Part din shi ya nufa ya bude da niyar ya dan huta a ciki saidai yaga kuran dakin da kyankyami kasancewar shi mai tsabta sosai.
Abu Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 570 min read
Fitowa yayi don ya duba mai aiki sukai kicibis da Nazifa ta fito falin sannu da zuwa ya J ta fada cikin nuna kulawa ba taee daya amsa ba yace ke dauko tsintsiya ki share part din nan.
Wa ni ya jafar ta fada tana wani turo baki gaba bake ba wancan zaki bace min kiyi abinda nace tunkan ranki ya baci wurin nan.
Ta juya tana gunguni zuwa kitchen yana tsaye har ta fito abinka da wanda bai saba aiki ba ji rakeyi kamar ta kurma hannu akai tayi ihu a lokacin.
Wajen gidan ya koma ya tsaya harta karasa can ya dawo ya samu wai ta gama kamar bata taba komai ba a dakin dakin na nan yadda yake.
Fita yayi da sauri yana kiran sunan ta da dan karfi ta fito ya balla mata harara yace common shara ma ba zaki iya ba.
Yayani fa bana shara wanan ma ai nayi kokarin yin sa yanzu kawai ba a sa yan aiki irin su , , ,
Ji kake fauuu ya wanke mata fuskan ta da mari da sauri ta kurma wani uban ihu daya fito da sauran daga daki.
Ta durkushe a wurin tare da dafe kuncinta da dukka hanayen ta biyu ta durkushe a wurin.
Saiga salma da Rufaida sun fito daga dakin da sauri suna ganin shi suka rikice sai sannu da zuwa suke mashi.
Kai ku fito ku gyara ko ina na gidan nan yanzu kafin indawo ko kuma ku samu naku hukuncin zaku zauna kubar gida haka a kazance kamar babu mutane a gidan.
Ya J mai sharan ne bata zo ba wai danta baida lafiya ku ba mata bane aikin me kukeyi a gidan ku ?
Ya j ba aikin mu bane shara fa yace oho relly ku din ba mata bane oya ban son in dawo gidan nan in sameshi a haka ya juya fita ya barsu nan tsaye nazifa na dafe da kumatunta tana hawaye.
ZAINAB IDRIS MAKAWA[25/12, 14:51] +227 98 36 59 34: 🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
3️⃣1️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH YAR UWA BARKAN MU DA WARHAKA DA FATAN ALHERI GAREMU BAKI DAYA ALLAHUMA AMIN.
LITTAFIN NAN NAN NA KUDINE DON ALLAH KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA YAR UWA DON KAUCEWA SHIGA HAKKIN WANI.
DON TURA KUDINSA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA 08036959257 UBANGIJI ALLAH YA HORE ABIN SAYA ALLAHUMA AMIN, , , , , ,
Daga inda nake kwance nake tajin dan kida na tashi a dakin sai dai dayake ba waya gareni ba yasa ban damu da in dago don ganin inda wayan ke kuka don a zatona ko wanine zai shigo dakin wurin hjy.
Don yanzu dakin bai rasa masu shigowa lokaci lokaci mussanman jikokin hjyn diyan mami ko wasu baki.
Haka yasa ko yaushe nake cikin gyaran dakin don kada a samu dakin yadda bai dace ba.
Wayan ne ya kara kira daga inda nake kwance rub da ciki don wanan dabi,a nane idan ina karatu in kwanta hakan duk da ance hakan baida kyau a musulunce.
Makan da hjy takai min a baya yasani dagowa a firgice tare da juyowa lokaci guda ina mamakin hakan take fadin sabon shiga wayan taki ce ke kida haka yana damun mu.
Kallon hjy nayi tace jeki ki dauka kada ya katse hjy kila ba kira bane wata kila alam ne wa nake dashi da zai kirani ni ?
Waya saya maki wayan idan bashi zai kira wanan lokacin ba ta fada a dan shagwabe da ban ma san nayi ba don ance ido wa ka raina yace wanda nake gani kullun idan ba hjyn ba wa zan tsaya yiwa wani shagwaba haka a gidan sai dai idan su mama kande da lami dan dama dama.
Jeki mana tun dazin waya na kara baki daga ba ta dan fada a cikin yanayin bani umurni don ba wasa a idon ta ko kadan a lokacin.
Dauka nayi sai kuma na tsaya ina kallon wayan don ban san yadda zan danata ba in amsa kiran.
Can dai na tuna da yadda anty Aisha ke daukan nata na daga tare da kara wayan a kunne na shiru babu sallama babu hello.
Yasa na sauke wayan ina kallon screen din wayan da sai lokacin ma na fara ganin yanayin ta na mayar da sauri na sake karawa a kunne na.
Jin har lokacin ba magana yasa na mayar da wayan kasa inda take canji na kara jona ta na juyo zan koma inda nake kwancene wayan ya kara daukan kara.
Na kara dauka na danna dauka a cikin siririyar murya nayi sallama badon naso ba sai naji sauke ajiyan zuciyar shi a hankali tare da fadin.
Barka da dare kuna lafiya saida na lumshe idona don jin muryan shi tar a kunne na da kuma abinda ya fada.
Da kyar na iya budan baki na amsa da lafiya kawai ban kara furta komai ba shima a nasa bangaren shiru yayi bai kara magana ba sai can yake fadin .
Wayar tayi maki ke nan ko ya fada don yarasa me zai fada, don jin muryana yasa shi jin kamar numfashin shi zai dauke a lokacin.
Dan murmushi nayi wanda bansan sautin shi zai fita waje ba har ya iya jina a cikin wayan.
Ashe kina murmushi da alama dai kina son waya a rayuwan ki tunda yau har waya ya sakaki yi min murmushi duk da bangani a fili ba nasan hakan yai maki dadi sosai.
Yaya sai anjima na fada don jin abinda yake fadi wanda kunnena ba zai jure daukan sautin muryan shi don yanayin dana soma ji a tare dani lokacin.
Ke ina wasa dakene zan kira kice zaki kashe min waya kina jina ya karasa magana dashi.
Kayi hakkuri yaya na fada a dan maraice kin kyautawa kanki da kika zamo mai saurin bada hakkuri don ni mutum ne da bai son raini ko a cikin abokaina.
Gabana ne ya fadi don jin abindaya fada tare da tambayan kaina yanzu wani raini nayi mai daga fadin sai anjima kawai.
Hjy fa tana ina naji yana fada donni har na shiga tunane a raina na manta da waya a hannu na lokacin.
Gata kusa dani na fada yace a bata wayan da sauri na mikawa hjy wayan ta karba naji sun fara gaisawa dashi.
Ka isa lafiya ya ka samesu nan yace hjy banje gidan kowa ba ina gida kwance tundana dawo.
Tace badai kana lafiya ba ko kadai kula da kanka ka dinga cin abinci don nasan halin ka jafari baka son cin abinci akan lokaci.
Allah sarki hjy zan kula kinsan ba komai nake ci ba hakana nagode da kulawan ki garemu kema ki kula da kanki ki dinga kashe kudin ki ba sai mami ta saya maki ba .
Idan na kashe zaka ban wasune ta fada a cikin zolaya kada ki damu hjy idan kudine baki da matsala su ko yanzu idan kina so zan turo maki.
A,a Allah dai ya karawa arziki albarka ta fada hjy wanan adduan muke bukata a wurin ku ko yaushe.
Addua kan muna yi ko yaushe ana kanyin tane Allah ya tsare ya kare ya kawo sauki a rayuwa.
Ya saki ajiyan zuciya tare da fadin shiyasa muma muke addua Allah ya barmuna ke a tare damu hjy don ki kula damu.
Kaida ka kara hakkuri kayiwa uwar ka biyayya a tafi a yadda take so don wuyan sha,ani kega uwar taku rayuwan turai ya bata ku ga baki daya yanzu.
Hjy turai basu da wanan halin ni kaina ina mamakin canzawan mami yanzu tun daeowan ta kasan nan komai nata ya canza a yanzu kamar ba mamin mu ba.
Ku daiyi hakkuri hjy nasan mami zata sauko da kanta idan ta gane gaskiya don mamud ma complain din da yake min ke nan ya rasa gane kan mami yanzu.
Kuci gaba da mata biyayya dukkan ku wataran zata gane gaskiya ta gyara da kanta Allah yace aiwa iyayye biyayya koda basu raye wasu nasu suna nan.
A hankali yace Allah ya bamu ikomn yi hjy nagode sukai sallama ya kashe wayan shi don yasan ba zan kara dauka ba.
Wayan ta miko min na karba take fadin kinga yanzu ai kwaji sauki ki daina wanan guje gujen da kike masa kamar kinga dodo.
Murmushi mai kama da yake na sake kasan fuskana tare da daukan takarduna na hada a jakkan makarantana.
Dan hira muka taba kafin barci ya fara daukana itakan sai dare da na falko fitsari na samu tana ibadan ta a zaune.
Idan na samu tana hakan watarana nakan yo alwalan inyi raka, a biyu in koma in kwanta idan an kira sallah zata tayar dani nayi sallah asuba zaman da banyi da kakana Asabe a gidan mu shi nakeyi da wanan tsohuwar don yadda ta daukeni take kuma sake min fuskanta tankar itace ta haifi mahaifana a cikin ta.
Barci ne ya daukeni ban sani ba bayan na idar da sallah sama sama naji muryan mami a dakin mu suna magana da hjy.
Bayan sun gaisane take fadin hjy kinji shirmen da yaron nan yaje yayi a kaduna wai jafar nason mu gama lafiya dashi kuwa hjy ?
Me kuma yayi kibi a sannu koma meye don yana da hankali ko me zai aiwatar.
Ina hankalin yake nan hjy yanzu aka kirani ake fada min wai yaje ya daki yaran nan har Nazifa da Rufaida sun kwana a gidajen su.
Yanzun kanwar daddy su ta kirani tana fada kan abinda yaiwa yar nata assha ita hjy ta fada tun kan mami ta karasa magana.
Wanan yar bata da tunane don jafari ya duki yar ta har zata kira ki ta fada maki ina wanta ne yana da ikon hukuntata idan tayi mai ba daidai ba.
Hjy meya kawo duka yanzu kamar jafar zai tsaya yana duka mace ina yaran nan yanzu dai sun wuce duka sai tsawatawa.
Ki dai yi bincike abinda ya hadasu fada aji haka kawai tunda ba hauka yayi ba, haka kawai ba zai farmasu da duka ba ai.
Wani abin dai sukai mai har hakan yakai ga faru a tsakanin su don haka ki binkita karki hau danki da mumunan zato har ki yanke hukuncin da bai dace ba a kanshi.
Hjy koma meye ba zaiyi hakkuri dasu wanan kawai wani sallon jan magana ne a guna yanzu kinji ita Binta tana fadin wai akan wanan yarinyar zeey ce ya daki yarta.
Wace yar tana nan ina suka ganta wai meyasa mutane basa son a zauna lafiya ne.
Kawai su dorawa yar nan bakin jini don kawai suna daukanta mara gata shi rashin gata rashin ubane halan ?
Yar nan fa ba shegiya bace don da ubanta don Allah ya nufa zataci daga tsatson su duk wani maganan bantanci sai ya kare akanta yanzu ?
Don kawai suna takana da iskanci irin tasu da basu san darajan dan Adam ba ina koke haka kikai ta fama da korafin su a lokacin saida Allah yai maki tsaye a kansu.
Hjy shine dalilina kan yaron don nasan ko bai samu matsala da kowa ba zai samu da yan uwan uban shi kan abinda yake son yi a yanzu.
Don daga sama,ila har ita binta din duk suna da bukatan ya auri diyan su kinga kuma ba abinda zai yuyu bane gareni.
Shiyasa nafi son ya fita can nesa yaje yai auren shi zaifi mun kwanciyan hankali tunda dai ba ganin su zasuyi ba idan yai auren sai dai idan yazo da tashi matar irin haka.
Duk ina kwance na lafe ina jin duk abinda ke wakana a tsakanin su zancen sukaci gaba dayi inda yanzu zancen ya koma akan hiran auren mami da mijinta .
Mikewa nayi daga inda nake kwance na sauko a hankali tare da kaiwa kasa na gaida mami da kwana ban tsaya dakin ba nafita zuwa dakin mami din na fara gyara mata.
Ga kudi nan a watse ko ina saman gadon kamar lissafin su take ta fita daga dakin da wayoyin ta aje saman gadon.
Ni dai na hadasu wuri daya na daga filo na saka karshin filon na gyara gado ta hanyar cire zanin gadon na shimfida wani don wanan kwanan shi biyu da shimfidawa ke nan.
Har na gama da dakin nata, tana dakin mu da hjy suna hira don haka na nufi kitchen kai tsaye don mu gaisa dasu mama kande da kwana.
Ina kitchen din suka hada abincin hjy na dauko na nufo dakin mu dashi inda na samu mami din tafice daga dakin.
Ina kika shiga ne tun dazun nake zancen ki a araina wankin tufafina da suka dan hadu nake son a kaiwa mai wankin can ya wanke min.
Ina kitchen wurin su mama kande kina aikin ko kindaiji abinda sahibin naki ya fada ki daina aiki a gidan nan gashi uwar taku yanzu nake fada mata abinda yace tace bashi ya dauko mata ke ba ai.
Kinsan iyami hutsuwace idan ba ita taso abu ba balle wanan da kamar jira takeyi ya zanta akai.
Hjy nidai don Allah ai masa magana ya daina kulani kada mami tazo tana ganin laifina a banza .
Yar nan aikin san yadda so yake ke idan kika fara kaunarsa ai duk abinda uwar taku zata fada ba zai taba damun ki ba gidan nan.
Hjy ni na fada da mamaki ni ina zan kai dangaye kamar yaya a kauyen mu ai sai suce yawon barikin na fita da gaske.
Kai yaro man kaza ke yanzu wazai samu tsalelen saurayi kamar jafari nidai hjy don Allah ki masa magana ya daina kulani kada su anty Rufaida su sakani gaba kuma ina zaune kalau.
A kul, akul na sake jin kiyi wanan zancen wata rufaibaida can dagasu har iyayyen nasu suma ba so suke ayi dasu ba.
Nasan wanan ba yanzu ba ina kula dasu a gidan nan duk take taken su ina karantasu a idona kece din dai da suka raina Allah ya makalawa son ki a ranshi.
Dukda suna ganin ki ba a bakin komai ba a gidan nan ba sai gashi Allah yana shirin daukakaki a cikin su shine suke neman hanyar da zasu bataki ga kowa yanzu.
Ni jafarin yayi min daidai daya gargadasu ya kora min yan banzan yaran nan suka bar gidan nan yara babu abinda suka iya sai munufi da iya shege a tsakanin manya.
To ba suna son shi ba su yaso su mana tunda sune yan uwan shi masu kudi nikan ya rabu dani hjy.
Yar nan kina data ido kuwa jafarin ne bakya so ko Allah zakiwa butulci da baiwan da yai maki na samun shi ta fada ranta a bace.
Bakina bude da zumar bata hakkuri don na fahinci jikan nata baya laifi a wurin ta amma sai ta dakatar dani tana cewa.
Ke matsoraciya ce ko mai zurfin ciki ke ko irin kishin nan ma bakya nunawa akan mai son ki sai faman gudun shi kike kamar kinga dodo.
Bance komai ba donni maganan tsohuwar ya fara wuce sanina don ni a ganina ko anty Aisha banjin tana maganan samari balle har aje ga magana na a gidan meyasa wanan bawan Allah keson ya takurawa rauwana hakane yanzu gashi ya saka tsohuwar nan ta hau zancen ta zauna a kai ba wanda ya isa ya furta wani kalami kan zancen shi.
Ganin yadda take magana rai bace bil,hakki yasa muryana rawa nace hjy don Allah kiyi hakkuri ban san ranki zai baci haka ba don na fadi ra,ayina.
Tsaki taja tana kawar dakai daga gefen tare da fadin ana baki kina roko idan uwar taku taji kina fadan haka ta samu inda zata fito masa ke nan ai akan cewa ya rabu mata dake tunda bakyason shi.
Fita nayi daga dakin tare da kayan wankin ta dana kwasa ban yarda na dawo dakin ba na zauna wurin su kande ko abinci ranan ban samu ciba don dan damuwan dana shiga najin wai akaina wani abu na shirin faruwa a family su kuma yanzu.
Ina jin su kande da lami suna hiran su wanda yawanci akan aiki dake masu yawa na yaran mamine wanan yace wanan yakeso a dafa mai wanan kuma yace baya son wanan dole sai sun kara dafawa.
Ga Nuriya matar yaya mamud da nata azzalzalan don ita din girkin daban suke mata dole don tace ba zataci na yawa ba da ake dafawa a gidan duk da haduwan shi ga dadi.
Ban tsika a zancen su ba kuma din sun san ba zan fadawa kowa wanan zancen ba a gidan.
Lamice ta kalloni tana fadin yau kan ke kamar wani abuna damun rayuwan ki gidan nan tunda safe nake ganin ki a haka.
Gida nake son komawa bakina ya furta kai tsaye gida yar nan kina nan kina rufawa kanki asiri da iyayyen ki zaki zabi zuwa kauye a yanzu.
Ke kuwa idan kinji zomo yaje kasuwa ai ba a banza bane dole saida dalili yar nan ina kula da ita akwai abinda ke cin zuciyar ta na kula matsalan nan ya kwana biyu a tsakanin ta da uwar dakin mu don yanzu dai tau Allah dai ya sauwaka.
Da gaske kande ke fadi zainabu lami ta jiyo tana fuskantata don son jin amsan da zan bata.
Taci gaba da fadin ina fatan dai ba wani abin kikai mata wanda bai dace ba har hakan ya faru ?.
Banjin hakan ne don ni dai nan hjy da kanta ta ban aikin sakawa zainabu ido sai dai ban yarda na taba fada mata komai ba yo mema zan fada tunda bangani ba.
Kallon kande nayi da mamaki lami kuma tana fadin akan me haka kande ?
Dan duban kofan kitchen din tayi kamar mai gudun wani yaji me take fadi kafin tace akan me kuwa sai mugun hali irin na wasu tunda mu masu aiki an dauke marasa galihu ma.
Sun manta su din ba rawa sukaiwa Allah da ya ba basu arzikin ba kai zai iya azurtaka a duk lokacin da yaso hakan.
Idan ba hakan ba dame wanan yan matan da hjy take kokarin hada danta dasu sukafi yar nan da Allah zai bata daulan itama sai kaga tafi dadin kallo da ma,ana.
Amma dayake shi ubangiji maiyin komai yadda yaso ne sai kaga yayo maikyau a gidan tallaka mumuna a gidan mai arziki kuma kowa a yadda ya tsunci kansa yake tawakkali ga ubagijin sa.
Amma da zaran anga tallaka yau yana kokarin tsallakewa talaucin sa yanzune zakaji an fara suka da sara akan sa duk da muma tallakawan muna da namu laifin a wani bangare don wani baya iya boye zalaman sa ga mai kudi.
Irin hakan shike kawo kaga masu arzikin suna kyamar tallakan ya shiga jikin su a dama dashi.
Saidai ba kowani tallaka ne yake zama butulu ba amma kaman wanan yar ai nata matsalan ma sai nace banga abin ki a cikin sa ba.
Waini kande tun dazun kina wanan bayanin nina kasa gane inda zanceki ya dosa tun dazun.
Cikin kashe murya ta dan duka tana fadin kinsan dan hjy ya turburewa uwarshi sai yar nan ita kuma uwar tace basu dace ba da wanan.
Cikin kashe murya lami tace wa ke nan a cikin su wanan dai dake zaune a turai dayazo shike da wanan maganan.
Ita hjyn da kanta yo ai idan ya samu yarnan yayi dace a rayuwan shi wanan son kowa kin wanda ya rasa ai itace daidai da irin su yarinya kin shigo birni a sa, a.
Saidai abinne kan da kamar wuya don masu kudin nan sai kansu suka sani sai yar wani da wance iyasu, , , ,
Ke mekike anan hjy nacan tana neman ki a daki ta aikeki kin dawo nan kin zauna Aisha ta fada a tsiwace.
Zeey din nan kin soma canza halin ki don kinga kamar kowa daidai yake dake yanzu ko ?
Mikewa nayi ina fadin ba zaunawa nayi ba aiki nake kama masu a nan tunda ban komai a ciki.
Kurban lemon dake hannun ta tayi tare da dan watsa min harara take fadin ni dan Allah wuce mu tafi mami ma tana kiran ki a ciki .
Da sauri nakarasa dakin wurin hjy na samu mami kamar suna magana na gaidasu lokacin Aisha ta shigo dakin mami ke fadin tana ina tundazun.
A kitchen na sameta zaune dasu kande suna hira da sauri na dago ina fadin ba hira mukeyi ba aiki muke tare.
Waya sakaki aiki hjy ta tambaya hjy aikin ne harsai an sakata yi nina bata umurni ta dinga zuwa idan bata zuwa school suna aikin a tare.
Tafada tare da fadin ke ina kudin dana aje dazun a daki gaba daya suka sako min ido don jin abinda zan fada a lokacin.
Kudi nace a cikin mamaki eh kudi dana zube saman gado dazun dana shigo wurin hjy da safe .
Da sauri na dago kai ina fadin sunan a dakin mami da zan canza zanin gado na saka maki cikin wardrobe.
Jeki ki kwaso min mami ta fada na juya da sauri don in dauko naji hjy na fadin na fada maki ba halin yar nan bane kada ki soma zargin ta da haka.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[25/12, 14:51] +227 98 36 59 34: 🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
3️⃣2️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ASSALAMU ALAIKUM WAHAMATULLAH YAR UWA BARKA DA WARHAKA FATAN ALHERI GAREKU YAN UWA MUSULMAI UBANGIJI YA TAIMAKI MUSULMI A DUK INDA YAKE AMIN, , , ,
LITTAFIN DAI NA SAYARWANE DON ALLAHU MU SAHILEWA JUNA DANI DAKE KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA DON KI SANI NA FADA IN FITAR DA HAKKIN HAKA GAREKI, , ,
Gaba na faduwa na nufi wurin kayan saidai ganin yadda na gyara komai ba haka na samesu ba yasa faduwan gaban nawa tsananta sosai.
Kaf na bincike kayan basa wajen haka ya kara tayar min da hankali muryan mami ne naji tana kwalla min kira dakin hjy yasa na fito ba tare dana gama bincika ba.
Ina shiga dakin da sallama a daidai lokacin da nake fadin mami gani ita kuma take fadin fadin ina kudin tare da kallona.
Na duba inda na aje ban gansuba mami na fada a dan firgice don a rude nake lokacin dan rashin ganin kudin da banyi ba.
Kamar ya baki gani ba dazun nan fa da zan fita na barsu saman gado dama na fitarne akai lami kasuwa ta sayo cefane.
Mami basa nan inda na aje asalima kayan ba,a jere suke ba yadda na barsu wani ya taba wurin kayan.
Wa kike nufin zai shiga dakin mami ya taba wani abu a gidan nan baya ke saiko mami din dake da dakinta.
Ni ai tasan ko kaya zan dauka itace mai miko min ban damu da daukan wani abuba ciki ba.
May ta canza haline ta fara dan hali yanzu tunda taga kudin kamar banza a gidan Aisha ta fada a cikin wani irin yanayi tana dukar da kanta kan wayan ta.
Wallahi mami ban dauka ba a nan na saka yanzu kuma ban samesu wurin ba an canza masu wuri.
Ke zeey kada ki kawo min rainin hankali wani yarona kikaga ya shiga dakina balle ya kai har cikin wardrobe dina bayan ke ?
Haba haba yar nan yau kuke da ita a gidan nan meya kawo wanan zance haka babu dadin ji sam wanan zance bai dace ba ai haba dai ku dinga tunane kafin ku furta magana man.
Wanan tsohuwar haka kike fa ga magana ta gaskiya zaki daurewa karya gindi ke hjyn nan sai sakawa mutane baki ga zance baki san abinda ke faruwa ba.
Ke yar nan nizaki kawowa diban albarka yan zamani dubani da kyau banyi kama da tsofin banza ba da jika zai iya kawowa rainin wayau yan zamani.
Ko uwarki kyaleta nayi take min yadda takeso a gidanta nazo kinga ko a karkashinta nake yanzu.
Idan bashi ba ita ta sanni sarai tasan binta nake kafin in kai ga juya mata baya ga duk iya shigen da kuke zubawa a gidan nan.
Hjy kiyi hakkuri Aisha wani lokaci haka take abindaba wasa ba sai ta mayar dashi abin wasa a wurin ta.
Iyami wanan ne zancen wasa kina zaune tana kokarin dorawa yar mutane halin daba nata ba yau yar nan take gidan nan tare daku.
Ada can batai maku haka ba sai yanzu ne zaku dora mata halinda ba nataba don kawai a bata mata suna .
Shin ko kin mata ne da wanan watarana itama wani gidan zata idan an wa yarki wanan sherin yaya zakiji a zuciyar ki ko ince yaya zamuji a zukatan mu.
Yar nan amana take a wurin mu da duk kowa naki don karbota akayi a hannun iyayyen ta Allah ma,aiki yanzu kuma a binta da wanan barnan sunan haka.
Kuka nake wiwi mara sauti don hawaye ke tsiyaya a idona ina maijin dacin satan da mami da yarta ke kokarin dora min.
Nagodewa Allah nagodewa wanan tsohuwar datayi min tsaye ta hana kowa ci gaba da abinda ake shirin min don dai na fahinci kamar sheri ake kokarin min a gidan kan kudin.
Muryan mami ne ya katse min tunanena tana fadin hjy bafa wani abu bane kudin ne kawai akeson sanin ina ta zubasu don a kiramin lami su tafi kasuwan wanan kuma ta tsaya nata shirmen.
Jeki ki kara dubawa da kyau ko ina a dakin ko kin manta da inda kika sakane.
Na amsa da to da sauri na barsu a dakin na nufi dakin mami ko ina nake dubawa banga kudin ba na rasa yadda zanyi in fadawa mami ban gani ba a dakin ko ina na duba babu kudin a inda na ajesu.
Da kuka na dawo dakin daga kofa na dan tsaya ina fadin mami bangani ba na duba a wurin gaba daya kayan basa wurin.
Jeki Allah ya sauwaka ta fada a cikin wani daure fuska tare da fadin jeki ki kiramin lami a kitchen a bata wani kudin tunda wacan kan an kwashe ke nan sai dai ba zan kara lamintan hakan ba gaskiya.
Allah ya kyauta hjy ta fada tare da fadin nidai nasan ba yar nan ta dauki kudin nan ba tunda ba yau take daku a gidan nan ba komai bai taba faruwa ba irin haka.
Idan da yarnan tana dauke dauke da tuni ansan da hakan kadafa a maidani tsofuwar banza don nagane abinda ake kokarin kullawa yar nan kuma ba zan taba yarda haka ya faru ba.
So ai da laifine, laifin namu ya kamata mu gani domin shine ya nuna yana sonta ba wai yarinyarce ta nuna tana son shi ba balle mu dauki laifi mu dorawa yar mutane ga banza.
Don haka iyami ina shawartan ki ki dauki yar nan ki maida ita hannun iyayyenta tun kan shedan ya zugaki ki aikata abinda ba daidai ba.
Amma idan har yar nan tana zaune gidan nan tare daku kuna kokarin dora mata laifin daba nata ba.
Hjy nima naso hakan tun farko saidai ina tunanen maganan ki kan yaron nan kada ta koma gaban iyayyenta ya bita can ba tare da sanina ba wani abu yazo ya faru a tsakanin su.
Ko tana nan a gaban ki idan Allah ya nufa akwai aure a tsakanin ku sai angi iyami.
Kada ki manta a kullun ina tuna maki baya ki daure yadda Allah ya turo yarinyar nan a karkashin ku har danki yaganta ya nuna yana ra,ayin ta.
Shin me zai hana ki daina hattaran yar nan ki sanya ido ga danki shida ke faman bibiyar rayuwar mutane haka.
Ita metayi za aga laifinta waya take masa ko binshi takeyi, ko kulashi take tana bibiyan shi inda duk ya saka kafa ?
Daki iyami shike wa yarinyar nan duk wanan abinda na lissafo maki a gidan nan kullun yar nan a tashin hankali take gidan nan .
Don haka ina gargadin ki karo na karshe da ki takawa danki burki ya rabu da yar mutane tunda dai baki aminta da wanan abin ba.
Don iyayyen yarinyar nan suna can suna fadin kina nan kin rike amanan yarsu da hannu bibiyu basu san ba haka ba yarsu na nan cikin ukubar ki don kawai danki yace yana ra,ayin ta.
Hjy kin san halin dan yau shi jafar na rasa gane kansa kan wanan abinda yanace sai zeey ni fa bawai niki zeey din nan bane don ina kyamarta ko wani abu.
A, a ba hakana bane zabin nasane ni sam bai kwanta mun raiba don idan har ilimi ko kyau ko wayewa ko arziki yaron nan nasan duk zai iya samo macen data tara wanan abin gaba daya da kansa.
Amma wai hjy sai ace yau yaron nan ya kafe shi sai zeey a cikin kasan nan abinnne da ban haushi da ban mamaki don yi iya tunane na rasa gane dalilin shi na wanan kafiyan tsiyar ta kare tare da jan tsuki mai nuna takaici.
Koda ta dago kai sai duk ta tsargu da irin kallon da hjy kemata don haka ta dukar da kanta.
Mikewa tayi don barin dakin iyami hjy ta kira ta fuska a daure cikin murya mai kaushi mami ta amsa da na,am hjy cikin girmamawa.
Tace wai me yake damun ki ne iyami zaman turai fa ba hauka bane mami tayi shiru tana sauraren yar uwan nata.
Hjy ta sake daga murya cikin bacin rai tana fadin kul naji wanan maganan batar kudin nan ya karde gidan nan har yawuce iyamu nan rayuka zasu baci fiye da tsamani.
Don ina da tabbacin yarinyar nan bata taba maki komai naki a gidan nan don da tana tabawa da tuni an gama gane ta.
A, a hjy aini na gama maganan don ya, , , , sallaman lamine a kofan yasa su yin shiru gabaki dayan su tace lami muje falo in baki sakon a can.
Na dade a inda nake ina hawaye saida naga mami ta koma daki sun gama da lami naja kafata da yai min nauyi zuwa dakin namu.
Ina shiga tsohuwar ke fadin kina ina tun dazun acikin yanayin damuwa na iya budan bakina da kyar ina fadin waje na zauna.
Kinga sake ranki idan kin so nasan bazaki taba wanan halin banzan daba a sanki dashi ba tun farko.
Hawaye masu dumi naji sun fara saukomin a idanu hjy ta nuna min matukar tausayawan ta gareni tana ta bani hakkuri.
Hakan daya farune yasa ranan gaba daya na wuni sukuku dani a gidan ban ko leka falo ba ina kwance a daki zazzabi yana neman rufeni sosai.
Panadol hjy taban nasha sai barci koda mami tasa murya ta kirani sai hjyn ce ta amsa tana fadin banjin dadin jikina na kwanta.
Kamar mami zatayi magana sai kuma tayi shiru don tasan idan tayima yanzu hjy zata kareni gareta ne.
Karfe takwas ya kira wayan ina barci ba wanda ya daga wayan har saida y kara kiran hjy ta dauka zuwa falo don wani ya karba min .
Aisha ce da hjy zaune saman doguwar kujera suna zaune sama a guri daya ta mika mata wayan tana fadi karba min wanan wayan don Allah yar nan tasha magani ta kara kwanci.
Wayar waye wanan ta fada tana karban wayan a hannun hjy din mami ta dan juyo ta kalli wayan tare da kawar da kanta gefe.
Receive din wayan tasa tare da kara wayan a kunnen ta sweety rowan daukan wayan ma kike min kuma tun dazun ina kira ba a daga ba .
Ehhy, , , ya J to ba ita bace yace Aisha yah kuna lafiya lafiya ya mami na kira bata daga ba gata nan tana kokarin karawa mami wayan a kunnen ta.
Don't dear touch me with dis dirty phone mami ta fada a dan hasale Aisha sorry mami a dan shagwabe.
Ta mayar da wayan a kunnen ta yace bar mami nasan akan yaran nan marasa tarbiya take fushi dani haka.
Where is my baby girl ya fada cikin katse Aisha din tace who ya J ?
Yace the owner of the phone wai wanan stupid girl din zeey tana daki tana fushin banza after she steel mami money .
What, ya fada dan karfi kamar a fili yake kusa dasu ba a waya ba yace it can't.
Wani irin wasane wanan da sata kuma satan kuma na kudi hjy dake gefe tana fadin kai amma keko an daiyi yarinyar kawai a gurin nan.
Ban wayan mara mutunci ina saidana gargade uwarki kar zancen nan ya fita har yakai kunnen yaron nan.
Hjy why are you always abusing me bata dauki kudin nan bane ko me kina wani kareta can mami dake daga gefenta take wani tunane yazo mata lokaci guda.
Take fadin Aisha meyasa kika fara yawan surutu ne yanzu sai kuma ta juya harshe a cikin turanci tana fadin kinsan hjy akwai tsufa a tare da ita ki daina biye mata kuna haka mana bana jin dadi haka nima lalaba abina nake ta karasa fadi ki bata hakkuri please.
Hjy yi hakkuri bansan kin fadi haka ba ai ta fada a cikin fushi hjy da ranta ya gama baci take fadin yanzu ai kanku ake ji yar nan .
Duk abinda ake waya a kunne take har lokacin a hannun hjy data fisge gun Aisha yana sauraren duk abinda ke faruwa lokacin.
Idanun shi ya runtse a cikin takaici da bacin rai why mami zata tsani yar mutane haka har su dora mata mugun tabo mai zafi hakan nan.
Ga kalman da baffan shi ya fada dazun cewa don zeey ya kama masu yara yai masu wullakanci don kawai yana takama shi mai arzikine ko yafi kowane yake gani.
Ya dade a zaune inda yake duk da dare ya soma sai yaji sam ba zai iya kwana bai fadawa wani daga cikin mutanen nan wanda baida wani aboki ko shakiki da sukafi mai yanuwan shi na jini.
Baida aboki ko wani amini a kasan daya wuce mai yan uwan haihuwan shi kasancewan shi wanda bai tashi a kasan shi na ainihi ba Nageria.
Haka yasa komai da zaiyi anan ya mamud ne mutum na farko da yake nema ga shawaran shi kamar yadda shima ya mamud din bai wasa da lamarin kanin sa don yana masa biyayya yadda ya dace ga kyautatawa ko yaushe a tsakanin su.
Sai kuma yan kannen shi biyu jamal da jalal sumafi dinkewa da jamal don halin su da yazo kusan daya sosai.
Bayan su akwai Bukar dan kanin mahaifinsu wanda kusan akwai dan shakuwa sosai shima don zai iya cewa shine mutum na farko ds ya yarda dashi bayan yan uwan nasa.
Don tun suna yara bukar din yake nuna ra,ayin shi akansu har wanan lokacin da suka kai hakan bai daina kula dan uwan nasa ba duk da yasan shi din mutum ne da baida saurin sabo lokaci daya.
Ya mamud dake shirin kwanciya tare da matarshi Nuriya yajo kiran dan uwan nasa ya shigo mai don yasa ba halin shi bane kira a cikin dare.
Furta suna shi da yayi ne yasa Nuriya dake gefen shi dan dagowa da sauri tana kallon shi da mamaki don ita a nata rayuwan ta tsani duk wani dan uwa mijin nata.
Tundai shi da take ganin yafi mijinta da komai a rayuwa kamar mijin nata, yana son mayar da kanshi a karkashin shi yanzu wanda ita kuma irun matan nan ne da basu son hakan.
Jafar ya akayine ya mamud ya fada lokacin daya dauki kiran na dan uwannasa normal ya fada saidai ina so zuwa safe ka bincika min meke faruwa a gidan nan don Aisha was telling that that girl ta saci kudin mami wanda nasan sheri ne wanan suke kokarin mata.
What sata kuma ya mamud ya fada da dan karfi wanda hakan yasa Nuriya dago kai ta dan kalleshi cikin mamaki don jin abinda ya fada.
No nima nasan da hakan wanan yarinyar ba zata taba haka ba jafar saidai idan wani sheri kuma ake kokari kulla mata yanzu which is bad .
Yanzu dare yayi sun rufe muma nan muna shirin kwanciyane da safe zan binciki hjy in fara jin abindaya faru.
Ya samu ya lalaba dan uwan nasa suka kashe wayan Nuriya take fadin wanan yarinyar ce tayi sata kowa ?
Ba sata ba kan yau take gidan nan tare dasu wani dai abinne kila yake faruwa a tsakanin su har haka ya faru.
Dama nasan haka zaka fada don har kai ina zargi akan wanan yarinyar da farko don kawai dan uwanka ya rigaka furta mata sone kaima nasan da hakan zakayi.
Da mamaki ya dago yana kallon ta tace eh na sani don yarinyar macijiyace babu namijin da zai ganta farat daya baiji yana sonta ba sai dai bakin tabo ya yanke mata kadari ai.
Don warin talauci da yake binta ita din kaskantatace a idon kowa don bakin talaucin iyayyenta har kasa riketa sukayi suka turota aikatau a birni.
What noses talking kike fada haka me yarinyar nan tayi maki haka wai kika tsaneta kema ina yanzu kika gama fadar dan uwana ke sonta da bakin ki .
Bazan taba lamunta hakan ba yarinyar nan abin tausayine bata da matsala da kowa a gidan nan ki duba yadda take kula yaran nan tankar ciki daya suka fito dasu duk da tasan ke baki son hakan da takeyi masu din.
Bai bata wani kafa da zata fadi wani abuba akai dole tayi shiru ba don taso ba ta kyale zancen a ranta.
Washegari na tashi da zazzabi mai karfi wanda har ya tayar da hankalin hjy a dakin ta nufi gurin mami tana fadin yar nan fa iyami zancen nan har zazzabi ya saukar mata jiya bamuyi barci da dadi ba.
Budan bakin mami sai cewa tayi wanan kuma ai matsalantane tunda nida taiwa laifin ban dauki wani mataki ba a kai balle ta zauna tanawa mutane ciwon banza a gida.
Anya ! Iyami kina da tausayi yanzu kuwa hjy abinne da ban haushi tun jiya nake ganin take taken yarinyar nan ita a dole gata mai zuciya ko.
Mikewa mami tayi ta ballo magani tana fadin ta sha wanan zai sauka idan na fito zan shigo in dubata.
Hjy dai ta karbo maganin cikin sanyin jiki dajin kuna a ranta yadda gaba daya yar nata ta sauya akidarta ga baki daya har yakai tsohuwar tana zargi a ranta kodai wani abu ya shiga kan mami din ne.
Nasha magani cikin ikon Allah naji daman jikin nawa gashi ina son zuwa inyi aikina a daki mami kuma ina jin tsoron shiga dakin yanzu.
Babu yadda na iya haka yasa na sauko daga kan gadon a hankali na dan zauna a bakin gado hjy data fitowa ban daki ta dauro alwala ta ganni a zaune take fadin.
Alhamdullahi sauki ya samu ke nan nace eh hjy ya fada min ina kokari tashi tsaye take fadin ina kuma zaki tafi yanzu.
Zan tafi in gyarawa mami dakine na bata amsa koma ki kwanta babu inda zaki yanzu kina jin jikin nan yarta ta gyara mata idan ta matsu.
Ban iya furta komai ba dole na koma na kwanta don bazan iya mussawa tsohuwar ba don nasan wanan tsakanin sune da mami kuma don nasan baida wuya hakan ya zama wani matsala kuma.
Kara rufa nayi har barci ya soma daukata naji hjy na fadin in tashi in kara karyawa kafin barci ya daukeki.
Zan tashi na fada ina gyara kwanciyana ya mamud yayi sallama a dakin ta amsa mashi suka gaisa ya samu wuri ya zauna.
Ina daga kwance ina jin hiran su a cikin ba, a kafin yace wanan da take rufe haka meya sameta ne kuma ?
Zazzabi ke damunta tunjiya gata nan a kwance yace subbahanallahi shine ba a kaita asibiti ba take kwance a gida haka.
Uwarku ta bata magani shine ta dan samu saukin nan Allah ya kara sauki ya fada kafin yace jiya da dare jafar ya kirani yake fada min wani zance mara dadin ji wai Aisha ta fada mai yarinyar nan ta satarwa mami kudi yaya zancen yakene hajiya ?
Dama nasan za a rina saidana gargadi uwarku kan zancen nan amma ta bari zancen nan yakai kunnen yaron nan.
Nawane kudin yaya jafar ya tambaya zaka biya mata ne mami ke fada daga kofan No mami ba wai zan biya bane kawai dai tambaya nakeyi don in sani.
Ka koma ka fadawa wanda ya aikoka cewa dubu dari ukune ina jiran inji alernt ta fada a cikin gatse ta juya inda nake kwance ina hawaye tana fadin ke zeey jikin bai saki bane ki gyaro min daki ni fita zanyi.
Nice nan na hanata zuwa don kowa yasan da ciwo a dakin shi ai don haka sai idan taji sauki.
ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
ZAINAB IDRIS MAKAWA
3️⃣3️⃣
BARKA DA WARHAKA YAR UWA UBANGIJI YA BAMU WUNI LAFIYA AMIN.
Tana tafe a fusace don ranta daya riga ya baci da yaranta a dakin hjy data shiga sallama da ita ta samu ya mamud suna zancen da hjynta ta ballashi ta fito da fushi ranta a bace cike da tunane.
Tun kan ta iso bakin motan security din ta suka mike tsaye tare da bude motar suna jiran isowan ta wurin.
Tsayawa tayi gaisawa da masu gadi da wanki da mai kulla da komai dake gudana a gidan massege ne yashigo wayan ta tayi niyar shiga mota ta diba sai kuma ta dakata a yadda take tsaye.
Kafatan daya na a motan yayin da dayan kafan nata yake waje ta dafa motan ta bude sakon da mamakin ko sakon meye ya shigo mata a wanan lokaci.
What ta fada da dan karfi, bayan ta karanta sakon dake a fuskan wayan nata a fusace ta juya zuwa cikin gidan tana shiga a kofa suka hadu da ya mamud.
Gaba daya yanayin fuskanta duk ya sauya ranta ya gama baci tanajin zuciyan ta bakikirin a lokacin.
Wani sakon ne ya sake shigowa a lokacin a hasale take duba sakon take idon ta ya kara kankancewa ga baki daya.
Mamud da suka hadu a lokacin ganin yanayinta mami lafiya ya ya fada a dan razane ?
Wani kallo tayi mai kafinta ce biyoni muje ciki kawai ta fada tana gaba yana biye da ita a baya.
Dakin namu suka shiga wurin hjy da sallama cikin wani irin yanayi hjy dake zaune take fadin lafiya dai ko iyami ?
Hjy yaron nan me yake nufine, me yake tunanen ya taka da har zai rainani ko ince su rainani.
Wai me ke faruwane haka iyami ya mamud daya karasa shigowa yake fadin .
Wai mami wani abune kuma akayi yanzu rufa min baki ta fada a cikin tsawa wallahi ka zama babban banza a gurin kannen ka mamud.
Wani kallon mamaki ya jefowa uwar don baisan dalilin wanan fada ba a sanyayye ya furta a cikin mamaki mami ni kuma me nayi yanzu kuma ?
Hjy wai ki duba yaron nan dan baida wayau kullun shi dan maganan nan danayi yanzun nan yaron nan ya kwashe ya fadawa dan uwansa.
Wai sai gashi jafar ya turo min kudi masu yawa haka har yana fada min ga kudin aikina nan tun lokacin dana dauko zainab a gidan ya biya.
Shike nan ta faru ta kare dan nan ya fashi yarinyar nan a gidan nan yanzun kuma sai ki samo wata.
Hjy me kike fada haka kuma sanda na dauko yarinyar nan nayi shawara da shine ko yasan su waye iyayyen ta?
Wallahi wallahi mami ga hjy nan idan nayi magana da Jafar a yanzu kan na fita dakin nan wurin ta ya mamud ya fada rai bace hankali a tashe.
Hjy tayi wani shu,umin murmushi a fuskanta kafin takai zaune cikin tagumi tana karkada kafan ta a cikin mamaki.
Hannu takai ta cire glass din dake sanye a idon ta na fadin ni jafar zai nunawa yanzu wuyan shi ya isa yanka.
Har zai turo min miliyoyin kudi waishi a dole ya fanshi zeey a hannu na to dashi da kudin nasa duk sun, , , , ,
Kai kai kai iyami karki soma furta wani zance mara dadi ga danki dan yau ne fa ke kuma uwar zamani kinga kuna kamanceceniya a wurin hali.
Ba yadda banyi dake ba a gidan nan tun kan zancen nan ya kainan na baki shawara da ki zuba masu ido ki kyalesu suyi soyayyan su.
Wasan gobe banda Allah iyami Allah kadai yasan meya tsara ga hakan kince ba hakan ba kin tsaya kina jayayya da hukuncin ubangiji.
Iyami ina ji maki tsoron irin abinda zaije ya dawo baya a kan wanan jayayyan da kikeyi a yanzu.
Yaron nan idan dai ba alhakinshi zaki dauka ba a banza wallahi baiyi waya da dan uwansa ba a dakin nan yanzun nan ya fita.
Hjy dan Allah bari lokacin da zai aikata hakan kina ina zai iya tura mai sako.
Mami baki yarda da rantsuwana ba kenan ya fada a dan mairaice yana maijin wani iri a ransa ba dadi duk yana jin mami ta muzantashi a lokacin.
Ya dubi mami fuska a daure yana fadin ki kira jafar din yanzu aji wanda ya fada mai don ni wanan abin gaba daya mami kin jefani a cikin zargi .
Idan bakai bane waye ko yarinyar nan ne zeey gata kuma a kwance tun dazun sai dai idan daga kwancen ta kulla wanan sherin ba abin mamaki bane kuma.
Haba mami ji wanan don Allah bai dace ba meye laifin yarinyar nan a yanzu kuma don Allah ?
Kai ke na ka fadamai saka fito fili kafada sukaji muryan Jafar na fadin hi bro ya akayi ne ka fito ke nan naji duk abinda mami ke fadi a waya dazun so na tura mata da kudin sai tai set din yarinyar free by now.
A samo wata daga yau ta dinga wanan aiki ita kuma tayi facing din karatun ta final.
Eehhee mara kunya beran tankwa nayi shawara da kaine da zan karbo ta yaji muryan mami tana fada a cikin tsawa.
No mami bakiyi ba saidai tunda abin har yakai wanan irin zargin yana shiga tsakanin ku let her set free by now tayi karatunta kawai.
Mami yanzun kin daina zargina a wanan zancen me zaisa na fadawa jafar wanan magana tunda nasan a cikin fushi kika fade shi.
Ni kuma ba zan so inga wani abu na tashi hankali haka ya faruwa a tsakanin kuba ko yaushe Jafar fa dankine mami.
Yau yace ga abinda yake so a rayuwan shi mami ya kamata ki sasauta zuciyan ki don in kin kula jafar yayi nisa a wanan zan, , , ,
Kaga dai yanzu na gane yadda zancen yake don haka katafi kawai kada ka makara a wurin aikin ka ta fada kuma a dan hasale.
Toh mami na gode ni zan tafi ya fada yana mikewa daga bakin gadon da ya zauna da farko a gigice.
Yama manta a kusa dani ya kai zaune a lokavin don haka bai kara waigowa ba ya fice daga dakin.
Idona biyu duk zancen da sukeyi yana a kunne na ina sauraren su ban yarda na motsa ko kadan ba don kar mami ta gane a falke nake duk da bana tantama da tasan a falke din nake a lokacin.
Mami naji ta mike tsaye tana fadin ni zan tafi hjy sai dai idan na dawo shi kuma ai zai dawo gidan nan zamu hadu dashine ai ni zai nunawa kudi har yaushe yai kudin nasa shi .
Ko yau din nan yayi dai ya wuce raini a garesa da kayan sa hjy ta bata amsa murmushin karfin hali mami ta sauke a fuskan nata ta fice daga dakin.
Nasan idon ki biyu yar nan bayan wuya sai dadi insha Allahu wata rana idan an daure sai labari.
Dagowa nayi ido shabe shabe da hawayen wahala ga ciwo ga tashin hankali a lokaci daya ya dameni.
Don ranan gaba daya wanan zancen ya hanani shakat a rayuwana don ko makarantar ban samu zuwa ba a ranan ke nan.
Kamar yadda hjy ta fada na mike tsaye da kyat na nufi bandaki ruwan zafin dana samu a heater na kunna ya dan taru na wasa a jikina.
Na fito na shirya a cikin wani blue din dongon rigan English wear mai adon stonen fari a gaban shi.
Fuskana ya koma fayau a dan lokaci guda bana jin karfin jikina ko kadan zama nagi gaban abincin karyawan dake gaban hjy na zuba ido .
Kici abincin mana ta fada a daidai lokacin na dago fuskana dake zubo hawayen dana kasa tare su a lokacin.
A bazata naji muryan hjy na fadin ki daina kuka nima wanan abin ya fara firgitani a gidan nan ki shiya kayan ki kaf zuwa gobe ki koma gaban iyayyen ki kowa ya huta.
Kada azo matsalan yazo yafi wanan abu ya taru ya rikice a lokaci guda ta yadda ba za a iya gyaran sa ba har idan kina da rana a gareta zata gani nan gaba.
Shi kuma ya tafi ya nemi wace uwarshi ke son ya aura din mu gani yanzu kici abinci ba a ciwo da rashin ci ko kadan ne.
Hakana na daure ba don ina so ba na tsakuri a bincin zuciyana yana cike da damuwa kala kala don a gaskiya naso duk wani cin fuskan su mami gareni in daure in karbi kwalin karatuna.
In yaso daga baya in nuna ni gida nake bukatan komawa gaban iyayyena yafi mun kwanciyan hankali.
Sai dai a yanzu kan banda sauran zabi fiye da barin gidan mami din gara in hakkura da karatun nan tunda abin har yakai ga dafa min sata abinda ban taba yi ba a rayuwana.
Gobe kafarki kafata a garin nan ba zan haifi da da cikina in zauna dashi ba tare da yaji magana ta ba duk ko abinda yazama.
Nabi iyami a sannu ne inga iya gudun ta gareni saida har yanzu shedan yayi shimfida a zuciyar ta ita bata bi magana ta ba ta yaya yayan ta take son subi nata don wani manufa nata can na daban.
Idan anyi magana ta farawa mutane kame kame akan zancen ta mata ita ba haka muka dorata ba ina mahaifin yaran nan da halin shi ta aure shi lokacin shima ba matsiyaci ta sameshi ba ba a cin arziki taci ita a rayuwanta.
Hjy ce ke fadan wanan maganan a cikin bacin rai ban yarda na tsuka mata ba sai faman tunanen da nake a cikin raina a lokacin.
Mikewa tayi don yin sallah walha haka ya ban daman gyara kayana kamar yadda ta umurce ni inyi har ta idan a daidai lokacin dana gama komai duk da yar jakar kayan da aka ban bai isheni hada yan tsumakarana ba don yanzu Alhamdullahi ina da yan waddatatun kayan da Aisha dashi jafar din suka waddatar dani dasu.
Falo ta tursasa min da mu fito ko jikin nawa zai kara ake min a kwance nake na dunkule saman kujera a daidai lokacin da mukaji takon tafiyan mutum yana shigowa falon mami din.
Ban dago kaina don ganin kowaye ba a lokacin ina kwance a yadda nake.
Muryanta ne ya sheda min da Nuriya ce matar ya mamud tana gaida hjy dake zaune saman kujera ban dago don gaishe ta ba don kowa na gidan ina kallon shi a makiyina.
Idan ka debe mazan gidan gaba dayan su da suke nuna min iya kulawan su idan sun shigo.
Tsiyata da dan kauye gadara ke me kika taka da bazaki gaida mutane ba dadin abin dai dan halin bera ke ga mutum bai gani ya kauda idon sa saiya dauka.
To ai sai ya gani yake dauka ko wani ko ai ko bai gani ba dauka yakeyi don abin yanzu ba sai dan kauye ba don har wanda baka zata ba sai kaji ya yaudari mutane mutanen ma mijin shi na sunna don kawai ya tara ya kaiwa tsofin sa gida.
Hjy kina nufin dani kike wanan zancen au kema da wani ke zancen ke nan ke kalleni da kyau banyi maki kama da tsofin banza ba da zaki kawo wa diban albarka ba.
Kin taba aje abu a gidan nan ta daukar maki ko wani naki ko dan gidan abinsa ya taba bata toyo dama shi ya kawo ki shiyan nan takalan magana ko me ?
Girman mahaukaci karamin mai wayau sai ya fishi ke abinda kikeyi a gidan nan ai ko kare baya ja .
Mayafi kayan dake jikin ta ta cire ta mayar a kafadan ta taja wani uban tsuki tare da fadin hjy tsohuwa ba mamaki dai kema an gama dake gun malam na kauye yanzu.
Idan bashi ba yanzu dai magana ta nake a wurin nan ba tare da ambatar sunan kowa ba shine har kike kokarin bata min suna haka ?
Bari shi mamud di ya dawo da uwarsa Inji wanda ya fada maki haka a cikin su don ba zan taba lamuntan wanan zancen ya tafi a banza ba gidan nan.
Allah dai ya dawo dasu din lafiya hjy tace tana nuna bajin tsoro a cikin zancen ta ko kadan tafito mata hjy zainabu Abun tana asali.
Wanan abin ya kara saukar min da hawayen bakin ciki masu dumi da kunan zuciya a lokaci guda sai me kuma ?
Ba hjy sai ta juyo gareni a zafafe ta hauni da fada a cikin takaici tana fadin ke yar da wanan bakin kukan naki dayaki ci yaki cinyewa gareki.
Wa yan nan ba mutuncine dasu ba zai ruwan jikin ki ya kare a banza basu san kina yi ba maza ki gyagije ki shiga tsabganki hankali kwance kamar Allah ya aiko ki.
Shi ai sheri ga dan wani takine babba ga wanda yayi shi ni dai nasan harga Allah ba shedun zurba baki daukan masu kwandala a gidan nan ba in har sun yayada wanan zancen haka suyiwa kansu sheri don min sai ya tambaye su.
Hjy nikan na yafe masu kada Allah ya jarabi kowa a cikin su da wanan abinda nake ji a yanzu don akwai zafi da ciwo a zuciya.
Kaji ya mai hankali nima bawai ina nufin hakan ya samesu bane ai ina dai fadin yadda abin yake ne don idan sheri ko hairan ka kuddurata wa dan uwan ka sai kwantankwancin hakan ya sameka kaima.
Kiran sallah azahar ya tayar damu a gurin sallah muka idar a daidai lokacin da lami ta shigo dauke da kayan abincin hjy dakin na gaida ita da aiki.
Take fadin yar hjy ance yau bakiji dadin jikin naki ba Allah ya karo sauki na amsa da amin kawai don yanayina babu dadi cikin sa ko kadan a lokacin.
Fitar lami dakin yayi daidai da shigowan shi da sallama a dakin kamar daga sama muka ganshi ya fado dakin a wanan lokacin.
Jafari ka dawone ashe yau zaka dawo garin hjy dake zaune saman sallaya tana jan tasbaha ta fada a cikin fara, a da kulawa.
Eh mun dawo hjy mun sameku lafiya ya gida ya tsufa da jinya ya fada fuskan shi a kaina na dukar da kaina gabana na faduwa tunda yayi sallama dakin kamar an aiko min da mutuwa nakeji.
Ya jikin naki ya fada a lokacin daya karaso yana zama a kujera kusa da inda nake zaune daga ni sai ni don na nade hijjabin danayi sallah.
Dagani sai dogon rigan dake jikina a lokacin sai duk na tsargu da kaina don ban so ya sameni hakan ba a daki.
Sannu da dawowa ya na fada can ciki ciki ya kara fadin ya jikin kunje asibitin hjy ya fada yana kallon hjy din don son jin abinda zata fada.
Asibiti ai sai yan gata ita ina taga gatan da iyami zata kaita asibiti yanzu tunda kajawa yar bakin jini ga kowa a gidan nan wai ace wanan zancen yakai har ga kunnen matar mamuda a gidan nan.
Zata zo ta nemi karawa mutane zafi akai ina fama da uwarku sai gata dazun gabanin azahar din nan wai tazo yiwa yar fade tayiwa uwarku sata a gabana don yarinyar nan bata data ido a gabana fa jafari don iyami ta mayar da yarinyar nan sabban gida yanzu.
Murmushin takaici kawai ya sake a fuskan shi tare da mikewa tsaye lokaci guda yana fadin zan shiga ciki hjy in watsa ruwa.
Naso hjy ta barshi ys fice a lokacin amma sai gashi tana ta janshi da fira daga tsayen da yake yana amsa mata da eh ko a, a da kuma Allah sarki.
Har ya samu ya fita bansan lokacin dana sauke wani irin gwarou nufashi da har ya fito fili ba a lokacin.
Ki daina tsoron shi kwana nawa ne kun zama daya yar nan ki duba saboda ke ya bar abinda yakeyi ya dawo garin nan yanzu bana ko tantama donke ya dawo a wanan lokaci.
Hjy don ni kuma na fada a cikin yar murya da mutum zai dauka a shagwabe nake magana na tace.
Don ke mana yar nan ya kamata ki fara nuna mashi yadda ake nuna mai yadda yake nuna maki kulawa haka nan.
Munci abincin na kwashe kaya don mayarwa kitchen din a can su kande suka tsareni da tambayan meya hada hjy tsohuwa da matar mamud dazun ?
Ke fadin ina barci ban san meya hadasu ba mama bata da kunya bata data ido sam wanan yar kowa sai kokarin takashi take a gidan nan haka take muna sai bayan mun karasa hada mata abinci tasa a dawo muna dashi wai baiyi ba.
Nidai ban tofa ba na bar kitchen din ina jin daci da kunci a tare dani dakin na dawo na kwanta a gefen hjy don jinta nake kamar kakata data haifeni da kanta.
A dakin shi bayan ya fito daga wanka yayi sallah har la,asar yakai zaune a inda yake bai daga daga kasan ba sai murzan kai da goshin shi da yake yana ji yanayin da yake wani iri.
Baison yayi komai a lokacin don yana jiran dawowan mami ne a lokacin yasan zasu hau sama da ita a yadda ta hasala dashi din a waya.
Don kawai yace ta yi set din yarinyar free shi bai dauka hakan ai lefi bane a gurin shi tunda ya biya abinda mami ke tunanen ta kashe wa yarinyar.
Waya ya karba hakan ne ya dauke mai hankali don suna neman shi kan wani ma,aikata da za a gina suna bukatan shi ya tsara masu wasu na,urori a cikin tsarin ginan wanda saishi ne yasan yadda abin zaiyi daidai yadda suke son shi a ginan don bayanin da yakewa sauran ma,aikatar su basu gamsu dashi ba.
Wanan dalilin yasa shi dole ya koma a bakin aikin shi sai dai zaiso kafin ya koma maganan shi da yarinyar nan ya tsaya kada ya bar baya da kura idan ya tafi.
Anyi magariba duk bai fito ba mami kuma tasan ya dawo yana gidan bata nemeshi yadda ta saba ba idan yai hakan.
Ba wai baison fitowa bane gurinta saidai abinda zai faru a tsakanin sune nai shirya mai ba alokacin.
Mami da ta gama fusata da lanarin da hjy ta bata tsakanin ta da Nuriya yasa ranta baci don abinda tayiwa mahaifiyar nata din don bata kaunar abinda zai taba mutuncin hjyn balle ta bangaren ta.
Sallama yayi kofan mami ya shiga dakin kai tsaye tana zaune a bakin gado a cikin rigar bacin ta sai farin tabarau da zai kare mata haske a idon ta na karatu ta duban wani takarda a hannunnta.
Ba tare data dago ta kalleshi ba ta amsa mai sallama a ciki ciki tana mai cigaba da kallon takardan.
Gefen ta yakai zaune yana fadi a dan shagwabe mami iam tearyed ubana ka dawo ta fada ya riko hannun ta yana fadin kasan nan akwai matsala mami.
Bazan iya abinda suke son nayi masu ba don ba zasu iya fitar da kudi ayi aikin kwarai ba mami nasan ba zaka iya dasu ba dama kada dai suga sun gaiyace ka baka amsa su bane kawai.
Duk maganan da take bata dago ido ta kalleshi ba taci gaba da fadin dana san haka zai faru da zuwan ka garin nan da ban bari ka tafi ba.
Dasun baffan ku ya kara kirana kan zancen ka har yana ikirarin ya baka wata daya ka fitar d mata a cikin yan uwan ka daga Rufaida Nazifa da su Rubby.
What mami me zanyi da yaran nan godforbid mami wanan meye a cikin su banda zalla rashin kunya a tare dasu.
Wa yaja kansa da har ya samu kafan wanan maganan dama ai na dade da sani nufin su kanka ko su jalal niko yarana ba wanda zanwa aure a gida .
Mami ku fitar dani a wanan zancen don wanan shirme na dauke shi gareni na riga dana fada maku matata don haka yanzu ku nake saurare.
Zaka fadi haka jafar tunda ka sayeta a hannuna kake gani kana da kudin da kai zaka ban ni maryam har zaka turowa kudi jafar ?
No mami ba haka nake nufi ba don Allah ina son tayi facing din studies din ta a yanzu ne idan haka ya bata maki rai kiyi hakkuri mami ki nemi wata.
Bazan nema ba ta fada tana juyowa gareshi kaje gaka ga yarinyar nan sai dai kasan inda zaka kaita yanzu kuma baida ma matsala hakan mami ya fada tare da mikewa ya bar dakin.
🦅ABU CIKIN DUHU SIRI NE🦅
3️⃣4️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
Bayan kwana biyu da dawowan shi garin na girshesu dakin mu na fito daga kitchen na nufo dakin da sauri na in fadawa hjy aiken da tayi min wurin kande a kitchen.
Da sauri na koma baya na kasa shiga dakin a cikin tsoro da fargaba don Nuriya dana samu a dakin tana kuka wiwi a tsakiyan su.
Kitchen na koma cikin fargaba tare da tunanen ko akan akainane ko kan waye sukayi wanan haduwan haka.
Na dade a kitchen din kafin in koma dakin bayan fitan su daga dakin wurin hjy duk dako sun dan dade a dakin suna tataunawa a lokacin.
Hjy tana zaune ita kade a dakin bayan dul sun watse daga dakin tana zaune da kullin abu a farar leda tana kallo.
Na shigo take fadin kina kitchen wurin kande ne nace eh na shigo dakin nasame ku a ciki na koma .
Muna nan da mara kunyar sarakuwar gidan nan yau tajimu a gidan nan don jarumina yai mata tas a dakin nan a gaban kowa ya tashi taka ta saida uwarku taja mashi burki.
Wanan dan maganan da tayi ne ya sani tunane tare da jin tsanar da nake mai a wautana gani shine ya jawo min duk wani tsagwama da akemin yanzun a gidan mami.
Sai naji ya dan ragu a raina don yadda hjy tayi min bayani sai naji tausayin shi ya dan tsirga min a zuciya tunda duk a kaina shima yake samun wanan matsalan da kowa haka a gidan yanzu.
Ban kai ga gama tunane ba sai ga yaran Nuriya din sun shigo da littafi a hannun su sun zo nayi masu assignment din su.
Kwasan su nayi muka koma waje kada mu damu hjy a dakin can lambun gidan muka je muka zauna na fara koya masu sosai nakan ji dadin zama da yaran don sukan sakani a cikin nishadi sosai idan muna tare da su.
Hakan ne ya kasance a wanan lokacin da muke tare da yaran a lambo na shagala sosai ga dariyan yarinyar dake shirin kuka don kawai bata gane me nake tambayan ta ba.
Daga can bangare daya ba tare da sanin mu ba ya jafar ne da zaman daki ya isheshi ya fito don ya sha iska a wajen.
Daga inda muke zaune yake kallon mu don mun masifan burgeshi da dauke mai hankalin don ya kula da abinda ke faruwa a wurin.
Ga yaran duk gaba daya suna zaune ne a saman jikina a hakan nake koyar dasu sai in basu takardan su kwashe akarshe.
Yakai minti biyar a gurin tsaye hankalin shi a garemu yana tunane shi kadai a wurin yana kallon mu ko kyafta idanuwan shi baiyi.
Ganin yarinyar ta tubure da kuka a lokaci guda yasa shi saki zafaffan ajiyan zuciya ya fara takowa zuwa inda muke.
Baiso ya karaso inda muken ba amma sai ya tsunci kanshi da takowa zuwa garemu din gadan gadan zuciyar shi na cike da jin tausayin yar dan uwan shi dayaga tana kuka akan karatu.
Kamar daga sama na tsinkayi muryan ya jafar yana fadin meya sa kuka sakata kuka haka zainab ?
A dan firgice na waigo baya ta inda nake jin muryan shi din yana tsaye ya zura hanayen shi a cikin aljihun wandon shi gami da zubo min idanuwan shi akaina yana son jin amsan da zan bashi.
Ganin yadda na dan dirance da ganin shi a wurin a bazata yasa shi fadin kuyi hakkuri don min naga kamar har yanzu bata gane me kike nufi bane.
Malaman kuma kina ganina kin firgice da ganina yanzu yana fadin hakan ya duka ya dauki yarinyar ya dora a cinyar shi tare da kaiwa zaune a dayan kujeran dake gefen mu, muna fuskantar juna dashi.
Da sauri na janye kaina gefe daya tare da kurawa kasan wurin ido ina jin yadda yake lalashi yarinyar dake jikin nasa.
Ina zaune a cikin tsarguwa sai kace wata gunki a wurin ko kwakwaran motsi ban yarda na karayi ba wurin tunda ya zauna din.
Da kyar ya iya budan bakin shi tare da dago kai yana kallona yace kiyi hakkuri ki kara fahintar da ita yadda zata gane me kike nufi da wanan lissafi din.
Bai tsaya yaji abinda zan fada ba ya jawo kujeran tare da dan matsowa kadan a inda nake zaune.
