu kowa a wajen sai yan aiki dake ta aikin su a gidan suna gaudashi yana amsawa a gurguje ya kai kofan ya kwankwasa.
Aisha ta amsa mai da fadin shigo yaya ya sakai da sallama ya shiga yana shiga ya hango mami zaune a kasa ta jingina jikin ta ga bangon dakin kamar tana tunane.
Mami lafiya ya tambaya yana kallonta jin ba amsa a wurin ta ya juya wurin Aisha yana fadin Aisha meke farune haka ?
Ka zauna yaya ta fada itama a sanyaye tana kallon mami din ya samu wuri ya kai zaune a hankali gefen gadon yana maimaita tambayan shi har lokacin ba amsa.
Shiru ne ya dan biyo a dakin kafin mami din tace mamud kasan wana ciwon da yarinyar nan zainab keyi a yanzu Jafar ne silar shi kuwa.
Jafar kuma mami ya tambaya a cikin mamaki yana kallon mahaifiyar tasu don son karin bayani a wurin taba
Eh jafar ki fada mai abinda kikaji yana fada tacewa Aisha dakw gefen shi zaune a takure cikin damuwa karara a fuskan ta.
Jine da kanwarta ke kuka bayan ta some din nan sai na jata zuwa baya ko zatayi shiru nan ta kora mai komaai wanda kafin ta gama ya kira sunan Allah yafi a kirga.
Saida Aishan tagama magana har lokacin kai yake gitgiza yana jin ta aje ya amsa da fadin mami na fada maki ina zargin haka gare shi kice in bar zancen nan kada in kara fadab haka a bakina.
Subbahanallahi wlh biri yayi kama da mutum mami duba da wasu halayen jafar na rashin son raban mutane da baiyi kuma a haka harkokin shi suke ci gaba kullun.
Ya kara fadin hasbunallahi wani imal, wakeel wallahi in har wanan maganan gaskiyane jafar ya cuci yarinyar nan don a tsaye take wallahi mami kan al,amarin shi .
Don shi da bakin shi wallahi yake fada min irin kokarin da yarinyar nan tayi a kanshi har ya daina shan giya da neman maza yan uwanshi a yanzu.
Ita zainab din mami ta tambaya cikin dago kai tana kallon shi yace wallahi mami ya fada min komai amma bai fada min yana cikin wani kungiya ba haka.
Ai ba zai fadama ba tunda yasan bai shuka gaskiya ba mana yarinyar da tayima wanan har zaka iya bada jinin ta ga tsafi.
A dai bincika mami don bamu san inda zancen nan yanufa ba kai tsaye kar muzo mu yanke kasa hukuncin da bashi ba a nan.
Idan ba gaskiya bane me zaisa ya fadi haka yana warning din su kada su kashe ta dashi suke da matsala ba ita ba.
Mami jamal yasan da wanan zacen ya mamud ya fada yana kallon fuskan mami din tace kai kadai na fadawa yanzu.
Don tun jiya ta fada min da dare na kasa barci a gidan nan sam ban runtsa ba tun jiya di data fada min zancen.
Bari mu tambayi jamal ko yana da wani masaniya ga hakan da sauri mami tace kada ka fada mai komai yanzu sai in hakan ya kama a fada mai din.
Kasan jamal da bakin zuciya wallahi zai iya kawo hatsaniy tsakanin ka dashi yanzu menene kada a fada min jamal din ya fada yana shigowa dakin.
Don tun shigowan ya mamud ya ganshi ya koma daki ya saka riga tare dayin brush yabiyo bayan dan uwan nashi hankali tashe.

Asibiti kusan a zaune yaya ya kwana a dakin sai can ya daga ya je dakin da aka kwantar da hjy ya leka ya samu suna barci ya dawo.
Ya kafa sintiri a tsakiyan ward din yana dan buga hannayen shi a cikin damuwa ya kuma koma ya zauna ya tsura min idanu na wani lokaci.
Zuwa asuba na dan motsa ya taso da sauri yana dan kiran sunana na dan bude ido na kalleshi na mayar na rufe kuma kamar ina barci a lokacin kuma idona biyu ba barcin na koma ba.
Saidai dakin da naga yana juya min yasa na kulle idanuna dan in ji saukin hakan .
Kai kai ya fada yana naushin hannu shi cikin dan uwa tare da fadin idan kuka cutawa yarinyar nan i will not spear any one in dat crimme.
A hankali hawaye dake idona suke silalowa gefen fuskana sai yanzu na dan gane abinda ke damuwa na a lokacin wani irin kukane yazo mi har yana dan jin sautin na a lokacin.
A hankali ya tako zuwa inda nake kwancen ya dan sunkuya daidai gadon yana fadin baki barci ba ke nan zainab.
Abinda nake gudan maki kenan ya faru dake tun farko ki gafarce ni zainab nasan na cuta maki da ban fada maki wanan tsarin nawa ba.
Ba a shiga dakina a kwanta saman gadona idan bana cikin dakin wanan dokane hakan shiyasa tun farko ban saba maki da shiga dakin nawa ba ma.
Don irin hakan nake maki gudu duk da nasan ba zasu iya maki komai ba a yanzu warning din ki kawai sukeyi a hakan .
Jin maganan da yakeyi a lokacin kamar almara nakeyi kafin in mayar da idona in rufe ina mai jin wani irin tsanar shi na shiga zuciyana lokaci guda.
Ba zan taba yarda a cuta maki ta bangare na ba zainab ko waye kuwa sai inda karfina ya kare don ke din amanace gareni zainab.
Insha Allahu zakiji sauki ki dawo gare da yardab ubangiji don na fada masu kowa ba zan bari ba idan sun taba min ke wallahi.
A hankali na bude bakina cikin muryan dake nuna zafin ciwo ga mutum don muryan bai fitawa mutum sosai a lokacin da yake son fadan wani abu ga wanda ke kusa dashi a lokacin irin hakane a lokacin nace dashi su waye wayan nan yaya ?
Meye hadin ka dasu har suke bibiyan rayuwan ka dani ya shafeni a yanzu wani laifi nayi masu suke son kasheni ?
Sai lokacin ya dago kai da sauri yana fadin ba zasu taba iya kashe ki ba zainab Allah ba zai basu ikon hakan ba don ya fimu sanin komai.
Ke din ba jinin daya halatta bane a garesu sun sani in ma wani abu suke so sukai maki haka ni zanyi maganin ko menene da yardan ubangiji.
Idona na runtse a hankali don jin abindaya fada tabbas akwai wani kulli tsakanin shi da wasu da ban sani ba amma kuma ai fuskan phlips abokin shi nagani a mafarkin.
Da budan bakina nace dashi your friends philips and others ko don shi nagani a wani wuri a cikin mafalki da ban san ko ina bane wanan wurin.
Kingashi ko zainab na gyada mai kai a hankali ina kawar da kaina gefe daya wasu hawaye na gangarowa daga idona a hankali.
Naji yace good zai gane baida wayau kuwa ido na mayar na kulle a hankali don nikan a zuciya nasan na gama da duniya ke nan tunda na shiga hannun wa yan nan mutane a yanzu.
Yanzu nasan kin fahinci ko meke gudana dani zainab saidai ina son don Allah idan zaki min hukunci kiyi min adalci a cikin sa don ni kaina a haka na tsuci kaina a cikin su badan nasa kaina ba.
Wanan yana cikin abinda bature ke kira da trust person yarda da shakuwan dake tsakanina dasu a baya yasa suka jefani a cikin su .
Don su a wurin su mutum bai zama dan baiwa bai kasance a cikin wani kungiya ba haka wanan shine dalilin kawai da suka halaka min rayuwa a yanzu.
Zakiyi mamaki idan nace dake su a wurin su hakan shine iya kaunan da zasu nuna min na zama tare da mukeyi.
Saidai ina son ki sani duk da sunan ina cikin su ban yarda da dokokin su ba da ake shimfidawa mutum inda na samu dama shine bani na saka kaina a cikin kungiyan ba sakani sukayi da kansu.
Don shi bature yana baka hakkin ka akan ka,ida komai ritsi kuwa ga abu dole sai sun ba mutum hakkin sa a kai.
Duk yadda suke sona a cikin su hakan baisa na yarda na sake ibadana ba don su kamar yadda da dama suke hakan idan sun shiga sai dai rauni dana samu wurun addinin nawa wanda ni kaina na sani kuma abin yana damuna sometimes.
Ina fada maki wanan ne badon ki yarda da abinda nake fadi din ba iya kuma gaskiyan ke nan nake fada maki a yanzu.
Haduwana dake shine sillar tabarbarewan komai a wurina wanda su basu so hakan ba don addinin da na juya yanzu ina yi akai akai yasa mun samu rauni sosai dasu a hakan.
Karshe kuma sai rabuwana da su taju da nabil daya kara tun zurasu suka sake jin haushin hakan da takaicina gashi a yanzu a kullun zasu ganin a kwance tare dakene a kuss dani wanda hakan yana cikin dokan mu.
Ba zamu kwanta da mace don muji dadin ta ba don su a ganin su mace haramtaciyace a wurin su dokane hakan.
Yawan adduan ki idan zaki kwanta yasa basu iya maki komai a lokacin ko jiyan dama suka samu har hakan ya faru dake wanda nasan kuma ba zasu maki komai ba sai tsorata kin da suke son suyi a hakan.
Nasan da ba wanda yasan da wanan zancen duk a kasan nan sai ke a yanzu ke din ma na yarda da sone yasa na fada maki komai don ki sani ki kuma kwantar da hankalin ki kada kiyi tunanen komai kan hakan.
Kuka nake a hankali ya mike don kiran sallah da yakeji a lokacin ko ina a cikin asibitin yana tashi yake fadin ki yi barci a yanzu idan na dawo sallah sai in kamaki kije kiyi taki sallah kada kice zaki tashi fa please ya fada yana fita daga dakin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA.FATAN ALHERI GAREKU MASU KARATU MARASA LAFIYAN MU UBANGIJI ALLAH YA BASU LAFIYA MASU LAFIYA ALLAH YA KARA MASU LAFIYA DA WADATAN ZUCI ALLAHUMA AMIN, , , ,

ANTY COROFFE UBANGIJI ALLAH YASA KAFFARA NE WANAN JARABTAN DA ALLAH YA AIKO MAKI DASHI ALLAH YA BADA IKON CIN JERABAWAN SA AMIN.

AKWAI WATA BOYAR ALLAH TANA BUKATAN ADDU,OIN KU DA BAKUNAN KU MASU ALBARKA ALLAH YA BADA IKON MATA DAMU DA ITA DUKA ALLAHUMA AMIN, , , ,


Tunda na runtse idanuwana ban budesu ba ashe har barci ya daukeni ina tunane a hakan.
Hayaniyan da naji a saman kaina yana tashi a dakin yasani bude idadanu na a lokacin naga har hasken rana ya haska gari a lokacin alaman dai gari ya dade da wayewa ko .
Muryan ya mamud ne naji a saman kaina yana min sannu tare da fadin kin tashi ke nan zainab ya karfin jikin naki ?
Na bude idona tare da kakaro murmushin dole a lokacin a fuska ina dan amsawa a hankali.
Yawa na soma yi da idona ina bin wa yanda ke cikin dakin da kallo na sauke idona a kan mami dana gani can daga gefe ta tsura min idanun ta kuri tana kallona.
A hankali naga ta tako zuwa bakin gadon tana fadin ya jikin zainab da sauki ko min shigo mun samu kina barci.
Da sauki mami na fada ina yunkurin tashi zaune take fadi a cikin sauri kwanta mana ina kuma zaki yanzu ?
Cikin daurewa na soma fadin sallah zanyi mami banyi sallah ba tun dazun na fada ina mikewa zaune.
A take na mayar da idona na rufe dan jiwan da nake gani idon nawa nayi lokacin dana tashi din zaune.
Lafiya mami da jamal suka fada lokaci guda ban iya basu amsa ba sai komawan da nayi na kwanta a lokacin da sauri ina zatane mami jamal ya tambaya.
Wai sallah zatayi ta bashi amsa yake fadin ta bari mana har taji karfin jikin zuwa dan ajima sai ta tashi tayi.
Lokaci yana shigewa idan zata iya a barta tayi ya fada yana karasowa wurin duk suka bishi da kallon mamaki a zukatan su.
Zata iya mana idan basu samu galaba a kanta ba kamar yadda suke son halaka yar mutane batai masu komai ba ya fada a hasale yana juyawa.
Duk da mamakin da yayi da abinda kanin nasa ya fada baisa ya nuna ko gezau ba a hakan sai ma kokarin dukawa da yayi yana tambayana abinda nakeji dana tashi din.
Ban bashi amsa ba sai yunkurawan da nayi da karfi Allah ya taimakeni na tashi da addua a bakina ina sauke kafafuna kasan gadon na sauka .
Kamani yayi da sauri zuwa ban daki da taimakon shi har na samu nakai yafito tare da rufo min kofan na tsugunna da kyar kami nayi sarki.
Ina fitowa a kofan yake tsaye saidai duk wa yanda ke dakin a lokacin sun fita shiya kamani zuwa wurin daya shimfida sallay a dakin nayi sallah a zaune yana gefe saman kujera tare da wayan shi a hannu yana dakila.
Fadilace da sadiya sukai sallama suka shigo dakin da gudu sadiya tayo kaina ya daka mata tsawa kada ta fada min a jikina.
Fadila ko tun a kofa take fadin alhamdullahi jiki yayi sauki tunda mun sameki zaune haka kafin ta juya wurin shi tana gaidashi bai wani amsa mata a sake ba.
Bayan sun gaidani ne ya mike tsaye yana fadin barin leka likitan koya fito kada ki zuba abincin kar taci sai munji abinda likitan zai fada.
Daga haka ya mike ya fice a dakin ya barni dasu yana fita nace fadila kamani in koma saman gadon zan kwanta.
Ta rikeni na tashi muka nufi gadon saidana kwanta tana min sannu ta koma ta zauna saman kujeran daya tashi sama.
Ina nan kwance a wurin suka shigo su ukku da likita sai ya mamud da suke tare likitan ya dan duba yayi rubutun shi yake fadin ba wani matsala har yanzu saidai za a bari har anjima aga yadda na kara ji sai a sallameni mu tafi gida.
Bayan fitan likitan ya kalki fadila yana fadin zaki iya bata abincin yanzu taci tace ok oga tana mikewa tsaye don zubawa .
Da sauri nake fadin bazanci ba don Allah ruwan zafi kawai zan sha na fada ina kawar da fuskana nan ya kama min fada don me ba zanci ko kadan ba inji karfin jikina.
Rabon ki da abinci tun jiya bakici komai ba sai lokacin ya mamud yai magana a dakin yana fadin ka barta ba aiwa mai ciwo hakana a sannu ake bin shi ai.
Ruwan zafin ta hada min nace kada tasa madara haka zan sha tana dan juyawa ta dago kai tana fadin oga kaje gida tunda munzo ka huta.
Ya mamud yace lalai kan zai fi kada kaima ka rafke muna da ciwo kuma ya dan yi murmushi kadan tare da dubana kafin yace.
Mamud mu tafi wurin hjy na kara dubanta kafin na wuce gida suka fita daga dakin ya rage mu kadai a dakin na kalli inda suke zaune sunyi shiru ina fadin.
Kunzo min da wayana suka amsa da eh yana a jakkan ki da muka tafi dashi jiya gashi sadiya tasa hannu ta dauko wayan a ciki ta miko min.
A hankali na bude wayan don malam nake son kira na kalli fadila ina fadin ku dan fita ku ban wuri na min ti uku don Allah.
Da sauri suka mike suka fita na danna kiran malam din ya dauka yana fadin yau uwar gidan jafaru ce da kira da safe .
Maimakon inyi magana saina fashe da kuka inajin yana fadin subbahanallahi me kuma ya faru dake zainab bar kuka kiyi min bayani a tsanake kukan nan naki yana daga min hankali sosai wallahi.
A cikin karfin hali nace dashi malam ina cikin wani hali yanzu haka ina asibiti a kwance tun jiya ance wai banda jini.
Subbahanallahi malam ya fada a kidime tare da fadin meya kawo hakan gareki nan ma wani kuka na sake kafin in koro maganan na fara fada mai tiryan tiryan har karshe.
Wa iyazu billahi ya fada tare da fadi cikin sauri ina zuwa ki kashe wayan nace to malam nagode na kashe wayan.
Banji malam din ya kirani ba har zuwa rana hankalina kuma yana wurin kiran malam din don sai ina ganin shi keda maganin a hannun shi.
Yasa na damu da in fadawa malam din a lokacin karfe hudu likita yace ina iya zuwa gida a lokacin ban bar asibitin ba saida na shiga na sallami hjy itama din ba laifi ta samu lafiya a lokacin.
Mun dawo gida dakina nashiga nayi wanka har lokacin ina jin jikina ba karfi kamar nayi watani a kwance ina jinya nake jin jikin nawa.
Karfe shida sai ga maizube da malam an shigo dasu gidan wanan ya ban mamaki don ban san zasu zo garin ba a lokacin.
Basu huta ba malam ke fadin a kaishi wurina yana son ya ganni a lokacin aka kaisu har dakin ina kwance duk da yamma yayi a lokacin na kwantane don zama bai mun dadi a lokacin .
Yana shigo da sallama a bakin shi bai min magana ba ya fara bin dakin da addua kuswa kuswa na dakin kafin ya dawo ta kofan dakin ya tsaya ya dade yana adduan da bamu ji abinda yake fadi a lokacin.
Yasa hannu ya ciro wani dan gora da rubutu a cikin aljihun babban rigan shi tare da wani fifiken wani dabba mai dan girma yana bin ko ina yana dan yayyayafawa a dakin ko ina har zuwa wurin gado.
Sai daya gama yazo inda nake zaune din ya mikowa maizube wani gora yana fadin ku shiga bayi ki mata wanka da wanan zamu samu abin yin hayaki ko a gidan nan ?
Burner muke dashi na bashi amsa tare da yimai bayanin yadda yake yace zaiyi ai tunda yana fitar da hayakin a jikin shi.
Nayi duk yadda yai min bayanin ayi min koda muka fito basu dakin shi da yaya jafar din hakan ya bamu daman yin yadda yace ayi din maizube na fadin ai da yardab ubangiji komai zaizo karshe ke nan yanzu don sai da malam din yaje Damau yaga aminin shi kafin muzo nan.
Ni da kaina nace aban abinci inci a lokacin ina ci sai barci mai nauyi ya daukeni ban falka ba sai cikin dare sosai koshi fitsarine ya tayar dani a lokacin.
Da safe koda na tashi jiki wasai dashi kamar bani bace a jiya ban ko iya daga hannuwana a lokacin.
Kwanan malam ukku a gidan mu yana burgan gidan damai gidan gaba dayab mu har mami da ya mamud sunzo ya zauna dasu sunyi maganan siri da jafar din dasu .
Wanda ban san abinda suka tatauna ba a lokacin nidai naga mami ta canza min yanzu tun a asibiti naga wani canji a gareta a yanzu gareni.
Washe gari su malam sukai min sallama suka tafi bayab yaja mun kunne koda wasa kada in fada wa wani a gida cewa sunzo nan Abuja .
Kuma haka din nayi duk da inna na kirana mu gaisa ban fada mata ai malam yana wurina a abuja ba.
Duk da malam ya tafi haka baisa mun daina maganin daya bamu inayi ba a kulun har kwanakin daya diban muna din muyi a tare dashi mukeyin maganin kullun kafin mu kwanta barci zamuyi wanka da hayaki sai adduan kwanciya din daya bamu safe da yamma.
Alhamdullahi zance a yanzu banda wani damuwa a jikina ko na tsoro a yanzu tun bayan zuwa malam wurin mu din.
Ana sallamo Hjy gidan mu akayo da ita don can tace a kaita kafin ta koma gida idan ta dan murmure jikin nata.
Mami bata so hakan ba saidai ba yadda ta iya da hakan dole ta barta taje gidan namu ta zauna hakana yayin da mu kuma hakan yai muna dadi sosai don son da mukewa tsohuwar.
Sabon zancen daya taso muna kuma a kan zuwan hjy gidab mu shine dawo da kwanan mu wuri daya da yaya a yanzu don zuwan hjy.
Don tun faruwan hakan ban kara komawa dakin na kwana ba sai yanzun da hjy tazo gidan namu zata kwana biyu damu.
Don sa idon tsohuwar duk da a daki take zama nan take wuni bata fitowa ko falon gidan sai dai kuma suna tare da mama Ramatu a gidan namu.
Wace mami tasa ta biyo mahaifiyan nasu su zauna nan tare da ita don halin jikin nata da take ciki a yanzu.
Hakan yasa a yau dole mu hada daki da yaya din wanda kowan mu na cike da tsoron hakan a cikin zuciyar shi tunda bamu san mai hakan zai haifar muna daga baya.
Na shiga dakin da sallama yana kwance yadda ya saba kwanci wani lokaci ya daga kafa daya ya dora hannu saman fuskanshi ya kare da hannu daya.
Yana jin sallamana ya dan dago kadan ya kalleni ya mayar da kanshi a yadda yaken na tako a hankali zuwa bakin gadon kamar a tsorace nake.a lokacin.
Zama na danyi a baki gadon ban karasa hawa ba gaba daya yake fadin idan kina ganin hakan da matsala ki koma part din ki ko hankalin ki zai kwanta nima ina dauting din hakan a yanzu ban son a kara samun matsala again.
Kada su mami su kara zargina don mun kwasa dasu wacan satin suke fadin wai nine na bayar da jinin ki a wurin tsafina.
Jin hakan yasa na juyo da sauri ina kallo inda yake kwance din yana nan yadda yake yake maganan shi hankali kwance.
Waya fada mata hakan na tambayeshi da mamaki a fuskana shine abinda ya ban mamaki don maganan yana kama da wanda muka sani din don haka yaya akayi suka san da zancen.
Nasan baki fada masu komai ba kan hakan saidai idan zargi sukeyi ko kuma sunji a wurin malaman su don nasan kowa na shige shige a kaina a yanzu.
Wanda ni nasan da hakan ba yau ba sai dai duk bata lokacin su sukeyi ga hakan don hanya fita ciki dayane nina sani idan lokaci kuma yayi zan daina din da yardan Allah.
Wani irin kallo nayi masa na tuhuma duk da bai kalloni ba yasan nayi masa sai naji yace yes matakin da basu so zan dauka shi zai rabani dasu lafiya.
A hankali na jingina bayana saman filon dake gefena nakai kwance ba tare dana iya furta mashi komai ba a lokacin.
Don a yanzu ya daina bani tsoro ko mamaki don sai nake ganin a gadarance yakeyin abinsa kai tsaye duk da yasan hakan ya sabawa addinin mu sosai.
Sai dai maganan malam ce da yake fadin in bishi a sannu don bayin kansa bane hakan zanga kamar komai yana yinsa a cikin sani ne saidai asirine dake aiki a kansa kawai ba a gane hakan ne ko shi kanshi bai gane hakan kai tsaye.
Sai idan an bishi a sannu zai zo ya daina komai wanan ne suka tatauna da mami da malam din ashe da zasu tafi bayan malam din ya fada mata komai akan dan nata da a yanzu ta yarda da komai da ake fada akanshi.
Ba wanda ya sake wani magana a cikin mu har barci ya dauke mu a hakan ko dadin barci ne ya kawo mu kusa da juna kowan mu ya dora hannu saman jikin dan uwa oho.
Sai dai mun tashi da asuba mun samemu a hakan nice ta farkon falkowa nayi mamakin gani shi rungume dani yau abinda bai taha faruwa a tarhin mu cikin jin dadi irin hakan.
Ban gama mamaki hakan ba ya falka shima da sauri ya dan ja baya ya zabura wanda hakan yasani na kara mirginawa gefe daya.
Ganin na matsa yasa shi sauka da sauri ya zauna a bakin gadon na dan wani lokaci kafin ya mike ya shiga ban daki nabi shi da kallon mamakin yin hakan.
Bai dade ba ya fito daga bayin na shiga wanka nayi na daura alwala ina mamakin wanan bakon yanayin yau da nagani a garemu.
Har na fito ban daina mamaki hakan ba ina idar da sallah na koma na kwanta don gari bai gama waye ba a lokacin.
A cikin barcin ne nayi mafalkin ga wasu nata kwasan kayan su suna tafiya kamar masu barin gari ina tsaye ina kallo su sai da suka gama suke dago hannayen su na duba sai banga kowa ba kuma.
Kakan maya na gani tsaye da abu kamar sanda a hannun ta tana min murmushi na mayar mata itama din tabi bayan su suka bace mi tare.
Tashi nayi firgigit ina kallon ko ina na dakin sai lokaci na gane inda nake kwance a dakin yaya nake har lokacin kwance .
Juyawa nayi shine zaune yana aiki a cikin laptop din shi ga tea a gefen shi yana tashin turin hayaki.
Na mike na saka hijab gaidashi nayi na nufi hanyar fita daga dakin naji ya dakatar dani yana fadin mafalkin me kikeyi kuma haka da safen nan.
Dan kallin shi nayi ban furta mai komai ba nasa kai na fice daga dakin kai tsaye zuwa dakina .
Idan ka ganni a yanzu zaka gane ina a cikjn damuwa don yadda na rame na danyi duhu ba sosai ba dai.


Don Allah ayi hakkuri da wanan din ba yawa sosai yar uwa dare yayi sosai ba zan samu karasa shafin nan ba yau.


ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI UBANGIJI ALLAH YA BAMU WUNI LAFIYA MARASA LAFIYAN MU ALLAH YA BASU LAFIYA MASU LAFIYA ALLAH YA KARA MASU LAFIYA .
YAN UWA MUSULMI DA SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA UBANGIJI ALLAH YAI MASU RAHAMA ALBARKACIN KALMAN LA, ILLAH HA,ILLAH MUHAMMADUN RASULILLAH ALLAHUMA AMIN.