Na cira kai da sauri na dubeshi babu wasa a fuskan shi don shima ni yake kallo a lokacin.
Tsoro da mamakin shi yadda ya zauna a gurin kuma yake son in koyar da yarinyar tasu ya kamani sai naji ya sake fadin yi mata bayani yadda zata fahinta a yanzu man.
A firgice nace nayi mata tace bata gane bane yaya kiyi mata yanzu zata gane din insha Allahu.
Ba yadda zanyi dashi haka na fara nunawa yarinyar yadda zata gane takuma fahinci abinda nake nufi a cijin lissafin tiryan tiryan nake mata bayanin komai ba tare da na dago kai na dubi inda yake zaune rike da yarinyar ba .
Duk da ban dago kai na kalleshi ba jikina ya bani yana kallona a lokacin har lokacin da yarinyar ta nuna ta fahinta ya saketa tare da umartan ta data rubuta din a nata littafin na karatu.
Hankalin yaran gaba daya ya dauku ga abinda suke rubutawa a lokacin don hankalin su baya kanmu ga baki daya muryan shi ya diro min a kunnuwa na yana fadin.
Zainab tun ranan dana fara jin labarinki nakuma gankii a gidan nan Allah ya jarabce da tausayin ki dakuma kaunar na tallafawa rayuwan ki a cikin harshen turanci yai maganan da kamar bashi yayi shi ba.
Da sauri na dubeshi don maganan nashi tazo min a bazata don ban zata zaimin wani magana makamancin wanan hakan a wanan lokacin ba.
A dab firgice saida na kalli kofan fitowa daga cikin gidan nace a harshen hausa yaya ka rufa min asiri ka barni don Allah hakan da kake nuna min yana jamin matsala a furin mami da sauran mutanen gidan nan.
Ya dan gyara zaman shi sosai ta hanyar yin balanced a saman kujeran da yake zaune akai kafin yace.
Idan na dauke kiki daga gidan nan zaki daina jin tsoron kowa a gidan nan kinga sai ki zauna ke kadai sai wanda kike tare dashi ya fada kai tsaye.
Hannuna na hade guri daya tare da kaiwa kasa a lokaci daya gwiwa bibiyu idanuwana suka kawo ruwa lokaci guda yanayina ya canza a lokaci guda.
Na bude baki a cikin kyarma ina fadin yaya don Allah ka rufa min asiri ka taimaki rayuwana ka tallafamin ina son karatuna ka barni in samu nasaran karasa karatun secondary dina kada mami tayi fushi dani ta koreni a gidan nan.
Sai naga ya mike tsaye zubur jikin shi ya dau kyarma yace look nasan ko waye shiyasa na shirya hakan a kanki.
Ban fito da zancen nan ba saidana gama shirya komai a kanki koda ace ke din baki shirya hakan ba a zuciyar ki ni a shirye nake na shaye duk wani barazanan da wani zai kawo min a wanan zancen.
Na kara fadi cikin razana don Allah yaya ka taimakeni ka rufa min asiri ka rufawa iyayyena da suka turoni don rufin asirin su.
Yai wani murmushi mai dauke da takaici kafin ya sake daure fuskan shi murtuk kamar bai taba murmushi ba a rayuwan shi.
Ya gyara tsayuwan shi tare da tura hannayen shi cikin aljihunshi yai min wani kallo da ba zan iya fassara ko na kiyayya ko na tsana.
Yadubeni da kyau ya kada kai a cikin alaman tambayoyi a fuskan shi tare da kara kallona kafin fadin .
Nima a lokacin tsoro ko shakkun shi ya fita min a rai don abinda naji ya fada na rabani da gidan ya kaini wani wuri da ban sani ba.
Don haka na tsura mai manyan idanuwana da suke min a firgice ina sauraren abinda zai fada min a yadda yayi min nuni a lokacin.
Shima da kyar ya iya tattara courage din shi ya kalleni ya bude bakin nasa yace dani yace haka na tsarawa rayuwan mu hakan kuma zai kasance damu.
Yaya wallahi ban yarda ba ni ban amince ba bana so kuma bantaba yin wani soba ka kyaleni ka barni a yadda ka ganni in samu in kammala karatuna.
Ya kada idanuwan shi tare da rausayasu yana fadin wanan kuma ruwan kine ko ki yarda ko kada ki yarda ba ra,ayin ki nake son ji ba a yanzu so take care as from now.
A hanzarce ya juya ya fara tafiya ya nufi hanyar shiga cikin gidan ta inda muka fito ya shige ya barni rusunne a wurin ina rusa kuka.
Takon Nuriya data fito ina wurin a durkushe take fadin tsiyar banza za a kawo min yara nan azo ana koya masu abinda bai dace ba a rayuwa don tsaban iya iskancin tsiya don ba kwabo ko tsawatawa gare ku.
Wani sabon kuka na kara barkewa dashi lokaci daya ina fadi a cikin kuka ni kan ba yar iska bace bani kuma naje na kira yaran ki zuwa inda nake ba.
Don haka ki daina aibantani da bata min rayuwa don kawai Allah ya kawoni a karkashin ku in zauna zaki ta min kallon wullakantantar matum ko yaushe.
Ta juyo ta kalleni tare da jefamin wani irin wullakantacen kallo mai tattare da tsana da takaicina taja hannun yaranta suka shige ciki.
Nan suka barni a yashe kasa karshe na dora hannuna a saman kai naja kafana daya gama yimin sanyi a lokacin zuwa cikin gidan ina rusa kuka.
Sam ban san yana dakin ba yasa na fada da kuka wiwi sai ganin sa nayi zaune a dakin ya mike kafa suna magana da hjy a dakin.
Lafiya hjy ta fada hankali a tashe tana kallona kokarin juyawa in fita daga dakin nayi don ganin shi a zaune dakin.
Yace ina zaki ba karata kika kawo mata ba a yanzu gani zaune ai saiki fada mata tayi min hukunci a yanzu.
Hjy taja wani dogon tsaki daga inda take zaune kuryan dakin tace yanzu a kan dan wanan maganan yarinyar nan kike wanan kukan haka ?
Kyaleta tayi hjy do ni a shirye nake na jure da duk wani barazana da wullakancin da zaki iya min a yanzu.
Hjy ki rokeshi ya barni hakan hakan ya isa hjy yanzu anty nuriya ta gama kirana da yar iska a kanshi nazo zan iskanta mata diya a gabansu muke iskanci don mu lalata masu yaransu.
A zabure ya fadi what da karfi saida na dan razana na dan ja da baya a daidai lokacin da ya mike tsaye a firgice zai bar dakin.
Yaka zonan kada ka fita dan nan dawo ka zauna wanan yarinyar babu abinda ke damun ta yadda na kula sai kyashi da hassada da bakin ciki a rayuwanta.
Kyashin me hjy ina ruwanta da yarinyar nan tunda ba mijin ta zai zauna da ita ba.
Kai dai ka barta a hakan kamar yadda na fada watarana zakace nace hakan koda bana raye kuwa.
Nasan kai a shirye kake da ka dauki duk wani cin fuska da zaka gani a gidan nan don haka ya saura gareki yanzu ki daure ki amshi zancen yaron nan da hannu bibiyu.
Hjy ba zan iya ba bazan iya jure wanan abinba a barni a yadda Allah ya ajeni tun kan sunana ya kara tashi ga barauniya zuwa yar iska.
Yadda nake magana a wurin ba hjy ba har shi kanshi a lokacin mamakina suke yadda nake fitar da lafazi a bakina babu shayin kowa a wurin.
Duk da suna min kallon mai dauke da ma,anoni a zukatan su hakan baisa na fasa fadan abinda ke a bakina a lokacin ba garesu.
Hjy sai kallon mamaki take watso min tare da tuhumar kodai wanan zancen ya taba min kwakwalwane har na hadu da wani lalura da damuwa ya jawo min.
Idan ba na samu tabuwa ba ko kurciya ta yaya Allah zai ban wanan daman inyi wanan sakarcin da nakeyi haka.
Ya mike duk da hjy ta hane shi da fita daga dakin ya kalleni tare da sakarmin wani malalacin murmushi mai wuyan fassarawa a fuskan shi kafin ya juya ya kalli hjy yana fadin.
Ya kirayi sunan hjy yana fadin ki kyaleta akwai kurciya a tare da ita duk wanan haukan a yanzu baya damuna ko kadan don wata rana bazata so ta tuna hakan ba.
Yana gama fadin hakan yayi hanzarin juyawa ya bar dakin ko juyowa bai karayi ba a lokacin.
Hjy ta bishi da kallo har ya bace mata da gani kafin ta juyo ta mayar da kallon ta gareni a cikin takaici tana fadin kaicon ki yarinya kurciya zai kaiki ga aikata abinda zai dawo ya dame ki a rayuwa da baya.
Tana fadan hakan itama ta juya ta bani baya ba tare data kara kulluni ba taci gaba da harkokin ta a dakin ita kadai ta barni a zaune a guri daya ina zaune a takure a gurin a cikin damuwa.
Ni da kaina sai na tsargu a wurin na shiga tunane da nazari ina neman mafita a kaina da rayuna.
Cikin kankanin lokaci saina tsunci kaina a cikin matsanancin tashin hankali mara misaltuwa ba tare da wani bata lokaci ba na gama yankewa kaina shawaran abinda zan aiwatar a zuciyana.
Don kwakwalwata ya fara hasko min abinda hjy dashi yaya jafar din suke nufi a gareni don rayuwana.
A sannu na fara hasko manufarsu a kaina kan son in amince da zancen da yadda rayuwana dana yan uwana zasu daukaka kamar yadda kullun suke shan fada min.
Tabas nasan ko basu fada aurena dashi kamar yadda yake fada alheri zai zamo min dagani har iyayyena nan gaba din.
To amma duk da hakan zuciyana ta kasa yarda da cewa wai shi yaya jafar so Allah da Annabi ne yake min har kasan zuciyar shi hakan.
Dole sai idan dai yana da wata manufane a zuciyae a kaina idan ba hakan ba ni nasan babu abinda zai kawo ya jafar din wurina da wanan zancen.
Duba da irin rayuwan su da kuma irin yan matan dake hariyar shi a rayuwan shi sam ni din babu ta inda na dace dashi duba da cewa.
Ko hausa sun fadi wutsiyar rakumi tayi nisa da doron kasa don ni din ba sa,an auren shi bace don nasan ya fini ga komai daga kudi ilimi kyau da wayewa.
Tun lokacin da na kula hjy ta fita zance na a gidan sai kuma hakan ya saukar min da damuwa a zuciyana .
Don nasan ni kaina nayiwa tsohuwar cin fuskan da baidace ba duk da kokarin da take min amma a gabanta na bude baki nake fada mata bana kaunar jikanta jinin ta.
Sai bayan sallah magariba ban yarda har lokacin na fito daga dakin ba daga sallah sai kwanci da nakeyi ina faman tunane barkatai a raina .
Ina zaune a cikkn muzanta bani baya da hjy tayi tun safe har dare ba tare data kara kulani ba har abin yana son ya zama min ciwo a zuciyana.
Saida na bari ta idar da sallah ta zauna cin abinci na taso daga inda nake nazo mannin ta na dan tsuguna tare da kiran sunan ta da hjy.
Ta dago kai fuska ba yabo ba fallasa ta dubeni kafin ta mayar da hankalinta ga abinda takeyi tace ina sauraren ki.
Sai kuma yadda tayi min din ya kara sani muzanta a gurin a dan maraice nake fadin kiyi hakkuri ki yafe min idan na bata maki ba zan kara maki hakan ba idan Allah ya yarda zaki sameni da maki biyayya a koyau.
Ban yarda ba hjy ta fada har lokacin bata dago kai ta kalleni ba taci gaba da cin abincin ta hankali kwance kamar bana a wurin.
Kiyi hakkuri hjy na sake fada hawaye na zubo min a cikin muryan kuka da nadama lokaci guda don na gama fahinta da tsohuwar ta hau sama dani a zuciyar ta.
Kinga jeki ya wuce a gareni duk da ta sallameni na dade a gurfane gefen kafin in daga na koma na rakube gefe daya a cikin damuwa.
Washe gari ma har na fita zuwa makaranta muna a halin da muke ciki da hjy babu wani sakin jiki a tsakanin mu dakin.
Kwana biyu da faruwan hakan ina dari dari da kowa a gidan ko me hjy ta gani ranan ina zaune nayi shiru saman kujera .
Naji hjy na fadin me ke faruwa ne dake haka kwanan nan yar nan kina kokarin susuta kanki a banza lokaci guda ina hankalce dake ko abinci baki son ci a gidan nan.
Na girgiza kaina cikin mamaki nake fadin banu komai hjy.
Hjy tace ban yarda ba ta yaya zakice dani babu komai bayan ina kallin ki a cikin damuwa haka ?
Ai duk mahalunkin mamalaki daya dubi yanayin ki da fuskan ki a yan kwanakin nan yasan akwai damuwa a tare dake sai dai idan boyewa kike son min.
Hjy ba komai saidai banjin dadin yadda kema kike fushi kamar yadda mami keyi dani akan laifin daba ni na kawo hakan ba akaina.
Baki daukan shawara ne yarnan a rayuwana nafi son mutum ya tsaya a inda na ajeshi kina ganin da tsufana za a hada kai dani a cuce ki idan ban tallafa maki ba.
Da sauri na girgiza kaina ina fadin hjy ba hakan a cikin zuciyana ko kadan nasan kina hakane garemu dan raimakawa rayuwan mu ga baki daya na fada a sanyayye cikin muryan dake shirin kuka.
Kinga wanan kukan ya isa haka yanzu taki kwantar da hankalin ki mu masu taimakon kine ba masu cutar dake ba.
Na tsaya inga wanan abin ya tabbata a tsakanin ku don ni nan na tsukayi wani abinda sai kece zaki iya hakkurin jure irin sa.
Wanda uwarshi ta kasa hango komai ga nufin yaron nan ya fada ba sau daya ba a gabanta da cewa din karinya da wani manufa ya zabi hakan a gareshi.
Da sauri na dago kai na kalli hjy daga inda nake tace kwarai jikata yaudai zan fada maki gaskiya a gidan nan.
Duk wani abinda iyami zatai maki ki daure ki fitar da mu akan wanan sarkakken abin da yake a cikin duhu wanda wani sirine dake rufe a duhu wanda Allah kadai yasan dalilin hakan a gareku.
Sai dai zan shawarceki duk ritsi duk wahala kada ki yarda ki fitar da wana zancen don idan zaka sadaukar da rayuwan ka ga wani ba sai maishi yasan da haka ba.
Don wanan abinda kike shirin yi zakiyi ne akan Iyakin da yanzu take wanan haukan a kanku don, , , ,
Sallaman wata mace ce da ta shigo dakin da abinci ta ta dire a gaban hjy ya hanata yin magana naji hjy na fadin wani abincin aka sakw girkawa ko me ?
Wanan ba abinci ba ta fada a cikin wani hausa dayasa saida na dago kai na sakw duban matan don na fahinci ita din yar garin abujane irin gwarawan nasu.
ZAINAB IDRIS MAKAWAZAINAB IDRIS MAKAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
3️⃣5️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
LITTAFIN KUDINE KI BIYA KI KARANTA YAR UWA BA TARE DA SHIGA HAKKIN WANI BA AKAN DARI UKU KACAL 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA, , , , , , ,
Zan iya cewa komai na tafiya kusan daidai tun wanan ranan sai dai abindake damuna shine hanani aikin da mami tayi a lokacin.
Don wanan bakuwar fuskan dana gani a gidan ranan yanzu itace keyiwa mami aiyukan da nakeyi a gidan .
Saidai can ba a rasa bane mami kan kwala min kira nazo nayi mata dan gyaran a wardrobe din ta ko in boye mata wani abin koshi ba kullun ba sai can ba a rasa ba.
Saidai wanan dan fadan da mami kan min abu ba abu ba zakaji mami ta falfalni da fada kamar ba mami dake kauna na da farko ba a gidan.
Wanan abin yana damuna sosai har ya jawo mi zama gurin su kande koda yaushe idan mami tana gidan.
Sai dai idan bata gidane zan zauna da hjy a dakin duk da ita hjyn tana fadan hakan ko yaushe saidai a gareni hakan shine mafita a gurina.
Sannu sannu har yakai na saba da hakan yayin da su kande suke jin dadin zama tare dani muna yan aiyukan gida a tare.
Daga wanan hutun damuke idan mun koma zamu zana jerabawan karshe hakan ya kara daukan min hankali ga komai.
Wanan matar ne ta sameni inda nake zaune ina karatu lami tana gyara kayan miya da zasuyi girkin dare dashi.
Naji muryan ta gatsau tana fadi da harshen hausan su zainab ana kira a dakin hjy tsofuwa jin hakan yasani dago kai na dan kalleta kafin na nade takarduna a guri daya na mike tsaye.
Dakinmu na nufa da sallama na shiga sai kuma na dan ja baya don ya mamud dana sama a zaune dakin suna magana da hjy.
Da sauri na dan ja da baya don ganin shi girshi da nayi a dakin lokaci guda don ban zata yana ciki ba a lokacin.
Daga kofa na dan tsaya kuma na juyo ina gaida shi ya amsa ba tare da komai ba yake fadin dama nina ce a kira min ke.
Ina jin hakan da sauri na durkusa kasa a inda nake tsaye don jin abinda zai fada min a lokacin ki fada muna sunan garin ku da yadda zamu samu iyayyen ki idan anje garin ku.
Kaina dake duke kasa na dago da sauri don jin abinda ya fada a lokacin kafin in kara dago kai nakai kallona gurin hjy dake zaune a kasa ta mike kafafuwan ta tana daga zaune.
Anchau ne garin mu na fada a sanyayye sunan mahaifin ki fa ma,ana yadda za,ayi saurin gane shi a garin.
A hankali na dago kai da yan yatsuna dake a harde guri daya ina wasa da yan yatsun hannun nawa nace.
Unguwar sarkin harbi muke da anje akace Habu mai faci dan gidan Asabe za a nunawa mutum gidan.
Dago kai sukayi suka kalli juna da hjy kafin yace dani ida an fadi hakan kawai za a gane nace eh ko ace gidan su Asaben sarkin harbi marigayi.
Yace shike nan jeki bayan yayi dan rubutu a wayan dake hannun shi ya juya wurin hjy yana fadin hjy zan tafi ina da inda zan tafi wanan ne ya dawo dani dama.
Sai bayan danaga fitan shi na dawo dakin na samu hjy tana kokarin diban abinci da kanta taci nasan ta gaji da kirana ko yaushe tunda ta gama fahintar halin da nake ciki na tsoro a gidan yasa ban faye zama kamar da a dakin ba yanzun.
Da sauri na karasa na karbi cibin a hannun ta na fara zuba mata a plate na gama ina rufe warmer din abincin take fadin kefa ba zakici bane yanzu ?
Da sauri na dago kai ina girgiza kai tare da fadin mami tace in daina ci a nan yanzu naci a gurin su kande ai.
Ikon Allah ita iyamin ta fadi hakan akan me zata hanaki cin abinci tare dani zama a gidan nan bai ganni ba don iyami ta bata wayau ta gareni yanzu.
Tsoro da fargaba ne suka ziyarci zuciyana lokaci guda nan na shigawa hjy magiya don nima saida na fada nagane nayi kure wurin fadin hakan a gaban hjy.
Zauna maza ki debi abinci muci ta fada a hasale rai bace da sauri na zauna na dibi abincin na fara ci don kada ta kawo wani zance.
Kamar daga sama ya fado dakin da sallama yana saye cikin shada mai ruwan dark ash karamin dinki na maza akaiwa shaddan ta dan matse a jikin shi kadan.
Ya shigo dakin a daidai lokacin da hjy ta mike zata shiga bandaki ganin shi bai hata shiga bandakin ba a lokacin.
Dadircewa nayi na rasa inda zan saka kaina ganin dagani sai shi a dakin ina wuni yaya na fada tare da dan rusunar da kaina dake kasa ina wasa da spoon din da nake cin abinci dashi.
Queen baki ganni ba baki ji wayana ba baki damu da kisan inda nake ba kuma ko ?
Saida nayi dan dum kafin in samun kaina nayi bakina na fadin kayi hakkuri yaya .
Yaci gaba da fadin a cikin harshen turanci a yanayi na tausayawa yake fadin Queen idan na kira wayan baki dagawa ya kike son inyi da raina ?
Queen kin kuwa san halinda nake a ciki saboda ke yanzu kuwa akan ki Queen zan iya komai, komai ma da baki zata ba my Queen.
Ki kallafa yadda na koma dan rikicin ki da mami ban taba samun matsala da mami irin wanan ba a rayuwana.
Na rame saboda ke saboda kece zabina duk nayi wanan lalacewan haka ke bakya tausayina ne wai ?
Nikan kasa magana nayi kaina yana duke a kasa din ba zan iya dago kai koda wasa in kalleshi ba a lokacin.
Don na shiga tsananin rudani da tashin hankali ga kalaman shi don abin kamar almara wai a kaina mutum kamar ya jafar ke wanan maganan.
Addu,a na soma don kariya daga ko wani irin masifa da yake son jefani a ciki don har lokacin duk da nake yarinya kalaman hjy yana yawo a raina.
Da take fadin ta fahinci yana da wani manufa daya boye akan aurena daya nace sai ni wanda mahaifiyar shi ta kasa gane hakan.
Wanan tambayan nakanyiwa kaina har yakai ina tsoron idan ba yankani ko sayar dani yake son yi ba don kawai banda gata a rayuwana don idan maganan hjy ba gaskiya bane don me yaya jafar zai tsalake kyawawan yan mata da mami ke taya mai ya nace saini.
Ji nayi ya sake tausasa muryan shi yana fadin Queen kece zabina don nasan kece zata iya hakkuri da yanayina da yadda nake.
Nikan kara tsorata nayi a raina don tabbas maganan hjy ya tabbata ke nan tunda yanzun ma ya fadi hakan da bakinsa a gabana.
Ban kai ga karshen tunane ba naji yaci gaba da fadin ni nasan kina sona Queen don ba zaki kini ba saidai saboda mami kike kokarin boye hakan ga kowa a zuciyar ki.
Zamu taimaki junane dani dake a rayuwan mu don kece kadai na yarda da inzauna da ita a tsarin rayuwana ba ko wace mace nake son aura ba.
Don haka ki taimakeni Queen ke kadaice na yarda da ita a rayuwana ina son na kasance a tare dake don mu taimakawa juna dana tare damu duk hukkuncin dana yake kada ki ki hakan ki yarda da kaddaran rayuwan mu.
Kaina na sunkuye a kasa nakai hannuna na share hawayen da suke zubo min don tsananin rudanin da na tsunci kaina a lokacin ciki.
Na ringa addua ya Allah ka kubutar dani daga sherin wanan mutumin da bansan abinda ke cikin zuciyar shi ba a game dani.
Ido kawai ya zura min yana kallon yadda nake faman sharan hawaye daga idanuwana a lokacin tabbas na bashi tausayi don nayi kankanta da abinda ke faruwa dani a yanzu.
To yaya zaiyi hakan ne kawai mafita a gareshi da irin fitinan da mami ke shirin kunnu mai a rayuwan shi na yarda ya auri yar kawanta ko daga cikin yan uwan shi kamar yadda baffansa ya fada harda diban mai wa,adi akan hakan.
Ya haka kuma ka zauna ka saka min ita a gaba tana sharan hawaye haka wani abin kuma ka sake mata na samu hankalinta ya fara kwanci a gidan nan yanzu .
Hjy ce data fito daga bandaki tana tsaye tana muna kallon mamaki take fadin hakan cikin kure shi da idanuwanta fuska daure.
Ya juyo gareta tare da wani irin sauke ajiyan zuciya yana dan gugan gaban goshin shi zuwa wuyan shi a cikin wani irin yanayi.
Hjy na gane yarinyar nan tsoron mami takeyi kamar ranta ba zata bani goyon baya yadda nakeso da ita ba.
Yadda yake magana ba kunya ta bude baki da ido tana masa wani irin kallon mamaki don hakan har hjyn ma saida taji tsoron shi a lokacin.
Kubi yarinyar nan a sannu kaida uwarta wanan rigiman jafari yafi karfin daukar zuciyar yar nan a yanzu.
Cikin takaici yace hjy kin san dai bana magana biyu na fadawa mami ban yarda da zabinta ba kuma zan taba yarda da hakan ba ta barni in zabi zabina shine kwanciyar hankalin mu gidan nan.
Ta kaici ya kama hjy take fadin dan nan wai kana a cikin hankalin ka kuwa wanan zancen da kake fada haka koda yaushe.
Shi kadai yasan halinda yakw ciki don haka ba tare da ya iya ba hjy amsa ba ya mike daga inda yake zaune cikin wani yanayi ya bar dakin namu cikin kunar rai.
Haka ya fito a dakin yana maijin zuciyar shi na masa wani kuna da suya don rikicin da suka kwasa da mami a office din ta a kaina kafin ya dawo gidan ya sameni da zancen.
Har dare banji hjy tayi min zancen ba ni kuma ban iya sake jikina da itaba har lokacin sai yawo muryan ya jafar kemin a kunnuwana kamar yanzu yake fada min maganganun daya fada dazun.
Sam ban san suna falo ana rikicin abu daya ba a gidan don dai shi ya dage akan zai tafi don aiyuka sun taso masa a lokacin mami kuma tace bata yarda ya koma batare da aure ba.
Shi kuma yace ta yarda da zabinshi don shi abinda ya zaba ke nan mami tace bata yarda ba ta fada mai a fusace.
Yadda na fadama ko yanzu zan sake maimaita ma hakan don ba zan taba yin magana biyu ba mun shirya zancen auren ka da Iyayyen Suraiya kafin ka koma za ayi bukin ka da ita ku koma tare.
Ta kare fadin hakan rai bace idanuwan ta sun kada sunyi jawur don masifa da takaicin sa da taji a lokacin.
Ya dago idanun shi da suka canza kala alaman idan ya fadi magana baya canzawa yace mami na fada maki yarinyar nan ce zabina.
Ni abinda nake nufi da yarinyar nan ba zaki taba ganesa ba a yanzu da na auri wanan din da kike nufi na aura mami gwara na zauna a hakan banyi aure ba.
Ni da farko nayi hakan be don sama mata jin dadi da walwala na dauka don ke nayi hakan mami a matsayinta na wace bata da gata a yanzun.
Koma meye manufan ka akan yarinyar nan nace ban yarda da hakan ba, idan zaka yiwa kankane kuma sai mu gani a yanzu.
Ya mike tsaye yana fadin shikenan mami zan zauna hakan tunda haka kika zaba min amma ni nasan akwai ranan da zakiso hakan ace ya faru da kinsan abinda nake nufi da hakan.
Ya mamud dake zaune yana sauraren su yace mami ki kyaleshi yayi abinda zaifi kwanta mai arai da wanan yawan gardaman da akeyi kan wanan zancen.
Rufa min baki idan ba zaka tayani yakarsa ba ya amincewa abinda nakeso don kawai wani ra,ayinsa can na banza da baida dalili.
Shima ya mike yana fadin kiyi hakkuri mami Allah ya zaba muna abinda yafi zama alheri a gareshi yai mata saida safe ya fita.
Wanan zancen da sukayi ne a gaban hjy dake zaune tare dasu bata tofa uffan ba ta kafa hujja ga hakan..
Bayan kwana biyu da zancen ne ya shigo dakin bana ciki a lokacin yake tambayan Hjy a cikin dan zolaya ina matana ?
Hjy ta dago ta kalleshi tare da fadin ubana ai ba wanan zancen tsakanin ka da yarinyar nan har abada.
Ka tsaya tsakanin ka na dan uwa mai tausayawa a gareta ko a hakan idan kayi niya zaka iya tausaya mata ka taimaka mata babu mai hanaka wanan a gareta.
Zuciyar shine ta harba da zancen hjyn take yaji wani irin kunci ya ziyarci zuciyar shi lokaci guda.
Kasa daurewa yayi take idanuwan shi suka kada sukai ja lokaci guda bai iya magana ba ya mike tsaye dan barin dakin.
Hjy ta dakatar dashi tana fadin kaga kada ka dauki wanan abin da zafi kaje kayi addua shine mafita ga mumini aduk sanda ya tsunci kanshi a cikin damuwa.
Har yakai kofa yaji tana fadin ina son ka rabu da uwarka lafiyane jafari don yadda ta hau wanan zancen a karkace bata jin kira ga kowa a yanzu.
Don dai yarinyar nan bata da wani gata a yanzu ka sani sai uwarka data daukota ta kawota gidan ta.
Ya juyo yana fadin mami ta yanke min hukunci mai tsauri wanan karon kuma hjy ba zan iya jure hakan ba a kaina.
Ka barta da yarta don Allah kaje ka auri wace take so din ita wanan din tunda kayi niyar taimaka mata sai ka zama mata gata nan gaba a rayuwan ta.
Amma idan kaki jin maganan mahaifiyar ka sai ka kara jefa yar nan a wani hali nan gaba wa kake tunanen zai zame mata bango bayan ku da uwarku din a duniyan nan.
Anan kuma ya kara dago kai ya sake kallon hjy din kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru ya juya ya fara tafiya yana fadi a cikin wani murya mai kariyan zuciya yana fadin sai da safe hjy daga hakan ya fice dakin rai bace.
Da safe ne hjy take min zancen mai kama da warning a gareni tana fadin duk da nasan baki dauki wanan zancen ba tun farko a ranki.
Hakan yai min dadi a yanzu yadda baki saka son yaron nan a zuciyar ki ba kamar yadda shi yasakaki din nan.
Don haka kici gaba da nisantan duk wani da na iyami da komai nata a rayuwa ku samu a rabu lafiya.
Saboda bana son ki sake shiga rayuwan kowa daya shafi a halin nan na iyami kiyi addu,a Allah ya kawo miji daidai ke a rayuwan ki.
Idona ya ciciko da hawaye tabbas nasan iya gaskiya hjy ta fada min don tsakani da Allah tsohuwar nan take zaune tare dani.
Na dinga share hawaye da bayan hannuna hjy tayi tankar bata ga me nake ba a lokacin tana maijin tausayina a kasan zuciyar ta.
Hakan yasa dakin yayi shiru na dan lokaci kamar babu kowa a cikin sa lokacin dagani har ita kowa da nazarin da yake a zuciyar shi.
Tabbas nasan nikan gaskiya hjy ta fada mami da ahalinta a yanzu sune gatana don a karkashinsu nake zaune idan wani abu nema ya same dolen dai sune zasuyi min tsaye akan hakan.
Sosai hjy take kara jana a jikin ta hira zamu zauna muyi sosai zata tsaya ta zauna tana ban labari ko shawara.
Na hanyoyin da zanbi na manta da komai har na taimaki rayuwana a cikin kwana biyune na sake sosai kamar baniba don har dan jikina ya fara dawomin a lokacin.
Hakama mami duk da daure fuskanta gareni bai hana in samu kulawan da nake samu ba da farko a gidan nan.
Iyaka dai zance nafi samun matsala gun mami da anty Aisha sai nuriya matar ya mamud ko shi din sai idan wani abu ya dan hadamu da su.
Sai dai su samari mami din jalal da jamal babu wani sauyin fuska da suka canza min don har yanzu mutuncin dake tsakanin mu yana nan a yadda yake.
Hankalin kowa a kwance don kowa ya fita wanan zancen shirmen da ya jafar ya tsiro min dashi tunda suna ganin ya fita zancen a yadda sukayi da mami a karshe.
Sai gashi ranan ya shigo gidan ina daki kwance ya shigo dakin namu wurin hjy don dai kakarsu tana dakin ne duk wani na gidan yakan shiga dakin namu don gaida hjyn .
Ina ganin shi na rikice ina kokarin barin dakin bayan mun gaisa dashi na mike da sauri zan bar dakin don har lokacin tsoron shi nakeji.
Yake fadin karki fita dakin nan don ni ba dodo bane ya fada cikin daure fuska.
Na juyo da sauri ina fadin kayi hakkuri ba don ka zan fita ba sai muryan hjy ke fadin ka daina kula yarinyar nan.
Don kwanciyar hankalin kowa a gidan kaga kwanakin nan komai ya gama lafawa a tsakanin ku da mahaifiyar ku.
Kwatsam sai ga mami ta bude dakin ta fado tana fadin me kake a nan ke kuma fice daga nan ki ban wuri.
Juyawa tayi ta fara fadin hjy kina zaune zai shigo ya kebe da yarinyar nan bana son wani abu ya sake faruwa a tsakanin su kuma
ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
3️⃣6️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BARKA DA JUMMA,A YAN UWA MUSULMAI UBANGIJI YA SADAMU DA ALHERIN DAKE CIKIN WANAN RANAN ALLAHUMA AMIN, , , ,
Bayan kwana biyu da faruwan hakan da har hjy da kanta tayi mai iyaka dani a gidan don samun kwanciyar hankalin kowa a cikin maganan.
Sai ya zamanto banda wani lakka a tare dani ni dai har ga Allah nasan bawai son yaya jafar nakeyi ba a raina.
Saidai na rasa me yasa na damu da yadda hjy din tayi a lokacin hakan ne ke wayan sakani a cikin damuwa har yakai na fara rama a jikina wanda ban taba irin saba tun zuwana gidan.
Da darene ni kadai a dakin ina kwance ashe hawayen ke zuba min a idanuwana ba tare da nasan hakan ba.
Ba komai nake tunawa ba a raina sai yadda iyayyena sukai watsi dani haka kan abin duniya har hakan ke faruwa dani ba tare da kowa nawa ya san da hakan ba.
Irin wanan tunanen da nakeyi yanzu ne ya karkare ramar dani hakan duk nabi na susuce har sai mutum ya dauka akan zancen mu da ya jafar ne nake wanan ramar haka.
Hjy da dawowan ta ke nan daga falo taja tayi turus tana kallona a cikon mamaki da al,ajabi yadda ta sameni din a dakin.
Jikin ta yayi sanyi lokaci guda tana fadin au kuka ke rusa haka yar nan ke kadai a dakin nan .
Da sauri na gyara ina kokarin goge hawayen dake fuskana a lokacin shiga tayi bandakin ba tare da ta tsaya sauraron abinda zan fada ba a lokacin.
Ta fito ta tayar da sallah da nake ganin shafa,i da wutirine zatayi har lokacin ina kwamce a yadda nake nade cikin kujera ban motsa ba.
Muryan ta naji kamar daga sama tana fadin ni yar nan meye abin kuka yanzu ?
Idan don maganan dayiwa yaron nan ne kiyi hakkuri wallahi ba nayi haka bane don in raba tsakanin ku.
Nayi hakan don kawai a samu kwanciyan hankali ga wanan zancen dayaki ci yaki cinyewa tsakanin shi da mahaifiyar shi.
Da kyat na iya motsa bakina na furta hjy ba wanan zancen ne damuwa na ba iyayyena da suka fita zancena a nan sune damuwana a yanzu.
A, a yar nan don wanan ai ba zai sa ki rame har ki lalace haka ba lokaci guda wallahi anyi farko anyi karshe insha Allahu ba zan kara maganan nan ba a gidan nan irin haka a kanku shima din na kula da fushi yake dani a kwanakin nan.
Aisha ce ta shigo dakin ta samemu muna wanan maganan duk da shigowan ta baisa hjy ta daina fadin abinda take fadi ba a lokacin.
A daidai lokacin da hjy ke fadin Allah ya baku hakkuri kuskure nayi na aikata hakan .
Aisha data fahinci maganan tsohuwar inda ya dosa Aisha taja wani irin tsuki tana fadin wanan zancen har yanzu nina rasa me yasa ya J ya nace akan wanan zeey din haka wallahi mami tace bata son zancen nan amma shi duk yabi yana kokarin dagawa mutane hankali akai.
Da sauri naji hjy tace a, a yar nan kada in kara jin kin fadi irin haka so ba a yi mashi irin haka abune shi mai cin zuciya rabu da namiji kan abinda yake so.
Idan an mashi hakan ba,a kyauta mashi ba don yaron nan bai taba nuna yana son wata ba haka kamar yadda ya nuna a yanzu.
Daga shi har yar nan ai yanzu an zama daya dan yar nan yanzu tankar iyami ce ai ta haifi abinta bata da maraba da wace ta haifa a cikin ta tunda iyayyenta sun bata amanan rikonta a hannun ta.
Da sauri Aisha ta dago tana fadin ba zasu taba zama daya ba kan da yaya jafar hjy ta yaya ma za a hadusu wai ?
Wani kallo hjy ta watsa mata lokaci guda kafin tace ni ba ruwa da zancen nan yanzu daga fadin gaskiya ya J ya tashi makeni gidan nan.
Dole ya makeki don kalamin ki baida dadi yar nan don yarinyar nan tana da hakkuri da mutuncine ko wanan maganan da kike fada yanzu haka ke kinga ya dace da ki fadi hakan a gabanta.
Tsam ta mike ba tare datayi wani magana ba ta fice daga dakin hjy ta bita da harara tana fadin sakariya mara wayau idan Allah yayi saiku hana mugani.
Indai biyayya gun nagaba nada dadi mu zuba gani nida uwarku data raina zancena a yanzu tunda ban isa in fada mata daidai ba a gidanta yanzu tana ganin ita ta ishi kanta ke nan yanzu.
Ta juya inda nake bayan fitan Aisha dakin tana fadin ke kuma ki barsu da dansu wa yan nan zuciyar su ya kyankyashe da wullakanta dan Adam.
Amma saboda shi har zaki wani shige daki kina hawaye haka don baki danayi yanzu sai tunanen shi.
Ki matsa ki yada kanki wurin wa yan nan mutanen da suke raina arzikin tallaka a rayuwan su.
Take jikina ya kara sanyi nace nifa hjy na fada maki ba wanan zancen kika samu inawa kuka ba dazun.
Don waye kike kuka idan bashi bane din idan fadan danayi ne bazan kara shiga harkunku ba a gidan nan.
A sanyaye na marairaice ina fadin kiyi hakkuri hjy insha Allahu ba zan kara ba tace shike nan ai.
Nidai shawaran da zan baki shine wallahi ki natsu ki bar saka wanan zancen a ranki ki kara kama kanki da wanan zancen.
Kinga tunda aka fara haka ko da Allah yayi kunyi wanan auren bazaku samu jittuwa da sarakuwar ki ba a hakan tunda har ta iya rufe idanun ta ta nuna hakan yanzu.
Don hakane yasa nace mai ya fita wanan zancen don abindana hango maku din keda shi nan gaba.
Amma badon bana son ku a tare ba ko wani abu can kawai dai abin ne da uwar taku keyi akwai cin fuska a cikin sa yanzu.
Abi komai a sannu sannu iyayye ku su amince da wanan zancen don ina gudin abinda kaje ya dawo daga baya.
Hjy kiyi hakkuri wallahi ba a kansa nake kuka ba nan na labarta mata abinda nake yawan tunane game da iyayyena a raina.
Saida hjy ta gama saurarena kaf take fadin koma dai meye ba zasu taba mantawa dake ba a rayuwan su mussanman ma mahaifiyar ki dole tana can a cikin rashin ki tare dasu a yanzu.
Haka ta kalleni a cikin tausayi tana fadin ki saki jikin ki ki kara kwantar da hankalinki ki nunawa iyami danta ke baya gaban ki a yanzu.
Nace hjy ni komai ya wuce a wurina tun farko ban taba nasa wani alaka a tsakanin mu ba bayan na yan uwantaka.
Can cikin dare ina barci nake jin wayana na varvirating a saitin kunnena duk da nasan babu mai kirana sai shi yanzun kuma ya daina kirana din tunkan ai wanan tsakanin su da hjy.
Har kiran ya kare ban dagaba sai ma kokarin danne wayan da nake gudun kada hjy taji kiran.
Kira uku na daga a dan rikice don nasan ba zai daina kira ba idan ba na daga wayan ba a lokacin.
Murya kasa kasa na amsa da sallama don kada hjy ta jini jin muryan shi take na rikice gaba daya na rasa a wani duniyan nake.
Wani irin tsoro da fargaban jin muryan shi suka ziyarci zuciyana wanda nake ganin kamar amsa wayan babban laifine nake aikatawa a lokacin.
Wani irin ajiyan zuciya naji ya saka yayin da yake ji a bangareshi kamar susa nake mai a kwakwalwan shi don rikicewa.
Ran sarauniyarta ya dade kin wuni lafiya ya rigiman hjy da tsufan ta ban san lokacin da dan murmushi ya subbuce min ba a lokacin.
Yace nasan kina nan kina fama da rudu irun nata a kullun sai kara firgita min ke da takeyi.
Aiko hjy ta wuce hakan a wurinta don da tana da iko da kai da ta faranta maka rai fiye da kowa a duniyan nan.
Na sani amma yanzu itama din sun fara in mata ai nake gani kan hakan .
Da sauri nace yaya ka daina irin zancen nan don maganan hjy shine gaskiya a garemu don Allah yaya ka barni da wanan zancen.
Ka tuna ni kamar marainiya nake a cikin ku kune gatana a yanzu na rokeka idan kai sanadin dana bata da mami zan shi, , , ,
Amma so ance hana ganin laifi ko nayi shiru yace don haka kada kiga laifina a wanan bangaren .
A raina nace tabbas akwai sauran rikici a tsakanin mu gidan nan yanzu don a gaskiya ba zan taba yarda da hakan ba a gareni don mami dai ba zata taba yarda da hakan ba a tsakanin mu tunda ni banda gata a wurinta.
Yace ina son inji kin shirya zaki zauna dani komai ritsi komai wahala ni kuma nayi maki alkwarin inganta rayuwan ki dana yan uwan ki da iyayyen ki tun daga ranan da bakin ki ya bude da kin yarda dani ko ba tare da yardan mami din ba.
Wanan maganan yafi karfin fahintana ka rufamin asiri a rayuwana koda zan soka yaya badan kudin ka ko wani abu zan soka ba zan soka ne tsakani da Allah kamar yadda nima kuka rikeni a cikin ku amana.
Koda kuwa yin hakan yana da wani illa a gareni nan gaba zan daure in ga nayi abinda zan sakawa mami a rayuwana.
To idan kuma mamin naki bata yarda ba kan wani dalili nata na daban zaki iya jure wanan daman da kika samu daga taimakon iyayyen ki da yan uwan ki ya tafi ga wata.
Nace idan yin hakan zai kawo fahinta a tsakanin mu da mami a shirye nake da mata biyayya ko wani lokaci.
Amma dai kin yarda har a zuciyar ki niba mai cutar dake bane zainab ya fada a cikin wani yanayi mai ban tausayi.
Yaci gaba da fadin ki yarda dani kanwata ke kadai zuciyana ta amince dake zainab kece zuciyana take hasko min a yuwana kece rufin asirina kada ki yarda ki barni zainab komai ritsin mami a garemu na maki alkawarin rikeki a mana a rayuwana koda kuwa duk duniya zasu juya maki baya akaina.
Nayi maki alkawarin rikeki amana har karshen rayuwan mu nidai muradina shine ki amince min zainab yardan ki kawai nake bukata a yanzu.
Nayi maki alkawarin rikeki amana harga Allah zainab ba zaki taba dana sani a kaina ba matukar kika yarda da amsa min da eh yaya na amin ce.
Ki taimakeni ki taimaki rayuwana kada mami ta zantar da hukuncin da zata dawo tana nadama a kaina daga baya akanshi.
Yadda yake magana a cikin wani irin yanayi kamar roko a gareni yasa tausayin shi ya rufe min zuciya ban san lokacin dana bude baki don dakatar dashi nace.
Na yarda yaya indai hakan shine rufin asirin ka da mami dama yan uwan ka na yarda da wanan koda kuwa hakan zai zama kadara rayuwana mutukar hakan zai zama rufin asirin ku a duniyan nan.
Yace Alhamdullahi zainab na gode tunda kika fahince kamar yadda hjy ta fahinceni ga hakan yanzu kema din kin fahinceni.
Zainab kece rufin asirina ke kadai ce wace na yarda da ita a rayuwana da zaki iya zama dani a irin yanayi na ko yaushe ba zabin mami da take soyi a kaina ba yanzu.
Fatana inje ga iyayyen ki yanzu su amince dani kamar yadda kema kika fahinceni kika yarda dani .
Na samu duk wani fari ciki da nike so a fanin rayuwan duniya ke kadai kika rage min a yanzu in mallaka .
Idan har mun daidaita a tsakanin mu muka shirya zama da fahintar rayuwan mu to tabbas bani da matsala a duniyan nan fatana yanzu mu samu kiyamar mu.
Idona na lumshe don jin abinda ya fada ina kiyasta maganganun daya fada min a zuciyana saidai na kasa fassara abinda maganan nasa ke nufi a fili.
Katseni yayi da yake fadin to yanzu sai ki shirya tsana da tsangwaman mami a gareki don kinsan itace matsalan mu.
Saidai hakan na dan lokacine ba mai dorewa bane idan mun bar kasan nan munyi nisa da ita komai a sannu zaizo ya lafa.
Mun jima a hakan shike zuba min hiran da ba amsa tun ina amsa mai da eh ko a, a har ya fahinci barci ya kwasheni a lokacin ya sararawa ranshi.
Washe gari koda muka tashi hjy bata nuna min komai ba har na shirya na tafi school sai bayan mun dawone da yamma muna zaune.
Naji hjy ta jefo min tambayan da ya girgizani lokaci gudan don ban zaci taji me muke tataunawa a tsakanin mu a daren jiya din.
Ina fatan kin fara shiri kan abinda koka tarawa kanki kika yarda da hakan da bakin ki ba wani ya fada min ba na jiki naji zancen ku kaf a kunnena duk yadda kukayi dashi.
Kai na sunkuyar kasa a cikin kunya dajin nauyin hjyn data fito min da wanan zancen .
Nayi rantsuwa akan wanan kudirin naku kece da hakkuri jikata a ciki nasan kuma babu wanda ya isa ya wuce kaddaran shi a rayuwa.
Nasan kin yanke wanan shawaran ne ba tare da kinyi nazari a rayuwan ki ba na abinda zaije ya dawo ga auren shi gareki.
Hakan kuma ya samo asaline ga yawan tausayin da raunin irin namu na mata ga da namiji da muke saurin yarda da bukatan su.
Naso ace kin manta da zancen jafar a rayuwan ki saidai a yanzu kadara ta riga fata don kin riga da kin amsa mai bakin alkalami ya riga daya bushe gare ki ko.
Dama ubangiji baya son ayi maishishigi ga al,amarin shi yanzu ni a nawa bangaren zan tayaku da addua insha Allahu ubangiji ya kade mana tsotsayin dake cikin wanan al,amarin naku amin.
Duk yadda naso hjy ta wayar min dakai kan wanan zancen hjy takiyin hakan fafir dole na hakkura na kyaleta da gutun sharhin da tayi min din.
A bakin hjy nake jin sunyi tafiya da ya mamud ko mami bata sanda zancen tafiyan tasu ba sai bayan tafiyan su ne tana neman ya mamud matar shi ke fada mashi sunyi dan balaguro da dan uwan shi zuwa wani business wajajen kaduna.
Kansu tsaye sukaiwa garin mu tsinke su isa misalin karfe daya da wani abuna rana a gidan dagacin garin mu sukaiwa kansu masauki.
Bayan gaisawa da gabatar da kansu gareshi dako waye mahaifin su take dagaci ya gane daga inda suke.
Bayan fahintar juna take suka gabatar mai da abinda ke tafe dasu ba bata lokaci take ya gane kowa ake nufi mai gari yadan musguda yana gyara zaman shi tare da fadin.
Kardai wanan yarinyar da uwarta ta kawo kara nan gurin mu kakarta da mahaifinta sunkaita birni aikatau ba tare da sanin wurin wanda aka kaita ba taka maimai.
Ya mamud ya tare da fadin a gidan mu take aiki a hannun mahaifiyar mu hjy maryam lerai take zaune tare damu.
Yanzun ma tafe muke da zancen auren yarinyar kanina gashi shike son auren ta sai kanin mahaifin mu gashi zaune tare da wan mahaifiyar mu Alh bello samu,naka.
Munzo da zancen neman auren yarku ne wa dan mu kuma dan danuwana kamar yadda addini ya kindaya muna da al,adan malam bahashe.
Maigari ya na,am tare da yabawa kamalan su da kuma yabawa ga iyayyen su ya nemi da sy bashi lokaci a nemo iyayyena da suka haifeni don a sanar dasu halin da ake ciki a kaina.
Ba bata lokaci aka aika neman mahaifina dake bakin aikin shi a lokacin jin maigari ke neman shi don zuwan wasu baki da ba a san meke tafe dasuba a lokacin.
Hakan yasa Abba ya nemi da yaje gida ya sauya tufafin aikin shi dake jikin shi da farko don zuwa amsa kiran maigari da bakin shi saidai gaban shi na faduwa don baisan abinda zaije ya sama ba a can fadan lokacin.
Tunda Abba ya tunkari fadan ya hango tarin motocin dake wajen gaban shi ya shiga faduwa don baisan dame sukazo gareshi ba .
Shida ba birni yake shiga ba kuma ya san wani ba ta yaya wa yan nan bakin zasu danganta dashi.
Bayan ya iso sun gaisa a ciki mutunci dagacin garin mu ya gabatar mai da abinda suke tafe dashi a lokacin.
Ikon Allah Abba yace lokacin da aka nuna mai ya jafar din da yake zaune ya hakince a gefe daya bai wa kowa magana ga cikar kamalanshi da zati kawai shida dan uwanshi daya gama cika wurin.
Bayan bayane ne Abba yake fadin yana da magabata ga maigari sai su taru suyi magana abindaya dace yana fadan hakan ya fita daga zauren maigari yace bazaiyi magana ba kasancewar yarinyar yar fari ce a gurin shi.
Ba a dauki lokaci ba yan uwan mahaifina suka gabata zauren maigari take aka tsayar da maganan aure kawun su wan mahaifiyarsune ya zo da wani zance da cewa mai zai hana tunda gasu ga jama, a a daura auren ga baki daya inyaso daga baya duk wani al,adan aure ya biyo baya.
Take akai na,am da zancen shi abu na kudi haka suka zube kudi a zauren maigari aka yi yekuwa take gurin ya cika aka daura aure akan sadaki dubu dari don maigari da sauran iyayyena sunce dags hakan ba zasuso akara kwandala akaiba.
Da mamaki a ransu da kawu ya bude bayan motar shi aka fitar dasu alawa da sauran abubuwa da duk ake bukata a wurun daurin aure.
Karfe hudu na yamma an gama komai kowa ya watse ya nufi inda ya fito suma dai a ranan suka juya suka koma kaduna sai cikin dare suka shigo don jirgin sai karfe bakwai na marance yabar garin kaduna.
ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
3️⃣7️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAR UWA INA MAKI FATAN ALHERI A KULLUN UBANGIJI ALLAH YA TSARE YA KARE YAIWA ZURI,A ALBARKA AMIN, , , ,
Ina bukatan addu,an ku gareni yar uwa badon halina ba sai domin Allah da annbinsa gareni Allah ya bada ikon yi lafiya Amin nagode ga wace ta samu lokaci tayi min dama wace Allah baiba dama ba taji tanasa hakan Allah ya kara haskaka muna al,amuran mu amin.
Tunda ya dawo gidan bai fita ko ina ba yana dakin shi har wayewan gari mami bata sakashi a idon ta ba.
A daren ranan ne kuma akai hira dashi a talabijin din NTA na kasa wanda mami tana zaune har da hjy kawai sukaga an haskoki shi a matsayin bakon da za ai hira dashi a ranan.
Mamakine ya kama mami dake zaune tana aiki saijin sunan dan nata tayi a matsayin babban bakon su na ranan a hankali mami ta zare glass din dake idon ta tana mamaki don bai fada mata cewa sun gaiyace shi ba .
Kowa dake falon ya mayar da hanlalin shi wurin sauraren hira da akeyi da ya jafar din a sannu ake masa tambayoyi yana bada amsa mami sai girgiza kai kawai take a cikin burgewa.
Bayani ne na irin business din su ta yadda zasu tallafawa kasa a samu cigaba hakan daga kasashe daban daban na duniya.
Ko wanan haskawan ya kasance sunyi nasaran shigo da na,urori n wutar lantarki da zata karawa wutan kasan haske ba tare da ansha wahalan wutan neper ba a kasa.
An dauki lokaci ana hiran falon yayi tsit hjy tsohuwa ke fadin ni wanan da an barni sai nace jafari ne ai don kamar su datayi yawa sosai.
Aisha dake gefe zaune ta nade kafafunta saman kujera taja tsuki tare da fadin dama wa kike kallo a tv idan bashi ba yanzu.
Yayin dasu jalal suka hau mata dariya daga inda suke zaune suma suna kallon shirin tambayan da aka jefo maine yasa mami ta daka masu tsawa akan suyi shiru su saurara.
Mai hira dashi yace mr jafar mu,azu mahadi laire kayi namijin kokari sosai wurin shigo muna da wanan kayan a kasan nan babu abinda mu yan kasa zamu ce maka sai godiya da kira ga irin ku matasa da suyi koyi da irin halinka a taru a gina wanan kasan ta farfado daga faduwan tattalin arzikin da take barazanan shiga a yanzu.
Sai tambaya na karshe da zamuyima a yanzu ko enginer namu zai dan fadawa masu kallo da sauraren mu shekarun sa nawa ?
Sai lokacin ya danyi murmushi tun fara hiran dashi tare da fadin iam just talatin da bakwai nake nema a yanzu.
Matan ka nawa a yanzu ido ya dan lumshe kafin ya bude ya kalli mai tambayan ya furta matana daya sunan ta zainab bello Anchau .
Itace matarka ta farko mai tambayan ya tambayeshi a cikin dariya sai ya dan lumshe idanu kafin ya waresu a hankali yace cikin murmushi itace auren namu baikai three days ba ai yanzu da mukayi.
Don aurene na siri da ba kowa yasan da faruwan hakan ba sai yan kalilan ya fada yana gyara zaman shi.
A daidai lokacin da mai hira dashi a tv ke fadin wow zanso naga wanan lucky girl din datayi nasaran sace zuciyar matashi kamarka da kasa ke alfahari dakai haka.
Daidai lokacin ne a falon mami kuma abubuwa suka faru da dama a wurin don ba mami kadai ba har yayanta dake zaune a falon saida suka mike tsaye a cikin fargaba da tashin hankali.
Hjy dai da ba turanci takeji ba sai binsu da kallon mamaki takeyi tare da mikewa tsaye itama tana fadin wai meke faruwane haka ?
Don ganin yadda mami ta sake kofin glass din daga hannunta ya tarwatse a gurin lokaci guda tana batun fita hayacin ta a take.
Tambayan su take meke faruwane haka a gigice Aisha na fadin ina wanan ma aiba zai taba faruwa ba wallahi wanan ai jawa kai raini ne da wullakanci.
Ya jamal ne dake kan mami da take kokarin kiran waya hankali tashe ta kasa sai jalal ta mikawa wayan ya kira matashi ya juyo yana fadawa hjy cewa.
Wai ya J ne ya fada yanzu sunyi aure da zeey kwana uku daya wuce din nan a razane tsohuwar tace aure ?
Haka ya fada yanzu hjy a duniya kin kuma san halinshi baya magana biyu shi hakan ne tunda ya iya fadawa duniya kai tsaye.
Shike nan hjy ta fada iyami kin kai ga yadda kikeso da yaran nan Allah ya gani yaron nan baida hakkin ki ko kadan.
Shiyasa ubangiji yai maki hakan kina raye ki ci barnan ki da hannun ki ba sai gobe ba ace mutum ya tsaya yana jayayya da hukuncin Allah haka ?
Allah ubangiji yasawa aure albarka ya kore shadan da shedanu a tsakanin yaran nan kuma Allah ya basu zuria masu albarka, , , , , haba hjy.
Aisha da ta raba hankalinta gida biyu ke fadi haka ki duba kikaga yanayin da mami take ciki da kike wanan maganan.
Ga kuma wayoyin mami din dake ake ta faman kira a lokacin wanan na shigowa har ya katse ba a daga ba wani ya sake shigowa daga kawayen ta da yan uwanta.
Ban san meke faruwa a gidan ba ina dakin mu kwance ina karatu don jerabawan da muka fara zanawa yasa yanzu ban wasa da karatu na.
Don damuwan da tashin hankali bai hanani mayar da hankali ga karatuna ba.
Dan haya niya nake ji sama sama tunda ba tv ne kunne a dakin ba sai dan karan nauran sayin dake aiki dakin lokacin.
Kamar ance in fita waje zubur na mike daga kwancen da nake na zura takalmina dake kofan daki a fararen kafafuwana da yanzu suka samu hutun jin dadi sun kara fari da kyai kamar bana taba kasa dasu don hasken su.
Har nakai kofa naji wayana na kara najuya ina kallon wayan dake gefen filo ajiye na nufi wurin duk da ban debe tsamani ga kirana din ba shine dai.
Na dauka da sallama muryan shine ya sauka a kunnena yana fadin queen kina inane yanzu ba tare daya amsa min sallaman ba.
Dakin mu zan fita waje ne yanzu ka kirani kada ki fita nasan mami na gida yanzu akwai matsala idan kin fita yanzu wurin su.
Kirjinane yai wani irin bugawa lokaci guda nace a hankali matsala akan me kuma yaya yanzun nan na gaida ita a falo ai.
Na fada maki kada ki fita ki bari yanzun zan karaso gidan idan ma zaki fitone ki bari in shigo.
Jikina yayi sanyi yayinda zuciyana ya shiga fargaba da tsoron jin abinda ya fada din naji yana fadin al,amarin mai girmane zai faru a yanzu tsakanin mu da mami don yanzu nagama fadi a tv an daura min aure dake.
Aure na fada da dan karfi kafin in wurgar da wayan saman gado inje kasa a sulale don firgicin abindaya fada din.
Shike nan wanan mutumin yaja min tashin hankali da fitina a rayuwana don me zai fadi haka a duniya dole mami ta dauka ai gaskiyane ke nan.
Kamar an tsikareni sai kuma nayi zubur na mike na kwasa da gudu zuwa falo ban tsaya sauren gargadin da yaimin ba a wayan.
Ina fitowa falon naja na tsaya turus don yadda gaba daya suka zubo min idanuwan su a falon lokaci guda.
A hankali nake kokarin takowa zuwa garesu naji Aisha da mami sun daka min wani irin tsawa kusan lokaci guda suna fadin ke dakatanan gurin kada ki yarda ki karoso wurin nan bakar manya kawai Aishan ta fada.
Hannu mami ta daga min itama tana fadin barta tazo ta fada min abinda ban sani ba tunda ta zamax munafuka tsakanina da dana.
Idona runtse hawaye ya shiga tsiyayya a idon nawa na kai kasa ina fadin mami bazan taba munafurtaki ba a rayuwana.
Idan nayi maki laifine don Allah ki yafe min mami idan kinyi fushi dani mami ina zan saka raina.
Rufa muna baki yar iska ba kauyan banza bakar manya mai nacin tsiya kamar karya wace, , , ,
Tas tas Jamal ya kwashe Aisha da mari biyu masu kyau sai data duka a inda take zaune tana jefo min zagin.
Mami ta dago da zuman ramawa Aisha marin yayi saurin kaucwa a inda yake tsaye ta hanyat jada baya kadan mami ke fadin ka mareta saboda wanan yarinyar jamal.
Mami bakiji irin mugun zagin da take zagin diyar mutane dashi bane ita waya zageta haka ko meye laifin zeey a cikin zancen nan yanzu wace ke gida always tare daku.
Shiru sukayi a dalilin shigowan yaya jafar da ya mamud gidan ya mamud da tun kan ya karaso yake fadin meke faruwane kuma yana kallon mami ya kuma juyo inda nake gurfane ina sharban kuka ya sake juyawa wurin da Aisha ke zaune yana fadin wai meya farune haka wai ?
Wani irin ashar mami ta wulwulo ta duramin a tsorace na jada baya na makure a jikin bango jikina na kyarma hankali a tashe ban daina kukan da nakeyi ba har lokacin.
Mami ta sake daka min wani uwar tsawa tana umartana da nadawo gaban ta take na mike jikina na kyarma na dan karaso inda suke zaune ita da Aisha.
Ya jafar din ya samu wuri a gefen mami yakai zaune a cikin kwanciyan hankali yanayin shi yake.
Banyi aune ba naji mami ta fisgeni da karfi nakai gurfane a gabanta da sauri ya jafar din yace subbahanallahi this is bad mami meye laifinta a wanan zancen.
Wani kallo mami ta watsa mai kafintayi kukan kura ba wanda yai aune da ita lokacin takai min mari uku masu kyau a fuskana saida duk diyan nata suka mike tsaye don firgita.
Ban samu bakin yin ihu na don gigicewan danayi a lokacin sai idanuwana da suka firfito waje kamar mai shirin bankwana da duniya .
Ta koma inda ta taso tana fadin mara mutunci kawai kin cuci kanki wallahi ni baki cuceni ba zainab.
Dama an fadi tsintarciyar mage bata taba zama magen gida sai ta hada da halin sata ashe zancen da ake fada min inyi hankali dake a yadda nasakaki a jiki ba karya aka fada ba.
Har lokacin falon yai shiru kowa yana sauraren ta taci gaba da fadin wallahi yau ba zaki kwana min a gida ba har in maganan nan gaskiyane ya fada.
Kuma yanzun nan ba sai anjima ba zaki barmin gidana babu ruwanki da wata zuri,ata yar iska.
Kije can ku karata da tsitanki keda tambadaddun iyayyen ki da suka sakoki a cikin duniya suka watsar dake haka.
Kai haba mami this unfear wallahi yarinyar nan ina ta sani a garin nan da za ayi mata wanan irin koran kare haka bafa itace mai laifin nan ba dankine mai laifi mami ya mamud ya fada rai bace.
Tsam ya Jafar ya mike tsaye ba tare da yayiwa kowa magana ba a wurin ya nufo inda nake gurfane ina rusan kuka .
Dakatar dashi mami tayi ta hanyar fadin jafar kana taba ta wurin nan saina tsine maka yanzun nan .
Jin hakan ya dakatar dashi daga niyar tabanin da yayi da farko yana shafan kanshi a hankali batare dayayi magana ba ya juya ya zauna inda ya tashi din.
Wani marin mami ta sake kaimin saida ya yunkura daga yadda yake zaune kamar zai tashi a lokacin.
Iyami kina da sauran hankali kuwa hjy da take zaune tayi mutuwan kasko a zaune ta fada rai bace.
Kai na girgiza don jin muryan hjy din nace wallahi hjy ban san komai ba akan laifin da ake nufin na aikata yanzu.
Yi muna shiru munafukan banza da wofi kawai wa zaki kawowa rainin hankali a nan bayan kun asurce min da mugun alkaba,in kuna kauye.
Yanzun wani karya zaki fada muna kin dauka bamu san me iyayyen ki suke maki bane a can gida kin rikita min kanda na rasa gane kansa gabaki daya.
Hannu na dora a kai tare da girgiza kaina ina fadin wallahi mami ban taba tunane ko wayau aikata hakan ba ga kowa balle wanan da ake tuhuman na aikata din yanzu.
Yadda ta zaburo zata kara makana yasa nayi wurin hjy da sauri na kankame a jikinta ina fadin hj ki ceceni ku mayar dani wurin iyayyena don Allah wallahi ban aikata komai da ake nufin munyi ba asalima iyayyena basu san wanan zancen ba .
Mikewa yayi zubur tare da fadi cikin wani tsawa enough ya tsaya yana bin kowa dake falon da kallo na dan second kafin yace indai ba kasheta kuke son yi ba please mami ku barta hakana.
Nina mai lafi ba yarinyar nan da bata san komai a wanan zancen ba don nina ganta nace ina sonta a duk yadda kuke ganin take ni tayimin a hakan.
Hannu ya mika ya wufci hannuna daya daga inda nake gurfanen ya mike dani tsaye tare da nufar hanyar fita waje dani.
Kon binshi nayi da karfi nake fadin mami ki taimakeni ki cece rayuwana kada ki bari ya tafi dani don Allah mami kicece rayuwana nima yarkine mami.
Jin ya rikoni da karfi yana kokarin jana da karfi mubar falon da karfi na fara fadin innalillahi wa,innalaihim raji,un mami kada ki bari yaya ya tafi dani don Allah.
Ganin mami bata ko kalleni ba yasa na juya wurin hjy ina fadin hjy ki taimakeni kada ki bari a cutar dani hjy.
Hannu hjy ta mika mai tana fadin jafari miko min yarinyar nan nan kaga dai uwarku ta nuna yar nan yau bata kwana mata gidan nan .
Mami ta juyo a fusace tana fadin hjy bafa zanbar yarinyar nan gidan nan ba yau taje can ta hadu da yan duniya irinta su dace.
Nasani iyami yar ba zata kara awa daya ba a gidan nan ko ince ba zamu kara awa daya ba a cikin gidan dani da yar nan.
Kai mamuda jeka ka da dan uwanka gamu fitowa ke kuma tashi ki shiga ki hado duk wani abin bukatanki dake gidan nan.
Na dan tsaya nawa hjy ta daka min wani uban tsawa na mike tare da dan dingisa kafata da yai min nauyi ina shiga dakin naja na tsaya daga kofa ina bin dakin da kallo kamar yau na fara shiga dakin.
Jin takon tafiya an nufo kofan dakin yasa da sauri na matsa wurin wardrobe dina na bude na fara fitar da takarduna sai wayana dana dauka na tura a school bag dina.
Hjy ta shigo a cikin wani irin yanayi dakin wanda ban taba ganinta a cikin shi ba ta nufi wurin jakkar kayanta tana kokarin dauka da karfin Allah.
Da sauri na karasa wurin ta na fada saman jikin ta ina fadin hjy idan kinyi haka kamar nice sanadin hadaki da yarki Allah ba zai taba yafe min ba kan hakan.
Ni ba donke zan bar gidan nan ba yau don kare mutunci da martaba na haihuwa gun yar dana haifa da idon ta ya rufe a gabana take wanan irin tujaran da nuna dan adam ba kowa bane a wurin ta.
Kamar yadda ta rantse nima haka yau din nan ba zan kwana a gidan nan ba sai mu tafi dake duk inda Allah ya nufa mu kwana a can.
Ina ji ina gani ban iya tabuka komai ba hjy ta fice da dan jakkar ta a hannu ta nufi falo dashi simi simi na biyo bayan ta dauke da jakkar school dina wanda shi kadai na iya dauka a gidan lokacin.
Kowa na tsaye cirko cirko a falon yanayin su babu dadi mami ke zaune ta sada kanta kasa a cikin wani irin yanayi na damuwa dkn bansan abinda ya faru ba bayan barina falon lokacin.
Yanzu da gaske hjy tafiya zakiyi don wanan maganan zaki bar gidan nan ai koshi yaya din baice hakan gaskiyane ba har yanzu.
Amma ke kin tashi kin hada kayan ki wai gida zaki bari saboda an taba yar dakinki ko ?
Kada ka kawo min diba albarka ta fada tana kallon jalal da yai maganan a lokacin a hasale kafin ta juya wurin ya mamud tana fadin mu tafi ka kaimu titi ka barmu a nan zamu samu na Annabi da zai iya taimaka muna daga sama do na Allah basu kare ba a duniyan nan.
Ta juyo inda nake tana fadi shige mu tafi kafin su halaki a gidan nan don an mayar dake bare.
Simi simi na zo na wuce a gaban su duk suka bini da kallo mami bata iya cira kai ta dago daga duken da kanta yake ba ga wayoyin ta suna ta kara naji jamal na fadi Aisha ki kashe wayan nan ga baki daya don Allah su daina damun mu haka.
🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
3️⃣8️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
FATAN ALHERI GAREKU MASOYA UBANGIJI YA SADAMU DA ALHERUN SA YA TSARE MU DAGA AIKATA SABO KOMAI KANKANTASHI AMIN, , ,
Nagode yan uwa da adduan ku gareni ubanginji ya yayewa dukkan musulmi damuwan shi a duk inda yake Allahuma Amin.
Sai bin hjy nake a baya tana jaye da hannu ina faman share hawa da hannuna daya.
Min karaso security din ya jafar suna tsaye cirko cirko a gaban gida suna dakon mu da fitowan mu kokarin amsan jakar dake hannu mu suka shiga yi lokaci daya.
Zuwa wurin motan da suka riga suka bude kofufinta tun kan mu iso wurin motar kofan yana a bude suna jiran isowar mu.
Ba bata lokaci mu shiga sai wani girma da suke bamu kamar yadda suke bawa ogan su bayan mun zauna a motar sai ga ya mamud da dan saurin shi yana fadin hjy kuje zan shigo zuwa an jima ko safe inda kuke ina son naga mami ne a yanzu.
Kada ka dami dani mamuda zauna da uwarku kada ta aikata abinda bai dace ba ga dan uwanka.
Saida safe sukayiwa juna suka kama hanya damu duk da kuka nake bai hanani kallon titin garin ba don ba fitan dare nakeyi ba a garin.
Wani gida da zance yafi na mami tsaruwa da komai ga motoci nan zube kamar wurin sayar dasu suka shiga damu gidan.
Bayan motar ta tsaya ne da sauri security din dake gaba ya fito daga motar ya bude mana muka fito daga cikin motar zuwa cikin gidan a tare da biyu daga cikin su sai faman nan nan suke damu kamar wasu manyan baki.
Gidane har gida don in tsaya fadan tsarin ginan zai bata muna lokaci yanzu ba zaka taba cewa wai a wanan kasan wanan ginan yake ba duk ko da lokacin darene don goma dare har ya dan gwauta a lokacin.
A falo muka zauna a daidai lokacin da sako ke shigowa wayan wanda nake gani shine babban su ya duba tare da daukan jakkar hjy da nawa zuwa sama.
Bai dade ba ya dawo da sauri falon suka fita ina makale a jikin hjy har lokacin don kamar dumin jikintane zai tsimakamin ga abinda nakeji a rayuwana.
Muryan hjy ne ke fadin kinga dagani haka kada ki karasani yar nan ina yanzun dai komai yazo karshe a wurin ki.
Ban daga din ba sai kara shiga jikinta danayi a lokacin bata kara tanka min ba illama tausayina daya kara shiga jikin ta a lokacin.
Sun dawo dauke da ledojin abinci a hannayen su tare da abinsha dayan da ban taba tsamanin yana jin hausa bane yake fadin hjy ga abinci oga yace mu kawo maku kuci mu tabbatar da kunci kun koshi kafi mu fita yana magana cike da bada umurni a gareni.
Kaiya dan nan wani abinci zamu ci a wanan halin kaimu inda zamu yada kan mu kafin gari ya waye mu kama gaban mu ko yanzu don darene da zance ka kaimu tasha kawai mu shiga motar kaduna zuwa gida.
Don nasan idan Allah ya saukemu kaduna lafiya gida ba zaiyi wahala a garemu ba.
Umurnin ogane mu sa kuci abincin nan kafi ku kwanta ya fada yana kokarin bude abincin dake gaban mu da sauri yaci gaba da fadin ki taimakemu tsohuwa kuci abincin nan kada mu samu matsala ga aikin mu don Allah.
Jin abinda ya fada yasa jikin hjy sanyi ta dago habana tana fadin kinga tashi koba dadi ya zama dole muci abincin nan don wanan mai kiran samudawan yabarmu mu zauna lafiya gidan nan.
Abincine irin na gani na fada sai kamshi ke tashi kallon abincin nayi na kawar da kaina daga kallon shi ina kokarin komawa in kwanta.
Kinsan duk wanan abin don ki nakeyin shi don haka kada ki bari mu samu matsala dake a wurin nan hjy ta fada batare da ta kalloni ba.
Dole na mike na sauko daga sama kujeran zuwa kasan wani kafet mai laushi dake shimfide a falon komai na gidan abin kallone.
Jin abinda hjy ta fada yasa na fara kai abincin a bakina a hankali duk da ba komai nake diba ba sosai a spoon din.
Bai wuce sau uku ba ina kaiwa a baki sai ga amai na shirin zubo min ganin hakan yasa hjy fadin ki barshi ida bakyaci kada ki jawa kanki wani matsala kuma.
Haka yasani tashi daga wurin na koma inda nake kwance da farko na kara nadewa a cikin hijjibin da Allah ya taimakeni na dauko kafin in bar gidan mami din daga shi sai rigar dake jikina kawai na fito dashi gidan da mami tayi min koran kare akan laifin da bani na aikata ba.
A can gidan mami kuma bayan fitar mu daga gidan tare da hjy mami ta kasa furta komai ga yaranta sai shiru da tayi tana faman karkada kafafuwanta a hankali.
Ita kadai tasan irin yanayin da take ciki a lokacin don yanayin da take jin kanta zuciyar ta zai iya bugawa take a wurin idan tayi yunkurin yin magana a lokacin.
Ya mamud ne daya dawo daga rakamu yake fadin mami da baki bar hjy sun tafi ba a cikin daren nan wanan abu bai dace ba mami hjy fa tai fushi dake sosai mami tunda har ta iya sa kafa ta bar gidan nan.
Jajjayen idanuwan ta ta dago tana fadi da kyat mamud ya kake son inyi da hajiyan mu a gaban ka akai komai amma kaji irin hukuncin da hjy ta yanke min a karshe.
Yau an wayi gari saboda wanan yarinyar mahaifiyata tayi fushi dani haka a rayuwana don kawai, , , ,
No mami don Allah ki daina fadin don zeey ce hjy tayi wanan don yaya J ne gashi a zaune badon zeey hjy tayi fushi dake ba mami jamal ya fada a cikin bacin rai.
Mami kina saurin fushi yanzu wanda hakan bai dace ba idan munyi maki haka ba zaki taba jin dadi ba a rayuwan ki don me zaki bari har wanan zancen ya kaiku haka da hjy .
Aurene dai an riga an daurashi a bisa jagorancin kawu hamza da baffa sulaiman da sauran yan uwa da abo, , , ,
Mamud zaka bace min a wurin nan kafin rayukan ku ya kai ga baci ko sai na saba maku gaba dayan ku wurin nan zaku fice ku bani wuri.
Mikewa tayi kokarin sai kafanta ya kasa daukan ta da sauri jalal ya karaso inda yake ya kamata zuwa daki ko kallon inda sauran suke bata kara yi ba.
Saida ya kaita daki ya zaunar da ita saman gado tare da tambayan ta ko akwai wani abinda zai mata a lokacin.
Kai kawai ta iya girgiza mai ya juya yana kokarin fita daga dakin yaji ta ambaci sunan shi haka yasashi juyowa gare ta.
Jalal ta sake fada ina son kai min aikin siri a gidan nan kayi kokarin bincika min inda yayan ku yakai hjy da yarinyar nan.
Haka kuma ka saka ido ga duk wani motsi na yayan ku har idan ya bar gidan nan ya fita kamar yadda na haneshi dayi ka fada min.
Yace insha Allahu mami zanyi abinda kikace yanzu kuwa zan saka ido ga duk wani motsi nasa Allah yai maka albarka ta fada tana kokarin hawa saman gadon da kyau tare da fadin ka turo min Aisha yanzun nan yace angama mami ya fita.
Ya turo mata Aisha shi kuma ya fice wurin dan uwanshi don yasan yana can yana jiranshi don bai ganshi a falo ba inda ya barsu.
Yana shiga ya samu jamal kwance rigingine yayi filo da kanshi ba tare da ya dago ya kalli dan uwan ba yake fadin.
Yanzu kaine dan leken asirin mami ashe a gidan nan kallon shi jalal yayi da sauri yana fadin yaya akayi ka sanda hakan yana kaiwa zaune gefen shi.
Nasan hakan zai faru kowama yasan da hakan ya dago yana fuskantar dan uwan tagwaicin nasa kafin yace dashi.
Amma kasan idan ka fadawa mami wani zance kan ya jafar kajawa kanka matsala a gidan nan ko ?
Hauka nake da zan fada mata wani abinda zai kara jefata a cikin damuwa komai ba zan fada ba koda kuwa nasan inda suke din .
Kaje ya j na kiranka ya fada yana komawa kwance bai tsaya ba ya nufi part din dan uwan nasu.
Ya sameshi yana waya don haka ya dakata a wurin har ya kare wayan shi inda ya fahinci dan uwan nasu yana shirin barin kasan a lokacin.
A hanku zan bar hjy da yarunyar nan don ni zan koma wurin aikina ina da aiyukan da suke jirana a can ya fada ba tare daya kallo dan uwan nasa ba dake gefen shi.
Amma bro in mami ta fahinci hakan zamu shiga cikin fushinta muna don yanzu ta ban assgment a kan ka da inda kuka kai hjy din.
Fine yana da kyau ka fada mata ai ban kaisu ko ina ba sai gidana da ba wanda ya sani nan cikin garin abuja .
Akwai wani abu kuma ya fada yana dago kai don kallon fuskan jalal din dake tsaye a gefen shi.
Zamu kulasu yadda kakw so saidai nasan mami zata saka ido muma a kan mu why not ka wuce da yarinyar nan gaba daya ku bar kasan nan a tare.
Ba yanzu ba ya bashi sa yana mikewa zai shige bedroom din shi ya barshi a wurin amma bro in har ma, , , ,
Ka iya bakin ka ya fada a gagauce ya shige ya barshi wurin tsaye girgiza kai yayi ya fita tare da rufo masa kofa ya bar dakin.
Mami kan wanan daren yadda taga safiya haka daren yazo mata don hankalinta a tashe yake har lokacin abinda zuciyar ta ke bata shine nine na jawo komai tsakanin mahaifiyar ta da danta.
Taga laifin anty safiya yafi dubu a wanan daren daga baya kuma ta fara hangen nacin jafar ne ya jawo wanan matsalan haka.
Don me su baffa zasuyi mata haka har su daurawa danta aure da wata yar aikinta ba tare da sanin ta ba ma,ana dai sun goyi bayan yayi mata rasgin biyayya ke nan ko me ?
Idan ko hakane zata nuna masu itace uwa a gareshi ba su ba don wanan auren yadda suka daurashi dolene su warwareshi da kansu kamar yadda sukaje aka daura din.
Washe gari haka ta tashi babu karfin jiki a tare da ita har hakan ya jawo mata saukan kasala a jikinta ta kasa fita zuwa office wurin aiki.
Kiran da ake mata a waya baya shiga yasa hjy maria nufo gidan mami din tsit ta samu gidan don ranan harsu kande sun shiga hankalinsu a gidan gani irin tashin hankalin da kowa yake cikin sa.
Don a gaban su komai ya wakana tsakanina da mami din da kuma hjy da irin hukuncin da hjy ta yanke a karshe wanda hakan ya kara daga masu hankali suna ganin wautar mami din data yarda har hjy tabar gidan dani.
A falo mami ta samu bakuwar nata ba tare da an kawo mata komai na motsa baki ba gaban ta wanda da ina gidan da yanzun na gama cika gaban bakuwar mami din da abin motsa baki koda kuwa ba zata taba komai daga ciki ba.
Duk da mami na a cikin fushi hakan bai hanata kwalawa sabuwar mai aikin ta kira ba tana tambayan ta dalilin rashin kawowa bakuwar ta ruwa.
Tace hjy kiyi hankuri bansan da zuwan ta bane tafi ki ban wuri da wanan magana kina ina har ayi bako baki sani ba meye aikin ki a gidan nan maza ki dauko mata kafin ranki yakai ga baci.
Ta juya wurin bakuwar data rike haba tana kallonta da mamakin abinda ke tafe da ita hjy maria kin taso ashe ta fada tana kaiwa zaune.
Na taso hjy maryam keda wanan labarin daya karade garin nan ko ince kasan nan baki daya jiya ke kuma ga wayan ki a kashe.
Tsuki mami taja tana fadin yaron yanzun aisai ka barshi inda ka ganshi ni yanzu ba zancen shine abin damuwa ba a gareni sai zancen hjy na data sha min yaji kan wanan maganan.
Subbahanallahi ta fada da mamaki tare da fadin mama din tayi fushi akan me kuma har hakan ya faru ?
Kan dai zancen nan daya fada don me zan dauki mataki hjy tace tare da nuna fushin ta a gareni.
Dama abinda yake so ke nan a tsakanin mu ai ya aikata hakan don yasan zata kama mashi ba hjy ba kawai could you imaging wai har da yayana da kanin mahaifinsu yaron nan yabi ta baya suka tsaya mai aka daura mai aure ban sani ba.
Kai ki bari don Allah hjy maryam suko don me zasu mana haka yaro da gatan shi ai mashi wanan aure na mumuke kamar mara gata.
Mami tace ai sai su san yadda zasuyi su walwale wanan auren don bai dauru ba wallahi indai nina haifi abina.
Hakkuri za ayi abi abin a sannu tunda an riga da an daura a yanzu sai dai in wanda zaki maine ya biyo bayan wanan din.
Kai ina nerve hakan ba zai yuyu ba ina fada maki ni har yanzu ai ban gama yanke shawara kan zancen ba don uffan bance da shi ba har yanzu.
Ranan dai haka kawayen mami sukai ta zuwa gidan wai da sunan zuwa tayata murna jin danta yayi aure ashe basu sani ba kowa dai da irin gulman dake kawo shi gidan.
A karshe dai mami tace duk wanda yazo masu gadi suce ta fita wani meeting sai dare zata dawo gidan.
Bata ga shi ba kuma bata tambaya ba saima da darene ya mamud ya shigo da likita tana falo a lokacin ya tsaya gaida ita yake fada mata ya dauko likitane ya duba Jafar tun safe yana kwance a dakin shi.
Bata tsunka mashi ba balle Allah ya sauwaka har suka shiga suka dubashi suka fito likitan yai mata saida safe.
Tana kallon yadda yan uwan shi ke sintiri a part din shi a karshe ma tashi tayi daga falon ta shige dakin ta da zuman ta kwanta ta huta ko zata samu barcin da batayi ba a daren jiyan.
Sai kuma ta samu dakin ba a gyare ba taja tsuki da masifa ta nufo waje tana kwalawa hannatu mai aikinta sabuwa kira da dan karfi.
Sai gata da sauri tun kan ta karaso mami ke fadin wai ke ko kinsan aikin ki a gidan nan kuwa.
Hjy nayi wani laifin ne kuma meya hana ki gyara min daki mami ta fada cike da takaici a fuskan ta a daidai lokacin ne kuma jamal yazo yana fadin.
Mami ya J fa baya jin dadi sosai tun safe yau a kwance yake bai kuma ci komai ba har yanzu.
Jamal ka ban wuri da wanan shirmen yaje ya kashe kansa idan zai iya indai kan wanan zancen ne ba zan taba yarda ba.
Amma mami ai da kin je kin, , , , jamal na fada maka ka kauce min a wurin nan kafin ranka ya baci kaima.
Jin hakan jamal din ya wuce a fusace ya nufi part din yayan nashi don ya kara duba halin da yake ciki.
Zama tayi a falon tana jiran Hannatu mai aiki ta karasa gyara mata dakin inda ba a dauki dogon lokaci ba hannatun tafito tana fadin hjy na gama.
Ta dan dago kai tare da fadin ok kawai ta mike don komawa dakin ta zauna saidai tana sa kai a dakin wani irin arm odor ya daki hancun mami kamar a lokacin hanne ke cikin dakin nata don hamamin warin hammatan dake tashi a dakin.
Da sauri mami takai bakin mirrow ta dauki room fresh tana fesawa a dakin a cikin takaici ta aje ta nufi bandakin don ta dan kewaya.
Bata saba ganin wurin nata a haka ba yasa bata tsaya jiran komai ba tafito ban dakin baya ta daure ta kewaya a matse.
Cikin takaici ta zauna bakin gadon ta tana jan tsuki tare da fadi a fili wanan banyi tsamanin zamu kai ko ina da ita ba.
Wanan gyaran daki kamar mahaukaciya ko yaro yana wanan aikin haka tana fada tana karasa shirin kwanciya matawa tayi ta dauko kwalin maganin ta da take sha duk dare kafin ta kwanta barci.
Tsuki taja tana bata rai tare da jin wani bakin ciki a ranta take ta fara tunanen wani abu a wurin wanda ya kara bata mata rai maganin dai a ranan mami bata shashi ba haka ta kwanta don kiuyan da takeji zuwa falon .
Baku zata iya kiran hanne yar aikinta takawo mata maganin don wani irin tashi da dakin kanyi idan yar aikin nata ta shigo dakin.
Mukan tun safe muke saka idon ganin wani daga cikin su yaya bamuga kowa ba hankalin hjy ya tashi don tacewa dayan security din ya kaimu tasha mu shiga motar kaduna..
Yace aiko bakin kofan gidan ba a bashi daman ya barmu mu taka do ance ya kulada mune sosai

3️⃣9️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
FATAN ALHERI GAREKU YAN UW MUSULMAI UBANGIJI YA KARA MUNA IMANI A ZUKATAN MU AMIN, , , , ,
Babu wanda yazo wurin mu a gidan har kwana biyu tun hjy na daurewa har ta fara magana a fili ina jinta don ba wani magana nake iyayi ba a lokacin don zunlumin da nake ciki da fargaba.
Naji hjy ta fara fadin kamar tana zargin jikokin nata anya kuwa ya yan nan suna da gaskiya kuwa zasu dauko mu su dangwaran a wanan gidan babu wanda ya waigomu a cikin su kaf.
Idan an dan jima kuma zakaji tace ni mamuda nafi ganin laifi shi da keda wayau ya barmu a nan zaune ga masu zubin kafirai din nan sun hanamu motsawa nan da can.
Da iyanzu ai mun tsufa a gida da wanan zaman bamzan da bamu san dalilin yin shi ba a nan, wa yan nan katan banzan da suka saka gadin mu kamar mun aikata wani mugun abu.
Nidai bankan tankata idan tana wanan magana don tsorona Allah tsorona mami da bansa matakin da zata dauka a kaina da iyayyena kamar yadda ta fada ba.
Don har yanzu idona yana da kwancin jinin marin da taimin a fuskana yasa idona yai alaman kwancinyan jini ta geden dama.
Ga damuwa fara exam dina dake damuna shima don ina ganin nayi hasaran shi ke nan idan ba, Allah ya gyara ba ina da rabo a rayuwa lokacin.
Wanan yawan jininin na hjy yake kara tayar min da hankali tare da sakani tsoro da abinda take yawan fadi ko yaushe.
Saida mukai kwana hudu cur a gidan ba tare da wani ya lekomu ba ga zaman kamar zaman takura da mukeyi .
Iyakan security din nan ya shigo ya tambayemu abinda muke bukata duk daba wani amsa yake samu ba wurin hjy bai hana idan lokacin cin abinci yayi ya dawo garemu yana tambayan abinda muke so a kawo muna.
Koda bai samu amsa ba haka zai kawo muna abinci mai rai da lafiya da kuma abin motsa baki wani lokaci.
A yammacin kwana na hudune hjy ta sha fada har ta gaji saiga yaya mamud da Jamal sun shigo gidan muna zaune a falo mukaji shigowan su.
Da sauri na mike zaune don a kwance nake a lokacin don jikina babu karfi saboda tunanen da yai min yawa a lokacin.
Har kasa nake ina gaida su kamar yadda na saba a koda yaushe idan ina gaidasu din a cikin girmamawa.
Da sauri na mike don barin falon a lokacin hjy ta dubeni da kyau tana fadin ina zaki kuma ke ?
Dan dago kai nayi na kalli hjy tare da fadin zan shiga dakin ne hjy ki tsunci uwarwa a dakin ai yanzu tunda sun tuno damu fitan su fitan mu a gidan nan.
Shiru su yaya sukayi sai dan bina da satan kallon tausayi da yakeyi yana kawar da fuskanshi gefe daya hjy dake gefe taci gaba da masifa tana fadin.
Haka kawai , daku da uwarku zaku sakamu a gaba haka da wullakanci kamar kun samu marasa daraja da galihu kuna wullakantawa kamar baku san inda muka fito ba.
Ko uwar takuce ta hana ku biyoni nan don na mara maku baya kan abinda Allah bai haramta ba take kokarin ita ta haramtashi.
Dan murmushi ya mamud ya sake yana neman inda zai kai zaune da kyau tare da fadin korata kike kenan yanzu mu tafi.
Ba koranka nake ba ta sake fada gwanin ban tausayi kafinta tace kasan hakan da kukai muna baida kyau mamuda dole raina ya dinga baci.
Hjy kinsan lamarin mami saida tako dan haka muka nuna mata muma bamu san inda kuke ba a yanzu haka.
Don ta dauka kuna gida samu,naka sai yau da mama Ramatu ta bugo waya take jin bakuje can ba hakan ne ya tayar da hankalinta yau ga baki daya.
Kun min daidai yaran nan gara da kuka nuna mata hakan itama dana haifa bata san darajana ba ta barni a cikin dare nabar mata gida.
Kada ku yarda ku nuna kusan inda nake wasan dadi sai kun barta ta ji jiki da kyau kafin ku nuna mata inda nake.
Ke wanan tsohuwar da mugunta kike yanzun ma da mami ke cikin wani hali bai maki ba sai kin kara fitgita muna ita ke nan .
Ja,iri uwarka kake goyon baya ko mai na kasa daurewa daga inda nake zaune haka yasa na mike tsam zuwa dakin da muke kwana da hjy.
Gaba dayan su suka bini da kallon tausaya min hjy dake zaune ta nisa tare da fadin ina shi jafarin yanzun ?
Yana gida baida lafiya ne aida kun ganshi nan tun ranan ya mamud ya fada yana mikewa tsaye tare da fadin .
Yanzu ma shiya turomu muyi maki bayani don kada kiji mu shiru don baida lafiya sosai yace a gaida ke a tambaye ki idan ba wani matsala a tare daku.
Ko kuma idan wanan gidan bai maku ba a canza maku wani ya fada kai wanan shike kara saka kuna shagala da duniya diyan nan.
Wanan gidan ko a fina finan zamani ina na taba ganin irin shi da zai wani ce idan bai muna ba a canza muna wani.
Fada mai ni ba wanan ne yanzu a gabana ba canjin gida ko wani abu kawai ina son in koma dakin mijinane albshin shi yazo ya dauki matarshi ya san inda zai nufa da ita kuma .
Don dai yar nan ba zata koma gidan iyami da zama ba har abada indai da sunan irin wanan zama na wullakancin nan da tayi a yanzu.
Shima ai ba zai taba hakan ba hjy yanzu damuwan shi shine da wanda yarinyar nan zata zauna a karshe a gidan nan don ta karasa karatunta kafin ya bar kasan nan da ita.
Hjy bata iya ma ya mamud magana ba sai wani kallo data watsa mai kafin tace au ashe shi ba zancen mayar da yar nan hannun iyayyen ta yake a yanzu ba ?
Don Allah hjy ki bar wanan zancen kedai yanzu munzo muji zaki zauna a nan tare da yarinyar nan nadan wani lokaci ko gida samunaka zaki koma a nemo muna wace zata kula da ita.
Jikin hjy gaba daya yayi sanyi lokaci guda ta fara fadi a hankali yanzu yar nan idan na tafi na barta a haka yadda take tsorancen nan anya ba zata fada wani hali ba nan gaba don ko yanzu a firgice yar nan take nan.
Goshi ya dafe kafin yace hjy mami ta kafe shima jafar ya kafe da nashi kudirin wanda kowan su yana da nasa manufa a nan.
Zama hjy ta gyara a cikin mutuwan jiki ta fuskanci ya mamud tare da kura mai ido tana fadin mamuda ka hango abinda na hango gun dan uwan ka ke nan ?
Wanda uwarku ta kasa zama ta natsu ta gane me yake nufi da kakaman shi a kullun kan wanan yarinyar don ni har gobe zuciyata ta kasa sakewa da wanan zancen.
Don girman Allah idan akwai wani abinda kasani a game da dan uwanka ka fada muna mu sani tun yanzu.
Ina mara masa bayane ga kudirin sa don samawa kanmu mafitan da yake fada a kullun daga bakin shi kada idanuwan mu su rufe akan kudi daga baya muzo aji kunya.
Hjy abinda nake fadawa mami ke nan amma mami ta rufe idon ta gaba daya da za,a barni sai ince an canza mana mami din mune yanzu.
Murmushin manya hjy tayi tare da fadin yaro yarone itace dai iyamin ba wanda ya canza maku uwarku, sherin mulkine da lokaci ke rudin rayuwan ta ya aiki a kanta yanzu.
Sun dan dade zaune da ita suna mata bayani yadda zata fahince su a karshe dai suka yanke shawaran daya dace akaina da kuma hjy din.
Sun dawo gida sun samu mami zaune a falo suna shigowa mami ke fadin mamud anya ba boye min kukeyi ba kusan inda hajiyan mu ta shiga kuke boye min haka ?
Mami anbicika yarinyar ma bata gidan su ne ya tambaya kamar mai son jin amsa a lokacin.
Ni rashin sanin inda take bai dameni ba yanzu inda mahaifiyata take shine damuwana a yanzu mami ta fada cikin kunnan rai.
Mami ba saidana fada maki ba a ranan kinsan hjy sarai da rigima wai ita ta waye yanzu gashi tana shirin ballowa mutane aiki yanzu.
Jamal ka fice ka ban wuri kafin ranka ya baci a nan mami kyaleshi hjy ba zata bata ba a cikin garin nan ai insha Allahu.
Ta juya tana basu baya a cikin damuwa satan kallon juana sukayi kafin ya mamud ya mike yana fadin barin leka part dina in fito mami.
Har ya fara takawa yaji muryan mami ta tana fadin shi jafar din har yanzu yana kwance ne wai yake nufi ?
Mami yau fa saida dr Smith yazo har gidan nan ya dubashi jin bata furta komai ba yasa ya fara tafiya don barin gurin nata sai yaji tace me yace yana damun sa da yazo.
Jin abinda ta fada yasa shi juyowa gareta ya fasa tafiyan da yakeyi a lokacin yana fadin mami ba wani abu sukace ba ai su hudune da abokan aikin shi suka shigo dayan ke fadin ya saka wani abu a ransa sosai ne ya jawo mai hakan.
Baki mami ta tabe kafin tace idan ya halaka kansa akan wanan diyar tallakawan shiya sani don dai a karshe shizaiji kunya akan wanan yar har yake wanan shegantakun haka.
Dan murmushin takaici dan uwan ya sake daga haka ya juya ya fice zuwa part din su bai nufi wuri shi ba saida ya biya ya gaida jafar din wanda a lokacin ya dan ji saukin jikin yana zaune a saman dogon kujera a mike kafa.
Jikin shi na saye da jallaniyan maza sai bakin dogon wando dake kafan shi sai fararen santala, santalan kafanshi da suke a mike yana dan karkakadawa a hankali.
Jin shigowan mutum a dakin yasashi dan juyowa yana kallon kofan tare da sauke idanunshi kan dan uwan nasa daya shigo.
Har kun dawo ke na ya fada a cikin wani yanayi mai nuna alaman yana dan jin jikin shi har lokacin.
Mun dawo ina tare da mami a falo tun dazun ya mamud ya fada yana kaiwa zaune tare da kallon dan uwan nasa kafin yace dashi kun zauna da hjyn dai ko ?
Hjy ko yar rigima mun zauna saidai ta kafe akan lalai sai su tafi har gurin iyayyen yarinyar nan zainab sun zauna dasu kafin ta dawo nan ta zauna da ita ko kuma a turo wani ya zauna tareda ita din.
Saidai ita ta tafi ta barta nan don ba zan so tayi missing din exam din ta ba a yanzu bana son tayin kukan hakan akaina ya fada yana yamutsa fuska.
Yau zan je gidan da dare idan naji sauki da sauri ya mamud ya dago kai ya kalleshi tare da fadin kasan duk wani motsi mami ta saka muna matakan tsaro ko dazun da dabara muka kai gidan ai.
Baida matsala don ni a yanzu ko mami ta sani ba matsala bane a gareni yanzu don kawai kace mu fito mata ta wanan hanyar.
Kasan mami yanzu sai a hankali lamarinta zan daiso mu bita a sannu din ya mamud ya fada yana mikewa tsaye.
Bai samu zuwa gidan ba kamar yadda yacewa ya mamud sai kashegari ne da ya kasance weekend ya fito zuwa don fita .
A falo ya samu yan uwan shi tare da mami ya fito cikin shirin shi tsab ya nufo inda suke zaune ya zauna a tsakiyan mami da Aisha yana dan jingina jikin shi a jikin mami din .
Cikin rashin ko in kula abinda ke faruwa a tsakanin su da mahaifiyar nasa normal kamar yadda suka saba a tsakanin su.
Daga haka kowa na fira ya ja bakin shi yai shiru lokaci guda sai Aisha dake zaune a kusa dashi takura mai ido cikin tausayin yanayin shi take fadin.
Ya J jiki yai sauki ke nan sai ina kuma yanzu ta fada a cikin zolaya sai taga bama sauraren ta yakeyi ba a lokcin.
Aisha tayi masa kuri da idanuwa tana kallon shi sai tausayinshi ya kamata lokaci guda ta sake fadin ya J ko jikinne har yanzu you look so warried.
Shiru bataga ya motsaba hakan ya tabbatar mata cewa yayi zurfi a cikin tunane gyara zama tayi a cikin kulawa a gareshi ta kara ambatar sunan shi da ya J ya akayine wai ?
Yayi firgigit ya dawo cikin hayacin sa tare da sake mata takaitaccen murmushi a fuskan shi cikin dan basarwa ya fuskamceta yana fadin.
Aisha ina tunanen tafiyanane ga kuma yarinyar nan zata fara zana exam a cikin kwanakin nan.
Da sauri Aisha ta dan saci kallon mami dake zaune a gefen su kafintace ya j wace yarinyar kake magana ?
Yace wife dina ko akwai wata da zanyi zancen ta haka a gaban ku bayan ita kin sani kin san ba wanan a gabana ai Aisha.
Da sauri Aisha ta dukar dakai kasa a daidai lokacin da yake mikewa tsaye yana fadin zan fita daga can zan leka asibiti in dubasu.
Aisha najin abinda yayan nata ya fada tayi saurin dago kai ta kalleshi da mamaki take girgiza kai tana kallon shi tare da fadin.
Amma ya j ka tafka babban kuskure da har ka daurawa kanka aure da wanan yarinyar da tsiya ya saka iyayyen ta sakota shigowa duniya don neman kudi.
A fusace ya juyo yana fadin shut up Aisha enough enough what ever she is, now she is free from that.
Idan ba zaki taimaka ki samo min mafita akan zainab ba to ki ja bakin ki kiyi shiru da maganan matana a gabana haka.
Kar ki manta she is part of us now don ta zama daya daga cikin mu ke nan kamar kowa wani kallo mami ke jefa mai kamar an hanata magana a lokacin.
Ba wai wani abu bane ko tunane mami keyi tsaban mamakine kawai daya rufeta a lokacin ya hanata nagana don gaba daya sai take ganin yanayin shi ya sauyawa sanin ta a yanzu.
Itako Aisha sai kai take girgiza mai tana fadin ya j kada ka tafka babban kuskure kazo daga baya kana daka sanin hakan da kayi.
Don tallaka ka barshi yanzu inda ka ganshi da tsiyar shi shine mami ke maka nufi ba komai ba ya J a matsayina na kanwarka ina mai baka shawara domin mami ba zata taba yarda da ita a matsayin daughter inlaw din ta ba tunda tasan asalin ta tun farko.
Waike Aisha ba zaki kamawa mutane baki ba a nan ke meye naki a cikin zancen nan manya na magana ki dinga saka masu baki haka.
Har ya fice falon mami sai faman tunane take akwai wani abinda ke damun dan nata domin gaba daya shi yanayinsa ya canza mata.
Babu alaman jin nauyin ta a idon shi ko bin zabin ra,ayinta kamar yadda ya saba nuna mata a baya don zata rantsewa da cewa yafi ko wani yaro mata biyayya a cikin yayanta kaf.
Duk maganganun da yayi a lokacin bai daga mata hankali ba sai bakon yanayin data fara hangowa a tare da dan nata ne hankalin ta ya fara tashi da hakan.
Ta shiga sake sake a kasan zuciyar ta ya zama dole gateta ta fuskacin danta tasa yanayin da yake ciki har ma idan asirine ta san wani irine aka jefoshi dashi.
Don tasan matakin da zata dauka kafin dan nata ya kaiga shiga wani hali bata farga ba do zuciyar ts na raya mata jafar din yanayjn sa y canza ga baki daya a dan kwanakin nan.
Ina zaune na rafka uban tagumi sai hjy dake sallah a gefe naji an turo kofan shigowa falon da muke din.
Jin haka yasa ni saurin dago kai don ganin wanda ya shigo falon duk da dai nasan mazan nan ne dake faman dawainiya damu tun zuwan mu gidan basu huta ba.
Saidai kuma dago kan nawa yayi daidai da shigowan ya jafar din falon da daddadiyan muryan shi da yake sallama daga inda yaja ya tsaya tsaye fuskan shi a gurina kai tsaye.
Sallaman na amsa a daidai lokacin da yake lumshe idon shi a cikin wani irin yanayi kafin ya bude yana mai takowa zuwa in da muke zaune.
Kaina na sada kasa cikin sauri a daidai lokacin da hjy ta shafa tana fadin yau a gidan duk da ina cikin fishi daku har uwar taku.
Ya karaso inda take yana murmushi mai hade da sautin dariya yana fadin a yafe muna nima hankalina yana gurin ki ga baki daya wallahi.
Sai daya zauna suka fara gaisawa dashi yana tambayan ta ya zama kadaici ya kuma hakkuri da abinda ke faruwa.
Tace duk suna nan tanayi saidai zaman ne gaskiya guri daya ya isheta hakana gara ta koma gida dakin ta ta zauna a can zaifi mata sauki.
Ya juyo a rikice yana fadin meya faru ne ko security din dake kula damune sukai mana wani abinda bai dace?
ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
4️⃣0️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
FATAN ALHERI GA YAN UWA MUSULMAI UBANGIJI YA KARA MUNA IMANI A ZUKATAN MU AMIN, , , , ,
Yadda na zauna na makure kamar ban falon a lokacin don yadda nasha jinin jikina tun bayan shigowan shi falon.
A hankali ya dago kai ya dan kalli gefen danake kafin ya bude baki a hankali yace ya kike cikin nuna basarwa yai maganan ta hanyar daukan remote yana kunna tv dake kashe baya aikin.
Ban iya bashi amsa ba don tambayan daya jefo min yai min nauyi a lokacin sosai.
Saida ya kunna tv yakai tashan da yake so ya sake juyowa inda nake zaune a takure yana fadin ya naji kinyi shiru koda wani matsalane kuma ?
Hjy ce tayi karfin halin bashi amsa tare da fadin ba dole ba matsala dai yafi wanan ka kawomu nan ka aje kamar wasu marasa galihu haka.
Balle wanan yar bata tare da wani matsala tunda tana tare dani a yanzu ai murmushi zancen ta yayi yana gyara zama yace.
Nagode hjy nagode da nuna kaunar ki garemu da ba don ke ba da komai baizo a sauwake haka ba yanzu.
Sai da hjy na rasa meke damun mami har yanzu mami taki ta amince min aka ra,ayina, a rude na dan dago kai na dubeshi don jin abinda yake fadi a lokacin.
Hjy naji tana fadin ka barta da kanta zata gane gaskiya ta biyo hanya don kanta amma gaba dayan ku saikun daure sai dai kafin hakan nafi tausayin wanan yar da ake nunawa hakan a yanzu.
Na sake wani irin ajiyan zuciya da bansan fitowan shiba lokaci guda ina mayar da kaina saman kujeran da nake zaune.
Daga hjy har shi lokaci guda suka juyo suna kallona sai shine ke fadin me ya faru zainab yanzu kuma ?
Jin an ambaci sunana yasani dan dago kai daga yadda nake a zaune ina a hankali nace ba komai idanuwana suna kokari sako da hawaye lokaci guda.
Idan da son samu ne ka bari muje in gana da iyayyen yarinyar nan ko hankalinta zai kwanta don yanzu gaba daya hankalinta ba akwance yake ba da kowa a nan.
Idan hakan zai kwantar mata da hankali sai a shirya tafiyan ku hjy indai haka ba zai shafi karatun ta ba da zasu fara jerabawan su nan da mako mai zuwa insha Allah.
Ba matsalan komai ai itama da alama bata wasa da karatun ta don duk wanan halin da take ciki bai hanata karatun nake gani ko yaushe tana rike da littafin karatun naku.
Muryan shi na sake jin yana fadin zan koma hjy zuwa gobe an gama maku shirin tafiya in Allah ya yarda sai zuwa gobe da dareb zan shigo insha Allah.
Kaji namijin gaske haka nake son mutum da saukin hali ko yaushe ba irin uwarka da ta kasa gane hakan ba har yanzu.
Oh hjy kina akawa mamina ido da yawa har na fara jin kosawan hakan a yanzu acikin alaman mamaki hjy ta katseshi da fadin Allah ko ?
To da kaida uwar taku duk saina juya maku baya muga ta tsiya a yanzu kuma .
Yana dariya ya mike tsaye tare da fadin ko zaki daina sai bayan kin gama min aikina sai ki juya muna bayan ba matsala a lokacin .
Amma a yanzu sarkin yaki idan kika ce kin juya min baya ai ban san ta inda zan fara kamawa ba a nan.
Tashi ki takawa mijin ki mana kina zaune wuri daya haka hjy ta fada tana jifana da harara a take annurina ya kara gushewa lokaci guda na hade fuskana ga baki daya.
Bazaki tashi bane a hakan har zaki kai ga yadda ake so kina wanan sanyin jikin haka da wanan yawan matan dake dakon shi kamar dan sarkin das.
Simi simi na tashi tare da daukan hijjab dina na saka akaina na fice a falon cikin sanyin jiki nabi bayan sa kamar yadda hjy ta umurceni dayi din.
Ban san da tsayin shi gaf da kofan ba, saida na iso gurin ne nakusa cin karo dashi a guri yana tsaye ya dafe kofan falon da hannu daya dayan yana waya dashi.
Da sauri na dan ja baya tare da fadin yi hakkuri bansan kana nan ba a tsaye maimakon ya amsa min sai idanuwan shi manyattatu daya watsa min lokaci daya kafin ya saki wani shu,umin murmushin da bai kai ciki ba yana fadin.
Kai na kawar gefe daya ina bata rai tare da turo baki gaba saboda neman hanyan da zan samu kawai nake in fita daga kangin shi ga baki daya.
Madadin inga fuskanshi ya sauya ga abinda nayi mai rashi ya baci sai kawai naga yana min murmushi kamar ba jafar din dake da aji da class mai yawa haka ba yanzu a gabana.
Hakan dana gani yasa a cikin dakewa nayi kokarin juyawa ina fadin dama hjy ce tace wai na biyoka nayima saida safe wai ina fadi har na juya na fara tafiya do barin wurin.
Muryan shi na tsin kayo yana fadin ashe da badan ita ba baki san ki zo ki sallami mijin ki ba haka zamuyi dake idan mun tare a gidan mu.
Ko irin tarbiyan da kika koya ke nan a yanzu baki san ki girmama na gaban ki ba kuma baki san tarbiyan ki na daga cikin abinda nakeso ba fiye da komai.
Kalaman da yake fadi suka saka jikina sanyi a lokaci guda har ba kasa aiwatar da dan shirin dana kulla a zuciyana kan nayi mai rasgin mutunci ko zai rabu dani gaba daya a rayuwana.
Sai gashi ya buge ga yabona wanda naji dadin hakan a raina don kowa ba son a yabeshi a rayuwan shi.
Sai dai duk da hakan na dan turza dan zuciyana ta ban kwarin gwiwan fada mai magana nace ya Jafar.
Don Allah kaji tsoron Allah ka rabu da rayuwana a yadda ka ganni kowa yasan ni ba yar kowa bace ban taba tunanen irin kalaman da mami suke jifana dashi ba a yanzu.
Sai gashi a sanadin wani bukatan ka a kaina yakai mami tana aibantani tana aibantamin iyayyena da basuci ba basu sha ba a ka wanan magana.
Kasa nakai gwiwa bibiyu a kasan tare da hada hannayena biyu guri daya ina fadin ya jafar na rokeka da kafita harkata kabar rayuwana ya samu sallama.
Yau sanadin ka mami ta koreni gidan ta tayi min kazafi kala kala dani da iyayyena a gaban kowa har sai yaushe kake son kaiwa ga fita a cikin rayuwata hakane ?
Duk wanda ya ganmu a yanzu haka yasan bamu dace ba don ruwa ba sa,an kwando bane ansan ni din ba ajin ka bane sai dai idan da gaske yadda nakejin ana fada da wata manufa kake son yaudarana.
Kamar yadda mami suke fada kowa yasan kaiba tsaran aurena bane yaya tsadadden namiji kamar ka sai mace mai irin ajin ku bani zainab yar matsiyata ba haka don Allah ya jafar ko wani irin manufane a zuciyar ka katai makeni kabawa mahaifiyata ni kada in halaka.
Hjy kaka ita kadai ce mai kaunata tsakani da Allah gaba dayan ku yaran mami a yanzu ban yarda da kowa ba a cikin ku ina maijin wani kunci da bakin cikin a zuciyana saboda abinda ake min a gidan mami.
Wanda hakan ya kara nuna min banda gata da daraja dama a idon kowa wanda hakan ke kara haifan min da kunci da bakin ciki duk a sanadiyan halin daka jefani a ciki.
Jin nayi shiru don kukan daya zomin a lokaci guda yana tsaye a inda yake kamar an dasa shi a wurin yana tsaye yai kasake idanuwan shi a kaina sai zuba hawaye nakeyi a inda nake tsugune na hada hannayena wuri daya alaman ina rokon shi.
Tunane barkatai yake a gurin da yake tsayen ya zuba min idanuwa a lokaci guda ya na kallon yadda nake magana cikin fitan hayaci a tare dani ya rasa lalubo mafita yadda zai haneni fadin abinda nake fadi a lokacin.
A hankali ya fara takawa don barin wurin ba tare da ya iya furta komai gareni don bai san amsan da zai iya ban ba a lokacin yasa ya zabi yabar wurin kawai zaifi mai saukin sauraren kalamina a lokacin.
Duk da bashi ke tuka motan ba haka bai hanashi jin wani iri ba a lokacin don ji yake damuwan shi na kara shiga damuwa a lokacin gareshi.
Motar na tsaya ya fito bai tsaya jiran a bude mai motar ba ya diro daga baya motar ya nufi hanyar shiga cikin gidan.
Wayanshi ce ta dauki kara ya tsaya ya duba ya mamud ne ya gani a layi bai tsaya jiran komai ba yake fadin
Kana ina gani nazo gidan ka wurin su hjy ban sameka a nan ba ya fada yace gani na dawo gida yanzu na barcan din na zo gida.
Kada ka shiga ka jirani a waje ka ban mimtuna kalilan gani tafe insha Allah ya mamud ya fada ya amsa da OK sai kazo.
Daga haka ya mayar da jikin shi gurin motar daya fito ya jingjna jikin shi a kai tare da tunanen dalilin dakatar dashi da dan uwan nasa yayi waje.
Kodana koma ciki hjy tana zaune a inda na barta tayi min kallo daya ta kawar da kanta gareni nasan hakan bai rasa nasaba da shigowan da nayi ina sharan hawaye a fuskana lokacin.
Don irin yadda ta kalloni din yasa na sake shan jinin jikina din tare da samun wuri na rakube kamar wata marainiya dani.
Ban dago kai ga kallon ta ba sai faman dan share fuska da nake lokaci lokaci na tsinkayo muryanta tana fadin.
Yarinya kin takurawa rayuwanki kin hana kanki kin hana rayuwa ki shakat babu farin ciki kullun sai tsangwama sai tashin hankali.
Shima da yake namiji kuma ya dauki duk wani laifi ya hada a kanshi shi kadai bai tayarwa kanshi da hankali haka ba kamar ke.
Mikewa nayi ba tare da nayi magana ba na nufi dakin da muke kwana a cikin sa na daura alwala tare da gabatar da sallah isha,i na kwanta.
Ita hjy a nata tsamanin fushi nake don kawai in koma hannun mami da zama ko wani abu can a nata fahintar ta kasa gano inda na dosa da wanan damuwan da nake saka kaina a ciki.
Don a tunanen ta ai hutu na samu na rayuwa ga hakan don ta dauka nasan koshi din waye da matsayin da yake dashi a lokacin.
Ban kara fita falon ko neman abinda zanci haka na kwanta sai da asuba ba falka koshi itace dai da bata fushi ta tayar dani daga barcin.
Bayan na idar da sallah ne naji muryan hjy na fadin idan kin sallame kije falo akwwi sakon ki a can yai min nauyi ne naga gara dai na barshi falon harda safe.
Ban damu da nasan ko sakon may ba don ni gaba daya yanzu kowa ma haushin sa nake ji idan mutum ya shafi bangaren mami din.
Taci gaba da fadin yanzu sun canza magana wai yau din nan zamu bar garin nan karfe bakwai na safe don haka ki tasho ki fara shirin tafiya ta kare da bani umurni.
Dan juyawa nayi na kalli bangaren da take zaune ina mamaki a raina yadda kowa ke juyamu yadda yaga dama tun yanzu na fara fuskantan abinda ke gabana gaskiya talauci wani abin kine a rayuwa don zance talauci ne ya jawo min wanan gararan ba da walagigin rayuwa tsakanin mami da ahalin ta a yanzu.
Badan naso ba namike don zuwa falo saboda abinda hjyn ta fada a karshe da cewa wata kila akwai wani fitinane kuma daga wurin uwar tasu yasa suka sauya ranan tafiyantamu.
Nima zan fi so ai mu tafi yau hjy na matsu in bude idona in ganni a gaban iyayyena hakana .
Au ashe ni ke nawa haukan ke nan yar nan ina ce ai yanzu daga gidan nan sai dakina zamu dira idan mun tashi nan.
Ban yarda na juyowa ba a lokavin don jin abinda ta fada din don bansan amsan da zan bata ba kuma idan har na tsaya din don tsohuwar ta cancanci kawaici sosai a wurina.
Akwatinane har uku a tsakiyan falon da sauran tarkace da ban san meye a cikin su ba tsaye nayi daga kofa kamar mai nazarin kayan a lokaci sai da murya hjy din ya dawo dani hankalina da sauri na dan zabura tare da kaucewa a hanyan da nake tsaye.
Karaso man ki gani ta fada tana kaiwa zaine a saman kujera ga carbi a hannun ta tana ja tace jiya kin kwanta yaron nan jamal ya shigo da kayan nan .
Tare da bayanin yau karfe bakwai na safe mu zauna a shirye kafin su shigo ban daga a wurin ba kuma banda niyar hakan .
Kina tsaye kimkam dake a wuri daya ki zauna in maki bayanin komai kamar yadda sukai min kan kayan.
Hjy ba sai na ji komai ni kawai a mayar dani gida ko zan daina jin abinda nakeji a zuciyana.
Af kinsan Allah idan kin mun tsiya yanzun nan zan saka a fasa tafiyan nan ga baki daya, da sauri na dago ido na dan kalle ta sai kuma abin ya dan ban dariya nake fadin .
Hjy ba haka nake nufi ba ai kawai dai na fadi hakan ne don ki ce wani abu gashi ko kin fada din tace yo dama ai nasan don ni kika fada ai.
Don shi jafarin baya laifi a gurin ki sai ni da kika raina yar nema kikewa shegan taka irin haka ko ?
Kinga maza dauki kayan na kije ki saka idan kinyi wanka donni nan da kika ganni a shirye nake ko yanzu suka shigo gidan nan na gama shirina tsab.
Kallon ta nayi da mamaki a fuskana kamar zanyi magana don dai ni kan bana son in taba komai a cikin kayansu karshe mami tazo tai min gori tunda ma yan kayan dana tara a gidan ta bata yarda nabar gida da ko tsunketa ba .
Haka na fito tsula sai dan jakkar littatafaina da nayi karfin halin daukowa a lokacin don ba zan taba yarda in zubar da karatuna ba a duk halin dana samu kaina a ciki.
Sallaman da akayi a kofan dakin ne yasa mu dago kai don amsawa da sauri naja baya ina gaida shi yace zeey baki shirya ba ke nan yanzu ya J ya umurce ni daga massallaci in nufo nan nakaiku airport direct.
Yanzu nan zancen da nake mata ke nan maza dauki wanan jakkan ki shirya a gurguje bamu da lokaci hjy ta fada .
Ba musu na dan dauki jakkan data nuna min zuwa ciki ban tsaya ba wanka na shiga agurguje din da tace na fito.
Sai lokacin na bude jakkan dake makare da kaya nau,i, nau,i na mata da sauri najawo wani jan material dake sama ko tsayawa dubawa ban yi ba.
Sai danake sakawane na fahinci tsadan kayan a lokacin tsab na shirya a lokaci na fito na samu suna magana kuskus da jikan nata saidai gaba daya yanayinta ya sauya lokaci guda.
Kalma daya naji shine tace ai gara ayita ta kare yau din a gaban iyayyen yarinyar nan tunda ba lalama take so ba ita.
Jikina yai sanyi a hankali na tako zuwa inda suke hjy ta kalloni tana fadin kinbar kayan a ciki ne kuma don yanzu tafita zamuyi daga nan ba zancen karyawa a nan kuma.
Zan mike ya jamal yace barshi na dauko da kaina ya mike ya shiga dakin bai jima ba sai gashi da dan troler din hade da school bag dina dana bari a ciki.
Babu wani alama daya bari na shedan mun zauna a gidan kafin mu bar gidan zuwa airport ba bata lokaci jirgin mu ya daga, don mun so makara zuwa wurin.
Baifi yan mintina ba ni a ganina sai gamu kaduna har jirgi ya diremu ko ga motoci sunzo daukan mu a filin jirgin .
Nikan ina biye da hjy a bayan ta sai ya jamal dake directing din mu akan komai motan bai tsaya damu ba sai Anchau.
Abin kamar a mafalki nake ganin shi son tafiya sai yake min sauri kamar masu tafiya a gajimare ba a mota ba.
Ba farga a garin mu nake ba sai lokacinda aka karya kwanan unguwar mu abin ya ban mamaki matuka sai kawai gamu a gaban gidan mu.
Mota biyu mukai amfani dashi a tafiyan ina kokatin fita daga motan don zumudi naji hjy na fadin ki bi a sannu ki tuna kina da aure a yanzu din.
Don haka ki natsu sosai ki tuna ko a nan din kina da makiya tare da mahasda da zasu so suga faduwan ki don haka sai ki natsu kiwa kanki fada da kamun kai ki fara nuna yanzu ba da bane garesu.
Hakan yasa naji wani iri n natsuwa yazo min lokaci guda na tuna da abinda na bari a gidan namu tun farko don haka har gyalen jikina saida na gyara yafashi kagin a bude muna mota don mu fito a lokavin dirin motar yaja hamkalin kannena sun fito don ganin ko waye yazo.
Sannu a hankali aka bude kofan daga waje a bangaren da hjy take zaune kafinta ta fito a hankali ta sauka daga motar.
Driver ya dawo bangaren da nake zaune ya bude min kofan a hankali na dan dauki lokaci kafin in sako kafana a kasa na sauke su a cikin kasan kofan gidan namu.
Kyau ta kalman dake kafana kawai ya isa daukan hankalin wanda ke gurin a lokacin na karasa fitowa waje ina dan gyara gyalen kaina da kyau a hankali.
Duk yadda zan kwatanta maku haduwa a lokacin ba zaki gane yadda shigan ya mayar dani ba sai dai idan kin gani a gaban idon ki.
Takalma iri hill shoes din nan ne fari sol a kafata sai madaurin sarka fari da yake dashi.
Dinkin material din dake jikina mai kama da half gown sai ta kasan shi akai ado da wani yadi mai kama da lace mai kore da baki a jikin shi.
Hannun rigan yana da dan shara sharan hannaye har zuwa kasan hannun.
Hjy ce gaba ina daga bayan ta rike da yar karamar jakka mai kama da post a hannuna shige guda da takalmin kafana ina takowa a hankali.
Ga kannena ina gani kamar in shaka in rugume su sai dai ina ganin irin kallon basu gane mai shigowan ba da suke min a lokacin.
Sai da muka karaso gaban sa,ade a hankali na bude baki kamar ban son magana tare da fadin haka aka koya maki taron baki.
Wani ihu ta yanka tare da fadin wallahi yayan muce ta kwasa cikin gida da guda tabar kayan da take suyan awara a kofan gida.
Ihun tane ya jawo hankalin kowa a gidan yayi daidai da Abban mu na gida dakin lantana a lokacin duk da misalin sha biyun rana ne lokaci ya nuna a garin.
Abin mamaki sai ga innan mu a guje don ranan bata nuna wanan kawaicin ba nata da take nunawa a kaina na yar farin ta.
Saidai gani tare da hjy yasa taja ta tsaya kuma da dan tsohon cikin ta da ya fara baiyana a lokacin a jikinta.
Nikan ganin inna taja baya ta tsaya don ganin tsohuwar mai kamala da muke tare yasa na kasa daurewa na nufi wurun inna a cikin sarsarfa na rugumeta.
Ina jin wani farin ciki da shaukin ganin mahaifiyata da nayi yau sai nake jin kamar anyayye min duk wani matsalolin da nake ciki a lokacin don ganin mahaifiyana a gabana.
Wai abune kowa nake gani haka a idona Asabe ke fadi daga bayan mu ta fito daga dan lungunta ds yanzu duk ya gama yakucewa ba gyara kamar farko da Abban mu ke yawan gyara mata idan ya dauko lalacewa.
Itace fa Asabe sa,adaty ta cabe tana fadin yau Allah ya dawo muna da yar uwan mu gida yan bakin ciki yau kan sai dai su mutu ko a kasa barci don bakin ciki.
Masu farin ciki kuwa yau barci harda nasari don Allah ya baiya na gaskiyan shi a filin Allah kowa ya gani.
Daga inda hjy take ta amsa da fadin kwarai yar nan dama haka al,amarin Allah yake ai idan ya tashi ikon shi ba wanda ya isa ya hana hakan.
Yau ga yar ku ta dawo gare ku a matsayin matan jikana al,amarin aure daga Allah yake matar mutum kabarim sa.
Da sauri Asabe tace balle munan ai kowa dan farin cikine da hakan ai hjy kayya hjy ta fada a daiyi sha,ani ai da ba haka akaso gani ga jikan nawa ba.
ZAINAB IDRIS MAkAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
4️⃣1️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
LITTAFIN KUDINE YAR UWA DON GIRMAN ALLAH KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA , IDAN KIN SAN DARAJAN ALLAH, , ,
DOMIN BIYA ZAKI IYA TURA KUDI TA WANAN LAYIN BAKIN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KI TURA KATIN WAYA NAGODE, , , ,
Bayan an zauna an natsu a dakin inna ina sai yan dabarun mata takewa hjy don taron ta duk da bata san ko wacece hjyn ba a lokacin.
Saidai cikar ido irin na hjy da kamala yasa kwarjinta ya dauki hankalin ko wa a gidan sai ga Asabe ta dawo tana fadin .
Sannun ku dai da zuwa ta kara fada tana kokarin shigowa daga cikin dakin takai gurfane.
Kaga Asabe do kinga yayar mu tazo da kama mai kyau har kina wani rawan jiki da zuwan ta a yanzu.
Duka inna takaiwa sa,adatu da bayan hannu tayi saurin gwaucewa tare da mikewa tsaye tana ja da baya don barin wurin tana magana ciki ciki.
Asabe na fadin rabu da ita sa,adatu ba hankali gareta ba ai koma me ye ai wanan zancan baya ne kike daukowa.
Duk abinda ke faruwa hjy na zaune ta lura da komai daga inda nake zaune ina mamakin yadda sa,adatu takewa asabe a yanzu.
Kamar ba Asaben da ko muryan ta mukaji a sa can baya sai gaban mu ya fadi don masifa da irin matsawa innar mu da sukeyi lokaci.
Amma sai gashi yanzu na dawo na samu suna mata abinda sukaga dama a gidan.
Haba dai sa,adatu ki daina haka mana na fada ina kallon ta don naga ran innan mu ya baci sosai a lokacin.
Kinga kawata yaki zonan ki kyale su naga sun taru a kanki ke kadai haka hjy ta fada tana mikawa sa,adatu hannu tazo wurinta.
A lokacin ne Asabe ke fadin ita wanan din ne hjy da kike aiki a gidan ta ko waye ita din tana kallona.
Kafin na bata amsa hjy tace a, a , aha nidin dai kakar mijin tane nice na haifi uwar mijin nata don haka ita din matar jikana ne yanzu.
Ikon Allah asabe ta fada sai mukaji zancen aure kamar a mafalki daga sama ba tare da wani sanarwa ba kawai.
Ai kin san aure habo ne shi idan lokacin yinsa yayi koda shiri ko ba shiri ranan sai anyi shi Allah ya nufa matar shice shima.
Har hakan ya faru da yar nan yarinyar arziki yar kirki aka dauketa aka mika a birni ba tare da an taba bin sawun wanan yar ba anga a inda take zaune ba.
Sai gashi ubangiji ya tarfawa garin ta nono ta shigo birni da kafar dama tayi gamo da arzikinta taci kuci har wani nata shima ya raba yaci ya huta a karkashin innuwar ta a yanzu.
Wani kuka Asabe ta sake daga gefen da take gurfane tana fadin yar nan naso cutan kaina da kaina da badan Allah ya gyara ba ki fada hannu na gari wa yasan hannun da zaki fada haka.
Na aikata abu a cikon duhun kai nabi zugin da ya jawo min zagi da zunde a gari kan na sayar dake a hannun yan birni.
Har zaure mai gari muke da iyayyen ki saida nayi rantsuwa akan ba sayar dake nayi ba a garin nan.
Allah da ikon shi an gama kulla min wanan sherin da kwana biyune zancen auren kin nan yazo muna garin nan a cikin bazata.
Wanda hakan kuma ya kara jawo muna kace nace a cikin garin nan wanda har yanzu mutane a kanshi suke wai ba a san mutum ba an dauki yarinya an bashi don kwadai.
Cike da takaici nake sauraren abinda Asaben ke fadi na rasa abinda ke mun dadi sai hawayen dake zubo min a lokacin a raina nace ni haka rayuwana zai kasance da barnan suna.
Wanan wace irin kaddaran rayuwace Allah ya jefoni a cikin sa don kawai ina ya mace nake gamuwa da wanan kaddarorin haka ko me ?
Da sauri hjy take fadin yo meye haka ana zaune kallau zaki sakawa mutane kula a nan haka godiya ya kamata kiwa Allah da yanufa ba abinda mutane ke zargi bane ya faru dake din.
Inna ma kuka take a lokacin cikin kunar rai tana fadin bari hjy munga abu a rayuwan mu kamar kaina farau haihuwa diya mata a duniya.
Diya mace alherine hjy ta tare inna tana fadi don ni nan nafi kowa sanin dadin hakan don uwarsu ce ta zame min gata ga zuri,a na.
Don haka ba za a zagi diya mace a gabana ba ban bada amsa ba don na haifa nasan dadin su a rayuwana.
Gyaran muryan da Abba yayi daga kofa inna yasa mu dan dago kai muka kalli kofan da alama daga barci yake a lokacin saboda yanayin shi ya nuna hakan.
Me kuma ya faru nake jin kamar kuka ke kenan baki gajiya dayiwa mutane kuka akan abunda baikai yakawo ba a gidan nan.
Bawan Allah kada kaga laifin yarinyar nan raba da da mahaifi ba abin wasa bane don kukan yanzu na zuwan yarta ne takeyi.
Sai akace don yarta tazo su mayar muna da gida kamar na makoki dama haka yana kallon Asabe data fada mai magana kamar ba Abban mu dana sani da farko mai taushi da sanyin raiba.
Fuska a daure ya juyo yana fadin mama sannun ku da zuwa ashe kuns hanya tafe ?
Hjy ta sauke ajiyan zuciya tana amsawa Abba gaisuwan a cikin dan sakin fuska sai bin kowa da kallo take tana mamaki a ranta.
Taci gaba da fadin tafe nake da jikana don taki sake jiki tun bayan zancen daurin auren nan dayazo muna bata a cikin walwala sam.
Shine na kawo ta gida zata kwana biyu mijin ta zaizo ya dauke ta su tafi don jerabawan da zata fara wani sati mai zuwa in Allah ya yarda.
Saidai zanso nasan ko akwai wace zamu samu daga nan da zata tafi ta zauna muna da ita a can gidan nata na Abuja.
Duk wanan bayani da hjy kewa iyayyena sai a lokacin nake jin komai daga bayanin da take masu din a yanzu.
Abban ya gyara zama yana fadin tau hjy abune dake son natsuwa a yanzu zamu zauna bayan tafiyan ki mu duba wace ya dace ta bita can din inda halin hakan.
Ba damuwa hjy ta fada tare da kara basu hakkuri kan yadda auren yazo batare da an gudanar da komai yadda al,ada ya tanada ba.
Duk sai naji na muzanta sosai yadda hjy din ta samu gidan mu duk da dama ai tasan tunda har na iya zuwa aikatau a birni babu abinda zata sama a gidan namu.
Ina tuna irin kallon kaskancin da Aishan mami ke min tun fara zancena da ya Jafar din wani kallon banza da raini take watso min aduk lokacin da zamu hadu.
Da ace daga cikin su ne sukazo gidan namu a haka Allah kadai yasan irin abinda zasu fada akaina kan hakan.
Saidai ita hjy babu hakan gareta zaune take saman tabarma da inna ta shimfida a dakin ta mike kafa hankalinta kwance dasu tana masu bayanin komai.
Abba ya mike ya fita yana fadin bari ya dan fita sai ya dawo a daidai lokacin da ya jamal ya bada tsaraban da sukazo dashi da kayana a shigo dashi gida ke nan.
Akuma fadawa hjy ta fito don rana nayi yau yake son ya koma Abuja ba zai kwana ba kaduna .
Har lokacin banga lantana ba ba kuma danta a wurin har nakai ga tambayan sa, adatu wai lantana fa ?
Saida ta tabe baki kafin tace dani tana dakinta mana tana bakin cikin da dawowan ki tunda tayi shela a gari da cewa wai an sayar dake gun yan birni.
Wanan bakin cikine irin na hassada ga mairabo taki ne don tasan yanzu kinfi gaban ta har abada don haka ki daina saka zancen irin su a gaban ki yanzu.
Fitan Asabe a dakin ya ba hjy dama yin zancen siri da innar mu sun dan dauki lokaci don gaba daya hankali na ga yan uwana da muke zuba hira agefe daya suna murnan ganina.
Yan iya magana sunce kafin kaga biri biri shiya dade da hango ka tundaga nesa karfe goman safe dirka dirkan motoci uku suka tsaya a kofan gidan da muka baro zuwa kaduna yau da safe, a daidai lokacin da mu ke kan hanyar anchau zuwa garin mu.
Su shiddane tafe mutum.bibiyu a mota dayasuke tafe saida suka karewa gidan kallon mamaki dan girman shi da tsaruwan shi kafin su nufi hanyan shiga daga ciki.
Masu tsaron gidan ne suka dakatar dasu da tambaya wurin wa suka zo kallo rainin wayau hjy saudat tayiwa security din tana fadin zai bude kofa su shigo ko sai ranshi ya gama baci yasan kosu suwaye da zai tsaya tambayan su suda gidan dan su.
Yana tsaye ko wace ta fito da abinda take fada mai a lokacin saidai ya kallesu kawai bai iya furta komai garesu ba.
Yasan mami don suna haduwa a can gidan da wani lokaci yasa mami karasowa wurin da kanta gaisuwan girma yaiwa mami din tare da nuna sanaya a gareta.
Tambayan shi tayi da fadin ko grandma da wanan yarinyar da ogan su ya kawo suna cikin gidan nan ?