NOVEL DIN KUDINE NA FADA BA HAKKI A TSAKSNINA DAKE RANAN TAMBAYA NAGODE ALLAH BADA IKON BIYA A KATANTA LAFIYA, , , ,

Zaman hjy a gidan mu zance kamar alherine a garemu baki daya don tsohuwar duk da tsufa da yai mata yawa a yanzu haka baisa ta barkace ba ga komai.
Wanan shi ake kira da tsufan mutunci zakaga tsofo a kamile komai nasa a cikin mutumci da addine yakeyin sa ubangiji Allah kabamu irin tsufan nan idan tamu tazo Allahuma amin.
Yau ma ina fitowa mukai kicibis da mama Ramatu da tafito kitchen yiwa mai aiki magana ta kawowa hjy ruwan zafi tasha shayi kafin tasha maganin ta.
Tana dawowa ina bude kofan yaya jafar din zan fito a lokacin mukai kicibis da ita jin karan kofan yasa ta dago ta kalli part din .
Nice ina rufe kofan ta dan sake dan murmushi a fuskanta daga can nisa inda take tana fadin har kin tashi ashe.
Ban iya bata amsa ba don nauyi da kunyan hakan a gareni ashe shigan ta take cewa hjy din ikon Allah koda ake cewa yaran nan basu damu da junan su ba auren nasu na gashi nayi kane sukayi ashe zancen ba haka yake ba hjy.
Nikan nasan cewa lokacin haihuwan nasu ne baiyi ba koda yaya ke fadin dama dai ai auren yinsa yayi don kada a matsa mai yarinyar ba sonta yakeyi ba har yanzu.
Tunda babu soyayya a tsakanin su da yarinyar yasa bai kulata har su samu fahinta nikan nayi mamakin hakan da yaya take fadi ai.
Dan murmushin manya hjy ta sake kafin tace da yar nata shin Ramatu kin taba ganin inda akai sharia kan mata da miji irin haka ?
Kyake yar ku kawai da halinta nina dauka kawai lokacine baiyi ba don Allah ba ai masa dole sai lokacin daya dibarwa mutum yayi.
Yaran nan duk kansu hankali ke garesu don basu fita fili suna fitsara irin na yaran yanzu yasa take fadin hakan amma ai mai hankali yana gane wani abu a tsakanin su shi.
Ina nan kuke hiran yadda ya rude da ciwon ta a asibiti har kuna masa sherin hakan kawai dai ku barta da halinta jinin sune bai hadu da yarinyar ba a yadda na dauka.
Sun dauki lokaci mai tsawo suna tataunawa akan mu da mami kafin su juya hiran zuwa hiran Nuriya matar ya mamud.
Nafito wanka na shirya kafin in fito dakin na nufi dakin da hjy take don in gaidasu da kwana a zaune na samesu suna hira ga abin karyawa da suka karya dashi a gefe daya.
Da sallama a bakina na shiga dakin suka amsa min nakai zaune ina fadin hjy ina kwana ya karfin jiki take fadin lafiya yar nan .
Ya naki jikin ina da sauki i yanzu nace Alhandullahi hjy na juya wurin mama Ramatu ina gaida ita ta amsa min a cikin fara tana fadin ya dare zainan an tashi lafiya Alhamdullahi na bata amsa.
Daga haka nakai zaune a gefen carper din da suke zaune suna hiran ga abinci nan ki karya hjy tayi min tayi.
Kafin inyi magana mama ke fadin a, a hjy da mijin ta suke karyawa fa yanzun kuma kyace ta zauna nan tace aiko zaku hadu dashi idan ya fito.
A daidai wanan lokacin yayi sallama ya shigo dakin saida ya kalli hjy kafin ya juyo ya kafeni da idanun shi har saida na tsargu.
Mama ya fara gaidawa sabanin ni dana fara gaida hjyn a lokacin dana shigo din dakin hjy ce tace kin gani idan na nuwa yar nan so da kauna kuga laifina a hakan kuna fadin wai nafi son ta da kowa.
Yanzu ki duba ina zaune amma dan nan keya fara gaiyarwa daya shigo shi dakin nan matar shi ko datafishi sanin muhinmanci na ai kinga ni ta fara gaidawa data shigo.
Bai bata amsa ba sai da yakai zaune kusa dani yake fadin wai mama mai wanam tsohuwar take fada ne haka tun dazun ?
Fada takeyi da kai ka fara gaidani kafin ita ya juyo inda take zaune yana fadin da me kike nufi in bar uwata da take zaune in fara gaida ke ?
Ai idan ina da rana ka fada randa babu ni yace baga iyayyena ba ina gani ta mere bakin ta tana fadin ke dai kawata kada ki biyewa wanan butulun mijin naki nayi murmushi kawai ina dukar da kai kasa ina dan wasa da hannuna.
Ta sake nunani tana fadin ka gani Allah ya baka mata mai.alkunya ba irin ka fitsarare ba mara kunya.
Haka ma wancan kanin naka mai irin zubin ka yazo jiya yana min huci kamar wani tsohon kimarci wai am bata masa rai.
Wa ke nan keda zubina ya tambaye ta take cewa masu suna irin dayan nan wanda yaso kwaso farin ka da tsayi.
Mama Ramatu tace jamal take nufi fa kasan ita hjy bata da gwani a wurinta jiya kuma kai aka yaba akan jamal din gashi yau kuma ana kushema.
Barta kawai ai idan mun tashi tafiya chaina da ita zamu tafi wanan karon hjy na fadin kadai je da uwarka gata zaune ni kuma ina dago kai ina kallon shi.
Don jin zancen komawa chaina da yayi a lokacin don na tsani inji zancen tafiyan nan namu a bakin kowa a yanzu.
Balle yanzu da nake ganin can din yake da babban matsalam rayuwa data shafi halin da yake ciki a yanzu yasa gaba daya na kara tsanar kasan a rayuwana.
Amma kai kadai zaka tafi wanan karon ko hjy ta tambaye shi ya kai hannu ya dauki wayanta dake gefe yana bin shi da kallo kamar yana nazarin wayan.
Ba tare da ya dago kaiba yace ita matar tawa gunki zan barta idan ban tafi da ita ba can din ?
Ni dai in tawa ce kabar yarinyar nan a kasan nan kusa da gida zaifi idan ka tashi kazo ka ganta yafi sauki wallahi.
Wayan dake hannun shi din ya aje mata a gefe inda ya dauka da farko yana fadin wanan sabon zance kike son dauko min hjy.
Yaushe zan iya zuwa in wani dawo nan kasan kuma yanzu banda wanan lokacin gara dai muna can din hankalina zaifi kwantawa ai.
Budan bakin mama Ramatu sai cewa tayi nima abindana fadawa yayan mu ke nan da take wanan maganan wai ba zaka koma da zainab din ba wanan karon.
Kamar ba hjy ce ta tsokalo maganan ba a yanzu dana dauka zata goyi bayan zaman nawa a nan sai ji nayi tana fadin.
Ku barshi ya koma da matarsa yafi mai kwanciyan hankali hakan ita lokacin da mijin ta yake raye ina can suke da zama gaba daya shekara da shekuru kuwa.
Ai kawai ku barta tabi mijin ta shi yafi, na fadawa mami hakan ba zai yuyu ba tun ranan don haka abar wanan zancen don Allah ya fada yana bata rai ya mike don barin dakin a lokacin.
Mama Ramatune ta tsayar dashi tana fadin nace ko zaka leka gidan yayane da safen nan ina son zuwa yau din akwai sakon da zan bayar akai min gida a can.
Haka yasa yaja ya tsaya yana sauraren ta kafin yace da ita ba yanzu zan tafi ba mama amma idan zaki tafi akwai driver a waje sai ya kaiki ai.
A lokacin na mike don barin dakin nima don idanuna ya riga da ya cika da hawayen takaici a lokacin nakai kofa yaja ya ban wuri tare da bina da kallo.
Yaki kawata hjy ta fada ban iya juyoba a lokacin kuma nasan dani take maganan sai dai naja na tsaya daga kofa kadan.
Au kardai ince kema din baki son bin mijin naki can ne yanzu mama Ramatu ta fada tana kallona.
A, a kada kuyi mata fassaran daba shi ba babu wanda zaiso yabar gida irin haka shekara da shekaru mutum naizo gida ba fa .
Tazo din kuma bai barta ta gama bin dangi ba ya tayarwa mutane da hankali kamar gareshi farau yin mata .
Yaki nan kinji kyale shi idan ba zaki koma ba yanzu sai ya tafi ya barki nan har ki kara ganin mu ai muma nan bamu gaji dake ba.
Baiyi magana ba sai fita da yayi daga dakin ya barni tare dasu baki hjy ta fara ban kan nayi hakkuri ai dama haka aure ya gada.
A cikin zancen su ne na fahinci tafiyan mu a yanzu bai da wani nisa ke nan duk da ni bai min zancen tafiya ba har lokacin.
Duk dana dan sake jiki munyi hira da hjy a dakin nata haka baisa na sake zuciyana kan zancen tafiyan namu ba a lokacin.
Tambayan da hjy din ta sako min ne ya dawo da hankalina gareta tana fadin ina dai kawata ba kin biyewa mijin ki bane kuna tsarin iyali nan da sukeyi na kafirai.
Lah hjy wallahi bai taba min wanan zancen ba tun zamana dashi kawai dai bama rayuwa irin na sauran ma,aurata dashine har yanzu , na fadi hakan don na kawo hanyar da tafiyan mu zai fasa a lokacin na fadi hakan.
Kamar ya ban gane hakan ba da kika fada yanzu don magana kikai min a dunkule hjy haka maganan yake dana fada.
Na fada ina dukar da kaina kasa lokaci guda ido hjy ta kura min na dan lokaci kafin tace ki min bayani yadda zan fahinta don wanan ba karamin magana bane kike fadi a yanzu zainab.
Shin kina nufin bai taba tabaki a matsayin aurataya ba zainab ko dai kina nufin bai gamsar dake ne yadda ya dace.
Zainab ki kwantar da hanlinki ki fada min gaskiyan komai yadda ya dace jafari ba fin karfina yayi ba dagashi har uwantasa zan iya daukan mataki a kansu kan hakan.
Jin ta ambaci sunana na sake fadin hjy haka maganan yake har yanzu bawai wani zama mukeyi dashi ba yadda ya dace haka.
Wai zancen nan gaskiyane ko al,mara nake ji don na dade da zargin hakan a gareku har in wanan zancen ya zamo gaskiya gaba dayan ku zan dauki mataki a gareku har uwan naku data boye min hakan.
Ba laifin mami a nan hjy don ina ganin bata san da wanan zancen ba har yanzu innalillahi hjy ta fada hankali tashe tana fadin shike nan yaron nan ya cuce mu a rayuwa.
Me yake nufi da hakan daya aikata ya tauye maki hakki yana daukan alhakin ki haka yar nan ko baida lafiyane ba a sani ba haka ?
Lafiyan shi kalau hjy kawai dai bai sha,awan mata ne yace na fada kai tsaye har ina mamakin kaina banda malam kakana ban taba irin wanan maganan da kowa ba a duniyan nan sai ita hjy da nake fadawa ranan.
Yau na shiga uku ni zainabu Abu kuna da wanan matsalan haka akai shiru aka saka maku ido a cikin sa.
A kira min mijin naki ta fada hankali tashe na mike da sauri na tashi zuwa kiran nasa inda nabar tsohuwar a zaune.
A falon shi yake zaune yana shan coffee mai zafi sai turiri yake tashi a cup din daga gefen shi ya bude laptop din shi yana aiki a cikin sa.
Na shigo ya dan dago ya amsa sallaman nake fadin hjyce tace na kiraka yace me kuma zan mata yanzu ya fada yana dan jan tsuki dagani aikine mai muhinmanci yakeyi a lokacin.
Akan zaman mune da kai na fada mata komai yau take kiran ka akanshi wani irin dago kai yayi yana fadin what da karfi tare da fadin me kika fadawa hjyn ?
Kanki daya kuwa zainab ko kin samu matsalane na dan kalleshi ina murguda baki kafin ince kaina daya wallahi.
Nadai fada matane don ba zan yarda in koma wurin wa yan nan muggan abokan naka ba a kashe ni a banza wanan kasan ba .
Ko a nan din sukaso kashe ki kina ganin ba zasu iya bane idan ma wasa kikeyi a hakan kinyi kuskure wallahi zainab ya fada yana ture computer shi a gefe daya ya mike tsaye.
Talkaman shi dake aje gefe daya ya zura a kafan shi ya fita nabi bayan shi ina kallon yadda hankalin shi ya tashi lokaci guda.
Har mun kai kofa yaja ya tsaya ya jiyo a hasale yana fadin ki gagauta gyara duk abinda kika fada a yanzu don kinsan condition din da hjy take a ciki yanzu .
Idan maganan ki ya kara ja mata matsala a yanzu ta kara kwantawa ciwo ki kuka da kanki ga duk abinda zai iya biyowa baya gun yayanta dake.
Baki da hankaki ne ko ina wayau ki ya shiga da zaki zauna kina wanan zancen da hjy at her age baki tunanen komai da zai iya biyowa baya ba.
Ya juya ya fara tafiya ina biye dashi har lokacin a bayan shi ba tare da jin komai ba na warning din da yai min din kan hjyn a raina ni dai kawai mafita nake nema a yanzu.
A tare muka shiga dakin dashi mun samu hjy tabar kasa inda na barta zaune tana jin mun shigo ta dago kai ta kalle mu .
Yanayinta gaba daya ya canza a lokacin kallon shi tayi ba tare data yi magana ba ta nuna muna kujera mu zauna.
Shi yakai zaune saman kujeran yana kallon ta na samu wuri a kasa na zauna sai dan shiru ya biyo a dakin .
Can ta dago kai ta kallemi tana fadin yanzun muna hira da kawata nake bugun cikin ta a haka naji wani maganan daya daure min kai a tare daku jafari.
Me kikaji hjy ya tambaya ta kalleni tace takwara sake maimaita abinda kika fada min yanzu a nan.
Na dukar da kai kafin na sake dagowa ina fadin cewa nayi a matsayin budurwa nake da kike tambayana ko nasha maganin haihuwane ban haihu ba har yanzu.
Hjy ya tare da fadi nasan zainab a yanzu zata iya fadin komai da zai kawo rashin komawan ta can tare dani .
Nagodewa Allah dake ta fadawa wanan maganan haka ba wani ba ai gata a zaune me na rage ta dashi na zaman takewan aure da akeso namiji yaiwa iyalin shi.
Duk mai hankali dai ya dubi zainab a yanzu yasan bata tare da wani damuwa a gidana shi haihuwa ba Allah ke kawo shi ba idan lokacin hakan yayi.
Nasan ina da rauni kwarai wurin mu,amula da taraiya da ita a yanzu na kuma sha bata hakkuri a kan hakan tun da ni din ba mazauni gida bane ko yaushe.
Hjy tace a, a takwara wai haka maganan yake dama kika barni ina tunanen wani abu har hankalina ya daga haka ?
Hjy ni dai ki masa magana gaskiya bana son komawa kasan nan wallahi na fada kamar zanyi kuka a lokacin.
Don ga daman magana ya samu a gareni kuma hakan yanzu ba zai yuyu ba don ya samu wurin fakewa akan ciwon hjy din wanda gaskiya ne ya fada kuma.
Wani abu zai iya samun hjy din a dalilin maganan mu din gaba daya zasu dawo su tsaneni kan hakan danayi tunane.
Sai kawai naja bakina nayi shiru ban fasa kwan gaba daya gun hjy ban da nasan zata dauki mataki a kanshi.
Sai ga hjyn ta koma fadin nasan maza da yawa a zamanin nan suna irin haka ga iyalin su wanda hakan ba daidai bane sam wallahi.
Kuna shiga hakkin iyalan ku da yawa akan aiki da iyakarshi a wanan duniyan zaku barshi yau ina mahaifin ka yake ya rasu ta ba kanta amsa.
Duk ko son aikin ka ina ganin bakai na balarabe ba shi da ko yaushe kaje gidan sa baka masa ganin daya kai uku ko biyu ko yaushe yana kashen duniya yana aiki.
Kuma hakan bai hana shi zama da iyalin shi ba ai har a sameku don haka ina kara tuna maka a yanzu tunda har kaji yarinyar nan ta fadi haka.
A gaskiya tauyewan yayi yawa a gareta ke nan tunda har yana cikin korafin da zata iya fada .
Kada ka manta da yadda auren ku ya kasance da yar nan a baya don haka ka guji duk wani abinda zai kawo matsala a tsakanin ku yanzu.
Hjy indai wanan shine matsalan za a gyara da yardan Allah ya fada har lokacin bai tare da walwala a jikin shi.
Tun daya fita dakin ya barmu hjy tana saman bakin ta dani har akai azahar muka mike don zuwa sallah.
A inda na idar da sallah naji kawai nayi amfani da kayan kakar maya a ranan ya kamata in gwada ko wani kamar yadda tace min inyi dasu.
Nayi din ko wani har sha da shafawa da dai sauran su don su ba hayaki a cikkn maganin su sai dai sha da shafawa kawai zanyi a jikina.
Tun dana shafa ban fito ba duk da baka sanin nayi amfani dashi ma don haka na shige daki abina shima bai leko dakin ba kamar yadda ya saba idan yana gida.
Ban kuma kara ganin shi ba sai da dare da zamu kwanta barci na shiga dakin na sameshi yayi zaune ya daga kai sama yana tunane har nayi sallama bai amsa min ba.
Nima idona ya bushe a yanzu game dashi don haka ban damu da amsawan shi ba a lokacin na gama abinda zanyi na kwamciya na kwanta abina ba tare dana tanka mashi ba.
Ban sani ba ashe maganin yana aiki a kanshi a lokacin ya fara jin wani irin bakon yanayi yana sauka a gareshi a hankali har bai san lokacin da magana yazo mai ba.
Ina hawa gadon naji muryan shi yana fadin ke wani irin abu kika shafa haka mai kamshi ya sawa mutum kasala da hawa kan mutum ya fada yana dan lumshe idanun shi kafin ya sake fadin yayi min karfi a kai.
Ba tare dana kallo shi ba nace ban shafa komai ba sai turaren dana saba amfani dashi kullun na shafa na fada ina jan bargo zuwa jikina.
Banji takowan shi ba sai ganin shi da nayi a kusa dani tsaye gaba daya idanuwan shi sun canza kala kamar ba nasa ba yana fadin ina tambayan ki kina kokarin kwanciya ki kyaleni.


ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH YAN UWA FATAN ALHERI GARE KU KO YAUSHE UBANGIJI ALLAH YA SA MU GAMA DA DUNIYA LAFIYA DAMU DA IYAYYEN MU DA ZURI,AN BAKI DA TARE DA DUKKAN MUSULMIN DUNIYA AMIN, , , ,

YAR UWA KADA KI MANTA DA NOVEL DIN KUDINE KI SHAGALA BAKI BIYA BA AKWAI NAUYI A HAKAN KIN SANI, , , ,


Allah sarki yar uwa novel dina bana soyayya bane ko wani jin dadin duniya ina novel ne don fadakarwa a yadda rayuwa ke tafiya a yanzu don ki gyara da kanki ko ki gyara wasu ta hanyar novel dina ubangiji Allah yasa mu karu da juna anan duniya ranan lahira ke shedace akan duk abinda na rubuta a ciki.
Bana fata ko in yarda alkalamina ya kaini wuta don kawai in gyara maki rai in saka zuciyoyin ku a cikin wani yanayin dana san za,a tambayeni a kansa gobe kiyama.
Novel dina kan abinda ke faruwane a cikin gidajen mu na hausawa a yanzu da kuma yadda zaki fitar da yar ki ko kanwarki a cikin kangin rayuwa don haka idan zaki karanta ki karanta a hakan don idan kin lura wanan rayuwan na yanzu bawai don kayi aure zuciyar ka ya huta bane da itun kalubalin dake baya.
Allah ya iya muna yasa mufi karfin zukatan mu a rayuwan mu na zaman duniya Allahuma amin Allah.

Zaune yakai bakin gadon tare da dafe kanshi na tsawon wani lokaci yayin da gaba ya shiga faduwa don basan halin da yake jin kasa kusa ba.
Sanin shi din ba cikakken mutum bane kamar kowa a yanzu kallon da nake mai ke nan a zuciyana karfin addu,an iyayyene da ikon Allah dake aiki a kaina na tabbatar ya zaunar dani a yanzu gidan shi.
Don wani lokaci idan ina tunane zanji zuciyana yana raya min na gudu na tafi can duniyan da ba,a sanni ba inyi rayuwana acan da zama a gidan wanan munafukin Allah a yanzu.
Amma koda zan tashi sai naji zuciyana ya canza min shawara akan hakan zanjini wani lokaci wasai ko kuma ina tausayin shi.
Kinsan zama na hana mutum ganin laifin wanda kake zama dashi ko yaushe wani lokacin zaka san ba a daidai mutum yake ba kuma ka kasa rabuwa dashi a hakan.
Idona biyu dai a lokacin ina sauraren shi dan filin dana bari a gefen dana kwanta naji ya kai kwance a wurin hakan ya sani dan bude idanuna ina kallon shi a fakaice.
Kwanciya yayi a rigingine tare da daga kafanshi daya ya tokare na dan kada shi kadan ya jingina bayan shi da kan gadon yana kallon saman dakin.
Zainab a tunane a yanzu ba zaki iya fadawa kowa matsalan ki na zama tare dani ba duba a yadda na rikeki a zuciyana nake gani.
Sai dai kash a she yadda na dauka abin ba haka yake ba ke a wurin ki a zuciyar ki kuma kuma koda yake kinyi kokari a hakan ma don sam banga laifin ki ba ko kadan zainab.
Nasan wanan kwarai ban cancanci wata mace ta zauna dani ba a hakan sam don yadda rayuwana yake da akasin da mu hausawa mukafi tsana a duniya.
Allah yasan nasan kinyi hakkuri kan hakan amma ki kara dora hakkurin ki akan wanan din don ni kaina jikina yana ban zan bar wanan harkan nan gaba kadan insha Allahu.
Sai lokacin na samu magana don hakkurina ya kai karshe a lokacin na fara fadin ka daina ka daina shan giya ko ka daina kwana da maza yan uwan ka ko kuma tsafin zaka daina ?
Naji yace hummm zainab ke nan a yanzu nasan kinsan komai don haka kome zaki kirani dashi ki kirani dashi a yanzu din ya fada yana runtse idanuwan shi a hankali.
Wani iri naji a raina ba dadi don hakan ya zama kamar gori nayi mai a yanzu din ban san lokacin dana bude bakina ina fadin
Nasan jarabtane hakan a gareka don Allah kan jarabci imanin bawan sa tako wani hanya don yaga karfin imanin shi to amma yaya tunda ka gane hakan ka yaki zuciyar ka ka mayar da lamarin ka ga ubangiji ka Allah shine mafita.
Ka dauka ba mai iya yiwa bawa komai a duniyan nan sai Allah shike kashewa ya raya kuma aduk lokacin daya so hakan ga bawan sa.
A jiyan zuciya naji ya sauke daga inda yake kwance din a gefena naci gaba da fadin yau yaya baka zama kayiwa kanka tunane akan wanan rayuwan naka.
Idan akace yau babu kai dukiyan naka da kake nema ya zama ganima da abin wasoso ga duk ahalin ka .
Tunda ba zuria ko wani ka aje a duniya da zai gajeka ba a yanzu a kadara kana da zuria din yaya yaya ka ke son su kasance a cikin al,umma da rayuwan su.
Ni kaina a yanzu a kunyace nake shiga yan uwan ka tunda ina ganin kowa yasan irin rayuwan kyaman da kakeyi a yanzu balle yayan ka na cikin ka da kowa ke maka fatan samu a duniyan nan.
Ina maganan nan ne badon kwadayin abinda kake dashi ba ko dan nagada a,a ina magana ne don tsakanin mu dakai ba a san gawan fari ba a wurin Allah .
Kadara kai namiji ne a kullun mami tana maka fatan samun wata macen wayayya wace ta dace da rayuwa irin naka.
Ya kake tunanen zataji idan ta riskeka a cikin wanan halin baka tuba ka koma ga ubangijin ka Allah ba kana zaton zata kyale duniya bata jiku ba ke nan.
Hannun shi naji ya dora a saman kaina lokaci guda ya dafa min kai yana gyara kwanciyan shi a yadda yake kwancen da farko.
Zai,nab naji ya fada a hankali tare da sauke numfashi a cikin wani irin yanayi ya fara magana a hankali yana fadin .
Nima a kullun akai zancen haihuwa gareki ina mai jin zafin hakan don nasan laifin ba naki bane nine mai laifin ga baki daya kuma ake dorawa a kanki.
Nasan ba ko wace mace bace zata iya daga min kafa a hakan koda kuwa duniyan nan da abin cikin sa nake bata alherin shi a kullun.
Sai a asirina ya tono ga jamma,an duniya zuwa yanzu din kowa ya gama sanin koni waye a hakan nayi nadama ina fada maki ko yaushe kan shigana wanan harkan duk da ba zance ga lokacin dana tsinci kaina a hakan ba duk da nasan ko nayi rantsuwa ba mai taba yarda da zancena a yanzu.
Tsam naji a duk kan ilahirin jikina don jin saukan hannun ya jafar da nayi ya sauka a jikina wanda hakan ya sani dan razana da yin hakan da yai min din a daidai lokacin da ban taba tsamanin hakan ba a gareshi.
Dan tsoratan da nayi din yayi daidai da runtse idanuwan shi a daidai lokacin yana jin wani bakon yanayi yana sauka mai wanda hakan yake ganin sa kamar zai aikata wani sabone gayin rikon da yai min din a lokacin.
Sai dai kuma duk da hakan ya kasa cire hannun shi daya riko ni dashi a jikina din a lokacin maimakon ya cire din kamar yadda zuciyar shi take gargadin shi da yi saima kara rikoni da yayi a lokacin ya matseni sosai a jikin shi .
A daidai saitin kunne yake magana yana fadin kamar mai rada kin san me zainab ban samu ko fadin a, a ba gareshi a yadda nake razane dashi a lokacin.
Tsorona daya shine kada ya matseni yace zai min dole ta baya wanda hakan tun lokacin da umma ta umurceni da zuwa dakin shi koda bana son hakan idan nazo na saba zanji duk abinda nake ji a kanshi ya gushe min a zuciyana.
Wanda ni ba komai nakewa tsoron haka ba sai gujewa bacin rana irin wanan yaga kamar ni din irin mazan da suka saba mu,amula da sune yazo ya halakani a banza banji ba ban gani ba.
Kaduwa sosai jikina keyi naji yana fadin ko kowa bai yarda da rantsuwana ba aduniyan nan ke zainab nasan zaki yarda da abindana fadi a kaina a ko inane kuwa zaki shedeni a kan wasu halaiyana da kika sani a baya da yanzun da nake fadin na daina din a yanzu.
Duk da tsoron da nake ji a lokacin nasa hakan baisa hankalina ya gushe har na kasa fadin yardan Allah da amincewan shi a yanzu gareka yafi na kowa da zaima ka.
Don Allah subbahanahu kaiwa sabo kuma yafiyan shi zaka nema a yanzu don ya yafe maka kurakuran ka yaya.
Komawa ga Allah gareka a yanzu shine babban abinda ke gaban ka duk na mutane mai saukine .
Allah zai iya sa mantuwa ga zukatan wasu su manta da ka taba aikata hakan a baya, tuban ka zai iya sa Allah ya shafar dasu komai a kanka ga baki daya.
Banyi aune ba a wanan lokacin da nake maganan sai ji alaman kukan nadama da naji yana yi a lokacin.
Nima kukan ne yazo min don ko banza naga wani na kuka haka nake nima sai hawaye yazo min balle wanan da yake shakikina a yanzu mafi kusa dani da kowa a duniyan nan yana cikin wani hali na rayuwa.
Da kyat yayi shiru koshi wayan shi dake ta ringing ne a lokacin ya sa ya mika hannu ya dauka ba tare da yayi magana ba sai sauraren mai magana a lokacin da yayi.
Yana gama wayan ya kashe ya aje a gefe daya ya rufo hannayen shi gaba daya a saman jikina lokaci guda ya matseni ta yadda muke iya jin numfashin juna a lokacin a haka kowa da nasa kalan tunanen barci ya daukeni a jikin shi .
Misalin ukun dare ina barcin kamar a wahalce acan cikin barcin nake jin wani irin nisi a kusa dani wanda tun kan na bude idanu nasan inda nishin yake fitowa .
Shine duk da yana cikin wani irin yanayi hakan baisa ya raba jikina da nasa ba yana rike dani da hannun shi daya a jikin shi.
Yayin daya dafe maran shi da hannun na hagu yana yanka wani irin gumi tun daga kafan shi har zuwa kanshi .
Na tashi a rude ina kokarin kwacewa don na samu na taimaka mai a halin da yake ciki yake fadin kada ki daga nan zainab .
A wahalce yake magana a lokacin duk da na saba da ganin hakan wani lokaci wanan yanayin yafi na duk wanda yayi a baya muni sosai.
Can yakai ga wani irin zabura kafin ya kai ban daki ya fara wani irin kakarin amai kamar zai zubo mai kafin yakai bayin a lokacin.
Ganin hakan yasa dole na mike zaune ina binshi da kallo a cikin yanayin da yake din na ban tausayi da al,ajabi.
Don nasan wanan halin da yake ciki a yanzu yana da nasaba da rikon da yai min muka kwanta a tare ya jawo mai wanan wahalan haka.
Raina naji yayi wani irin baci lokaci daya na gyara zama ina hada kaida gwiwa na takure a wuri daya na dinga kuka a hankali.
Yafito bayin dafe da maran shi yana tafiya dakyat yazo bakin gadon ya dan zauna a gefe ya dukar da kanshi kasa kamar mai tunane.
Sauka nayi zuwa ban daki na dan dauki lokaci na gyara ko ina koda na fito na samu yana sallah a zaune na bishi da kallo.
Muna zaune ba wanda yai magana a cikin mu kowa na lazumin shi motsin da naji daga bayan mu yasa na dan firgita kamar anyi tsoki an fita daga dakin nashi lokacin naji da kunnuwana sai dai Allah ya gyara ban yarda na juya ba .
Wani irin iskane aka fara yi a wajan gidan kamar hadari ya yaso a garin ko guguwa mai karfi cikin dan lokaci kuma muka daina jin hakan.
A daidai lokacin ne na kula da yanayin da yaya da ke zaune a kusa dani yake ciki yana wani irin kaduwa kamar mai jin sanyi ko zazzabi mai karfi a lokacin.
Ni kan naga ta kaina a wanan rayuwan yau nice auren dan giya dan luwadi dan mafia kuma ashe shiga kungiyan ma bala,ine kala kala a rayuwan mutum irin haka.
A dadafe mukaga safiya dashi saidai wanan karon akwai bambamci ga yadda na saba ganin shi a baya idan yayi ciwon shi gari yawaye sai ya mike tamgararan.
Wanan karo kan yasha bamabam da wacan din don zuwa safe kamar ciwon karuwa yakeyi a lokaci.
Sai amai da gudawa yakeyi sosai wanda hakan ya tayar min da hankalina ya mamud na kira a boye don yayi min kashedin fadawa kowa halin da yake ciki din a ranan.
Ba bata lokaci ya iso gidan layina ya kira na fada mai ina sama wurin shi ya sameni a nan saman dakin shi do ban fito ba har lokacin.
Yana ganin yanayjn da dan uwan nasa yake cikine ya rude tare da tambayana zainab yaushe ya fara hakan nace dashi.
Lafiya lau muka kwanta dashi zuwa rabin darene hakan ya faru dashi har wanan lokacin wanan kan ba abin kyalewa bane dole mu sanarwa mami taji ya mamud din ya fada .
Layin mami ya fara nema ya fada mata nan ta hau fada don me ba a wuto dashi asibiti ba tun dazun ko so muke ya halaka a gida.
Mami kizo fa wanan kan ba abin kaiwa asibiti bane gaskiya sai jikinta yayi sanyi ta koma magana a hankali tana fadin .
Wani irin yanayi ne mamud kuyi wani abu don Allah kafin na karaso ta fada hankali tashe me zamu iyayi ga hakan mami sai kawai ta fashe da kuka ya kashe wayan.
Ina jin haka nace yaya ina zuwa na fita zuwa dakina bincike na fara yi kafin ingane maganin da tsohuwa kakan maya tayi min bayani ranan idan naga irin yanayin nan tare dashi.
Na fito da sauri zuwa kitchen na jona heater dan kankanin lokaci ruwan ya tafasa na hada komai na nufi dakin yan aikin gidan sai faman gaidani sukeyi da kwana ban tsaya binta kansu ba yadda na saba sama sama nake amsawa idan sun gaida ni din.
Dakin na nufa na samu yaya ya kamashi zuwa bandaki sun fito na shigo dauke da cup din maganin ina mashi sannu.
Saidana aje cup din nake fadin ya ko zaisha wanan maganin kafin mami tazo mu gani yace zaisha mana zainab kin hadane ya fara sha agani.
Na dan zauna ina fifitawa har yayi sanyi don ta fada min sai yayi sanyi sosai zaisha kamar yadda tace din haka nayi komai daki daki.
Yana kurbawa na farko ya saki wani irin gyatsa mai karfi lokaci guda sai kuma ya fara hamma ba kakautawa muna tsaye muna kallon shi nida ya mamud din .
Ya kara sake wani irin gyatsa har mai warin tsiya saida muka kawar da kanun mu ga kallon shi da sauri anan kasan ya leme sai barci .
Dan uwan na fadin ka hau gado idan barci zakayi zaifi ma dadi jafar ina har barcin ya kwashe shi ko a lokacin.
Daga inda nake na sauke ajiyan zuciyar da har ya fito fili ban sanda hakan ba sai ji nayi ya mamud na fadin .
Zainab kiyi hakkuri da wanan jerabawan da Allah ya aiko maki dashi haka tun ran gini ran zane Allah ya rubuto kece zaki shiga a cikin wanan wahalan haka.
Godiyan mu ga Allah da hakan ya kasance kece a gidan shi a matsyin matar shi a yanzu da wata ce ko wace mami ke gani a lokacin itace ta dace da jafar din ai da tuni zancen ya wuce nan ko.
Amma yanzu kinga tun mami naganin kwadayine har yanzu ita da bakinta ta gane gaskiya tana godiya da haka ya kasance kece a matsayin mata a gareshi.
Nasani zainab watarana mami zata rokeki gafara da bakin ta kan hakan tunda yanzu tasan abunda Allah ya shirya a zaman ki dashi haka.
Hakuri yana da dadi zainab don hakkurin ki yayi muna amfani kowa yanzu ya sani Aisha kanta jiyan nan nake jin tana fadin bata san da wani ido zata kalleki ba a yanzu.
Ko yanzu na sani maganin da kika bashine Allah ya taimakeshi ya samu barcin nan da yayi a yanzu don wallahi da badon Allah ya gyara ba yasha wanan abin da bansan me zai faru ba zuwa yanzu gareshi.
Hawaye ke fito min a idona na kurawa inda yaya din yake kwance ido kawai ina kallon shi ga mutum har mutum idan ka ganshi amma ya samu akasin rayuwa a tare dashi.
Muryan ya mamud din ne yake fadin ni nasan babu yarinyar da zata zauna da jafar ko na tsawon wata daya a wanan hakin haka da yake ciki.
Yanzu ne kowa zai gane shi mutum yana da ranan shi ta hanyar da baka taba zato ba don ance ke yar tallakane baki cancanci auren shi ba a lokacin.
Sai Allah ya nuna muna tallaka yana da ranan sa sosai don zaiyi abinda kudi baya iyayiwa mutum shi a rayuwa don na tabvatar da zabin mami din ya aura a lokacin da yanzu wallahi duniya ta gama sanin komai a yanzu.
Sallaman mami da su jamal ne da suka shigo hankali tashe dakin ya katse shi ga maganan da yakeyi a lokacin.


ZAINABASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH JUMMA,AT MU BARAK YAN UWA MUSULMAI ALLAH YA SADAMU DA ALHERUN DAKE CIKIN WANAN RANAN AMIN, , , , ,

Bin yadda yake kwance a cikin wahala kowan su keyi jamal ke fadin yana numfashi kuwa ?
Yanayi ya mamud ya bashi amsa ai don zainan ma ta taimaka ta bashi wani magani dazun ya sha shine har yake hakan.
Da sauri mami ta juyo ta sauke kallon ta gareni tana fadin me kika bashi ya koma haka zainanb me kika shirya kike son ganin bayan shi a yanzu.
Wallahi idan wani abu ya samu dana bazan taba yafe maki ba kema sai naga bayan ki har iyayyen ki.
Kai haba mami wanan maganan bai dace ba haka dan Allah ba don yarinyar nan data take tsaye a kanshi ba ai bamu san halin da yake ciki ba.
Wa yasan hanlin da suka tsunci kan su zuwa wanan lokacin da badon ita data bashi wanan maganin ba dazun da wallahi kila da yanzu mun rashi ga baki daya har abada.
Itace tafi kusan dashi take zaune dashi tasan irin laluran shi a yanzu don haka ba zamu zargeta ba mami, kan halin da yake bayan duk munsan da abinda yake damun shi a nan.
Jamal ne ya fara fadin gashi kuma mami kai brother asibiti haka kamar tonon asirine a wurin ki a garin nan sai nake ganin kamar a samo yarddaden likita a dauko shi gida yazo ya dubashi a nan.
Nima haka nagani ya mamud ya fada daga gefe mami kan ta koma ta zauna saman kujera ta kurawa dan nata dake kwance a kasa cikin wani hali sai hawaye take sakewa a lokacin.
Bata iya furta komai a wanan lokacin don bakin ciki da takaici da yai mata yawa a zuciyar ta ina zata kai wanan abin kunyar da jafar ya dauko mata a cikin iyalin ta yanzu .
Kai kome zasu fada a kaishi asibiti kawai wallahi a dubashi a san halin da yake ciki zaifi jalal ya fada.
Nima dai abinda naga yafi ke nan Aisha ta sake fada daga inda take zaune a takure a lokacin na dago kai da sauri tare da fadin .
Don Allah kada ku kai shi asibiti a cikin wanan halin da yake ciki haka ku taimaka ku rufa mai asiri da akaishi asibiti gara dai likitan yazo gida ya duba shi don Allah.
Ya mutu kike so Aisha ta fada a hasale tana kallona kamar zata cinyeni danya a lokacin da take wanan maganan cikin kunan rai take tambaya na hakan .
Mami ta dagp kai tana fadin gaskiya zainab ta fada fitar dashi haka zuwa asibiti tonan asirine kamar yadda kuka fada da farko.
Don haka kai mamud wani likita kake ganin zamu nemo a wanan case din nasa yanzu har lokacin idon ta na kansa inda yake kwance tana kallon shi.
Ina gefe ina sauraren shawaran nasu kai mutum dai ba abakin komai yake ba lafiya itace jarin ga mutum da ya kumce ma ka rasa komai, komai arzikin ka kuwa.
Wani likita ya mamud din ya kira yace a bashi dan lokaci yana tafe duk zaman da nakeyi wurin bakina na dauke da addua a lokacin.
Tun ina yi a boye har na fara fitar da sauti ina karatun a fili duk suka bini da kallo kamar kullun amanal rasulu nake karanta mashi sai yasin haka ma wanan lokacin shinakeyi a hankali suna saurarona.
Dakin yayi tsit sai muryana dake tashi a lokacin can ya dan motsa hannun shi kadan alaman yana son ya falka a lokacin.
Gaba dayan mu ido muka zuba mai kafin can ya bude idanun shi da kyat yana fadin zainab bani ruwa in sha don Allah ba wanda zai gane me yake fadi a lokacin don muryan shi daya dakushe bai fita sosai.
Na dago kai na dan kalli ya mamud dake kusa damu ina fadin wai ruwa yake son sha.
Bashi wanan can da kika rufe dazun ya sha tunda a kwai sauki sosai daya sha shi dazun na tashi a daidai lokacin da mami ke fadin ruwan meye wanan din sauran kuma duk suka bini da idanu har na dauko ruwan dake rufe a gefen gado cikin cup din glass.
Na kawo mai tare da dan kiran sunan shi ina fadin yaya ga ruwan ya bude idanun shi da kyat ya sauke a kaina.
Dan yun kurawa yayi don ya sha ruwan dake hannuna ya kafa kai yaja sosai kafin kuma ya dakata na dan lokaci ya dago kai ya kalleni.
Muryan ya mamud din ne yake fadin shanye mana jafar don Allah yana da amfani a gareka sosai.
Ya dan daga kai ya kalli inda ya mamud din yake kafin ya mayar da kanshi ga kallon dakin ga baki daya sai a lokacin yasan a kasa saman ties yake kwance don neman wa jikin sanyi a lokacin.
Muryan mami da yaji tana fadin kasha maganin mana jafar ka tsaya kana kallo kuma da sauri ya juya inda take tana zaune tana magana saman kujeran dakin nasa.
Sannun da yan uwan ke masa ne ya kara juyawa wurin su yana kallon su kamar bai ganesu ba a lokacin.
Karbi ruwan kasha yaya na fada daga inda nake tsungune ina bashi ruwan da zai sha ya juyo a hankali ya karbi ruwan daga hannuna.
Tunda ya kafa kai bai cire a cup din ba sai daya shanye ruwan ga baki daya ya miko min cup din na karba daga hannun shi.
Ki kamani in koma saman gado ya fada a hankali don haka sai na aje cup din sa sauri har yana faduwa kasa .
Ban damu da hakan ba nayi saurin kai hannu ina kamashi ya mike a hankali muke tafiya har zuwa bakin gadon ya dan zaunan kannen nasa suka kara mashi sannu ya amsa da kai kawai.
Har saida ya kwanta sannan na dago ina sauke ajiyan zuciya ya jamal dake tsaye ya tokare jikin shi da mirrow dakin yace dani sannu zainab da kokari.
Nayi dan murmushi na juya inda na aje cup din na dauka tare da nufan kofan fita daga dakin kai tsaye.
Fitana daga daki yayi daidai da mikewan mami ta nufi bakin gadon da yake kwance ta zauna a gefen shi a hankali jin hakan yasa ya dan juyo kai ya dan kalli wurin.
Ganin mami ne ta zauna a kysa dashi yasa ya dan juyo gareta yana fadin yaushe kuka shigo mami ina barci ko na dan samu barci ke nan ashe.
Don jiya bamuyi barci da dadi ba dagani har zainab a wahalce muka kwana a gidan nan amma yanzu naji sauki sosao barci kawai nake ji da kasala ya fada yana gyara kwanciyan shi.
A falo na samu su fadila da sauran yan aikin gidan suna zaune a cikin jimamen meke faruwa ne sunga su mami sunzo rai bace.
Gashi kuma har lokacin basu ga na fito part din ba hjy tana ta aika sadiya a duba ko lafiya anace mata ban fito ba.
Suna ganin fitowa na fadila tare da mai aikin wanke wanke da shara su kayo kaina suna gaidani sauran ma suka biyo bayan su suna gaidani.
Na amsa ina wucewa har na dan taka nake fadin anty in ganki mana ta biyo bayana da sauri sauran ma suka watse a lokacin.
Tunda basu ga wani alaman komai a tare dani ba muna shiga dakina a tare tana bayana nake fadin ko za,a samu freash meat da milki a gasawa oga yau baya jin dadin jikin shi tun daren jiya.
Aiya da sauki ko ta tambaya nace yaji sauki yanzu sosai yana can tare da su mami da yan uwan shi don Allah a gasa mai idan za a samu a aika da wuri na fito da kudi ina mika mata.
Take fadin jiya an bada kudin da za ayi sayayya barin aika a ciki a sayo komai yanzu ta fada da sauri tana fita na dan bita da kallo.
Wanka na shiga don a matse nake a lokacin ina shiga na sakewa kaina ruwan zafi sosai don har saida naji ya kama min jiki na goga sabulu na fito .
A gurguje na shirya duk da barcin daya cika ni a lokacinn don har idona sun fara nauyi a lokacin don barcin da nake ji.
Saidai babu daman yin hakan gareni don su mami dake gidan a lokacin dole in koma in sallamesu kafin su tafi.
Saidai ina shiga dakin ban samu mami da Aisha har jalal a dakin ba sun fita zuwa dakin hjy su gaisa da ita .
Sai ya mamud da jamal tare da wani likitan da aka kira shi ya jafar din yana zaune ya dan jingina jikin shi da gado.
Ina shigowa suka dan kalloni sai na dan tsargu da hakan na daburce ina tambayan mami su har sun fitane ?
Ya mamud ke fadin sun shiga wurin hjy yanzun nan da likita ya shigo zai duba jafar din na dan juyo ina gaida likitan kafin na sake juyawa zan fita daga dakin.
Muryan ya makud ke fadin ki tsaya zainab ga maganin da likita ya bashi da lokacin da zaisha idan time yayi na dan dakata likitan yana yi min bayanin komai.
Na tsargu da irin kallon da yaya jafar din ke min yasa ban ko tsaya fahinta ba na juya na fice daga dakin, wanan halin da yaya jafar yake nuna min na kishi a gaban wasu.
Dakin hjy na nufa a nan na samesu zaune nake gaida hjyn da kwana bata amsa ba take fadin ke yar nan ashe abinda ke faruwa ke nan har wa yanda basu kwana a gidan ba sunji sunzo mu bamu sani ba.
Kiyi hakkuri hjy ban fito bane sai yanzu ya mamud ne ya kira ya fada masu bani bace na kira na fada a ladabce.
Yanzu ya jikin nasa da sauki ko nace yana ma zaune suna hira na fada sai ga fadila ta shigo tana fasin madam an gama komai kamar yadda kika ce ayi.
Na amsa da godiya ina fadin gani fitowa in duba mami ke fadin bari su leka ta ji me likitan ya fada game da jikin nasa ni dai kafin su fito na bar dakin kai tsaye.
Na samu sun shirya komai yadda ya dace na dan duba kafin na dauka na nufi dakin nasa dashi suna cikin dakin dukkan su a lokacin na samu likitan ya mike yana tsaye suna magana da mami na shigo dakin.
Kai tsaye na kai gaban shi na aje na dauko dan stole na dora akai ban kai ga mikewa ba mami ke fadin wanan meye kuma aka kawo mashi ?
Duk idanuwan su yana kan abincin na bude va tare dana bata amsa ba kamshine ya game dakin lokaci guda da tururin abincin yana tashi sama.
Gurfane nakai a gaban shi tare da dan dago kai ina fadin a zuba da yawa zakaci ko ya dan kada kanshi kadan ba tare dayayi magana ba na fara zuba mai a hankali saida ya dan kai yadda yake tunanen zai iya ci yace ya isa.
Good likitan ya fada yace wanan ya dace dashi a yanzu yadda yaji jikin nan dole sai irin wanan abincin dama normal milk danye na tsiyayya mai tare da ajewa gefe na mike tsaye duk suna kallon abinda nakeyi a lokacin.
Juyawa nayi zan fita yake fadin ina kuma zaki ki zauna muci don nasan kema baki karya ba har yanzu zan tafi in duba sadiyace ban gata ba tun dazun na bashi amsa na fita.
Gaskiya zainab tana da kokari wallahi tasan duk abinda ya kamata ba sai an fada mata ba jalal ya fada Aisha ta amsa da gadkiya kan .
Da gaskiya gun sadiya din zan tafi don duk abinda nakeyi hankalina yana gareta na rashin ganin ta da banyi ba din.
Tana kwance ta rufe jikinta wai sanyi take ji alaman dai bata da lafiya ke nan na karasa wurin ta hankali tashe.
Ina kware abi rufan tare da dan kiran sunan ta ina tambayan ta meya sameta ta nuna min kanta ke ciwo.
Fadila ce ta shigo dauke da abinci a ture take fadin dama yanzu nake fadin kila baki san bata da lafiya ba haka ashe kina nan ma.
Ta aje kayan tana fadin dama ina son in fada maki daren jiya bamuyi barci ba a gidan nan duk wanda ya kwana a gidan nan a jiya yaji tsoroa gidan nan da bamu san dalili ba.
Allah ya taimaka daga hira sadiya tayi barci a wurina nan muka kwana a dakina a tsorace sai kusan asuba muka daina jin tsoro .
Basar da zancen nayi ta fadin kai kodai iskan da kukaji anyi jiuan ne kuke jin kamar motsine anty tace wata kila ko hakan ne wallahi.
Nan dai muka zauna a tare mukayi break fast a daki mu uku muna hira wayana ne ke ringing a lokacin na dauka .
Malam ne kakana jin na ambaci sunan malam din yasa su kallona muna gaisawa na mike na fice a dakin .
Mun dade muna magana dashi yana ban labarin artabu shi da bakin shi a daren jiya din inda yai nssaran koran su fata fata ta yadda ba zasu kara tunkaranshi ba da yardan Allah.
Nan ya fada min wasu abubuwan da zanwa jafar din nayi mai godiya bayan munyi sallama na fito zuwa dakin hjy na samu tana sallah a lokacin.
Na juya na fita daga dakin fafila ke fada min su mami sun tafi ya mamud yace naje na duba jafar din da suka bari shi kadai a dakin shi.
Na shiga na samu ya dan mike zai watsa ruwa shigowana ya jiyo yana fadin wanka nake son inyi ko zan kara jin karfin jikin nawa a yanzu
Bari na gyaro ban dakim na fada ina kallon shi jikin shi yayi wani irin radau radau kamar yasha duka ko sunyi fada da wani a lokacin.
Bi jikin nasa da yaga inayi da kallo yasa ya dan juyo yana kallln jikin nasa yace wanan kike kallo aiba komai bane tunda sun barni da raina.
Ke nan su din ne suke baka wanan wahalan na tambaye shi ina kallon shi yace ya zasu dani tunda yanzu na daina duk wani abinda suke so na taka masu doka suke gani
Zaman lafiya shine kabi tsarain su da dokan su a zauna lafiya ko kinsan kwamciyan kinan a tare danine dalilin wanan azaban da nake sha a yanzu.
Na zargi hakan dama tunda naga wanan wahalan naka yayi yawa a yanzu idan har shiga dakin zai saka su dinga baka wahala haka zan daina shigowa yaya don su daina.
Kina tsoron hakan ne ya tambaye ni nace ba wai tsoro hakan nakeji ba tun farko yaya ka riga da kashiga kungiyan su yanzun ko ya zama dole a bisu a sannu don ka zauna lafiya dasu din .
Dan murmushi ya sake a fuskan shi tare da fadin koma me zasuyi min a yanzu sai dai suyi don na daina wanan harkan har abada ke nan insha Allah.

ASSALAMU ALAIKUM FATAN ALHERI GAREKU DUKKA MASOYA ALLAH YA TAIMAKA YA BADA SA,A A RAYUWA AMIN


LITTAFIN NAN NA KUDINE YAR UWA KIBBIYA DARI UKU KI KARANTA A CIKIN SALAMA YAR UWA.


Idan na tsaya fadan irin wahalan da yasha a wanan lokacin zamu bata lokaci a labarin don amai da gudawa yayi shi yafi a kirga tun yana iya tashi yaje da kanshi har yakai baya iya tashi a lokacin.
Kuma ban daina mashi amfani da maganin wurin malam da kakan maya da suka bamu ai amfani dashi don matsalan.
Duk da nasan maganin suna da karfi suna daya daga cikin abinda ke karasashi zama weak a yanzu saidai hakan baisa na tsorata ba don malam dake kara min kwarin gwiwa da shi da maya a ko wani lokaci.
Har yan uwan shi ba,a bari sun san da zancen wanan rashin lafiyan nasa ba cewa ake ya yayi tafiya a lokacin.
Haka kuma ya mamud ya gargadi duk wani wanda ke gidan a lokacin idan azo nemasa yayi tafiya dazun da asuba duk da sunyi mamakin jin ogan nasu yayi tafiya ba tare da sanin su ba.
Don ya saba idan zaiyi tafiya ya tarasu ya dan raba masu dan kudin kashewa a hannun su sai sukaji ya tafi bai samu ganin su ba hakan sai bai masu dadi ba a zukatan su.
Sannu a hankali jikin ya fara dawo mashi daidai duk da hakan kuma ba a leka asibiti dashi ba nice sai yan uwan shi muke fama dashi haka a gida har Allah ya kawo mai sauki a hankali ya fara fitowa falo yana shan iska idan ya gaji ya koma daki kuma.
Yau da kanshi ya fito dan karamin falon shi ya zauna ya dan mike kafan shi a saman dan karamin stol dake wurin.
Ya dafe goshin shi da hannun shi daya tare da kurawa kasan dakin ido yana tunane.
Yayana yau da kanka kafito na fada abinda yasa shi dan dagowa ke nan daga yanayin da yake zaune din, ya dan dago kanshi ya dan kalleni tare da dan sake murmushi ta gefe fuskan shi.
Aje dan cup din da na shigo dashi a hannuna nayi daga gefen shi ya kalla ya wani bata rai kamar karamin yaro a lokacin.
Dan murmushi nayi na koma gefen shi na zauna ina kallon shi kafin ince sauki ya samu ke nan tunda har ka fara tsanar magani a yanzu.
Bana jin dadin sha sa a yanzu ya fada yana kawar da kanshi gefe daya nace hakkuri zakayi kasha daga gobe shike nan ya kare ai.
Zama ya gyara a irin yanayin dana riskeshi a ciki da farko sai dan shiru daya biyo falon tsakanin mu na dan lokaci.
Kafin muryan shi ya maye shirun da fadin zainab nasan kina kokari dani ba kowa bane zaiyi wanan abinda kike min duk da kinsan makasudin matsala kika zauna dani haka kuma kika yi jinyana a hakan .
Duk da irin halin da mami da yan uwana suke nuna maki a kaina hakan baisa kin gujeni da halina ba duk nasan abin yana damun ki a cikin zuciyar ki kuma.
Kiyi hakkuri ki yafe min duk wani abinda nayi maki tun haduwana dake zainab ina rokon ki da kiyafe min don Alla.
Da sauri nakai hannu saman bakin shi ina rufe bakin nasa da hannu ina fadi cikin murya mai nuna alaman kuka a lokacin .
Ka daina fadin haka yaya ko nayi aurena nayiwa kuma wa mijina nayi don ance aljannan mu mata yana karkashin kafan mazajen mu.
Kai din kuma koba aure a tsakanin mu kacancanci hakan a gareni ya don kaimun komai a rayuwana yaya ka ingata rayuwana ka taimakawa kanwa da yan uwana ashe nima din ba zan saka ma da irin alherin da kake min ba a kullun.
Taimako a tsakanin mu Allah ya hada zaman rayuwan mu a wuri daya hakan na nufin mun zama daya da kai a yanzu.
Idan kana cikin farin ciki ko akasin hakan nima hakan ya shafeni don nayi ma abu ba sai ka gode min ba kaina nayiwa hakan.
Wasu hawaye masu zafine suke zubo min na kasa magana naji ya jawoni zuwa jikim shi yana dan buga min baya kamar karamar yarinya a lokacin.
Zainab ki godewa Allah da ya sa kika zama silar shiryuwana a duniya dana mutu a cikin wanan halin da ko uwata ta kasa fitar dani a ciki sa ya zanyi me zan fadawa ubangijina a wanan halin.
Ke din zainab alherice ga duk wanda kika zauna dashi ke haske gun duk na tare dake zainab farin cikine ya dace dake a yanzu ba kuka duk da wani farin ciki sai a kuka bawa ke iya nuna hakan.
Don haka kiyi kokan ki a yanzu don kukane ya dace damu a yanzu don godiya gun ubangijin mu.
Ina son ki sani ni jafar nayi maki alkwari a yanzu duk wasu munanan halaiyan da nakeyi a baya na daina su har abada kuma inawa masu irin halina na baya da Allah ya fitar dasu a cikin sa kamar yadda yai min sanadi dana barshi nima a yanzu.
Yakai yanzu kunyan kaina nake ji da duk wani na tare dani dayasan hakan a kaina ina bakin ciki a yau dana wayi gari ina tuna nayi wanan halin dabbobin a baya zainab.
Sai kawai naji ya fashe da wani irin kuka mai taba zuciya a lokaci daya , rudewa nayi na rasa abinyi sai can na koma fadi in girgiza kai don Allah yaya ka daina wanan kukan bashine yanzu a gaban kaba.
Dacewa yayi ka koma ga Allah har idan kasan akwai wani sauran abin haramun a tare dakai har yanzu kayi gagawan fitar dashi a gare ka .
Ta hanyar yin sadaka ko ka tambayi malamai abinda ya dace kayi da wanan abin shine nake ganin abinda yanzu ya saura kayi .
Ma,ana a cikin dukiyan ka ko wani kaddara daka aje da kudin hharamun sai kayi gagawab fitar dashi a hannun ka don a yanzu ya haramta a hannun ka tunda ba ta hanyar halal aka sameshi ba.
Ajiyan zuciya naji ya sauke tare da lumshe idanuwan shi yana gyara zaman shi tare da mike kafafuwan shi duka biyu kafin yace.
Duk ba wanan bane damuwa na zainab don nasan dukiyana na zufanane na sameshi a kashin kaina ga baki daya.
Elimenatis din mu kawai na wayewa ne da harkan homo bawai don arziki bane ko wani abu kawai dai hakan wayewa ne a garemu duniya ta dauki mutum da tsoro ko wani abu can.
Ai akwai wa yanda basu da komai kuma suna ciki kungiyan tare da kowa kawai ni yanzu abinda ke damuna shine.
Sai ya dan ja numfashi yana girgiza kai kafin ya bude ido ya kalleni yana nunani yace damuwa na shine zaman mu dake zainab a yanzu.
Ban san a wani matsayi aurena dake yake gun malamai idan zasuyi bayani zainab ina tsoron kada su fada min ke din ai kin haramta a gareni yanzu .
Don tsawon dadewan da mukayi a tare ban sauke hakkina a kanki ba da kuma manufan da na aure ki akai a yanzu wani matsayi aurena dake yake ga Allah ?
Da sauri na daga na kalleshi kafin na mayar da kaina na dukar a sanyayye wani irin harbawa kitjina keyi lokaci guda don sam wanan tunanen banyi a lokacin ba.
Tunanen hakan sam bai taba zo min ba don ban dauki hakan a wani matsayi ba can na daban da zai iya kawo shamaki a tsakanin mu.
Tsam na mike daga yadda muke zaunen na dan gusa nisa dashi ina jin faduwan gaban nawa na tsanan ta.
A yanzu wani iri nake ji azuciyana da yayi wanan maganan dan jinyasa kawai ya kara saka shakuwa sosai a tsakanin mu wanan lokacin.
Shima din da alaman hakan ke damun shi cikin zuciyan shi a lokacin na sameshi yayi shiru dana shigo yana tunane.
Karshe mikewa nayi don ba zan iya jure zama a falon ba a lokacin bina yayi da kallo har na fice ya mayar da idanun shi yadda suke yana maijin tausayin mu a zuciyan shi .
Ina shiga daki na fada saman gado na sake wani irin kuka lokaci guda kukan da bazan ce ga dalilin yin shi ba a lokacin shin kukan bakin cikine koko na murna nakeyi a lokacin.
Abin mamaki nida na dawo Nigeria da zuman rabuwa dashi har abada a zuciya sai gashi yau abin mamaki ina sake hawaye akan ya furta zaman wata kila dashi a yanzu ya haramta.
Don wasu dalilai dabai cika ba na sharia tun yin aurena dashi dana zauna a tare dashi a matsayin nazo aure gare shi.
Ni kadai a dakin na kasa samun natsuwa a tare dani zuciyana ina jin ba dadi a yanzun tun bayan wanan maganan da mukayi dashi a part din shi din.
Haka na wuni sukuku dani da damuwa cike tare dani na rasa sukuni a wanan wunin ba abinda ke min dadi a zuciyana.
Bayan na sallame sallah isha,i ne na jawo wayana na tasa a gabana ina kallon lokaci a wayana ina dakon time din da nake tunanen malam ya shiga gidab shi a lokacin karfe tara ke nan na dare.
Saida na dan bada lokaci kafin na dauki kiran na danna maaa kira kamar kiran zai katse ya daga da sallama muka fara gaisawa dashi.
Yake tambayana jikin jafar din na fada mai yadda yanayin jikin nasa yake a lokacin yayi masa fatan samun sauki a tare dashi har abada.
Kafin nace da dashi malam tambaya nake dashi yace na,am ina sauraren ki zainab nan na jefo mashi tambayan sai naji yayi murmushi ya fata min bayani tiryan tiryan yadda zan fahinci yadda maganan yake a addinance.
Saida ya gama min bayanin nayi mai godiya mukai sallama na kashe wayan a hankali na kai kwance a wurin ina lumshe idanuna.
Dare yayi ban iya lekowa ko falo ba balle nace zan tafi na duba shi don yanayina ya koma kamar na mara lafiya yin yau.
Ina kwance a kasa a inda nayi sallah kuma nayi waya da malam ya wayar min da kai kan maganan kamahin turaten jikin shi ne ya ziyatci hanncina a lokacin.
Jin hakan duk dana gane shine ya shigo dakin a lokacin amma hakan baisa na daga ba daga yadda nake kwance a kasan dakin saman salayan.
Tun da ya shigo idon shi yake a kaina ya karaso yana dan kiran sunana da zainab ko barci kikeyi ne wai ?
Na dan daga tare da fadin idona biyo banyi barci ba ya kalleni ya dan sake murmushi a fuskan shi yaja jikin shi zuwa bakin mirrow ya tsaya tare da jingina da jikin mirrow din yana face dina.
Sake ambatar sunana yayi yana fadin zainab meke damuwan kine yau ko bakya jin dadin jikin ki ne yau din ?
Sai lokacin na dan dago na zauna a hankali ina kallon shi kafin na mayar da kaina na duka ina fadin lafiya ta kalau nake.
Kin manta da kina jinya ne baki lekani ba tun dazun ya sake tambayan yana hakan sai dan sake murmushin dole ina dan gyara hijabin dake jikina nace.
Ban manta saidai naga majinyacin nawane a yanzu ya samu sauki yasa na nisanta kaina dashi har zuwa lokacin da za a warware matsayin zamana da kai.
Shima dai dan murmushin yayi ya gyara tsayi yana fadin au kan wanan maganan yau yasa ban samu kula yadda aka saba min ba kullun ?
Ko kema bakya son rabuwan namu ne a yanzu kamar yadda nima nakeji idan hukuncin hakan ya hau kanmu ?
Na danyi murmushi tare da girgiza masa kai ina fadin a, a ko daya saidai kawai ina jiwa sabone da juna da mukayi da kai a yanzu.
Amma nasan ko mun tafi kai baka da wani kewa ko damuwa ai irin wanda mu zamuji na rabuwa dakai a yanzu.
Don dama a shirye ake da a aura maka wace ta dace dakai a rayuwan ka don farin cikin kowan ka koni a yanzu nasa ba sa,an ka nake ba.
Ya dan kalloni da mamaki a fuskan shi kafin yace wanan shine tunanen ki a kaina zainab ?
Har kina tunanen akwai wata macen data dace dani a yanzu kuma bayan ke ? ke dince zabin da Allah yayi min koda akadara hukuncin rabuwa a yanzu ya hau kaina sai dai in zauna hakana ba tare da aure ba a gareni.
Aiba kai zaka aurawa kan ka ba wanan karon aure za aima kamar kowani da dan gata a duniya irin naku na yayan attajirai a kasan nan don duniya tasan da auren ka.
Murmushi kawai yayi ya dago tare da fadin idan kin gama fadin abinda ke zuciyar ki yanzu saiki hado min magani nasha na kwanta.
Daga haka bai tsaya ba ya fice daga dakin na sauke ajiyan zuciya ina maijin daci a kasan zuciyana kamar ya fashe a lokacin.
Ban bita yadda nake ji a zuciyana ba na mike na hada mai maganin nakai masa na samu har ya kwanta saidai ba barci yakeyi ba a lokacin.
Ina tsaye har ya mike zaune yasha ya miko min cup din na juya na fita daga dakin bai kara ganina ba sai washe gari dana kai masa maganin yasha ba tare da yai min magana ba har na fita.
Yasan dai dalilin hakan a yanzu kan wanan maganance da yayi min da yanzu yake daya sanin furta hakan a garebi.
Don ya fahinci zan juya maganan ya zama wani manufa ta daban a gareshi saboda ya fahinci kawai wani aure nake zato a gareshi a yanzu.
Ya tambayi kanshi dama ina jin shi a zuciya har hakane ashe don gashi na fara nuna kishin shi da wata mace a duniya a fili.
Niko ina komawa dakin hjy na nufa na samu tana zaune tana dan kirga kudin ta tana jin na shigo dakin tayi maza zata boye kudin sai kuma ta fasa tana fadin .
Ai kece na zata ai wanine zai shigo dakin bake ba har abin yaso ban dariya na dan dara kadan ina fadin.
Hjy duk wanan kudin nakine haka tace ba kaji ba shiyasa bana son a gane su haka kada a saka min baki tana kokarin daure kudin cikin jikinta.
Sai kuma ta fasa tana fadin ko na dan baki wani abune ki rika dama dan kudin da bayin Allah dake zuwa gaida nine nake tarawa kinga dana koma sai in taimakawa kawun ku Amadu dana cefane kome kika gani yar nan.
Kinsan shi Amadu baidashi kuma ga tarin iyali Allah ya bashi kullun a cikin wahala yake na iyali shiyasa nake dan tausayin shi a cikin su.
Kaina girgiza jin takai aya ina fadin hjy bar kudin ki kaiwa kawu ya fini bukatan kudi a yanzu ni nan babu abindana nema na rasa a rayuwa.
Tace wanan nake maki fata yar nan ko yaushe gashi har kina fadi da bakinki a yanzu hakan shine shedan kwarai wurun mace ga mijinta.
Ni kaina naga alaman hakan a tare dake a yadda kika koma din nan kamar a tabaki jini ya fita din nan hakkuri ke nan idan ka yishi kana da riba sosai a wurin Alllah tun a nan duniya.
Ki kara rike mijin ki dakyau yar nan irin mazan ku yanzu tsadane dasu a duniya ba kowane ke samun su ba a rayuwa na dan murmusa na ciki na ciki ina fadi a zuciyana.
Kedai tsohuwa ayi sha,ani an cuci na kauye baki san komai ba don ABU CIKIN DUHU SIRINE namiji ko tallakane indai halinsa yana da kyau shine dace.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAWA IDRIS MAKAWAZAINAB IDRIS MAKAWAZAINAB IDRIS MAKAWAASSALAMU ALAIKUM YAR UWA ALLAH YA BAMU WUNI LAFIYA ALLAHUMA AMIN ALLAH YA TAIMAKI MUSULMI A DUK INDA YAKE AMIN YA ALLAH, , , ,