Da sauri ya girgiza kai tare da fadin babi kowa a gidan su kadai ne a ciki ko zan iya shiga in gani da idona mami ta fada.
Kofa ya nuna tare da dan dukar da kanshi alaman girmamawa a gareta ta nufi kofan sauran dake mara mata baya suka bi bayanta zuwa cikin gidan.
Bin ko ina na gidan da kallo sukeyi komai na gidan abin kallone don ya tsaru iya tsaruwa dai a kasan nan ba karya a cikin sa.
Saida suka gama duba ko ina na gidan guide din na tsaye daga kofa ya rufe fuskan shi da madubin ido baki fuska babu sauki a gareshi.
Da hannu mami ta yafutu wanda ke tsaye a kofa kamar an dasa shi a gurin yazo da saurin shi cikin girmamawa gaban mami din.
Are you sure grany bata gidan nan ko ta zauna tare da wata farar yarinya haka kai ya girgiza yana fadin baiga kowa ba a gidan nan yana fadi yasa kai ya bar gurin ya koma inda ya fito da farko yaja ya tsaya ba tare daya kara kulasu ba.
Yaran nan me suka mayar dani mami ta fada a hasale ta soma tafiya sauran suka mara mata baya suka bar gidan cike da takaici a ransu.
Duk da mami bawai ta saba da ciwa mutane mutunci bane a yau kan data sameni a gidan nan da tayi min cin mutunci ta uwa ta uba don ta kula ba karya mutane ke fadi ba na asirce mata dane da saddabarun mu na yan kauye.
Don wai ba a sako mu daga gidajen a banza kafin mu bargida sai anshirya mu da asiri idon mu idon mazan wasu da yayan su kamar yadda ya faru a tsakanina da ya Jafar din yanzu.
Duk abinda hjy maria ke fadi a gefenta mami bata samu bakin bata amsa ba a lokacin don burin mami ranan shine ta same tayi min koran kare tsakani na da danta.
Inyaso daga baya sai ta nemi shiri da hjyn su su shirya a tsakanin su sai gashi tazo ta samu gaba daya ma yadda ta samu labari mun rigada mun bar gidan a lokacin.
Gida ta dawo bayan ta sallami kawayen nata na birni da yanzu suke manne da ita koda yaushe suna kara sakata shagalta da duniya .
Dakin ta nufa kai tsaye don ta samu natsuwa a yadda take jin kanta magani ta fara sha kafin tabi lafiyan gado ta kai kwance.
A daidai lokacin da barci ke shirin daukanta ne wayan ta yake ruri a jakka har ya katse bata daga ba .
Wani kirane ya sake shigowa again da tsuki a bakin ta takai hannu tana daukan wayan dake cikin jakkan tare da duban screen din wayan nata taga sunan mama Ramatun tace ke kiranta.
Ramatu ta fada a fili tana dauko wayan zuwa kunnen ta tayi sallama tare da gaida ita da kwana.
Sama sama ta amsa mata gaisuwan mama Ramatu ke fadin sai ga hjy ta dawo yanzu wai ashe tana kaduna duk wanan neman da ake mata haka.
Kaduna fa mami ta fada da mamaki kafin tace kaduna gidan wa ke nan wallahi wai ashe tana gidan hjy Tantano duk wanan neman da ake mata.
Wani ajiyan zuciya mami ta sauke kafin tace da wanan yarinyar suke ke nan ko ?
Wace yarjnyar Ramatu ta tambaya kafin tace au nagane ba tare suke ba gaskiya ita kadaice da kayan ta yanzu aka sauketa gida masu shi basu ko zauna ba wai suna saurine.
Guntun murmushi mami ta sake a fuskan ta tare da ajiyan zuciya tace Ramatu yanzun na yarda da ake fadin jika yafi da dadi wallahi wanan abinda hjy tayi min akan yaran nan.
Anywhere zan kira in an jima ki ban hjy din muyi magana tunda yanzu nasan mutanene a tare da ita ina fatan dai baki bari kowa yasan da wanan zancen ai.
Haba dai antyn mu tayaya zan dabawa cikina yuka da kaina kan wanan magana ai wanan ba abin bari na waje yaji bane ace hjy tayi fushi dake tabar maki gida har baki san inda take ba tsawon kwanaki haka.
Bari kedai Ramatu ko wa yan nan dake tare dani ai ban bari sun fahinci yaya kan zancen yake ba sam kinga min yar iskan yarinya zata ja a bagani a bangon jaridan kasan nan don tsiya.
Dariya mama Ramatu ta kwashe dashi tana fadin ai sai dai kada a kara amma wanan yarinyar ta rigada ta cuci mu saidai kawai a dauki mataki don gaba kuma.
Mataki kan kamar na dauka Ramatu don gaba dayab su saina nuna masu kuren su har shi jafar din ina binshi a sannu ne yanzu in samu akaiga auren nan shi da yar gurin saudat.
Har yanzu zancen yana nan ke nan da kawai ki barshi ai daga baya zao gane irin gatan da kike so kimai idan yaga matsiyatan daya jawo a jikin shi suna batun rufeshi da bani bani.
Barni da mara hankali mami ta fada tana maijin zafi a zuciyar ta kan abinda yar uwanta ta fada yanzu.
Bayan ta kashe wayan idanunta ya dade a runtse tana tunane kafin ta mike zubur kamar ta tuna da wani abu a lokacin.
Ficewata da dan sauri zuwa part din dan nata jafar har tana hada kafa a wurin sauri lokaci guda .
Tayi sa,a tana murda kofan taji shi a bude bata tsaya jiran wani abu ba ta afka ciki part din kai tsaye da sallama.
Yana zaune saman kujera sai farar takarda dake nade a hannun shi ya duka yana zukan farin garin dake saman dayan farar takardan dake aje saman table.
Wani irin ja tayi baya kamar zata fadi lokaci guda kuma tabi bangon dakin tana dafa a habkali don yai mata makari daga inda take tsaye.
Saida ta dafa bango ta samu numfashita ya dan daidaita ta samu fadin Jafar sai kuma idon ta ya sauka akan wasu tarin kwayoyin dake watse a gefen shi.
Da wani irin rawan jiki mami ta ke nunashi da yatsan hannunta tana fadin Jafar yaushe ka fara wanan halin ban sani ba ?
Yadda take maganan kamar wacce ke gudun wani yaji abinda take fadi din a lokacin a hankali ya dago kai ya kalli mahaifiyar nasa yana fadin .
Mami kiyi hakkuri bansan zaki shigo a yanzu ba har na kai ga shan abinda zai kwantar minda hankali.
Idan naci gaba da zama haka ban samu abinda zai taimakawa kwakwalwata ba zan samu matsala sosai shiyasa na sha wanan a yanzu don ya dauke mi ragamar hankalina na dan lokaci zuwa yanzu.
Don ba zan iya jure ji da gajin yadda kike kokarin hanani abinda nakeso a rayuwana ba mami sai kuma ya mika mata hannu alaman dai ya fara fita hayaci shi a lokaci.
Kamar wawiya haka mami ta koma lokaci guda do haka tabi hannun nasa daya miko mata zuwa gare shi.
Don bata son ko cikin diyan ta wani ya riskeshi a wanan halin da ita ta riski dan nata a ciki.
A hannu kuera ta zauna ta tsura mai idanu yayin da nasa idanuwan suke kamar a lumshe duk da tasa ba barci yayi ba a lokacin.
Kanshi ta dauka zuwa cinyanta ta fara shafa a hankali take hawaye wani na bin wani suka fara sintiri a idanun ta lokaci guda.
Babu abinda ya fado mata a rai sai irin wasoncin daahaifi su yabar mata kafin bari shi duniya akan ta kula mai da tarbiyan diyan shi kamar yadda sharia ya sharadawa musulmai.
Mami hawaye wasu nabin wasu ta kasa controling din su tuni kanta gaba daya har jikin ta ya dauki canji lokaci guda ta rasa wani duniya take ciki a lokacin.
Wai yau jafar dinta ne haka dumu dumu ta kama shi yana wana dabia da tafi kyamata ga diyanta.
Ta rasa meke mata dadi a ranta gashi tana son fita ta koma dakinta ko zata samu ta fasa hawayen ta su samu zuba kasa ko zataji sanyin abinda takeji a ranta.
Gashi kuma tana tsoron fita a lokacin kada wani ya shigo part din bayanta ya same shi a wana halin ko kuma ganta a cikin wanan yanayin da take yanzu a tambaye ta dalili.
Asalima idan son samune daga ita sai shi idan ya farfado ta samu ta gargade shin sosai kan hakan don ya tsira da mutuncin shi a idon jama, a.
Jin mami ta zurfafa ga tunanen da takeyi ne yasa shi dan dago kai ya kalle ta a hankali ya ke fadin go back to your room mami.
Idan na tashi za shigo muyi magana dake anjima murya cikin rada mami ta sake fadin zan koma amma sai ka ban duk wanan abinda kake sha yanzu na fita dasu dakin nan hankalina zai kwanta.
Murmushi yayi yana dan mikewa daga zaune tare da fadin kiyi hakkuri mami nasan na bata maki saidai nima din ba hakan naso ba dani.
Nasani jafar yarinyar nan ta cuceni ta gama min da rayuwa jafar a sanadin ta yau jafar har shaye shaye ka koma yi haka.
Cikin wani iri kuzari ya dago yana kallonta fuska daure kafi yace mami idan ma cutane ai yarinyar aka cuta tunda ita zata zauna da mashayi irina yanzu.
Wani irin sauti gaba mami ya bada lokaci don ji abinda yake fada a cikin maye jiki babu karfi ta mike tare da aza kanshi saman filo tana fadin .
Ka kwanta da wanan shirmen da kakewa mutane a yanzu yanzun ba lokacin maganan komai bane.
Murya kasa kasa irin na wanda baya cikin hankalin shi a lokacin kamar mai shiri barci yace iam telling you mami itace muka zalinta, , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
🦅 ABU CIKIN DUHU SIRI NE 🦅
4️⃣2️⃣
ZAINAIBA IDRIS MAKAWA
ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA DA FATAN KOWA NA LAFIYA UBANGJI YA BAMU HASKE GA AL,AMURAN MU AMI YA ALLAHU, , ,
YAR UWA LITTAFIN KUDINE KI TUNA HAKAN DON ALLAH KADA MU RIKE JUNA DANI DAKE DARI UKU NE KACAL SISTER TA BANK KO KATIN WAYA NAGODE, , ,
Kai duniya muji tsoron Allah wai mutane yanzu basa tunane ba a duniya za a tabbata ba zamu koma ga mahailicin mu Allah .
Amma saboda son kai sai kaga idon mutum ya rufe akan duniya ya manta da za a koma wurin ubangijin talikai ya dinga yin abinda ya ga dama.
Mami batai tunanen laifin daga gurin ta bane sai kokarin dora laifin abinda idon ta yagani akan dan nata yau takeyi a kaina.
Tana tunanen da badon ni ba da danta bai shiga wanan halin ba data sameshi a ciki don kawai wanan matsalan har yakai ga wai ya fara shaye shaye haka saboda idon ta ya gama rufewa a lokacin.
Ta dade kwance ita kadai a dakin kafin tayi karfin halin mikewa tsaye don zuwa gahatar da sallah la,asar da yayi tun dazun tun safe ta kasa kai komai a cikin ta har zuwa lokacin.
A Inda ta idar da sallah take zaune har lokacin tana cikin zulumi da tunane halin data riski dan nata a cikin .
Wayan dake gefen tane yake ta ringing ta kasa tashi ta dauka sai bin waya takeyi da idanuwa kawai a saman gadon.
Mami wayan kine fa ke ringing Aisha ta fada daga kofa tana shigowa daki lokacin idon ta akan mahaifiyar tasu dake zaune wurin da take sallah.
Dago kai tayi ta kalli yar nata a ciki wani irin yanayi na ban tausayi a gare ta da wanda ya ganta a lokacin dole ya fahinci bata a cikin hayacin ta.
Mami lafiya Aisha ta fada tare da kaiwa zaune a bakin gado tana kokarin daukowa uwar wayan dake kara saman gado.
Ajiyan zuciya ta sauke kafin tace duba min yayan ku idan ya dawo daga wurin aiki har ta mike tace ya mamud ke nufi mami kin yanzu bai dawo ba ai sai after six zai shigo.
Hannu biyu ta dauka ta dora a fuskan ta a cikin yanayin nuna takura a rayuwanta a lokacin sai kuma ta fashe da kuka mai tsuma zuciya da tashi hankali.
Take hankalu Aisha ya daga sai wanan lokacin ta fara nadaman rashin grany dinsu a tare dasu yanzu ina tasan zata dosa da wanan matsalan na uwar su da bata san abinda ke damun ta ba.
Mami Aisha ta fada a sanyayye mami lafiya meke faruwa ne wai dake barin duba idan ya j na gida na kira maki shi.
Karki soma ta fada a cikin wani murya mai nuna cikkaken umurni a gareta da sauri don tsoro ta koma ta zauna a inda ta tashi da farko.
Ido ta kurawa mahaifiyar tasu kamar tana nazarin ta kafin tayi karfin halin fadin mami koma meke damun ki kiyi hakkuri don Allah ki daina zubar da wanan hawayen haka.
Aisha will you believe da irin halin dana riski dan uwan ku yau a ciki koda yake barshi kawai bai dace ma in fada maki ba a yanzu.
Mami wani abin yayi kuma after all he has gone through na yin aure bai fada maki ba ko ya dauko zeey din ne zuwa gidan na kuma ?
Wani kallon takaici ta jefawa yar nata tare da mata gargadin ke yarinyace Aisha ta kawar da kanta ga kallon ta do takaici data kara bata na ambatan sunana a wurin.
Aisha ta dade a zaune tana kallon yanayin mahaifiyar tasu dake a cikin tashin hankalin data kasa gane dalilin hakan a yanzu.
Mikewa Aisha tayi daniyar barindakin dob ba zata juri ganin uwar a cikin wanan hali ba na bacin rai.
Sunanta mami ta ambata ba tare data dago kai a yadda take ba taci gaba da fadi kada ki fadawa kowa halinda kika sameni a yanzu.
Naji mami Aishan ta fada har ta soma tafiya taja ta tsaya tare da fadin but mami da sauri ta fara tafiya bayan hannu da uwar ta kara daga mata kuma.
Koda Abba ya dawo gida da dan ledan shi dayayo cefane din a dafawa hjy ya samu hjyn ta fito zasu tafi don azzarlazalan da ya jamal ke mata tafito kada su makara.
Af hjy wai tafiya zakiyi ne yanzu ga abin tabawa har na sayo a gyara maki kada kizo garin baki taba komai ba.
Cikk yar fara a da nuna jin dadin yadda ake kulata a gidan namu hjy tace ai yata ta gama ban komai yaushe rabona da nasha fura da nono haka mai dadi.
Ga kawata ta nuna Asabe bayan innar mu tana fadin ta kawo mi ganye shima na taba ko hakama aina gode.
Ta nunani tana fadin saidai ga matar jikana nan don Allah ina son a bata duk wani kulawan daya dace da ita don yanzu ita din ba abin wasa bane a guri kowa.
Kanne dakr gefe tsaye duk suka kalloni a lokaci daya don jin abinda hjy din ta fada akaina suna murmushi.
Nauyi da kunyane ya kamani lokaci guda muna gaba nan muka barta da Abba da innar mu da Asabe suna maganan abinda bansan kome suke fada ba a lokacin.
Muna tsaye a bakin mota tare dasu ya jamal duk da dai gaisuwa kawai mukayi dashi ya juya abinshi bai kara bi ta kan mu ba kuma.
Wanan fa mai kama da balarabe yayar mu amma dai bai iya hausa ba ko don naji hausan nasa kamar da turanci ya amsa mana.
Yayan mune ba bata amsa dashi batare da kara furta komai ba hankalina yana gun abinda suke tataunawa a kai.
Abba ya san fito ya bar hjy da innan mu sai can ta fito ta amemu a wurin motar hannu ta mika min na nufi wurinta don na gane abinda take nufi da hakan.
Dan rugumeni tayi kakar mai rada take fadin in kula da kaina zamuyi waya idan ta isa gida tana son in zama mai biyayya a duk yadda na riski kaina a ciki da mijina.
Nauyi da kunya ne suka dan rufeni saiga idanuwana suna dan ciciko da hawaye a lokacin guda kamar kada in rabu da tsohuwar muna kalo haka ta barmu a gurun suka tafi bayan alherin databi kowa dake wurin dashi na kudi.
Mun juya da zuman shiga gida muka tsinkayi muryan Abba da lantana har da innan mu da sauri muka karasa zuwa ciki don ganewa idon mu abinda ke guda.
Lantanace ta cikuwaikuye abban mu dake tare ta a dole sai ta karbi ladan da Abba yabawa inna mu a gyara min abinda ya sayo a yiwa hjy dan abin motsa baki.
Tunda na tunkaro wurin nayi arba dasu a halinda suke ciki na runtse idanuwana a hankali do abinda idona ya gane min .
Kai kai kai amma yar nan baki da albarka yanzun nan da bakin ma a gidan sai kinyi wanan saida halin da kika saba ashe.
Da badon mutane na sun tafi ba haka zaki barmu da abin fade a gidan nan saboda baki fitina irin naki.
Inna don Allah ki mika mata ko manene a daina wana fitina indai a kaina ne ake wanan abin na fada cikin dan marairaicewa inna mu din.
Ba ita kadaice mai bakin ci ba yau ina sin i gani idan na karfi ne tazo takwata tunda an fada mata mu bamu da hakki akan shi komai sai itace za a sayawa taci muna kallo.
Af don kin fadawa yarki tsoron karba zanyi ko me ni kunya ma kika ban ace wai yarka ta dawo yawon bariki haka tana haska gari har zaki tsaya fada kan wana dan ledan hannun ki.
Ina kwalayen da kaya dadin da aka saba zo maki dashi wanan karon ta kwabe ba a kawo din bane ko meye don naga kamar su dawo muka da gaiyan tsiyan ku gidane sun gaji da kwallon mangoro sun yar sun huta da kuda .
Inna mu dai bata sake ledan ba tayi daki dashi muka bita ga baki daya mu yan dakin namu saboda Abban mu dake wuri ya hana ai magana a lokacin.
Muna shiga daki akan kwalayen da aka jera a daki wanda lantana kewa gatse sa,adatu ta nufa tana tambayana ko kwalayen meye ina mata bayani .
Banso akaiwa lantana ba a lokacin kada ta dauka don gatsen da tayine yasa aka kawo mata din kuma in ba akaidi ba inna tace sai tace ai daga bayane aka sayo aka kawo muna.
Kwalayen madara ne na tea sai milor da sauran tarkacen kayan tea da katon din lemoka na sha masu tsada wani abinma sai baya mun bude muka ga meke cikin don har da kaji da ke dankare da kankara ga buhun shimkafa har uku ajiye.
Kamar ba gobe har ina mamakin hali iri na innan mu kamar ba yanzu lantana ta gama mata cim mutunci ba don haka aka diban mata komai aka kai mata Asabe hakan aka kai mata komai da mukazo dashi.
Mamakon injin tace a dawowa inna da kayan sai naji tana fadin wallahi karba zanyi ko yanzu don ba a barin mugu da makami ai.
Ba a san zafin nema ba tunda ba jikin mutum aka kurza ba wanda yaje shi aka sani kuma sunan shi ya lalace ai.
Kowan mu a dakin yaji me take fadi saidai da idanu kawai innan mu ta kallesu kowa ya shiga natsuwa a cikin dakin da alama dai warining inna ta bayar gaba daya a dakin .
Allah sarki wallahi yahanasu ko yau na fadi na mutu a gidan nan kin biyani don bani da kaico gurin haihuwan ki don yar ki zata iya rungumar ku a yanzu ta zame muna gata.
Gorin da aka zugani nasha maki na rashin haihuwan dana mijin yau ga diya macen ta jawo muna arzikin da za,a fade mu a gari muma.
Aiko Asabe bata rufe baki ba saiga lantana na fadin kai Allah mungode ma dadin mu da gobe saurin zuwa wallahi.
Yanzu ai sai muga ankai mutum makka shine zamuyiwa mutum ai murna ko a sauya mai gida kinga an rufe baki zagin diya mata a gidan nan ga baki daya.
Har sukayi suka gama ina lafe a dakin inna ban samu abindana fada ba sai faman tunane nake a kasan zuciyana.
A yanzu zancen ya jafar ya fara tasiri a zuciya don gaskiya innan mu tana so hutun da yake kira masu a yanzu.
Ba inna kadai ba har yan uwana da Abban mu shi kanshi yana bukatan kulawan daya dace a yanzu.
Kafin innan mu ta karasa girkin ta har barci ya daukeni a gurin saida akai kiran sallah a zahar kafin sa,adatu ta tayar dani daga barcin da ya dab daukeni.
Sai lokacin na fito waje tun bayan shiga dakin daga wurin rakiyan hjy da muka tafi tun lokacin ban fita wajen ba ina dakin mahaifiyar a ciki damuwa .
Nazo gida ban huta ba a can kuma ba zancen hutu ko kwanciyan hankali a gareni fara ma nan din na samu na lafe a dakin innan mu din.
Bamu samu natsuwa da inna ba sai dare baya kafa ya dauke ne muka zauna zaman hira da inna din.
Ban boye mata komai ba yadda komai ya faru a tsakani na da mami na labarta matashi a cikin daren nan ko zan samu sa,ida ga abinda nake ji a raina.
Ikon Allah Inna ta fada tana ajiyan zuciya tare da fadin wata sabuwa cakwakiyar kenan ke shirin tunkaro mu ashe.
Yanzu ita hjy da kanta take kyamatar ki da danta don kina yar tallakawa ko don wani mugun halin naki da koka boye min bansan da shi ba ?
Da sauri na dago ido duk da babu wadattacen haske a dakin lokacin inna taga kallon razanar da nayi mata alokacin .
Inna ki yarda dani da tarbiyan da kuka dorani tu farko ban kara wani hali ga wanda kika sanni dashi da farko ba ban yarda duniya ta rudeni ba inna don nasan kudi daine iyayyena komao dadewa wurin ku zan dawo zaman can din na dan lokacine.
Kafin in kara inna ta tare da fadin kimar ki da kamalanki ne ne basu kai ta hada iri da ke ba kamar yadda mafi yawan masu hannu da shuni suke da wanan akidar bawai ke dince bata so ba a zahiri a yadda na fahinci zancen.
Inna bata sona yanzu sam zama kawai nake a gidan dan hjy da danta daya jamin duk wannan abin a yanzu.
Inna har fa sata mami da yar ta suka dora min a gidan sai da shi dan nata ya biya kudin yakuma sakatar dani duk wani aiki da nake a gidan da sunan biya haka na zaune a cikin su babu walwala ko sakewa komai akan hattara da tsamgwama nakeyin shi gidan na karasa fadi a cikin kuka.
Subbahanallahi wanan wani irin rayuwa muke shirin fuskanta karfin mu ba daya ba balle na nuna jayyaya ko nace zan kwatar maki hakkin ki garesu.
Bazanyi izzigili acikin sha,anin aure ba don aure abune mai rai da Allah ya hallita kamar rayuwa idan kaddara sai anyi shi idan kuma zama ya kare ko ana so sai an rabu a tsakani.
Shine dalilin da yasa akeson musulmi ya yadda da kaddaran ubangiji maikyau ko marakyau ka yarda daga Allah komai yake.
Kuka na sakawa inna don gareta kadai na dogara da zata tsaya ta kashe wanan auren don ita kadaice nake hango gatan mu a gareta da tausayawa don Abban mu yanzu sai a slow tun shigan lantana rayuwan shi.
Da mamaki inna ke kallon yar nata a cikin tausayi da kulawa take fadin menene ne a ciki aure ne bautan ubangiji kowace mace da yadda akasin nata yake zo mata.
Idan ma wani mugun haline gareshi har yake boyewa na roki Allah a sandiyar ki ubangiji ya sauwaka mai ko menene a rayuwan shi.
Idan kuma da zuciya daya ya aureki ubangiji ya kara mashi sonki da kaunar ki a rayuwan zaman ku tare da zuri,a masu albarka.
Bazan taba ja da ikon Allah ba don haka kema nake gargadi ki da ki yadda da kaddaran ki a yadda tazo maki.
Allah yasan hikimar daya shimfida a nan ya tsameki daga cikin mu ya kaiki can cikin su kika zauna tare dasu har hakan ya faru yanzu.
To a barwa Allah sanin sa a hakan illa iyaka gobe zan turaki can gurin kawuna Inda addu,oin da zai baki sai ya taimaka muna dashi kafin nan nizan fara zuwa naimai bayanin komai insha Allahu.
Dan sheshekan kuka nakeyi kafin inna tayi shiru tana saurarena ba abida nake tunawa sai irin tsana da kiyayyana da yanzun nake hangowa a idon mami din ko yaushe.
Sai zuwa can naji inna tace yoke ai ya kamata ki hankalta tun daga yanzu ki sancewa ubangiji mai sonki ne yar nan baki da wani zabi dayafi kita godewa ubangijimu .
Dazun nan kika shigo gidan kin dai ga abinda ya faru a gidan nan shi kadai ya isheki ishara a rayuwa duk wani izzigilanci da ji da kai na lantana bai hana ta karbi abinda kika kawo a karkashin ki ba.
Ko wanan ai wani babban baiwa ne da cigaba a wuri Allah wanda yake zaton ka da komawa baya yau a wayi gari yaci ta karkashin ka.
Don haka hakkuri zakiyi kaddarar kice a hakan haka ubangiji ya tsara maki baki isa ki kaucewa hakan ba.
Don yanzu idan nayi fushi nace zan kwata maki hakkin ki da karfi da yaji na dauki mataki sai mu taru mu nunawa ubangiji ke nan bai isa garemu ba.
Haka dai inna tayi ta rarashina har barci ya dauke ni ban sani ba tun ina dan bata amsa har taji nayi shiru hakan yasa ta gane barci ya daukeni ne ta shiga nata tunanen a nan don abubuwan da take hangowa bata dai yarda ta nuna min hakan bane kawai.
Tasan ina ciki wani mawuyacin hali mai wuyan sha,ani da wanan baiwar Allah da Allah ya hada rayuwana da ita don mutum ya nuna bai kaunan ka a cikin ahalin shi abune mai wuyan sha,ani don ita kanta zaman abinda take fuskanta ke nan in badon ta kwabe tsakanin lantana da Asabe ba aka gansu a rana.
Don haka dole itama ta jajirce ta dinga yiwa yarta adduan fatan alheri ga halinda ta riski kanta a cikin shi duk da tsohuwan bata boye mata komai da take hasashe ba kan wanan auren nawa.
Don haka take son inna ta kara kwantar min da hankalina na samu tsuwa ingano mai hakan da yayi, yake nufi akaina dashi din.
Dole sai a cikin hikima da basiri inna zata iya fahintar dani manufan hakan a yanzu don hakane kawai zan samu natsuwa akan zancen.
Washegari tunda ba idar da sallah barci na koma duk daba gajiya a jikina saidai rashin barcin da bamu samuyi da wuri ba nida inna.
Can ciki barcin wani hayaniya ya kara tayar dani don muryan lantanace har kofan dakin mu tana magana kamar a cikin dakin take a lokacin.
Da mamaki na mike kome ya faru suke wanan fitina haka da sassafen nan a cikin maganan na dan tsunci zancen daya hada fadan wai ashe lantana tace bata yarda da rabon da inna tayi a jiya wanda asalima ba inna bace ta raba kayan sa,adatuce ta diban masu komai ta aika dashi.
A hankali nake gyara rigan barcin dake jikina a lokacin tare da fadin inna don Allah kuyi hakkuri meya kawo wanan zancen yanzu kuma.
Daga gefe dayan kanwata ke fadin wai shikafa aka aika mata dashi shine tace yayi maya kadan ko jiya dai ta karbi abinda aka kai matane.
Shine tazo yanzu take wanan fadan da innar mu wai sai an raba daidai ko a kara mata Abba kuma ya daure mata ginda a hakan wai a kara din.
Karbo roban ki kara mata din Allah halima wanan fitina ya kare hakana baza a karaba tayi abinda zatayi din sa,adatu ta fada a hasale.
Sa,adatu dan Allah ki bari a bata koda baku bata karewa zaiyi don ba zaku tabbata dashi ba ai har abada nafada tare da mikewa na nufi kofan dakin da lantana take tsaye.
Abin mamaki ba lantana kadai bane akofan har abban mu yana tsaye a bayan ta tare da dan yaron su rungume a jikin shi da ganinsa a ckin damuwa yake sun kwana suna fitina kila a dakin.
Buhu dayan na mika mata iyakata kofa dashi tana ganin haka tace yanzu naji magana kan dama wanda bai fita ya nemo ba yafi me nema rowa ai.
Tana kokarin jan dayan buhun da muka kai mata kofa zata tafi dana baho da aka zuba nace halima dauki na bahon ki kawai kaka ta kara.
Daya da rabi zamu tsira dashifa yayan mu kanwata Amina ta fada cikin dan marairaice murya nace ki godewa Allah da wanda kuka samu Amina.
Kinsan wanda zaku samu gobe ai,shi alheri takine barta Allah zai kawo muna wani wanda yafi wanan din data dauka.
Nayi mamakin ganin tunda safe ashe girki inna ta hada a gidan lafiyayye da zamu karya dashi da kayan miyan daya hadasu fada da lantana wanda Abba ya kawo muna da hjy.
Kowa na gidan saida ta zuba mai daga Asabe kakarmu har lantana naji tace a kaiwa dan lantana abincin ma,anade tayiwa dan lantana kara.
Wa yan nan dabi,un na inna sukan ban mamaki zakaga an mata abu saudayawa da zaran ta mayar da marta jan abu daya ya waddatar da ita ke nan bazata sake bi kan abinba kuma.
Tana gamawa wanka ta shiga a gurguje ta shirya tare da fadin zata dan fita unguwa mukai mata sai ta dawo wurin muka zauna zaman hira da yan uwana ranan sa,adatu batayi sana,a ba sai labarin abinda daya faru bana gidan suke ban.
Wanda hakan yasa na kara jina wasai kamar babu abinda ke damuna a rayuwa neme kuncin da nake ciki na rasa ga baki daya sai fari cikin daya mamaye zuciyana.
ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
4️⃣3️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BARKAN MU DA YAU YAR UWA UBANGIJI ALLAH YASA MU DACE DA RAHAMOMINSA AMIN, , , , ,
Kofa a rufe yake koda ta murda don haka ta tsaya kwankwasa kofan don a bude maya daga ciki.
A hankali yake bin kofan da kallo kafin yaji an tsananta buga kofan yazo ya bude yana tsaye mutum din shi sak saye da jallabiya baka a jikin shi sai farin jikin shi daya karawa jallabiyan kyau a lokacin a jikin shi.
Yana buda kofan sukai arba da mami dake tsaye a cikin daure fuska da dakewa baya yaja ya matsa mata ta karasa shiga cikin dakin.
Mami lafiya da safen nan ya fada yana msi bin bayanta zuwa wuri kujeran data nufa don ta zauna har lokacin tana mai bin falon da kallon abinda ta gani jiya yana dawo mata a ranta sabo fil.
Saida ta zauna dakyau suna fuskantar juna dashi dole irin kallon da take mai yasa ya dan dukar da kanshi kasa don nauyi da kunyanta da yaji lokaci guda duk da baiyi tunane tasan halin data riske shi a ciki jiya ba.
Sake dago kanshi yayi sau karo na barkatai yana dan kallon mahaifiyar tasu yana dukar da kai da idanuwan shi da suka fada a cikin yan kwanakin nan kamar wanda yayi cutar wata daya dashi.
Saidai wanan karo ya kasa jimirin dukar da kan nasa gareta don irin idin data zuba mai tana kallon shi wanda ya kasa fassara ko kallon meye hakan.
Wai mami lafiya na ganki a haka hannu mami din ta daga mashi kafin ta sauke wani irin zuciya da sai daya sake dago kai.
Wani ajiyan zuciya mami ta sauke kafin tace friend magana nazo muyi a matsayi na uwarka kuma abokiyar shawaran ka a kullun.
Jin hakan yasa ya gyara zama ya mayar da hankalinshi gareta sosai din jin abinda zata fada mai a lokacin.
Wani ajiyan zuciya mami ta kara saukewa kafin tace Jafar yaushe kafara shaye shaye a rayuwan ka ban sani ba ?
Tare da mika hannu gare shi tana fadin bani abinda kasha jiya a dakin nan na shigo har na fita baka a cikin hankalin ka.
Ba tare da fargaba ba ko tsoron data tsamaci zai baiyana a fuskan shi ya dago kai yana fadin ba wani abu mai wahala ai nasha ba mami kawai dai don hankalina ya dawo daidaine nasha.
A ciki tsoro da fargaban gami da tashin hankalin, abinda ya fada mami ta dago kai tana kallon shi a firgice tace kasan abinda kake fada kuwa ?
Kwayoyin dake a ciki hijjab dinta ne data kwashe a jiyan ta fitar tare da watsa mashi su a gaban shi sama table yayin da idanuwan ta suka kada sukai jawur a lokaci guda fiye da yadda ta shigo dakin da farko tana fadin a cikin wani murya dake nuna gab take da fashewa da kuka a lokacin tana fadin.
Why Jafar why da zaka jefa kanka a drug additct saboda wanan yarinyar kake kokarin bata rayuwan ka kome ?
Mami yarinya ?
Wace yarinya ke nan kike magana da har zata iya sakani wani abinda ba a sanni dashi ba dafarko kada a zargi kowa indan na aikara wani abinda bashi ba wanda ya isa ya sakani yi abinda ban tashi yi ba kai tsaye.
Ya karasa fada yana kallon mahaifiyar nasa ido da ido babu wani nauyi ko kunya a yanayi shi ranan.
Damm mami taji gabanta ya fadi don kallon da dan ke mata tare da bata amsa haka kai tsaye ba tare da jin nauyin komai a gareta ba.
Wasu irin hawaye ne suka ziyarci fuskanta a lokaci guda tare da fadi a cikin rauni Jafar haka ka koma ban sani yaushe zuciyarka da rayuwan ka shika fara wanan harkan ina raye ?
Mami ya fada a cikin wani murya mai nuna samuwa kafin yace kiyi hakkuri don Allah amma ni bansan na aikata wani abinda har zai sakaki hawaye haka ba a yanzu.
Mami kan duk inda tashin hankali yakai hankalin mami ya wuce nan ga tashi ita kadai tasan irin halin da take jin kanta a lokacin.
Shima kanshi halinda mahaifiyar tasu take ciki a lokacin ba zai iya jure ganin hakan ba gareta karfi hali kawai yake dakewa a lokacin.
Mikewa yaga mami din tayi wace a tunanen ta har zuwa lokacin abinda yasha di a jiya bai sakeshi ba.
Mami ta nufi kofa hankali tashe ya bita da kallon mamaki ba tare da ya iya furta mata komai ba a lokacin har ta fice daga part din nasa.
Komawa yayi ya zauna saman kujeran daya mike tsaye gareshi da farko tare da dafe kanshi zuwa sama suman shi da hannun shi daya yana mai shafan gashin kanshi zuwa baya a hankali kafin ya furzo iska daga bakin shi ya mike zubur daga zaunen tare da fadin Oh shit .
Don tuna ko meya faru dashi jiya din bayan security din shi ya fada mai zuwan su mami din gidan sa nacan daya ajemu da hjy.
Direct wurin window din glass din dake falo ya nufa wanda zaka iya hango haraban gidan mami din ga baki daya, daga inda mutum yake tsaye daga cikin part din nasa.
Glass din ya zuge tare da shakan iskan dake shigowa ta tagan alokacin yana mai lumshe idanuwan shi a hankali.
Allah ya gani baiso hakan ba a yanzu baiso ace mami ta fara fahintar rayuwan shi na boye ba wanda daga shi sai mahaliccin sa yasa da yana wanan halin da a boye.
Shikan shi bazai ce yasan lokacin da rayuwan ta fara mai hakan ba saida kawai ya tsunci kanshi dumu dumu ne a cikin harkan da ba addinin shi ya yardan mai yayi ba.
Muna a cikin wani lokaci mai wuyan fassara a yanzu da dole sai iyayye da yan uwa an dage dayiwa yara addua da saka ido tare da nasiha ko yaushe.
Baka zama talent a banza yanzu ko wani kuru a duniya sai ka karkata idan ba Allah ya tsare kaba da kaifi adduoin iyayye dake bin bawa.
Kusan hakan ne ya faru da Jafar din don shi kanshi ba zai iya cewa ga taka maiman lokacin daya fara wanan harkan ba a rayuwan shi.
Iyaka abinda ya sani shine shidai ko a yanzu yana iya kokarin shi wurin ganin ya gyara harkalan shi a kullun sai dai abin yaci tura har yanzu.
Yau gashi har mami ta fara riskanshi ga yanayin da bai dace ace ta sameshi a ciki ba, Allah kadai yasan a yadda ta riskeshi din a jiyan ya fada yana maida hankali a wurin haraban gida tare da bin motan mamud dake shigowa gidan da kallo yana mamakin dawowan shi gida a wanan lokaci.
A hankali ya bar wurin tagan zuwa cikin sakin bacin shi har lokacin yana mai jin kunan rai a tare dashi don baisan amsam da zai ba mami ba a yanzu tunda ta riga da ta kamashi red hannded a shaye ko.
Ruwa ya shiga ya watsa a jikin shi duk sa safe saida ya watsa ruwan don jikin shi da yai mai nauyi a lokacin.
Yanzu kuma zafin da yake ji ta ko ina a jikin shi yasa shi ya nufi bathroom kai tsaye tare da sakewa kanshi zuwa jikin shi ruwa gaba daya don yaji sanyi.
Karfe hudun yamma mun gama duk wani shiri zuwa unguwan da innan tace muje mu gidan wani baffan ta dake can karshen layin su.
Sea tsawale nake tafiya don idon mutane dake yawo a kanmu a duk inda muka wuce dan gungun mutane a zaune.
Gidan irin ginan kauyen mune akwai zaure har biyu kafin ka kai kanka cikin gida gidane mai dauke da matan aure guda uku ko wace daga ciki an kewaye mata part din ta da dan kishefa guntun katanga da bazata iya ganin sasshen yar uwata ba sai idan ta shiga daga ciki.
Nasan gidan don yana daga cikin gidajen da muka bude ido dasu tunda mukai wayau muna kai masu abincin sallah da yawon sallah kamar yadda al,adan bahaushe yake a karkara.
Sashen uwargidan muka nufa tana ciki da taranta ta amsa muns muka shigo tun a waje muka fara gaida ita da yaran don zaman uwaye suke a gare mu tunda inna diyace a wurin su.
Matar da fara,a take fadin a, a lale marhabi ga amaryan birni a gidan nan yaushe garin inji maki bako ?
Kafin in bada amsa halima kanwata ta cabe da jiya suka zo gobe ko jibi zata koma idan anzo daukan ta.
Ke kan fafi ba, a tambayeki ba sa,adatu takai mata dan duka a aika suna kokarin rikicewa da fitina a tsakar gidan mutane lokaci guda.
Tsawa na daka masu tare da masu fadan haka da sukeyi matar baffan ina na fadin indai wa yan nan ne ai mun saba da halinsu ko yaushe suna gidan nan tare damu ai.
Zama nayi saman tabarban da dayan yarta ke kokarin shimfida muna lokacin da muke maganan muka kara tusa sabom gaisuwa tare da tambayana yaya can ya nabaro su.
Sai mukaji dauri aure kawai daga sama haka kokaiwa malam ashe kin gama karbe mai dan kudin sadakan shi kin tafi birni kinyi auren ki a can kin bar mallam a soro ko ?
Da murmushi nayi tace ai ba a mamaki sa ikon Allah don wanan auren naki Allah kadai yasan manufan hakan gareku ubangiji yasa alheri ne hakan ya kawar da duk wani sheri daga gare ku .
Wanda ke sakin suka amsa da amin ni dai a zuciyana na amsa ban iya amsawa a fili ba don kunya da kawaici irin na yayan hausawan asali.
Tsaraban da inna ta debo masu muka zo masu dashi nayiwa halima signal da ido ta mika mata tare da mata bayani kamar yadda inna tayi muna bayanin a gida.
Ta amsa da murna tare da fadin barin kaiwa malam ya gani kafin ya fita wurin daliban shi yasan kunzo don idan ya fita baku samu ganin shiba sai bayan magariba zai shego gidan kuma.
Ta mike tare da daukan su kayan shayi da sabulen da nazo masu dashi ta nufi turakan malam din dake zaune saman buzun rago mai launin fari da baki a shimfide a kasa.
Ga kwanon hura a gefen shi da kofin silver maidan girma na ruwa ya amsa sallaman umma hari matar shi lokaci guda.
Bai daina shan furan ba saida ta kare mai bayanin tsab ya dauki kofin ruwan dake gefen shi ya kora kadan kafin yace sun iso ashe tun dazun su nake dan dako ban fita ba dama.
Ki masu iso su karaso ya fada a cikin yanayin da malam bahaushe kanyi magana da matarshi a cikin gadara da isa .
Har takai kofa yake fadin ji mana da sauri ta dawo baya don jin mai zai fada kafin yace na yanke shawara kecev zaki bi wanan yarinyar kamar yadda uwarta tazo ta bukata ai mata gada don ba wani abinda yahanasu zata nema muddin ina da karfin sa in kasa yimata shi kamar yadda zanwa dan cikina abu babu jin kyashi ko wani abu haka itama yahanasu din .
Na sani malam inna habbi ta fada tana gyara tsayin ta don maganan yazo mata a bazata kuma bata da halin da zata musa hakan ga maigidan nasu.
Da sanyi jiki ta fita daga dakin kafinta kawo wurin mu babu wani alaman damuwa a tare da ita alokacin sai fara,a dake fuskanta tana fadin mu isa mu yake jira a sashen shi dama ashe.
Nan muka barta ta aika karamar su watau amaryan malam tazo ta raba abinda muka kawo masu din na tsaraba.
Yana zaune a yadda matar tasa ta barshi muka shigo muka gaisa ya dan jamu da ba,a kafin ya dago yana sallaman su sa,adatu da su dan fita daga waje ya gama magana dani.
Ba bata lokaci suka mike zuwa wajen mutanen gidan inda suke zaune kafin ya dago yace min amarya watau kin koma birni kin mana wayau ko ?
A cikin dan kunya nake fadin ba gani na biyo ku kauyen ba malam tunda nan na saba dashi ni yadan yi murmushi yana tono wani abu a cikin kayan shi kafin yace.
Dazun uwarku tazo min nan hankali a tashe tana fada min wani magana wanda nina dauke shi kamar zancen matane kawai.
Don a iya bincike na tun dazun din ni alherin hakan nagani ta ko ina dan akasin shi baida yawa sai dai abinda ba,a rasa ba kawai wani lokaci na zama tare.
Don haka yanzu dai karbi wanan ki fara sha ya miko min wani ruwan rubutu a wani tsohon goran yought daya dan dushe kalan farin shi.
Dole hakana na karba na kafa kai kamar yadda yace insha da bissimillah in raga in shafe kaina har zuwa wuya sa fuska da sauran ruwan.
Yayin da nake faman yi shi kuma yana kokarin yan tone tone acikin kayan shi yana nema wani abu, har lokacin dana aje mai goran magani a gefen shi.
Kin sha kenan ya fada ba tare daya jiyo Inda nake zaune ba, na amsa da eh nasha malam nagode na fada a sanyayye.
Kai haha dai wanan aiyiwa kaine ne hidima mukaiwa banza don a zauna lafiya balle namu jinin mu fatan mu dai ladabi da biyayya ga miji shine abin bukatan mu.
Karbi wanan ya miko min wani abu kamar bawan icce yana fadin ki saka a baki ki dinga taunawa a hankali koda a wayane ki fadi bukatan ki gareshi yau kiga aiki da cikawan wanan.
Na baki wanan din ne ba do komai ba sai irin bayanin sa uwarki tazo mi dashi koda yayi wana auren ne da nufin ya cutar dake Allah ba zai taba bashi ikon hakan ba a kanki wanan kuma dan bawan iccen da kike gani a hannun ki aiki shi gareki yafi akirga ki dai saka a baki kamar yadda nace dake yanzu ya kara bada da sauri na dan balle na jefa a bakina sauran na bude yar jakkana na kada a ciki.
Addu,oi masu ma,ana ya ban tare da min nasiha akan zaman aure da rike duk wa yanda na sama a gidan da zuciya daya duk wanda yace zai bini da sheri abinsa zai koma mai zuwa safe zaibawa yaron shi wani rubutun akawo min na sha.
A nan yake min bayanin tafiya da matar shi tare da hikimar shi nayi hakan wanda shi yasan dacewan zuwa da ita din da zamuyi da irin ranan da zatai min a can din idan mun tafi baidai fito fili ya fada min komai ba ya barshi a dunkule hakana.
Munyi sallama dashi da matan gidan da muka samu su fito dukkan su waje ana girkin abincin dare gwanin ban shawa dasu kansu hade ake komai a gidan.
Yamma lis muka shigo gidan mu don dan biye biyen da muka yan gidajen yan uwa da kawayena kafin mu shigo gidan .
Sallama mukeyi ga lantana a tsakar gidan mu kamar ba musulma ba ta kyalemu bayan sai data juyo ta kallemu kafin ta hakademu gefe guda tana jan tsuki taci gaba da abinda takeyi a wurin.
Muryan innan mune da taji sallaman mu daga dakin ta tafito tana fadin kundawo ke nan yanzu nake fada daku a raina don me zaku bari ai magariba kuna waje.
Marigaba fa matattaram sheri ne ko sa,an ka ake son a samu a daidai wanan lokacin akanci galaban mutum ai mai sheri.
Muna ta sauri wallahi inna nasan bakya son ai fita a wanan lokacin na fada ina kokarin cire hijjab din dana saka a jikina da zan fita.
ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
4️⃣4️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAR UWA FATAN ALHERI A GAREKU KO YAUSHE ALLAH YASA MU DACE DA RAHAMAN UBANGIJIN MU AMIN YA ALLAH, , , ,
YAR UWA KADA KI MANTA LITTAFIN NAN NA KUDI DON ALLAH KADA MU SHIGA HAKKIN JUNA DARI UKU NE KACAL ZAKI BADA , , ,
Kofa aka turo tare sa sallama a lokaci daya wanda hakan yasa ta mayar da hankalinta ga wanda ke shigowa dan karamin falon a lokacin wanda ba kowa ke zuwa falon ba sai lokaci lokacin don takardun aikin ta masu mahianci da take adanawa a falon nata.
Mami lafiya naga kira yafi a kirga a wayana ban san da shigansu ba sai yanzu na duba mami ta dago kai a cikin wani irin yanayi mai ban tausayi ta kalli dan farin nata dake tsaye daga kofa a cikin damuwa ga yadda ya samu uwar nasu alokacin.
Kara rikicewa yayi lokaci guda kai tsaye ya karasa shiga dan falon tare da samun wuri ya kai zaune a gefen ta.
Mami wani abu ne kuma ya faru ko kuma jikin ne don office din ki na fara zuwa yauma akace min baki samu fitowa ba.
A hankali takai hannu ta zare glass din dake idon ta yanayin da fararen kwayan idonta da suke ciki na bacin rai ya baiyana a sarari har dan na iya ganin yanayin nata.
Jikin shi yai sanyi sosai lokaci guda yasan ba karamin abune ke jefa mahaifiyar tasu ga tashin hankali irin haka ba ga sanin da yai mata na jajirttatan mace a duniya.
Dan gyara zama yayi ya fuskance ta sosai da kyau don jin me zata fada mai a lokacin kafin ta dago kai tace dashi.
Mamud for long ka san da Jafar yana shaye shaye dama ?
Maganan tazo mai a bazata saida yadan razana don yasan ta kwabewa kanin nasa ke nan yau tsakanin shi da mahaifiyar su din tunda har ta sanda hakan gareshi.
Mami yasha wan, , , , hannu ta sake daga mai tare da dago kai ta kalleshi tana fadin ai tambayan ka nayi kawai ka ban amsa in sani.
Ajiyan zuciya ya dam sauke kafin yace gaskiya mami ba zance na san lokacin ba saidai tun kan dai ya tafi Hong Kong nasan da yana dan taba abubuwa kadan ina kuma kokarin tsawata mai ko a lokacin.
Sheshekan kukan data sake ne a lokaci daya ya kara tayar mai da hankalin shi sosai har ya mike ya isa gareta da sauri yana fadin.
Haba mami kuka kuma at dis stage da jafar yake a kanshi aini ina ganin wanan bai kai abin kuka ba tukun illa a tsaye a fahinci waye jafar a yanzu ?
Da sauri ta dakatar da kukan da takeyi din don jin abinda dan nata ya sake fada mata kan dan nata da take gani shine hasken rayuwan da kowa nasu nan gaba.
Wanan dalilin yasa take kokari ganin ginashi a kasan nan tun tana raye don ko bayan ta ya kasance suna da bangon dafawa kamar jigon su.
Shine hikima da kokarin mami na nacewa da auren shi da yar gidan mamman bello mai ritaya tsoho wanda ke daya daga cikin dattijan kasan nan dake fada aji a arewa.
Sai dai shi dan baisan manufarta kan hakan ba duk da ya hango hasken a zancen ta tun farko saidai shi sam baida ra,ayin hakan a rayuwan shi.
Yasa ya kaucewa wanan hadin da mami din ke sonyi mai da ko wace yarinya da bashi yaji zai iya zama da itaba a rayuwan shi don kawai wani siri nasa na daban can da bai damu da kowama ya sani ba a yanzu .
Muddin dai din ya samu daidai da yadda yake son macen ta kasance a rayuwan shi nan din gaba.
Mamud me kake son fada min a yanzu mami ta fada a cikin wani sabon tashin hankali a fuskan ta kuma wanda yafi na farko hadewa.
Mami ba wani abu bane dubaga yadda jafar ke samun cigaba yanzu a kullun idan anyi duba ga yadda rayuwa yanzu ya koma ga mutane.
Mumunan faduwan gaba ya kara zowa mami din hankali tashe ta furta hakane mamud nayi babban sakaci da damana na uwa a gareku da bana bibiyan bayan al,amuran ku akoda yaushe.
Haka kawai daga kwancen yaji ranshi na raya mai yakira layin wayana a lokacin don jin yadda na samu gida da yan uwana.
Kiran farko har zai katse yaji an dauki wayan ana fadin bata nan tana waje muryan karamar yarinya da bata kai mace sosai ba ke fadi a wayana.
Ke wacece ke maganan ua fada yana dan murmushin da bai tashi yinshi a lokacin na sai yajo tace ni, nice halima kanwar ta.
Au halima ya fada kamar ya santa a fili dama , kina lafiya ?, ta amsa da lafita kalau , ina yayan naki ta tafi ya tambaya .
Bata fitaba tana nan tana gyarawa innan mu wurine yanzu aka gama fada da inna da lantana saboda wurin girji dan murmushi ya sauke don jin abinda yarinyar ta fada.
Kafin yace fada kuma tace eh kullun lantana sai taja innan mu fada tace a raba wuri yana sauraren ta a daidai lokacin yaji wani murya na salati ana fadin yanzu wayan yayan tamu kike jagula halima?
Ba jagula nake ba an kirata ne na daga ta fada daga a dan shagwabe amma ke din nan yana ji zasu kaure da fadan su da suka saba yi ko yaushe.
Samun kamshi yayi da rashin kashe wayan yana saurare duk abinda ke faruwa har dawowana dakin da mukai magana akan abindaya faru yana jin komai bai kashe ko ya damu da kudinshi da a Ke jayewa ba a lokacin.
Basu fada min komai ba tunda na dawo dakin sai da nayi shirin kwanciya barci ne waya ya dauki sabon ringiing a dan daburce na daga wayan, murya kasa kasa ina amsa mai sallaman shi .
Don nagane shi duk da ban tubuta mai komai a wurin sunan shi ba har yanzu muryan shice take fadin ke idan ba,a kiraki ba ba zaki taba kiran mutum ba ko ?
Ganin har innan mu na dakin zaune yasa na dan saci kallon inda take a dan kashe murya nake fadin kayi hakkuri na mantane ban kira ba.
What ya fada da dan karfi har saida na dan razana da hakan na samu da kyat cikin rashin damuwa na sake fadin na mantane bankira ba.
Ji nayi ya sake wani wawan tsuki a wayan tare da fadin ke kina da hankali kuwa ?
Sai kuma ba bata lokaci yaci gaba da fadi kai tsaye ba tare daya saurari mai zan fadaba wanda dai bai wuce kalman hakkuri ba gareshi a lokacin
Ke ki saurareni da kyau kiji may zan fada maki don gobe zamu fara deal din mu na abindana fada maki zai faru tsakanina dake na taimakon junan mu a tare.
Don haka goben nan akwai wanda zaizo garin ku da safe daga kaduna zasu diba fili a saya a ginawa mahaifiyar ki wurin da zata zauna tare dasu halimatu fada ya kare daga yau a zauna lafiya.
A cikin mamaki na dago kai na kalli inda inna take zaune tare da sauran yan dakin namu dake zaune a lokacin kafin in mayar da hankali a wurin wayan ina kallo a cikon mamakin ji abinda ya fada din.
A Ina ma yasan wata halima can na fada a raina muryan shi naji yana fadin akan karamin abu za a dinga batawa inna rai yadda naji tana fadi dazun.
A ina yaji wanan zancen na fada a fili ba tare da nasan zan furtan hakan ba yace wacce abin ya dama ta fada min tunda ke ba zaki kira ki fada min ba asan abinda za a kan wana case din.
Koda na dago kaina gaba daya dakin idanunsu a kaina yake lokacin suna sauraren meke faruwa duk da bajin maganan sukeyi ba a lokacin.
Har ya gama maganan shi na kashe wayan ina kallo da mamaki sa,adatuce ta fara fadin me yaji yayan mu ?
Zancen fadan inna da lantana na dazun yake min fada ban sanardashi ba sai ji yayi ke nan yasa wani ya samai ido a kaina a garin nan kome ?
Da hannu sa,adatu ta nuna min tsakiyan kan halima take zaune a kusa da ita tana lasan miya a kwanon data karasa cin abinci a lokacin.
Itace dazun ta dauki wayan ki da aka kiraki ta fada mai komai yaji inna takai mata magara daga inda take zaune tana fadin waya aike ki mai shegen bakin tsiya da yawan magana.
Inna tambayana yayi ina yayar mu nace tana waje wurin da lantana ke fada dake shine na fada mai komai daya faru inna ta karasa a cikin sanyin murya.
Yanzu me kikayi ke nan yarnan zaki jawa mutane zancen gori da zunden mu a cikin garin da gidan nan kaf yanzu idan wanan zancen yazo kunnen jama,a ai sai a saka mu a baki.
Da kyat na hade wani yawu mai daci da dumi daya taru min a baki tun barin wayan na kasa magana in furta komai sai binsu da kallo da nakeyi dakin duk lokacin da wani yai magana a cikin su.
Bayan dogon nazarin danayi na yan mintina da har ya hana inji karshe fadan inna da halima ashe har dukan ta tayi a wurin ban farga ba.
Ba komai na tuna ba sai abinda ya fada da bakin shi ki huta kowa naki ya huta ta karkashin ki ayi alfahari dake a cikin yan uwan ki wata rana idan kin daure zama dani yadda nake.
Indai hakane na zan gwada in tabbatar da hakan daya fada min din idan har gaskiya yake har cikin ranshi abinda ya fada din a lokacin.
To ya zama dole kodan farin cikin mahaifiyata da yan uwana in amince da tasa bukatan mutukar hakan ba zai sabawa addinina ba ko ya taba min mutuncina .
Duk da nasan yin hakan wani gangancine nake kokarin aikatawa a rayuwana a matsayina na ba yar kowaba a duniyan nan nasa na tarawa kaina babban ganganci a rayuwana.
Haka kawai na dauki waya da sauri na rubuta idan hakan zai zama farin cikin mahaifiyata da yan uwana a shirye nake da inyima biyayya idan hakan bai kauce wa addinin mu ba.
Ina gamawa na sake karantawa batare da nazarin komai ba na tura mai sakon kai tsaye ina mai runtse idanuwana a hankali.
Muryan inna ne ke fadin wani abin yace ta fada mai ne ko me yafaru ya furta hakan.
Ba komai bane inna na bata amsa don hankalinta ya dan kwanta ina kokarin kawar da damuwan dake fuskana a lokacin.
Ba zan so mu jefa ki a cikin wani halin rayuwa harda zaki takura ba saboda wanda daga baya za a dawo abin yazo ya damu mutane kuma.
A,a inna don Allah ki cire damuwa a ranki kan wanan zancen don shi haka rayuwan shi yake da taimakon na kasa dashi ko yaushe.
Allah ya kyauta inna ta fada tare da kaiwa halimatu wani sabon rankwashe akai ta sakr sake wani ihu mai karfi tana fadin inna bansan hakan zai maku zafi bane ai.
A daidai lokacin dana tura mai da sakon yana kokarin fita falon mami don ya dubata a daidai tsakiyan falon sakon yashigo mai a wayan shi.
Wani irin shu,umin murmushi ya sauke a fuskan shi wanda baisan lokacinda ya sakeshi a fili ba don saurin kamawa da tarkon shi danayi a lokaci guda.
Caraf idon shi suka sarke dana mami dake zaune ta hakince tana ba mai aikinta umurni a lokacin.
Ya karaso zuwa saman kujera ya zauna a kusa da ita ba tare data samu mai magana ba don ta lula acikin tunane halin da dan nata ya shiga ba tare da saninta ba.
Idan ko har akan wanan yar matsiyatan abu kamar wasa ga zance naso ya juye ya zama mata babban magana a rayuwa yanzu kuma.
Har yau kan ita mami a daure yake don ta rasa gano me yagano a jikin wanan yar har ya mace haka a cikin sonta .
Yarinyar da ba a bakin komai aka dauke ta ba don yar aikine ba wata mai galihu can ba ko asali har yake neman jefa kanshi ga halaka haka ?
Saidai maganan babban danta mamud ya kara jefata a cikin zargin dan nata a yanzu don tsoron ta Allah kada abinda dan uwan nasa ya fada ya kasance gaskiyane hakan .
Ita dai a iya sanin ta da dan nata tun yana karami komai zayi a duniya zaiyi shine a cikin hikima da fasaha irin na masu hazaka da kwakwalwa.
Sai gashi yanzu ta kasa gaskanta zarginta na canza halayen dan nata ga baki daya ga yadda suka san abinsu da farko.
Fuskan shi a wayan shi yana duba tun bayan zaman shi wurin hankalin shi ya koma kan wayan mami tana magana da mai aikin da bazaice ga fuskanta ba tunda yakai zaune a wurin.
Juyowa mami tayi tana masa duba irin na tuhuma lokaci guda don yadda ta ganshi din yazo ya zauna mata ba wani jin darr din ta ko kadan akan laifin da take ganin ya aikata dole yaji nauyin hakan a lokacin.
Jikin shine ya bashi a lokacin da ana kallon shi yasa ya dago kai dan jin hakan da yaji a jikishi.
Caraf idanuwan shi suka hade dana mami din lokaci guda sai yaji ya dan tsargu da hakan shima don irin kallon da uwar tasu take mai a lokacin don haka ya dukar da kanshi babu shirin haka saboda nauyin ta dayaji.
Jafar may ye matsalakane yane yanzu mami ta fada tana mayar da hankalinta gareshi baki daya don ji amsan da zai bata a lokacin.
Amma sai ta lura kuma har ya mayar da hankalin shi ga wayan ba tare da yasan tanayi ba a wurin da kai nake magana ta fada da da karfi tare da nuna bacin rai a fuskan ta.
Firgigit yayi tare da sake dagowa yana kallonta yana fadi mami ban jiki bane na dauka da wanan kike ai har yanzu ya dan fada a tsarge.
Jafar wai yake damun rayuwan kane a yanzu koka sake shan wani abinne kuma saboda wanan banzan yarinyar daka kwallafa rayuwan ka gareta don jaraba.
Nafa gaji da wanan kwanaye kwanayen da kakein a gidan nan aure dai ne nace bada yawun bakina ba sai kasan yadda zakayi da yar mutane tun yanzu.
Shiru yayi na dan lokaci kafin ya dago kanshi da yake a sunkuye ya dubeta tare da sake wani guntun murmushi a fuskan shi yana fadin.
Mami kina ganin akwai wata wace har zata iya sauya min rayuwana a yadda nake har yaushe na hadu da wanan yarinyar taki da zata sakani wani abinda ba halina ba yanzu.
Ran mami ya baci ainun da abinda ya fada a ranta tace mamud yayi gaskiya al,amarin yaron nan yayi girma ban sanda hakan ba kenan.
Jafar yanzu duk yarda da amana dana baku ashe akwai wani rayuwa da zaka fada wanda ban san dashi ba a tare da kai har ka boye min kanayi. .
ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
4️⃣5️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
FATAN ALHERI GAREKU HAR ABADA YAN UWA MUSULMAI ALLAH YASA MU GAMA DA DUNIYA LAFIYA ALLAHUMA AMIN, , , , , ,
LITTAFIN NAN NA KUDI NA YAR UWA IDAN BAKI BIYA BA KADA KI SHIGA HAKKIN WANI DON ALLAH , , ,
Zan iyacewa gaba dayan mu dakin mun shafa da zancen zuwa wani bako da yafada a jiyan do bamu dauki abinda muhinmanci ba a rayuwan mu.
Sai gashi kawai an kwadawa Abban mu sallama da sassafe ya fita zuwa waje ya dan jima sai gashi ya shigo yana kwalla min kira kamar a kidimance shima yake a lokacin.
Da sauri na dago daga saman raggan katifan da nake kwance na sa,adatu data barmi in kwanta don ina bakuwa a cikin mu.
Abba ina kwana nake kokarin fadi yayi da Abba ya dakatar dani da fadin yar sani wasu mutanene suka zo min da wani zancen yanzu a waje wai maigidan ki ya turosu daga birni zasu duba fili a nan kusa ko wani wuri za aiwasu aiyiuka ko ?
Da sauri na dago kai na dan saci kallon Abba din dake tsaye ya kura min ido don jin karin bayani daga bakina a lokacin.
Kai na girgiza tare da fadin Abba ban san da wanan zancen ba gaskiya na fada dan azauna lafiya kada Abba yayi zargin wani abu innan mu ta hada a lokacin.
Ko wani zargi yazo ya shiga wanda hakan zai iya jawowa innan mu wani matsala a rayuwan ta tunda ba zanso hakan ya faru ba.
Baki da labarin hakan Abba ya fada a cikin mamaki tare da kara kallon yanayin da nake tsaye kafin yace ikon Allah .
Ya juya ya tafi ya barni a wurin runsunne kafin in tsinkayi muryan lantana daga sashinta tana kwalawa Abban mu kira da dan karfi kamar tana bashi umurni.
Abba dake a rude a lokacin bai samu amsa kiran nata ba sai fita da yayi zuwa waje ya nufi gidan dan uwansa a nan cikin unguwan namu.
Hakan baiwa Lantana ba naga ta yafa zani ta bi bayan Abban sai dai ganin bakin datayi a wajen gidan namu wanda wata kila ta firgitane da ganin fuskokin su a lokacin.
Sai gata ta juyo da sauri ta dawo cikin gidan dama da daura gaba kawai ta dan yafa wani ragga a kanta tana rike da danta a hannu jalo jalo, ta fita daga gidan .
Ba kunya ta nufi sashen Asabe don gulma innan mu sai aikinta takeyi ba tare data mayar da hankali ga abinda ke faruwa a gidan ba lokacin.
Bamu san meta fadawa Asabe ba mundai ji Asabe na fadin subbahanallahi da safen nan haka baki a cikj bakin kaya idan dai ba wani yai masa cune ba aka turo akama min shi.
Umma lafiya inna ta fada a daidai lokacin da Asaben ta fito a rude daga wajenta lantana na binta a baya.
Ina fa lafiya yanzun nake jin mugun labari a bakin yar nan wai wasu baki da bakin kaya sunzo sun tasa dan nan a gaba zasu tafi dashi.
Anya kuwa umma haka zancen nan yake yanzu fa ya fita nan naga ya kira yar sani yana tambayan ta wani magana kafin ya fita.
Koma dai menene barin leka wajen in gananwa idona abinda ke faruwa dashi din haka tunda safen nan.
Bayan fitan Asaben itama sai gata taja ta tsaya don irin mutanen da suke wajen gasu Abban mu a gefe daya tare da wasu yan unguwa suna magana a tsanake.
Haka asaben ta fita tana ratsa mutane a dan gigice tana tambayan abinda ke faruwa ba wanda ya koma ta kanta karshe ma suka kwasa suka shiga mota zuwa gidan maigari.
Nan suka bar asabe tare da wasu yan tsirarun mutane a wurin yan gulman da basu gane komai ba ala dole ko sai sun gano hakan suji kwam.
Sai kusan sha dayan rana mudai tun muna saka rai da dawowa Abba har muka koma daki don mu karya masu wanka kuma suka shiga yin wanka don ka,idar innan mu ce tasa ruwan wanka kowa yayi wanka kafin rana ya dago.
A wanan lokacin ne Abban mu ya dawo gidan ko yanzu shigowan ujula yayi yana kokarin fita daga gidan Asabe ta dakatar dashi.
Abban ya dawo tare da dan mata bayani a takaice tare da fada mata cewa umma ba komai bane sai alheri haihuwace ke kokarin nuna dadin ta a gidan nan yau.
Do yaron nan mijin Abu ne ya turo a sai fili a kusa damu nan za, ai masa wani aiki a wurin wanda bansan me za,a gina maiba amma dai aiko maiye dai karuwa mune ai.
Hakane inji asabe ta fada tana gyada kai alaman gamsuwa da maganan shi tana fadi ikon Allah .
Akan ya mace ne wanan baiwan ya sauka a gidan nan haka duniya kabar mutum a inda ka gansa don baka san baiwan da Allah yai mar ba.
Ranan dai mutanen basu bar wurin ba saida suka tabbatar da an fara aiki yadda suke so sukayiwa kowa sallama suka bar garin da yamma lis.
Injiniyan sa zaiyi aiki da ma,aikatan shi aka bari bayan sun samu masauki inda zasu zauna ko washe gari haka suka tashi da aiki wanda hakan ya jawowa mutanen unguwar mu ciniki a wurin su da safen .
A kwana biyu da fara aikin kwantsan saiga shi a garin yazo dagashi sai wani abokinshi saikuma security dinshi da yazo dasu inda kallo ya dawo garesu.
Zatinshi, izzashi da wayewa da kamala uwa uba ilimi da isa ya kara hakashi idon duk wanda ya ganshi a lokacin .
Duk wanda aka fadawa wai shine mijina bai yarda don sam ansan shi din ya wuce ajin aurena saidai idan an masa dole a kaina sai ya aureni da wata manufa dai.
Zancen zuwan shi yabi gari lokaci daya duk wanda yasan da hakan saida ya tofa albarkacin bakin shi kan zancen auren kowa da irin abinda yake fada kinsan kauye da samun magana.
A ranan bayan ya gama ganawa da iyayyena tare da zaga aikin ginan da akeyi babu kama hannun yaro don kudi na shan kashi sosai ga aiki ga kayan aiki sai shigo dashi ake tun ranan da aka fara aikin.
Ganin zuwa matar malam illiya yasani shan jinin jikina sosai don abinda malam din ya fada min ranan da naje gidan shi din.
Ba wani bata lokaci muka hada tafiya inda halima ta nace saita bini nan dai aka kwasa sai karshe aka yarda mu tafi tare idan matar malam zata dawo su dawo tare.
Ba takura ga zaman mu don motar mu daya ni matar malam da kanwata motar daya sai scurity din dake gaban motar a zaune tare damu.
Munbar kauye da zance a bayan mu tafiyan dan lokaci ya kaimu kaduna na dauka ba zamu tafi gidan mami ba kamar zuwan mu.
Sai gashi mun sauka a gidan inda muka samu Nazifa da anty salma kawai a gidan Rufaida bata nan sunce bata faye zama gidan ba yanzu sosai.
Sunyi matukar mamakin ganin mu a lokacin saidai sa yake a tare muke dashi daga mu harshi babu fuskan yun wani zance a lokacin .
Na dauka zama kwana kaduna sai baya munyi sallah munci abincine anty salma ta shigo tana fadin wai ya J yace mu fito zamu tafi.
Ba a cikin wani sakewa muke ba dukkan mu har anty salman da take min kallon mamaki a fakaice ta kasa ko dan sakewa damu Nazifa kan tun ganin farko da mukai mata a falon ban sake sakata a idona ba har wanan lokacin.
Rufaida dasu Ruby sun zo gidan gulma sun samu mun wuce don ko mami dake Abuja har labarin zuwan mu gidan ya isar mata a lokacin.
Sai ashar ta kundumawa dan nata damu tare da fadin a fada mai maza mu bar mata gida kafin ranshi ya kaiga baci.
Ba wanda zai iya fada mai sakon har muka bar gidan don dama da abinsa zaiyi a kadunan yasa muka tsaya a nan.
Karfe takwas na dare muna a cikin wani rantsetsen gida da ban san ko a ina wanan gidan yake ba haka mudai namu idone kawai.
Alhamdullahi komai a kwai a gidan babu ne kawai babu ga gidan da girma duk da darene bai hana mu gane hakan ba.
Irin su cultizen su club ko Iliminaties, dai da sauran su ai zubur mami ta dago tana fadin what, what, mami ta kara fada tana gyara zama jalal yace yes of course mami don yanzu ai kinsan duniya saida wanan kuma muddin sunan har zaiyi fice ka kaiga wani matsayi nan gaba.
Kirji ta dafa tare da fadin innalilllahi wa inna,alaihim rajin sai ra hada da mikewa tsaye a daidai lokacin kuma shi ya mamud ya shigo falon tare sa jamal.
Jalal ke fadin mami nifa bawai nace hakan bane naga kin daga hankalin ki sosai kwatance kawai nayi maki ai da hakan ya fadi a cikin damuwa.
Mami kan ta shiga wani hali a lokacin don bata masan me take fadi a gaban diyan nata ba a lokacin.
Mamud naci amanan mahaifin ku nayi sake da zamani ya cuceni ta fada tana komawa zaune yarfan saman kujera a cikin wani irin yanayi na damuwa da tashin hankali.
Jalal ya mamud ya kalla tare da fadin kai wai meke faruwane hakane naga mami a wanan yanayin ?
Ina fa daki kwance yazu ta kira ina zuwa take tambayana wai irin su culties din da turai da saura Asian countries ke sashi nake mata bayani shine na ganta a hakan ?
Da sauri ya juya inda mami take zaune yake fadin haba mami hakan ai ba kyau ki fara zargin dan cikin ki da kanki har duniya ta zarga mai hakan akan shi.
Mamud idan har jafar ya kasance a cikin irin wanan kungiya bazan taba yafe mashi ba a rayuwana ku sani.
Haba mami ki bar wanan magana don Allah ko akan dan wani ne balle naki yana illiminaties zai dinga sallah jamal ya fada .
Da sauri ta mayar da kallonta gun jamal din tana fadin Allah yasa hakan ne jamal na shiga uku da wanan yaron abinda ban taba zato da tsamani ba a cikin zuriata yana kokarin faruwa dani haka.
Jin sam batun na mami yai yawa yasa ya mamud dagowa da sauri a cikin bacin rai yana fadin kai jalal take her to her room kai jamal zo muje ya fada tare da fara tafiya.
Jamal din ya mara mai baya nan suka bar mami da Jalal yana kokarin lalashin mami din don ta daga su shiga part din ta su kaucewa idon yan aikin gidan a falo.
Ranan dai haka suka kwana a cikin tashin hankali a don kosu hankalin su a tashe yake kan wanan zancen sabanin mu dake gidan nasa tsundum ciki zaune sai damuwa da kewan gida kawai a lokacin ne a ramun babu wani tunanen komai a tare damu.
Kusan zance zuwa da matar malam.yai min dadi don sai ta zame min kamar hjy data tafi ga kuma halima da ba abinda ya dame ta a rai sai faman zuba surutu da tambayayoyi da takeyi hankali kwamce tana ci da sha duk ko da dare ne muka shigo gidan bai hanata bude ciki ta dura abinci ba.
Duk da munga shigan shi gidan a lokacin hakan baisa ya kwana nan tare damu ba gidan mami ya wuce ya kwana a can kamar yadda ya saba kwana din .
Da safe dan uwan shine ya tayar dashi daga barci ta hanyar buga mai kofa ya fito da mamaki yake kallon ya mamud din dake tsaye a kofa ciki damuwa.
Lafiya dan uwa ya fada bai bashi amsa ba tasa kai zuwa ciki dakin kai tsaye ya bishi a baya daga inda ya barshi tsaye a kofa .
Zama sukayi suna fuskantar juna na dan lokaci kafin mamud di yace kai abubuwa fa suna son baci a bangaren mami don yanzu kokarin zarga wani zance takeyi.
Daga baya ke nan ya fada yana mikewa tsaye don ni yau zan bar kasan nan da dare zan koma baki aikina ba zan dawo ba sai yarinyar nan ta gama zana exam din ta zanzo in tafi da ita.
Ya zakayi da mami mamud ya fada yana kallon dan uwan nasa yace cikin ko in kula akan mefa ?
Komai ma kana ganin zancen nan data dauko zata barka ka koma idan kuma har ka tafi kabar yarinyar nan baka gudun wani abu ya biyo baya .
Wani abin me zai biyo baya matace fa ba zaman kowa takeyi agarin nan ba yanzu sai zamana don haka duk wani mataki daya kamata na dauka akan hakan na riga dana dauka a yanzu ko.
Saida ya mamud din ya dan kurawa kanin nasa ido na dan lokaci kafin ya ware hannayen shi yana fadin shike nan har idan ka shiryawa hakan ai ba matsala.
A shirye nake ga duk wani barazanan da mami zata iya kawo min kan wanan matsala ya kare da fadin OK ga dan uwan nasa sai ya gyada mai kai alaman gamsuwa.
Bayan fitan dan uwan daga part din shi ya dade zaune a wurin yana dan tunane a ranshi kafin ya mike ya shiga bandaki ya watsa ruwa jikin shi tare da shiryawa kafin ya fito.
Kai tsaye part din mami ya nufa daga nan dakin yana rufe yasan tana gida don babu inda take fita idan ba wani dalili ba a irin wanan ranan ta jumma,a.
Da sallama a bakin shi ya turu kofan tare da dan rike hannun kofan kafin ya sake turawq ya shigo cikin dakin gaba daya.
Tana zaune a cikin shirin ta na doguwan riga leshi sai mayafin kayan dake saman jikinta da alama dai shirin fita take a lokacin itama duk da baranan fitan ta bane yau.
Tunda mami ta hango dan nata taji gabanta ya fadi don kwarjin sa sai kara fita fili taga yana mata tunda zancen auren nan nasa ya taso .
Wanda take gani a yanzu zancen sa ta fara zargi nasane ya fara baiyana mata hakan gareshi don wani asirttacen baiwa nasa da yanzu ta kara hangowa gareshi.
A hankali ya kai zaune a gefenta yana kamo hannunta tare da fadin mami antashi lafiya ya gida ya aiki ba tare dajin shakkar komai ba.
Cikin basarwa mami din ta jaye hannun ta tana fadi kalau nake tunda yanzu kana ganin kakai ba zaka iya bin umurnina ba koka fada min idan zakai abu.
Jiya me ya kaika kaduna ba tare dana san zaka shiga ba sai kawai wai inji kana min gida da wanan shegiyar yarinyar kauyen.
Yasa na ce ace kabar min gida tun kan na bata ma rai daga kai har ita sai in saba maku ba wani aiki bane gareni hakan.
Mami ai ba wanda ya fada min sakon ki sai yanzu nake jin hakan garwki but iam sorry hakan ba zai sake faruwa ba insha Allah.
A hankali ta lumshe ido cikin jin wani irin yanauin amsan daya bata din a cikin rashi damuwa da furcinta garshi ke nan.
Yau kaduna zan tafi ta bashi amsa tana mikewa daga inda take zaune lafiya dai mami zaki tafi kadunan ya tambaya cikin son jin amsan da zata bashi.
Eh akwai abinda zai kaini mai muhinmanci can yau din idan na gama da wuri yau din zan dawo garin nan.
Tana magana a cikin wani irin yanayi dake nuna akwai abu a zuciyar ta sake damun ta a lokacin shidai shiru yayi bai tankata ba a lokacin yana zaune a inda ta barshi.
Saiga jalal ya shigo dakin kallo daya yaiwa yayan nasa ya kawar da kai a cikin tsarguwa mami take fadin dauki jakkar can fita min dashi gurin mota kafin in fito.
Ok mami ya fada ya nufi jakkan ya dauka Allah Allah yake ya bar dakin a lokacin don a tsarge yake kada yai laifi a wurin yayan nasa kuma don ya dauka mami ta fada mai komai zai zargeshi.
Bayan fitan dan uwan da kaya shima ya mike yana fadin mami Allah ya tsare hanya ya dawo daku lafiya sai dai yau da yamman nan na nake son in, , , , ,
Jafar wani kungiya ka shiga da ban taba sanin kana a cikin wani hali ba sai daga bayan nan nasan da hakan tare dakai ba.
Mami kungiya kuma name ya fada yana kallon ta a ciki mamaki karara a fuskan shi don jin abinda ta fada mai din game dashi.
Wani cultu kakeyi jafar don jikina ya bani wani abu a game dakai ba dadewan nan ba.
Mami ya fada a cikin mamaki tare da fadin cult kuma ai da ina cikin wani cult din daba haka ba da yanzu na wuce sanin kowa a kasan nan ni wanan baya gaba ko kadan ya fada yana hade rai ya nufi hanyar fita daga dakin ta bishi da kallo kawai da nazari a zuciyar ta.
🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
4️⃣6️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
FATAN ALHERI GAREKU YAN UWA TARE DA KARA BAKU HAKKURI DA YANAYIN DA LABARIN YAZO MUNA SABODA KARATUANA A YANZU DON ALLAH A KARA GAKKURI DANI YAN UWA NAGODE, , , , ,
Zan iya cewa tunda gari ya waye ban leko waje ba daga dakin da muke ciki zaune mu uku din kamar muna gidan kaso don tun shigan mu gidan muka shiga sakin ba wanda ya fito daga cikin mu har halima dake daukin zuwa abuja din a lokacin.
Sai gata baki ya fara mutuwa tun ba,aje ko ina ba a lokacin tunda taji matar malam na fadin Allah ya cecemu da wanan gidan har za a yanka mutum a bizzime ba,a san an yanka kaba.
Hankali halima din ya fara tashi tun jin furcin Maizube matar malam din muna zaune ga gari ya waye zugun zugun a dakin da muka kwana din wanda shima munsan da zamu kwana ne ta hannyan kai muna kaya dakin danaga anyi yasa na jasu zuwa dakin muka shiga.
Kofan aka kwankwasa wanda yasa kusan lokaci daya muka dago kai zuwa kofan kafin a sake nocking na biyu wanda yasa nayi karfin halin mikewa zuwa kofan lokavin guda .
Na bude tare da kallon wanda ke bakin kofan a lokacin shine yana tsaye yabawa kofan baya ta hanyar saka hanayen shi a ciki aljihun wandon jikin shi.
Wanda jin karan budan kofan shima a lokacin yasa shi dan juyowa zuwa gun kofan mukai arba dashi da sauri na zube kasa don girmamawa ina gaida shi da kwana.
Bai amsa ba sai cewa da yayi zaki kashe mutane karfe sha daya ake nema baku fito kun karyaba har wanan lokacin haka ?
Dan daburcewa nayi na rasa me zanyi a lokacin don rudewa da nayi yau shine a gaba muke magana haka kai tsaye dashi sabanin da can da hjy kan muna shamaki a tsakanin mu.
Zasu fito yanzu na samu bakina na fada lokaci guda na fada ya juya ya bar kofan kamar maiyin sauri kada wani ya ganshi wuri lokacin.
Dakin na koma tare da fada masu abinda yace sai maizube ke fadin aiko nan ma aka kawo saimu karya ko.
Ciki da daurewa nake fadin kinsan su a table ake karyawa nan saboda haka mu fita zuwa falon inda zamu karya din yanzu, don yana fada wai naki fitowa daku can ku karya.
Maganan da maizube keyi yanayine dake nuna alaman tsoro da karfin hali a lokacin don gaba daya ta gama tsunkewa da al,amarin gidan ga baki daya.
A takure dai kowa yake haka muka iso falon dana lalubu muna inda dinning din yake da abunci a jere sama shi a aje muna.
Dole na nemo karfin hali da jarunta lokaci guda na sakawa kaina don kawai halimatu da matar malam da kiris suke a lokacin su fasa ihu a gidan don tsoro.
Basu ba ni kaina duk da zama a gidan mami ya taimaka min matuka saidai duk da hakan wani abu ban san shiba a gida wanan ne farkon ganina a gida nasa.
Abinci ne mai rai da lafiya aka shirya muna don karyawa wanda nasan halin yadda ake abin karyawa nawai don mu din bane yasa aka shirya hakan .
Kawai dai haka abin yake a garesu ko yaushe dan magana halima tayi min na zuba mata harara daga inda nake take fadin yayan mu duk wanan mu zamuci duka ?
Na watsa mata harara tare da cigaba da kurban tuwan shayin da nake kurba a lokacin a hankali duk zuciyana ina ji wani irin yanayi a lokacin.
Text ya shigo min a wayana na dan saci duba a hankali ko daga waye duk da wayana layin mutum.dayane a cikin sa lokacin.
Ki bisu a hankali kada ki takurawa bakina a gidan nan yin hakan yana cikin bin umurni na a yanzu kiyi duk abinda zakiyi su kwantar da hankali su gidan nan da kowa, ya rubutu min saida hakan ya ban mamaki don ban san a inda yake tsaye yana kallon mu ba alokacin.
Ki dibi duk abinda ranki ke so a gurin nan halimatu duk namu ne do mu aka ajeshi a nan na bata amsa a cikin dan wayen cewa da fuskana kamar babu komai a raina.
Ba laifin sun sake jikin kamar yadda ya kamata sunci abinci daga nan bamu koma daki ba a kokarina na bin umurnin shi a lokacin kamar yadda yace din.
Sai zuwa karfe daya saura ya shigo suka gaisa da maizube matar malam kamar yadda muke jin a gida kowa na kiranta da wanan sunan na maizube matar malam.
Ba wani sakin fuska ko sabo a gaisuwan ya mike tare da fadin halimatu zo naji mana ya fada ba tare da ya tsaya ba na kalleta itama ni din take kallo da mamaki tare da jiran umurnina .
Dan dukar da kaina kasa nayi kafin na dago na kalleta ta mike don ta gane me nake nufi da hakan daga kallon ta danayi din.
Tun ina zuba idon ganinta har na dan far tsoron haka sai gata tare da security din gidan niki, niki da kaya ana shigo mata dasu cikin gidan.
A hankali na sauke ajiyan zuciya tare da bin kayan da ake shigo dasu da kallo inda na dan fahinci wani abu a lokacin.
Maizube tana gefe a zaune itama dai ba sai an tambayi damuwa a yanayin nata ba lokacin har zuwa lokacin da suka gama shigo muna da komai acikin gidan.
Wata mace tayi sallama ta shigo da fara,a a fuskanta ta zauna suna gaisawa da maizube tare da muna bayanin itama a gidan zata zauna tare damu .
Itace wai mai aiki kula da komai yadda ya dace da fatan zamu ji dadin zama da juna yadda ya dace ta kare da fadin .
Itama dai musulmace yar uwan mu don haka mu sake jiki da ita don Allah don komai ya tafi daidai a gidan.
Abubuwan dake faruwa a lokacin koda nake yarinya mai san karancin shekaru da ban wuce sha shidda ba na dan fahinci wasu abubuwan a lokacin saboda natsuwa da fahintar dake gareni .
A waya yai min bayanin komai yadda zan fahinta daga kayan har yadda zamu zauna da matar data gabatar muna da kanta a matsayin mai kula da gida ya min bayani tare da ja min kunne akan komai.
Yana fadawa halimatu a ranan zaiyi tafiya bata fada min ba sai bayan mun sallame sallah a azahar tana muna hira fitan su da inda sukaje ashema ba tare dashi suka fita ba da wanan bakuwar matarce ta sayo muna kayan nan da akazo dashi gidan.
Kallom halimatu nayi tare da fadin yau zai koma ina ya fada maki halima tace yace wuri aikin shi kuma wai muyu karatu sosai kafin ya dawo.
Na dauka shirmen halimatu ne sai gashi da yamma kawai ya shigo yana sallaman maizube da niyar zaiyi tafiya a ranan zai dan jima bayana nan .
Ta shiga jero mai addu,an neman tsari da kariya a gareshi da alaman yaji dadin hakan don irin alherin da ya aje mata yana karbawa da amin ya mike.
Ta kalleni tana fadin wai nikan ba zaki bishi baje harda kinji zaiyi tafiya kina zaune a daki kinki ki motsawa tun dazun.
Ba don naso ba dole na mike nabi bayanshi kamar yadda tace dani din inyi sai gashi har muna kokarin cin karo dashi a kofan da sauri naja dan baya kadan kada mu gwaure .
Ya lura sarai da yanayin kaduwa dana shiga na kaduwa dana ganshi a gabana lokacin.
Tsadadiyar muryan shi ya ratso dodo kunne na yana fadin lafiya ina zaki tafi ko wani abu kike nema ne ?
Dan dukar da kaina nayi kasa tare da fadi a cikin dan damuwa dama dama dai na fito ne don in sallameka kawai ina wasa da yan yatsun hannuna duka biyu nake magana.
Yana tsaye yana kura min ido yana kallona tare da dan sake murmushi a fuskan nnasa tare da dan gyara tsayin sa dakyau har lokacin idon sa a fuskana.
Kamar aafalki naji muryan shi again yana fadin to ai gani saiki sallameni din inji tunda ke baki san abinda ya dace ace kinyi ba.
Kada ki manta komai da zamuyi a tsare yake a kan mu ba tare da kowa ya fahinta a gidan nan ba ina nufin kuwa har wanan yar aikin da zata zauna daku ba zata fahinci zaman mu dake ba kawai dai a matsayin mata da miji masu kula da junan su kowa zai dauke mu.
Na dago kai da sauri na kalleshi do jin abinda ya fada din sai yayi daidai da idon shi a kaina ya daga min gira da kafada tare da fadin idan kinyi hakan kin taimaki kanki.
Yana fadin hakan ya juya ya wuce ya barni tsaye da mamaki a wurin don na kasa fahintar inda zancen shi ya dosa a lokacin.
Gashi ba wai wata kawa ko abokiyar hira ke gareni ba a lokacin da zan kaiwa shawara na har mu gane me hakan ke nufi da zancen shi a kaina.
Ance idan bawa yana son walwale al,amari shiafi yawa haka yafi zuwa mai a daidai tsakiyan sallah don sai shedan yaso ya shagal dakai daga barin sallah ya hasko ma abinda ya shige ma duhu a lokacin.
Nima kusan hakan ne ya faru dani a daidai sallah la,asar danazo yi don yanayin damuwan dana shiga yasa na tayar da sallah a vikk kuncin zuciya.
Tiryan tiryan abinda yake nufi kr zuwa min a rai na har da wanda ban san zankai ga tunane ba saida na fahinci komai a lokacin.
Sheda kenen yaso ya ribanceni ta hanyat bata min sallah a lokacin na farga da hakan da sauri na mayar da hankalina a gurin ibadana.
Bayan na idar ina zaune wani shu,umin murmushi mai hade da sautin dariya yazo mi lokaci guda .
Hannu na daga tare da yiwa Allah godiya akan haska mi hanyar dayi a lokaci daya.
Sai muryan maizube ke fadin lafiya dai yar nan daga idar da sallah kin soma dariya haka kamar an maki bushara da aljanna.
Karfe shidda saura kiran shi yazo min na sameshi na falon shi duk sa bansan wurin ba haka nayi kokarin mikewa zuwa amsa kiran nasa.
Yana zaune a cikin shiri shi sai kamshi ke tashi ko ina a falon na shigo da sallama a bakina ba dauka ya karba hakan ba don ba lale bane ya amaa din.
Banyi gigin hawa kujera dake falon ba a lokacin don haka naja nakai kasa zaune dan nesa daga inda yake hankalin shi yana gun abinda yake a system din shi yayin da falon yai shiru na dan lokaci kamar babu kowa a wurin.
Kafin yadago kai yana fadi a uzurce OK kinzo ko tare da dan lumshe ido ya sauke su akaina a hankali kamar yana nazarina a lokacin.
Yau zan tafi kamar yadda kikaji na fada dazun wa mama don haka komai na kula sa gidan a yanzu zai dawo karkashi ikon ki a garin nan.
Duk wani kokari idan kinga dama ta yadda ba wanda zai fahinci meke tsakanina dake a wanan zama namu yanzu.
Yanzu wasan mu zai fara don a bayana abubuwa zasu faru da dama na sani saidai idan kin iya tsirar da kanki abin zaizo mako da sauki ko yaushe.
Da sauri na sake dago kai na dan kalleshi inda yake zaune din yace yes daga ni sai ke muka san irin zaman da zamuyi a tsakanin mu a yanzu.
Barazan mami ko wani dan uwana kada ki yarda ya kaiki ga furta masu komai dake tsakani mu ki tsaya kaida fata a matsayin matana kike a gidan nan barazan wani ko wata ba zai fitar daken ko ya tsoratar dake ba garesu.
Kaina gyada a hankali don ganin yana maganan ya tsureni da idanuwa shi idona suka dab ciciko da hawayen nadama .
Don tabbas na jefa kaina a tsaka mai wuya duka bangare biyun da nasa dana mahaifiyar su din dama wanda ka taso daga baya.
A hankali ya lumshe idsnuwan shi tabbas tausayin yarinyar ya kamashi don yasa ya jefa yar mutane a wani hali .
Wanda rashin wayau da ilimi ya kaita ga yarda da bukatan shi a kanta ba tare da nazari komai a game dashi ba kuma.
Yace kada kiji komai ba zasu iya illanta min ke ba dan kina a cikj matakan tsarona ta ko ina muddi dai kin iya kanki da bakin ki ko yaushe.
Ba tare dana iya furta mai komai ba na sunkuyar da kaina kasa hawaye na ci gaba da zuba min a hankali.
Shigowan yaron shi da shima na gansa a cikin shirin shi da alaman tare zasu tafi ke na tafiyan.
Ganin yadda nake zaune ina hawaye ya da kalle ni ba tsamani ko zato naji yana fadin lafiya take wanan kukan haka ko an mata wani abin ne kuma ?
Bai bashi amsa ba sai mikewa da yayi tsaye yana gyara kayan jki shi tare da fadin zamuyi sallama da ita ka bamu wuri ya fada mai ba tare da kallon inda yake ba yana daukan kaya.
Haka ya fita daga daki ranshi bace yana dan satan kallona a inda nake kamar mai tuhumana a lokacin.
Murya shi naji a daidai inda nake tsugune ina hawaye yana fadin zainab al,amarin mai girmane ba zaki gane ba a yanzu sai nan gaba zaku gane manufana.
Sai dai ya yanzu ke din kanwa ce a gareni zanso ki rikeni tankar kece Aisha na da muka fito ciki daya da ita wurin kulla da amanata da komai nawa.
Idan ki mun hakan na maki alkawari har abinda baki zata ba a rayuwan ki bikatana kawai ki nuna ma duniyake din matatave ta suna kuma yar uwata a badali.
Kin min alkari hakan ya fada tare da dan tsugunowa saiti inda nake makure ina kuka kafin in magana aka turo kofan tare da fadin kasan fa jirgin mu takwas zai daga kana nan tun dazun.
Kabar falo nan na fadama ya dan fada a hasale tare da nuna mai kofan a ciki zafin rai da sauri ya juya ya fice shima bai tsaya din ba ya mike tare da fadin ga key din daki nan zamu dinga waya duk abinda kike so zaki iya fada min idan na kiraki mu zamu tafi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
4️⃣7️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
JUMMA,AT MUBARAK YAN UWA MUSULMAI UBANGIJI ALLAH YA SADAMU DA ALHERUN SA ALLAHUMA AMIN, , ,
Duk yada naso na boye damuwana a lokacin nayi iya kokari wurin boye hakan saidai hakan bai samu ba don saida maizube ta fahinci hakan a tare dani .
Sai gashi ta koma lalashina wai a zaton ta saboda tafiyan ya jafar dinnne nake haka idanuwa da suka hau saboda kukan nadama danayi a lokacine.
Ba komai yasani wanan kukan ba sai fahintar inda na jefa rayuwata dan kawai tausayi da biyayya ga ya jafar din da yake zaton don deal din shine na yarda dashi da bukatan shi gareni.
Saidai kuma a yanzu kalaman shi sun fara jefani rudani don ban san a matayin da nake a garshi ba da wanan tunanen ya barni a gidan suka daga zuwa inda yake aiki.
Ranan kan mami tayi fushi sosai Allah ya taimaka a gaban hjyn taya kira yana sheda mata zancen tafiyan shi inda ta haushi da sababi saidai ta makara ga hakan don yana shiga jirgine ya kirata.
A zaton mami din tare dani ya wuce don idonta ya rufe a wurin har take ikirarin da sai dole ya dawo dani kasan nan inma don hakan ne ya guje mata din.
Aikin ma gaba daya zai bar can ne ya dawo nan kasan kusa da ita inda take iya ganin komai da yakeyi din a gabanta.
Saidai mami bata san da ta makaro ga hakan ba gareshi don a yanzu kan ba zata iya taro dan nata ba kai tsaye yadda take so din tayi.
Wai ke iyami yaushe kika koma hakane hjy ta fada a hasale daga gefenta ta dora da fadin zaki raba auren da Allah ya nufa sai anyi a tsakanin su ne ko me ?
Ta dago don fadin abinda ke a ranta hjy ta katse ta da fadin yadda kike zaton zaki iya yiwa danki baki ko ki tilasta shi ya saki yarinyar nan.
Ki tuna nima hakan ina da hakkin da zan tursasa ki a kanshi dan ni dince dai na haife ki ai .
Hjy yarinyar nan bawai sonta yake ba ko wani abu shima dole da akwai abinda yake nufi da yin hakan a zuciyar shi tunda bawai sone ya hadasu ba ai.
Iyami bana sonki da shiga tsakanin yaran nan wallahi wararana kunyan hakan zakiji da kin daure kinba yaran nan goyon baya a yadda yakeson abinsa .
Da Komai da zaiyi ai dole ya fada maki ko ya sanar dake amma zuciyar ki yana rudin ki kin hana kanki sakat da nasu haka .
Karfi da yaji kin hana yaron nan ya zauna ya huta a zuciyar shi balle kiji sirin zuciyar shi kinsan irin illan da kike jawa kanki ga yin hakan da kikeyi kuwa.
To idan ma har baki sani ba gara ki san abinda kikeyi ki bar yaran nan hakana idan ko kinki kin tsaya kina jayayya da ubangiji ne .
Sai Allah ya dauke ki a zauna lafiya ayi kuma bada ke din ba kinga sanadin hakan sai sauran diyan naki su zauna a marayu ke nan ba uwa ba uba garesu kuma.
Ina kema idan har talaucin yarinyar nan ne damuwan ki a haka uvan yaran nan ya aureki baki da komai a tare dake ilimin ma a gidan sa duka kika same shi ai.
Jikin mami yai sanyi ga abinda hjy ta fada dan tabbas kawar da ita din ba komai bane a gurin ubangiji ai.
Ganin tayi shiru hjy taci gaba da mata nasiha sossi inda take fadin ki kyakeshi da abinsa inma har akwai abinda yake nufi da hakan ai lokaci zai fadi hakan ga kowa.
Jalal da yanzu ya zama dan gaban goshin ta yana zaune a gefe yace mami gaskiya hjy ta fada ya j ai ba yaro bane yanzu.
Yana da right din da zai zabawa kansa abinda duk ya dace dashi kuma ai kinji hjy ta fada kila daddy mu ya biyo a wurin zabe shima.
Ran kwashi takai mai saida ya dafe wurin don zaifi tare da fadin aini na bar wanan zancen yanzu tunda na gane gaba daya kuna goyon bayan sa a yanzu kan hakan tunda yanuna maku yana da kudi da zai iya yin komai.
Ni kuma wallahi bana rsoro ko shakkar sa idan da ya biyo ta hanyar arziki dani zai iya hakkura dashi a hakan yaje yayi abinda yake so din ai duniyace dai ko , ?
Baki zaki masa ya kara lalacewa ko mai idan ma kin masa din dake dashi duniya zata zaga ai hjy ta kare magana a cikin zafin rai.
Har suka dawo abuja mami bata kara tayar da zancen komai akan da nata ba ko ni do tana zaton tare muka tafi dashi hakan yasa fushinta ya kara karuwa a zuciyar ta saidai batayi zancen da kowa ba kuma.
Sannu a hankali muka fara sakewa da wanan matar da ta gabatar muna da sunan ta da anty Fadila kamar yadda muke kiranta dashi.
Don da safe zata shigo har dakin da muke su gaisa da maizube ta dan ja halimatu da fira tun bamu sakewa har muka fara sakewa da ita a yinin farko da mukayi tare a gidan.
Sai ya kasance duk abinda zatayi zata kirani muyishi a tare da ita a cikkn sakewa da kulawa kamar uwar da ke koyar da yarta wani ilimi na duniya a yanzu.
A cikin hikima da basira take koyar dani zaman duniya da tako aka komai da rashin saka ido ga wani ko wani abinda bai shafeni ba can zamu zauna tana da bamu labari da zai dauke muna hankali ga komai.
Sai gashi mun dan sake da ita har ina iya tambayan ta abinda ya dan shige min duhu wani lokaci tayi min bayani akan komai .
Tun Saturday ta kaimu saloon aka wanke min kai akai kitso shiga school monday driver ya kaimu school don fara shirin jerabawa.
A school di muka hade da yaran ya mamud wanda a wuri su ne mami ta samu labarin ina kasan bai tafi dani ba ashe .
Tayi mamaki matuka don jin hakan koda ta tura ai mata bincike sai ta gane ina zama da fadila ce inda ta zaci ko wani alakane a tsakanin mu bata danta bane ya hada mu.
Inda ta gano ko waye Fadilan da kuma aikinta saidai ta kasa fahintar komai ta kawo ido ta saka a hakan don nasihan da hjyn ta tayi mata a kanmu.
Wanda nasan Allah ne ya dorani a kan mami din ta basar da zancen binciken komai a kaina har na samu daman fara jerabawa hankali kwance.
Yanzu kan ina waya da innar mu tun zuwan mu sabanin da cab da dif idan mun tafi har take fafa muna ginan da akayi a gefen gidan mu itace ashe aka ginawa gidan da zata zauna a ciki.
Inda sa,adatu take labaranta muna abinda ya faru bayan angama aikin ginan dayasa a ginawa innan mu sai lantana ta fara bala,i akan bata yarda da hakan ba dole sai Abban mu ya san yadda za a yi itama ta shiga ko a gina mata nata sashen da zata shiga.
Wani wan mahaifin mu kuma makwabcin mu ya fito yana fadin baki isa ba lantana don arzikin yartane ya kaita ga hakan don babu abinda baki fada akan tafiyan wanan yarinyar birni.
Yanzu da tafiyan ya kai ga alheri gare ta zaki fito kice ke baki yarda da hakan ba dole sai mijin ku ya dauki mataki a kan hakan wani irin mataki kike son ya dauka kan haka din a yanzu ?
Ko so kike yace ba zata shiga ginan da arzikin haihuwan ta ya jawo mata ba ta dalilin diyar ta data haifa .
Yanzu sai kije can ke mai haihuwan diya maza ki jira su girma kema su gina maki naki ai don Allah ba ai mashi ganganci ga hukumcin sa.
Idona ya kawo ruwa lokaci guda da take muna wanan bayanin ban karasa sauraren abinda take fada ba na kashe wayan .
Zama nayi cike da nazarin wanan abinda ya faru da innan mu din wanda a sanadiyan na da abindana jefa kaina a cikin sa wanda bansan ko me hakan ke nufi ba har yakai innan mu din ta fara samun saukin rayuwa a tare da ita.
Don haka ya zama min dole in jure duk wani kalubalin rayuwan gidan dan mami dana mami din a yanzu tunda har na gano hakan zai iya haifarwa mahaifiyata da yan uwana da zaman lafiya a rayuwan ta.
Karatuna nake sosai kuma ina fahintar hakan don bamu tare da wani mstsalan komai a tare damu a gidan zaman kadaicine kuma wanan Fadila din tana iya kokarin ta wurin ganin bamu shiga damuwa da komai a gidan.
A haka har Allah ya taimaka na gama zana waec dina muka zauna jiran zana neco din mu wanda a lokacin ne na samu dan natsuwa sosai tare da maizube da halimatu da yanzu itama take zuwa makaranta tare dani.
Na mayar da hankali sosai wurin koyon girki tare da anty fadila da sauran abubuwan da take koya min na zaman duniya a cikin hikima da basira .
Zakace ya da kanwa muke da ita a yadda nakan bata girma da kuma daraja sai hakan ya kara sawa matar sona a ranta sosai.
Don a yanzu mun sake da juna zata fada min kai tsaye idan nayi wani abinda ba daidai ko bai dace nayi shi ba a take zata tsawata min kan hakan a karshe kuma in bata hakkuri.
Sai ya kasance a dan watannin da mukayi da ita wani irin sabo da shakuwane ya shiga tsakani mu sosai har yakai ranan take tambayana labarina ?
Sai kawai na danyi murmushi ba tare dana furta komai ba a hakan muka bar zancen ba tare dana fada mata komai ba.
Da yake ita din mace wayayyiya a cikin hikima irin nasu nasu na manyan mata take dan tambayana wasu abubuwan a cikin hikima har take samun amsa daga gareni.
Take kuma sakani a hanya yadda zan kula da komai da zaizo min a bazata daga ko wani bangare.
Yau ban tun safe ban leka falon ba ina daki kwance na tashi sa ciwon mara wanda kan dameni duk karshen wata.
Har daki anty Fadila ta kawo min magani nasha wanda hakan ya sakani barci bayan nasha magani sai bayan karde hudu na samu fitowa falo na zauna.
Bandade da zama a falon ba halima ta shigo dauke da ledan corn a hannunta tana ci ta samu wuri a gefena takai zaune.
Na dago kai na kalleta ina mamakin ta a raina ban kaiga karshen mamakin ba ta jefo min tambaya tana fadin wai anty sai yaushe zamu tafi gaida hjyn ki sa kike aiki a gidan ta.
Gabana ya fadi don jin abinda ta fada saida na tattaro dauriya a raina kafin ince da ita kin santane ko wani abin kike son yi a gidan nata ?
Kai ta gyada min alaman a,a tare da shan jinin jikin ta a yadda na bata amsa din cikin bacin rai don bansan zancen gidan mami duk da ina kwana ina wuni da zancen mami din a raina.
A hankali na zame na kai kwance daga inda nake zaune tsaban tunane sai kawai naji hawaye suna zubo min ba tare da nasan zuwan su ba.
Dafanin da akayine yasa na dago kai anty fadilace a tsaye kaina tana kallona yadda hawaye ya bata mun fuska lokaci guda.
Badai ciwon bane har yanzu ta fada a cikin kullawa tana zama a gefena tare da mayar da hankalinta gareni.
Kafin in bata amsa halimatu dake gefena take fadin yayan mu bansan ranki zai baci ba da bance muje gidan hjy din ba .
Wace hajiyan anty fadila ta tambaya da mamaki a fuskanta a hankali na amsa da mami mahaifiyar ya Jafar.
Anty fadila tace kan me kukai zancen ta har ya kawo wanan hawayen haka ?
Bazaki ba tunda tun farko ta nuna bata kaunar ki da danta kina garin nan kuma ta sani bata nuna kulawanta kan danta ya barki amana a gurin su ba maizube ke fadi daga bayan mu.
Don haka ki nisanci su kamar yadda suka nisance ki a yanzu saboda da talaucin ki ko rashin gata ta nuna bata kaunar danki dake dafarko .
Sai yanzu kuma ke zaki kwashi kafan ki zuwa gidan ta ko zaki kai kanki ne su kara wullakantaki a can .
Ki zauna a matsayin da Allah ya ajeki gidan nan ki bi umurnin mijin ki har sai idan shi ya furta zuwan ki gidan dan mahaifiya ba wasa bace ai amma yanzu kan babu inda zaku tafi gaskiya.
Maizube nima bance zan tafi gidan mami ba a yanzu don nasan mami har yanzu tana rike dani a zuciyar ta.
Duk da ba zan iya matawa da alherin ta a garni ba har gobe don ta dalilinta har na kai hakan a yau da sunan auren danta a kaina.
Maizube tace dani ato ki daiyi wa kanki fada don babu inda zaki tafi don ni bazan zama babban kwabo ba a cikin ku duk da muke matalauta muna rike da mutuncin mu a idon kowa.
Murmushi Fadila tayi tare da fadin hjy maizube ba a hakan ai idan ma har zasu tafi din aiba haka kawai zamu barsu su kadai din su tafi ba dole saida shirin hakan ko ?
Maganin dai kar ayi kar a soma dan ba a san da wace zata tare su ba abar zancen nan har wanda take zama don shi ya dawo kasan nan inma zuwan ne sai su tafi tare dashi din zaifi.
Jinsu kawai nake yi don sam ban amince da zuwan ba nikaina a lokacin don nagama tsiracewa da mami din yadda muka bar gidan tare da hjy a yadda tayi min koran kare a gidan ta harta amince da mahaifiyar ta tabar gidan donni.
Wanan zancen da akayi a gaban Fadila yasa ta dauki wani haske a cikin zancen sai da muka zauna daga ni sai ita take kara tambayana abinda ya faru a tsakanina da mami din.
Shiru nayi na dan lokaci kamar mai tunanen wani abu sai can naji tana fadin zanso nasan wani abu daga bakin ki duk dana dade da gano komai amma zanso ji dafa gare ki din yanzu.
Wani tsorone ya lullubeni lokaci guda na janye na dauki hannuna na dora a fuskana kafi in sauke na dukar dakai na kasa.
Karo na biyu ta koma kiran tana fadin kina jina kada ki boye min komai ki daukeni kamar yar uwa a gareki don ni din a yanzu mai taimakon ki ne zainab.
Wani sanyi naji a raina tare da yarda da ita lokaci guda duk da
Banso fada mata komai ba amma ya zama dole ta danji wani abu a gurguje na dan fada mata saidai ba duka ba don ban san yadda zata dauki zancen ba a ranta.
Bakina ta zubawa ido har na kare na kare fadan abinda zan iya fada mata na zamana da mami da haduwan mu da ya jafar din a gidan mami har na kare sai tace.
Zainab yau zan baki shawara kamar yarda ya da diyarta zata bata shawara ya amfaneta.
Tagumi nayi ina sauraren abunda zata fada min din a lokacin ita kuma taci gaba da kawo min misali na zamantakewa da mutane a duniya.
Yadda mama maizube take nufin kiyi danzun nake ganin bashine mafita ba gareki zainab don ko yaya suka samu matsala a kanki da mahaifiyar shi ki tunafa uwa uwace a gare shi.
Duk yadda kika dauka da zafi ko iyayyen ki suka dauka hakan ba zai taba mashi dadi ba a ranshi duk ko yadda yake sonki.
A sake na ce yanzu yaya zanyi anty don mami ba zata taba yarda dani ba a cikin a halin ta ni kuma na sani auren nan namu nadan lokaci ne dashi.
Tsaki taja tana fadin ki bar wanan zancen do Allah kefa mace ce zainab duk wani abu da ake bukata a mace kina dashi zainab lokacine kawai zai nuna hakan akan ku.
Kedai kawai yanzu duk abinda nake koyar dake ki maida hankalinki ki koya do zama daku na dan lokacine da zaran contrac dina ya kare daku tafiya zanyi in barku a gidan nan.
Yanzu lanbanta zamu nema zaki dinga tura mata sakon gaisuwa da girmawa tare da nuna mata ke din yace a gareta har gobe.
Ya zama dole ki koyi halin kissa da kisisina irin na mata masu son kama gidan su a hannun su yanzu .
Ta yadda zaki iya tunkaran kowa da wanan kalubalin dake gaban ki domin yanzu sai da wanan akan samu riban rayuwa mai dorewa wanan sanyin ba zai kaiki ko ina ba a rayuwa.
Rashin wayen ki ko sanin duniya zai iya haifar da komai a kanki har aci galaba akanki a cikin sauki don wanan shirun da kike ganin tayi irin su hjy da abinda take shiryawa a hakan.
Da sauri na dago kai don jin abinda ta fada din nace amma anty ta yaya kamata zan iya ja da mami matar da ta kafu da komai akan danta dama kowa ?
Murmushi tayi tare da fadin kina kwankwanton hakan ne zainab ai tun damazo gidan nan na fahinci akwai wata a kasa tsakani ku.
Naso tafiyan ya tafi a hakan inyi aikina in wuce saidai ke din yarinyace mai saurin shiga ran mutum a lokaci daya saboda halinki na sayi da girmamawa ga kowa don baki dauki duniya da zafi ba a yadda na fahince ki.
Don hakane ma kike ganin har abinda ba a ssni na koyar dake ba nake kokarin koya maki don na taimakawa rayuwan ki.
A sanyayye nace anty nagode da wanan taimakon naki gareni in Allah ya yarda zaki sameni da amfani da duk abinda kika koyar dani insha Allahu.
Tayi murmushi tana fadin ya zama dole in taimaka maki zainab don nasan wata rana hakan zai min dadi nima a rayuwana.
Kin ganni nan nasan halin maza kamar yunwar cikkna ina da yara biyu na barsu badan naso ba saboda halin da namiji a yau.
Don haka ba zanga wata mace yar uwana zata fada a halaka ba in barta ta dandani irin ukubar dana sha a baya.
Sau nawa ya kiraki a waya tun bayan tafiyan shi ta jefo min tambayan da ban zata ba a lokacin da sauri na dago kai ina tunanen hakan ?
Bai kirani ba anty na bata amsa kai tsaye do babu zancen boyo yanzu a tsakanin mu kuma tunda ta fahinci komai.
Zai kiraki naji ta fada idan mun fara dana masa tarkon muna mata ai idab yasan wata baisan wata ba zamuyi mai karya baki da lafiya zai zo idan har kina da muhinmanci a rayuwan shi .
Saidai zaki bani goyon baya zaki koma ki kwanta ciwon na kwana biyu do wanan kanwar taki mai shegen surutun tsiya zai iya tambayan ta idan hakan gaskiyane kin sani.
🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
4️⃣8️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
FATAN ALHERIN GAREKU TARE DA BAN HAKKURI RASHIN SAMUN UPDATE KO DA YAUSHE DA FATAN ZAKUYI MI AFUWAN HAKAN YAN UWA, , , , , , ,
Ina kwance tun safe kamar yadda ta umurceni da yi hakan din sai dai tunane ya addabi rayuwana yadda wanan wasan da take shiryawa zai kaya muna.
A gogon dakin na bango na duba da karfe sha daya saura na safe tun bayan sallah asuba nake kwance ni ba barci na koma ba don tunane ina kwance a falke ina faman dakon tunane a zuciyana.
Wayana dake gefen gado wanda tun daren jiya na ajeshi da zamu kwanta ban kara bi ta kansa ba ya dauki kiran agaji.
Hannu na mika daga inda nake kwance din na dauko wayan da zuman ganin wanda ke kira layin don ban taba zaton kiranshi bane a lokacin.
Lanba ce ta kasan waje aka kira layin dashi na kurawa kiran ido ban daga ba ina nazari a raina har kiran ya gaji ya katse lokaci guda .
Wani kiran ne ya sake shigowa lokaci guda ina kallon wayan na fitar da sautin kida na kasa dagawa don na farko ban sheda ko lamban waye ba a lokacin.
Na biyu kuma idan na dauka shine mai kirana me zan fada mai don bamu riga da mu aje magana abinda zan fada mai ba.
Jikina gaba daya yayi sanyi a lokacin a cikin daurewa kiran na gaf da tsukewa na kai hannu na danna dauka.
A hankali na kara wayan a kunne na lokaci guda ina sauren mai kiran nawa hello din daya fada a gadarance yasa na fahinci ko waye a layin shidin dai ne ya kira wayan a lokacin.
Ya kara fadin hhy ya kuke me faru dakene dazun fadila ke fada min baki da lafiya tun jiya ko fita daga daki bakyayi.
Saida na tattaro wani karfin hali a tare dani kafin in iya budan bakina nace a hankali cikin yanayin wanda ciwo yake damun sa na furta banda lafiya ne da kyar.
Baki sa lafiya ita fadila me take jira dake a gida bata kaiki asibiti ba ko bata san aikin ta bane wai ?
A hankali na lumshe idona tare da fadi a marairaice cikin sanyin murya ta sani ita dince ma take kula dani yanzun haka na basa amsa.
Ta kaiki asibiti ya kara tambaya ta kaini jiya da yamma na samu kaina da fadin hakan duk da nasan komai karyane shirin hakan mukai masa.
Zan turi maku da sako idan wanan bai isa ba aimin magana ya fada kamar a kage yake da ya kashe wayan shi a lokacin.
Yaci gaba da fadin idan har kuna da matsala da ita zan iya canza wata a samo wace zata kula dake fiye da ita.
Ban san lokaci danace a rude laifin me tayi koda mahaifiyata ce ita ai iya kar taimakon da zatayi min ke nan .
Naji ya saki ajiyan zucuya tare da fadin ta kyautawa kanta don bana son wasa da aiki a rayuwana.
Idan ma laifi ne ai ba ita bace mai laifin don ba itace ta rabani da uwata ba na fada can kasan makoshi na a hankali na dauka ba zaijini ba.
What me kike fada ?
Shiru nayi tsayin lokaci babu amsa daga bakina bai kuma kashe wayan nasa ba a hankali na runtse idona ina sauke numfashi da kyar don gabana sai faduwa yake daurewa kawai nayi a hakan.
Ba zaki magana ba naji ya fada a cikin dan daga murya nace to ai kaine ka rabani da mami kuma ka , , , ,
Look ina wasa dake ne zainab yaushe har raini ya shiga tsakanin mu haka dake ko so kike na bar aikina nan na dawo na zauna Nigeria daku ?
Kit na kashe wayan tare da maida nufashin dake sauka min na tsoro da sauri don ban zaci zan iya fadan hakan ba ni kaina.
Aje wayan yayi daidai da shigowan anty fadila dakin cikin sauri na dago kai a firgice ina fadin anty wallahi shine ya kirani yanzu din na fada ina kallon ta kamar mara gaskiya.
Na sani ta fada tana zama a gefen gadon da nake kwance nima mikewa nayi ganin ta zauna din a dakin.
A haka zamu kamo shi sannu a hankali har hankalin shi ya karkato zuwa gare ki don maza a yanzu sai da kisa da iya zama dasu a cikin dabara.
Na bude baki da zuman magana ke nan aka turo kofan inda nayi shiru maizubd ce ta shigo tana fadin wai nikan jikin ne yau ta hanaki leko waje yar nan ?
Fadila tace jikin ne nima yanzu naji shirun yai yawa na leko ta na same ta a kwance sannu ta fada tana kallona a cikin damuwa da nuna kulawa a gareni.
Na amsa a cikkn daurewa ina kokarin yaye bargon dake saman jikkna wanda ya dameni a lokacin don dole nake kwance dashi.
Ki tashi ki karya fadila ta fada a cikkn kulawa nace zan watsa ruwa kafin na fita yasa suka bar dakin don na samu kintsawa hankali kwance.
Dogon riga mai laushi green mai adon dawisu a gaban rigan zuwa kasan shi na saka a jikina sai gyalen shi danayi dan kwanlin dashi a kaina.
A falo na same su zaune suna kallo na fito daga yanayi tafiyana ya nuna ban cikin dadin rai a tare dani.
Dining na nufa kai tsaye abinci na nan a gurin na diba kuma sai na kasa cin komai don hankalina yana gun yadda mukayi a waya dashi.
Da ido Fadila ke warning dina a yadda nake cin abincin da sauri na gyara sallon cakulan abincin a hankali cikin yanayin yauki da yanga kamar yadda ta koyar dani.
Muna falon har lokacin da halimatu ta dawo daga school tashigo da murnan ta tana kokarin fada min ajiki.
Anty fadila ta daka mata tsawa tana fadin kada ki fada mata yinin yau bata da lafiya gaba daya da sauri ta juinda inda nake zaune ta dan langabe kanta tana fadin.
Yayan mu sannu ya jikin na dan gyada mata kai alaman amsawa gareta ta zauna gefena tana fadin kinga yau tare da yaran gidan hjy din nan muka yi yawo a school.
Wanan akwai ki da iyayi har sai kin daukowa mutane zance a garin nan yaushe har kika sansu da kike kokarin cusa kanki garesu maizube ta fada.
To ba saboda yayan mu nake kula suba ta fada tana turo baki gaba alaman zancen da maizube tayi bai mata dadi ba.
Halimatu tashi ki shiga ki cire kayan ki na fada cikin bata umurni ta mike da sauri zuwa dakin kamar yadda na umurce ta tayi.
Alwala na dauro na gabatar da sallah tare da mika kukana ga sarki Allah wanda yafi kowa sanin dumbin damuwan dake tattare dani a rayuwana.
Kafin na mike na koma na kwanta dan banjin fita falon da ya zame muna wurin fita kawai a gidan don ko haraban gidan bama fita idan ba fita ya kama yi ba.
Amma kuma sai barci ya gagareni a lokacin sunayen Allah mai girma na dinga kira don na samu natsuwa har barci ya daukeni a hakana.
A cikin barcin nake mafalki da ya jafar yana tsaye ya harde hannayen shi yana kallona na tun karo inda yake tsaye.
Saiga wani yazo ya tsaya a tsakanin mu ya bani baya don haka ban samu ganin fuskan maishi ba .
A haka ina kalon su ban samu karasowa inda suke tsaye din ba ina kallo wanan mutumin ya jayeshi gareni ya tafi yana waigena a inda nake tsaye.
Sunan shi na kira da karfi wanda hakan yai daidai da bude idanuwana daga barcin da nakeyi din na falka a razane na gannin a cikin gumi.
Zainab wanan ihun fa Anty fadila ta fada daga kofan tana tsaye kai na dago ina kallon ta a tsorace take fadin nazo zan wuce naji kamar kina ihu na shigo.
Anty mafalki nayi na bata amsa take fadin barci a wanan lokacin baida kyau gashi har biyar na yamma yayi yanzu kina kwance.
Dago kai nayi na kalli lokaci sai na tuna da zancen sallah na mike don zuwa nayi alwala bayan fitan ta na samu fashin sallah yazo min a lokacin don haka na tsaye kawai na gyara jikina na fito daga bayin.
Naso na manta da zancen mafalkin nan danayi saidai abin ya tsaya min a raina sosai har yakai ina ganin abin kamar a zahiri a idona don irin kallon da yake min a lokacin.
Jafar da tun safe hankalin shi na ga ya sake kiran Fadila yaji ya jikin nawa saidai kuma aiki yai masa yawa yau din sai dare ya samu kansa yana hutawa a gidan sa.
Wayan shi dake gefene ya dauki kara ya dan dago yana kallin wayan da mamaki don gani mamice ke kiran shi a lokacin.
Duk da yasan a can Nigeria yanzu akwai sauran lokaci dare bai wani yi ba a can ya dauki wayan kafin kiran ya katse mai.
Da sallama a bakin shi ya daga wayan tare da mika mata gaisuwa a cikin girmamawa kagin ta furta dalilin kiran nata garshi.
Ba tare data amsa mashi ba take fadin Jafar wai me kake son mayar da kanka a cikin kune ?
Duban wayan dake hannun shi yayi cike da mamaki kalamin mami din yana fadin mami nayi wani laifi ne yanzu kuma ?
Au baka ma san da kayi min ba daidai ba ke nan ashe har yanzu kana nan da zancen yarinyar nan zainab har wata can wai kanwarta tana kokarin cusa kanta gun yaran nan a school din su.
To kayi gagawan yiwa zainab da duk wani nata iyaka da zuri,ata a garin nan tunkan ranku gaba daya ya gama baci gareni.
Jafar din ya kasa gane me mami take fada don haka ya natsu da kyau yana gyara zaman shi do n kara fahinrar inda zancen nata ya dosa dashi.
Idan kana son kanka da lafiya na fada ma ka sallami yarinyar nan zainab tun kan raina ya gama baci dakai a gidan nan.
What mami ya fada dan jin abinda ta fada a kan zainab din wace ke matsayin mata a gareshi duk da yasan auren bawai wani abu ya daukeshi ba shima.
Yace mami amma kinsan akwai aure ai a tsakanin mu dan haka babu zancen saki a tare damu mami kinsan da hakan.
Jafar ni kake fadawa akwai aure a tsakanin ku in yarda tunda nasan baka fito ta inda ya kamata ace zan yarda da hakan ba.
Kamar yadda na aurar da dan uwanka a inda nake so haka kaima nake da burin maka aure na gata kowa ya san da zancen.
Bazan taba amincewa da wanan aure naka ba na fadama gata da daraja kamar ko wani da zan ma a kasan nan ban yarda da auren da zaka sa mutane su kalle da ban san komai ba.
To wallahi kaji na fadama koda wasa na kara jin zancen wanan yarinyar ya fito a bakin ka gabana saina bata maka rai fiye da yadda bakai tsamani ba.
Dan haka na gargade ka da ka ja mata kunne akan yayan gida dan karsu kara nuna sun sansu ko a ina ne kuwa.
Jafar din dake jin zancen mami din kamar al,amara dan ya shiryawa hakan ko wani lokaci yace.
Mami za a kiyayye ba zasu kara shiga harkan diyan ki ba ko jikokin ki insha Allahu zan tsawara masu kan hakan.
Har ta gama fadan ta sai hakkuri yake bata ranshi idan yai dubu ya gama baci da hakan don shi sam baiga abin fadan mami ba a nan.
Aikin da baiyi ba ke nan dan gaba daya ranshi ya gama baci da zancen mami din a hankali idanun shi suka soma sauya launi.
Ya dinga jin zuciyar tana masa radadi da zogi ya mike zaune game da dafe kanshi tare da sake wani irin huci mai zafi lokaci guda.
Ba shakka har idan ya yarda da abinda mami din su keso a gare shi komai zai iya faruwa dashi a karshe.
Don haka ya zama wajibi garshi ya jawa zainab kunne kan duk wani abinda ya shafi mami dawani nata .
Saidai kuma ta yaya zaiga laifi zainab di bayan tana gida kwance bata da lafiya a inama ta fita har taga wani da mami ke wanan maganan haka wai.
Shi a rayuwan shi ya rasa gane dalilin wanan kiyayyan da mami takewa wanan yarinyar da bata san komai ba a game dashi.
Idan ma taimako ne ai ita zainab din ta taimaka amma son zuciya ya rufewa mami din ido ta kasa gane hakan ta ko ina saboda wani dalili nata can na daban.
Ba shakka son zuciyar mami din yayi yawa ga wanan magana data kasa hakkura da jerabawan ubangiji a gare shi .
Don haka ya zama dole ya nunawa duniya yarinyar nan tana zaman matar shine da kowa ya kamata ya sanda hakan yanzu .
Ba zai damu da wani ra,ayi ko son kai da mami ke shirin nunawa ba a nan don sam yarinyar bata da laifi asalima ai laifin nasa ne gaba daya bana yar mutane da ya jefa a tsaka mai wuya ba.
Duk da yasan da ita kanta zainan din idan hankalinta yazo ta mallaki hankalin kanta akwai kalubali mai yawa a gaban shi.
Wanda yasan kafin lokacin zai iya magace komai a tare dashi da duniya ba zata zargeshi ba kan hakan.
Wanan wani damane ya samu da zaiyi amfani dashi don kawai ya fitar da kanshi daga wani tarko da mami ke shirin dana mai wanda zai dawo ya damesu gaba daya.
Da kyat ya tashi ya iya kulle kofan shi do baya bukatan kowa ya dameshi a wanan lokacin yana da bukatan ya kebe kanshi shi kadai ko zai samu natsuwa a wana lokacin.
Zazzabi mai zafine ya rufe shi a wanan lokaci tare da dumbin damuwa a zuciyar shi tabbas da mami tasan koshi waye ba zata tsaya tana fada akan shi ba.
Da mami ita kanta ba zata yarda ya auri yarta da ta dauko amana ya gani a gaban ta har yaga dacewan ta da wanan dama nasa ba ya kulla alakan aure da ita.
Wani iri yake jin kanshi a lokaci daya ga azaben ciwon kai dake damun sa ga matsanacin kasala gaba daya ya rufe shi a lokaci guda sai yake jin duk zaman garin ma ya fita mai a rai tankar ana hura masa wuta a jikin shi.
Wani irin nadama da dana sanin biyewa abokai na kurciya ya kamashi a lokaci daya a haka har gari ya waye mai duk da bugun kofan da yake ji ana masa baisa ya bude kofan nasa ba a lokacin.
Kwana biyu ya dauka a gida bai fita ba don yanayin jikin nasa da yake ji wanda ba komai ya haddasa masa hakan ba sai tsananin samuwa da halin da yake ciki.
Ya mamud ne da ya sha kiran shi a waya ana fada masa yana barci har yakai ga fahintar dan uwan nasa baida lafiya ya samu mami da zancen.
Da farko mami bata tayar da hankalin ta ba saida sukai waya da babban yaron shi yake fada mata yadda jikin ogan nasu ya tsananta a lokacin hankalinta ya tashi.
Da kyar ta samu aka sadasu a waya dashi take fadi a cikin tsigar lalashi jafar baka da lafiya baka kira gida ka fadi.
Yanayin yadda yake magana ya kara sa mami a cikin damuwa ta kara kwantar da murya gareshi tana fadin meke damun ka hakane friend ?
Mami kirji na da zuciyana kamar zasu fashe nake jin su ina jin zuciyana kamar an daure min shi gaba daya na rasa abinda yake damuna.
Mami tace kayi hakkuri ka daure kuje asibiti dukkan al,amari ubangiji yasan dashi ka daina saka aiki ko wani damuwa a zuciyar ka hakan nan.
A haka mami ta samu ta rarashi dan lelelen nata har dai yaji zuciyar shi yadan sausauta mashi daga irin kuncin da yake jin kansa a ciki lokaci guda.
A bangaren mu kuwa bamu san wainar da ake toyawa ba iyaka dai anty fadila ta kasa samun shi a waya.
Tun hakan yana damun ta har takai ga furta min cewa kwana biyu fa bata samun oga a waya idan ta kirasa.
A cikkn rashin ko in kula nake fadin anty isan ya damu ai shi da kansa zai kiramu yaji lafiyan mu wata kila aikine yai masa yawa.
Kai ta gyada min alaman a,a zainab raina yana ban ba lafiya dai sai dai duk abinda ake ciki zan barshi zuwa gobe ko jibi idan bai kiraba zan nemi abokin sa na nan muji ko lafiya yake a can.
🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
4️⃣9️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
FATAN ALHERI AKULLUM YAN UWA MUSULMAI TARE DA FATAN CIKAWA DA IMANI A GAREMU HAR KULLUM, , , ,
Alhamdullahi na kammala karatuna lafiya tare da fatan nasara ga abinda muka rubuta dan ni kaina nasan da na sha wuya wurin mayar da hankali ga jerabawan dake gabana.
Har ubangiji ya bani nasaran kammalawa lafiya na dawo zaman jiran tsamani daga bangarori daban daban na sha,anin rayuwana da nake fuskanta.
Don yanzu ban san makomana ba a rayuwa gashi wasa wasa mun share wata uku a gidan ya jafar din dake a garin abuja tare da maizube da halima sai anty fadila dake tare damu a gidan.
Bani ba har maizube da halima gabaki daya mun sake sunyi kyau sun canza jikin su ya nuna jin dadi a tare dasu duk da babu inda muke fita a gidan saidai komai akwai na more rayuwa.
Traning kan na samu gwargwado kamar yadda anty tayi min alkawarin samu daga gareta don a cikin dan lokaci kankani na canza yanayina ga baki daya ya koma na wace ta waye ta fara sanin kan duniya.
Gashi a lokacin na shiga ganiyar budurcina da kyau ko ina nawa ya ciko ya cike ga baki daya lokaci guda.
Ashe da gaske samun kwanciyar hankali da cima mai kyau yana karawa mace budewa da jin dadi a rayuwan ta idan tana samun hakan tare da ita don na sheda hakan a kaina yanzu.
Ga farina na asali da ya kara fitowa fili a yanzu nayi wani irin fari na ban mamaki dani kaina bansan ina dashi ba sai a yanzu danayi wanan cikan haka.
Saidai a yanzu na kula da maizube hankalin ta ya koma ga iyalin ta duk ko da daulan duniyan da muke ciki don yanzu daya biyu zakaji tayi zancen gida daga bakinta.
Wanda hakan ke nuna hankalinta ya koma gida ko kuma ta zauna ta rabka tagumi sai kai maga ba zataji me kake fada ba a lokacin.
Nima sai hakan ya fara damuna don nasan iya kokari tayi yadda duk akeso ga dan uwa gareni don ba abun wasa bane babban mace kamar maizube ra baro dakinta da mijinta har tsawon wanan lokaci haka.
Hadari sosai aka hada a garin lokaci guda yanayin garin ya canza ga baki daya dukkan mune zaune a falon gidan.
Maizube ne ke fadin ikon Allah lokaci daya yanayin garin nan ya canza da alama dai damana ya tsaya ke nan a garin nan.
Fadila dake gefe zaune take fadin ai abuja ya wuce haka kedai mama don a take suke samu ruwan sama akai akai.
Don ma yanzu damanan bai gama shigowa ba yasa ake dan hada hadarin yana washewa .
Wani irin iskane kamar guguwa ya taso lokaci guda ya turnike garin muna jin yadda karan iskan ke kadawa a lokacin daga falon da muke zaune duk da ko ina glass di falon yana rufe.
Mikewa halimatu dake gafena tana gyaran farcen ta tayi na bita da kallo tare da tambayan ta inda zata a wanan lokacin.
Kai tsaye take fadin zan leka waje ne inga idan hadarin sosai ne aka hada kafin na bata amsa maizube ke fadin wanan ya akwai bakin iyayin tsiya da ita.
A cikin wanan iskan haka kowa ya rufawa kansa asiri kike zancen fita ke ?
Ai da alama ma ruwane ya sauko a yanzu anty fadila ta fada saboda iskan dake kadowa da kanshi ruwa mai nuna alaman sabuwan damana a lokacin.
Wani irin ajiyan zuciya na sauke don yanayin da ya tuna min da abubuwa da dama a cikin raina Allah ya gani ina jin dadin wanan irin yanayin tun ina karama idan anayin sa a gari.
Fuskana dauke da murmushi nake fadin lalsi ruwa ya sauko kuwa dan ga kamshi yanayi ya canza a lokaci guda na fada.
To bashi yasa nake son fita waje ba naga ruwan farko hakimatu dake tsaye tana cika ta fada a shagwabe.
Ke kan wanan ya da badan a kauye yahanasu ta haife ki ba dakin ce asalin ki ba anchau bane nan gaba.
Kai haba uwargidan malam wanan kuma ai ba da halimatu kadai kike zancen na ba don mu duka ai yan anchau din ne na fada ina dan dariya.
Yo ai da kina da irin rawan kan wanan yar da ba haka ba Abu wanan da itace a matsayin ki ai ko gidan nan kila da bamu zo shi ba.
Anty fadila tace zakuzo mana mama ai halimatu harda watan kauye ke damunta don taki ta waye har yanzu .