Yanzu sai kuma zaman namu ya dan sauya don wanan kalman daya furta min din sai nake ganin ai
kawai a yanzu na haramta a gare shi .
Zuwa wurin shi din bai zama wajibi a gareni ba kada muzo mu aikata wani zunubi a hakan do gashi yanzun da dabi,an son rugumeni a jikin shi ko yaushe .
Wanda hakan nakewa tsoro tunda ban san matsayina a zuciyar shi ba kamar yadda malam din yayi min bayani.
Don haka a yanzu ya zama dole a gareni na nisanta kaina dashi don ina ganin rashin dacewan hakan a garemu baki daya gujewa afkawa ga fushin ubangiji a kan mu.
Gashi a yanzu duk wani laifi nasa dake zuciyana a baya na daina ganin hakan illa zalla tausayin shi dake cikin raina a yanzu.
Ba komai nakewa tausayin ba na farko dai ko dadin bakin mazane da yaimin daya nuna shima kamshi baisan lokacin daya fara wanan harkan ba.
Haka zalika badon kudi yake irin rayuwan ba kawai dai don giyar kurciyane dake diban mutum a ganuwan kurciyar sa.
Malam kuma ya fada min cewa akwai asiri a kanshin tunda kurciya akaso ya lalace saidai da yake a lokacin mahaifin su yana nan bai zauna hakana ba yasa asirin a lokacin baiyi tasiri a kanshi ba.
Amma yanzu da uwar suce kawai wace tafi maida hankali ga aiki da neman duniya kawai bata da lokacin tambaya da neman taimako akan zuri,anta a yanzu.
Sai uwa uba irin nuna min da yayi shi a yanzu ko ance ba auren mu don irin dadewan da mukayi da taimakon dana bashi baiga wata macen da zai kara zama da ita da sunan aure ba a duniyan nan bayan ni.
Wanan hujojin yasa na hauna zauna a kai ina jin tausayin mu a zuciyana don yanzu in ma haushine nafi jin haushin mami fiye dashi don ganin da nake kamar ita duk munanan halaiyar sgi ba dame ta ba ita.
Bata dauki hakan abin kyama a gareta ba kodan rayuwan turai da tayi ta saba da ganin hakan har yasa take daukan abinda karamin zunubi a wurinta oho ?
Idan nace bata damu ba ba laifi bane duba ga yadda wasu mata a yanzu suka ba aikin su muhinmanci sama ga zama su ba yayan su tarbiya da kansu inganttace .
Nasan wasu na da lokacin hakan saidai kosu ba yadda ya dace din bane akeyi a yanzu don ya zama dole a gareki ke uwa kisan a ina kike barin yayan ki idan zaki fita koda kuwa ba wuein aiki bane a yanzu.
Cusawa yaro tsoron Allah tun yana karami a zuciya da irin azabobin da Allah ya shimfida ga wanda ke masa sabo.
Wanan idan uwa tana hakan yana kawo yaro ya tashi da tsoro a cikin zuciyar shi sabanin wasu uwayen na yanzu da yaro zai ga abin asha a tv yana kwakwayo uwaye su zauna suna dariya ga abinda yaron ke koyo na bata tarbiyan shi.
Zama da dan ki walau namiji ko mace kuna hiran abokan sa tanan zaki fahinci dawa danki ke mu,amula a bayan ki.
Yawan dafa kai ko a cikin wasa kina sakawa dankin albarka tare da adduan kariya yana sa yaro ya kara imani yaji tsoro da tausayin ki ke uwa azuciyar shi koda bayan kine kalan irin yabon da kike masa zai tuna ya fasa aikata wani abin.
Idan kinga da ko yar wata ta lalace bakin ki ya saba da fadin ubangiji Allah ya shirya muna ku kiyi shi a cikin jam,i kada a zauna dake ana gulman dan wani dan sheri jifane dawo kan maishi yakeyi komai dadewa ubangiji ka bamu ikon gyara halayen mu da zurian mu Amin.
Naga abinda nakeyi tsab na shirya kamar yadda na saba samun shi a dakinshi in mashi ina kwana idan yana bukatan wani taimako nayi mai a gurguje in fito.
Yau ma hakan nayi na nufi dakin sai kamshin oud din jikina ke tashi duk inda nabi don a cikin gida nake nakan shafa abina son raina don gasu nan aje kala da kala a dakin wani ma ban taba amfani dashi ba.
Da sallama a bakina na shiga dakin nasa zaune na hangoshi saman gado ya mike kafafun shi ya harde su a wuri daya tare da hade hannayen shi suma ya saka a tsakiyan cinyar shi yana aikin tunane.
Kallo daya za kai mai ka gane yana a cikin wani yanayi na damuwa a lokacin duk gaba daya ya fita a hayacin shi a yanzu.
Kai ya dago a hankali yana kallon kofan tare da amsa min sallaman ya mayar da idon shi kasa wurin kafafun shi yana kallo.
Ina kwana yaya na fada tare da jan in tsaya daga dan abin zaman bakin gado da ake ajewa a yanzu gaban gadajen kasan waje a yanzu.
Ba tare da ya amsa min ba Kai ya sake dagowa a hankali ya kalleni da kyau kafin inga ya dan sake murmushi a fuskan shi can kuma ya girgizan kan nasa a hankali.
Zainab na gane yanzu guduna kikeyi bakya kaunan zama a kusa dani ko kadan a yanzu ko kema kin koma kyama nane a yanzu abinda bakiyi min ba lokacin da nake cikin aikata sabon da nayi a baya.
Ko kuwa har yanzu kina zargina a rankine akan ban daina abubuwan da nayi a baya bane a yanzu ?
Idona kura mai a inda nake tsaye ina kallon shi tare da sauraren abinda yake fadi a lokacin har sai daya dakata na dan gyara tsayuwana ina fadin.
Ba haka bane yaya ina gudun mu fadawa fushin Allah ne ga hakan tunda kayi wanan furcin a gareni nake tsoro da taka tsantsan a zaman mu yanzu.
Me zaisa na gujeka a da can ban guje maka ba balle yanzu da nasan kafi bukatan a zauna dakai zan fara gudun ka kuma ?
Laifi Allah kawai ai yaya yanzu tsakanin kane da ubangijin ka kanemi gafara a aurin shi mu kuma na tare dakai mu taya ka.
Murmushin da yanzu ya kara zama dabi,an shi ko yanzu shiya sake min din don abindana fada a lokacin gefen shi ya dan bubuga alaman in zauna a wurin.
Kallon wurin nayi kamar mai nazari kafin nayi ajiyan zuciya na kai zaune a hankali kamar mai tsoron hakan.
Zamana dan shiru dakin yayi kafin yace dani banyi tsamanin za a samu matsala a kan zaman namu ba a yanzu sai dai shi tambaya yana da amfani don yanzu ban kaunan wani abu da zanyu wanda zan sabawa ubangjji na a yanzu.
Wanan yasa nake son nayi tambaya akai dan kada muzo mu tabka sabon Allah kema in jefaki a cikin fushin ubangiji.
Ni kaina zainab nasan na cuta maki na tauye maki hakkin ki daya rataya a kaina kuma kikayi hakkuri ga hakan bawai don abin hannu yasa kikai hakkurin zama dani di ba a a .
A yanzu na kara fahintar kawai dai Allah yayo ki mai tausayine da jin kai na tare da ita tun a zamanin zaman ki gidan mami na fara fahintar haka.
Saidai ban gaskantan hakan ba sai zamana dake a yanzu na kara fahintar hakan akanki any way anjima ki shirya zamu fita sha biyu zuwa gidan mami akwai malamin da za a kira jan matsalan namu a can yau.
Gabana ne naji ya fadi lokaci guda har yakai ba dan dago da sauri ina kallon shi ido ya dan lumshe tare da kada min kai alaman eh.
Nayi karfin halin fadin Allah ya kaimu a sanyayye ko dan ya kawar da zancen ne a lokacin ya jefo min tambaya da maganin nawa ya kare ke nan naga kin daina ban.
Ajiyan zuciya na sauke tare da fadin iya adadin da akace ayi amfani dashi ke nan na fada ba tare dana dago kaina ba.
Hjy fa ta fito yau kuwa ya sake jefo min tambaya nace yau banji motsin ta a falo ba ta fito ba tukun na dai je mun gaisa da ita dazun tana lafiya.
Yunkurawa yayi yana fadin muje dakin don da ita zamu tafi gidan mami din an jima ya fada yana tashi zaune kafin ya mike nabishi da kallo.
Kada kiji wani abu zata kai masu ziyarane ita ba abinda zai kaimu zai kaita ba ya fada yana tsaye.
Ban bishi dakin hjy dakina na wuce ina tunane kafin na kira layin inna na labarta mata abinda ke faru sama sama.
Sai ji hankalin ta ya tashi lokacin kuma nayi dana sanin sanar da inna din duk da ban fito fili na fada mata ga dalili ba amma sai ta rude .
Har na dan fara zargin iyayyena a raina ina fadi cikin zuciyana wai ko sun damu da damuwana kuwa ?
Sai nake ganin kamar dan abin duniyan da ya jafar ke basu akai akai yasa basu ganin laifin shi a kan komai .
Saida abinda ban sani a lokacin shine komai munin aure ga diya babu uwa ko uban da zasu so auren yarsu ya kare sai in hakan mukaddari a wurin Allah dama akai rabuwa a cikin auren .
Sai dai kuruciya ya hana in gane hakan a lokacin nake ganin laifin iyayyena kan son na zauna gidan jafar don abin duniya da ya rufe masu ido a lokacin.
Kafin sha biyu har na shirya shi kawai nake jiran fitowan shi don bani da kwanciyan hankali a lokacin son har na fara yanke hukuncin abinda zanyi idan na bar gidan nasa don kada rayuwana dana iyayyena ya wahala gaba.
Sai gashi ya shigo dakin nawa a cikin shirin shi yasa wasu shadda masu ruwan sky clour dinkin su ya tsaya masa iya gwiwan shi hannun rigan karami shima iya gwiwan hannu ya tsaya mashi sai kamshi ture ke tashi a jikin ranan har yar hula baka mai kyau ya saka a kanshi sai hakan ya kara fito mashi da kyawon shi fili duk da ya rame a lokacin.
A falo muka samu hjy zaune tana jiran mu yake fadin lalai hjy kina jin fita yau din nan har kin rigamu fitowa ke nan suka dan taba wasan jika da kaka kafin mu fita daga gidan.
A gida nabar sadiya don tace bazata gidan mami ba ita dataji can zamu tafi duk da fadila nasan tasan komai dake faruwa a gidan sabanin sauran yan aikin da basu san abinda ke faruwa ba sai aikin gaban su da sukeyi.
Amma ita kan nasan ta san komai dake faruwa a lokacin nuna kawai take bata sani ba nima kuma ban mata wanan maganan ba sam.
Ko lokacin da muka fito zamu fita din dagani akwai magana a bakin ta saida babu idon yin maganan ne a gareni balle ta tambayi abinda take son ji din.
Mota daya mukai amfani dashi zuwa gidan mami din shine gaba zaune da driver muna baya nida hjy.
Dan tafiya muka shigo unguwar su mami din ban dago kaina ba daga yadda nake zaune a bayan mota nayi tagumi sai faman sake saken da nakeyi a cikin raina .
Tsayawan motan yasa na dago kai ina kallon get din gidan da maigadi ya bude a lokacin a raina nace kila zuwan karshe kenan da zanyiwa gidan nan a hankali na mayar da idona na rufe har muka karasa shiga cikin gidan.
Muryan jalal yasani bude ido don jin yana fadin a, a bros kune tafe ashe gara da ban fita ashe tun dazun ya fada yana karasowa bakin motan.
Ganin hjy yasa ya koma kanta yana janta da ba,a har dai muka shiga cikin gidan yana wani ja mata hannu suna tafiya a hankali ina bayan su nima tare da yaya dake waya daga gefena.
Gaba dayan su kowa na falon zaune kasancewa ranan ba aiki duk suna gida ga baki dayan su har mami tana falon tare dasu.
Sallaman suka amsa na jalal amma sai idon su ya dawo a kaina sun kasa boye kyashin su a zukatan su a kaina.
Gaida hjy sukeyi da yayan su sai Na,imace take ce min zainab sannu da zuwa na danyi murmushi ina amsa mata a cikin dan fara, a har take fadin ga wuri kizo ki zauna tana kokarin tashi ta ban wuri.
Da sauri nace a,a anty ki barshi in zauna a nan na nuna kasa yace No cikin dakewa ya kalli Rufaida yace ke bata wuri ta zauna.
Saida tayi wani iri kafin ta mike a cikin fushi zata bar falon mami tace keko tsiyana dake ke nan wallahi saurin fushi Rufaida.
Tace to mami sai kuma tayi shiru ta kasa karasawa don wani irin kallo daya watsa mata yasa tayi shiru.
Dole ta dawo ta zauna a gefen mami din tana wani irin shagwaba mami tace kedai zuciyar nan naki zata wahal dake wallahi .
Ni kan zaune nakai a bina duk ina kule dasu irun yadda kowan su ke satan kallona tundaga kafa zuwa samana.
Na fara gaida mami bayan na zauna ta dan juyo da dan fushin fadan da takewa Rufaida ta amsa min tare da fadin ya gidan ya dawainiya da hjy.
Nayi dan murmushi na gyara zama bayan haka ba wace muka gaisa da ita a cikkn in bayan Na,ima da tun shigowan mu tayi min magana.
Sai suka wayen ce hakan da hira da hjy na nuna ban masan suna hakan ba gareni ina dakalan wayata daya dauke masu kuma hankali ga ganin ta.
Jamal ya shigo shima da alama baisan da zuwan mu ba sai lokacin suka gaisa da dan uwan shi nice na fara gaidashi yake fadin.
Zainab kun sha Nageria fa nasan ba don ciwon yaya ba da yanzun kun koma ai jalal ya karba a bayan shi daga inda yake tsaye.
Me zaisa ta damu ta koma tunda ba karatu takeyi ba yanzu Aisha da tun shigowan mu batayi magana ba ta fada a yanzu.
Ke lokacin da aka dawo kasan nan ai kuka keyi zafi ya isheki zaki koma jalal ya fada budan bakin ta sai cewa tayi aini a lokacin na tashi cikin jin dadi na sai kawai a daukoni a kawoni nan.
Amma kuma a yanzu kinsan zainab ta fiki samun dadin da kike fadin kin samuba can don haka ai ba abin mamaki bane don tace zaman Nigeria ya ishe ta a yanzu.
Wani tabe baki tayi tana kawar da kai gareshi bata ji dadi amsan daya bata ba daga inda mami take zaune tace koma dai meye a yanzu ba zaka taba hada Aisha da zainab ba ko ku ke nan kullun cikin gwatsale yar uwan ku a gaban kowa.
Look ba nazo nan da mata na bane don a riga challangen din ta haka koma meye a yanzu zainab zamana takeyi bana son jin wani zancen bataci a gareta again.
Falon yayi shiru kafin hjy tace dasu banda abinku ai ka zama matar mai hali yafi ace ai yar me halice ke a wanan zamanin.
Kafin wani yayi wani magaba akai sallama aka shigo ya mamud ne a gaba sai wani mutum mai cikar kamala a bayan shi suka shigo.
Nan aka shiga gaidashi sai lokacin na gane shine wanda zai warwale matsalan zaman mu da yaya din da mukazowa jin abinda hukuncin ya tanadar muna yanzu.
An dan taba hira kafin su mazan su fita su barmu a falon kamad kada yaya ya fita duk sai naji na tsawala a lokacin cikin su sai dai da yake hjy na wurin ba halin wani yai min wani maganan banza.
An dan dauki lokaci kafin yaya mamud ya shigo yana fadin zainab dan zo mijin ki na magana dake a waje.
Duk suka bishi da kallo ya fita na dan daga nabi bayan shi nima nasan kallona sukeyi a lokacin ba mamakin hakan a garesu.
A can na tsinkaye su zaune saman fararen kujerun roba su hudu na isa wurin da sallama a bakina suka amsa min.
Kusan a tare suke nuna min wuri in zauna na danja kafa a hankali nakai zaune a takure nake cikin su din kafin naji mutumin ya fara jan dogon addua tare da godiya ga Allah daya hadamu a wanan wurin.
Kafin yace ina gida zaune dazun malam gashi ya nuna ya mamud ya sameni da wani zance wanda ya daure maku kai .
Sai dai Alhamdullahi don addinin islama yazo da wayen kaine ga al,umman Annabi ga baki daya Annabin rahama bai bar duniyan nan ba saida ya warware muna irin matsalolin nan idan zun taso gare mu.


ZAINAB IDRIS MAKAWAASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI FATAN ANTASHI LAFIYA UBANGIJI ALLAH YA SADAMU DA ALHERUN SA MARASA LAFIYA ALLAH YA BASU LAFIYA MASU LAFIYAN ALLAH YA KARA MASU LAFIYA AMIN.


YAR UWA LITTAFIN KUDINE DON ALLAH KI BIYA KI KARANTA KADA MU SHIGA HAKKIN JUNAN MU.

Zowan mami da ta biyo bayan mu ta samu muna zazaune malam na bayani hakan baisa malam din yayi shiru ba a lokacin har saida ya tsaya don kan shi.
Malam ya kare bayanin shi a lokacin jikin kowa yayi sanyi a wurin don irin bayanin dayayi a lokacin kan addinin Allah.
Ya dago tare da fadin kada in katse ku da bayani haka zan so wanda suke da alhakin zaman mu wanan wuri suyi min bayanin komai a tsare yadda zan fahinci zancen.
Sai lokacin mami ta samu bakin magana tana fadin akan meye akai wanan zaman ya mamud ne ya bata amsa da fadin kan matsalan matsayin auren su da kika fara magana ranan muke son malam ya warware muna.
Sai ta dan bimu da wani irin lalattacen kallo tana kawar da kanta gefe daya ba tare datayi magana ba a lokacin.
Sai ya mamud yayi sauri fadin dama watau malam kamar yadda na fada ma dan matsalane aka samu tun farkon auren har yakai an kwashi tsawon shekarun nan, ana zaune ba wani abinda ya taba shiga tsakanin su shiyasa muke son a warware muna matsayin wanan auren a yanzu.
Saboda mahaifiyan mu ta fara furta wanan kalamin wai an dade an dauki lokaci a yanzu kan ba sauran aure a tsakanin su.
Da sauri mami ta dan dago kai ta kalli ya mamud din tana fadin au don hakan dana furta kuka kira malam a kanshi to ai gaskiya na fada dan aure ko watani masu tsawo ya diba ba saduwa a tsakani ai akwai bincike a kai.
Malam din cikin murmushi ya karkada kai ba tare dayayi magana ba sai murmushin da yakeyi a lokacin.
Ya jafar yace dakata mamud jin haka kowa yayi shiru a wurin a lokacin ina faman tunanen zancen ya mamud din da yace mami ne tazo da wanan zancen ke nan haka na nufin mami dai har yanzu tana son in bar mata danta kota halin kaka ke nan yasa take wasu tsire tsire zance a yanzu din.
Sai gashi kuma yanzun din ma ta kara maimaita hakan a gaban kowa ba tare da jin komai ba a zuciyan ta.
Wani dan iska ya furzo mai cike da sautin zafi da takaici irin yadda yake jin kanshi din a lokacin nan dai ya bude bakin shi da yai mashi nauyi a lokacin kafin ya fara fadin .
Watau malam bayanin da zan ma ba akan wanan zaman bane kawai kamar yadda dan uwana daya gaiyace ka yayi maka bayani a yanzu.
Duk kallon shi mukayi kafin yaci gaba da fadin malam ni din dai na kasance mai aikata sabo a baya, da sauri malam yace wa,iyazu billah.
Yace kwarai malam a kuma cikin irin wanan halin na auri matata zainab gata nan zaune a gaban kowa .
wanda da farko nayi wanan auren ne don in fake a gareta da sunan aure a kaina ga idon mutane don kowa ya san ina da aure kada mutane su kawo wani zargi a gareni.
Duk kallon shi sukeyi har ni din da yanzu na kara gaskanta manufarshi a kaina a baya daya aureni din sai naji wani irin bakin ciki ya kara tokare min makoshina lokaci guda kafin sauti muryan shi ya dawo dani a daidai lokacin da yaci gaba da fadin.
Watau malam bayan auren namu da ita hakan baisa na bar aikata fasadi a doron kasa ba wai don ina da mata sai na dauki abin kamar yadda na tsara zaizo min a baya yadda nake so
A gaskiya na auri zainab ne akan zan samu rufin asirina a wurinta don tana yar tallakawa zata zauna dani ko don talaucin ta dana iyayyenta alokacin a yadda nake hange.
Saidai kuma nima ba wai haka kawai wanan tunanen yazo min ba sai bayan nayi nazarinta da irin hakkurin ta naga ya kamata in taimaka mata ta wanan hanyan kaga kenan zamu taimaki juna a takaice dani da ita amma ba cikin ta sanda hakan ba saboda tana da karancin shekaru sosai a lokacin.
A lokacin mami bata gane hakan ba don tana ganin na bijirewa zabin tane don tana ganin zainab din bata cancanceni ba ga aure.
Malam ya dago kai ya dan kalleni a hankali ya mayar da kanshi kasa yaci gaba da fadin.
Sai dai kakata da take jin ina yawan fadin zainab ce ta dace da rayuwana a lokacin duk da bata san mugun halina na boye ba da nake aikatawa a lokacin.
Amma hjyn ta bani goyon baya dari bisa dari ga wanan auren da nake son yi da zainab din.
Inda a karshe da mami din taki jin magana da shawaran mahaifiyan nata muka yanke shawara da hjyn da yayana mamud gashi a zaune kan naje na nemi auren zainab din a boye tunda mahaifiyarmu ta kafe kan sai zabin ta a lokacin.
Wanda ni kuma nake hangen zabin nata a gareni kamar wani hanyar tonon asirinane a wurin jama, a wanan auren na mami, don zai iya jawo min ga duniya don nasan koni waye.
Saidai ashe wanan zaben da nake ganin nayishi ne kawai don bukatana, shine haske a garemu baki daya .
Don shigowan zainab a cikin rayuwana a sannu a hankali ta fara kawo min sauyi na canza min lissafina da nakeyi da farko a kanta.
Kasancewan zainab din yarinya mai wayau da ilimin addini yasa abubuwa suka fara cabe min a rayuwa .
A lokacin haka nake gani don yawan nasihanta a gareni da saka min ido kawai da tayi kan duk wani abinda nakeyi ba tare da takura min ba .
Sai hakan yasa na fara kunyar kaina na da jin nauyin ta har ya kai na rage wasu abubuwan da nakeyi a fili saboda kaucewa idonta din.
Tunda nasan tasani amma bata nuna min tauye mata hakkinta da nakeyi yana damunta ko abin yana bata mata rai sai har idan ta kamani da idon tane mukan kwashi fitina sosai da ita.
Nasan kuma hakan da take min yana a cikin rashi gatan da take ganin bata dashi ko kuma fin karfi iyayyene dake aiki a kanta.
Don ga nawa tunane sai nakan yawaita yiwa iyayyenta da yan uwanta alheri don na kawar da zargi ko kaskanci a idanu su.
Nasha shawaran da zuciyana akan in rabu da ita kamar yadda mahaifiyan mu keso hakan, amma sai in kasa hakan don hankalin yarinyar da nake gani kuma gashi duk da tasan dabi,u na marasa kyau baisa ta wullakantani ba.
Ban kara tabbatar da hakan ba saida na sakasu karatu ita kanwarta da suke tare idon ta ya kare budewa a can chaina din sosai amma hakan baisa zainab ta raini ba ko naji watarana ta fadawa wani ga halaiyana marasa kyau.
Mun sha fama da zainab akan rayuwan maza da maza da nakeyi wanda take iya kokarin ta a kai taga na daina wanan akidar .
Amma sai hakan ya gagareta da farko na dauka tanayine don na kasa, kasancewa da ita a matsayun muna ma,aurata .
Sai daga baya na gane abin ba haka yake ba har kasan zuciyar ta tanayine kawai don ta fitar dani cikin wanan rayuwan na fasadi danake aikatawa.
Yan kungiyan mu sun sha ban shawara in kasheta in huta idan zata kawo min matsala a rayuwana, ko su kansu suyi yunkurin hakan in hana su.
Naji mami tace ikon Allah wai a kashe mutum kamar dan kiyashi kai haba jafar wanan wani irin rayuwa ka jefa kanka a ciki hakane ?
Lokacin na dago kai na kalle shi da idona da yake tab da hawaye bakin ciki tare da tausayin kaina da nakeji akan abubuwan da yake fadi din da bakin sa.
Malam ne ya katse shi da fadin gaskiya malam jafar ka aikata sabo mai girma a rayuwa.
Ya aikata kan sai dai addua a yanzu tunda Allah ya taimakeshi ya daina a yanzu ga baki daya.
Yanzun malam saika fada muna matsayin da auren su yake ciki a yanzu don kowa yasan zaman shi a yanzu din mami ce duk take wanan maganan tana kallon malam din.
Taci gaba da fadin don a nawa fahintar ya tsaya yana gyaran wani zance haka mai tsawo da bashi ya taramu a nan ba tun dazun.
Why mami why zakice kada na fada ya zama dole in fada a gaban kowa don in kara samun addua da taimakon da Allah zai gafarta min zunubai na jafar yace.
Kafada din ba,a hana ba kana kawo muna wani zancen zainab can tun dazun mami ta fada a hasale.
Malam dake kallon su yace Na,am watau ainihi danki yana da gaskiya haka ake son mai tuba da gaske ya kasance kada yaji kunyar fadan girman zunubin sa komai girman sa don tuba.
Haka zalika ita wanan yarinyar ya nuna inda nake yace tayi matukar kokarin azo a yabe ta kuma a sota ko dan halinta.
Don a wanan zamanin ba ko wace mace bace zaki samu da aikata hakan ta iya boye sirin mijinta a cikin ta daga ita sai shi sai Allah kadai su san da sabon da yake aikatawa haka.
Jafar ya tare malam da fadin wallahi malam abinda zai baka mamaki shine ita din zainab ta shiga ta fita a kasan chaina ta samo min maganin da a yau zan iya komawa kamar kowa.
Na,am malam yace tare da kara masha Allah yarinya kinyi kokari da kika samu wanan yabon a bakin mijin ki haka.
Wallahi malam ba gyarata nakeyi ba ko don wani ya sota a yau ina fadin gaskiyan abinda tayimin ne a rayuwa nan dai ya kora masu labarin komai har da na kakana malam da yake bashi.
Humm,umm ita zainab din duk ta iya hakan ashe ba karya ake fada ba da ake fadin yan kauye komai karantan su ka barsu inda ka gansu.
Shige shige da biye biyen malam ya kare a gidin su yau na kara gaskanta wanan maganan .
Kwarai mami in dai wanan din shine shige shige zainab ta shiga inda yafi nan din data shiga ya mamud ya fada.
Don kuwa mu zainab ta gama muna komai na rayuwa tunda ta kwato muna dan uwan mu cikin bala,i.
Rufa min baki kada in saba maka a wurin nan yanzu mami ta fada dama nasan shirin ku akan hakan yasa na biyo bayan ku inji me kuke kullawa.
To bari kuji koda malam yace akwai zama a tsakanin su aure sai na karawa jafar shi tunda nayi niyar hakan kuma zan nuna masa ni na haifeshi ba wani ba.
Enough mami enough don Allah in anyi magana kice aure zaki kara min aure zaki kara min ga abinda ya dace kimin bakiyi ba lokacin da nike bukatan taimako.
Yanzu da zainab din tayi shine kuma abin laifi ai Allah yace tashin in taimakeka baki tashi din tsaye ba a kaina ita ta tashi har yanzu tana a mai laifi a wurin ki mami ?
Me wanan yarinyar tayi maki haka mami kika tsaneta ne lokaci daya haka halarcin zainab a gareki ba kadan bane har idan ke kika haifenin da kike fadi.
Yarinyar da zan yi amai ta kwashe in fitar da kazanta da namiji dan uwana ta zauna tana gani iyaka taci kuka ta gaji ta share hawayen ta bata taba fadawa wani wanan maganan ba har yau itace kike kokarin ganin kin bakantawa mami ?
Wallahi dani kadaine danki mami da sai ince bake kika haifeni ba kila don son baki kawai na kina nuna min don yadda zainab zata zaunar dani tana min wa,azi mami kin taba min hakan ?
A matsayina na mai,aikata babban laifi irin wanan don haka mami ki gafarceni akan zainab a yanzu zan iya batawa da kowa a duniyan nan.
Zainab tayi min komai a rayuwa ta yadda ba zan iya kimanta darajan ta a zuciyana bayan naki daga ke sai zainab ne mata mafi daraja a idona har abada.
Yau zainab ta tunar dani nauyi da kunyar ubangijina da ke kaina wanda na manta dasu saboda rudin duniya da nake bi a baya.
Aiko mami zainab tayi min komai a rayuwana, kukan da nasake ne ina kaiwa kasa ya dakatar da dan rigiman daya kaure a tsakanin su lokaci daya a wurin.
Malam ka taimakeni kai mun rai ka ceci rayuwana ka rabani da ahalin mami ga baki daya a yanzu nima na gane mami ba zata taba kauna ta ba a duniyan nan.
Duk abinda yaya ya fada anyi shi har ga Allah dama wanda bai sani bai fada din ba duk anyi su a baya.
Kuma bayi don kowa ba sai don Allah da halarcin mami a gareni da kuma shi kanshi ya jafar din ya taimakeni da abinda ba zai taba barina a rayuwa na bashine illimi.
Mami ta sanadiyar ta nabar kauye rayuwa na ya inganta a sanadiyar ta haka tayi min riko na tsakani da Allah da ba zan taba mantawa da hakan ba don ita uwace hakkun har gobe a gareni.
Aurena da ya jafar shine kadai kiyayar mu da mami a fahintana don haka malam ka yake duk wani alaka na aure dake tsakanina da ya jafar a yau don Allah.
Na karasa cikin wani irin kuka ma idaga hankalin mai saurarena a lokacin duk sukai shiru suna saurarena tare da zuba min ido gaba dayan su.
For god sake mami dame wanan abin yai kama haka yarinyar nan dai kema kin sani ta dalili ki ta san bros ta kuma fadi don ki take masa komai.
Koma bata fada ba kowa ya sani don zainab yarinyace mai hankali da natsuwa ke kanki kinsha fadin haka ko a bayan ta yan aiki nawa kika canza zuwa yanzu jamal ne mai wanan maganan rai bace.
A ranan nasan tarbiyan yahudawa mami tayiwa diyan ta ashe tunda kowa na iya fadin magana kai tsaye a gareta ba tare da ta damu da hakan ba.
Don da ace hakan yai mata zafi da wata uwarce a take zata yankewa kowan su kauna a wurin yau naga amsan abinda ya dade yana min yawo a zuciyana .
Kan yadda mami bata damu tabi umurnin hjy ba idan ta tsawta mata kan wani abu da takeyi wanda bai dace ba din.
Salamu Alaikum malam ya fada cikin muryan uztazai wanan ya saka masu natsuwa a wurin malam din yaci gaba da fadin .
Wa,izu billah wanan abin bai kawo kallo ba a tsakanin ku watau anihin dai wanan zancen naku yasani nazarin abubuwa da dama a cikin yanayin zancen nan a yanzu.
Da farko na fahinci akwai wani abu da ke a kasa tsakanin ku a gidan nan tun farko sai abu na biyu shine.
Watau ainihi kan zancen wanan boyar Allah watau hjy zainab gata a zaune watau anihi hajiya iyami ina son ki san wani abu.
Shi lamarin ubangiji mai sauki ne idan bawa ya daukeshi da sauki watau wanan boyar Allah ita din haskene a gareku baki daya a gidan nan.
Haske irin wanda ake kira da Nurul dar sai ya kasance a cikin wanan zancen gaba daya kunyi amfani da baiwan yarinyar nan kun kuma amfana da ita ko.
Yanzu duk ba wanan ba don lokacin sallah ya gabato sai mu gagauta yin bayani kan abinda ya kawo mu nan a yanzu.
Na farko dai bayan nasiha da zan ma kai malam jafar akan tsoron Allah a yanzu dai Alhamdullahi sai ka ya waita istgifar wanan yafiya yana tsakanin Allah da bawan shi.
Ba wani dan Adam da ya isa ya furta wani kalami akan hakan face mu godewa Allah ga baki daya muka yawaita istigir akan mu da dukkan musulmi baki daya .
Ke kuma hjy zainab ki godewa Allah da har kika samu yabo haka gun abokan zaman ki ga baki daya ko wanan ya ishe ki alfahari a duniya.
Zancen akwai aure ko babu aure a tsakanin auren nan yanzu zabi ya rage gareka kai mai auren a hannun ka.
Idan kaga zaka bar matan ka auren ku na nan daram har abada sai dai idan kaika janye igiyan auren ta a kanka yanzu.
Aure dai an riga da an daura a tsakanin a bisa tsarin musulunci ba tare da wani manufa ba ga madaura auren ku din a lokacin kaga ke nan aure ya dauro a tsakanin ku ke nan.
Wanan zancen da ake hasashe ba addini ya fadi hakan ba tsarine na wasu mutane da suke fadab hakan.
Amma dai da ace har yanzu baka tuba ka koma ga Allah, ka daina wanan abubuwan bane to sharia ta yarda da a raba auren naku don taje gaba itama ta samu daidai da ita kada ka cuta mata a nan
Sai dai ina kira a gareku gaba dayan ku kiyayye kyautatawa iyayyen ko da a wajen tausasa harshe ga mahaifa musanman uwa .
Duk wanda yaji hakan yasan dalilin fadan hakan da malam din yayi garesu ya kara da fadin sai na karshe mu kyautatawa wanda ya kyautata muna koda na rana daya ne shima zai bukaci kyautatawan ka watarana a kan shi.
Don haka kada mu zamo masu manta alheri komai kankantanshi don kada Allah ya jarbce mu ta hanyar da bamuyi tsammani ba a rayuwa.
Da wanan nake son inyi sallama dakuba taikace Allah ya gafarta muna kurakuran mu da wanda muka sani da wanda bamu sani ba Allahuma amin.
Yayi muna sallama bayan anyi addua an shafa ya mike zai tafi ya jafar ya saka hannu a cikin aljihun shi ya ciro kudi masu yawa yace a bashi.
Da sauri malam din yace sam ba don kudi ko wani abin sadakan ku nazo ba son kunfi karfin hakan a gareni.
Zanso na gana daku ku ukun nan kafin ka bar kasan nan idan kun samu lokacin haka yayi masu sallama ya tafi.
To ai shike nan bukatan kowan ku yanzu ya biya shiyasa kuka dauko min malam khalid don shi din ya inma bakin sa yazo yai muna wa,azi.
Wa,azi kuma mami akan me zaizo yayi maki wa,azi mu mun kirashi ne yazo ya warware wanan zancen kowa yasan matsayin shi.
Please is enough a bar zancen komai a yanzu ke zainab tashi muje gida daga nan ya fada yana mikewa.
Kamar banji me yake fada ba a lokacin kaina na kasa sade ban dago daga yadda nake ba tun dazun din.


ZASSALAMU ALAIKUM YA YAN UWA MUSULMAI BARKAN DA GANIN WANAN RANAN NA ALHAMIS UBANGIJI ALLAH YA SADAMU DA ALHERUN SA AMIN.
KADA KI MANTA TASHIN DARE A WANAN RANAN MAI ALBARKA KI YAWAITA ISTIGIFAR GA ALLAH KI NEMAWA KANKI GAFARA ALLAH YA BAMU IKON TASHI YA KUMA KARBA MUNA IBADUN MU AMIN.


TUNI LITTAFIN DAI NA KUDINE BA A YARDA WATA TA KANTASHI BA IDAN BATA BIYA BA.


Yana tsaye a kaina yana kallona ba tare daya sake magana ba duk sun zuba min ido suna kallo na don ganin ban motsa daga yadda nake ba sai hawayen da nakeyi.
Sai ya mamud ne ya mike ya tako har inda nake tsugune ina sake hawayen bakin cikin dake cina abu goma da goma sun taru min a kaina lokaci guda.
Zainab kiyi hakkuri ki tashi ku tafi ya fada a gefena cikin nuna damuwa a gareni jin haka na dago kai da idona daya yayi ja don kukan da nasha ina fadi da kyar.
Tare da girgiza kaina gareshi yaya ba zan koma gidan ya jafar ba kai masa magana yayiwa mahaifiyar shi biyayya kan abinda take so dashi.
Allah ya gani da zuciya daya nake zaune dashi tankar yar uwa ta jini don duk abinda mami take nuna min banta jin kinta a raina ba haka diyan data haifa ina jinku tankar yayyuna ne na jini don yadda kuka rikeni tun farko.
Bada case din ya jafar daya hadani da mami ba wani sabani daya taba shiga tsakanina da mami duk zamana da ita.
Ban yarda na auri ya jafar dan son raina ba sai bisa tursasawan hjy gwaggo dashi kanshi ya jafar din da sukai min barazana a lokacin.
A daidai nan na dago kaina na dan kalleshi ido da ido tare da fadin yaya a wanan maganan meye laifina a cikin hakan ina duk saboda darajan mami na aikata hakan.
Yanzun kuma kaji a gaban kowa shima ya fadi bai aureni don yana sona ko wani abu nawa ba sai dan bukatan kanshi da yake ganin zai fiddashi ga idon jama, a.
Alhamdullahi kuma dukkan su bukatan su ya biya a kaina don Allah kusa ya sake don wanan abin ya kare daga yau din nan yaya ?
Na fada ina kara sake wani itin kuka mai tsuma zuciya lokaci guda daga inda mami take zaune ta zuba min ido take fadin kenan da sanin hjy dama duk hakan ya faru ashe ?
Shiko ya jamal sai cewa yakeyi ai gashi idan za ai magana a fadi gaskiya mami ki hana duk wanan abin da yarinyar nan takeyi ni nasan taimakon ki takeyi wallahi.
Kune dai da baku yarda ba da farko kuke ganin don bukatan kanta take hakan yanzu sai ku sama mata maslaha itama taje ta huta.
Jafar daya juya ya bamu baya yana cika yana batsewa ya juyo a hasale yana fadin wallahi baku isa ba babu mai rabani da matana wallahi .
Sai ko idan bana raye wanan kan na yarda da hakan naji mun yaudare ki din da farko daga ke har hjy data shawo min kanki a lokacin baku san komai ba .
Yanzu da nayi comfessing ina neman gafaran Allah da naku duk wanan din bai maki ba zai ba ya fada yana tsureni da idanun shi da sukai wani ja dasu.
Fine naji ya fada cikin wani irin zabura yana fadin sai ki fadi yanzu me kike son nayi maki don ki hakkura mu tafi ?
Na duka na baki hakkuri ko kudi kike sin na zuba maki fadi iya yawan kudin da kike koda duka dukiyanane zan iya ko mami kike son ta baki hakkuri gata zaune.
Ki fada duk a yanzu ko wanine daga ciki za ai maki a yanzun nan ba sai an jima ba.
Kai kai kai Allah ya rabamu da rashin tarbiya wallahi da tashi a cikin daulan da ba kwabo wadattace ga mutum.
Duk wanan abinda ya fada a yanzu shi a nasa zaton sune abinda zai kwantar min da hankali ko wani abu can.
A hankali na girgiza kai tare da fadin ko daya yaya jafar bana rayun ko daya daga cikin abinda ka lissafo min din a yanzu.
Na farko kana ganin dukawan ka a gareni ka ban hakkuri zai iya dawo min da farin cikin bakin cikin da nasha a wurin ka da mami da yan uwanka dake kina.
Ko kuma kana ganin kana da kudin da zai iya sayen mutucin na da imani na a hakan.
Sai mami gata a zaune mami uwace mafi soyuwa a gareni mafi girma da daukaka a idona ita da innata data kawoni duniya don bayan inna sai mami tayi imin komai a rayuwana ba zan taba manta harcin su ba a gareni.
You see mami kinji, kinji yarinya karama tasan halarci irin wanan, ta yaya ku manya zaku kasa gane hakan ?
Har ma wani dadi zainab ta samu a lokacin da take ta fadan kin mata halarci bayan tauyen ta da akeyi ana mai da ita kamar wata boya a ciki gidan nan kowa ya tashi ko ruwane zainab dai zainab dai ku din nan yau kunji inda akewa mutum alheri ya rama ta wani hanya.
Don ku din nan ba irin wullakancin da bakuyiwa zainab a gidan nan ba yau gashi tafi ku da komai a duniya.
Don ko kafanta ba wanda ya taka a cikin ku kaf din ku ba wanda yayi lilmin zainab a yanzu ya fada yana nuna su da yatsan hannun shi.
Ku rage wullakanta dan Adam don Allah don watarana baku san me Allah zai mai dashi ba jamal ya fada a hasale yana mikewa tsaye.
Ya girgiza kai ya saka hanayen shi cikin aljihun shi yana kokarin barin wurin.
Sautin muryan mami ne dake kuka yaji ya hanashi tafiya a lokacin ya juyo da mamaki yana kallon mami din da kuka takeyi wiwi a lokacin.
Ya mamud da sauri ya karasa wurinta yana fadin haba mami me yai zafi haka wanan ai saiki tada hankalin mutanen gida da wanan kukan naki.
Zuwa lokacin ko har sun karaso don Rufaida datake labe saman bene tana sauraron abinda ke wakana duk da bata ji sosai a lokacin daga inda take labe.
Tadai labe din tana kallo don tasan wani abu ke faruwa a lokacin a yadda taganmu zazaune yasa data hango mami na kuka kuma kaman ana fada ta fito da sauri tana fadin kuzo akwai abindake faruwa a waje da su mami don Allah.
Hakan yasa suka fito a cikin tashin hankali zuwa waje sai dai suna tunkaro wurin suka tsaya duk abinda ake fada a kunnuwan su ne lokaci.
Sai suka fara dan kalon juna a tsakanin su kafin hjy ta karaso tana fadin wai meke faruwa a wurin nan ne haka tun dazun ?
Sai kuma dan yanayin mami ya dauke mata hankali ta kurawa yar nata ido tana binta da kallon a cikin mamaki.
Iyami kin bata wayau ki yau har abin naki yakai ki zaunar da yarinyar nan haka a waje kina ci mata mutunci haka.
Ki duba nan duk yayan kine a nan aure kuma zasuyi suje gidan wasu shin kinsan irin *abifaru
sakamakon hakan zai zo masu ?
Shifa komai ka aikata a duniyan nan kai da kanka zaka girbi abinka da hannun ka shin iyami baki gudun yaran nan su tarar da uwar mijin data dara irin gasawa yar nan da kikeyi ?
Kowa yai shiru a wurin ana sauraron abinda hjy din take fadi sai rufaida ce ta bude baki tace wa tsohuwar kinyi kuskure hjy don mu kan ba zamuyi aure irin wanan na cusa kai haka ba gaskiya.
Ki min shiru Rufaida mami ta fada wa yar nata cikin tsawa a hasale taci gaba da fadin ana nuna maku hanya har kina ci gaba da magana haka.
Fada min yanzu meye laifin yarinyar nan zainab a nan don kawai ta auri yayan ku ko dan ta zauna a cikin mu har abada.
Yanzu na gaji da wanan halin da kukewa yarinyar nan zainab ku barta ta zauna lafiya da mijin ta don ko ta muna komai a rayuwa don ta zauna da dan uwan ku tsakani da Allah ba don wani abuba.
Yau na gaskanta hakan abinda kuke yawan fada min tayi ko kun gani sam abin ba haka yake ba ashe .
Don yanzu a wirin nan na gaskanta hakan na gane gaskiya abin ba hakana bane bawai ta asirce shi bane ko wani abu.
Tayi ne don ta farauta min rai wanda nasan da wuya a nan a samu wace zata iya yin abinda zainab din tayi min.
Kowa wurin sai kallon mami yakeyi don jin furcin ta a kaina taci gaba da fadin ina son ku sani daga yau ba raini ko wullakanci ga yar uwanku kuma matar yayan ku gata a zaune gaban ku zainab.
Ikon Allah hjy da takai zaune ta fada har lokacin tanawa mami din kallon mamaki kafin mami din tace hjy don Allah ki tafi gida dasu in an jima zanzo gidan da mamud da jamal mu sameku a can.
Mamakine ko al,ajabi ya cika min zuciya a lokacin don saukowan mami haka da sauri sai abin ya fara daure min kai na.
Wanda nasan ba ni kadai nashi yin wanan tunanen ba a wanan lokacin kusan duk wanda ke wurin yana mamakin hakan.
Hjy ta kalli jafar tana fadin mu tafi tashi zainab mu koma gida tun lokacin sallah bai shige muna a hanya ba.
Ba yadda na iya haka na dago kafata da kyat na fara ja don barin wurin ba tare dana iya yiwa kowa magana ba na fara tafiya.
Sai Anty Na,imace kewa dani zainab Allah bamu alheri sai munzo maku yawon weekend tunda naji ance kun kusa tafiya.
Dan murmushin yake na gefen fuska na sake ba tare dana bata amsa ba na wuce wirin motan mu kai tsaye.
Driver na ganin hakan ya mike ya taso da sauri ya nufo inda nake ina kokarin bude motar ya bude min na shiga na zauna ina jiran isowan su dan shi ya tsaya yana magana da su ya mamud.
Ita kuma hjy da mami suke tafe a hankali zuwa wurin motan da alaman dai duk maga sukeyi daya shafemu.
Yayin da yan matan suke tsaye suna kallon mamaki na sauyawan mami lokaci guda haka bayan zuwan mu gidan ne koma meye ya faru.
Bayan sun karaso bakin motan mami ta dan leko tana fadin zainab kada ki nuna masa komai don Allah sai nazo anjima din insha Allah.
Da kyat na iya budan bakina ina fadin to mami nagode cikin yanayin damuwa don shi kawai zan iya fada a lokacin.
Yana shigowa ya buga kofan motan da karfi saida na kadu mami take fadin kabi sannu fa kada ka tayarwa kan ka da wani ciwo kuma.
Ok ok don't mind ya fada tare da girgiza kanshi yana amsawa ba tare daya kallo inda take tsaye ba.
Hjy na fadin yama ja din aishi zai wahala shi daya sai kuma matar shi da zai wahalal a banza daga dan maganan fatan baki zai bata rai haka kamar soja a filin daga.
Mami ta daga, daga bakin motan tana fadin Allah ya tsare hjy ta amsa da amin sai kinzo.
Shiru cikin motar ba wanda ke magana sai driver ke faman sharara gudu don umurnin da ya bashi na yai sauri.
Allah ya gyara mun isa lafiya ba wanda yai magana haka muka fita wanan karon bai tsaya jiran hjy ba su jera kamar yadda mukafita a gidan.
Sai nice ba tsaya muka jera tana fadin tana tafiya ikon Allah yar nan nace ko wanan uztazun daya zo ya sauko da uwar taku da sauki haka a kan ku ?
Ai bai isa ya canza ta ba hjy sai Allah din dai da kika fada yanzu tace ai kuwa yar nan .
Tana dafa step din da zai hau da ita shiga cikin gidan take fadin a, to ai tace zata shigo anjima ai Allah ya kaimu, muji dame kuma zata zo din.
Har muka shiga gidan tana magana akan mami din muka shiga ciki ana muna sannu da dawowa sai ita ke amsawa a lokacin..
Har dakin ta na kaita kafi na juya na nufi nawa part din a gajiya ga kasala ga tunane dake cina da yunwa a lokacin.
Wanka ba shiga a gurguje don na makara da ga sallah a lokacin na fito na tayar da sallah din bayan na idar ne na zauna na dan gyara jikina na saka wani simple riga a jikina da zan dan sha isaka a lokacin.
Na koma na haye gado don ina bukatan hutu da kadaicewa ni kadai a dakin lokacin don yin nazarin abun da nake son ganowa kan nadaman da mami ta nuna tayi din a yanzu.
Kofa aka turo a lokacin ban dade da kwanciya ba na dan juyo a hankali ina kallon mai shigowa dakin anty Fadila ce ta shigo tana fadin .
Kun dawo a gajiye abinci na dinning tun dazun an gama sai dai nakaiwa hjy nata yanzun kafin in zo nan.
Nakine dana oga a dinning din yanzu sannuku da aiki nace a hankali sai dai anjima zan fito in danci tace shi oga fa ko za a kai masa nasa ne part din shi ?
No ki barshi idan yana so zaiyi maga ai na fada ina gyara mike kafana tare da bayana dana jingina da gado.
Tace da a debo maki ko ferfesun ki sha zaifi zama ciki ba komai na girgiza kai kafin ta karasa fadan abinda zata fadi din.
Sai kuma ta kara fadin ina ganin fa zuwa friday aikina zai kare daku zan bar gidan nan ke nan a ranan ta fada a cikkn murmushi tana kallona.
Da sauri na juyo gareta ina fadin wanan satin ke nan tace eh insha Allah ranan ne zan kamala komai in tafi a yadda aka tsara min.
Haba dai gaskiya da son samu ne zaifi kyau ki hakkuri har mu tafi idan mun tafi ai kinga shike nan saiki tafi a binki ko ?
Gaskiya hakan da wuya don iya month din da aka ban ke nan kuma na gama hada duk wani bayani da suke so a yanzu .
Gashi ban taba zywa aiki wani gida har wani yasan abinda ya kawoni a gidab sai wanab gidan naku abin kamar sihiri wallahi yadda har kuka gane me ya kawoni gidanku da sauri haka ?
Dan murmushi na sake ina kawar da kai tare da tunanen maganan data fada sai na dauka tana sk jin wani abune daga bakina duk da tasan ba zata taba samun amsanta a wurina ba amma ta gwada sa,an ta ta gani ko zataji din.
Kwanciya na gyara ina fadin tare da hamma kin san shi din mutum ne mai natsuwa da lura da komai.
Tace wanan kan na sani ai shiya ja min wanan dadewan tare daku don na kasa fahintar komai a kanshi duk zama tare daku din .
Ganin da tayi alaman ina son hutawa ta mike tana fadin barin baki wuri ki huta naga kamar a gajiye dai kike yanzu baki jin hira nacs wallahi na gaji gaskiya ta mike ta fita daga dakin tare da rufo min kofana.
Fitan ta daga dakin tun ina tunane har barci ya daukeni ban sani ba ban falka ba sai kusan karfe biyar na tashi ina salati.
Ban samu fitowa falon ba sai dana kamala komai a lokacin na samu fito har shidda ya wuce koda na fito.
Jin hayaniyan tunda na fito dakin hakan ya sanar dani muna da baki a gidan ga yadda naji ana dararaku na dauka wasu bakina sai ina karasowa naga ba wasu baki bane su mami ne da hjy a falon ake wanan dariyan haka.
Kunyan kaina naji a yadda na fito falon tun kan ya watso min irin kallon da yake min na warning na riga na tsargu da hakan.
Hakana na daure na karaso ina gaida su da zuwa ba kunya ko wani dar a idon mami take fadin diyata mun zo mun samu kina barci ai nace kada su tasheki a barki ki huta.
Lah mami ai da an tasheni din nayi sallah na fada ina dan dariyan da bakai ciki ba na kai kasa ina gaida ita kamar yadda na saba take fadi cikkn dakewa ke zo nan bana son in kara ganin kina jin kunya na haka kikaga yan uwan ki suna min.
Na gaisa dasu yaya duk ina zaune suke dan hira kafin mami din ta juyo gareni tana fadin tun dazun fada mukewa mijin ki .
Kina daki don Allah zainab ina son ku kawar da komai daya faru a baya a zukatan ku a zauna lafiya .
Wani zance a yanzu duk a bar tuno da abinda ya riga ya wuce duk da nasan hakan yana da wuya amma dai a daure.
Hjy da bata san zancen ba ta dora da fadin sabani dai suka samu har ya kaisu gareki yau din ai amma kuma zuwan nasu gaban ki kuma yayi rana sosai.
Tunda hakan yasa har tsakanin ke dasu a yanzu kun fahinci juna don ni abunda yafi damuna shine irin yadda kika sake wa yan nan kattan yan matan naki sukewa yarinyar nan iya shege ko a gaban kowa.
Don kawai suna takaman ta taba zama a karkashi su a baya wanan abin yana cimun rai sosao wallahi
Amma yau yadda kikai masu din nan yasa na fara fita kwakwanton da nakeyi na uwayen yaran nan .
Don sai nake zargin idan kuna wani abu dasu kamar ba kai sake suka barki ba Allah.
Budan bakin mami sai cewa tayi nima hjy watarana nakan yi zargin hakan a kan su wallahi don kinga Rufaida halin uwarta sak ta dauko ga hali.
Bata kaunan taga wani yazo ya rabeni a gidanan ko kadan sai naci mata mutunci wani lokaci takan shiga hankalin ta.
Laifi kine iyami yaushe za a zauna da uwayen mata nan dasu wai kuma budurwai duk ki sa su fito da miji ki aurar da yan banza.
Mami tace ai mazan sunki fitowane har yanzu ba mashinshini suna nan min zube cikin gida sai karyan banza wallahi.
Basu rasa mazajen aure ba kawai dai basa son masu son su dinne suna ganin sun fi karfi su auri kalan mazan ne ya mamud din ya fada.
Su koma gida mana idan hakane karatune dai sun samu yanzu ba sai ko wacen su ta koma gidan su ba inji jamal.
Kai a bar cen nan please ayi wanda ya kawo ku don Allah 3ni wa yan nan yan iskan yara ina ga nine zan koresu ranan da wata ta karawa zainab iskanci a gidan nan..
Bama zasu ba a yazu indai ba yaran banza suke ba yadda uwar nan nasu tayi masu dazun da haka har mami ta gaiyaceni zuwa dakina da sunan zatayi sallah .
A can ne muka samu kebewa da ita bayan mun sallame ta kira sunana na dago kai a hankali na kalleta


ZAINABASSALAMU ALAIKUM JUMMA,AT MUBARAK YAN UWA MUSULMAI ALHERIN DAKE CIKIN RANAN NAN ALLAH YA SADAMU DASHI.