Amma ita zainab ai kinga saukin kanta yana kaita ga cin riban duniya lokaci guda saukin kanta har ya kaita ga mallakan maigidan nan a matsayin miji a gare ta.
Mama in fada maki ko yan birnin samun mijin irin wanan ba karamin aiki bane a garesu don nima a karon farko dana ga zainace a matsayin matar wai ba karamin mamakin hakan nayi ba a raina.
Sai yanzu dana zauna dakune nake gane hikimar shi nayin hakan da yayi don shima ba karamin sa,an hakan ai yayi ba a rayuwan sa don mama ka auri macen da zaka iya juyata ka tsayar da ita inda ka ajeta a yanzu ba karamin aiki bane gaskiya.
Yo kina wanan ancen haka ke fadila mufa na kauye har gobe akwai biyayyan aure da girmama miji a garemu har yanzu duk ko da muma din muna da masu kaifin kai a cikkn mu.
Ina amdanin wanan irin rayuwan da mata sukeyi a yanzu na halaka a garesu mace ta dunga fita inda taga dama kamar ba aure ne akanta ba ?
Wanan ba wayewa bane illa shiga halaka da yawacin mata suke jefa kansu a ciki a yanzu don dan abin nan da suke rainawa zai iya kaisu wuta lokaci guda.
Ai mama yanzu mu bamu dauki wanan a bakin komai ba don mazan da kansu hakan suma bawai ya damesu bane yanzu.
Suna ko kona ku don sun barku da Allah yana kallin wanan bakin al,adan da kukeyi ne a yanzu mace ta fita da sunan zuwa gida daya sai ka tsunceta har kasuwa ko wani gidan buki kai har ma wai da zuwa gidan gaisuwa a hakan.
Mama Allah dai ta kyauta anty fadila ta fada tana kokarin mikewa tsaye tare da fadin ruwan nan sosai yau akeyin sa don ga lokacin salla har ya karaso bamu sani ba.
Mikewa mukayi lokaci guda don zuwa yin sallah kada mu makara yayin da ake ta faman sheka ruwa har lokacin kamar ba ruwan sabon damana ba.
Har na idar da sallah ruwa akeyi kamar da bakin kwarya yadda ruwan ya gwauce a lokaci guda mikewa nayi na gyara komai yadda nake so a dakin kafin mu fito falo don cin abincin dare da bamu ci ba alokacin.
Mun ci abincin mu lafiya mun dan taba hira kafin mu shige saboda sanyin da garin yayi a lokacin wanda hakan ke iya saukarwa mutum da kasala da nauyin jiki.
Dakin a gyare yake tsab don haka ban tsaya jiran komai ba na saka kayan barci na fada saman gado duk da barcin da nake ji a lokacin hakan bai hanani yin addu,oin dana sabayi na kwanciya ba.
Mafalkin nan dai dana saba shine yazo min yau ma din wanda hakan yasa na falka a razane daga barcin na zauna gami da salati a bakina ina hada gumi a fuskana.
Wanan mafalkin yana damuna na rasa me hakan ke nufi dani wai a rayuwa don a cikkn zamana a wanan gidan kusan sau hudu ke nan ina wanan mafalkin haka wanda na kasa fadawa wani wanan maganan.
Saidai na yau din ya zama dole in tun kari wani da wanan zancen ko zan samu mafita a gareshi.
Tunane na fara tsakanin anty fadila da maizube wa zan fara tun kara da wanan abin dake damuwana a rai sai hankalina yafi kwantawa da in fadawa maizube don itace dai tawa ko banza.
Wanan kuma ai kamar sirinane duk da na yarda da fadilan itama a zuciyana amma dai hankalina yafi kwantawa da mauzube din a yanzu da nake shawaran wanda zan tun kara da zancen abinda nake yawan mafalkin shi din.
Washe gari bayan na idar da sallah na dan dade a zaune a gurin kafin in mike zuwa wurin maizube nayi sallama daga kofa ina jiran umurnin ta na inshigo dakin da take zaune a cikin sa din.
Ta amsa min da fadin Abu ce yanzu nake tunanen in sameki ai don ban sani ba ko kun tashi ko kun makara da wanan bakon yanayin na yau da muka tashi dashi na damana.
Na tashi tun asuba na fada ina karasawa cikkn dakin tare da samun wuri na zauna ina gaida ita da kwana tana amsa min gaisuwan .
Dan shiru ne ya biyo baya kafin tace ina lafiya dai Abu don yanayin ki ya nuna kamar kina da damuwa a ranki ko ?
Matar malam wallahi ina da damuwa sosai a zuciyana don wani irin mafalki nake a gidan nan kusan karo na hudu ke nan idan ban manta ba ina wanan mafalkin haka.
Subbahanallahi ta fada tare da kara mayar da hankalinta gareni a cikin nuna kulawanta a gareni sosai don jin abinda nake kokarin fada mata a lokacin.
Sannu a hankali na zaiyana mata yadda mafalkin ke zuwa min a kullun tare da yadda nake falkawa a cikkn matsanacin faduwan gaba da ciwon kai.
Ido ta tsura min na dan lokaci kafin ta sauke ajiyan zuciya tana fadi a hankaki babban maganace wanan Abu.
Don wanan maganan saidai mu nemi gaban malam ko yana da wani haske da zai kara muna a cikin wanan mafalkin naki.
Abu waima kina addua kafin ki kwants barci kuwa don shedan yakan ari fuskan wanda ka sani wani lokaci yayi wasa da hankalin bayin Allah.
Wallahi maizube bana yarda in kwanta da ba tare danayi adduan kwanciya a tare dani ba kamar yadda aka koyar dani hakan.
Allah ya kyauta ya mayar da koma menene ke shirin faruwa dake alheri a garemu baki daya yanzu nasan malam yana wurin wazifan safe sai zuwa anjima bayan goman safe za a same shi gida.
Zuwa wannan lokacin sai mu nemeshi a waya ai masa bayanin komai a tsanake yadda zai iya fahintar mu ya bamu haske akan wanan magana.
Allah ya kaimu anjima na fada bayan sauke ajiyan zuciya danayi don jin kamar har na samu haske kan wanan matsalan dake tunkaro rayuwana a yanzu.
Haka na mike zuwa dakina wanka na shiga na gyara jikina tsab na fito na dan dade ina kwalliya a gaban mirrow kafin in fito daga dakin.
Falo na samu su maizube an zuba masu abinci suna ci a dining ita da halimatu nima zama nayi don mu karya a tare ko zan samu inci da yawa saboda damuwan dana sakawa kaina a lokacin kan mafalkin da ya tsaya min a rai.
Wanda na kasa gane me haka ke nufi dani wai waye kuma wanan da bana ganin fuskanshi a mafalkin na ko yaushe idan nayi irin wanan mafalkin saidai inga bayan maishi.
Muna tsaka da cin abincin ne fadila ta fito daga dakinta tana fadin yau da wuri haka kika fito ?
Dan dariyan yake na iya mata ba tare da bata amsa sai ina kwanan dana jefa mata kafin ta kai zaune itama tana kokarin diban abinci don ta karya itama.
Na riga kowa aje cibin dake hannu na ina kokarin tashi a wurin naji fadila na fadin yau ina son indan zaga gida na diba su na kwana biyu ban lekasu ba.
Jin hakan sai yai min dadi a raina har nake fadin anty ashe yau gida zasuyi bakuwa kin kai sati baki fita gidan nan ba ai.
Zainab bana son fita ko yaushe ne kada a bata min aikina kin san yanzu mutum ake kiyo ba dabba za a iya fadawa maigidan nan bana zama ko ina wayan fita har hakan ya ja min matsala ga aikina.
Hakane maizube ta fada inda kake samu baka wasa da wurin samun ka don yanzu mutane sun baci da gulma.
Kamar yadda na saba mata tun bayan danaji tana da yara a gida da tabarsu gun mahaifiyar ta nakan dan bata abu takai masu idan zata tafi dubasu din.
Tana murmushi ta karba tare da fadin bakya dai gajiya da dawainiya da yaran nan naki zainab ko yaushe suma suna damuna da zasu zo inda anty mai sweet take muka sa dariya a tare.
Bayan fitan tane muka samu kiran malam din maizube ce ta fara masa bayani kafin yace a ban wayan yaji daga bakina.
Na karba nayi mai bayanin komai yadda nake gani a cikkn mafalkin sai fada yake ikon Allah saida na kare bayani yake fadin.
Naji komai da kika fada zainab insha Allah zan duba in gani abinda ke gudana zan kira insha Allah saidai duk da hakan ki daure ki kara kaimi wurin yin addu,a da sadaka domin sune kariyan mumuni.
Na amsa da insha Allahu malam mukai sallama na kashe wayan tare da masa godiya maizube ke fadin kinga hakan yafi kada mu zauna a cikkn duhu har wani abu yazo ya same ki.
Rashin fadila a gidan yasa gidan ya koma muna shiru yau dan karfin kan gidan itace dama zata dinga yi wanan yi wancan idan muna zaune a falo.
Tunane barkatai nake yi a zaune don abinda zai biyo fassaran da malam din zai min nice har da tunanen ko jinina ya jafar din ya bayar ?
Ko kuma dai dama manufan shi a kaina shine ya halaka min rayuwana yasa ya nace da zancen aure na dayayi ba tare da wani kwakwaran hujjan akan hakan ba.
Bakin gadon dakina na karasa na zauna tare da zuba tagumi abin duniya ya dameni a lokacin a raina .
Ba komai nake ba sai dan banzan tunane da dana sani wanda yafi a kirga na abinda zuciyana ke kiyastamin kan ya jafar din da mami.
Har barci mai nauyi ya daukeni a haka ban sani ba sai falkawa nayi wuraren karfe biyar na yamma .
A razane na mike akan gadon a zatona har magariba yayi a lokacinn saboda yadda gari yai duhu sosai da sauri na fada ban daki na dauro alwala na gabatar da sallah azahar da la,asar a tare don naga lokaci yayi.
Falo na fito halimatune kawai a falin zaune tana kallin wani hausa film a tauraron dan adam na zauna ina fadin halimatu shine baki tasheni inyi sallah ba ?
Ta dago tana fadin yayan mu na shiga in tashe ki naga kin samu barci sosai nafito na barki kada naja maki ciwo.
Sallah ai yana gaba da komai na bata amsa tare da fadin kinci abinci ko tace tun dazun mukaci da maizube itama tana maganan baki fito ba ai.
Anty bata dawo ba har yanzu na sake tambayan ta bata dawo ba ta bani amsa tana mayar da hankalinta wurin tv dake aiki.
Ban dade da zama ba aka turo kofan shiga gidan anty fadila ce ta shigo da kaya niki niki a hannun ta tana sauri don feshin ruwan da aka fara lokaci guda.
Anty kin dawo na fada inda nake zaune tana fadin kin gani sai yanzu ban farga da hadari a garin ba sai ganin wuri ya rufe kawai nayi ina kasuwa.
Ina can kuma mijin ki ya kirani yana min masifa dan yace a kai maki waya nace bana kusa dake ya fara min sababi.
Wai ya kira baki dauki waya ba yasa ya kirani yana tambayana kina inane ya kira baki daga waya ba .
Barci nayi anty tun bayan fitan ki na kwanta sai yanzu na falka na fito amma don me zaiyi fada dake mutumin da ba damuwa yayi da kiran mu ba ko yaushe.
Fada sosai fa yai min har saida hankalina ya tashi na baro gida ba shiri wai bamu dauke shi da muhinmanci ba da zan fita meyasa ko text ban masa zan fita ba.
Idan wani abu ya same ku fa bana gidan ke fada sosai yayi yau din kan hakan ta fada tana kokarin kaiwa zaune.
Uhm kawai nace ba tare danayi magana ba dan ban san me zan fada ba taci gaba da fadin na gano yana da dan saurin fushi sai kin kula da hakan.
Don namiji mai saurin fushi yana da wuyan sha,ani sosai irin su idan sun soma shiru kawai ya kamata mace tayi masu har zuwa lokacin da zai sauka da kansa.
A,a kin dawo fadila maizube ta fada tana fitowa daga part din dakunan kwanan mu haka yasa muka mayar da hankakin mu wurinta.
Saida ta zauna take fadin yanzu dai garin nan ashe baida wuyan samun ruwan sama akoda yaushe.
Wayan hannun tane yai kara ta dauka tana fadin baya baida kadan malam ne yake kiran layin na ta mike ta bar wurin zuwa inda tafito da wayan a hannun ta.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAW🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
5️⃣0️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAR UWA IDAN KIN GANI KARKI KARANTA IDAN BAKI BIYANI HAKKINA BA NA FITAR MAKI DA HAKKI NA FADA LITTAFIN KUDINE DON ALLAH, , , ,
Kina jina malam ya fada na amsa a sanyayye da ina ji malam kada kisa damuwa ko kadan a wanan mafalkin naki don har gobe haske na gaban duhu.
Matuka kina rike da ayar Allah a tare dake babu wani shedani ko wani mahulunkin da zaiyi galaba a kanki face sai in hakan mukaddarine daga Allah dama yana a cikin kaddaran ki.
A iya binciken da nayi na gano wanan mutum wani shedanine dake tare da mijin ki a kullun wanda ya sha alwashin ganin bayan duk wata macen da zata rabi mijin naki.
Ba akanki kawai yake shedan shi ba duk wata mace hatta uwar data haifeshi da zai iya sai yayi sanadin raba alakan shi da ita.
Saidai a garemu wanan abin matukar zaki rike adduan dana baki kafin kuzo wanda shi din makamine dama ga mumuni ga bayin da suke mika al,amarin su gurin ubangijin su koda yaushe.
Malam shidin ba mutum bane kamar yadda nake yawan ganin sa a mafalki ko na tambaya a cikin sanyin murya da damuwa.
Murmushi naji malam din yayi tare da fadin a buncike na dai shi din mutum ne kamar kowa saidai shedanin gaske ne na kwarai.
Hasbunallahu wani imal wakil na fada a sanyaye tare da sauke ajiyan zuciya don tsoro da fargaban da ya ziyarci zuciyana a lokaci daya naji malam din yace.
Saidai abinda nake so dake Abu shine ki kwantar da hankalin ki da sannu zaki fahinci waye shi wanan mutum din cikin masu alaka da mijin naki.
Shi mutum masheranci ba kasafai kake saurin gane shidin makashin ka bane sai idan ka kwantar da hankalinka a sannu zaka fahinci duk wani mai binka da sheri a doron kasa ko ta wurin maganan sa ko yanayin kallom sa gareka da dai sauran su.
Mun dauki lokaci tare da malam yana kawo min ayan Allah da hadisai har saids hankalina ya kwanta naji duk tsoron dake raina a lokacin yana gushe min a lokaci guda.
Bayan sallama da malam din na koma gaban gado na zauna da wayan a hannuna na fara tunane wanan wani sabon kaddarane kuma ke shirin tunkaroni a yanzu.
Ina zaune ashe hawaye na zubo min ban sani ba sai jin muryan anty fadila nayi a kaina tana fadin me kuma ya faru haka zainab ke kadai a daki zaune kina hawaye haka ?
Kaina dago ina sauke sanyayyen ajiyan zuciya ina kare mata kallo tana tsaye da wani leda a hannunta fari ta karaso shigowa cikkn dakin tana maimaita tambayan ta a gareni lokaci guda.
Meya farune kuma don nasan ba zaki zauna haka kawai kina zubar da hawaye haka ba ke kadai a daki zainab ?
Ki saki ranki dani wallahi na fada maki ni mai taimakon kine ko da yaushe zainab don ciwon ya mace na mace ne yar uwanta ko kuma zancen fadan da mijinki yayi min ne ya sakaki wanan kuka yanzu ?
Kaina girgiza ina kokarin kakaro murmushin dole a fuskana kada ta dauka wani abu nake boye mata haka don ban da niyar fada mata wanan sirin nawa.
Nace anty ba komai bane kawai tunanen makoma na a gidan nan nakeyi sai hawaye yake zubo min ban sani ba ina kokarin share hawayen dake fuskana din.
Dafani tayi tana fadin kinga irin mazan ku dama tsada sukeyi koga matayen auren su idan kinga mutum da kyau ga ilimi ga dukiya uwa uba wayewa lamarin shi gaskiya sai a hankali dama.
Nasha fada maki ba sanya zakiyi ba saifa kin dage zainab a wanan zaman naku kada ki damu da duk wani hali da yake nuna maki a yanzu .
A sannu a hankali komai zai daidaita a tsakanin ku ke barin fada maki gaskiya daga yan mata har manyan matan barikin garin nan.
Duk idon su akan irin mazajen nan suke ko yaushe burin duk wata mace a yanzu shine ta samu gidan hutu irin wanan ta yadda zata shiga tsara ta nunawa duniya ita watace a gari abin kwatance.
Ke bari ma dai in maki na mahaukaci ai yanzu idan kayi sa,a ka damki namiji kada kayi sakaci dakoma wayeshi kama abinki ki damke ta yadda matan waje zasu gane ayya yana gaba da tsakuwa wurin taunawa.
Don haka kama jiki kafin yazo ki nuna mai ke yanzu ba da bane a gurin ki kinsan kanki kinsan ajin ki ta yadda zaiji shayin yi maki wani iskancin su na maza can.
Dago kai nayi da sauri ina kallon ta don jin abinda ta fada ni ta yaya zanwa mutum kamar ya jafar wani sallo ko kissa can har yasan ni din mace ce ta fada a duniya.
Tace kina mamaki ko zainab zakice nace maki lokacin da zaki kama shi a hannun ki kina juyawa yadda kike son abinki da kowa zaiji a ransa dama ace shine a matsayin ki a lokacin .
Jin abinda ta fada yasani sauke wani irin ajiyan zuciya mai dan karfi don jin zancen ta nakeyi kamar almara a kunnuwa na.
Har yaushe hakan zai faru da take ta fada a gareni ni din da ban ko gama sanin matsayina ba a zuciyar shi har take min hasashen hakan yanzu.
Kina da kyau da zaki sace duk wani zuciyan da namiji zainab irin kiran ki maza da yawa suke so a rayuwan su saidai in hakan bai samu garesu ba dai.
Kin koga yadda kika koma a cikkn kan kanin lokaci zainab yanzu wasu kayan ne na sayo maki irin wanda ya kamata mace na sakawa a cikin gidanta don jan hankalin mijin ta ba yanzu zaki amfani da wanan kayan ba sai lokacin da mijin ki ya dira a kasan nan.
Dan murmushin yake na sake mata a fuskana kawai ta fara daga kayan har kala biyar babu wanda zan iya fita ko falon gidan dasu a ganina balle wai gaban shi ya Jafar din da take nufi.
Godiya nayi mata a fili a zuciyana kuma fadi nake Allah ya sauwaka min sakace wata karuwa can riguna haka duk a bude kamar rigan turawa marasa tarbiya.
Zai maki kyau sosai ta fada tana kara dagasu tare da fadin ina gani su naga sun dace dake sosai yasa na sayosu tunda akwai kudi a hannuna.
Nagode na kara fada a cikkn kulawa da nuna girmamawa a gareta kuma na kula da hakan yayi mata dadi sosai ta mike tana fadin don Allah ki saki ranki na fada maki saifa kin jajirce sosai ba a sanya a harkan aure.
Kwana biyun nan nikan na mayar da hankalina a wurin addua ne sosai da kai kukana gun ubangijina Allah kuma sai nake jin natsuwa da kwanciyan hankali yana kara shigana ko wani lokaci.
Hakama maizube na kula da tana tayani da addua don itama tana bata lokaci sosai wurin fadawa Allah al,amarin mu.
Falon gidan muke zaune bayan sallah la,asar wanan ya zama muna kamar dabia a gudan a wanan lokacin mukan hadu nan mu dinga fira da juna ana dariya.
Wanda hakan kan min dadin a rayuwana har in manta da wani abu a tare dani gashi a sannu ina matawa da tsoron mami a cikin zuciyana.
Saidai tunanen hjy da kewan ta har yanzu yana nan daram zaune a raina don tsohuwar ba abun mantawa bane a rayuwana don jinta nake kamar itace Asabe kakata a guna.
Yun hadarin yamma ya zama kamar al,ada a garin abuja din haka yanzu ko an hada bai faye damuwan mu ba kamar farko.
Da wandone baki irin na mata mai dane jiki a jkina iyakarshi idon kafana hakan yasa santala santalan kafana fitowa fili gasu fari sol dasu don tsaban samun dadin da nake ji yanzu tare da rashin wani aiki da banayi a yanzu yasa kafan ya kara min haske sosai.
Sai dan riga irin na mata dake dan bude daga kafadunshi zuwa iya gwiwana mai launin kalar kampala jikin rigan wanda ya dauki kalar jikina da kyau.
Sai hula dana saka a kaina mai ribon ta baya ya gashina dana daure yasa yadan dago ya kara min kyau.
Wanan duk aikin anty fadilace wace take matsa min da nayi wanan shigar tun ina kunyan hakan har nazo na daina ina fita hakan kamar yadda ta umurceni dayi din.
Ruwane ya gwauce kamar da bakin kwarya muna zaune muna hiran mu bamu daga a falon ba don sanin lokacin sallah baiyi ba a lokacin.
Duk da ruwane mai karfi da akeyi hakan bai hananu mu jin dirin motoci da horn a gaban gidan ba lokaci guda saidai hakan bai wani damun ba don ji muke kamar hadirin ne haka.
Don haka hankalin mu kwance muke hiran mu batare da kawo komai a ran mu ba lokacin sai ji mukayi kawai an turo kofan falon da muke zaton a rufe yake.
Don bamu barin kofan kasafai a bude hakana a namu zaton yana rufe a lokacin ashe a bude yake jin aturo kofan yasa hankalin mu ya koma a kofan lokaci guda.
Shine ya shigo falon ba tare daya dago kai yasan damu a falon ba yana dan kakabe ruwan daya dan taba mai jiki daga waje wajen shigowa gidan.
Gaba dayab mu a cikin mamaki muke kallon kofan don jin anturo da mamaki karara a fuskokin mu sai ganin shi mukayi tsaye yana kakaban ruwa a jikin shi.
Kafin ya dago kai ya sauke idon shi garemu idanuwan shi masu haske kamar kwan lantarki ya kura min ido da maki a fuskan nasa.
Tsaban rudewa da fargaba yasani mikewa lokaci guda don rabona da ganinsa yanzu kusan shekara daya ke nan ake batun rufewa tun bayan daya dauko mu a kauye tare dasu maizube da halimatu ya tafi sai wanan karon dana gansa.
Idanu ya kara watso min sun kara fari da girma gasu dal dasu tankar hasken lantarki saboda tsaban jindadin da yake samu.
Ga wani girma da kwarjini daya kara baiyana mai alaman jin dadi ya zaunu mai a yanzu fiye da lokacin daya barmu a baya.
Masangalin kujera na dafa a cikin kyarman murya nake fadin sannu da zuwa yaya .
Sai lokacin ya dan yi kamar wanda yai shock a cikin basarwa da dakewa ya amsa da uhmmm yana karasowa cikin falon.
A daidai lokacin ne kuma aka sake turo kofan saiga wanan yaron nasa ya shigo dauke da jakkar kayan shi yar karama.
Shima tsayawa yayi yana kare muna kallo cike da fara,a anty fadila take masu sannu da zuwa da signal ta nuna min in karbi kayan a hannun yaron nasa da yake rike dashi a bayan shi.
Na karasa cikin takon da bansan inayin shi ba zuwa inda suke tsaye din na dan gwauta ya jafar din zuwa amsan yar jakkar kayan.
Sai cewa yayi cikkn wani murya mai shrge dana mata barshi kawai zan karasa dashi ciki ya fada yana kokarin wuce inda nake tsaye.
Da sauri anty fadila ta amsa da fadin is her duty give it to her ya dago yana kallon ta a cikin mamaki kamar ba zai bayar ba sai kuma ya mika min jakkar.
Kamar kullum wanan yaudararen idon nasa ya watso min wanda na riga dana saba ganin wanan kallon nasa tun ina a gidan mami zaune idan sun shigo tare da yayan.
Zama sukayi a falon yana gaiswa da maizube da halima datake murnan ganin yaya din sai faman washe baki da takeyi don ganin sa.
Bankai kayan dakin ba don a rufe yake tun lokacin kitchen na nufa a can na samu anty fadila tana hada masu abin sha tana ganina tace good oya dauki maza kikai masu wanan.
Na dauko har lokaci yana zaune suna hira da maizube sama sama na dire masu ruwan da drinks a gaba shi kamar yadda ta koyar dani din inyi idan ya shigo.
Wanan yaushe ta koma haka yaron nasa ya fada a daidai lokacin da nake mikewa daga dukawan danayi ina aje ruwan cikin kashe murya.
A takaice na amsa masa da kwanaki wanda ni kaina bansan zanba da amsar hakana ba alokacin fito min tayi a bazata.
Kaishi kawai ya girgiza cikin wayayencewa gami da basar da disgashin da nayiba take.
Na juya zan bar wurin naji ya din na fadin dawo ki zuba muna yanauin maganan sa kamar a kasalace yake a lokacin.
Na dawo badon naso ba na fara zuba masu a hankali abin mamaki sai bayan na zubane wanan yaron ya mike ba tare daya dauki nasa yasha ba yana fadin.
Zai fita yaga sauran wa yanda suke tare dasu a waje ba tare da ya jafar din ya bashi amsa ba yaba zaune ya dafe kanshi da hannun shi daya har ta fice falon bai masa magana ba.
Dauka nayi nikan na mika mai a cikin ladabi da girmamawa sai naji yana fadin thank you bayan ya karba daga hannuna.
Banyi mamakin jin kalman daga bakin shi ba don godiya ga bature ba wani abu bane wanan na saba da godiyan su tun a gidan mami.
Saidai naji dadin hakan a raina don godiya wata kalmace mai nuna yabawa ga mutum ga wanda akaiwa hidima.
Yana gama sha ya mike tsaye ya nufi hanyar dakin da yake shine nasa din a gidan wanda har lokacin dakin yake rufe.
Ina ganin ya shige na sauke wani irin ajiyan zuciya lokaci guda kamar wace ta tsira daga wani abun tsoro.
Maizube ne ta fara mikewa tana fadin wanan yaron yai muna bazata shigowa haka babu sanarwa a garemu Allah yasa dai abincin da akayi zai gamshe shi.
Anty fadila tana kitchen din zata bada umurnin abinda za a girka masu yanzu na fada ina kokatin zama.
Ke kuma ina zaki zauna nan miji yana gari ai tashi zakiyi kije inda yake ko da wani taimako da zaki masa yanzu.
Wani iri naji a raina idan naje mezan masani don dai kawai in basar da zancen ta sai kawai na mike kamar zan nufi dakin sai bayan ta shige dakinta na dawo na shige nawa ba tare da nayi abinda tace min din ba.
Ban dade da shiga daki ba wayana ya dauki kara da mamaki na isa inda wayan yake na dauka anty fadilace ke fadin kina inane ?
Daki na bata amsa a takaice tace ki sameni a kitchen kai tsaye ta kashe wayan haka yasa na mike tsaye nafito zuwa kitchen din.
Nan na samu sunata aiki a kitchen din tare da banufar dake dafa muna abuncin a gidan tana min bayani muna aikin har muka karasa daidai lokacin da aka shiga sallah magariba don dama yanayin hadarin ne yasa garin duhu kamar magariba yayi a lokacin.
Bayan mun gama jera komai nakaiwa su maizube nasu a dakita na koma dakina don gabatar da sallah na.
Wanka na farayi kafin nayo alwala nafito na tayar da sallah din ban daga daga gurun ba sai danayi duka sallalolina gaba daya nayi kafin in tashi in gyara jikina.
A cikin wani dogon riga har kasa mai laushi sai kaina dana gyara tare da daura dan kwalin rigan ta hanyar sako bellen daurin gefena duka biyu wanda yin hakan yabada wani ma,ana a gareni.
Fitowa nayi falon ban samu kowa a falon ba sai kayan abincin da aka jera masu saman table masu kyau na zamani da daukan ido wanan duk aikin anty fadilace.
Ina shirin komawa bayan na karewa falo kallo da irin kamshin dake tashi a cikin sa saboda gyara na musaman daya samu dan shiga dakin danayi don yin sallah.
Anty fadilace ta fito take fadin yyauwa dama yanzu nake shirin shiga surin ki na kiraki ki samu mijin ki a daki ki fada mai abinci na dinning ki kula da wanan matukar yana gari a tare dake wanan yana a cikkn aikkn ki daga yau.
Dan jin nayi ina tunane a raina na yadda zan iya tunkaran shi da wanan zancen kamar ta shiga zuciyana taga abinda nake tunane a lokacin.
Take fadin kwaliyan ki yayi kyau matuka yanzune kika nuna min kina amfani da shawaran da nake baki kullun.
Don haka sauran aiki yana gareki kije ki sameshi a dakin shi tunkan ya fito hakan zai kara kawo kusanci a gareku ko yaushe.
Idan kuma ya fito ki tabbatar da kin zauna sai idan ya gama ci kina zaune a gurin wanan ma wani isimine na mata da mata da yawa suke sakaci dashi tana gama fadi ta juya don barin wurin
A hankali na ja kafana zuwa dakin bakina yana cike da addua na tun kari dakin nasa yayin da gabana sai faduwa yake min din tsoro da fargaba abinda yin hakan zai iya jawo min idan na kai kaina gareshi din.
A kofa na tsaya na da runtse idanuwana tare da tattaro karfi da kuzari azuciyana na kai hannu ina kwankwasa kofan.
Kusan sau uku ina kwankwasa kofan kafin naji ana kokari bude kofan daga ciki hakan ya dan sani ja baya a hankali tare da tsoron hakan a raina.
🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
5️⃣1️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAR UWA DON GIRMAN ALLAH YAR UWA KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA, DARI UKU NE KUDINSA DON NEMAN KARIN BAYANI KI KIRA WANAN LAYIN 08036959257, , , , ,
Shiru babu wanda ya bude kofan hakan yasa na tura kofan a hankali na shiga dakin csn na hango shi zaune saman sallay yana azzakar da counter a hannun shi.
Jin alama an shigo mai dakin yasa shi dago kai a hankali daga inda yake zaune ya hada gwiwan shi biyu wuri daya ya hade da hannayen shi saman kafan da counter din shi yana danawa a hankali.
Idon shi ya sauke a kaina kafin nayi karfin halin karasawa wurin shi a hankali ina fadin bansan kana ibada bane dama nazo fadama abinci na saman dining an shirya ma.
Kai ya gyada min a kasalance ba tare da yai min magana ba ganin haka yasa na juya da sauri don barin dakin don gabana dake fadawa ban ko tsaya yiwa dakin kallon tsab ba don ganin irin alatun dake cikin dakin nasa.
Duk da ganin namu dakin da muke ciki ya kai iyakar haduwa wurin tsaruwa sai naga wanan din nasa kamar shagone na shiga.
Ke jimana naji muryan shi a bayana yana fada a hankali naje na tsaya ba tare dana jiyo na fuskance shi ba don yadda yai maganan.
Da ban nan mami tazo gidan nan naji tambayan yazo min a bazata don haka na basa amsan tambayan da fadin ya mamud daine yakanzo dubamu sai ko ya jamal da yazo sau biyu .
Tsaki yaja yana mikewa tare da fadin ba wanan na tambaye ki ba ai nasan da mamud yana zuwa dubaku ai.
Gabana yayi dam sai nayi shiru don yadda ya katseni a cikin fada lokaci guda abin ya ban mamaki matuka.
Don haka tun bai fadi komai ba kuma naja kafana na bar dakin don gudun wani fadan kuma.
A tsakiyan falo na hango Tajjuddeen tsaye kamar yana nazarin wani abu saidai yana ganina ya nufo inda nake da sauri yana fadin.
Me kika shiga yi dakin ogo a yanzu wa ya baki daman shiga masa daki a wanan lokacin?
Idanu na zaro a tsorace don don jin irin tambayan daya jefo min a bazata wanda imani da tsoro tambayan ya mamayeni lokaci daya.
A cikin karfin hali na bude baki nace waya aikoka tambayana wanan dalilin yanzu.
Wani irin kallon tsana ya watso min kafin yace dani babu saidai hakan kada ya baki daman kusanta kanki gareshi kuma.
Kaina na dukar kasa nayi dan shiru kafin in dago a fusace ince dashi matsayin ka da kimar ka baikai ka yi man wanan tambayan ba a yanzu .
Kafin in bude baki in bashi amsa ya nunani da yatsa a fusace shima yana fadin ke ni zaki rainawa hankali ashe baki da kunya da nake ganin ki haka ?
Gaskiya jackson ya illanta maki rayuwa daya tsaya ya mayar dake mace haka mara moriya gashi kina neman kai kanki ida matsayin ki bai kai ba.
Idanun sa sun kada sunyi jawur zuwa tsatsan bacin rai dani haka nima domin maganganun shi sun daga min hankali sun tsoratani lokaci guda.
Na runtse idanuna ina jin kuna da radadi a zuciyana kafin in bude udanun nawa na sauke su a kanshi cikin tsana ina fadin .
Dakata wai malam ka daina yaba min kalamai kamar wani ya aikoka gareni kai a wani matsayi kake da zaka tsareni da wanan maganan akan mijina.
Ciki da alaman mamaki ranshi bace ya ware idanuwan shi a kaina yana fadin what ke kanki daya kuwa yarinyar nan kinsan ko wa nake a wurin jackson ?
Nima a fusace nace gomane gareni kai waye da har zaka tsareni da wanan dokan akan ya jafar din.
Daki kuma ko gobe zan shigesa ne don dakin mijinane bana wani ba kai wani matsayi kake dashi a wurin shi daya har ya baka daman yi min wanan tambayan ?
And kuma ka sani duk duniyan nan banga mahalukin da a yanzu ya isa min wanan banzan tambayan da kai min ba a yanzu kokai ka fadane a cikkn maye kila.
Kamar yadda kace rayuwata ta samu illa idan har hakane ina ganin ai wanan damuwatace bana wani ba ko ?
Daga hakan na juya na barshi a wurun tsaye baki bude yana bina da kallon mamaki don jin abindana fada.
Nayi kokarin mayar da mood din fuskana a hakan bai dameni ba saboda kar ya gane maganan shi yayi min ciwo sosai a raina.
Harna nufi hanyar dakina sai na canza shawara na nufi dakin anty fadila a lokacin saidai bata a cikkn dakin yasa na jiyo don na koma dakina cike da bacin rai atare dani.
Da kyar na samu na karasa daki na shige a take naji wani irin zazzabi yana neman ya rufeni lokaci guda.
Gado na fada na dafe kaina gabana yana faduwa nake fadin wanan sace irin bakar ranane haka gareni da har wani dan aiki zai fada min irin wanan magana kai tsaye.
Komawa nayi na zube rigingine ina lumshe idona yayin da buguwan zuciyana yake karuwa gareni lokaci daya.
Na dade kwance a hakana kafin tunane yazo min ina tambayan kaina shi din wai wani irin matsayi yake dashi a gurin ya jafar din da zai min wanan kalamin haka ?
Cikin wani hanzari na mike zaune bandaki na fada na dauro alwala nazo na hau sallaya na fara sallah ko wace ruku,u da sujjada sai na gayawa mahaliccina Allah damuwata kafin na danji sanyi a zuviyana.
Ban kara fitowa falon ba kamar yadda anty fadila ta umurci inyi don wanan maganan da mukayi da tajjudeen din ranan ga abi kuma ya tsaya min a raina sosai don ko barci bai barni nayi ba sai faman tunane da nakeyi a daki ni kadai.
Washe gari ma ban leko waje ba har wuraren sha biyun rana ina dakina a cikin damuwa da fargaba da zancen wanan mutumin a raina .
Gashi lokaci daya duk nabi na susuce ga baki daya idan mutum ya kalleni zai fahinci ina cikin damuwa a tare dani.
Suko a zaton su maizube ina wurin yaya jafar dinne a can na kwana a wurin sa don hakane ma tunda ta shige dakinta bayan zuwan shi bata sake fitowa ba har wanan lokacin.
Anty fadilace da tajini shiru ta leko dakin sai ta sameni a kwance cikin wanan yanayin na damuwa a tare dani din.
Tunda ta shigo dakin take watsa min kallo a razane kamar tana nazarin yanayina yayin da niko ganin ta dakin nawa yasa na dan kakaro fara,an dole a tare dani.
Saida ta kai zaune a kusa dani take fadin meke faruwane dake haka kin rame haka a cikin kwana daya ?
Kina da wata damuwa ne a tare dake da ya mayar dake haka lokaci guda duk kin zabge ko wani abin ke damun ki haka ko kuma ganin mijin kine ya sakaki fargaba ?
A ladabce nace da ita a, a anty lafiyata kalau illa dai kewan innata da kannena da nakeyi duk kwana kin nan.
Murmushi tayi taba fadin baki tashi kewan su ba saida mijin ki ya dawo kika saka damuwa haka a zuciyar ki lokaci guda.
Kaina na sada kasa ina dan murmushin yake kafin naji tace kinga fada min damuwan ki zainab don nima akwai abinda yake damuna dan zuwan mijjnki garin nan .
Don ba wani ya fada min ba Allah ya nufa inji komai a kunnuwa na yau din nan da safe na fito don duba masu girki dazu.
Da sauri na dago kai ina kallon ta don jin karin bayani daga abinda take hashe din lokaci guda kuma sai kunyar hakan ya lulubeni dan ganin yadda take kallona na kasa fassara hakan.
Naji tace watau zainab dazun din ne na tsunkayi wanan mutumin na tare da mijin ki yana waya a hasale .
Saidai jin abinda yake fadane yasani maida hankali in saurare shi dan na fahunci zancen kamar ya shafeki ko wani a gidan nan duk da ban tabbatar da hakan ba gaskiya.
Don naji yana fadin gaskiya ogan mu bai kyauta min ba ni a yanzu na tsani na bude ido inga wanan yarinyar a gidan nan.
A yanzu nayi nadaman yardan da mukayi har wanan mukai sake yarinyar nan ta kai haka tare dashi don yanzu gaba daya ta juye ta zama wata haddadinyar mace sosai.
Katseta nayi ina fadin anty wallahi dani yake don jiya nan da kika turani kiran yaya don na fito part din ya tsareni yana fada wai in daina shiga gun yaya din nan dai na labarta mata komai daya faru tsakanin mu.
A gigice tace wanan zancen da daure kai yake wallahi don haka kawai baki masa komai ba zai tsaneki haka ba tunda bashi ke aureki ba ai.
Me hakan ke nufi ne gareni kuma anty na tambaya cikin damuwa da tashin hankali a tare dani.
Kinsan wasu basu iya samun wuri ba ai sai sucd basa son kowa ya rabu yaci arziki sai su kadai hanyar jirgi daban ta mota daban don haka ya tsaya a matsayin sa zanwa maigidan magana kan hakan ai ta fada tana mikewa tsaye.
Ki tashi ki fita ki sake gidan kine mijinki ne banga wani da ya isa yazo yai maki wani iyawa ba a nan yanzu gaskiya don haka kada ki fara kiyi sake har hakan ya faru dake.
Har ta soma tafiya nace anty dama kin kyaleshi ai kada ki masa magana har sai idan ya kara min irin hakan zan so ayi mai magana din.
Saida ta dan tsaya kamar tana nazari kafin tace to shike nan tunda haka kikaga yafi a barshi in halinsa ne zai sake raina maki wayau ai dan iska damani sam bai kwanta min a rai ba ko kadan.
Bayan fitan ta wanka nayi na fito saida na dan dauki lokaci sosai ina kimtsa jikina a gaban mirrow kafin in shirya in fito waje sha biyu har ya gwauta a lokacin.
Tun daga nesa nake dan jiyo hayaniya a falon gidan ina dan jin muryan ya jafar din kamar yana fada sama sama wanda ban taba ganin hakan ba a tare dashi.
A hankali na tako ba tare dana san ko su waye yake tare dasu ba dasu
a falon a lokacin hankalina kwance na nufo falon .
Wanda na gani sanya saura kiris na juya don saida na kadu sosai ba kowa bane sai mami da anty Aisha a zaune tare dashi a falon .
Gaba dayansu suka juyo suna kallona a cikin mamaki da kaduwa da ganin canzawa da nayi na lokaci guda.
Mami ta dan yatsune fuska gami da tsuke fuskan a lokaci guda ta mike tana fadin ni zan koma ke nan tunda na ganka kaji sauki.
Saura kiris na sake futsari tsoron ganin mami din a bazata naga Aisha ma ta mike kamar a bazata ta ganni tana fadin cike da mamaki a fuskanta.
Zee a gidan nan dama kike zaune wai ko zuwa kikayi kema bata karasa ba don wani tsawa da mami ta daka mata lokaci guda yasa tabi bayan mami din da sauri.
Har lokacin na kasa magana sai ido nake binsu dashi a cikin tsoro da fargaba kafin na tattaro karfi da kuzari lokaci guda na bisu zuwa kofan fitan da suke shirin fita ina kokarin gaida mami din a cikin ladabi.
Tana kokarin shiga mota na karaso wurin da sauri tare da dan rusunawa ina kokarin gaida su banyi mamaki ganin irin yadda ta amsa min gaisuwan nawa a dakile ba don ba yabo ba fallasa.
Irin kallon da Aisha ke bina dashi na mamaki yasa na kara shan jinin jikina ban bar wurin ba sai da naga motarsu ta daga daga farfajiyan gidan don ko kallona mami bata kara yi ba a wurin.
Ajiyan zuciya na sauke don abin ya ban mamaki wanan wani irin kiyayya mami take nuna min hakane na ba gaira ba dalili a kaina.
Juyawa nayi na koma cikin falon gidan jiki ba karfi don ban taba zaton zamu hadu da mami irin haka ba a wanan lokacin.
Bansan har na tsaya ina tunane ba a wurin saida naji takon mutum a bayana firgigit nayi tare dajuyowa shine a tsaye daga kofa ya tsura min ido kafin ya fara takowa zuwa inda nake a nutse.
Yaja ya tsaya a gabana sai nayi saurin dukar da kaina kasa ina wasa da yan yatsun hannuna a hankali.
Maman ki har yanzu fushi takeyi damu kiyi don haka kiyi hakkuri da duk wani abinda zaki ga tayi maki a yanzu.
Samun kaina nayi da sake dan guntun murmushi a fuskana ina fadin ayyah mami har abada mami a matsayin uwa take a garen ai.
Don nima nayi missing din uwata mai tausayina da kauna na har kullun saboda kin bin umurnin ta danayi
Zan shanye duk wani bacin rai da mami zata nuna min har zuwa lokacin da Allah zai huce mata zuciyar ta akaina.
Ina fadin hakan na juya na fara tafiya don barin wurin don kiris nake dana sake hawaye a fuskana don bacin rai ga yadda mami din tayi min kamar taga mugun abu a lokacin.
A bangaren mami kuwa rai bace ta shiga mota sai masifa takeyi tare da fadin na fara yarda da zancen mutane da suke fadin harda asiri a
wanan zancen.
Yaushe na koma haka har yaushe na samu sauyin yanayi haka gaba daya na canzawa ganun ta idan badon a ko ina ta ganni zata iya shedani ba don zaman da tayi a tare dani da shakuwan da mukayi a baya.
Da sai tace wanan watace mai kama dani dai amma ba ni zainan din da ta sani band na canza haka lokaci guda a dan watannin da tayi bata ganni ba.
Muryan Aisha ya katse mata tunane da take fadin mami kinga yadda yarinyar nan ta koma lokaci guda.
Aisha ki rufa mi bakinki indai a kan zancen yarinyar nan ne zee ne kada in saba maki a gurin nan yanzu ki barni naji da abinda ya dameni please.
Jin hakan tayi shiru ta barwa ranta abinda ta hango a tare danni wai zeey din mamice wanan ta koma haka kuwa kodai mai kama da itace takoma haka haka wai ?
Har mami takai gida hankalinta a tashe sai innuwana take hanngowa a idanun ta tana kokarin kawar da zancen a ranta.
A gaskiga tasan yarinyar ba laifi a ko wani ba gare saidai zuciyar ta ya kasa natsuwa da hakan a kanta
🦅 ABU CIKIN DUHU
🦅
5️⃣2️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BARKA DA JUMMA,A YAN UWA UBANGIJI YA SADAMU DA ALHERUN DAKE CIKIN WANAN RANAN ALLAHUMA AMIN ALLAH, , , , , ,
KADA KI MANTA LITTAFIN NAN NA KUDI NE DARI UKU NE NA FITAR MAKI DA SHIGA HAKKIN WANI NA FADA MAKI GASKIYA YAR UWA DON KIRA ZAKI IYA KIRANA DA WANAN LAYIN 08036959257.
Don Allah yar uwa ki guji shiga hakkin wani kada ki raina nauyin hakki a gareki kiji tsoron Allah don akwai ranan tambaya.
Ganin mami ya tayar min da sabon miki a rains don haka na shige dakina kai tsaye na fara darza kuka kaman an aiko min da sakon mutuwa.
Tambayan kaina nake menayiwa mami dana cancanci wanan sakamakon haka a gareta ?
Kafin in koma neman mafita a raina na abinda zai fitar dani wanan sarkakkiyar duhun dana jefa kaina a cikin rashin sani.
Duk da nasan ba nina jafa kaina haka kai tsaye ba yadda ake zato banda zabi a kan hakan daya faru dani sai yadda akayi dani a yanzu.
Ina cikin wanan tunanen naji an banko kofan dakin an shigo da sallama ta murya na sheda anty fadilace ta shigo dakin ashe.
Tun a kofa take bina da kallo rai a bace don a zatonta kuka nake na wani abu a yanzun ma kuma.
Sai bina take da kallon mamaki na wanan sallon iskancin dana tsiro yi a gidan bayan dawowan shi kasan ga yadda muka aje zanyi a baya da ita yanzu nazo ina masu faman koke koke haka a gida.
Wanda hakan ke nuna alaman kasawa a gareni bayan duk abinda ta koyar dani a bayan shi wanda hakan ke nufin zaman mu a tare baiyi tasiri ba kenan a yadda nake nunawa yanzun.
Wuri ta samu takai zaune a gefena ba tare da tayi min magana ba na dan lokaci kafin na dago kai na dan kalleta cikin wani yanayi ina fadin a cikin muryan kuka.
Anty me nayiwa mami da take nuna min wanan irin kiyayyan haka a fili shin anty don danta ya zabeni a matsayin sarakuwa a gareta hakan laifine anty don kawai banda gatan daya dace in zama sarakuwar nata ko mai ?
Ajiyan zuciya naji ta sauke tare da fadin meye damuwan ki da matar da ba,a gida daya kuke zaune da itaba yanzu.
Na katseta da fadin amma ai a gidan danta nake zaune anty don haka mami nada daman da zata shigo gidan nan ko wani lokaci kamar yadda dazun tazo na ganta ina gaida ita ta kyaleni.
Tazo gidan nan yau ke nan ta tambayeni cikin mamaki tazo anty na bata amsa wasu hawayen suna zobo min a idanuna lokaci guda naci gaba da fadin .
Har kofan gida na bita ina gaida ita mami ta kyakeni shin anty ni a haka rayuwana zai kare a gidan nan bansan matsayina a gun mami din ba ?
Zata soki zainab na fada maki hakan yafi a kirga kedai kawai a yanzu kiyi kokarin Allah ya mayar dake wani abu a rayuwa.
Amma fa sai idan kin cire damuwa da wanan shirmen hakan zai faru dake don idan kin matsa kin tayar da hankalinki karshen sa ki zama wani abin ki fiye da hakan ga kowa.
Do haka nake fada maki a kullun ki daure ki zama wani abin kwantace a duniya kafin hakan ya faru in ma har bata kaunar ki da danta ai ba kece kika dauko kanki kika kawo gidan nan ba kawo ki akayi da sunan aure.
Don haka ta samu danta daya kawo ki din tayi fadan haka dashi bake ba ke meye laifin ki a cikin zancen nan bayan cutar da rayuwan ki da akeyi yanzu.
Ta yaya mijin ka zaiyi tsawon tafiya irin wanan ya dawo a cikkn kasa ba tare da nuna maka wani kulawa ko damuwan shi a kan ka ba.
Don hakane nake kokarin nuna maki hanyoyin da zamu bi har mu samu a samu kanshi gareki idan ma wani abin ne akai maku a tsakanin ku har hakan ke faruwa.
Har wani lokaci muna dakin tana bani shawara akan mami dama shi ya jafar din akan inta kokarin in kawar da wani kunya ko nauyinsa a raina indinga cusa kaina gareshi ko yana nuna min baya son hakan da nake mai.
Jinta kawai nakeyi a raina sai fadi nake ta yaya zan kai kaina inda za,a wullakantani a daukeni ba kowa ba.
Zandai zauna a matsayin tallafawa rayuwan iyayyena da yan uwana a gidan sa don ni kaina nasan da bankai matsayin mata ko masoyiya a gareshi ba.
Bayan nayi sallah la,asar ne na fito zuwa dakin maizube inda na sameta zaune tana shan ferfesun a cikin wani plate mai zurfi a gaban ta sai tururi da yake tashi da kamshi a cikin plate din.
Ta dago tana fadin yanzu nake fadi in gama in kara lekaki zuwana biyu dakin yana rufe na dauka ai kina wurin mijin kine tun dazu ?
Dan murmushin yake nayi iya fuskana a raina ina fadin wani miji da baima san da zamana a gidan nan ba .
Zama nayi saman gado ina gaida ita tare da fadin tun safe ina daki kwance ban dai fito bane tunda yanzu gidan akwai maza masu shigowa ko wani lokaci.
Tace nima abinda ya zaunar dani dakin nan ke nan kada su takura da zaman mu haka shiyasa ma na fadawa malam zan dawo zuwa jibi tunda dai Allah ya dawo da mijin naki lafiya kuma.
Da sauri na dago kai ina kallonta tare da fadi cikin mamaki ki koma gida kuma maizube shifa ba mai zama bane kasan nan wata kila wani abin ma ya kawoshi yanzu haka dayazo din.
Don dazun ma naga mahaifiyarshi tazo gidan nan da safe sai naji tace a cikin mamaki ta shigo gidan nan bamu sani ba yar nan ai a gaisa dai ko ?
Maizube koni fitowa nayi na gansu a falo tare dashi haka kuma naga ta mike a cikin bacin rai ta bar gidan nan ko gausuwa dana bita waje nayi mata ban samu amsawan arziki a wurinta ba ta wuce.
Kai wasu dai sun dauki duniyan nan da zafi a ransu har yaushe wanan matar zata sauko daga fushi da kaddaran Allah da takeyi ne daku ?
Kada ki yarda ki biye ma duk wani hali datake nuna maki na kyama a gareki dan ba ita kike aure ba biyewa halinta kuma mijin ki ba zaiji dadin hakan ba don mahaifiyarsa ce ita.
Kinga kuwa ba zai taba lamuntan hakan ba koda itace bata da gaskiya kuwa ranshi zai bacine ga abin da zaki mata ke don haka ki daure ki hade tunda ba ko yaushe ne kuke haduwa da ita ba sai irin haka idan tazo ko kinje inda take din.
Shima kasa ki daure da halinsa ki zauna kiyi hakkuri mai hakkuri yana tare da riba wata rana duk wanan abin zai zamo tarihin rayuwa a wurin kine a kuma hada da addua ga komai da sadaka don kariya ga ko wani irin bala,in rayuwa.
Insha Allahu zan yi maizube na gode da shawaran da kuke bani a kullun keda anty fadila a gidan nan ba zan taba matawa daku ba a rayuwana na fada idanuna yana kawo hawaye a lokaci guda.
Nikan yaya kowa keson nayi ta cusa kaina ga ya jafar ne mutumin da har yau ko murmushin arziki ban samu a gurin shi ba balle wani maganan arziki irin na mata da miji ya shiga tsakani na dashi.
Ta yaya ake son in biye masa har muyi zaman auren da mutane suke hasaso min rayuwan jin dadi nan gaba dashi.
Don in kawar da zancen nace amma dai ba yanzu kike nufin komawan ki gida ba matar malam ?
Me zan zauna inyi a nan kuma tunda Allah ya dawo da mijin ki lafiya wurin ki kuma ai sai a raina muna hankali kuma idan na zauna haka.
Haba dai wa zai damu da zaman ki a nan don Allah kada kice zaki tafi ki barni a gidan nan ni kadai ba zan iya zama dasu ba wallahi.
Zaki iya mana ta ban amsa ko wace mace da kike gani haka ta koyi zama a gidan mijin ta harta saba da hakan kema a sannu zaki saba da zama ke dayan ai.
Maizube ban dauka wanan zaman da nakeyi a gidan nan ba na aure ne ba subbahanallahi naji ta fada da sauri har naji tsoro na dago kaina.
Idan ba zaman aure kikeyi ba zaman me kikeyi a nan kada ki yarda ki bata auren ki don wani dalili can da kike hange .
Kowa da yadda kaddaransa ke zo masa a rayuwa wanan shine naki kaddaran rayuwan kke zuwa mai Allah yayi akwai aure a tsakanin ku wanda muke fatan harda zuria idab Allah ya yarda nan gaba a tsakanin ku .
Jinta kawai nakeyi duk da nake yarinyace ni amma nasan hakan ba mai yuyuwa bane a tsakanin mu don ruwa ba sa,an kwando bane.
Tambayana tayi da naci abinci kuwa itama dai nasan kokarin kawar da damuwa a zuciyana takeyi lokacin.
Idan nabar nan zanje na duba abinda zanci na bata amsa da hakan na dan dade zaune ina tunane kafin in mike zuwa falo na bar dakin nata.
Ina ficewa falon na nufa dining erea dan samun abinda zan saka a cikina don naji cikina ya fara kugi a lokacin.
Kai tsaye wurin dining din na nufa kayan abincin dake wurin na fsra budewa a hankali gaba daya hankali na gurin abinda nake dubawa din duk sai naji ba zan iya cinsu ba a yadda nakeji lokacin.
Haka yasa sam bansan yana falon ba a lokacin yana zaune shi kadai a cikin falon ya tasa takardu da laptop din shi a gaba yana aiki a cikin su.
Zaune yake yabar abinda yakeyi ya zuba min ido daga inda nake tsaye ina bude kayan abincin danaga basu min ba nakai zaune daga inda nake tsaye din a cikin damuwa na kai zaune ina dafe kaina da alaman damuwa a tare dani sosai a lokacin a fuskana dana kai zaune din.
Kaman ace in dago kai daga inda nake zaune din don jin nauyin da jikina yayi kamar akwai mutum da yake kallona a lokacin yasani dago kai zuwa inda kujerun falon suke ina dagowa na dora idona akansa zaune.
Shine a zaune saman daya daga cikin kujerun dake falon zaune ya zubo min manyattatun idanuwan shi a kaina sai kace wani tsohon maye.
Wani kallo dana kasa fasarashi a lokacin naga yayi min mai nuni da ma,anoni da dama a gareni lokaci guda nayi saurin kawar da kaina gareshi tare da kara daure fuskana sosai na tamkesu.
Saboda kawai na kona masa rai don na dade da sanin halinsa yanzu a dan zaman danayi dasu a can gidan mami din don ba abu bane mai wuya ya disgani a wurin.
Karshema sai na mike don barin falon a lokacin don ba zan iya zama a cikinsa ba yana zaune a gurin yana zuba min idanu duk da naga tulin takardu a gaban sa.
Ina zaki naji ya fada a daidai lokacin dana mike ina shirin tafiya din jin hakan yasa na dan juyo dan kallon inda yake zaune din.
Ni ya zubawa ido yake kallo wanan karon ma dai babu daure fuskan nan nasa a idon shi don haka ban tsaya bashi amsa ba nayi kokarin barin wurin kai tsaye.
Muryan shi na koma ji yana fadin wai ba dake nake magana bane kina da alaman taurin kai a tare dake zainab .
Har sau nawa kike son in maki magana akan mami da yanzu kike wanan damuwan akan ta mami ni ta haifa ba ke ba don haka ki barni da mahaifiyata wanan ba damuwa ki bane ke .
Kalaman daya fada din sun matukar ban mamaki a raina ko dai wanan mutumin ya mata da shi yai sanadin rabuwana da mahaifiyar shine haka?
Don Allah ya jafar ka barni da abinda kaja min a rayuwana kayi sanadiyar hadani da mahaifiyar ka data nuna min kauna ta hanyan mai dani wani abu a rayuwana.
Ban zauna a gidan nan don wani dalilin ka ba sai don haka iyayyena suka zabar min a rayuwana yau gashi har wani daga cikin yaran ka yana ganin kamar auren Allah da Annabi kayi dani har yake kokarin yi min iyaka da kai a gidan nan.
Don Allah ya jafar na rokeka kamar yadda wanan mutumin ya fada min jiya a kanka na nisanci kaina daga duk wani lamari ka .
Nima a yanzu ina rokon ka ka samin ido kawai a gidan nan inyi zaman salama da rugumar kaddaran rayuwana a yadda yazo min dakai.
Ni kaina nasan gaskiya mami da wasu ke fada nidin ban dace dakai a sa,an aure ba idan makana da wani mafunune a kaina kan hakan da kayi yaya ina rokon ka ka tausayawa iyayyena kada kaja a illanta min rayuwana a gidan nan tunda har an fara yi min gargadi a kanka.
Wani kukane yazo min lokaci guda na kasa karasa abinda zan fada a lokscin don kukan dayazo min a lokaci guda din.
Yayin da shiko tun dana fara magana ya zuba min ido tare da tattara hankalin shi zuwa gareni yana kallona ba tare dayayi maganan komai ba har lokacin dana ja gwiwana da yai min sanyi a cikin karfin hali don barin falon.
Kasake yayi wani irin kunci da makina suna suna sauka mashi a zuciyar shi tunane barkatai yayi a wurin don ba mamakin karfin halin tunkaransa in fada mai wanan maganan gaba da gaba hakane ba ya daneshi.
Sai jin abinda na fada akan wanin danace yana kokarin yi man iyaka dashi a gidan nan ne tunanen shi a yanzu don yasan ba kowa ne zai mun barazan hakan ba sai Tujudeen kawai.
Ranshi yaji ya baci lokaci guda don me tajudden din zai masa wanan katsalandan a rayuwan shi ya tsorata yarinyar nan har ta tsorata dashi haka ?
Mikewa yayi da zuman bin bayana sai kuma ya koma ya dakata don zuciyar shi data gargadeshi dayin hakan a lokacin.
Da karfin gaske yake jin zuciyar shi na buga masa ya fada kan kujeran ya koma ya zauna yana lumshe idanuwan shi tare da jin magana kamar a yanzu nake fada mai su.
Mai Tajuddeen ya dauki kansa ne a yanzu da har zai mai wanan katsalandan din a rayuwan shi ba yau ba ya sani yana kishin wanan yarinyar duk da yasan dalilin shi na auren ta din.
Gashi har ya kai yaja masa raini a wurin ta ta yadda har ta iya kallon tsaban idanun sa ta fada mai magana haka iya son ranta ba tare da taji nauyin sa ba kamar yadda take ji a baya can.
A daidai kofan fitowa daga dakin sa muka hade da taju din wani kallo ya bini dashi na tsana ban tsaya bi ta kansa ba na wuce zuwa cikin part din mu kai tsaye.
A hankali ya tako zuwa tsakiyan falon har yakai bakin kujera bai iya dago kanshi ya kalli mai zuwa ba a lokacin kafin yai wani yunkuri ya tsunkayi muryan anty fadila tana fadi a bayan su.
Sir ko kuna bukatan wani abin motsa bakine a yanzu a kawo maku tana kokarin karasawa inda suke zaune take magana.
Sai lokacin ya cire hannun shi daya dafe goshi shi dashi ya dago jajjayeb idanuwan shi ya sauke a kanta tare da kada mata kai cikin karfin hali alaman a,a.
Ganin hakan koda baiyi magana ba ta gane mai yake nufi da hakan yasa ta juya da sauri ta bar wurin donta fahinci ogan nasu yaba cikin bacin rai a lokacin.
Zama taju din yayi a kusa dashi tare da tsura mai ido don ganin yanayin daya ke zaune a ciki.
Don baya son yana ganin sa a wanan yanayin yafi son ganin sa a cikjn yanayin nishadi da kuzari a tare dashi ko yaushe.
Don haka bayi kasa a gwiwa ba ya soma fadin wai lafiya na ganka haka ka zauna jiki a mace ?
Bai bashi amsa ba sai mayar da kanshi da yayi saman kujera ya daga kai sama tankar yana tunanen wani abu mai muhinmanci a lokacin.
Taju din ya kai hannun shi saman kafadan shi yana fadin wai meke faruwane da kai my man ka fada min matsalan ka ko wanan yarinyar ne take son bata min ranka ?
Cikin yan dakiku taju din yake jerawa jafar din wanan tambayan cikin bacin rai tare da kulawa a gareshi.
Yayin da jafar din ya sauke wani yar gajeruwan ajiyan zuciya ya dago kai tare da sauke jajjayen idanuwan shi ga taju din .
Kai taju din ya gyada mai tare da fadin nasan itace damuwan ka a yanzu don tun da muka shigo gidan nan naga yadda ta koma lokaci guda nasan za a samu matsala dakai don canzawan yarinyar nima ya ban mamaki matuka.
Bai bashi amsa ba sai dan shiru da yayi ya kurawa carpet ido kamar yana nazarin abinda zai fito bakin shi lokacin.
Kafin yace dashi ba itace damuwana a yanzu ba kaine taju don me kuma waya baka izinin shiga harkan gidana haka kai tsaye har kayi kokarin wuce iyakarka dani.
Taju din ya dago kanshi a razane yana kallon shi tare da shan jinin jiki don jin abinda ya fada din.
Kasan al,adan kasan mu kasan komai don me zaka wuce iyakar ka dani ka shiga harkan matana waya baka wanan daman yaushe har ka samu wannan matsayin haka ?
Kai ya dago da sauri yana dan kallon sa kafin jafar din ya nuna shi da yatsa yana fadin daga yau ban son ka kara shigowa gidan nan matukar bani na nemaka da kashigo ba.
Duk da ran taju din ya baci amma a fili sai ya daure yana fadin yanzu don wanan shine har ka wani tashin hankalinka haka ?
Sai kace wanan wani babban matsalane ni kawai nayi warni dinta ne don ta kiyayye shiga dakin ka kai tsaye bada wani manufa na fada mata hakan ba ai.
Murmushi jafar din yayi cikin bacin rai kafin yace dashi kasan nasan ka nasan halinka duk abinda zakayi ina warnin din ka akan yarinyar nan a tare dani.
Taju din ya marairaice murya kamar zaiyi kuka cikin ban hakkuri da nuna yayi laifi a gareshi nayin hakan iam sorry hakan ba zai kara faruwa ba tsakanin mu.
Shiru sukayi a falon yayin da kowa da abinda yake tunane a ransa kafin taju din ya sake fadin cikin yanayin kyarmar murya kayi hakuri please.
Sai lokacin ya dago kai ranshi a bace yana fadin kasan da kayi babban kuskure na bata min shirina akan wanan yarinyar don bazan so na rasa wanan yarinyar ba a rayuwana don ina matukar jin tausayin ta a rayuwana zaman ta yana da ma,ana mai yawa a gidana.
Taju din ya kara fadin nayi kudkuren yin hakan zuciyanane ya kasa hakkuri da ganin tana yawan shige maka da take kokarin a yanzu.
Wani kallo jafar din ya watsa mai da yasa ya mike ba shiri yana fadin iam sorry hakan ba zai sake faruwa ba tsakanin mu.
🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
5️⃣3️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH SARKI YABON GWANI YA ZAMA DOLE JINJINA GAREKU ADMINS DIN WANAN GROUPS DIN WATAU ZAURE BIEBI ISAH DA HUGUMA GROUP DA ZAINAB MAKAWA GROUP1
WA YANNAN GROUP DIN SUNCANCANCI YABO A KO INA WALLAHI DAMA SAURAN GROUP IRIN NASU DA BANSAN DASU BA A SHAFIN SADA ZUMUNTA NA WHAFFS,
DALILI KUWA SHINE DUK KYAU DA DADIN NOVEL IDAN NA KUDINE BASU YARDA A JAFASHI A WANAN GIDAN NASU.
WANAN YA NUNA SU DIN UWAYENE NA GARI MASU IYA BADA TARBIYA GA IYALAN SU DAMA AL,UMMA GA BAKI DAYA A DUNIYA SABODA KARE HAKKIN DAN ADAM YA ZAMA DOLE IN YABAWA WANAN ADMINS DIN GASKIYA IDA BAN FADA BA BAN MASU ADALCI BA A RAYUWA.
ALLAH YA KARA TSARE MUNA IMANIN MU DA ZUKATAN MU ALLAHUMA AMIN DON HAKA ZAN TURA WASU NOVEL DINA KYAUTA GA WANAN GROUP UKU AKYAUTA SABODA ALLAH DA ANNABINSA .
Tsaye yake a tsakiyan dakin yakai gwauro yakai mari ya kasa zama a dakin ya tuhuta babu abinda yake tunane sai abinda ya faru a tsakanin mu dashi din da yammacin ranan.
Ya akayi har wanan yarinyar ta samu courge din da zata iya duban tsaban idanun shi ta fada mai magana haka kai tsaye ba tare data jin tsoro ko kunyar idan shi ba.
Anya kuwa zai iya wanan yarinyar nan gaba a yadda yake tunane idan ta kara wani shekaru a hannun shi kuwa ?
Kai da sake ya fada a fili yana dafa gado ya kai zaune tare da hada hannayen shi wuri daya yana fadin yaushe ma ta zama hakan ne a gidan nan.
Wanan tana da banbaci da zainab din da ya sani a baya wanan kamar idanuwanta ya bude yake gani idan ba karya yakewa kansa ba.
Tun shigowan shi garin nan ya fahinci canjin rayuwa a tare da ita gaba daya ta canza mashi ta koma wata babban mace da bai taba zaton kawan ta hakan ba a yanzu.
Ya zama dole ya lalubo hanyar da zai kwantar mata da hankalita har ta iya manta da wani zargin da take dashi a yanzu akan tajudeen din dayayi mai katsalandar a rayuwan shi ya tashi rushe masa komai daya shirya a baya.