INAWA YAN UWA TUNI GA YAWAITA ADDU,A A WANAN RANAN ALLAH UBANGIJI YASA MU DACE AMIN, , , , ,


Mun idar da sallah kowa na saman sallaya a zaune yana addu,a kafin mami ta shafa ta juyo tana bin dakin da kallo ta ko ina kafin muryan ta ya biyo baya tana fadin.
Zainab nasan zakiyi mamakin ganin saukowa na haka da sauri cikin dan lokacin da bakiyi tsamanin hakan ba ko ?
Kallon ta kawai nayi duk da gabana yana faduwa daga yanayin da take kallona din hakan baisa na katse addu,an da nakeyi ba a lokacin .
Saidai kawai kan dana kadawa mami din a lokacin alaman naji taci gaba da fadin kada ki dauki hakan wani dama a gareki yanzu da zaki ga kin kai wani ko kinfi wani ne a yanzu a gida na zainab.
Kada wanan dama ya saki dauka na manta me kukai min a baya duk ina fada maki wanan zancen ne ki san matsayin ki a cikin mu.
Don ban shirya dana ya ma zauna zaman aure dake ba balle a kaiga haifan jikokin da basu da usulin da nake so.
A raina nace ashe shiyasa kika aurowa ya mamud Nuriya take garaku yadda take so itin hakan kike so ke ko ?
Ganin na fara shiga dogon nazarin kan zancen dake fita a bakinta din ko ina mamakin abinda take fada min din yasa taci gaba da fadin kwarai zainab.
Na sani kin yi kokari kan jafar din fine dama ai duk mace da take hasashen wani abu dolene ta dage ga abinda take so har ta cinma burin ta.
Bance bakiyi kokari ba kamar yadda ya fada kinyi kokari kowa ya sani amma wanan bashine dama a gareki ba.
Allah ya gani ba irin ki nake so da dana ba zainab nafida son diyana su auro min wa yanda ke da asali don hakane ma bani kaunan ki hada shimfida da jafar a yanzu.
Wani kallon mamaki nayiwa mami din har lokacin ban samu bakin magana a gare ta ba don mamaki tace kwarai kuwa zainab don.
Kin fi kowa sanin son da nakewa jafar cikin diyan dana haifa kuma nake dasu a yanzu a duniya.
So da kaunan da nakewa danane yasa na nuna a gaban kowa komai ya wuce a wurina har na gane kurena don gudun halin da zai sake fadawa nan gaba kan hakan, shiyasa na daure nayi hakan don fitar shi cikin halaka.
Wanda nasan bani kadaine wanan abin zai shafa ba a yanzu har ke da kike kirarin matarsa ce ke, don Allah kadai yasan abinda kikawa jafar a yanzu yake mutuwar a gareki haka.
Murmushi na sake a nan, don na kasa hade maganan da take fada min a lokacin nace mami ke nan nasan da wanan nasan kuma hakan kafin ki furta a yanzu din don tun a gidan ki na hango hakan a idon ki.
Sai dai saukin abin ni Allah bai dora min son daki ba tun farko a zuciyana don har yanzu kallon kyama nake masa ga irin abubuwan sabon daya aikata a baya.
Ba wata mace ko uwa da zata so a danganta da mai itin wanan bakin fasadin a duniyan nan yanzu.
Kuma kada ki manta cewa ko lalacewan tashi ta farko banice sanadin shi ba a haka na sameshi da abinshi kuna tare dashi hakan na zauna a kyamace dashi ?
Don me kuma a yanzu zan jefashi cikin wani rayuwa bayan nina san irin wahalan da nasha a baya don naga ya dawo mutum kamar kowa abin alfahari a yanzu ga wasu.
Sai dai kuma mami a yanzun wanan maganan naki ya haska min idona sosai kan daki din yanzu na gano manufarki ga hakan a kan danki don haka.
Ni a yanzu har na fiki son jafar don ga alama nina fiki sanin zafin shi a yanzu don jafar mijina ne ke kuma danki.
Kinga ma,ana nan ina nufin koda yaushe ina tare da jafar ke kuma uwace sai lokacin daya tuna dake yaje gareni kinga na fiki damuwa da damuwan danki.
Ido tas ba kunya nake fada mata wanan maganan da umma ta tsara min in fada mata idan bukatan hakan ya taso don mami tasan yanzu ba da bane a wurina.
Ko zan samu saukin irin hattarana da suke nuna min ita da diyan ta mata da bansan abinda nayi masu ba har yanzu.
Zainab ni zaki kalli idona ki fada min magana irin wanan haka a gabana ashe dama karyan yi min biyayya kike a gaban mutane kike nuna hakan ?
Lah mami bana karya ko a kan gaskiyana sai dai maganan ya dangaci hakane a yanzu a da ina tunanen barin danki din don kwanciyan hakanlin ki gareni.
Amma yanzu na gane kurena a kan hakan ko aure nawa nafita nayi dole a saka sunan jafar a na farko a cikin mazajen dana aura a duniyan nan.
Don haka barin shi ma bai taso a gareni ba kamar yadda kike son in barshi din ki auro masa wata wace kike ganin itace ta dace dashi a yanzu din bani da banda asali ba kamar yadda kika fada yanzj.
Don haka zama da jafar yanzu na fara tunda mijina naso na bai damu da koni wacece ba ya gani yasoni a hakan da wani manufa da a yanzu ya zama muna alheri ga baki daya mu.
Idan asiri nayiwa jafar har yake sona sai nake ganin ai banice farau wurin yin hakan ba aga yar kauye a aureta ta zama wani abu a duniyan nan.
Ta joyo a hasale zata kai min duka aka budo kofan shine a tsaye a yadda ya gamu ya tsaye rike da kofan a hannun shi yana raba idanu a tsakanin mu
Kafin na wayance da fadin mami kiyi hakkuri in Allah ya yarda ba zan sake ba kuma nayi maki alkawarin komai zai kara daidaita a tsakanin mu insha Allahu.
Na fada a dan maraice kamar ina ladabi kan wani zance data fada ya bata min rai a lokacin ya karaso cikin dakin yana fadin .
Mami is ok ai ku tafi gida kawai zamu zauna mu sasanta kan mu zainab me hakkuri ce da yafiya wanan zance ya wuce a yanzu ai.
Nace don Allah ya jafar ka tayani bawa mami hakkuri bisa abinda nayi a dazun ya bata mata rai ba zan sake kuskure irin wanan ba insha Allahu.
Don't mind with that mami ba zatai fushi dake ba zainab tunda kina son mu da zuciya daya kina kuma zaune damu a cikin amana.
Da ba don ke bace a gidan da yanzu yar leken asirin gidan nan ta gama kai rahotona zuwaga magabatan ta ko, akan abinda tazo nema game dani a gidan nan.
Sai Allah ya taimakeni zainab din ba mai yawan surutu bane haka don haka bana tsamanin ta samu abinda take son samu a wurina a yanzu.
Sabon zance ke nan kuma a yanzu mami takeji daga bakin shi akan fadila, a cikin rawan jiki mami din ke tambayan shi wai wata yar aiki dai yace wanan dai da take zaune damu a gidan nan.
Yar sandan ciki ce ita an turota ne gidan nan ta zauna damu duk tsawon shekarun tana bincike ne a kan mu haka.
Labarin da sirin mutum wani lokaci akan sameshi ga matar ga matar mutumce mami sai ya kasance zainab din bata fadawa kowa sirin takeyi ba har nawa din bata hiran hakan da bakuwar fuska.
Innalillahi ya akayi kuke zaune da yar leken asiri a cikin gidan nan me take nema a wurin ka har tazo ta zauna maka a gida hakan nan tana maka zagon kasa.
Aiki tazoyi a kaina bata san mun gane hakan ba zaune kawai muke da ita me zata fada mami tunda bataga abinda tazo bincike ba a kaina din.
An turotane tayi bincike a kaina, don su gano irin abinda nakeyi nake samun kudin da suke gani nake dashi don su a zaton su ina wani smogling din wani abu da gwaunati bata son a shigo dashine a kasan nan.
Ko ina kaiwa wani kasan abinda suke tuhuma ke nan suka turo min ita a maysayin yar aiki a gidan nan take zaune tare damu.
Mami me zata fada tunda bata gani ba ni wanan abin baya damuna ko kadan kawai dai ta gama zaman ta ta kara gaba.
Mami ta amsa da fadin dama na sani wanan matar munufukace tun farko sam batayi min ba rayuwan ta yana nuna ta faye wayewa da yawa.
Tun da naga kansu hade da matar ka nake tsoron wanan matar wallahi ashe hasashena ya zama gaskiya a kanta.
Kai mami don kawai tana gidan nan ne kike ganin su da zainab din amma ai zainab ba halinta magana haka ba.
Zainab din ma idan mun koma karatu zata fara kuma zata fara aiki da mun koma din zakiyi alfari da wanan sarakuwan naki nan gaba kadan insha Allahu.
Karatu ni ba karatune a gabana ba in daiga kun fara haihuwa a tsakanin ku in samu jikoki irin su ihisan daga tsatson ka.
Kai ya fara sosawa yana dan murmushi tare da fadin with time mami zasuzo har sai kin gaji da dauka.
Ya juya zancen mami din ya juyo dashi dashi da tace wanan matar taka ai ba haihuwan take so ba ita sai dai idan da wata matar zaka haihu jin hakan yasa ya juyo da sauri yana kallon ta a cikin mamaki.
Mami wanan maganan fa inma zolayan zainab kikeyi ki daina don Allah kada kisa hankalinta ya tashi a yanzu
A kan wanan zancen hankalina zai tashi sam wallahi na fada ina dan murmushi naci gaba da fadin ai bazan so in kasance cikin irin mata dake tauyewa mazajen su hakkin ba.
Su hanasu aure alhalin suna son karawa auren a zuciyan su ni alfahari zanyi da hakan ba nuna bakin ciki ba .
Kaida Allah ya bawa ikon yin hudu a lokaci daya don me zanyi bakin ciki don za a kara maka aure a yanzu .
Abin alfahari ne a gareni yanzu idan zaka kara din aini ban son zama kamar laya a wuya.
Na mike na bar inda nake tun idar da sallah mu din zuwa bakin gado ina daukan wayana dake aje a kunne ina recording din zancen mu da mami a ciki.
Mami muje ko ya fada haka ya dawo da ita cikin tunanen jin zafin maganan dana saka mata din don itama ai hana mijin ta kara aure tayi a lokacin.
Rai bace mami tafito a dakin duk da kokarin da takeyi na wayace hakan a fuskan ta sai haka bai yuyu ba a lokacin.
Gaki mana ranki a bace kika fito hjy dake kallonta ta fada tace ba komai hjy gajiyene kawai .
Har kofa muka kaisu na dawo tare da hjy mun dan zauna kafin in mike zuwa dakina na shiga na sake alwala nayi sallah.
A wirin na zauna na dauko wayana na kira layin umman su Nafisa na kwshe duk yadda mukayi na fada mata.
Umma tace dama na fada maki ban yarda da nadamar wanan matar ba a lokaci daya haka tace wai ta sauko.
Tayi hakan ne kawai don ta batarwa mutane da hankali ke kuma ta jefaki a cikin damuwa yanzu sai ki zage sosai ki bi mijin ki ki kara kwantar da hankalin ki a kan auren ki.
Bayan mun gama waya da umma Nafisa ta karba ta bar wurin tana fadin yau kin min daidai kan matar nan wallahi wai me take nufi dake ne zainab ?
Nace koma me take nufi ai yanzu ya saura gareta tace tunda ta nuna hakan wallahi yanzu ki shirya ma zamakin sosai kada ki tafi baki shiryawa zaman ki ba don zata iya yi maki komai a duniyan nan tunda bata kaunar ki dai a ranta yanzu.
Dama tasone ta more maki kawai suci moriyan ki karshe ta hadaki da yan aikin gidan ta aure taci gaba da more maki ko yaushe.
Sai Allah ya fitar dake ya dora ki saman ta da bata taba zaton hakan ba a rayuwan ta ai dole ta yi bakin ciki dake yanzu .
Don alama ya nuna duk cikin diyan ta mijin ki tafi so a rayuwan ta fiye da yan uwan shi .
Allah zainab ki tari mijin ki a yanzu kuma kija hankalin shi sosai tunda kinsan ba sabawa yayi dayin hakan ba kila sai kin koya mai a yanzu.
Nace cikin harara kamar tana ganina a lokacin nake fadin akace maki ni din na iya ko ?
Ko baki iya ba dai kedin mace ce ai don haka sai ki koya kawai daga yanzu zan turo maki wani wa,azi na abubuwa ki saurara sai ki fara daga yau zanyi magana naji ta kashe wayan tana dariya.
Ba a dade ba naji massage suna shigo min na duba itace ke fadin ki bude ki saurara na turo maki sakon Allah bada sa,a sauraren in samu lada ga hakan nima.
Tsuki nayi na jefar da wayan na shiga wanka bayan na fito ne wayan yana ringin na dauka sa,adatu ce a layin take fadin inna ce tace yau baki kira ba tun safe ko lafiya in kira mata ke taba inna muka gaisa tare da tambayan lafiyan su.
Muka dan taba hira kafin taba kannena wayan muka gaisa dasu kowa na fada min abinda yake so in sayo mai idan zanzo sallaman su .
Na kashe wayan ne har zan aje saina tuna da zancen sakon Nafisa hakan yasa na kunna data na na shiga sakon na fara saurare ina shafa mai ajikina lokacin dare ya somayi har goma da rabi yayi gashi ban ko ci abinci ba a lokacin.
Ashe shima rashin fitana ya hanashi cin abincin sai gashi dakin ya shigo a daidai lokacin ina kashe wayan dana saurari wa,azin a ciki.
Zama yayi a bakin gado ina saka rigan dana dako saida na gama yake fadin me kika fadawa mami dazun daga maganan wasa kika sake mata magana haka ?
Amma kinsan mami ita kadaice gun mahaifin mu ai zata dauka da ita kike wanan maganan ai jin hakan sai nayi murmushi ina fadin.
Ba zan taba fadawa mami maganan da zai bata mata raiba don mahaifiya take a gareni saida wani dalilin yasa kaji na fadi hakan a yanzu ma.
Oudio wayana ne ya soma magana ya dago kanshi da sauri tare da juyowa a inda nake tsaye yana sauraren zancen mu da mami na dazun din.
What ya fada har ya mike ya koma ya zauna tare da dafe kanshi na dan wani lokaci ina tsaye na hade hannaye a wuri daya ina kallon shi.
Tare da fadin tsamanin hakan yasa na danna wayana ya dauki komai don sheda a gareni duk da hakan ba wai haka na nufin raini ko wani abu zai shiga tsakani mu bane da mami.
Har kayi tunanen na fada mata maganan da zai bata mata rai dani bayan an shirya mu a yanzu di nida ita.
Kawai na fadi hakan ne don abinda nima take tunanen yi a gareni don haka a yanzu ka barni don Allah in koma gidan mu don ka shirya da mahaifiyar ka a zauna lafiya.
Koyin hakan zai kawo maku kwanciyan hankali a tsakanin ku daga fadin hakan naja bakina nayi shiru tare da zuba mashi ido.
Sai kawai naga ya mike zubur ya fita daga dakin ya barni nan a tsaye ina binshi da kallo kafin in fada saman gado don takaici.
Nakai minti talatin a hakan ina sakawa ina warware a zuciyana kafin in mike zubur na shirya duk wani shiri da zanyi najawo kofan dakina na saka masa key na fita zuwa part din shi kai tsaye.
Yana kwance saman gadon kamar yadda ya saba idan yana cikin yanayin damuwa har na rufo kofan na karaso bakin gadon bai motsa ba.
A hankali na kai zaune ba tare da nayi mai magana ba ina karatun addu,oin kwaciya na gama na kai kwance a gefe shi da dan nisa a tsakanin mu .
Ranan tuesday in Allaj ya kaimu zamu koma don haka ku fara shirin tafiyan mu ya fada ba tare daya motsa din ba.
Na fada ma ba zan zauna ba yaya gidan mu zan koma don mami ta tsaneni har cikin ranta ba zan taba yin haske a zuciyar ta ba.
Idan zaman kanki kikeyi ki koma gida din a yanzu ya fada tare da gyara kwanciyan shi duk a zatona dana shigo zancen mami din zai min kan musayan maganan da muka fadawa junan mu.
A hankali yakai hannun shi ya kashe hasken dake dakin kawai ji nayi ya mirgino ta gefe na ya rungumeni a cikin jikin shi gaba dayan shi ya sakar min nauyin shi yana wani irin ajiyan zuciya.ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI BARKAN MU DA WANAN SAFIYAN ALLAH YA SADAMU DA RAHAMOMIN SA ALLAHUMA AMIN.

LITTAFIN KUDINE DON ALLAH KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALLAMA KADA MU RIKE JUNA GA HAKAN, , , ,


Yar uwa ko zaki tuna da wata boyar Allah mai suna mama Ai ko mama Aisha a cikin groups din mu da Allah ya karbi ranta a sanadiyan ulcer rana daya duk munyi hira da ita a ranan zuwa yamma Allah ya kirata zuwa gareshi.
Yar uwa ko kin gane ta ko baki gane ta ba ina mata baran addu,a a wurin ki ubangiji Allah ya kai haske a kabarin ta ita da sauran yan uwa musulmai da suka kwanta dama tun zamanin Annabi Adamu har zuwa wanan ranan ta yau ubangiji Allah ka haskaka kabarin su idan tamu tazo mu cika da kyau da imani Allahuma Amin, , , , ,

Wani iri naji har kasan zuciyana a lokacin duk da ya saba rike ni sometime sai dai wanan rikon yayi daban da na kullun daya ke min a baya.
Don rikone dake nuna yana a cikin zafin rai a lokacin da farko nayi yunkurin hana hakan a gareshi don yadda nake jin zafin shi dashi da mahaifiyar su a lokacin.
Tunanen kalamin umman su Nafisa ne cikin huduban da tayi min da cewa ki rugumi kaddara ki karbi mijin ki da hannu biyu don shi Allah ba ruwan shi a shanin aure idan kin saba mai zai tuhume ki ga hakan.
Ruguman mijin shine zai kara kawo mai natsuwa a zuciyan shi don akwai wani sirin boye dake tsakanin miji da mata da sai Allah ne yasan wanan.
Zakiga komai sabanin daya shiga tsakanin ki da mijin ki da zaran sun kwanta a wuri daya komai sai ya wuce a zukatan su a koma daidai.
Koda ko abin bai tafi duka a zuciyan su ba a sannu zaizo ya gushe ba tare da sun san dalilin hakan ba a gare su wanan sirine da Allah yabarwa kanshi sani.
Idanuna na runtse danayi wanan tunanen ina jin yadda yake ajiyan ziciya hannun shi nabun sassan jikina a hankali hakan ya zame min bakon abu din babu na mijin daya taba taba min jiki da suna jin dadi a zuciyar shi sai wanan ranan.
Inda hannun shi yakai ne yasa ni dan yi kamar na zabura lokaci guda shi din ma wani irin haniniyar da dawakai keyi yayi a lokacin wanda har hakan ya bani dan tsoro da sauri na bude idona na sauke a kanshi.
Yanayin da naga fuskan shi duk rashin wadattacen haske dake dakin lokacin hakan bai hana na yadda fuskan shi ya sauya ba zuwa wani yanayin da ban taba ganin shi ba a cikin sa.
Ganin na bude idona yake fadin kamar mai rada a lokacin bayason wani yaji abinda yake son fadi.
Be cool bby i don't wana hurt you, be cool dis my first time to be with a girl like dis, , , , ,
Dan abin da zan iya tunawa ke nan yana fada a lokacin dan cafkan da yakai min a saman kirjina tun wanan lokacin na fice a cikin hayacina ga baki daya ban san duniyan da aka kaini ba .
Sai hawayen dake dan gangarowa ta gefen fuskana da ban san kona meye ba don kanshi ya gaji da jagulana ya barni a lokacin.
Saida na dan dauki lokaci ban iya motsawa a yadda nake ba kafin can na dan fara daga hannu na a hankali ina neman rigana daya cire a cikin dabara saman godon.
Daga gefena nake jin yadda yake ta faman sauke numfashi tare da ajiyan zuciya duk a lokaci daya yake wanan kamar wani wanda yai tseren gudu tsira daga abin cutarwa ya tsere mar.
Ko ya fahinci abinda nake nema ne a lokacin sai naga ya dan miko min kamar cikin fushifushi daga hakan ya koma ya mirgina yana gyara kwanciyan shi da kyau.
Hakan ya ban daman samun in mike da sauri na nufi banda ina tsugunawa sai fitsari shaaaa don tsoro ko bakon yanayine oho ?
Har wanka saida nayi ina hawaye ga nawa wautan har da wankan tsarki saida nayi kafin in fito ban dakin don naji ana fadin daka kasance da namiji wanka ya hau kan ka kenan.
Hakan yasa na hada da tsarkake kaina a bandakin a zato na yayi barci a lokacin ina hawa gadon naga shima ya mike ya nufi bayin a hankali na rufe ido na mayar dasu lumshe sai dai tunanen da nakeyi kawai a lokacin har barci ya dan saceni ban sani ba .
Jin ruguman da yayi min yasani dan bude idona a firgice ina kallon yadda ya matseni a cikin jikin jin da yayi na dan falka a tsorace yayi saurin fadin shiiii baiyi amfani da baki ba wurin fadin wani magana.
Gabana yana faduwa don haka kawai dan tsoron daya fara yi dani yasa na tsorace da al,amarin shi ga baki daya ganin yadda yai min din.
Can murya kasa kasa kamar maganan ya zama mai dole a lokacin ya fara fadin Fadila ta fada min asabar zata bar gidan nan kwata kwata .
Wani irin ajiyan zuciya na sauke tukun kafin ince haka ta fada min amma na roke ta da tabari har mu bar kasan ta tafi.
Ta yarda da hakan ya tambaye har lokacin ina rike a cikkn jikin shi bai sakeni ba nace batayi min wani bayani ba bayan hakan.
Ba zata yarda ba na sani don aikin tane ya kare a gidan nan zata koma masu da bayanin abinda ta samu a nan din jin hakan yasa na danyi yun kurin barin jikin shi.
Saidai bai sakeni din ba yana matse dani yake fadin kiyi tunanen abinda ya dace muyi mata kafin ta tafin jibi.
A haka mukai barci yana rugume dani a cikin jikin shi sai gashi gaba dayan mu, ranan mun makara ga sallah asuba, a gagauce muka samu yin sallah lokacin shidda da rabi na safe tayi a lokacin.
Ina idar da sallah na gaida shi a cikin kunya ban tsaya a dakin ba na koma dakina ina shirin kwanciya karan wayana dana bari ne ya tayar dani.
Na dauka kada ya katse Nafisace sai mamakin kiran da take min da safe haka ya kamani na daga da rawan jiki gaba yana dan faduwa don kiran safe ba dadi ke gareshi ba wani lokaci.
Ina dauka abinda naji tana fadi yasa hankalina ya fara kwanci tana fadin amarya amayra a cikin dariya naja wani tsuki ina fadin.
Ke yar iskace wallahi, ni har kinsa gabana faduwa wallahi wanan kira haka da sasafen nan haka ai saiki tsorata mutum dashi.
Ai dole gaban ki ya fadi tunda yau kinji maza a jikin ki da sauri na tareta da fadin ke dan Allah magulmaciya to abinda kike son ji bashi din ya faru ba.
Naga alama tunda naji muryan garau ai amma jafar bai kyauta min ba da bai samu banza ya lalatsa muna ke ba wanan bakin ya mutu a yau din nan da anyi magana kice kema daidai kike da kowa har yanzu.
Allah yafiki Nafisa don adduan ki bai karbu ba wallahi yayan naki da yake mace kamana shima matsoracine irina .
Har me zai iyayiwa mace a yanzun duk da kirarin da yakeyi wai ya warke a yanzu ta kwashe da dariya tana gadin.
Yarinya kidai bi sannu wallahi kada muji ana kara maki ruwa asibiti wata rana sai abin ya ban dariya na kashe wayan ina fadi a raina hakan ai ya kusa faruwa dani a jiyan Allah daine ya taimakeni.
Ban iya fitowa dakin ba sai wajajen sha biyo da rabi koshi don lokacin sallah ne da yayi a lokacin nasan na tashi a wanan lokacin.
Wanka nayi na fito yi sallah kafin na gyara jikina na fito waje na lura da baya gidan don motocin shi da bangani ba a lokacin.
Babu kowa a falin na nufi part din hjy in gaida ita na samu bata gidan wai sun fita tare dashi zuwa gidan mami .
Banyi mamakin jin hakan ba don nasa zancen bai wuce maganan jiya daya farune tsakanina da mami zai kaisu gidan a yau.
Dan tun barin hjy asibiti sai jiyan da muka fita tare da itane taje gidan saidai su mami din su zo gaida ita a nan gidan nasa.
Abu bai dameni ba tunda nasan ina da gaskiya akan zancen don haka na share maganan a raina don yanzu an kai bana jin shakkar mami din kuma ko kadan a zuciyana kamar baya can da nake jin tsoron ta.
Don ada can ko muryan ta naji sai gabana ya fadi don tsoron ta da gudun saba mata da nakeyi amma a yanzu sam na daina jin hakan.
Ko dan na kara shekarune ko kuma dan budewan da idona yayi a yanzu ne ban sani ba wanda nasan ita ma a yanzu dai tasan da hakan.
Abinci na zauna naci don har sun gama abincin rana a lokacin ina kanci sadiya ta fito ta ganni zaune take fadin.
Anty kin tashi dazun nayi ta lekawa kina barci har yaya yasa na dauko mashi wayan ki a daki ban san me yayi dashi ba kuma ya bani na mayar maki dashi.
Ina anty take na tambaye ta ba tare dana bata amsa ba na kawar da maganan tana dakin ta ta shiga tayi sallah ta bani amsa.
Mikewa nayi bayan na gama zuwa dakin sai da nayi sallama ta amsa na shiga tana zaune tana waya ganina baisa ta daina wayan ba.
Abinda naji tana fadi yasa na gane da yan gidan su take wayan a lokacin har ta kare a gurguje ta juyo tana fadin na barki zaune ko madam.
Mun tashi lafiya na fada tace lafiya kalau, zuwa na biyu gaida ke na samu kina barci wallahi sai yanzu na tashi nabata amsa.
Abinci yana falo ta sake fadi ai har naci yanzun dana tashi din ashe hjy ta fita ita da yaya na tambaye ta.
Eh naga sun fita duk ransu a bace bayan sun dade a daki suna magana dashi da ita kafin su fita din hjyn ma ke fadin gidan mami zasu tafi yasa na san inda zasu din.
Nasan kin san komai anty tun farko abindake akwai tsakanina da mami shine jiya din muka tafi akai muna sulhu ta nuna komai ya wuce a wurin ta ai.
Jiya kin gansu a gidan nan da yamma ai tace eh nace bayan sun zo nan din kuma ta sake nuna hakan a gaban kowa komai ya wuce a tsakanin mu din.
Bayan munje sallah da tace a dakina zatayi nan dai na kwashe komai na fadawa fadila din yadda mukayi da mami din ranan.
Na karasa da fadin to yanzu nasan a kan wanan zancen ne suka tafi gidan don wanan maganan yasa yaje mata harda evidence din shi da yake dashi kan hakan don na dauki komai a lokacin.
Tace kai subbahanallahi wanan matar kamar bata da imani wai bata tunanen ita din uwace haka na iya faruwa ga wani nata koda bata da diya macw ne ?
Irin uwanyen mijin nan suna da yawa saidai wasu basu taba yarda a gane hakan a garesu har duniya ta gane zasuyi tayin abin a boye ne sai sunga bayan mutum idan ba Allah ya hau da kai kansu ba.
Wasu kuma baro baro suke fitowa fili su nuna bakin cikin kan matan diyan su din tunda kinji cikin maganan ta ai ta fadi tafi son shi fiye duk diyan ta.
Kinga ke nan koba keba zata iya yin hakan da kowa a kanshi don haka zainab don darajan Allah ki zauna da mijin ki lafiya.
Nayi nazarin mijin ki na gane shi mutum ne mai kyautatawa iyali da son kulawa na tare dashi don haka yadda take sone bata samu ba a gareshi din ba kuma zata taba samun hakan ba tunda a yanzu ya gane ko waye mami din kan iyalin shi.
Ba zai taba yarda da hakan ba idan ba wani kaddara ya kaddaro hakan ba a gareku nayi saurin fadin idan ma zata yi din tayi ai wanan bai damuna a yanzu.
Umm,umm zainab kada kice hakan don yanzu ba zakice ga kan aure ba tukun don baku fara zama zamana aure ba dashi a tsakanin ku.
A lokacin zaki gane waye miji a wurin ki da barnan da mami din ke son tayi maki a lokacin.
Jin hakan yasa na danyi murmushi sai nake fadin motar ki tana ina yanzu na daina jin kina zancen ta fa ?
Kai wanan motar ai wahala ta fara bani daga baya kawai na sayar da ita nasa a cikin ginan da mukeyi don ina son mu samu gida na kan mu nida mahaifana.
Allah sarki na fada kawai muka dauki wani hiran rayuwa mun dan dade a dakin muna hira kafin mu fito dukkan mu waje.
Su hjy sai bayan la,asar suka dawo gidan kowan su ya nufi part di shi bayan na fitone nasan sun dawo gidan na shiga wurin hjy don mu gaisa.
A zaune take tana duban wani abu a cikin leda na zauna muka gaisa nayi masu an dawo lafiya.
Kafin ta amsa min saida ta tabe bakin ta tana fadin ke dai mun dawo da wanan abin kunyan da uwar ku tazo jiya tayi a gidan nan.
Nikan da ba don ba sai ince an sauya iyamine ta koma haka ko ince an min hurhuren ta a can turai data zauna a can.
Yarinya da kafiyan tsiya kamar mutanen farko yau ai dai taji dan nata dama haka duniya take ai ka yi aimaka.
Idan tace ba zataji magana ta ba ko shawarana ta daukeni da mutunci itama yau taji a jikin ta kamar yadda nake ji a kanta din.
Don yau danta ya fada mata data rabaki da shi ta rasashi har abada a duniyan nan don haka ta rabu masa da mata haka.
Shigowan shi hjy tace kinga sa nan yau a kanki yayi fadan da bai taba yi ba a gabana sai dana tsawata mashi ya daina haka.
Common kin faye surutu ya fada yana fadawa saman gadon dake dakin a rigingine ya kwanta yana kallon daking din dakin.
Shiru yayi muna ta hiran mu da hjy kafin yace zainab kinyi shawara kan magana fadilan din nace eh nayi .
A cikin turanci yake maganan na fada mai abinda na hango a kanta din yace is ok kawai zuwa can ya mike ya fita daga dakin.
Mikewa nayi nabi bayan shi abinci na hada na sameshi ya fito ya zauna bai wani ci ba ya mike ya koma saman kujeran dake falon ya zauna.
Na gama hada kayan na biyo bayan shi muka zauna a wurin sadiya na fitowa take gaidashi yace sadiya kin fara shiri ko.
Zamu koma ne yaya ta tambaye shi yace next week insha Allahu nake son mu koma .
Zamu je Anchau ke nan kwanan nan ta sake tambayan shi da hakan zaku koma kuma again ya tambayeta shima.
Zamuje mana mu yi masu sallama na fada don ba zamu wuce bamu sallamesy ba gaskiya ke nan ba next week zamu tafi ba ke nan idan hakane.
Kowan mu yai shiru shi yace ok sai kusa ranan da zaku din kafin mu tafi yana fadin haka ya mike ya shige part din shi.
Bai kara fitowa ba sai da dare na sameshi zaune ya maida hankalin shi gun laptop din shi yana aiki a ciki.
Jin motsina yasa shi dan dago kai yana fadin hado min ruwan zafi na aje wayata da zanin sallah na juya nabar dakin zuwa yi abinda yace nayo din.
Saida ya sha tea din shi ya gama ya hau gadon ya dan dade ko me yakeyi ban sani ba sai can najishi yana dan kiran sunana ban bude ido ba.
Ba kunya ba tsoro abinka da tashin turai ba kunya ko sanin ya kamata kegaresu wai nice yau ya jafar ke fadin yana son ya kasance dani .
Ki taimaka a yau nake son na kasance dake if posible ya fada min kai tsaye kai wa,iyazu billahi wani irin naji wanan maganan a kunnuwana.
Jin bai samu amsa a wurina ba yasa naji yakai hannu a jikina ya fara tabani na dan zabura don ban gama fargaban zancen shi sai jin hannun shi saman jikina nayi.
Sannu a hankali yake bin ko ina da sallo yana dan kara matse ni ina runtse ido tare da kiran sunan Allah a zuciyana.
A lokacin nake tunanen maganan shi ta farko dani zuwan mu chaina da yake fadin shi da mace sai friendship ko zumunci kawai ke tsakanin shi da mace babu wani sha,awan da yake jin gun diya mace a rayuwan shi.
Sai gashi yau shine kuma din yake yin abinda mai sha,awan wani abu a jikin mace yakeyi yana sake wani irin sauti dake fitowa daga ko ina din jikin shi.
Ban kara yarda shi din bane saida yake kara sautin gurnanin da yake sauka min a kunnuwa ina jin kamar a mafalki hakan ke gudana a tsakanin mu .
Sautin ya zo min a baza da kuma tsoro a lokaci guda dan wani irin ihun daya yanka lokaci guda tare kokarin shigana da yake kokarin yi a lokacin .
Duk ilahirin jiki shi na wani karkarwa nima hakan nawa ya shiga yi a lokacin gaba dayan mu muna a cikin wani irin yanayine mai ban tsoro s garemu .
Ina jin yadda jikin shi ke wani irin bada sauti mai kama da ana kara wani bangare na mutum a lokacin kas kas kas amma kuma hakan baisa ya dana yin abinda yakw da niyar yi din ba a lokacin.
Wa,izubillahi a cikin lokaci gudane komai ma da zai faru din ya faru damu don dai ya samu din yakai garemu yayin daya koma kamar mara hankali lokaci guda.
Zai shiga cikin wani yanayin da bai taba shiga ba ke kuma baki taba gani ko jin hakan ba ki daure ga duk wanan abinda zaki gani hakan shine karshen wani fitina ko shirin shi ke nan a duniya.
Hakan shine rushewan duk wani abinda bai sani ba dake boye a ruyuwan shi zancen kakar maya ne ya fado min a rai .
Tace zaki jirki kamar yadda zai jirkitan idan kinga hakan ki jika wanan kusha a tare ta daga hannayen ta ta ware su a lokaci guda alama komai ya wuce ke nan.