Kwance yakai saman gadon rigingine yana mai lumshe idanuwan shi a hankali kamar mai wani nazari a lokscin.
Kafin ya mike zubur yana kiran layin wani abokin shi ba,ajima ba ya dauki kiran suka fara gausawa dashi.
Bayan gausuwa daya biyo baya yake tambayan abokin nasa kai mota nake so na mata lates one wanda sai ya girgiza mutum idan an bashi shi.
Dariya abokin nasa ya kwashe dashi yana fadin mutumina kayi sabon kamu ke nan kuma ?
Dama nasan wanan zaben yar kauyen da kayi zai dawo ya bata ma rai daga baya dan irin diyan tallakawan nan ba ka taba samun su a yadda kake son su.
Balle kai mutum irin ka wayayye na gani na fada idan babu wata a kasa har zaka fada tarkon irin wa yan nan diyan kauyawan masu kame maza har gwiwa.
Dan murmushi ya sake dan ya gaji da sauraren maganganun shirmen da abokin nasa Amadi yake fada mai a lokacin kan zainab din da shi kadai yasan abinda ya tsara a tsakanin su.
Cikin karfin hali yake fadin ba abinda kake tunane bane Amadi wanan dai yar kauyen da kake fadi din itace zan sayawa motar da babu wace mace dake da ita a garin nan ko akwashi kuwa baifi mace daya ko biyu ba a cikin kasan nan.
Kai mutumina da gaske kakeyi wanan magana kace yar kauye tayi tasiri a rayuwan ka haka ban sani ba nafa sanka a baya da kyakyamin mata balle wanan data zama yar , , , , ,
Dakata Amadi banson jin haka ga iyalai na don Allah ya fada muryan shi na nuna warning ga abokin nasa lokaci guda.
Amadi din cikin sauri yake fadin Iam sorry mutumina nasanka da riko da wasa nake maka nima nasan ai kai baka harka da mata dama.
Idan an samu sai ka kirani ya fada yana kokarin kashe wayan da yake ji kamar ya yarda ita lokaci guda don haushin da abokin nasa ya basa a lokacin.
Ya rasa meyasa mutane suke shiga zancen abinda bai shafesu ba kodan irin haka yanzu ya zama dole yayi wasa da idan mutane akan wanan yatjnyar su sancewa ita din mata take agare shi kamar matan kowa.
Ya dade a kwance kafin ya mike tsaye ya shiga bandaki ya watso ruwa ya dawo ya tayar da sallah ya dade zaune a gurin shi ba addua yakeyi ba kuma shi bai daga ba sai faman tunanen daya addabi zuciyar shi a lokacin.
Yana jin ana kwankwasa kofan shi yaki tashi ya bude sai kallon lokacin da yayi ta hanyar daga kai ya kalli agogon bangon dake dakin nasa makale don gwajin lokaci.
Har kusan sati daya nikan bamu hadu ba dashi a gidan duk dako nasan yana gidan haduwane kawai bana yarda muyi dashi.
Dan nima da baya na danyi nadaman tsayawa in masa rashin kunya a gaban shi duk da hakan ba halina bane aro nayi na yafa a lokacin.
Saboda bacin rai da takaicin maganan da tajudeen ya fada min a ranan na kwata na juya na rasa gano dalilinsa na fada min wanan bakar maganan haka kodan yaga maigidan bai dauke ni a matsayin mace bane a gurin shi yasa hakan ban sani ba.
Bawai yadda yayan ya daukeni yake damuna naba a,a hakan ni bai taba damuna ba a rayuwa saidai yadda shi taju din yai min magana a cikin tsanane damuwana a lokacin.
Da yammane ina zaune a keance a dakina ban dade da fitowa daga gurin maizube ba da yanzu kusan duk zaman daki muke a gidan ga baki dayan mu.
Naji an turo kofan dakin nawa bayan an kwankwasa saudaya sai turo kofan da akayi din lokaci daya da kwankwasan kofan.
Ba tare dana juyoba ina kwance a yadda nake jin kamshin turaren yasa kirjina bugawa lokaci daya nayi yun kurin juyowa da sauri don ganin wanda nake zaton ya shigo dakin nawa.
Yaja ya tsaya a bakin gadon da nake kwance din yana kare min kallo na dan lokaci guda yana karewa dakin dake gyare fes da kallo.
Ido nima na dan dago na kalleshi na lokaci guda kafin in mayar dasu kasa ina kokarin mikewa zaune.
Ki kwanta abinki ba wani abu nazo yiba dama na shigone in ganki tunda kina wasan boyo dani a gidan nan yanzu.
Yana fadin hakan fuskan shi yana a kaina dauke da bada umurni a gareni lokaci guda.
Ban kwanta ba kamar yadda ya bukata din sai gyara zama danayi ina mai sadda kaina kasa lokaci guda dan kallon da yake min din.
Da kyar na iya buda bakina ina fadin kayi hakkuri koda zan fito ka fita lokacin yasa baka gani na.
Yace ke nan ba,a koya maki gaida mutane ba kike nufi ko me daba zaki iya shiga ki gaidani ba ?
Na dago ido da sauri don in saci kallon shi don jin abinda ya fada lokacin still dai ni din yake kallo har wanan lokacin.
Ya tsura min idanuwan shi manya shi da suka canza cikin kankanin lokaci da fara maganan shi a kaina .
Karasa saukowa saman gadon nayi ina gyara bujen jikina dayan yi squeeze nadan hade hanaye a wuri daya ina fadin .
A cikk kyarma ina gudun naje dakin nakene kuma ai min wani fassara na daban shiyasa na daina shiga amma kayi hakkuri dan Allah.
Har zuwa lokacin baiyi magana ba sai na kara dukar da kaina kasa ina wasa da yatsun hannuna a hankali.
Hannu ya tura a cikkn aljihu yana fadin nasan matar malam ta gaji da zama a garin nan don haka gobe za a mayar da ita gida ita kuma halimatu tunda tana karatu sai a barta a nan tare dake .
Kai na dago da sauri ina kallin shi wanan karon nan kawar da idona ba daga kallon shi cikin murya mai dauke da son yin kuka nace.
Don Allah ka barta ta kara min wasu kwanaki kafin ta koma don idan ta tafi zan shiga damuwane sosai ga hjy har yau ban daina kewar ta ba a gidan nan.
Babu mutanene a gidan ko kinmata itama tana da aure ne kamar ki da zan aje matar mutane anan na wata da watannk ai sai a yaba min rashin hankali.
Hakan da naji ya kara sa hankalina tashi sosai ya juya kamar zai tafi yana fadin gobe ma zanso na roke shi arziki yai min ai.
Kinga yanzu ai gidan kine zaki iya zama ke kadai yadda kika girman a lokaci guda da sauri nabi kaina da kallon dan jin abinda ya fada min din.
Yes ya fada tare da sauke min wani irin kallo daga sama na har zuwa kasa yana fadin wa zai ganki a yanzu ya dauka kece zainab din mami a baya mai gudun mutane.
Baki na turo gaba ina fadin niban wani girma ba dan Allah ka barmin ita nidai mu zauna a nan tare na fada kamar zanyi kuka a lokacin.
A dan rikice yake fadin me akai maki kuma yanzu don shagwaba kawai daga magana kina shirin yiwa mutane kuka yanzu kuma.
Idona dago kamar zanyi kuka nace bakai bane kake shirin mayar da sai nayi shiru kuma dan na rasa abinda zan fada mai a lokacin.
Yace a cikin zaro idanun shi waje da akai maki me a hankali na furta zaka maida maizube gida mana.
What me kike fada dama nufin ki a nan zata tabba tare dake ko me kedai yarinyar nan da alama shagwababiyar mace ce ke .
Zama nayi a cikin fushi saman gadon na basa baya yasa kai ya fice daga dakin saina tsunci kaina da sake hawaye lokaci guda.
Shike nan yanzu maizube zata wuce ta barmu ke nan ba zan sake ganin wani dan gida ba sai yadda hali yayu ke nan dani duk da naji bada halimatu za,a tafi ba hakan bai hana hankalina tashiba a lokacin.
Karshe na mike zuwa dakin nata sai dai na kasa fada mata abinda nayi niyar fada har na shigo dakin a lokacin dan bansan yadda zance da ita kada ta tafi ta barmu ba tunda itama tana son zuwa gidan a lokacin duk da daulan da muke cikin sa kuwa.
Washe gari ba karamin mamaki nayi ba abinda ya hadawa maizube na tafiya kowa sai sam barka da ita da anty fadila da take hada mata kayan tafiyan a wuri daya don kuka ya hanani tabuka komai a lokacin.
Nasiha da bn baki nasame su gwargwado wurin boyar Allah nan sai kara jadda min kalman inyi hakkuri da rayuwa wata rana idan Allah ya yarda zan dara kan aurena.
A mota sukai tafiyan don har gida za a kaita ga tsaraba mai tarin yawa an hadata dashi ban tsaya naga tafiyan ta ba don kukan da yazo min a lokacin dole na koma gida na fada saman gado.
Duk dauriyan halimatu itama da taga zasu wuce saidai tayi hawaye a lokacin ranan haka muka wuni sukuku damu sai gidan ya koma muna shiru kamar babu kowa a cikinsa lokacin.
Ban fito ba wunin ranan ina daki rufe sai faman tunanen da nakeyi na gida wayana yai kara na dauka innan muce a layi ta kirani tana min godiyan abinda ya jafar ya aika masu dashi.
Saidana hade wasu hawayen bakin ciki tare da saita muryana nake fadin inna ai hakan yiwa kaine duk da bansan abinda ya aika masu dashi ba a lokacin.
Bayan mun gama waya da inna na sake wani irin kuka mai karfi ni kadai a daki babu wanda zai ban hakkuri dole na kyale naba kaina hakkuri.
Suna zaune da ya mamud a haraban gidan mami zaune suna shan iska yazo mami bata gida ta fita zuwa unguwa yasa shi fitowa haraban gidan ya zauna nan ya mamud ya saneshi suka zauna suna magana.
Ganin yadda yake ta bayani dan uwan yai shiru ya zurfafa a cikin tunane yasa ya mamud din dan kiran sunan shi a cikin kulawa tare da mayar da hankalin shi gare shi.
Jafar meke damun ka na ganka haka yau ko wani abu ya farune yana kallon fuskan shi cikin kulawa yake tambayan shi.
Ya sauke ajiyan zuciya firgigit yana kallon dan uwan nasa ya mamud din ya sake fadin meye matsalan kane jafar a cikin yan dakiku ya mamud din yake jera mai wanan tambayan.
Ido ya lumshe a hankali tare da sauke numfashi mai kama da ajiyan zuciya yana fadin watau mamud ina cikin matsala da damuwa dani kadai na sani.
Sai kuma wani abin mamaki shine a dawowan nan nawa da nayi sai na sake tarar da wani abin mamaki a gidana wanda shine ke kara ban mamaki a yanzu.
Shiru yayi na dan lokaci kafin ya numfasa yana kada kafa a hankali yayin da mamud din ke sauraren shi.
Ido ya bude yanaci gaba da kada kafan shi yace abin mamaki wanda ban taba tunane bashine waina dawo gida na samu wanan yarinyar gaba daya ta sake min lokaci guda.
Guntun tsaki ya mamud din yaja lokaci guda yana fadin yanzu akan wanan har kabi katada hankalin ka haka sai kace wanda yake cikin wani babban matsala.
Shi girman ya mace aiba wani abu bane duba ga irin rayuwan da a yanzu take a cikinsa ko kana nufin a yadda ka dauketa haka zata tabbata a gidan ka koda yaushe.
Kai ya girgiza yana fadin bashine nufina ba mamud sai ka jira kaji karshen zancen mana kafin ka yanke min hukunci kasan abinda ya sakani a damuwa akan hakan.
Ya mamud din yayi kasake yana sauraren dan uwan nasa tare da zuba mashi ido don a yanzu ya tabbatar da duk abinda kanin nasa ke shirin fada mai matsalace babba don ba akan girman nawa dayaga na masa bane lokaci guda.
Huci yayi ga bakinsa sai wani gumi dake tsarso masa a goshin sa tankar wanda ya watsa wa kansa ruwan zafi a lokacin.
Shikan mamud yana ganin yanayin dan uwan nasa yayi saurin fadin wai jafar meke damuwan kane haka ?
Nifa gaba daya duk ka sauya min kamar ba kaiba wanan wani irin damuwane akan zainab din wanda ya susutaka haka har ka tayar da hankalin ka haka wai ?
Mumushin karfin hali yayiwa dan uwan nasa yana fadin mamud kafi kowa sanin bawai na auri yarinyar nan bane don na zauna da ita irin na ma,aurata a yanzu.
Jafar wai wani irin magana kake kokarin fada min a yanzune wai don me ake aure a rayuwa badan mutum ya aje iyali ya haiyayya fa shima ya bar baya kamar yadda iyayyen mu suka barmu.
Yanzu fa jafar kana kokarin rufe bayan talatin da biyar ne a rayuwa don in ban manta ba wacan zuwan naka mami ke fadin kana talatin da biyu a duniya.
Me zaka jira da matar ka Allah ya baka mace ta gari da zaka inya controling dinta yadda kake so agidan ka tun a yanzu kan kanta ya karasa wayewa.
Nida aca tun farko irin matar da mami ta zaba min ke nan ba wanan ba da nake fama da ita a gidana yanzu don ban isa in tsayar da Nuriya wuri daya ta tsaya ba.
Shine abinda nake lurar da mami akan auren ka da yarinyar nan zainab a kullun do ko ita mami Nuriyan bata ragawa ba kasani.
Jafar din ya dukar dakai kamar yana sauraren dan uwan nasa abinda yake fada nan ko wani duniyan tunane ya fada a lokacin.
Can ya dago kai yana kallon dan uwan nasa kafin yace a cikin kyarmar murya kaman mai shirin kuka a lokacin, mamud mafita nake so a yanzu kan wanan auren nawa.
Shiru mamud din yayi don ya rasa inda dan uwan nasa ya dosa da maganan shi yaji jafar din na fadin bana son in rasa wanan yarinyar a yanzu mamud don ina matukar jinta a cikin raina rasa zainab a rayuwana tankar rushewan wani bangaren rayuwanane a yanzu.
Cikin mamaki ya mamud ya dago kanshi yana kallon dan uwan nasa da mamaki don har yanzu ya bai fahinci abinda dan uwan nasa yake nufi ba.
Can ya dago kai yana ftambayan kanin nasa No jafar ka daina fadan haka don Allah ko akwai wani abinda yarinyar nan tayi makane kake son ka boye min dai ?
Kai ya girgiza yana gyara zaman shi tare da lasa saman labben na sama yana mai shafo kanshi a hankali cikin damuwa.
To jafar wanan wani irin wullakanci kake son yiwa yarinyar nan haka koka mai damu mutanen banza a daukemu wawaye wadanda basu san abinda sukeyi ba .
Nace ka fada min meye damuwan ka da ita kana kawo min wasu dalilai marasa tushe a yanzu.
Mamud ba zaka gane bane amma gaskiya nasan bazan iya kula da hakkin yarinyar nan a yanzu ba ko nan gabama.
Innalillahi ya mamud ya fada tare da wani irin zabura daga inda yake zaune din kafin yakai ga cire hulan dake kanshi yana dan fifita dashi a hankali don ya samu iska a jikinshi.
Kafin ya iya buda baki ya furta a sanyayye jafar baka da lafiyane ko wani abinne ya sameka kake boye muna.
Kai jafar ya kada mai alaman a,a ba hakan yake nufi ga maganan shi ba da akwai dai wani zance can kasan zuciyar shi.
Jafar ka tuna koni wani abin ya shigewa duhu daya shafi rayuwana kai nake nema in fadawa ka ban shawara akan hakan don me kai a yanzu ba zaka fada min naka damuwan ba a gabana.
Mamud nasan da hakan shawara kawai nake son ka ban har lokacin da komai zai daidai min a rayuwa na fuskanci matata.
Wani irin ajiyan zuciya ya mamud din ya sauke lokaci guda tare da fadin anya jafar kana da lafiya kuwa ?
Yanzu dai na gama fahintar wanan yarinyar batai maka komai ba don haka koma menene yake damun ka a rayuwa ka lalaba matar ka ta hanyan kyautata mata a rayuwa ta yadda zaku zauna lafiya da ita.
Saidai ka tuna kada ka yarda ka cutar da yarinyan nan da yawa katuna ba a duniyan nan zamu tabbata ba har idan ka cutawa rayuwan wanan boyan Allah Allah zai saka mata ta ida baka zata ba.
Kai jafar din ya sunkuyar a kasa don baida abinda zai fadawa dan uwan nasa a yanzu saidai ina son wanan maganan ya tsaya iyani dakai kafin komai ya daidaita ya mamud din ya fadawa dan uwan nasa.
Da sauri jafar din ya dago kai yana fadin nima hakan nakeso bazan so mami taji wanan zancen ba don zata dauke shi da wani fassara na daban.
Kada kaji komai jafar ka tuna duk abinda ya same ka mekyau ko mara kyau kamar ya shafeni ne koni.
Saidai zan so ka maganan ta makakewa ya mamud din don motan mami daya shigo gidan zuwa parking spece yasa suka mayar da hankalin su gareta tare da mikewa suka nugi wurin motar nata lokaci guda.
Kujeran da nake zaune sama anty fadila ta kala kafin tace dani waini na tambaye ki mana zainab wai tunda maigidan nan ya dawo ya nemi ki a shimfidan shi kuwa ?
Kai na dago da sauri ina kallon ta don ban fahinci inda zancen nata ya dosa ba yasa nace a cikkn mamaki shifida kuma anty ?
Kamar ya shimgidan shi don ban fahinci mekike nufi ba wallahi kayya ta fada cikin daure fuska a gareni.
Tana fadin waike zainab wace irin yarinya ce haka mara wayau da hankali ke an fada maki haka zaman aure yake wai ?
Iyakar mace taci tasha ta saka mai kyau ajikinta ta kwanta shine zaman aure tsakanin mata da miji kawai a rayuwan su.
Idan shi bai neme ki ba bana fada maki hanyar da zaki bi ki ja mijin ki a jikin ki ba zainab kada fa tunanen da nakeyi ya zamo gaskiya a gareku gidan nan.
Me kike tunane anty na tambaya cikin marairaice murya don a zatona wani abin kuma ta hango a tare dani sai naji tace dani barshi kawai hasashen hakan kawai nakeyi akan ku bai zama lalai haka din bane.
Amma dai gaskiya zuciyana ya fara zargin wani abu a gidan nan yanzu, saidai abinda nake so dake shine koda shi bai nemeki ba zainab kiyi hakkuri ki daure ki kai kanki a gare shi mugani .
Da sauri nace ban fahince ki bafa anty ina mai kallon fuskanta don karin bayani a gareni ki dai gwada abinda na fada maki din ta fada tana mikewa daga wurin da take zaune din zuwa kitchen din gidan.
Nan ta barni zaune ina tunanen maganan ta ta yaya zan kai kaina da kaina wurin ya jafar din yadda take nufi din.
Sam hakan ba zai taba yuyuwa ba kenan nidin fitsarariya kenan take nufi ko ms sam hakan ba zai yuyu dani ba wallahi sai dai duk abinda zai faru ya faru na fada a raina ina masifa da ita cikin zuciyana.
Ni a wurins tun daga ranan da nashigo gidan shi har rana mai kama data yau nan taba tunanen wanan abinda take nufi ba a yanzu a tsakanina da yaya jafar din don haka sai maganan nata baiyi tasiri ba a zuciyana ko kadan.
Itama daga wanan ranan bata kara yimin irin wanan maganan ba ta kawo ido kawai ta saka min naci gaba da yan harkokina na yau da kullun duk da bawani abu bane illa zaman falo saiko dan fita haraban gidan da yamma wani lokaci musha iska a waje shine kawai abinda nakeyi a gidan.
Don shi kanshi ya jafar din bayama zama a gida ko garin kwana biyu zakaji baya kasan ya dan fita zuwa wano kasa na kwana biyu kafin ya dawo.
ZAINAB IDRIS mAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAWAZAINAB IDRIS MAKAAW
ZAINAB IDRIS MAKAWAA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
5️⃣4️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAR UWA DA FATAN MUN WUNI LAFIYA UBANGIJI YA SADAMU DA ALHERUN SA AMIN,
KADA KI MATA DA LITTAFIN KUDINE KIBAN HAKKINA KO KI BIYA RANAN DA NADAMA BAIDA AMFANI GA BAWA.
DON KIRA ZAKI KIRA WANAN LAYIN KAMAR HAKA 08036959257 KO TURA KUDI BAKIN ZAKI TURA GA WANAN ACCOUNT DIN KAMAR HAKA 2254380105 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA AMIN, , ,
Shi hakki gaskiyane yar uwa zaki ban a ranan da nadaman hakan baida amfani a garemu baki daya don haka karatun wanan novel bai zama dole a gareki ba yar uwa ki barshi shine sauki a gareki da zaki gane gaskiyan hakan a gareki da fatan masu imani zasu fahince ni.
Ya mamud yana zaune sai faman tunanen zancen shi da dan uwanshi yake a zuciyan shi tun ranan da sukai wanan maganan ya kasa sukuni a zuciyar shi.
Don ya rasa dalilin dan uwan nasa na fadan wanan maganan haka dole akwai wani dalili nasa da yake boye mai a zuciyar shi.
Don haka ya zama dole yasa ido kan kanin nasa har ya fahinci halinda da dan uwan nasa yake boye mai.
Ta yaya zai iya fahintar hakan bayan ba agari daya ko kasa daya suke rayuwa dashi ba a yanzu koma dai meye zai gane a sannun wanan alkawari yai wa zuciyat shi.
Don haka ya yanke shawaran da zuciyar shi zai fara tunkarana ko zai iya fahintar wani hali daga gurin dan uwan nasa saidai kaico ta yaya zai iya fahintar hakan dadin mace mai mutunci ke nan da ace matarshi mai kaunar yan uwanshine da ita zaiyi amfani har ya gano abinda yake so a wurina din.
Ko yanzun ma bai baci mai ba don zaiyi amfani da daman shi na namiji ya tursasata zuwa gidan don kawai su sada zumunci a garemu ta hakan har dan shakuwa zai shiga tsakanin mu ai.
Da dare suna zaune cikin ikon Allah itace ta dauko zancen jafar din da kanta take cewa dashi yanzu dai kanin ka shi ya fita zancen kowa a garin nan tunda yazo sau daya nasa shi a idona yana ganin bai neman komai a wurin kowa yanzu.
Shi jafar din ya dago yana tambayan ta da mamaki tare da fadin ina mamakin wanan halin naki Nuriya ?
Jafar naga ko yau muna tare dashi a gidan nan shekaran jiyama mun dade dashi muna hira a waje saida mami ta dawo muka bar wurin.
Kece dai bai samun fuskan da zai sake dake a wurin ki don hakane shima yanzu bai damu da ya shigo inda kike ba don yana jin rashin mutuncin da kikewa mahaifiyar shi ko yaushe.
Ni din ai duk wani laifi a kaina yake karewa dama a gidan nan fon hakane na kama kaina da kowa don na fahinci ba kauna akeyi ba.
Babu wanda bai kaunan ki gidan nan saidai halinkine basa kauna a yanzu don ba kowa zai zauna anaciwa uwarshi mutunci ba yana kallo a zauna lafiya da maishi.
Ko haka kokaga sunayi wa naki iyayyen su don kawai ina auren ki shine laifi a garsu baki daya ya kamata ki natsu ki gane hakan zai iya jawa yayan kima bakin jini a gurin su.
Bai damu da bacin ranta ba yaci gaba da fadin kin rasa gane cewa shi arziki na Allah ne ba fina jafar yayi ba daya bashi arziki ya barni duk da ina gaban shi .
Yanzu haka da taimakon jafar din nake samun ci gaba a rayuwana ko yaushe ba tare da mami tasan da hakan ba din shi ke tallsfa min ba tare dana roke shi ba.
Kai kaga zaka iya hakan don ni ban gaji komawa baya ba a gidan mu don haka kaje kaita jiran ya taimaka maka din.
Fita batun ta yayi yaci gaba da abinda yakeyi a falon ba tare daya kulata ba harta kare fadan ta ta shige daki ta barshi falo zaune.
Kai ya girgiza a cikin takaici yana fadin kina da matsala wallahi ni dai baki isa ki rabani da yan uwana ba wallahi ya fada cikin jan tsuki.
Kwana biyu dayin wanan maganan ta fito don zuwa unguwa ne motar ta haka kawai ya tsaya tayi tayarwa yaki tashi ranta ya gama baci sosai tana ciki tana kokarin ganin motar ta baci taga fitowan shi daga cikin gidan nasu yana waya.
Kaita kawar gefe kamar bata ganshi ba sai kokarin tayar da motanta takeyi kawai motar taki tashi kuma.
Har ya dan wuce ta ya nufi inda motocin shi suke ya dawo inda take ya tsaya tare da kashe wayan da yakeyi yana fadin madam lafiya kuwa ?
Wani nauyi da kunya ne ya kamata lokaci guda bai tsaya jiran me zata fada ba yace motar taki ta tashine ya tambaya yana kallon ta.
Wallahi lafiya na ajeta yanzu kuma na tayar taki tashi ta bashi amsa yace fito mu gani da hannu ya kira yaran shi mutum biyu sukazo wurin banda taju dake can ya kura masu ido yana bin Nuriya da kallon tsana.
Donshi ya ki jinin yaga wata mace ta rabi jafsr din a rayuwan shi koda kuwa yan uwan shine idan ba Aisha daya san kanwar shice ita har yakan dan sakar mata fuska wani lokaci.
Da sauri sukazo wurin ya nuna masu motar su duba matsalan ta a daidai lokacin Nuriya din ta koma gefe shi ta tsaya itama.
Ganin suna bata mai lokaci yaja tsuki yana fadin idan ta fara baki matsala a kawo maki wata ki daina hawan wanan din don kada ta tsaya maki wani wuri da babu kowa a kusa.
Sai taga ya shiga kiran layi ba tare da ya tsaya ba yake fadin a kawowa matar brother din shi mota yanzu mai lafiya na mata zata fita unguwane yanzu.
Bin bayan shi tayi da kallo tare da mamakin abinda taji yana fada a bakin shi tace a ranta lalai mijinta yayi gaskiya daya fada mata halin dan uwan nasa gashi tun ba,aje ko ina ba Allah ya nuna mata hakan .
Wanan dalilin yasa suka yanke shawara da mijin ta su sameshi har gidan shi suyi mai godiya wanda hakan ya zama dalilin zuwanta gidan namu a wani rana.
Na gaji da zaman daki da takura kaina yasa na fito falo na samu halimatu zaune tana kallo na zauna ina fadin halimatu wanan kallon yai maki yawa baki damu da duba littatafan ki ba na karatu.
Wanan film din nake son kallo yayan mu yanzu ai na fito dan na kalleshi inga yadda za a ci gaba ta fada hankalinta yana kan tv dake aiki.
Wuri na samu na zauna kafin in kalleta ince da ita amma dai kin san sanyin AC din nan yayi yawa halimatu anya halimatu kin dauki rayuwa da sauki kuwa ?
Ina jiye maki ranan da zamu koma gida a gaban iyayyen mu ranan da zaman gidan nan ya kare muna dagani har ke don baki dauki duniya da sauki ba ke nake gani.
Da sauri ta dago kai ta kara kallona tana fadin gida kuma anty me zamuje yi gida har mu zauna kuma ?
Halimatu kanki daya kuwa na tambayeta a cikin bacin rai sosai don dai nasan yanzu halima ta dan san duniya tana da shekara goma ko sha daya ai wurin haihuwa.
Tundani inada shekara sha shidda da dan kai da haihuwa yanzu na sha bakwai nake nema in rufe a duniya saidai tashin mu da wayau mu ba iri daya bane da nasu yanzu.
Sallama akayi bakin kofan duk da garin ya hade da hadari ruwa na iya saukowa ko wani lokaci .
Bakon abune garemu muji sallaman bako a gida don haka gaba dayan mu hankalin mu ya koma ga kofan don ganin mai shigowa din.
Ya mamud ne tare da Nuriya da yaran su biyu ke tafe ban san lokacin dana mike tsaye ina sake fara,a a fuskana ba kafin in tuna da waye Nuriya a gurina na mayar da fara,a na dan daure fuska ba yabo ba fallasa garesu.
Sannuki da zuwa na samu kaina da fadi tare da dan matsawa a inda nake tsaye a cikin farin cikin ganin su a wanan lokacin.
Zainab kuna lafiya ya jafar ya fada a daidai lokacin daya karaso cikin falon gaba daya ya fada ya samu wuri ya kai zaune da gudu yaran suka shige min jiki don murnan ganina da sukayi kafin yarinyar tace anty kin barmu yanzu bamu da mai koya muna assignment a gida kullun sai aunty ta dokemu a school.
Kan yarinyar na shafo naji dan namijin na fadin ke ba mommy tace mu barce mata anty ba mu kirata da zainab .
Ba uwarba har uban yaji kunyar maganan sai naji yace kuce mata anty matar unclen j daga yau kunji ko ?
Kasa nakai gurfane a gefen kujeran daya zauna din ina fadin yaya ina wuni ya gida ya aiki dasu mami da anty Aisha ?
Ya amsa dan maganan shi a cikkn sauri sauri da lafiya kalau zainab ya kuke na komai dai lafiya ko ?
Na amsa kai kasa da lafiya kalau yaya na juya gurin matar nasa ina gaida ita ba tare dana mike ba sai bina takeyi da kallo ta amsa min da kyat tana wani shan kamshi a fuskan ta.
Ko jafar na gida ta fada a cikin wani yanayi na nuna gajiya a tare da ita tana bin ko ina na gidan da kallo da sai kamshin ke tashi wanan aikin anty fadilane hakan.
Kafin in bata amsa Anty fadilane a bayan mu take fadin au baki mukayi gidan ashe sannun ku da zuwa a cikin fara,an ta ta karaso inda muke a falon a daidai lokacin na mike daga gurfanen da nake din tana gaisawa dasu.
Don ita koda yaushe fuskanta a cikin fara,a yake irin mutanen nan ne da baka saurin gane fushinsu tare dasu.
Nuriya ta amsa tare da kara maimaita min tambayan ta da jafar nace yana gida wurin shi muka zo ta fada tana kawar da kai gefe daya daga kallon mu.
Bari matarsa ta duba maku shi don dazun nan naga shigan shi gida anty fadila ta fada tare da kallon inda nake tayi min nuni da ido.
Cikin sanyin gwiwa naja kafana da har lokacin ina rike da hannun yarinyar jikan mami da suke kira da husna zuwa part dinshi din.
Kwakwasa biyu nayi a kofan kafin naji an bude kamar dai kofan da remote yake amfanine don sai kaji an bude ka dade tsaye ba wanda zai bude ya fito kamar dai wance karon da nazo.
Don haka sai na murda na shiga da sallamana a bakina can na hangoshi yana kwance saman gadon shi da laptop dinshi a gaba ya daga kafa daya yana aiki.
Ga cup a gefen shi da wani ruwa mai ruwa zuma a cikin kofin da alama dai yana aiki yake shan juice din.
Kai ya dago yana kallon mu har na karaso bakin gadon ina fadin sannu da aiki yaya su ya jafar ne dama suka zo suna falo.
Yarinyar dake rike a hannuna ya tsurawa ido kafin yace Husna tare da daddyn ku kukazo ne yana mikawa ya yarinyar hannu tazo wurin shi.
Bin dakin nayi da kallo ko ina na dakin a gyare yake fes sai walkiya yakeyi don gyara ga komai na dakin farine tundaga kan gado wardrobe da mirrow zuwa labullayan dakin duk farare kalane.
Juyawa nayi dan fita daga dakin yake fadin ki tsaya ki hada min wanan takardun jin haka yasa na tsaya har saida ya sauka daga saman gadon na nufi gadon don tattara mai takardun nasa.
Ba wasu takardu bane masu yawa zube saman gadon don haka sai bai daukeni lokaci mai tsawo ba wurin hadawa na aje mai kusa da jakkan dana gani nasa saman gadon .
Gyara gadon karayi dan dan takuran dayayi don hawan saman gadon dayi a lokacin nafito tare da ja masa kofan dakin.
A zaune na samesu a falon yana hira dasu a cikin sakin fuska ga abin sha da motsa baki an cika masu gaba dashi wanda nasa hakan aikin anty fadilace .
Har lokacin Husna tana makale dashi ajikin shi yana dan mika mata biscuit tana ci a hankali haka yasa na gane yana da son yara ashe shima.
A daidai lokacin dana karaso ya mamud ke fadin kawai nazo na samu madam tana murna da motar daka bata .
Na dade ina gurin canza mata mota tun lokacin da motar ta fara bata matsala saidai hakan bai samu ba sai gashi ka rigani bayarwa ashe zaiyi godiya yace
Kai haba dai madam ai tafi nan garemu wanan yaran haka data haifa muna kyawawa haka dasu ai taci a biyata da abinda yafi wanan ma yanzu.
Ai, ashe dama dan yaran ka ka bani wanan kyautan to nagode Allah yanu muna naku yaran watarana kuma ta fada tare da dago ido tayi min wani kallo da bansan ma,anan shi ba.
Wanan kamar gobe ai ya mamud ya fada yana mika hannun shi cikin snacks din dake gaban su ajiye dakina na juya na nufa dan in duba abinda zan iya ba yaran a lokacin.
A cikin dakin na samu halimatu a kwance tana karasa kallon da takeyi a falon suka shigo gidan a lokacin ban tsaya ta kanta ba na bude wardrobe dina na fara bi da idanu don na rasa me zan basu a lokacin.
Idona ne ya sauka wurin sunkin sabulan kasan waje dake a wani gefe sai turaren da bab san ranan shafasu ba a jikina don ko yaushe cikin kawo min turare aka a gidan tun kan wani ya kare.
Suna debo na saka a leda nafito kitchen na nufa wurun kayan kwalaman da ake ajewa na zuba a ledan saida ledan ya cika na fito daidai lokacin da har anty Nuriya ta mike tsaye a lokaci suna shirin tafiya.
Da sauri na karaso ina fadin cikin yar murya karama har zaku tafi ke nan anty dan har yanzu ina da dan tsorin su da shakkun su a raina don haka bana iya sake jiki dasu.
Eh dama ba zama zamuyi ba don akwai hadari a garin saida muka fito mukaga hakan ta fada tana fara takawa don fara fita daga falon.
Da sauri na mikawa yaron namiji ledan dake hannu ina fadi karbi wanan ka rika maku nagode yaron ya fada don tun lokacin dana koya masu yin godiya a makaranta idan wani ya basu kyautan wani abu na koya masu yin godiya ga mutum.
Ya mamud ne ya tsaya yana fadin zainab mun gode mu zamu tafi sai a kara hakkuri a zauna lafiya da kowa da sanu zaki saba da bahagon halin wanan mijin naki ya dan karasa maganan sa a cikin barkwanci.
Nagode yaya na fada a cikin ladabi gareshi yaci gaba da fadin ina fada maki kullun zainab ki daukeni kamar dan uwan ki na jini har in jafar yayi maki wani abu zainab don Allah ki kirani ki fada min.
Har wurin motan su muka rakasu saida kyar Husna ta yarda ta shiga mota wai zata zauna a wurin uncle ita ina jin ya mamud yana lalashinta da tabari zai kawo ta sufita yawo tare da uncle da anty sai ta washe baki tana dariya dan yarda da hakan daya fadamata din.
Bayan tafiyan sune na sauke zuciya tare da juyawa don nakoma ciki tsaye yake ya dora hannayen shi duka biyu saman weist din shi.
Tare da kura min idanuwan shi a kaina sai hakan yasani na tsargu dashi dan irin idanuwan daya watso min din lokaci guda .
Na fara tafiya naji yana fadin da alama kina son ganin baki a gidan nan ko don naga kamar zuwan su ya sakaki nishadi yanzu haka ?
Tambayan nasa ya ban mamaki saidai babu hali bada amsa a gareshi don gargadin kowa a gareni shine nayi mai ladabi da biyayya a kullun.
Don hakane na kakaro murmushin dole a fuskana da ban tashi yiba na soma tafiya don na kagu na bar gurin a lokacin.
Saidai kuma zuwan su baida ma,ana gareki saboda kin nuna masu irin zaman da kikeyi dani a gidan nan .
Da kina da wayau da kin nuna masu nidin mijin kine ai ta hanyar zama a kusa dani ko kiyi dan wani abinda zai nuna mudin mata da mijine ai.
Da sauri na dago kai ina masa kallon ido da ido na dan lokaci kafin na mayar da kaina kasa na dukar da sauri dan ba zan juri mai irin wanan kallon ba.
Da fatan kin fahinci abinda nake nufi da hakan koda kuwa mamine ta shigo gidan nan ya zama dole ki nuna nidin mijine a gareki yanzu ina fatan kin fahinci mai nake nufi da hakan ?
Kai kawai na gyada mai ba don na gama fahintar mai yake nufi da hakan ba a lokacin sai washe garine nake fadawa fadila yadda mukayi dashi .
Nisawa tayi tare da kallona a cikin mamaki take fadin akwai magana ke nan zainab mijinki bai shirya amsan ki a matsayin mata a yanzu .
Na rasa me hakan da yakeyi yake nufi don yana da wata manufa ta daban ke nan akan ki koda ya aure ki.
Kallonta nayi cike da fargaba a tare dani tace kwarai burin ko wasu ma,aurata shine su raya kansu da madara ko zumar kauna .
Amma shi mijinki nasa daban ne akan auren ku zainab dole akwai inda ya dosa dake a rayuwan shi don babu zancen kankanta a tare dake yanzu.
Kedin kinkai matsayin da duk wata mace cikakkakiya ake tunanen takai kamar yadda yace hakan ba laifi mu kuma sai muyi amfani da wanan daman wurin jefa mashi kaunarki a zuciya mu gani bashi din ya fadi hakan ba bude kunnuwan ki ki saurareni da kyau yanzu.
Mutukar baki ko mamin naku sukazo gidan nan ke kuma sai kiyi amfani da naki daman na ya mace ki dinga shammatar shi dole shi har idan lafiyayin namiji yake dole ya fada tarkon da zamu haka masa din.
Amma fa zainab hakan ba zai samu ba sai idan kin kara jajircewa sosai kin kawar da wanan kunyan naki da kike dashi irin na matan hausawa.
Zaki iya hakan koba zaki iya ba don in sani kada in bata lokacina don naga kema kina da kafiya akan wani hali naki na daban.
A hankali na gyada mata kai tare da furtawa a hankali cikin kyarmar murya da zan iya anty insha Allahu.
Nan dai tayi ta koyar dani hanyoyi dabab daban da zan tunkari matsalan dake gabana din ina mata godiya wanda ni kaina nasan gaskiya ta fada min ga wanan bahagon auren da Allah ya kaddareni da yinsa a yanzu da kurciyana.
Ban yarda da shawaran fadila ba kadai don jajircewa nayi sosai ina raba dare wurin mika kukana ga ubangjji mahaliccina sai gashi ina ganin sauki ga al,amarin nawa cikin dan kankanin lokaci.
Eh dole ince hakan do kuwa yanzu ankai shi da kansa zai shigo har dakina mu gaisa da safe haka kuma idan zamu kwanta barci duk na fahinci hakan a yanzu.
Duk da dai ba wani sakin fuska amma zai shigo mu gaisa ya tambayeni idan banda wani matsala a tare dani ko kuma idan ya dawo wani lokaci ko dakinsa baya shiga zai shigo har dakina yayi min ya gida tare da tambayan badai matsala ko ?
Idan muna dashi zan fada mai ko idan muna son wani abu zan dan sake infada mai komai sai yin hakan da yakeyi ya dan jawo muna kusanci a tsakanin mu.
Inda nakan shiga part dinshi da safe in gaidashi kafin shi ya shigo nawa part din da sunan gaisawa dani.
Bangaren taju kuma yanzu ba kasafai nake ma ganin sa cikin gidan ba sai can ba a rasa ba zamu dan hadu dashi sama sama muke gaisawa dashi din ba tare da wani sakin fuska ba ga kowan mu.
Kwaliya kuma irin na daukan hankalin maza kamar yadda fadila tace na jajirce gutin yinsu iya gwargodon hali ina bakin kokarina saidai kallo daya zai min ya kawar da kanshi gareni.
Sai wanan abin kuma ya fara damuna a zuciyana mutum kamar dutse shi baya ko sanin na ina mai wani kwaliya a hakan.
Kamar yadda yace indinga nunawa udan baki sun shigo hakan na daure tun ina jin kunya har na fara daina kunyanshi ina nuna muna normal dashi ai a zaman mu .
Don a gaban baki mu har wasa da dab dariya zamuyi kamar ma,aurantan gaskiya ne ni da shi ai sai idan sun tafine mukoma kamar yadda muke baran baran.ws🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
5️⃣5️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
FATAN ALHERI GAREKU HAR KULLUM MASOYANA TARE DA FATAN GAMAWA DA DUNIYA LAFIYA ALLAHUMA AMIN.
YAR UWA BAZAN GAJIBA WURIN TUNATAR DAKE SAUKE NAUYIN HAKKIN WANI A KANKI DON ALLAH IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WANI AKANKI NAGODE IDAN KIN FAHINCI MAI NAKE NUFI.
Rayuwa mai dadi haka rayuwan namu ke gudana a gidan har zuwa lokacin daya fara zancen komawa inda ya fito.
Ban dauki zancen wani abuba ni dai nasan ya share sati uku a kasan nan ban kuma san mr ya kawo shi kasan nan ba balle.
Iya ka dai nasan da cewa dan zunwan shi kasan yasa na dan saki jiki dashi don zaimun magana in bashi amsa ba tare da jin tsoron shi ba a yanzu, ko kunyar shi ba.
Inda shima kamar hakan yana mashi dadi yadda na dan fara sake jiki dashi din ba tare da nuna tsoro a garshi ba.
Don haka kawai tun ranan da ya mamud ya kawo su husna muka fita tare yawo dasu da halimatuna .
Sai hakan ya zama mai kamar jiki ina zaune kawai zai bugo in shirya mu shiga gari .
Inda a dan fitan da mukeyi din zai saya muna abubuwa mu dawo gida dashi sai dai duk fitan da mukeyi din bamu taba zuwa gidan mami har zancen komawan shin nan ya taso.
Zaki iya cewa banda zuciya don har yau ban manta da mami ba a cikin raina .
Ba hakana bane mai karatu mami ina jinta a wani bangare na zuciyana sosai ta yadda ba zan iya mantawa da alherin ta gareni ba har wanan lokaci.
Da yammaci ana gobe zai tafi ya shigo gidan ya sanemu zaune a falo a falon shima ya zube sabanin yadda yake idan ya samemu a zaune yawuce mu saidai mu gaida shi, ko juyowa bayayi garemu yake amsa muna gaisuwan mu.
Muna gaida shi ganin ya kai zaune ya zuben saman kujera tare da kai wuyan shi ga masangalin kujera ya nisa da dan karfi lokaci guda yasa duk muka sha jinin mu a falon don dama mu uku ne zaune a falon.
Zainab naji ta ambata a cikn wani murya dake nuna kasala a tare dashi har lokacin kanshi yana dage a yadda yake saman kujeran.
Yayin da idanuwan shi suke rufe har lokacin alaman lumshewa a dan sanyaye na amsa mai da na,am yaya hannu ya miko inda nake zaune din yana fadin zo ki min massage din kai.
Dan jim nayi kafin in juyo in kalli inda anty fadila take zaune daidai lokacin da take yunkurin tashi don barin falon lokaci guda.
Jin ban taso daga inda nake ba don ni ban ma fahinci mai yake nufi ba a lokacin yasa shi bude idanuwan shi ya sauke a kaina.
Babu kowa a falon dagani sai shi a lokacin don da hannu fadila tayiwa halimatu nuni da su bar falon har suka fice bai sani ba din idon shi dake rufe kanshi kuma dage a sama.
Bakiji me na fada bane ya dan fada cikin daure fuskan shi zubur nayi na mike ina fadin banji ba yaya .
Kizo ki tausa min kafa na da kai ki fara tausa min kafana tukuna ya fada yana mai da kanshi a yadda yake zaune da farko.
Mikewa nayi na fara takawa a hankali zuwa inda yake din a hankali kamar wace kwai ya fashewa a ciki lokacin.
Har na zagayo zuwa bayan kujeran saida na runtse idanuwana kafin in daga hannuna in dora a kan nasa a hankali na fara dan cakula mai kai din.
Wani irin shock naji a daidai lokacin dana dora hannuna saman kan nasa don taushin kan da kuma santsin sumarsa kamar na dan bature ba african ba.
A hankali na ci gaba da dan matsa masa kan ina jin yadda yake sauke numfishin shi shima kamar yana jin dadin abinda nake masa din.
Saitin goshinshi ya nuna min adaidai lokacin yana gyara zaman shi yana fadin ki tausa min nan gurin yana min ciwo sosai wallahi.
A raina nace yanzu da ciwo ya sameka ne kasan amfanina a gareka ko ko a fili kuma cewa nayi dashi sannu a hankali yace nagode.
Can naji ya sake wani irin ajiyan zuciya tare da fadin ki kara tausa min shi da karfi zaifi don ciwo yake min sosai.
Hakan yasa na takankare iya karfina ina dan dana masa saitin goshin nasa da dan karfi kafin inji ya rike min hannayen nawa lokaci guda yana fadin.
Ai sai ki fasa min goshi da wanan irin dannan da kike min a daidai lokacin kuma mukaji an shigo falon babu ko sallama.
Wanda haka yasa dagani harshi muka dago don ganin ko waye ya shigo a lokacin haka babu ko sallama tunma dai ni da naji kunyar yadda maishi ya same mu din.
Don sai a dauka ko wani wasan mata da mijine mukeyi a lokacin do yadda yake rike da hannayena a hannun shi.
Ba kowa bane sai taju tare da wani dayan security din shi suka shigo a lokacin idanuwan su kar akan mu tundai taju din da kamar idon shi zasu fado kasa don mamakin yadda ya samemu din a lokacin.
Ganin su baisa ya sake hannuna dake rike da nasa ba a lokacin saima kokarin zagayo dani ta gaban shi da yake kokarin yi din.
Ki matsa min kafana ya fada kafin ya sauke kallon shi garesu a inda suke tsaye di kamar an dasa su wuri daya.
Can na tsinkayi muryan shi yana fadin me kuke anan kun tsaya mi saman kai haka ?
Kamar wa yanda aka tsikara lokaci daya suka fara takowa zuwa inda yake zaune din ni kuma na kama kafan shi na fara murzawa a hankali lokacin .
Naji dayan yana magana duk da acikin harshen turanci suke maganan nasu na gane mai suke fada don zancen ticket din jirgi naji sunayi wai babu jirgin da zai tashi direct a gobe sai sun shiga na wani kasan an sauke su a can.
Tsuki naji yayi tare da fadin shi ba zai sauka ko wani kasa ba saidai su bari ranan da jirgin zai tashi suyi booking zaifi.
Yana fadan haka ya mayar da idanuwan shi a yadda suke mai da farko ya kara lumshe su a hankali.
Duk da ban dago kai ba nasan da mai kallona a cikin su don jikina da ya bani hakan lokaci guda yasa na dan dago kaina da yake a duke na dan kalli inda suke tsaye din.
Wani kallon tsana da ki taju din ke aika min dashi lokaci guda wanda yasa nayi saurin kawar da kaina daga inda suke din tsaye.
Daga haka suka juya dan barin falon saidana dan dauki lokaci ina matsa masa kafafun nasa kafin yace dani ki huta hakana nagode.
Daga haka kuma ya yun kura da niyar mikewa a daidai lokacin da nima na mike din muka dan gwaura kan mu da juna da sauri ya ja jiki shi yana fadin kiyi a hankali fa.
Nikan falon na bari gaba daya don a rikice nake sosai a lokacin tun wanan shigan da nayi ban kara lekowa falon ba sai washe gari.
Don dan tunanen dana fada yasa dana samu barci ban falka da wuri ba sai da gari ya waye tarrr, .
Wuraren takwas saura na safe aka buga min daki a hankali kamar maishi baison aji shi da mamaki na mike zuwa kofan na bude.
Anty fadilace a tsaye ina budewa ta shigo da sauri tare da mayar da kofan ta rufe taja hannuna zuwa bakin gado tana fadin.
Zainab kinji abinda naji jiya a gidan nan kuwa idan ba kunnuwa ke min karya ba wallahi tunane na ya zama gaskiya ke nan kan mijin ki.
Anty meya faru na fada a dan rikice tace wai kina nufin ke bakiji hayaniyar da akayi a gidan nan ba jiya duk saboda ke .
Ni kuma anty na fada ina nuna kaina a cikin mamaki da abinda ta fada din kaina.
Wai ke duk wanan hayaniyar kina nufin bakiji ba zainab wallahi fada sosai naji sunayi idan ma banyi karya ba zainab har djka naji wallahi a tsakanin su
Innalillahi na fada sai data kalli inda kofa yake tace cikin kashe murya wanan mai kama da mata din taju shine ke nuna kishi ki a kanki .
Ni meye ruwana dashi dan Allah na dai gane wanan mutumin baya kauna na sam a gidan nan don irin kallon tsanan da yake jifana dashi ko wani lokaci.
Ba zai kaunace ki ba don yasan kedin zaki iya canza mijin ki ga rayuwan da sukeyi a ko wani lokaci idan kuna kebewa daga shi sai ke a gidan nan.
Ke ni da farko har naji tsoro na dauka barayi ne suka zo muna saida na saurara na gane a cikin gidan nan muryan ke tashin kuma fada sosai naji a tsakanin su.
To Allah ya sauwaka na fada ba tare dana fahinci komai a cikin zancen nata ba takeci gaba da fadin wanan abin ya ban mamaki matuka wallahi.
Wata kila wani aikine ya hadasu fada don jiya naga sunzo mashi da wasu takardu a hannu su suna mashi bayani.
Zaisa su ambaci suna ki a cikin fadan su zainab ke yarinyace karama wallahi don magana a yanzu baida amfani dake sai nan gaba.
Baki na turo gaba ina fadin kai anty yanzu fa na girma nima ina da wayau kamar kowa.
Mikewa tayi tsaye tana tsuki tare da fadin ni bari in fita kada ya tsurani da farar safiya haka cikin dakin nan ya dauka gulma mukeyi.
Tana fita nikan ban kwanta ba na shiga wanka tunda gari dai ya waye tarr a lokacin na dan dauki lokaci a bayin don haka dabi,ana yake ina dan dadewa a cikin bayi idan na shiga.
Ina wanka zuciyana cike da tunane zancen da tazo ta fada min din sai cewa nake me ya hadasu fada hakane har da duka kamar yadda anty ta fada duk dai ba abinda ya shafeni bane don tare na gansu ai.
Na fito daga bayin ina tsane ruwan daya taba min kaina dagani sai dan tawul karami da daure gaba don dakina ne ko halimatu sai jefi jefi take shigowa inda nake .
Banyi sanyi a gwiwa ba don ganin ko waye ya shigo dakin a lokacin na dago kai da sauri ina kallon kofa da dan karamin tawul a hannuna.
Ar,ba mukayi dashi yana tsaye a kofan dakin bai karasa shigowa ba yake fadin ke me wanan matar ta shigo yi dakin nan yanzu.
Da sauri na dan kara kallon shi ina fadin wace mata ke nan yace wanan mai aikin nace abinda zata girka ta shigo tambayana.
Saida ya bini da wani irin kallo kamar yana zargin abindana fada mashi din don rashin yarda da hakan yace
Are you sure na daga mai kai kawai ashe bakin mu yazo daya da ita don itama data fita daga dakina ta same shi zaune falon sai data kadu tana gaidashi a cikkn tsawa yake fadin ina ta fito ?
Tace mai wurin madam ina son tambayan ta break fast ne ya bita da wani mugun kallo kamar na tsana ta wuce zuwa kitchen kai tsaye.
Abinda yasa nace hakan kuwa don akwai ranan da ta taba fadan haka a gareni a cikin wasa yasa na rike wanan kallaman nima a yanzu.
Fita yayi daga dakin da sauri ta hanyar bugo min kofar dakin da karfi da ganin sa a hasale yake dai a lokacin.
Nikan har na shirya ina mamakin hakan a raina duk dana shirya ban fito da sauri ba sai wuraren goma da wani abu na safe.
Da alaman har ya karya ya fita lokacin don kamshin turaren shi daya bari a falon wanda ke nuna ya shigo ya fita don wani lokaci da haka nake gane fitan shi gidan ko dawowa shi gida .
Zama nayi na karya kummallo nima ba tare da wani damuwa da kara bin zancen shi ba don na fawalawa Allah al,amarina da dadewa ko.
Ibadane dai akansa nake ko yaushe ina raba dare ina kai kukana ga Allah kamar yadda malam mijin mai zube da innan mu ke yawan tunatar dani yin hakan ko wani lokaci.
Sabbin masu gadi da security na forces ne aka watsa yanzu a gidan ta ko ina ban san da hakan ba saida fadila tazo tana fadi.
Banyi mamakin hakan ba don girman gida dama yaci ace akwai masu aiki wadattatu kamar hakan a gidan.
Kwana biyu tsakani suka bar kasa ya tafi ya barmu da tulin abi arziki a tare damu ta yadda ba zamu nemi komai mu rasa ba a gidan ko a waje.
Bai kira wayana ba tunda ya tafi har kusan sati uku da tafiyan shi gashi ina son zuwa wanke kai a saloon don yanzu na saba da hakan.
Gashi kuma fita bada yardab shi ba yana cikin gargadin da maizube tayi tamin kafin ta wuce hakan yasa na gane wanan dabi,an baida kyau.
Mace ta dinga fita gidan ta ba tare da sanin maigida ko umurnin sa tunda naji maizube tana faman jaddada min hakan ko yaushe yasa na rike wanan a raina sosai.
Don hakane nake faman jiran kiransa a waya don na fada mai ina son fita zuwa wurin wanke kaina da yake min kaikayi yana son wanki a lokacin.
Bai kira ba kamar yasan ina jiran kiransa sai bayan kwana biyu sai ga kiranshi ya shigo a wayana .
Banyi gagawan daukan waya ba don haka fadila ta koya min sai gab da zai katsene na daga wayan nasa da sallama a bakina.
Ke wata irin yarinyace wai a dinga kira baki daga waya sai ya katse sai naji yaja tsuki kayi hakkuri na fada a hankali .
Numfashi naji ya sauke tare dan ja kadan kafin yace ya kuke hope ba matsalan komai a gidan kowa kuma na aikinsa yadda ya dace.
Bamu da matsala na fada a sanyayye saidai wurun wankin kai nake son zuwa dama kuma sai baka kira ba in fadama.
Sai idan na kira zaki fita a wanke maki kanki ke wata irin yarinyace wai da gidadanci haka wai ?
Amma kasan fita bada umurni ba baida kyau a musulunci don haka iyayyena suka horeni dashi tun a gida .
Shout, up ki kama min baki da wanan irin maganan meye amfanin motocin dana aje maku a gida hakana .
Shiru nayi banyi magana ba sai sauraren shi da nakeyi kawai yadda ya hauni da bala,i don fadin gaskiya kawai.
Waishi wani irin mutum ne haka mai bahagon haki kamae dai ba musulmi ba duk wani dabi,a na musulmai shi sai a slow harkan shi dai .
Muryan shi na tsikayo a cikin wayan yana fadin akwai wasu masu aiki da kabir zai kawo maku yau zasu dinga dafawa masu gadi da sauran aiyukan gida abinci da fatan zaki kula da hakan.
Insha Allahu na bashi amsa ina sauke numfashi don tunanen dana danyi na da lokaci nasa saida naji muryan shine na dawo a cikin hankalina.
In tafi wurin wanke kai din na kara tambayan shi lokacin dana fahinci yana kokarin kashewayan nasa lokacin.
Ki tafi ya bada amsa a dan hasale yana kashe wayan shi sai bin wayan nayi da kallon mamaki kamar shine a gabana.
Abin mamaki kwana biyu dayin wanan wayan dashi sai ga wani kiran nasa ya kara shigo min dauka nayi da mamaki ina bin wayan da kallo tare da tambayan kaina wani abu ya samu kuma yanzu yasa ya kira wayana.
Don dai na fahinci shi baya kirana sai idan akwai wani dalili magana da zai sa ya kirani din zai kira layin nawa ina dauka da sallama naji muryan shi yana fadin.
Ke ki shirya kuje asibiti ku gaida hjy samu,naka tana nan an kawota asibiti jiya tana tambayan ki .
Innalillahi nace kafin in tambaya cikin muryan dake shirin sake kuka ina fadin yaya meya sameta da sauki jikin nata ko ?
Idan kije zaki gani ya fada yana kashe wayan sai nabi wayan da kallo a rude don iya kacin maganan ke nan daya fada min.
Banyi sanyi a gwiwa ba na fada wa fadila muka shirya a gurguje don zuwa duba jikin hjy din duk da ina fargaban haduwa da mami a wanan lokacin.
Ba yadda zanyi don dole in tafi koda bai umurce da haka ba don hjy tafi gaban haka a wurina don nima a matsayin jika makusanta ta daukeni a zuciyar ta.
Abinci lafiyayye da mara lafiya zata bukata da sauran abin sha duk anty fadila ta shirya wanan muka fito driver yana waje suna jiran mu tare da wani security daya.
Dukkan mu uku baya muka shiga munsha kyau sosai damu duk da asibiti zamu tafi gaida mara lafiya din.
Ba wanda yai magana a cikin mu ido kawai muka zuba masu sai gashi sun kaimu har asibitin da aka kwantar da hjy din.
Bamu sha wani wuya ba don komai na zuwan mu kamar a tsare yake busa umurnin shi a wurin su din don yai masu bayanin komai kafin mu fito.
Gabana yana faduwa sosai duk da a cikin dan dakewa nake saboda zaunar dani da fadila tayi ta tsara min kkmai.
Dakin maikyau kamar mutum a gidansa yake fadila nagaba ina tsakiyan su muka shiga dakin da sallama a bakunan mu.
Mami ne saman gado zaune sai Aisha dake gefe da wayan ta a hannun ta tana duba har yanzu wanan bakar sana,an nata yana nan mata ashe Nuriya kuma da yaranta suna saman kujera suma suna nasu harkan na daban.
Amsa sallaman sukayi batare da sun san ko suwaye suka shigo ba a lokacin sai daga baya da suka gane mune naga mami din ta kawar dakai ga duban mu.
Gaida su mukayi a bisa al,adan bahaushe idan yaje dubiya ya samu mutane a gurin ya fara gaudasu tare da tambayan jikin mara lafiya din.
Ba yabo ba fallasa suka bamu amsa wanda Aisha ce ta iya amsa muna din a lokacin ba wanda yai muna nuni da wurin zama don haka muka tsaya a tsatsaye daga dan nisa kadan dasu.
Ba wanda ya kara bi ta kanmu muna tsaye saiga security din da mukazo dashi ya shigo dakin rike da basket din abinci da sauran tarkace.
Yana gaida su da tambayan mai jikin mami bata samu amsa mai ba take tambayan wanan kayan fa a cikin daure fuskan ta .
Yace madam ne ta zo dasu duba mara lafiya ku koma dasu ta fada a gimtse fuska babu sauki sai ga ya mamud ya shigo dauke da ledan magani mai tambari asibitin a hannun shi.
Daga kofa yaji abinda mami din ta fada ya cewa security din ya aje tare da fadin zainab ashe kun shigo yakuke ya gidan.
A dan rakube na amsa mai tare da gaida da tambayan ya maijiki yace taji sauki ko dazun da safe saida ta tambayeki ai.
Kai mamud nace a fita da kayan nan kace a ajesu koda matsiyaciya nake banga abinda zai kaini cin abincin yar yaudara ba ai.
Komai idan na wa yan nan ne bazan taba karban shiba ni haba haba mami haka bai dace ba wallahi.
Zainab fa tana da daman zuwa nan ta kawowa hjy a bu don yanzu itama she is part our family ai tunda danki ke auren ta nagani.
Zainab din tazo ne hjy dake barci ta fada kamar a mafalki lokaci guda shi ya amsa mata da eh hjy ai gata a tsaye ma akanki.
Hannu hjy ta miko min tana fadin yar nan ashe da rabon kara ganawan mu zo kusa dani ki zauna tana kokarin yunkurawa daga kwancen da take.
Da sauri na karasa bakin gadon ina fadin hjy ashe baki da lafiya hakane wallahi ban sani bane sai dazun nake ji.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
5️⃣6️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAR UWA UBANGIJI ALLAH YA KARA MUNA IMANI YASA MU CIKA DA KALMAN LA,ILLAHA ILLAH MUHAMMADAN RASULLILAH ALLAHUMA AMIN, , , ,
Hannuna ta rike na wani dan lokaci tare da sauke idanun ta gareni tana fadin ance mijin naki baya kasan nan ashe ya koma inda yake ke nan.
Ganin gani kusa da mami a inda take zaune har kamshin jikina yana dukan hancin su daga ita har Aishanta.
Yasa mami jin wani irin tsana na ya kamata tundai data dubu yabayina gaba daya na canzawa sanin da tayi min a baya can.
Hakan yasa ta mike dan barin dakin ga baki daya ranta kuma a bace da abinda idonta ya gane mata game dani din lokaci guda .
Don a kullun zata ganni sai taji tsana da take min yana kara karuwa a zuciyata duba ga yadda danta ya gyarani cikin dan kankanin lokaci kadan.
Ina kuma zaki hjy ta tambaya a cikin yanayi zafin ciwo har lokacin hannuta ya rike da nawa take fadin.
A zuba min abincin da zainabu ta kawo min inci tana rufe baki Aisha da kanta ke duke saman wayan ta tace kai amma hjy nan dazun nan fa aka gama fama dake kici abinci kika ki ci.
Yanzu kuma kice wai a zuba maki wanan da baki san ma komeye a cikin sa ba don gulma da iya yin ki na tsofi.
Uwarke ce gata gabana yar iyayi a zuba min abuncin gidan jikana in ci inace dazu da abinfa mamuda yakawo min na karya dashi.
Sam basu ji dadin wanan maganan tsohuwar ba a lokacin babu yadda zasuyi dole aka bude abincin a lokacin sai kamshi ya bude dakin lokaci guda.
Ya mamud ne ke fadin zako taci ko don wanan ganyen da akai amfani dashi don alaihu ne da anty zanci kaidai da albarka hjy ta fada a hankali.
Ina kallo don keta Aisha ta zubo mata da yawa tana wani toshe hancinta kamar maijin warin abincin a hancinta.
Da sauri anty fadila ke fadin kai ina zata iya cinye wanan abinci haka mai yawa ai saidai dan kadan yanzu tunda bata jin dadin jikin ta.
Ban iya bawa mutum abu kadan ba ta fada a dan hasale tare da nufar hjy da abincin bayan ta gama fadan bakar magana ga anty fadila din.
Da kyar hjy ta dan tashi zaune tare da taimakona a daidai lokscin da mami ta fake ga waya ta fice daga dakin ke ban.
Fitan ta yasamu sakewa don har ajiyan zuciya na dan sauke a hankali don naga ta fice daga dakin hankalina ya koma a kan tsohuwar dake jin jiki a lokacin karfin hali kawai takeyi a yadda take din.
Mun dade a zaune kafin mami su shigo tare da kawayen ta su uku dakin wani kallon banza suke bina dashi hakan yasa na kara shan jinin jikina sosai.
Sannu sukaiwa hjy din tare da fatan samun lafiya a gareta daga nan suka buge da hira wanda yai kama da haibaici a gareni.
Muryan hjy ne daga kwance take fadin kowa dai ya iya wanke allonsa sai bangon ya tsage kadangare ke samun wurin labewa.
Kai mutum bakai kayi kanka ba balle kayi wani shi dan mutum dama ba abin rainawa bane a duniya wata dan hakin nan daka raina wata rana yazo ya tsone ma ido.
Shiru dakin yayi na wani lokaci kafin dayar matar da tun dama na santa a gidan mami din ta fara mikewa tare da fadin babba Allah ya kawo sauki tare da aje mata kudi gefen gadon ta ta bar wurin.
Kusan duk haka sukayi suna ficewa daga dakin kafin mami ta mike tana bi bayan su a can waje suka tsaya suna gulmana .
Ba komai suke fada ba sai cewa da matar nan ta farkon fita da tayi daga dakin kai hjy wanan yar ko zaki iyata nan gaba ?
Sai dayan tace aini imani duk ya kasheni gani wanan yarinyar gaskiya hajiya danki yaki sauraren ki a kanta don gaskiya wanan yar matar manyace sak.
Ki duba lokaci guda yadda yarinya ta sake a baki daya kamar wata da wani a kasan nan ina ga ta kara nan gaba don ba iya nan zata tsaya ba.
Humm bari kedai hjy dada ni kaina abin yana ban mamaki sosai a raina canzawan wanan yar a cikin kankani lokaci haka kamar abin hadin baki.
Don yanzu ma baya ko saurarena akanta dana dauko mashi zancen zai nuna min baya so shifa matar shi yake so .
To ba,a barshi banza ba hjy ina kuwa zai saurara maki akanta yana ganin wanan a tare dashi ai ba zai saurare ki ba.
Ni ai yanzu matsalata hjyce don naso yi masu koran kare a asibitin nan sai dan bakin nan hayaniyar shi ya tayar da hjy daga barci da yau na nuna mata iyakana a wurin nan.
Kai da kin barsu dayan matar da batayi magana ba tun fara zancen gaba dayan su kallonta sukayi lokaci guda.
Taci gaba da fadin aurene dai ya riga da yayi shi don haka nidai naga kiyi hakkuri kawai ki bar yara nan su zauna lafiya a tsakanin su tunda kinsan halin wanan yarinyar tun farko.