ZAINAB IDRIS MAKAWAASSALAMU ALAIKUM YAN UWA DA FATAN MUN TASHI LAFIYA ALLAH YA BAMU WUNI LAFIYA DA ALBARKA DAKE A RANAN NAN AMIN, , , , ,


Dare mahutun bawa ne a lokacin kowa ya kwanta yana hutun gajiyan rana da samun sauki a cikin rayuwan yini.
A wani gida dake unguwar sarki a cikin garin kaduna kamar yadda kowa yake kwance yana barci haka kuma ahalin gidan nan suke kwance suna hutu suma kamar kowa.
Ihun da aka sakene a lokaci daya ya tayar da duk ilahirin wanda ke barci a gidan lokacin sai dai wanda ke wani abin baiyi barci ba.
Wani ihun ta sake sakawa wanda yasa kowa na gidan fitowa waje da sauri don ganewa idon su abinda ke faruwa.
Ihune yanzu ba kakautawa sai kiran sunan iyami da mijinta marigayi matar keyi a cikin tashin hankali.
Wanda hakan yaba duk wanda ke gidan a lokacin tsoro sai faman fadi takeyi Allah ya isa Rakiyan hayi.
Ko kuma tace kai ina karya dai sam wanan ba zai taba yuyuwa ba ace ka karye bayan nice kadai mai iya karya wanan kwalban haba dai sai kuma ta fashe da dariya da tabe tana son fita waje da gudu.
Ke ke ke haulatu wai meye wanan haka kikeyi kika tayarwa mutane da hankali ki duba har kananan yara sun fito don wanan ihun da kike sakewa mutane haka s cikin dare.
Wani irin mikewa tayi tsaye da karfi tana fadin ni ni ni sai kuma ta gitgiza kanta tana fadin karyane iyami karyane wallahi.
Ba zaki shigo ki fini ba a gidan nan na fada maki iyami sai naga bayan ki har diyan ki wanan dan naki jafar da ake fadin yafi kowa taurari masu haske a cikin zirian nan sai na mayar maki dashi abin kyama a gun jama,a.
Wani tsaya Alhaji Adamu ya dakawa matar tashi uwar gidan shi kuma uwar yayan shi manya ke nan a gidan.
Yana fadin wai haulatu kina da hankali kuwa kikw fadin wanan maganan haka Rakiyan hayi dake mukaje dauko kwalba wai yanzu kwalba ya fashe ya tarwatse a sanadiya wata.
Zance ta fara sakewa kamar mai bada labari sai salati duk wanda ke wurin suke sakewa diya ta naja baya daya bayan daya suna kuka.
Hankalin kowa a tashe don sun gama fahintar abinda ke gudana a lokacin yayiwa iyami da jafar danta asirine yanzu asirin ya kare ya koma mata..
Dole aka sakata daki aka kulle don tonon asirin yayi yawa a lokacin suka dawo sukai zugun zugun a waje suna jinta tana ci gaba da fadin irun abinda tayi a gidan.
Kowa hankali tashe gabani asuban farko sukaji dukan kofa a zabure samarin gidan dake waje cirko cirko suke tambayan waye da daren nan haka.
Alhaji hayi yace nine Alh hayi na layin ku mijin aminiyar hajiya haulatu matar kanin mahaifin su jafar uwa kuma ga Rufaida a yanzu.
Da sauri Alh Adamu ya karaso kofan yana fadin lafiya Alh a cikin daren nan haka yace daga waje inda yake tsaye ina fa lafiya Alh wanan matar Rakiya mai dakina tun cikin dare muke fama da ita da hauka tuburan .
Sun je sun aikata sheri tare da maidakin hjy ta nan gidan yanzu kuma abu ya koma mata tana can tana faman tonawa kanta asiri gaban diya da kishiyoyin ta tun dazun.
Kai innalillahi Alh Adamu ya fada yana bude kofa kafin yace muma nan tun misalin sha biyun dare muke fama da Haulatu cikin irin wanan halin.
Wa,iyazu billahi ai zance ya baci ke nan kuma da na dauka tana a hayacin tane muji abinda ya kawo haka a bakin ya don sai sunan hjy iyami da danta take ambata cikin sambatun nata.
Abinda itama take fada ke nan shiyasa na gane cewa sunyi wani aiki akan iyamin da yanzu ya karye ya koma kan su kuma.
Yanzu dai dole mu nemi malamai su warware muna abinda ke faruwa ko kuma a kira ita hjy iyamin aji ko tana da masaniyan hakan.
Ba sai an kirata ba a yanzu don hakan kamar sirin mu ne Alh gara a fara neman malamai din don kada hakan ya kawo wani fitina kuma.
Fitina Alh Adamu ai ita da ta dauko fitan sai dai ya kare a kanta wallahi banji ban gani ban kuma aiketa aikata hakan ga wani ba balle abun ya dameni.
Wanan zancen ma yasa ka fargar dani hanya yanzu gidan su zan bugawa waya suzo su dauke ta su tafi can su karasa wanan abin kunyan badani ba wallahi.
Da sauri Alh Adamu yace kada ai haka Alh ai lafiya suka baka ita shi zaka duba ba sai yanzu da haka ya cika da ita ba zaka tura masu ita gida yanzu.
Nasani amma hakan zanyi kai in zaka tsaya gidan ka ya koma gidan kallo zuwa safe daga haka ya juya Alh na kiran shi bai tsaya sauraron shi ba ya tafi.
Sai dai abinka da babban gida sai gashi tunda asubahin nan a samu wanda ya kira mami ya fada mata duk abinda ya wakana a gidan.
Hankalin mami din ya tashi sosai haka yasa bata iya kara komawa barci ba da sasafen nan ta tayar da yaran ta take fada masu abinda ke faruwa a kaduna din.
Itama Rufaidan yan uwanta sun kirata tun a cikin dare suka labarta mata abinda ke faruwa kuka ta rushe dashi har hankalin yan uwanta ya tashi sun dauka ko mutuwa aka aiko mata anyi.
Sunyi tambayan duniyan nan tana cewa dasu ba komai har suka gaji suka kyaleta saidai basu koma barci ba suna hira a dakin su.
Har akai sallah kowa ya watse don zuwa office da zasuyi don ranan aikine ranan sai dai kuma jin tun safe an bude get dib gida mami ta fita yasa hankalin su kuma tashi.
A falo suka hadu da Aisha data fito tana mamakin fitan mami din a wanan lokacin suka hade dssu falon nan suke fada mata zancen Rufaida din ta shiga dakin wurin ta.
Tayi tambayanta tana ce masu ba komai ita gida zata tafi ranan ganin haka yasa Aisha daga waya ta kira hjy dake hanyar gidan mu tana fada mata abinda ke faruwa da Rufaida din.
A cikin hasala hjy ke fadin kada ku barta taje ko ina munafukan banza da wofi kawai ta kashe wayan.
Mamakine ya kama Aishan jin abinda mahaifiyan nata ta fada kan rufaida din da take ji da ita kamar yar cikin ta.

Ganin irun mikan da yake faman yi yana hamma da wani irn nishi yasa naja jikina da kyat har na sauka saman gadon ni kaina ina cikin wahala don yadda ga baki daya nake jin jikina kamar ba nawa ba a lokacin.
Ga zafin wahala dake cina ga hankalina da yake tashe a lokacin don tabbasa nasan da a cikin hayacin shi yake da ba abinda zai hana shi taimaka min a lokacin.
Bandaki nayi karfin halin shiga na sakewa kaina ruwan zafi kafin na dan fara jin sa,ida a karkashina da nake jin bakon yanayi a gareni.
Da kyat na fito bandakin da bin bango har na kai kofa na bude na fita zuwa dakina Allah ya taimakeni ba kowa daya ganni a lokacin har na bincika kayana nafito na koma dakin da sauri.
Na shiga na samu ya fado saman gadon da gani akwai alaman ciwon ciki mai karfi ko wani abu dai yana damun shi sosai a lokacin.
Da kyat na iya kai gwiwana kasa na dago kansa da kyat ya dan bude idanun shi kadan ya mayar dasu ya rufe nayi dubaran bude bakin sa a hankali na fara dura mai maganin ya hade.
Yana shiga makoshin shi ina jin wani kara da yakeyi har ya sauka mai lokaci daya naga yayi wani irin zabura da karfi badan Allah ya gyara ba daya barar da kofin maganin dake hannuna a lokacin.
Idanuwan shi ya ware yana kallona nayi mai sannu tare da kara daga kofin ruwan maganin da niyar kai masa a bakishi.
Yayi saurin rike min hannu yana kallona kasha zaka samu lafiyan abindake damun ka a yanzu na fada a cikin damuwa.
A take ya bata fuska nace yi hakkuri ka hade ya bude bakin na kara dura mai ya karba yasha yana bata fuska ya hade da sauri.
Ya maida idon shi ya lumshe wanan karon kan zaune ya mike da sauri jikin shi yana wani irin karkarwa tsoro ya kara kamani lokaci guda can naji ya sake wani irin gyatsa mai karfi saidana zabura.
Bai jima a zaunen ba ya koma ya kwanta a kasa inda yake da farko din sai ga wani irin zufa yana karyowa a goshin shi lokaci daya kuma sai gaba daya jikin shi zufa ya karyo mai.
Nidai ina gefe daya ina kallon ikon Allah kafin ya bude idon again ya sauke a kaina yana nuna min AC dakin da hannu don har yanzu ya kasa bude baki yayi magana har lokacin.
Tambayan shi nayi a kara ko a rage ya gyada min kai haka yasa na mike da kyat na kara karfin AC har karshe a hankali ya fara sauke ajiyan zuciya.
Ganin da nayi kamar zaiyi barci a lokacin yasa nace dashi ko zaka daure ka koma saman gado ka dan kwanta a can .
Kamar bai jini ba sai can ya mike da karfi a lokacin ma na farga da jikin shi babu komai dan abin rufane kawai daya kwaso ya dan rufa a gaban shi.
Saida naga ya kwanta ya dan fara samun natsuwa na dauki sauran maganin da yake aje nashanye gaba daya maganin idan ya sauka ciki yana da zafi nikan da cikina baida komai banji irin abinda shi yaji ba.
Na sake gyatsan kamar yadda shima ya sake din daya sha ina jin wani zafi a jikina na koma saman gadon na dan kwanta sai barci.
Lokacin dana farka shidda ta gwauta na samu nakai ban daki da kyat ina sake ruwa a jikina ina gasa ko ina .
Wai sai lokacin kuka yazo min na dade a ban dakin ina kuka kafin in fito in tayar da sallah sai da na idar na tayar dashi ya zabura yana salati kafin kuma ya koma ya dafe kai da sauri na dan wani lokaci.
Sai can ya mike ya shiga ban dakin ya dan dade kafin ya fito wurin wardrobe din shi ya nufa ya dauko riga ya saka saida naga ya tayar da sallah .
Na nufi gadon da nake gyara na canza zanin gadon zuwa sabo ban tsaya har ya idar ba na fice dakin zuwa dakina.
Don a matse nake komai wuri kawai nake nema da zan kai kwance a lokacinb kaya na saka a jikina na kwanta tunanen abinda ya faru a daren jiyan ne yake dawo min a raina.
A hankali na mayar da idona na runtse a cikin takaici da bakin ciki ina nadaman kasancewa a cikin wanan halin.
Yau mace idan ka ganta tare da mijin ta ka barta kawai a inda ka ganta ba sai ka tono abinda ke boye ba.
Don matsalan gidan wani daban yake dana gidan wani sai dai abin na wata yafi na wata abin ban mamakine .
SHI ABU A CIKIN DUHU DAI SIRINE kawai a barshi a boye a yadda yake zaifi sauki.
Barci ya dauke ni har na tsawon wani lokaci a cikin barcin nake jin ana tashe ni sadiya ce tsaye a kaina take fadin ki tashi anty ina ga kamar ba lafiya a gidan nan.
Don ga mami nan tazo tun dazun a cikin kuka har ya jafar ta shiga dakin takirashi suna dakin hjy ana hayaniya tun dazun din kowa sai kuka yakeyi.
A zatona abinda ya fado min a rai shine zancena da mami daya faro a jiyan da sukaje mata dashi.
Shine har yanzu basu bar zancen ba a tsakanin su saidana danyi wanan tunanen na dago ina cewa sadiya ki zauna nan kada ki kara fita falin ga baki daya.
Ta kalleni a cikin mamaki kamar zatayi magana sai tayi shiru kafin ta kai zaune gefen gado ta kurawa kofa ido.
Mikewa nayi a hankali cikin dabara na daure ina tafiya zuwa ban daki na samu na kai da kyar nayi fitsari na dade ina gasa kaina kafin na fito a lokacin naji dan dadin tafiya a yanzu.
A daidai lokacin da nake zama take fadin wai anty mami din tana da kishiyane jin haka yasa na dago ina kallon ta nace sadiya meye damuwan ki da zancen mami ne ?
Anty ji nayi mana yanzu suna fadin wai kishiyan mami din ta haukace jiya da dare wai tayi masu asiri ya karye.
Wani irin faduwan gaba ne ya ziyarce lokaci daya dana ji hakan a take zancen malam kakan mu ya fado min a rai.
Da yake fadin akwai asiri a jikin mijin ki karyewan shi zai samu ne kawai a jiki ki duk ranan da mijin ki yakai jikin ki komai zaizo karshe da yardab Allah.
Kedai kawai kuci gaba da amfani da maganin nan da wanda tsohuwar nan ta baku a can akwai waraka a cikin sa sosai insha Allahu.
A sannan ne za ku gane waye yake bibiyan mijin ki tun yana karamin shi har zuwa yanzu din don dai akwai hannu sosai ga al,amarin shi.
Kallon sadiya din nayi kamar zan yi magana sai naga wanan maganan bata kai ta gane abinda ake nufi ba.
Na dan jima a zaune kafin na mike ina fadin barin zo sadiya ki jirani a nan na fada na fita daga dakin.
Ina kokarin shiga dakin nake jin muryan ya mamud yana fadin ko an kaisu kotu dawa zaki sharia mami ?
Kawai dai ki barsu da Allah tunda har Allah ya fara tona masu asiri tun nan duniya kowa ya gama jin abinda ya faru a gari dama duniya.
Kawai ko haka aka barsu ai ya wadatar sai mu kara godewa Allah da har aka gane su a yanzu.
Na shiga dakin da sallama sai hjy dasu yayane suka iya amsanin sallama su mami kan basu iya amsa min ba a lokacin.
Na gaida hjy tare da mami na juya wurin yaya ina gaidasu ya jafar ke fadin ni abinda yake ban mamaki me nayi mata da har take kiran sunana a zancen ta na hauka.
Dama an fada muna haka zai faru ai amma sai ta wani dalilin asirin zai karye daga wata mace kuma don komai da mata ake karya asirin shi ai dama.
Sai nayi tunanen wani sabon sheri mami kuma zata dora min don ban karkare sanin maganan da sukeyi din ba a dakin na san dai kan zancen da sadiya ta fada min ne .
Yanzu dai kunji abinda daddy sulaiman ya fada ai tana fadi wai itace sanadin hana jafar haihuwa kohin aure ys mamud ya fada.
Haba innalillahi wa,inna alaihim raji,un ga magani a jikin mu muna ta faman wahala da abu a jikin mu shekara da shekaru haka.
Dolene ma mu tafi kadunan a yau din nan don ayi komai a gaban mu su san muji komai tunda shi Alh Adamun wai baya son mu ji zancen.
Dama dazun muna hanya Aisha ta kirani wai Rufaida sai rusan kuka takeyi taki kuma fada masu abinda ya same ta.
Ina fa zata fadi wanan abin kunyan garesu hjy ta fada taci gaba da fadin ni ko zamar yar nata a gidan ku ban yarda dashi ba tun farko wallahi.
Yanzu ku tashi mu koma gidan kai jafar ka shirya sai mu hadu a airport dakai idan lokaci yayi.
Kai ya kada masu yana fadin ba inda zanje mami ku tafi kawai na barta da Allah don yau ni jikina haka na tashi bana jin dadin shi hutu kawai nake son samu a yanzu.
Ka zauna din amma mu dole ne mu tafi do ba a san iya sherin da sukai ta bin mutane dashi ba haka tunda ba imani ke gareta ba.
Ta yaya mutum zai yi wanan sherin hakan tsawon wanan shekarun kuma hankalin shi kwance ya mamud ya fada.
Ka bar mace shu,uma inda ka ganta komai akace wanan matar tayi zata iya don irin yadda akasha fama da ita a baya har saida lokacin iyayye suka shiga tsakanin su hjy ta fada.
Mami ta sauke wani ajiyan zuciya tace ni ai jikina ya mutu wallahi sai nake ganin abin kamar a mafalki.
Har suka tafi basu daina maganan ba a ranan kuma suka isa kaduna duk da sun so ganin matar amma sai suka samu wai an tafi da ita wurin mai magani.
Kafin wani lokaci magana ya zagaye unguwa da gari duka kowa yana fadin albarjacin bakin shi akai.
Ya jafar din ne yayi min bayanin abunda ke faruwa a tsanake kafin hjy kuma ta kara ban labarin zaman su da abinda akace din tayiwa mami da jafar din.
Nikan abin mamaki ya bani don nasan matan sosai zamana a gidan mami takan shigo lokaci lokaci zance ita din bata damu da zuwa gidan mami din ba sai idan haka ya kama na tazo.
Sai dai idan tazo din akwai yin iko gare ta don ban da shakat sai idan ta tafi nake samun sauki.
Ranan kan yasha waya daga mutane daban daban da suka shafi yan uwan su na bangaren mahaifin su da tunda nazo gidan ba gane mami bata yadasu ba.
Da dare ma zancen daine sukayi da hjy da take fadin ai ka bar mamaki don ba mijin su daya ba take wanan kishin da uwarku.
Shi mutum mai hassada haka Allah kan yo shi da halin sa a jini kawai kyashi da hassada ke kamasu har su aikatawa dan uwan su keta.
Dama irin wanan kishin yafi zafi a tsakani don daya bata kainan taga daya ta fita da komai alhalin kuma ba miji daya suke aure ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI BARKAN MU DA YAU BARKAN MU DA GIDA FATAN ALHERI GAREKU A KULLUN, , ,


Haka abubuwa a kwana nan biyun suka taru sukai muna yawa ga abin daure kai mutum na gani a filin Allah don abinda zai baka mamaki bini bini mami zata kirani wai tana ban labari yadda abin yake faruwa a can kaduna.
Yanzu ma din hakane ina zaune misalin sha biyun rana wani kiranta ya shigo min sai naji gabana ya kara faduwa don nasan wani maganan daya dangaci wancan din na uwar Rufaida da ake fama a yanzu.
Ina dauka da sallama tana fadin wai zainab kin san matan nan har akanki wai taje gidan boka ai muna asiri in tsane ki da duk wanda ke tare dani.
Sai yau dai da mukaje gidan tana ganina ta shiga tono tonon asiri tana hintar kanta tana fadin kinfi karfina iyami kin fi karfina .
Sai abin ma yaso ban dariya amma na daure a fili ina fadin wa,iyazu billahi mami me wanan matar take nufine dake ?
Mami naga dai duk yadda akeyi kin masu a rayuwa ga yarta kuma a hannun ki kina rikewa tsakanina da Allah.
Mami din tace to ai zainab baki sani ba wai ashe ko zaman Rufaida din wurina wai ashe da dalili sun shirya hakane don ita Rufaida din ta auri daya daga cikin diyan dakina.
Wai ashe kuma jafar dinki take so shine suke faman neman asiri da zasu samu kan jafar dani da kuma karya wanan asirin da yanzu ya kare take wanan fallasan haka.
Na nisa tare da fadin O ikon Allah ita kuma kalan nata rayuwan ke nan mami, ba zata iya dogara ga Allah yayi mata mafita ba na rayuwa sai ta danganta rayuwan ta da gidan boka da malamai ?
Su saba ne da hakan tun farko ni kingani na ban taba yarda da irin wanan halin bin malamai da bokaye ba a rayuwana.
Komai yazo nakan saka hannu bibiyu in rungume shi in fadawa Allah damuwa akan lamari injira sauki daga gare shi.
Allah yasa mufi karfin zuciyan mu na fada tace to amin kedai zainab aisu masu wanan irin halin zakiga kullun a cikin talauci suke.
Saboda hassada da bakin ciki suka sakawa zuciyan su da haka mukai sallama da ita wanda nasa ko zuwa dare zata kara kirana a kan zancen.
Ina kashe wayan nake fadin a fili Allah mai iko yau nice da mami haka muke hiran arziki a tsakanin mu.
Dama hakkurine da wuya duk abinda kaji ana fadin kayi hakkuri a kansa har ka iyayidin insha Allahu hakkurin ka baya zama banza.
Yau da banbi maganan magabata na da shawaran manyan dake tare dani da ban kaiga cin ma hakan ba a rayuwana.
Shine ya shigo dakin yayi tsaye tare da tsura min ido kafin yace dawa kikw magana hakane tun dazun nake jin ki.
Dan dago kai nayi tare da saurin mayar da kaina kasa don yanzu tun faruwan wanan abin a tsakanin mu bana iya hada ido dashi sosai a yanzu din.
Mami ce ta kirani take ban labarin mamab su Rufaida na bashi amsa kai tsaye kafin inji yace kai mami tasaka zancen matan a ranta sosai.
Ni na riga na barta ga Allah ga duk abinda tayi min nasan dai ban taba cuta mata ba a rayuwa tunda nake ta iya min wanan mugun sihirin haka.
Ni yaushe ne matar nan zata bar gidan nan wai ya tambaya na gane fadila yake nufi don haka nace dashi ina ga rokon ta danayine yasa ta janye tafiyan har lokacin tafiyan mu.
Kina ganin hakan bata sabawa dokan aikin su ba ya tambayeni yana kallona nace bana jin hakan don da zai saba din ba zata yarda ta tsaya ba ai.
Kafada ya daga tare da fadin ok a fili idan dai ta tashi ga wanan ki bata ya miko min key da envelope sabo na karba tare da masa godiya kamar nice akaba kyautan .
Ko ban san komai ba nasan wanan makulin motane ya bata ya juya yana fadin ida ta tashi sai ta tambayi Hadi driver zai nuna mata motar ta dauka.
Na kara mashi godiya ya fita daga dakin sai abin ya ban mamaki kwarai da gaske don ban taba tsamanin zaiwa fadila irin wanan kyautan ba haka.
Dakin ta na nufa kai tsaye bata cikin dakin yasa na fito na shiga surun sadiya a can na samesu zaune suna kallo nace ashe kina nan yanzun daga wurin ki nake tafe ai baki dakin.
Tace ina nan tare da mutumiyar muna kallo sakon ta dake hannu na na mika mata ta kalla a cikin maki kafin ta karba daga hannuna.
Yayan mu yace a baki idan zaki tafi naga ya dace in baki tun yanzu don ki sani ta bude baki cikin mamaki sai kuma tace wanan duk nawa ni kadai a take yanayin ta ya sauya.
Sauka tayi daga saman gadon sai kawai naga ta zube a kasa tana godiya kai haba anty bani ya kamata kiwa hakan ba ai na fada ina zama.
A sanadiyan ki ai na samu duk wanan alherin da ace banyi zaman lafiya da kuma tsakani da Allah daku ba duk wanan alherin ba zan sameshi ba ai.
Sadiyace ta katsemu da fadin yaushe zamu tafi gurin su inna anty ta jefo min tambayan nace ina gadai a cikin satin nan ne don baiyi magana akan tafiyan ba har yanzu.
Ke nan zakuyi tafiyane kuma nace eh zamu mayar da hjy daga nan mu wuce gida muyi masu sallama.
Lalai hakan na da kyau ku koma kafin ku bar kasan nan zaifi amma kuma kune zaku mayar da ita gida ke nan na dauka mamice zata kaita gida ?
Mami yanzu haka tana kaduna a can zamu samesu don gaba dayan su suna can kadunan kwana biyu ke nan da tafiyan su.
Naji hjy na fada jiya a waya wai mami tayi hakkuri ta bar zancen ga Allah sadiya ta fada ba zata iya kyale zancen ba don ko waye dole hankakin shi ya tashi .
Amma tunda Allah ya mata fada a yanzun gaskiyane ta barta da Allah zaifi laifi akai mata ke nan ko fadila ta fada ?
Eh to laifin ne nan dai na dan fada masu komai sama sama tayi saurin fadin ummhum nasan da hakan wallahi don inda ta taba zuwa a kanki wani lokaci an fada min hakan .
Sai dai abinda bai shafeka ba tunda bashi ya kaini ba a lokacin yasa ban dauki zancen da karfi ba mun dan dade muna hira kafin mu watse a dakin.
Duk kwana kin nan yaya bai kara cewa zai nemini ba nima kuma naji dadin hakan da darene mun kwanta yake fadin ya gama shirin tafiyan hjy mu shirya gobe da yamma zamu kaduna daga nan muje anchau muyi sallama dasu.
Allah ya kai mu na fada ina gyara kwanciya naji saukan hannun shi yana fadin ban son zuwa kaduna a yanzu don gaba daya garin ya fice min rai.
Dan juyowa nayi ina fadin laifin mutum daya zai shafi sauran yan garin itama din da tayi ai Allah ya fitar ma da hakkinku tun a nan duniya ta fara ganin mugun halin ta.
Kome mutun zai aikata idan ba alheri bane a rayuwan shi banzane don komai dadewa sai ya tambayi mutum ?
Abinda nake tunane ke nan a yanzu na rasa me nayiwa wanan matar har bata sona haka ?
Bakai tawa ba da farko ta dauka ta cuci mami ne don da ita take hamaiya bada kai ba.
Ajiyan zuciya ya sauke tare da dora hannun shi saman jikina naji gaba na ya fadi lokaci guda duk da tsorin shi da nake yanzu har ya san da hakan.
Shine dalilin da ya dan sarara min ya kyale ni a yanzu din amma ni kuma sai nake ganin ai rashin sabawa da zama da mace da bai iya bane yasa bai wani damu da kulani din ba.
Ko wanan ranan gaskiya nasha bakar wahala gun yaya don bai tausaya min ba haka ya koma kamar wani zaucace a gareni.
Washe gari mun isa kaduna bayan sallah magariba gidan na mami shiru da a yanzu duk sai na ganshi wani iri can kamar bashi ba.
Kodan yanzu idona ya bude da ganin ginan zamanine oho abinci mukaci kawai yace wai mu fito mu tafi .
Nayi mamakin jin ba a gidan zamu kwana ba ashe abinda ban sani ba shine yana da wani irin keraren gida cikin kaduna ashe haka ma ya mamud shima a yanzu ya bar gidan mami din.
Gidane na gani na fada na shiga tsara nayi mamakin hakan sosai danaga gidan lafiya lau komai ba laifi gida ya hadu.
Nan ma dai din bai kyakeni ba don mun zuba soyayya a wanan gidan sai dai kawai a kawo muna abinci daga restaurant muci safe da yamma .
Ko gidan mami bamu lekawa sai dai su ya jamal dake dan leko mu a ranan mu na ukku a gidan ne da dare muna falo bayan mun gama cin abinci wayan shi yai ringing ya dauka.
Naji yana fadin ina gida mana lafiya jin hakan yasa na dan dago ina kallon shi daga inda nake kwance na dan kishin gida saman jikin shi.
Banji me akace ba yace ku shigo mana ina kokatin jaye jikina a nasa don jin abinda ya fada din amma kuma sai naji ya rikeni ya hana in tashi din .
Ga mamakina Aisha ce suka shigo tare da wani saurayi da ganin shi irin samarin nan ne yan karya diyan masu kudin garin.
Mun gaisa dasu idon saurayin yana kaina hakan yasa ya jafar din kara daure fuskan shi sosai yake fadin umm, humm .
Kince kina son ganina ne akwai magana fadi abinda zaki fadi ina sauraren ki sai ta dago ido ta kalleni kafin tace dama magana nazo muyi yaya a kan magana na da Hashim gashi nazo maka dashi ku gaisa.
Yace waye shi tace kai tsaye shine wanda nake so kuma mami bata yarda ba har yanzu ya kalli yarin yace mami din ta fada maki haka da bakin ta sai tayi shiru.
Nan ya fara yiwa guy din tambayoyi yana bashi amsa kafin yace da ita alright zanga mami din muyi magana da ita kafin in tafi.
Daga haka ya fita batun su ni kan ba wani maganan kirki ne a tsakanin mu ba tunda na fahinci wani irin daukan kai da take min tun dawowan mu din kasan na kama kaina ga al,amarin ta ga baki daya.
Sallama sukai mai suka tafi ya tashi ya rufe gidan ya dawo ya zauna yana fadin ban san meke damun yarinyar nan ba zata kwaso min wanan ta kawo mi shi har gida.
Haba dai gidan dan uwanta tazo fa ba wani wuri ba kuma da gani tana son yaro nan sosai yasa tazo wurin ka ka taimaka masu .
In ba haka ba ai ya mamud ma yana garin da gurinshi zasu tafi ba wuri ka ba amma kuma ta zabi nan din tazo.
Wayan shi ce ke ringing ya dauka saurare ya tsaya yi har na wani lokaci kafin naji yace yanzun nan suka fita nan ita dashi.
No ban samu mata fada ba don tana tare da yaro a lokacin ni dai mikewa nayi ya bini da kallo don ranan sadiya tabi ya jalal da yazo zuwa gidan mami wurin hjy saboda idan muna daki da yaya ita kadai ke zama ba abokan hira.
Ya gama wayan ya shigo daki ya samu na shiga wanka koda na fito yana tsaye a wurin window kamar mai tunane.
Zama nayi bakin mirrow ina shafa mai yazo ya tsaya a bayana yana fadin ana magana kan Aisha kin bata rai.
Ba tare dana juyo ba muna facing din juna a cikin mirrow din nace dashi shi sha,anin aure ne yaya ba ai masa haka tunda shi take so har ta kawo shi gareku ai idan ba laifin sai ku bari tayi abinta.
Wa zai bari ta auri wana guy din kece yarinya da baki san komai ba wanan da ganin shi tashin waje ne bai koyo komai ba a can sai iskanci .
Wani kallo nayi mai da sauri don jin abinda ya fada din yace yes nasan abinda zakice ai ko nayi nawa a lokacin ina kokarin danne hakan a kasata ai.
Amma baka zaton auren shi din a dalilin ta zai iya gyaruwa ya bar wanan a kidar ya dawo dai dai ba dai wanan din ba na fada maki ke yarinyce ya wuce ya shige ban daki ya barni zaune ina tunane.
Ban san yadda sukayi da mahaifiyar su ba ni dai ranan sai ga Aisha din da gani tasha kuka tun a gida don idonta da yayi ja ga duk wanda ya ganta.
Sun dade da dan uwan nata a dakin shi suna magana don ta shigo ni fita nayi muna waya da Nafisa da tace zasu shigo dasu umma.
Ta fito ko sallama ban samu ba ta fita tana sharan hawaye su umma suka zo gidan sai hankalina ya dauku garesu na manta da zancen nasu.
Ranan a gidan su umma suka wuni tare dani da zasu tafine yayi masu alheri mukai sallama suka tafi.
Mun je gida mun samu Asabe na cikin wani hali na rashin lafiya kai tsaye yace a kawota asibiti kaduna wanan kuma ya kara dauke hankalin mu sai dai Asabe din duk da gatan data samu lokaci yayi ba magani a wanan jinyar ta rasu tana saka muna albarka ni dashi har innan mu.
Mun kuma koma can gida muka kwana daya na dawo kaduna daga nan muka dawo Abuja .
Sai muka fara shirin tafiya sai kuma ga zazzabi har saida na kwanta asibiti don jirgitan danayi ga zazzabin.
Hankalin jafar din ya tashi sosai da ciwon nawa sai da mami take ce masa kowa fa haka yakeyi idan an samu juna biyu duk da hakan bai gane me mami din take nufi ba.
A karshe dai tana murmushi take fadin nifa naga kamar matar ka na da cikine amma a bari saka makon ya fito a gani.
Ciki mami ciki ke ga zainab din sai kuma ya shafo kanshi zuwa fuska yana dan murmushi ya rungumi mami din lokaci guda.
Itama mami din dadi taji a lokacin tana dan bubuga bayan shi tare da fadin Alhamdullahi jafar tunda baka halaka ba ga baki daya gashi yanzu har zaka iya haihuwa ashe.
Koda na falka suna zaune su uku sun tasani gaba suna kallona dan binsu da kallo nayi na dan lokaci kafin in dan motsa baki ina gaidasun
Suka amsa tare da yi min ya jikin nace da sauki ina yun kurin tashi don aman daya tayar dani daga barci a lokacin.
Shine yake tambayan ina zan tafi da yaga ina sauka daga gadon da sauri na kaaa magana sai dana ns bude baki wani amai yazo min da sauri na nufi wirin da nake zaton ban dakine a wurin daga gefen dakin.
Tin ina amai a duke har na koma yi tsugunne haka yssa shi shiga bayin yana min sannu na fito a galabaice bayan na kurkure bakina da ruwan daya ban.
Wasa wasa wanan ciwon saida yasa muka kara kwanaki a kasan don jikina yaki dadi sam ga mutane sai faman zolayata sukeyi da sunan mai ciki da har lokacin ban yarda da hakan bani.
A haka muka tatara muka koma Chaina sai dai saboda yanayin jikin nawa yasa yace in nemo wace zamu zauna ko a gidane mu tafi tare.
Akwai wata babban yar malam dake gida auren ta ya kare kuma bata taba haihuwa ba gorin kishiya ya fitar da ita gidan miji tana gida zaune da itace zamuyi tafiyan don kanwa take ga innan mu ke nan don haka muke kiranta da mama Ladi.
Duk da mami bata so hakan ba a cikin ranta ba wai bata son zuwa da ita din bane don tana bangarena a,a.
Saidai a ganin ta matar ba zata iya bani kulawan da ya dace ta bani ba don tana yar kauye har ta kula mata da abinda ke cikin cikina a yanzu.
Ba wata dole din da ita muka tafi hakana don na nuna ita nake son muje don yadda nayi zama da mahaifiyar mama ladi din maizube.
Ban samu wani wahala ba ga tafiyan don mun isa lafiya sai dai barcin da nayi tayi bayan saukan mu din.
Zaman mu da mama ladi ba wani matsala a cikin shi don ina jin dadin zama da ita sosai kuma ina bata girman ta na uwa a gareni haka shima a bangaren shi kamar yadda yaji muna kiranta da mama Ladi hakan yake kiran ta dashi.
Yayin da sadiya kan tuni ta koma school din su don tana da permition na barin wurin dan lokaci daya daukan mata.
Ban yarda na zauna ba tun da muka dawo duk da laluran dake gareni na ciki din bai hana mai da hankali wurin tsare ibada na ba don samun kariya a wurin Allah.
Haka itama mama ladi mace ce mai yawan ibada sosai bata da wasa wurin aiwatar da ibadun ta .
Tsorona kada yan wanan kungiyan su kawo muna hari ko su kara jan ra,ayin shi ya koma cikin su tunda yanzu sunga ya barsu kwata kwata bai tare dasu.
Don tunda zamu dawo mami tayi min magana akan na taimaka na mayar da hankali akan shi sosai don Allah don ita da son samune ma ba zamu koma wani kasa ba a nan gida zamu zauna tare dasu.
Wanan na rike a zuciyana ina kallon duk wani shige da ficen shi a yanzu din bana yarda in yi nisa dashi ko a dauki lokaci banji inda yake ba.
Sai hakan kuma ya kara jawo muna shakuwa sosai dashi don ko ban kirashi ba shi zai daga waya ya kirani yaji lafiyan mu.
Har mama Ladi na fadin don lura da tayi dashi idan ya dawo aiki sai yazo inda nake ya rungumeni a jikin shi ya dan zauna tare dani na dan lokaci.
Take fadin wai irin wanan zaman namu ba na malam bahaushe bane da iyakarshi da mace sai idan dare yayi yana da bukatan ta.
Nayi dariya ina fadin mama aiko a hauwan na da can baya ke irun wanan dabi,an na yanzu kan sun waye suna abinda ya kamata suyi na kulawa da iyalin su.
A kwana a tashi har cikina ya isa haihuwa a lokacin mami wayan ta ko yaushe kiran mu takeyi taji halin da nake ciki.
Har dai Allah ubangiji ya saukeni lafiya na haifi da na miji mai kama da ubanin shi sak don bai raga su da komai ba har tsayin su da irin yanayin yayan mami duk ya kwaso su sak.
Basu wani tsayar dani ba a asibitin don ina da lafiyana na dawo gida duk abinda kakan maya ta bani da an haihu na fadawa mama ladi komai tunda na karbo maganin.
Don haka batayi wasa wirun bashi maganin ba tun a asibiti tayi dubaran dura mashi ya fara sha yana bata fuska.
Sai dai abinda ya dan sa jikina sanyi shine yanayin yaya jafar din game da haihuwan nawa dana zata zai nuna farun cikin shi sosai ga hakan.
Sai banga hakan ba ga fuskan shi sam kamar yanayin shi yana a cikin damuwa a ranan ya dan dade tsaye a kan yaron yana kallon shi kafin ya juya ya fita ya bar dakin.
Na bishi da kallo haka har muka dawo gida sai ya zauna yayi shiru shi kadai kamar mai tunane ganin hakan da nayi ne yasa na fahinci akwai wani abu a kasa wanda ni din ban sani ba.
Wanka na fito mama da Sadiya suna zaune dashi ta gama shirya shi na dan kalleta nace mama zaki iyayiwa yaron nan hayakin nan da malam ya bamu da sauran maganin shi duk a dura mai koda kadan ne ki kuma shafa mai su.
Tace mai zai hana yanzu kuwa hakan tabi ko ina da hayakin bayan ta gama masa komai yadda ya dace naga kuma ta daga shi tana addua har muna iya jin abinda take karanto mashi a lokacin.
Mun kwanta lafiya Allah kuma ya tashemu lafiya tunda asuba naji ana buga muna kofa na fito daga wanka ke nan kamar yadda mama ta umurceni da yi.
Muka kalli juna da mama Ladi din kafin ta nufi kofan ta bude kai mama Ladi ta san kanta sosai a wurin addini gaskiya don zuwan ta ba karamin rana yayi min ba.
Shine tsaye a kofan idon shi a kan mu yake fadin lafiya dai kuka kwana ko yake tambaya ba tare da ya amsa mata gaisuwan da take mashi ba.
Lafiya kalau gashi har tayi wanka shi kuma dan yanzu nake batun in masa yana da rai ko ya fada .
Ban san lokacin dana dan sake man dana dauko zan shafawa jikina ba a lokacin na nufi wurin gadon da yaron ke barci shida sadiya hankalin su kwance a lokacin.
Hannuna nakai a daidai saitin kirjin yaron kafin na mayar zuwa hancin shi naji numfashin shi yana sauka lafiya.
Na dago ina kallon shi daga inda yake tsaye ya tsura min ido nace dashi me hakan ke nufi ban gane wanan tambayan da kai min ba yanzu ?
Nima ban sani ba ya fada yana barin dakin zaune nakai dabas na kalli mama Ladi da itama mamaki ya kashe ta a wurin ta kasa magana a lokacin.
Kada ki dauki wanan wani abu wata kila dai mafalki yayi daku ya razana ai kinga kamar a firgice yake koda ya shigo dakin .
Na bude baki da kyat ina fadin mama kashe yaron nan zasuyi don tun jiya a asibiti naga hankalin shi a tashe sosai daya tambaya akace namijine na haifa.
Wanan sai Allah ya isa ya kashe bawan sa zainab kada ki sa hakan a ranki har kikai ga yin sabo tunda zargi kike masa yanzu.
Har in ma akwai wani kulli tattare da yaron nan Allah yafi mai shi da sherin shi duka don mu da ayan Allah muka dogara bama tsafi bama tsubo.
Duk wanan zancen na mama hankali bai kwanta ba mikewa daga inda nake zaune a gurguje na shirya na fita daga dakin zuwa wuri shi.
Na sameshi yana sintiri a dakin yana rike da casbaha a hannun shi daga shi dogon jallabiya a jikin shi lokacin.
Jin motsina yasa ya dan juyo yana kallo na har na karaso inda yake tsaye din har yanzu yana numfashin normal ya kara tambayana.
Nace eh sai dai ban gane dalilun wanan tambayan dakake tayi kan yaron nan ba tun dazun na tambaye shi.
Bai ban amsa ba illa juyawan da yayi zuwa bakin gadon shi ya zauna na bishi da kallo kafin in iya daga kafa zuwa wirun shi din naja na tsaya.
Don gaba daya na fita hayacina tunda na fahinci akwai matsala kan yaron nan dan mala,ikin Allah dako nonon uwa bai fara iya jaba sai ma da darene kafin mu kwanta mama ta matsa a fara koya mashi jan nonon da taimakon ta ya dan fara kamawa bawai ya iya jan ba.
Ko ka bada jinin shi ne dama ka barmu a cikin duhu na tambaye shi a cikin wani irin kakausan murya dake nuna ba tsoro a zuciyana lokacin.
Sai lokaci ya dago kai ya kalleni idanuwan shine suka kada sukai wani irin ja dasu lokaci guda yace nasan ba zasu barshi ba zainab .
What na fada a razane kagin in koma fadin innalillahi wa,inna alaihi raju,un nakai zaune kafin in fashe da wani irin kuka lokaci guda .
Hannun shi naji a jikina yana kokarin rikeni zuwa jikin shi nayi maza na jaye ina fadin kada ka tabani mugu azzalumi kawai.
Nayi nadaman sanin ka a yau din nan yaya da wanan rayuwan bakin cikin zan dinga riska a tare dakai na kwamace Allah ya kasheni kafin in girma har in sanka.
Wani kallo yai min da jajayen idanun nasa yace cikin karfin hali zainab ni kike kira yau da azzalumi haka a gabana.
Nace idan ba azazlumi kake ba me kake jafar jin na kira sunan shi kai tsaye haka a karo na farko yasa ya danyi min wani irin kallo kafin yace dani.
Ban zata a yanzu zaki min wanan judgen din ba ke da kanki bayan kin fi kowa sanin tubana da nadamana na gaskiya shi har ga Allah.
Akan me zan shede ka bayan ga abinda ka fada a yanzu kuma tun jiya din naga alaman damuwa a tare dakai don bakayi farin ciki da haihuwan yaron nan ba.
Fine naji kin gani din kuma kin gane amma ya kamata ki saurareni tunda har kinga damuwa a gareni.
Ni nasan ka,idan sune har idan mutum ya kubuta daga garesu zukaga da gaskiya ya barsu din sai sun dauki fansan akan abinda ya haifa idan namiji ya fara haihuwa a duniya.
Cikinane yabada wani irin sauti kulululu, , , lokaci guda numfashina naji kamar zai tsaya a lokacin kafin naji yana fadin saidai nayi mamakin ganin basu taba yaron nan ba har ya kwana yana numfashi.
Akwai abu dayan biyu zuwa uku walau addu,an mune dana yan uwa Allah ya karba .
Walau kuma addau,an ya hade da tsarin da kikai muna amfani dashi don gaba daya basa son zuwa wurina don sun daina bibiyata sam a yanzu.
Kokuma yaron nan ya soma cin abinci ko kafin suzo gareshi yaci wani abu ko yasha nonon ki shine dalili zainab ba wani abuba don haka ki daina zargina da hakan.
Allah yafisu jini dana dana yafi karfin tsafi ko wani abu don ina tare da Allah da ayar Allah a tare dani.
Dana ya sha zamzam da dabino haka kuma yasha nonona tun daren jiya din ba zasu iya min komai da yarda ubangijin mu Allah.
Ba zasu iya ba har abada na sani don da zasu iya din da sunyi suma sun fada kuma sun barmu din sai dai tsoron wanan nakeyi dama akan su.
Nasan da diya mace ce basu ko kallon ta yarinyar ta tsira ke nan shi yasa ake son bawa idan zai tuba ga sabon da yaiwa Allah yayita har kasan zuciyar shi.
Kuma tsakani da Allah ya tsarkake zuciyar da mu,amulan shi ga kowa sai Allah ya tsaya mashi ga duk al,amuran shi .
Na gane hakan a yanzu da kuma wani samir da hakan ya faru dashi don a yanzu yaran shi biyar komai sun kasa yi dashi da iyalin shi.
Haka nima na tsira ke nan zainab tunda har yaron nan a yanzu shima ya gagaresu tabawa ke nan har abada dashi da duk wani dan da zan haifa a bayan wanan din.
Jin hakan yasa na dan tsagaita kukana ina fadin dama Allah ya fada duk wanda ya barshi yabar imanin shi da kariyan shi daga abin ki.
Sabon Allah baida wani fa,ida sai tarin nadama a karshe da wahala da mutun zai dinga gani a rayuwan shi.
Yace wanan haka yake zainab tashi muje na kara ganin yaron nan in masa addua don ya tsira ya kuma tseratar damu daga wanan bala,in nasu har abada insha Allahu.
Jikinane yayi sanyi lokaci guda na kasa motsawa daga inda nake zaune din hannu ya kai ya mikar dani daga aurin muka fice daga dakin.
Tun kan mu karasa dakin muke jiyo kukan yaron muka isa da sauri yana hannun mama Ladi tayi masa wanka tana masa gashi nayi mamakin hakan ashe da abin gashinta tazo irin namu na gargajiya na gida .
Ya dade tsaye yana kallon yadda mamadin kewa yaron kafin ya fice cikin walwala da annuri a fuskan shi.
Gado nabi na lafe ina sauke ajiyan zuciya a hankali tare dayiwa Allah godiya bisa kariyan da yake bamu a kullun nayi ta tasbihi har barci ya daukeni ban sani ba.
Sai can na tashi a dan firgice ina kallon inda yaron yake goye a bayan mama ganin na motsane mamake fadin ki tashi kici abinci ba a son cikin mai haihuwa da yunwa ko kadan .
Hamdala nayi namike na tashi na shiga ban daki sai da darene nake fadawa mama komai daya faru sai bayan ta gama mamakin hakane tace insha Allahu Allah ya fisu yafi karfin tsafin su kuma.
Yan gida sun kiramu gwargwado sun muna barka mami ta nace akan sai yan suna sunzo anyi suna a nan chaina.
Dole ya yarda din suzo ciki masu zuwa aka bawa bangarena mutum biyu mami kuma ta kafe dole da inna a cikin masu zuwa din .
Don tazo taga inda nake zaune da badon hakan ba inna ba zata taba sanin inda mu biyu diyan ta muke rayuwa ba.
Sai ta wanan dalilim suka zo tare da Nafisa kawata daga kaduna suka zo da ita sai bangaren su ya jafar din suma mutum uku sun zama su biyar sukazo muna sunan.
Satin su biyu a wurun mu suka juyo suka dawo yaro yaci sunan mahaifin su jafar din Isma,il suna kiran shi da Anur.
Farin cikin inna nan baya musaltuwa don bata iya boye hakan ba saida muka kebe ne nake fada mata komai daya faru dani a rayuwan aure tunga farko har karshe kodana kai karshe inna na hawaye .
Tace Lalai zainab ABU CIKIN DUHU SIRINE yanzu kabar mutum a yadda ka ganshi kada ka tona cikin sa zakaga abinda baka zata ba idan ka tona din.
Musanman wa yan nan masu kudin na zamani da zakaga mutum yayi arziki a cikin dan kankanin lokaci ba a san inda ya samu arzikin shi ba.
A haka kuma zaka ga mutane na shige masa don kawai su samu abin duniya a hannun shi Allah ne sheda ban yarda kin zauna da bawan Allahn nan don nasan yana da abin duniya haka ba.
A,a Allah ne shedan zuciyana ya kuma ga manufata a hakan na baki hakkuri don halarcin mahaifiyan shi a garemu.
Nafisa ta amsa da fadin haba mama ta yaya zaka san irin haka har ka dauki danka ka kai wanan wurin koda kana da yaya da yawa ai akwai tausayin rai ko ?
Don ma shi jafar yana da imani da tausayi da halin halarci a zuciyan shi yasa abubuwan suka zo mai da sauki haka.
Sun tafi sun barmu da kewan su ina shayar da dana da yayi wayau ya girma har lokacin ban daina bunshi da addua ba da neman taimako munayin shi gaba dayan mu gidan.
Ban mantawa mun fita da ANNUR da baban shi lokacin ina da karamin ciki a jikina ciki na biyu muka hadu da philis a wani mahada.
Yana ganin nin mu saida ya kadu na shedashi bayi saurin fadin A,uzubillahi mina shetanin rajin .
La,ilaha illa anta subuhanaka inni kuntu minal zalumin sai ji mukayi daram yayi hatsari nayi mamakin yadda ya jafar bai nuna yasan shi ba a wurin .
Muka tafi muka barshi a cikin wani hali mutane sun taru a kanshi har muka dawo ina mamakin hakan a zuciyana daga baya nake jin wai ashe daga hadarun nan bai kara tashi ba har ya mutu a hakana karfin ayan Allah ya hau kanshi na fada a zuciyana.
I zuwa yanzun da nake baki labarin nan haihuwana ukku duka maza muna kuma lafiya na kara karatu yaya yai min hanya an daukeni aiki a wani babban company a nan chaina ina aiki.
Bukin kanwata sa,adatu yazo lokaci daya dana Aisha da Na,ima shine zuwan mu Nigeria da yara na uku lokacin don koda hjy ta rasu kakar su jafar bamu samu zuwa ba a lokacin ina da cikin dana na biyu.
Tunda Nuriya ta kyala udo ta gammu ta kasa biye kishin ta ga hakan don duk yaran data haifa matane bayan dan ta na farko.
Har yakai ta kasa boye hakan a zuciyan ta sai da ya kai har mamu tayi mata kashedi kan hakan kada tarihi yazo ya maimaita kan shi .
Ayin buki lafiya nasu Aisha aka farayi kafin na kanwata sa,adatu mun shiga mun fita nida kawata Nafisa da baka gane kawance ne kawai a tsakanin mu don mun zama yan uwa itama tayi auren ta a jos har da yara biyu.
Nan nazama abin kallo ga mutane wanda baisan irin rayuwan dana sha a baya ba yana min kallon na more miji.
Ni kuma ina masu kallon basu san ABU A CIKIN DUHU SIRI BANE.


Alhamdullahi godiya ga Allah ma daukakakin sarki daya bamu rai da lafiyan kai karshen labarin mrs jafar lafiya nima mai rubutawan ina rokon duk wanda na sabawa a dalilin wanan labarin ya yafe min don Allah .
Tsokaci gareku iyayye don Allah a dunga kula da irin mutanen da ku kanku iyayye kuke zama dasu don wani ba da zuciya daya yake zaune dakai ba a wanan zamanin.
Haka a dage wurin yiwa zuria addua ko wani lokaci muna cikin wani zamani mai kama da rashin imani yanzu ya kaura a zukatan bayin Allah.
Haka yan mata a daina ruwan ido aga mai kudi ba bincike a fada mai sai anje gida aga abinda bashi bane a gidan .
Ubangiji Allah ya tsare ya kare dukkan musulmi daga fadawa ko wace irin fitin nan wanan zamanin Amin taku

ZAINAB IDRIS MAKAWA

SAI MUN HADU A SABON NOVEL MAI SUNAN( ANA DARA)
ZAINAB IDRIS MAKAWA IDRIS MAKAWAAINAB IDRIS MAKAWA.
Chapter 5 · 0% Book details