Ki duba fa ita matar namuda fa bata gaida kowan mu ba har muka fito dakin nan yanzu ina laifin wanan din da har kasa ta gaidamu tunda tasan mu din yaya muke dake.
Amma dai hjy karima zancen nan naki baimun dadin ji ba wallahi akan me zaki wani ce ta barshi da matar sa wa zata nuna a matsayin mahaifin matar shi ranan da hakan ya taso.
Kai hjy saudat kina wani zance wallahi yaushe har haka zai taso din kowa fa da ubansa yake tunkaho komai lakacewan shi kuwa .
Nidai a wanan zancen hjy maryam hakkuri zan baki kiyi hakkuri ki zauna lafiya da yarinyar nan kada aje har girman ki yakai ga faduwa a wurinta wata rana don zuciya bata da kashi.
Daga haka ta fara takawa zuwa wurin motar ta inda driver ke jiranta su tafi ba tare da ta tsaya koda yin sallama dasu ba.
Muyi sallama dasu don ba fuska a garemu da zamu dauki lokaci a wurin su don haka muka fito don mu tafi bayan hjy din ta dan samu barci a lokacin.
Ashe da daren ranan batayi barci da dadi ba haka yasa washe gari ya jafar yanke shawaran zuwa Nigeria din don hankalinshi ya tashi da yadda ake fada mai ciwon nata.
Ban san da zuwan shi ba saidai nayi sa,a mun aika da breakfast da abincin rana asibitin duk da mami tayi magana da aka kai na safe din amma bamu fasa aikawa dashi ba.
Don ko washegarin da jikin nata ya rikice mun tafi asibitin mun duba jikin nata duk da mun sameta tana barci a lokacin.
Har muka fito kuma bata falka daga barcin ba sai ya mamud ne yace zai fada mata munzo idan ta tashi kuma ya fada mata din don da aka kai abincin dare take fadin tana gaidamu gobe akawo mata abinci da wuri don abincin gidan mu take iyaci nasu mami yana da yaji sosai.
Can cikin dare muke jin ana dokan kofa kusan tare muka fito lokaci guda da fadila saida ta tambaya yake fadin shine ta bude kofan.
Ta bude da sauri ya shigo muna mai sannu da zuwa ya karba muna yana kokatin shigewa part din shi yar jakkar hannun shi aka shigo mai dashi ciki na karba don in kai mai daki.
A tsaye na sameshi a dakin yana kokarin cire kayan jikin shi sama sama na gaiyar dashi na fito saida safe ne ya fice zuwa asibitin .
Ya dade a can har muka aika da abin karyawa kamar yadda muka saba bawa driver ya kai ko anty fadila taje da kanta.
A can aka sameshi tare da hjyn da sauran yan uwa da sukazo daga kaduna don duba jikin tsohuwar da suke jin ya matsa mata ana fama da ita yana son zai wuce da ita can a dubata taki yarda.
Wai ita tafi son a barta ta mutu a dakinta idan mutuwa ya tashi zo mata ana dai ta fama da ita taki yarda har lokacin da ya dawo gida don ya huta saboda gajiyan dake jikin shi din na tafiya.
Barci sosai yayi daya dawo sai yamma ya tashi don kansa tunda dai mu ba shiga part din mukeyi ba sai idan wani abu ya taso yake kaini part din nasa.
Har mun gama abinci da za a kai har fruit's salad mun hada mata ko zata sha duk wanan dabaran anty fadilace don kawai a burge mami dama wanda ke wurin lokacin.
Fitowan shi sai cewa yayi in shirya mu tafi asibitin a tare duk wanan yana cikin hikimarshi na kawar da idon mutane ne a kan mu.
Hakan bai zama min bako ba a wirina don nasan yakan yi mun hakan idan yana son fita tare dani wani lokaci kafin ya tafi.
Dakin makil yake da yayan hjy din da sukazo zasu kuma kwana a nan kashe gari su koma wurin su biyar ne mata sai maza ukku.
Ana faman hayani da dararaku kamar ba mara lafiya a dakin ya shigo ina biye a bayan shi fuska murtuk don halin daya samesu din a ciki.
Suna gaidashi yana amsawa sama sama bai tsaya ba sai bakin gadon da hjy take kwance mama Ramaru tana kusa da ita suna da magana.
Yake fadin hjy na fada maki ki yarda mu tafi a kaiki asibitin can a dubaki ki daina wanan wahala haka don Allah.
Budan bakinta sai cewa tayi bazan tafi ba sai idan da matarka zamu tafi nima wanan kafan yana damuna wallahi.
Dakin ne yayi tsit sai mami da tace aiko tare da Ramatu zaku tafi hjy tunda dai Ramatu tafita sanin komai ai .
Ta yaya zamuyi tafiya zuwa gidan shi matarshi na nan idan ba da ita zamu tafi ba saidai a fasa wanan tafiyan kuna abu kamar baku da lissafi a zuciyar ku.
In dai wanan ne ai mai sauki ne har in kin yarda din zaki tafi yaya mamud din ya fada yana dan dariya.
Ya juyo gareni yana fadin zainab ko ba zaki rakata ba tunda hankalinta yafi kwantawa da tafiya dake din can ?
Dan murmushin yake na sake a fuskana mami tace dama ai burin ta ke nan ita tunda iyakarta kaduna Abuja dama.
Yanzu ko abin nema ya samu ga ba saban ba ai sai tafiya hjy rigima kawai kike son dorawa mutane kan tafiyan nan.
Wani iri naji kamar hawaye zasu zubo min lokaci guda don yawan muzantanina gaban mutane da mami din ke mun .
A cikin dakewa na daure Allah ya taimakeni hawayen bai zubo min ba sai dan dukar da kai danayi kasa sauran mutanen dakin duk sun zubo min ido a kaina.
Ji nayi ya riko hannuna yana fadin mami yarki ai ta waye yanzu ba kaduna ba ko Abuja ba ko inama zata iya shiga yanzu ai ya fada yana kokarin rugumeni a jikin shi cikin rashin damuwa da duk wanda ke dakin a lokacin.
Kai jafar a gaban mu kake kokarin rugume matar ka don ka saba da dabi,un ku na turawa a can mama Ramatu ke fadin hakan tana mashi dakuwa.
Mama ai matatace ko ina ina iya rike abata wanan shike nuna irin son da nake mata ai kuma ku sheda koba haka ba besty na ?
Ya dan rugumo kafadata zuwa jikin shi yana dan murmushin da shine iya dariyan shi a hankali na lumshe idanuwana don irin abinda naji a lokaci guda.
Kada ka bata muna yarinya din nasan zainab na da kunya ita mama ko kin mata ita din matanane a yanzu ?
Kai jafar kaikan a Allah shirye ka yanzu kan sai a barka inda aka ganka wanan aure ya saka zama mara kunya yanzu.
Mama ai idan ban kulata kuma bakwa jin dadi don amana take garemu baki daya a wurin nan ai.
Ni kaina nayi mamakin yadda ya bushe idon shi haka a wanan lokaci yana zuba masu rashin mutunci mutumin da baya magana sai yaso hakan.
Yanzu dai kinji mamaku tace saida matana zatai tafiya don itama tasan amdanin ta gareni ai shike nan gobe za a fara shirin tafiyan mu a tare.
Amma sai naga kamar ku tafi kawai da Ramatu don ko anje da zainab din can me zata iya maku banda karin nauyi kuma.
Wata daga cikin matan tace ba haka hjy je so ba ai gara dai a tafi da ita din zaifi ko banza ai gidan mijin tane za a.
Ni dai ina daga tsaye ina jin irin shawaran da ake yankewa a kaina akan tafiyan da hjy tace ayi dani tare da ita.
Mami bar wanan zance don Allah tunda hjy ce ta zabi yin hakan ya mamud ya fada a dan hasale yana kawar da kanshi gefe daya dan baiji dadin yadda mami din take nuna min a gaban mutane ba.
Saida muka fito daga asibitin yana waya har lokacin da muka baro dakin wani kuka yazo min lokaci guda tun ina kokarin rike kukan ban san lokacin da yazo min ba da karfi.
A rude yake fadin subbahanallahi ke ke maye haka wani abin akai maki yanzu ko meye ki keyi kuma zaki tayarwa mutane da hankali a banza.
Ban sauraren shi ba illa sheshekan kukan da nakeyi wiwi kamar an aiko min da mutuwa don bacin rai.
Umurni ya bawa driver da karfi ya dakatar da motar har na bayan suka tashi dakan motar da muke cikin sa Allah dai ya gyara basu dake mu ba din.
Wai me ke faruwane haka kika tayarwa mutane da hankali haka da kukan banza kaina na nade cikin gyalen dana yafa a jikina sai sharban kuka nake babu kakautawa.
Shirune ya dan biyo a mitan bayan security din shi sunzo ya karesu ta yanyar dakatar dasu da hannun shi suka koma baya da sauri.
Can na dago kaina a hankaki tare da hade hannayena a wuri daya ina fadin don Allah yaya ka mayar dani wurin iyayyena don mami ba zata taba kauna naba muddin ina tare da kai.
Ke kanki daya kuwa kike fadin wanan maganan gareni yanzu zaman mami kike a yanzu ko nawa da tasoki ko kada ta so ki ai ba akarkashin ta kike ba .
Dan Allah rufe min baki kada na saba maki yanzu a wurin nan haka kawai dan shagwaba zaki saka mutane a gaba kina min kukan banza.
Dan Allah yaya kayi hakkuri ka mayar dani gaban iyayyena ba zan iya zama haka mami tana kina a kullun ba tsanar da mami take min yana min yawa a zuciyana.
Maimakon inga yayi fushi sai kawai naji ya dan rungumoni zuwa jikin shi yana rarashi a cikin tsigan da ake rarashin yaro idan yana shagwaba wa iyayyen shi.
Saida yaga nayi shiru ya ba driver umurni ya tayar da motan har muka kai gida ba wanda yai magana a cikin mu.
Mota na tsayawa nayi saurin kokarin budan motar ta gefen da nake zaune saidai motar tana rufe har lokacin ba,a bude ba.
Sai lokacin na dan juyo da fuskana zuwa duban shi a hankali da fuskana daya koma ja saboda kukan da nasha a lokacin abu ga faran mace take gaba daya fuskana duk ya sauya kalar ja lokaci guda.
Ban yarda mun hada ido dashi ba nayi kasa da kaina don nauyin shi da nake ji yadda ya zuba min ido yana kallona da yanayin dana kasa fassaran shi ko na tausayine ko kuma wani abu.
Ki share haayen ki ya fasa a hankali don kada su dauka anyi maki wani abune idan kika shiga masu haka kinsan halimatu nada wayau sosai zata iya gane kinyi kuka.
Dole badon naso ba na share fuskana da gyale na yana kallona har lokacin kafin yaba driver umurnin ya bude motar na fita a hankali shikan ko motsi baiyi ba alaman fita daga motar.
Haka na dinga hada kafana har na shige cikin gidan nayi arzki babu kowa a falon suna cikin dakunan su do magariba daya kawo jiki.
Gado na fada na saki wani kuka gwanin ban tauayi ni kadai a dakin har na gaji naba kaina hakkuri na mike don gabatar da sallah saboda lokacin dake wucewa .
Ina wurin da nayi sallah a zaune na kasa tashi aka turo kofan dakin nawa fadilace ta shigo don ta duba ko mun dawo a lokacin ta samu mun dawo din.
Kallo guda tayi min ta fahinci cewa nasha kuka tare dani da sauri take fadin zainab meke faruwane yanayin ki ya nuna kinyi kuka haka mai yawa.
Zuwa tayi inda nake zaune din tare da zama a kusa dani tana fadin meya samu kuma zainab kun fita lafiya kin dawo da kuka haka ko yayi maki wani abinne kuma.
Kai na girgiza idona yana kawo hawaye nace a cikin kuka mamice dai ta tsanane bata kaunana har cikin ranta yanzu.
Meye laifi ne anty don kawai ya jafar ya aureni meye laifina tasan bada yarda na haka ya faru ba tsakanin mu ?
Baki da laifi zainab kowa ya sani amma zata daina ai idan ta gane hakan ba laifin ki bane kema nan gaba zata gane dantane mai laifin bake ba ni abinda na yarda dashi ke nan kedai ki kara hakkuri zainab.
Bafani nace ai tafiyan nan dani ba anty hjy ce ta kafe sai dani zata yarda ta tafi can inda yake zance ba zan tafi bane ni ?
Dake zai tafi zainab ta tambaya cike da mamaki a fuskan ta tana kallona kai na gyada mata alaman eh.
Za ako samu matsala wallahi saidai idan kin daure hakan ba komai bane zai zamo maki alheri ta wani bangaren rayuwa.
Anty idan mami ta barni ke nan har haka zai faru ni dai kawai gara yaya yace ya sakeni ko rayuwana zai zauna a cikkn sallama yafi.
Ina amfanin wanan zama namu da mukeyi hankalin kowa a tashe gara kawai ya sallameni na koma gidan mu in zauna a gaban iyayyena ko kasa sukeci muci shi tare dasu.
Ki bar fadin wanan magana kiyi addu,a Allah yasa hakan shine alheri a rayuwan ki dama kowa da abin ya shafa.
Anty kina ganin haka zamu zauna da sunan aure tsakani da mami da danta har ma da kowa daya shafi mami din ?
Yanzu fa a asibiti babu wanda ya nuna damuwan shi a kaina danaje sai hjy hjy kuma kinga ai tsohuwace basa jin maganan ta ko a yanzu.
Duk zasu bari ta fada amma fa idan kin jajirce wa kowa haka zai faru nidai shawarana har gobe gareki shine .
Kiyi kokari shakuwa da sabo ya shiga tsakanin ki da mijin ki har ki fahinci wani abu daga halayen shi na boye da baki sani ba tayi min wanka da jurwaye cikkn maganan ta.
Kaina daga hawaye naci gaba da zuba min a idona take fadin kwarai zainab don ba mami bace matsalan ki a yanzu matsalan ki shine mijin ki ya daukeki a macen aure ya dauko ki.
Kada kiji ina yawan fada maki haka ki dauka da wasa nakeyin zancena a a zainab akwai matsalan da nake hango maki nan gaba wanda yafi wanan da kika saka a ranki duk na mami shirmene gaskiya .
Anty wani matsalane wanan na tambaya cikin son karin bayani daga gareta kafin tayi murmushi tana fadin ba zaki fahinceni ba a yanzu.
Saidai shawaran da zan baki shine ki sa ido ga wa yanda mijjn ki yake mu,amula dasu sosai ki fahinci wani irin rayuwa yakeyi dasu.
Musanman wanan taju din don ni sam ban yarda dashi ba amma don Allah ki boye wanan zancen a cikin ran ki har lokacin da zaki gane wani abu din.
Sai ta kawar da zancen data dauko din da fadin yaushene tafiyan naku yanzu kuma mu a nan za a barmu ke nan ko me ?
Ban sani ba anty saidai tunda hjy za a kai asibiti ban tsamani tafiyan zai dauki lokaci ba don naji yana fadin za a soma shirin tafiya daga yau din nan.
Kai amma zanso na danje maki wani guri kafin tafiyan duk da hakan ba matsala bane gobe insha Allahu zan fita na dan je wani guri ai gara da naji da wuri tun lokaci bai kure muna ba.
Don haka kada ki yarda ki saka uwar miji a damuwan ki don irin su mami hakan suke son gani a gareki ko yaushe sai ransu su kuma yayi dadi da hakan .
Sun san komai ya lalace maki ke nan daga bangaren su har na mijin naki baki ba sauran kwanciyan hankali a tare dake.
Don haka ki saki ranki ki duba matsalan mijin ki dake gaban ki ba wanan shirmen ba da tana da iko ko auren ki ba zaiyi ba ai.
Ta fita ta barni da funanen meye wanan matsalan da kullun take kiramin ne ni har yau na rasa gane me hakan ke nufi waine wai ?
Ina shiri kwanciyane ya shigo dakin nawa ina saman mirrow zaune halimatu bata dade da fita a wurina ba don tun tafiyan msizube ta koma kwana tare da anty fadila watarana kuma mu duka ukun muke kwana a daki guda idan mu kadai ne a gida.
Wuri ya samu ya zauna bayan na amsa maushi sallaman daya shigo dashi fuskan shi a kaina yana kallon yanayi na a lokacin .
Saida ya zauna yake fadin kin gama kukan shagwaban naki ke nan ke sai yaushe zaki girma ne wai a gidan nan?
Daga cikin mirrow na dago kai muka hada ido dashi nayi saurun dukar da kaina kasa da sauri don ba zan juri kallon da yake min ba din saboda yanayin da hakan yakan sakani idan yana min wanan kallon.
Gobe sai ki shirya zamuje ai maki photo na fita waje saura idan mun fita kuma ki min wanan shagwaban naki da kika iya .
Ban tankashi ba har ya kare maganan shi ya fita waje sai lokacin na sauke ajiyan zuciya tare da fada da kaina watau shi wanan mutumin bai ma san ina yi ba ke nan ya mayar dani wahalalallah .
🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
5️⃣7️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAR UWA BAZAN GAJI DA TUNATAR DAKE KAN HAKKIN WANI BA WANAN LITTAFIN NA KUDINE DON GIRMAN ALLAH KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA.
Yar uwa kada kiga namatsa da magana don tunatar dake sauke nauyin haki nake fadan wanan kalman a kullun don akwai ranan tambayan hakki ga kowan mu.
Kamar yadda fadila tayi alkawari hakan ne ya kasance don tun safe yati muna sallama kan zata duba haifiyarta da yara.
Sako ta bari a fada mai idan har ya neme ta bata gidan a fada mashi ta tafi duba mahaiyar nata bayan tafiyan ta sai gidan ya koma muna shiru.
Don hakane ba fito ba tunda ni kadaine a gidan kwanciya nayi daga nan barci mai nauyi ya daukeni har tsawon wani lokaci ina kwance.
Ashe shima ya fita zuwa asibiti duban hjy tun safiyan har lokacin daya dawo gidan baiji motsin kowa ba sai yan aiki dake aiyukan su a kitchen da wajen gidan.
Hakane ya bashi mamaki don rashin jin duriyan kowa daga cikin mu ba yasa shi zuwa dakina direct daya fito daga part din shi.
Kofan yake ta bugawa har sau uku ba a bude ba yasa kai tsaye ya turo kofan ya shigo dakin nawa.
Akwance ya hango saman godon nayi ruf da ciki ina sharan barcina hankali kwance sai hannuna dana danne da zai iya min ciwo idan na falka daga barci.
Sai gashina dake daure dan kwalin dana daure ya koma gefe daya da barcin da yai nisa a lokacin ban ma sanda hakan ba.
A hankali ya tako zuwa inda nake yana tafe yana kare ma fuskana kallo mai kama da barcin ma a wahalce nakeyin sa a lokacin.
Da dukawa yayi a hankali yana kokarin dan dagani tare da ciro hannun dana danne saboda dadin barci tare da sauke idon shi a kan fuskana kurruciyana da yake gani ko yaushe ya kara fito mashi fili a idon shi.
Yanayinb Numfashi da naji ya surku min duk da a cikin barci nake lokaci hakan bai hanani sanin bakon yanayi ya surkumin ba a lokacin.
Da sauri ba bude idona a daidai lokacin daya kura min idon shi a kaina shine tsaye a kaina saidai ina ganin hakan kamar duk nauyin barcine mafalki nake a lokacin.
Don haka na mayar da kaina saman hannun shi din da yake kokarin gyara min kwanciyan tare da juyawa a yadda nake kwance din.
Bai san lokacin daya dan saki murmushi a fuskanshi ba don wautan kurciyan daya ga nayi a lokacin har da Ac dakin ya rage min yadda yaga na koma takure na kwanta kamar sanyin yana damuna lokacin.
Saidaya fita daga dakin karan rufe kofan yasani bude idanuna da sauri tare da kallo kofan shigowa dakin.
Ya riga ya fita a lokacin sai kamshin turen shi daya bar min a dakin lokacin yake tashi ta haka na gane cewa ya shigo dakin a lokacin ba mafalki akeyi ba ashe.
Da sauri na zabura na bude idona tare da mayar da hankalina gun agogon bangon dake manne a bangon dakin.
Mika nayi kafin in koma in lafe ina runtse idona a hankali tare da tunanen meya kawo shi dakina a wanan lokacin.
Ganin anyi azahar har ana neman uku da wani abu yasa na mike zuwa ban daki da sauri na dauro alwala don sallah a zahar.
Ban fita ba bayan na idar don sanin da nayi yana gidan a lokacin ya hanani fita duk da na fara jin yunwa a cikina amma haka na daure na lake a dakin ban fito ba.
Banyi tsamani akwai wanda yasan tare da halimatu zamu tafi ba don koni sai a wanan shigowan na san da zancen tafiyan ta a bakin shi.
Ya shigo yana fadin yau ina wanan mai aikin naki ta shiga dago kai nayi na dan saci kallon shi tare da fadi ina wuni yaya.
Saida ya da bata fuska kadan nasan halin malam baushe ne yaki jini maikom in bashi amsa sai kuma na dauko mai wani topic yanzu na gaisuwa.
Bayan ya amsa min tare da maimaita tambayan shi garen ta tafi gaida mahaifiyan ta tace a fada ma kara daure fuskan shi yayi kamar hakan baimai dadi ba.
Kada ku dauki kaya mai yawa don tafiya ya fada yana daidai fita daga kofan dakin nawa daya shigo jin haka yasa nake masa kallon mamaki ta hanyar binshi da idanu.
Ko baki gane abinda na fada bane cewa nayi kada ku dauki kaya mai yawa daya wuce kala biyu ko ukku .
Nida wa kenan na tambaya batare da na shirya tambayan shi a lokacin ba saiji kawai nayi bakina ya subuce min lokaci guda ina tambayan shi.
Dake da sadiya mana ko a nan dama zaki barta kike nufi ya jefo min tambaya kamar a hasale yana kokarin juyawa ya fita daga dakin.
Nan ya barni zaune mamaki da imani ya cika min ciki don ban taba zaton haka ba daga gareshi sai tunane nake ni kadai a dakin .
Wai shin dama haka rayuwan shi yake kodai nine yakewa hakan yanzu don ina matsayin matar shi amma kuma naji ko anty fadila takan yaba kokarin shi sosai garesu kaf masu aiki a gidan.
Sai lokaci na tuno da ita don haka na mike ina zaton ta dawo zuwa wanan lokacin sai bayan magariba ta dawo gidan.
Inda ta leko dakina ta samu ina sallah a lokacin ta wuce zuwa dakinta ban fito ba saida na gama duk ibadan dana sabayi kafin in fito zuwa dakin nata.
Na shiga da sallama tana waya sai ido datayi min nuni dashi in zauna na nufi bakin gadonta na zauna tare da bin dakin da kallo.
Zainab kingani sai wanan lokacin na samu dawowa ko da sauri na juyo inda take tare da dan nisawa nadan sauke a fili na mayar da hankali gareta ina fadin sannu da dawo ya su mama yaran ?
Ban samu ganinsu ba don na fada maki inda zantafi ai tun jiya dan dama mama na bita wurinta na karbi sako tare da fada mata zancen tafiyan ki.
Dan murmushi nayi cikin jin kunyan abinda ta fada taci gaba da fadin tayi murna kwarai dajin haka tana maki fatan Allah yasa ki zauna can daga wanan tafiyan kusa da mijin ki kada ya dawo dake nan kuma.
Nan ma dai kaina sada kasa don nasan abune mai wuya zamana a can tare dashi tunda ba hakan ya tsaraba a tunane na.
Kai yau nasha wahala zainab sosai wurin zuwa wanan kauyen can kauyen Narasawa ne naje don shi can yake zaune yana bada magani.
Da sauri na dago kai don jin abindata fada ina mamaki kuma a raina da irin halinta na kula yanzu a kaina tayi wanan tafiyan tun safe har dare haka ?
Kinsan nasan zaman da kikeyi a gidan nan dole hankalina ya daga dan ganin zai tafi dake can inda babu kowa da zai saka maku ido tsakani ki dashi.
Duk da dai ba tsanmani da zai iya cutar dake ba ko wani abu makamancin hakan tunda naga yana da dama sosai gaskiya saidai riga kafi ance yafi magani.
Hannu ta mika tana jawo handbag dinta data fita dashi zuwa unguwa da safe tare da dauko wani dan kwalba karami tana fadin wanan yace in baki da zaran na iso dashi zaki shanyeshi gaba dayane lokaci guda saura sai ki shafa a fuskan ki amma sai kinyi bissimillah zaki kafa baki ki shanye shi.
Miko min tayi na karba hannu na rawa tace yanzu zaki shashi dan haka kiyi bissimillah kisha yanzu don nasan halinki da rashin daukan abu da muhinmaci zainab.
Dan dariya mai kama da yake na sake a fuskana tare da kokarin bude dan kwalban data miko min ba tare da tunanen komai ba danjin bissimillah datace inyi kafin insha nasan koda na cutarwa ne Allah zai tsareni don bissimillah danayi kadin insha din.
Duk da inada yakinnin tsakani da Allah take taimaka min dinndon naga alama hakan sau tari da yawa a gurinta.
Saida na zuke dan ruwan dake cikin kwalba a gabanta kafin tace makaru ne sosai kingan shinan yana da amfani sosai a jikin mutum.
Sai wanan kuma wanka zakiyi dashi sau uku kinga yau ke nan zaki fara gobe da safe kuma kiyi sai da yamma kuma shike nan kin gama dashi.
Sai wanan gaskiya shi amfani dashi kamar zai maki wuya nake gani zainab don yace zaki shafa ne ta yadda zai iya shakan shi sosai a jikin ki.
Ni kuma naga yaushe har zai shaki wanan din idan kin shafa saidai kawai mu gwada sa,an mu akai kinga kamar yadda zaku shiga jirgin nan har in wuri daya zaku zauna dashi hakan zaiyi tasiri gareshi ko ya kika gani ?
Banda abin fada don haka na kada mata kai kawai da na amince da hakan tunda banda zabi bayan wanan tunda don ni take wanan kokarin haka.
Miko min tayi na karba ina fadin nagode anty tace babu godiya a tsakani mu zainab don nima kin mun kokari sosai shiyasa dole nataimake ki ai zainab.
Kinga aikin nan wallahi ba don ke ba da yanzu na rashi ga baki daya to sai Allah ya taimakeni ke din yarinyace mai dubaiya sosai wallahi.
Don ba karamin rufamin asiri wanan aikin yai min ba wallahi don har mutane suna ganin yanzu na samu wani babban aikine don rufin asirin da suke ganin mu a ciki ni da iyayyena a yanzu.
Saidai ina jiwa karki tafi ki manta dani zainab don kin san mu mata zumuntan mu sai idan muna tarene yafi karfi sosai haka ke faruwa tsakanin mata da yawa wani lokaci idan ana wuri daya anfi zumunta mai karfi.
Saidai saukin abin tunda muna nan tare da halimatun ki zaki dinga tunawa dani don rabuwan mu a yanzu gaskiya zan shiga wani matsala nake gani.
Duk da naji wani iri a raina saidai ya zama dole in fada mata tare da halimatu din zamu tafi yace duk da ban san yadda mami zata dauki tafiya da halimatu din ba idan taji hakan.
A sanyaye nace anty ai dazun ya shigo yana fadin tare da halimatu din zamu tafi can wai bai yarda a barta na ba .
Yanayin fuskantane ya sauya lokaci guda kafin tace min dama nayi tunanen hakan tuntuni don da wuya ku bar halimatu a nan tare damu bakinan.
Shike nan nasan sallamata zaiyi idan zaku tafi don aikina ya kare ke nan a gidan nan dama dan kunake zaune a nan.
Tausayi maganan ta ya bani a kasan zuciyana ban san lokacin danace da ita ba koda ya kama ki bimu can din anty ba zaki iya hakan ba.
Zainab ke nan yanzu har kina tunanen zai aminta da ku tafi dani can idan ma shi ya yarda da hakan idan kin roka min iyayyena nakejiwa da hakan.
Yanzu dai tashi kije kada mu makara kiyi wanka da wanan ruwan maganin kamar yadda malam din yace ban fada maki ba yace ki dage da addu,a da sadaka.
Saidai abune mai wahala a can ki samu wanda zaki bawa sadaka kamar nan hakan yasa nayi tunane idan kina da hali saiki bar dan wani abu anan wanda za a rika bayar maki da sadaka lokaci lokaci.
Ko ba a hannuna ba zaki iyabawa innan ki tana maki wanan sadakan don yana da kyau mutum ya dinga sadaka lokaci lokaci.
Mun dauki lokaci tana dan kara min haske kan abubuwa da dama sai nake jin wani iri a raina kamar nace na fasa badon hjy kakarshi ba babu inda zanje gaskiya.
Nayi kamar yadda tace dani kan maganin yayin da tafiyan mu ya kan kama don sai shirin tafiya sukeyi gadan gadan mu namu idone kawai lokacin.
Karfe uku jirginmu zai tashi zuwa kasan ghana sai ya biya can ya cika fasija kafin mu dauki hanyan tafiya kasan da zamu din.
Ranan kan na shiga damuwa sosai kafin tafiyan mu don yadda zamu rabu da anty fadila wanda ban sani ba ko mun rabu ke nan har abada kamar yadda ta fada min dasafe.
Zama nayi na dafe habana da hannayena duka biyu har hawaye na zubo min a lokacin ban sanda hakan ba.
Kai wanan kuka naki yai min yawa wallahi kada mubi hanya dake kina min wanan kukan a dauka sato ki nayi haka.
Anty fadilace nake tunane yaya ya zamu barta a nan yanzu mu tafi gashi aikin nan dashi ta dogara kuma yanzu, , , ,
Kukane ya kubuce min daga hakan na kasa fadan abinda zan fadi a lokacin don kukan daya rinjayeni a lokacin na rabuwa da matar data nuna min kauna bayan uwata da mami ke nan.
Wani irin kallon banza ya watsa min tare da fadin kinsantane ko ta dalilin wa kika santa ke wai wace irin yarinyace da bata da tunane.
Wani irin sani kake son in mata bayan wanan danayi mata mun saba da ita a gidan nan ta dauke mu kamar yan uwanta na jini tana zama damu tsakani da Allah yanzu kuma ace za a rabamu da ita.
Baiyi magana ba illa fitan da yayi daga dakin ranshi a bace nan ya barni na ci gaba da kukana ba wanda yasan inayi har sai lokacin da tafiyan mu ya gabato mai aiki ya shigo yana fadin ance mu fito da kaysn da za a tafi dashi.
Duk da yahana mu tafiya da kaya mai yawa hakan bai hanani daukan kayan da muke so ba kuma baiyi magana kan hakan ba.
Kuka sosai mukayi lokacin rabuwan mu da anty fadila din kamar ba gobe a ranmu yana ciji mota zaune yana kallon abinda mukeyi din uffan baice damu ba don haushin da muka bashi a lokacin muma yaya ya iya damu ina batun dauko mashi wata yayi ya damu mata duka can.
A airport din mun samu mami dasu hjy a can suna jiran mu sai bayan mun fito daga mota lokacin mami ta bamu baya tana magana da wani da nake zaton dan uwansune .
Muka iso inda suke tsaye gaidasu mama Ramatu nayi har kasa kafin in juya wurin mami din in gaida ita ta amsa a cikin wani irin yanayi ba yabo ba fallasa gareni haka na mike jiki ba karfi na koma gefe daya na tsaya halimatu tana biye dani duk inda nasa kafana.
Bayan mami ta gama magana da mutumin ta juyo tana fadin ita wanan fa ina rakiya tayo maku dai ko ?
Ban bata amsa ba don yadda take magana akwai rashin mutunci a idanunta gareni ya mamud ne suka karaso shida iyalinshi yake fadin.
A,a mai masaukin hjy ashe har kun karaso kuma hjy dai tace sai da kece zata yarda ta je a dubata don bata zuwa gidan gwauro ta zauna ba mata a gidan.
Dariya akasa mata tana fadi da kyar kunga laifinane kan hakan muryan mami ke fadin wai wanan da kuka zo da ita fa tana kallon halimatu din.
Kila da ita zasu tafi mana mami Nuriya matar ya mamud ta fada tana wani yamutse fuskanta ita kamar me kyamar mu.
Dama abinda nakewa gudu ke nan gashi ko ya fara faruwa a mayar da gida kanar kasuwa kowa yazo cin banza ya tafi.
Haba haba mami hakan baida kyau wallahi kema ai gidan ki a cike yake da yan uwa dan ta dau, , ,
Ya jamal bai karasa maganan shi ba mami ta katseshi da fadin jamal ni kake kokarin yiwa wa,azi akan abindana sani kome ?
Ba wa,azi bane mami ya fada yana juyawa don barin wurin ranshi a bace don dashi zamuyi tafiyan ashe .
Wai me ke faruwane kuma ya jafar ne daya iso wurin yake tambaya shiru kowa yayi har mami din dai nuriya ce take fadin mami ke magana kan wanan yarinyar tana nuna halimatu din wai da ita zaku tafine ?
Eh tare zamu a ina zamu barta tunda tare da yar uwanta take zaune dama ni nace a bamu ita don kada zainab din ta zauna ita kadai dama.
Amma ai baka fada min da ita zaku tafiba ko ta fada a dan hasale shima cewa yayi but mami wanan ai issue din family dinane OK.
Zatayi magana hjy tace kai iyami ki bar wanan zancen tunda kinji abinda ya fada daga nan aka fara kiran masu tafiya har aka kawo kanmu.
Duk da na taba shiga jirgi daga kaduna zuwa abuja sai naga wanan din kamar daban ne shi saboda checking din da yai yawa sosai.
Kujeran mu daya dashi su hjy da mama Ramatu suna bayan mu sai na jamal da halimatu a can baya.
Tunda muka zauna tunane ne a gabana shiko system din shi ya bude yana wani aiki a ciki har jirgin ya daga damu na runtse idanuwana a hankali ina tunanen iyayyena da a waya kawai nayi sallama dasu.
Ba wani dadewa ake sanarwa mun iso kasan ghana za a dauki sauran fasinja anan muci gaba da tafiya tun wanan lokacin naga ya lumshe idanuwan shi a hankali.
Jirgin bai dade a nan ba ya daga bayab fasijan sun shiga mukaci gaba da tafiya har lokacin yana a cikin wani irin yanayi da ban kawo komai a raina ba a lokacun kan hakan da yayi din.
Barci ne ya daukeni har ban sani ba na dan kwanto saman jikin shi bai tayar dani ba ya barni a hakan yadda nake don na samu barci sosai a lokacin.
Bumu isa ba sai washegari mun dai dan fita a wani kasa sai lokacin na yaba da karfin halinshi dana gani na zyaa Nugeria a hakan din nabina gaji ga hjy da ake bata taimako don kada ta galabata don jikin da take ji.
Mun isa lafiya kuma mun samu taro a wurin su don har mota uku suka zo taron mu wanan baiban mamaki ba ga dan sanin da nayi koshi waye din .
Kallo kan bani kadai ba harsu hjy da mama Ramatu da jalal da suka saba shiga kasashen duniya saida suka kalli abubuwan mamakin da muke gani a kasan kamar ba duniyan mu daya dasu ba.
Bayan tafiya mai nisa daga airport din muka shiga wani unguwa mai yawan gine ginen zamani sosai na kasan wani katafaren gida aka shiga damu.
Tun abin yana babu mamaki har muka gaji da kallo muka zubawa sarautan Allah ido zuwa lokacin hjy ta gama gajiya sosai don tafiya mai nisa da mukayi.
A cikjn gidan ma munsha kallo don kamar gaba daya yan aikin gidan mazane duk suna saye da uniform a jikin su iri daya.
Wani katafaren falo aka shiga damu sai nake ganin abin kamar a mafalki wallahi ba ido bude nake ba.
A falon ne naga wasu mata biyu yan kasan sun fito suna muna sannu da zuwa tare da kawo muna ruwa da drink's suka aje a gaban mu.
Ban yarda nayi nisa da halimatu ba duk da wuri daya muke zaune dasu mama Ramatu har hjy dake kukan kafanta yana damunta sosai shi kuma bai shigo ba har lokacin.
Muna kanta muna faman mata sannu da jiki sai gashi sun shigo tare da ya jamal da sauri sukayo kanta tare da tambayan meke faruwa da ita.
ZAINAB IDRIS MAKAWAZAINAB IDRIS MAKAWA[13/02, 21:11] +234 802 916 3341: 🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
5️⃣8️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAR UWA FATAN ALHERI A KULLUM UBANGIJI ALLAH YAJI KAN MAGABATAN MU YASA IN TAMU TAZO MU CIKA DA KALLAMAN SHAHADA AMIN, , , ,
A rude yake magana cikin waya a dan kallaman da nake dan tsunta daga abinda yake fadi shine naji cewa ai sauri ai bucking din asibitin da kuma abubuwan da za,a nema ya sani.
Su kawai na danji daga cikin wayan da yakeyi din a harshen turancin su na can mai kama da yaren kasan.
Yana gama waya yake fadin a kira masa julie sai wanan mutumin da suka ahigo tare da sauri ya nufi cikin gidan yana kiran mai suna julie din .
Kamar yare yayi mata don sai naga tana kada kai kafin ta juyo guri mu da fara,a a fuskanta tana muna magana ido kawai muka zuba mata don bamu fahinci mai take nufi da hakan ba.
Saida ya jamal yake fada muna tace mu biyota zuwa ciki za,a shigo muna da kayan mu dakin na daban aka ban za a bawa halimatu nata nayi saurin dakatar da hakan tare da fadin zamu sharing din daki daya da ita she is my sister.
Wani kallo tayi mi sai kuma ta dan dukar da kai cikin girmamawa tana fadin shike nan ta juya ta tafi muka bude dakin muka shiga.
Bamu dade da shiga ba sai ga kayan mu ta shigo muna dashi dakin lokacin ina tsaye ina bin dakin da kallo ikon Allah wai yau mune a cikin wanan irin daulan da muke gani a film din turawa.
Kofan ban daki na nema na shiga nan ma saida na tsaya naba ido abincin sa wurin kallo da dabara har na gane , inda zan danna ruwa ya zubo.
Wanka nayi sosai ga sabulan wanka nan sai wanda ka zaba kayi dashi kafin in fito har halimatu tayi barci don haka ban tayar da ita ba.
Jakkana na bude na fitar da zani sallah da hijjab sai dai ban san inda gabas yake ba a gidan don haka dabara yazo min a karon farko nayi amfani da app din wayana na gane gabas din galrin.
Sallolin dake kaina na fara ramawa a gurguje don kada lokaci ya kara wuceni na dade a zaune ina neman kariyan Allah daga duk wani sheri da tsari dazamu tunkara a wanan garin dama mutanen da zamu zauna dasu din ga baki daya.
Barcin na fara ji don haka na mike na samu gefen gado na kwanta nima a gefen halima ina kallon yadda take barcin ta hankali kwamce.
Sai tunane nake barkatai akan yadda rayuwan mu zai kasance a wanan tafiyan namu da bamu san kowa ba babu alaman kuma yan jinsin mu na hausawa a wana gidan ko akwaisu ma banga alama ba dai .
Barci sosai mukayi har suka fice kai hjy asibiti ban sani ba don ita ta hana a tayar damu don cin abinci tace muna tare da gajiya kasan yaran basu saba irin wanan dogon tafiyan ba haka.
Sai bayan karfe uku da rabi kamar an tayar dani na falka don wanan irin mafalkin danakeyi a baya shine yau ma na sakeyin shi don tun bayan da malam mijin maizube kakan mu ya ban addu,oi ban sakeyin wanan addu,an ba sai wanan ranan kuma.
Gabana ke faduwa sosai ga wani irin zufa dake fita min a duk kafofin jikina lokaci guda muryan halimatu naji a bayana tana fadin .
Yayan mu halan mafalki kikayi hakane ina ta kiran sunan ki sai faman wani irin magana kikeyi kamar kina shan wahala a cikin mafalkin naki.
Addu,an da nake karantawa ne ya hana in juyo in fuskance ta don a lokacin duk a rikice nake sosai don wanan mafalkin yafi sauran da nakeyi rikitani sosai.
Abinka da yarinta ina wanan addu,an sai na nemi damuwan nawa na rasa shi lokaci guda a daidai lokaci kuma na fara jin cikina na kugin neman agaji don rabona da naci wani abu tun a gida Nigeria kafin mu taso.
Banci komai da aka aje min ba a ciki jirgin don hankalina ba a kwance yake ba lokacin fin tsorin daya mamaye min zuciyana.
Ki tashi ki watsa ruwa a jikkn ki ki canza wanan kayan mu fita mu leka hjy daga nan mu samu abinda mukaci na fada ina kallon halimatu da har lokacin take kwance.
inane ban dakin ta fada a dan kasalance don har lokacin bata gama warwalewa daga gajiyan datayi a jikinta ba da hannu na nuna mata ta mike ta shiga.
Ajiyan zuciya na sauke tare da mayar da idona ina bin dakin da komai dake cikin sa da kallo ina mamaki a raina.
Yayan mu ban iya kunna ruwan ba don ban taba ganin irin wanan kayan ba muryan halimatu a kofan ban dakin ta dan rufe jikinta da tawul di bandakin dake rataye a ciki.
Mikewa nayi ba tare da nayi magana ba na tura kofan na shiga nuna mata yadda zata kunna ta kashe nayi na fito.
Bakin gado na zauna na hada tagumi ina tunane wanan rayuwan tawa shine rana zafi innuwa kuna don rayuwa rashin incin kai nakeyi a gidan nan yanzu.
Har lokacin da halimatu ta gama shirmenta ta fito daga cikin ban dakin ina zaune ina faman tunane kokarin shafa mai takeyi na dakatar da ita da fadin baki dauro alwala bane kiyi sallolin dake kanki halan ?
Ban tsaya jin amsan taba naci gaba da fadin halimatu kin dai ga rayuwan da muka fuskanta sai kinyi da gaske wurin maida hankali ga ibada a wanan gidan yanzu.
Kina daijin idan innan mu ta bugo waya zancenta garemu shine kada muyi sakaci da ibadan mu kuma mu guji duniya da abinda ke cikin ta ga baki daya.
Kada ki yarda inji ko in gani kina sakarwa wani namiji fuska koda kuwa shi wanda yakawo nan dinne don yanzu mutum ba abin yarda bane.
Don Allah halima kada ki yarda mubawa innan mu kunya a idon duniya kina daida wayau kin kinsan komai don yanzu ido aka zuba mata damu a garin mu.
Nagane yarinyar ta fahinci abinda nake nufi take naga yanayin ta ya canza itama lokaci guda take fadin yayan mu idan nayi wani abinda bai dace ba inna tace kimin fada kadana sake.
Zanyi halima kuma ina kanyi don ban yarda da wa yan nan mutanen ba wallahi don haka ki kara kama kanki da kowa wallahi.
Yanzu kiyi sallah dai mu fita kada ace mun shige daki mun kyale hjy bamu kulata ba tun da muka shiga.
Sallah ta tayar kamar yadda na umurce ta sai bayan ta idar ta shirya muka fito daga dakin gidan tsit kamar babu kowa a cikinsa.
A hankali muke takowa babu kowa dakin su hjy kuma yana kulle don na murda naji shi a rufe na juya ke nan ina shirin fadin dakin a rufe yake naji ana fadi a bayan mu.
Da sauri na juya wanan matar ne da aka kira da julie tsaye a bayan mu tana magana cikin girmamawa a garemu taci gaba da fadin dun tafi asibiti tun sha biyun rana.
Boss yace idan mun tashi a fada muna muci abinci kafin ya dawo gida a cikin harshen turanci take min bayani yadda zan fahinta.
Da taimakon ta har muka je dining din abunci ne gurin a jere ta shiga bude muna tare da muna bayanin shi duk ciki babu abincin da muka sani dan dama dama wani shinkafa da aka dafa da ganye shi nake zaton zamu iya ci daga cikin abincin dake gaban mu din.
Halimatu jan ta raja,a ga wani katon tallatalo da aka bamkareshi sai maiko yakeyi yana daukan ido naji tana fadi a hankali wanan din naman meye yayan mu ?
Ban sani ba halimatu don haka kadama ki sa rai zakici shi don bamu san ko naman halal bane.
Tace amma aishi yaya yana sallah don haka ba zai yarda a ci mushe a gidan sa ba ko ?
Kada ki fara kici wanan nama na fada fuska a daure abincin dana zuba na mika mata taja plate din zuwa gaban ta dagani har ita bamu iya cin wani abin kirki ba don dan danon abincin da mukaji daban danamu na Nageria.
Bamu kai ga tashi wurin cin abuncin ba aka turo kofan duk da muna dan nisa da wurin hakan bai hanani jin lokacin da aka shigo gidan ba.
Shine tafe tare da mama Ramatu sai jamal dake bayan su dauke da jakkar kayan hjy da suka fita dashi .
Da sauri na mike tsaye ina masu sannu da zuwa shida jamal suka amsa min gaidasu danayi mama Ramatu idon ta ta sauka kan abincin dake gaban mu din.
Yauwa jamal mama sai ku zauna kuci abinci zan dan shiga in watsa ruwa a jikina don duk a gajiye nake wanan tsohuwar taku duk ta rudani wallahi.
Ya jikin nata mama na tambaya ina kallon fuskanta jiki da sauki tana asibiti anbarta can suna dubata koda yake ku ai ba damuwa da jikin nata kukayi ba kuna nan kun saka abinci haka a gaba.
Da sauru na dago kai ina kallon mama Ramatu din don jin abinda ta fada haba mama idan basuci abinci ba zamu taru a hakane a rasa wanda zai kama wani a cikin mu.
Jamal ai gaskiya na fada kana sane dai hjy tanace sai azo da zainab kasan nan anzo din kuma har ta fara manta abinda ya kawo ta nan yanzu.
Amma mama sai nake ganin itama mutumce kamar kowa dole tana bukatan hutu tare da ita don me kuma yanzu za a kawo wanan magana koke da kika tafi ai cewa akayi ki dawo basu bukatan kowa a can.
Ni dai jikina ya mutu ina tsaye ko kwakwaran motsi ban iya ba don cin fuskan da nake fuskanta a wurin sarakuwan nawa ina tunanen na rabu da mami ashe kuma ga wata tare damu yanzu.
Juyawa nayi na fara tafiya don zuwa dakin mu naji halimatu ma ta biyoni a bbaya gado na fada ina sake kuka lokaci guda.
Yayan mu ki daina masu kuka haka shi yasa suke jin dadin maki abinda sukaga dama ko yaushe dan Allah kiyi shiru ki kyalesu yaya.
Halimatu cin abinci laifi ne kuma yanzu shike nan yanzu mu bamu da yancin yin komai a gidan nan don kawai mu din iyayyen mu suna tallakawa kome halimatu ?
Kyalesu yayan mu muma ai watarana zamuyi kudi mu rama abinda suke muna tunda suma badashi aka haifesu ba ai.
Zancen halimatu ya dan sakani dariyan yake a cikin kuka har nace kai halimatu kedai yarinya ce yaushe zamu arziki irin nasu a duniyan nan mu da gidan mu ko akuya bamu da balle shanu.
To aini ina tara kudin da nake samu tun zuwana wurin ku sunanan idan mun koma gida sai inba inna tasai abin kiwo dashi ko karamane ta sake.
Halimatu amma dai ke din nan da sheg, , , , ban karasa ba aka turo kofan dakin wanda ke rufe da sauri muka juya don ganin waye mai shigo muna indai ba mama Ramatu bace ta biyomu har daki tazo tayi muna wani cin mutuncin na fada a cikin zuciyana.
Ya jafar ne ya shigo yayi wanka ya sauya kayan jikin shi zuwa na mazan kasan maleshia mai zubi irin na indiyawa a jikin shi sai kamshi ke tashi jikin shi sosai.
Da murmushi dauke a fuskanshi ya karaso yana fadin halimatu bataci abincin ba kema baki ci ba donta tashi kada ki damu da rashin cin abincin ta damuwa ta saka a zuciyar ta ita.
Keko kinga idan kina wasa da cin abinci mama zasuce ban rike amanan dana dauko naki ba idan kin koma gida akaga kin rame sosai.
Zan dinga ci ta fada sai kuma tace saidai abincin ne baya da dadi a bakin mu naso kuma in dan dibi naman nan naci sai yayan mu ta hanani ci wai don ba a san ko naman meye ba.
Zainab kika hanata cin abincin ko me ya fada a dan hasale yana kallon fuskana a cikin mamaki yaci gaba da fadin ko kina zargin naman ne ko wani abu.
A hankali na girgiza mai kai ina fadi da kyat naga munyi kankanta da mu fara cin abinci hakana manya basu fara ba .
Halimatu tace kuma yayan mu kaji abinda wanan maman ta fada dazu bayan ka shige daki wai bamu saba ganin abinci haka ba munzo mun zauna munaci bamu damu da ciwon hjy ba.
Da sauri ya dago yana kallona tare da fadin wace mama kardai nace mama Ramatu ne tayi wanan maganan mara dadin ji gareku ya tsatsareni da ido yana kallona ranshi a bace.
Ganin nayi shiru na dukar da kaina kasa sai hawayen dana fara fitarwa daga idanuna yasa shi fita daga dakin da sauri ya barmu muna binshi da idanu.
Halimatu zaki ja min wani tsana a gidan nan kuma wurin mama yanzu don mami zata kira tace ga abinda nayi mata yanzu kuma shiyasa duk abinda akai min bana yarda ya sani ko yaji don gudun irin hakan.
Bansan ya sukayi ba dai can da dare shi da kanshi yazo ya kiramu har dakin wai mu fito muci abincin zance mai a koshe muke sai dai yanayin fuskanshi bai barni na fadi hakan ba.
Bayan fitan shi daga daki na kalli halimatu ina fadin tashi kije kuci bana jin cin komai a yanzu kuma na koshi dana dazun.
Haka ta fita kamar bata so jin abindana fada ba can sai gashi dakin yana fadin ki taso muci abinci na fada ko bakiji bane a cikin umurni yana tsareni da idanun shi manya masu ban tsoro.
Da sauri na aje littafin dana dauko ina karatu na nufo inda yake saida yaga fitana daga dakin kafin ya biyo bayana naji yace min dakata a nan.
Da sauri naja na tsaya ya karaso inda nake hannayen shi ya raba yasani a tsakiya yana bina da idanuwan shi.
Da sauri nayi kasa da kaina don irin kallon da yake min din ki saurareni da kyau kiji me zan fada maki kuma ki kiyayye.
A duk lokacin da muke tare dasu mama ko wani na gida dole ki nuna masu cewa ni di mijin kine kuma kina kula dani kina bani hakkina na miji ki a gaban kowa.
Da sauri na dago kai yace yes kin san dai abinda nake nufi da hakan ba sai na tsaya maki gwarigwariba kan hakan.
Don ban son wani ya zargi wani abu a tsakanin mu zamu zauna a daki daya yanzu har zuwa lokacin da zaku bar kasan nan ku koma Nigeria tare dasu.
Don zaman ku a nan zai iya takurawa rayuwana da sauran aiyukana amma for now zaki nunawa kowa cewa kina kula da hakkina nima hakan zanyi kokari in nuna masu a fili.
Understood ya fada yana kara tsareni da idanuwan shi sosai cikin warning dina ga abinda ya fada din da sauri na gyada mashi kaina don dai kawai ya jaye jikin shi a kaina lokacin.
Jikina sai wani irin rawa yake min don tsoro banji ya daga gurin ba kamar yadda nayi tsamani sai can naji ya sauke ajiyan zuciya ya ya jaye jikin shi a hankali.
Nima jin hakan yasa na bude idanuwana da suke min a rufe na sauke a bayan shi don har ya fara tafiya a lokacin cikin wani irin yanayi sai kuma naga yaja ya tsaya nima tsayawa nayi dan nisa kadan dashi.
Zoki rike hannuna a haka zamu karasa wurin su ya fada ba tare da ya juyo ya kalli inda nake ba yake magana.
A hankali na tako zuwa inda yake hannu shi daya miko mi har lokacin bai kalli inda nake ba na rike tare da dan runtse idanuwana ina jin wani zafi a raina naji ya fara takawa dani kara matso dani yayi a cikin jikin shi sosai a haka muka karasa wurin daning din.
Suna zaune su uku halimatu mama Ramatu da ya jamal duk suka dago kai suna kallon mu kafin shi ya jamal din ya sauke kanshi daga kallon mu yana murmushi a fuskanshi na gani mu tafe haka a gaban su.
Don shi ya gama fahintar komai a game da dan uwan shi din don yayi sancin sosai ya ga me yake ciki a rayuwan shi ko kokarin boye masu hakan kawai yake yi yanzu.
Muna zama yake fadin amarya da angone waya fada maki ana fushi da cin abinci zainab ai kinga angon ki yaje ya rarashe ki kada ki ja mashi wani matsala kuma ana fama dana hjy.
Zata iya yin fushi jamal tunda abincin da aka dafa don ta ana mata gori a kansa gidan nan nikuma ita nace a girkawa .
Murmushi yake mama Ramatu tayi kafin tace fadin gaskiyan da nayi dazun shine fushinta a yanzu don kawai na fadi gaskiya .
Mama bazan so wanan halinba gun iyalina gaskiya ban kawo kowa a nan dan ya takurawa wani ba ina hjy da bakinta tace a barsu su huta mu tafi dazun irin hakan bai kawo girma gun babba.
Yana magana yana kokarin zuba abincin daya bude tare da turo min plate din abincin daya diba a gabana tare da dan kashe murya yana fadin ci koda kadan ne don Allah.
Ni wanan draman na mutumin nan dame yayi min kama hakane idan yana abu sai ka rantse da Allah da gaske yake abinsa bazaka dauka hakan shiri bane yake a gaban mutane.
A haka cikin kulawa ya samu har na danci abincin zaikai cibi biyar ita kuma mama Ramatu har ta kare cin abincin bata sake yin magana ba saida zata mike ne take fadin ke sai kizo mu kwana a dakina tare dake .
Tunda ita a daki mijin ta zata kwana da sauri ya dago yana kallonta don jin abinda ta fada sai kuma ya wasance da fadin hakan ma yana da kyau zaku iya kwana a taren idan yin hakan ba a takura maki ba mama ?
Ba komai ainina bukacin yin hakan kada a barta a daki ita kadai ta juya wurin da halimatu ke zaune tana fadin idan kin gama saiki sameni a dakin mu ina kinsan dakin dai.
Zan rakota ya fada batare daya dago kaiya kalli inda maman take tsaye ba sai cewa mama tayi ina jiranta don dakin yai mi girma na kwana ni kadai a cikin sa.
Kaina yana duke a kasa zaka dauka kunyar maganan mama nake ji yasa ban dago kaina ba a lokacin.
Mama juyawa don ta tafiya dakinta yayi daidai da shigowan mutum biyo a gurin banyi saurin dago kaina ba don ganin ko suwaye suka shigo lokacin.
Saida jikina ya ban ana kallona na dan dago kai a daidai lokacin da mukai arba da taju tsaye ya dan duka a bayan ya jafar din suna magana saidai idon shi a kaina yake.
Gabana na ya fadi lokaci guda a take na tuna da kalman shahada na dinga jerosu har uku lokaci guda kafin inji dan natsuwa ya sauka min lokaci guda.
Sun gama magana yana kokari barin wurin da sauri naji ya jafar din na fadin kun gaisa da madam da tazo .
Juyowa yayi ba tare daya bashi amsa ba yana fadin anzo lafiya ya hanya lafiya kawai na bashi amsa dashi ina kawar da kaina daga kallon inda yake tsaye.
Barin su wurin yayi daidai da mikwan ya jafar din yana fadin yana zuwa suka fita tare dasu lokaci guda.
Sai lokacin na sauke wani irin ajiyan zuciya dana baiyana shi a fili wanda ke nuna nayi zurin tunane a lokacin.
Ki yi hakuri zainanb kici gaba da masa addu,a da sannu komai zai daidaita a tsakanin ku nasan ki da yawan ibada a baya ko yanzu ki dage da adduan don ba wanda yai tunanen hakan ma zai iya faruwa ga wanda yasan mijin ki ko waye.
Saukin abin bai yarda kowa ya takaki yadda yaga dama ba don yana tsaye a kanki akoda yaushe.
Dago ido nayi na kalli ya jamal din dake magana yace kwarai duk abindake faruwa a tsakanin ku na sani zainab shima yasan nasan komai akai.
Ki kara daurewa muci gaba dayi masa addua wanan shine jerabawan da Allah ya sako mai a rayuwan sa shikuma .
Ba zanso inyi magana mai zurfi dake ba a yanzu nan gaba zamuyi maganan idan muka samu lokaci irin haka kedai ki kara hakkuri har zuwa lokacin da gaskiya zatayi halinta.
Idona da suka ciko da hawaye lokaci guda na daga ina fdin nagode ya jamal ba komai ya fada yana mikewa daga gurin don zuwa dakin shi.
Kallom gurin da halimatu take zaune nayi itama ni take kallo don bata fahinci me maganan namu ke nufi da ya jafar din ba.
Nace idan kin gama saiki tashi mu tafi ki shirya zuwa dakin mama din kada taga kin dade bakije ba tare muka mike zuwa dakin mu.
Tana shiri kwanciya naji ta jefo min tambaya yayan nikan sai banga wani abinda har suke ganin laifin ya jarar akanki ba kowa ya tashi magana sai yace kiyi hakkuri dashi.
Baida laifi halimatu sune kadai suke ganin hakan don kawai baida lokacin tsayawa tare damu koda yaushe na bata amsa da hakan.
Kema kuma ina son ki kama bakinki idan kije kwanciya dakin mama duk abinda ta tambaye ki koba yau ba ki fada mata baki sani ba.
Kai kawai ta gyada min alaman taji tana min saida safe har kofan na rakata na dawo dakin nayi shirin kwanciya tare da tunane kala kala a raina.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[13/02, 21:24] +234 706 064 0038: 🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
5️⃣9️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAR UWA LITTAFIN KUDINE KI BIYA KI KARANTA DARI UKUNE KUDINSA DON ALLAH DON SON ANNABI KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA DON ALLAH.
Dakin na mayar na rufe kafin in koma in kwanta a takure a wuri daya saman gadon ba mama Ramatu kadai ke tsoron wanan gidan ba harni kaina tsoro gidan ke bani don girman shi.
Wanda zuwa yanzu ban gama tantace cewa gidan ko mutum nawa ke cikinsa ba komai kan yaji na alatu saidai gareni hakan duk raggagene a idona.
Don a yanzu dai na fara fahintar akwai wani boyayyen al,amari da ya jafar din yake boyewa mutane wanda kuma dan uwan shi yasan da wanan zancen a yadda yai min magana dazun kafin mu shigo daki.
Koma meye ina rokon Allah ya kara tsareni daga fadawa cikin halakan shi don ni zuciyana yafi tsaya min da shan jini kila yakeyi.
Idan ba haka ba ta yaya mai shekaru kamar ya jafar zai tara wanan arziki haka a duniyan nan .
Mutum nawa yazo ya sama a duniya suna neman kudi fiye dashi basu tara hakan ba wani irin tsorone ya lulubeni lokaci guda ni kadai a dakin.
Can barci barawo ya fara fisgana naji kamar ana dukan kofan dakin da nake ciki a dan firgice na bude idona na saurara da kyau.
Kofan ne ake kwankwasawa ba karya kunne ke min ba saida aka kwankwasa kusan sau uku na mike tsaye a cikin kyarman jiki nakai kofan tare da tambayan waye ?
Ki bude kofa kin tsaya kina tambaya a ciki rawan jiki nakai hannu na bude kofan daga ciki shine a tsaye yana saye da kayan barci a jikin shi yana kare min wani irin kallo da bansan na maye ba.
Bayan sa nabi da kallo kamar ina tunanen zanga wani tare dashi ya taka zuwa cikin dakin yana fadin da a haka kika kwanta ba tare da kashe wuta ba ?
Kasa nayi da kaina ina wasa da yan yatsun hannuna da nakejin kamar suna taimaka min wurin kare kaina daga abin sherin daya zo min a lokacin don zuciyana ta fara zargin sako.
Kizo ki zauna magana zamuyi dake da fatan zaki fahince ni ya fada yana mai bina da kallo inda nake tsaye.
A rude na kai kasa ina fadin don son da kakewa manzo ya jafar kada ka cutar dani kamar yadda kaiwa iyayyena alkawari hakan kafin ka daukoni daga gidan mu.
Yarda da amicewa yasa suka bakani da kuma girman mami da suke gani ga idon su don Allah kayi hakkuri bazan kara ba .
Zaune yayi sororo da mamaki yake kare min kallo tare da sauraren abinda nake fada mashi din a cikin tsoro.
Cikin karfin hali ya iya furta zainab wai meke damuwan kine haka naga a tsorace kike dani tunda muka sauka garin nan .
Ko kema kin fara daukan zancen mutanen me a kaina yanzu ki zo ki zauna magana nazo muyi dake don Allah ban kuma son ganin wanan hawayen da kike zubarwa tun safe a gidan nan yanzu.
Jin abinda ya fada yasa na dago ido na kalli fuskan shi babu wasa a cikinsa ko kadan a lokacin yasa na dan tako zuwa bakin gadon nakai kasa zaune.
Kai kawai ya girgiza tare da bina da wani irin kallo kafin yace ki saurareni da kyau kiji abinda zan fada maki yanzu.
Kindai san bamu kadai bane a wanan gidan yanzu akwai mama da jamal sai kuma hjy dake asibiti kafin ta dawo gidan nan ko ?
Daga inda nake zaune na gyada mashi kai a hankaki yace good abinda nake so dake shine yanzu kin daiji maganan da mama Ramatu tayi dazun wurin cin abinci ?
Kai na sake dagowa na kalleshi gabana sai faduwa yake lokaci guda don bansan abinda zai fada ba kan maganan mama din.
Yace kokin manta da abinda ta fada na a matsayin ma,aurata muke don haka a daki daya zamu zauna dake right ?
Na gyada mai kai a tsorace alaman eh nagane yace toh don haka zan baki zabi duk wanda yafi maki sauki zaki dauka a ciki.
Na farko zaki dinga zuwa dakina da sunan kwana a can dan kaucewa idanun mama tunda ta fara wanan maganan ina zargin ko mamine ta sakata saka muna ido a gidan mu.
Sai zabi na biyu ko ki bar kofan ki a bude zan dinga shigowa karfe hudu na asuba yadda zata dauka a nan gurin ki na kwana tare dake .
Ido na sake zubo mashi lokaci guda don jin abinda ya fada din ya gane me nake nufi sai naji yace indon ni ki saki ranki don mata basu a gabana ko kadan .
Do bantaba daga ido na kalli wata mace da sunan sha,awa ba a rayuwana saidai inwa mace kallon dayan biyu shine ko in kalleta a matsayin yar uwa a gareni ko kuma abokiya kawai ni haka rayuwana yake.
Don haka zuwanki dakina bashi zaisa wani abu ya kasance a tsakanin muba dake zuwa kawai zakiyi don kaucewa idon mama da sauran mutane.
Ajiyan zuciya na sauke lokaci guda ta yadda har yake iya jiyo sautina daga inda yake zaune baki ya mere min tare da fadin wani kika zaba yanzu.
Na amince na bar kofana a bude ya tareni da fadin baki gudun mama ta gane wanan din plain ne muka shirya hakan dake ?
Sai nayi shiru kaina a kasa don haka ni zabina shine ki je can part dina zaifi min kwanciyan hankali don ba daki daya bane a gun saiki zauna a cikin guda hakan yayi maki ko ya kika gani.
Yayi min na fada ina maidana sanin zuwa wanan tafiyan da hjy ta saka ayi dani ina zaune kalau a gida a cikin kwanciyan hankaklina.
Ya mike tsaye a daidai lokacin tare da fadin sai ki tashi mu tafi part dina a yanzu saidai ban son sa ido ga duk abinda zajiji ko ki gani a can din wanan ba hurumin ki bane kinji.
Ya fara tafiya ni kuma na kasa tashi don jin irin dokokin daya tsara min wanda nasan suna da wuya in iya ketare su duk lokaci guda.
Jin ba motsa daga inda nake ba har yakai kofa ya jiyo gareni yana fadin ki tashi mana kinyi zaune ko baki fahinci abinda na fada bane yanzu ?
Da sauri na mike na dauki hijjab dina da zanyi sallah dashi nabi bayan sa kofan ya rufe da kansa muka nufi part din nasa.
Tsaruwa iyaka ke nan dan an narka dukiya wurin hada part din kamar wani aljannan duniya wani daki ya bude min muka shiga yake fadin nan yayi maki ?
Kai kawai na gyada don a tsorace nake da za ai min ihu koda kadan ne zan iya sake fitsari ko in ruga da guda a yadda nake tsorace.
Zaki iya yin komai iyaka dakin nan daga haka ban yarda ki leka ko ina ba idan kin shigo dan dama da rana kina da right din shiga ko ina na part din nan daga haka ya fita naja wani irin ajiyan zuciya tare da bin ko ina na dakin da kallo.
Na gano inda bandaki yake na shiga na dauro alwala don in gabatar da sallah saboda barci ba nawa bane kuma yanzu ya zama dole in kai kukana a wurin Allah maji rokon bayin sa.
Ban yarda na gusa daga kofa ba nan a kasa barci ya kwashe ni a gurin da nayi sallah tare da jera kirari gun ubangiji mahalicci ina mika rokona garesa.
Rashin barcin da ban samu da wuriba yasa har na makara ga sallah asuba sai da rana ya haskani ta window dakin na tashi ina sallati na nufi ban dakin da sauri.
Ban fito ba saida na gabatar da sallah a kofa mukai kicibis dashi a cikin shirin sa naja baya ina gaida shi da kwana ya amsa min a dake kamar bashi ba kuma.
Dakina na nufa sai dana kusa na tuna da dan makullin dana aje a dakin don haka na nufo don na dauko a kofan muka hade da taju dake fitowa shima a cikin shirin shi.
Ban ko tsaya gaida shi ba na wuce dakin ya bini da wani iri kallo nidai na shige na dauko key din na fito na bude dakina na shiga.
Zuciyana fam da tunanen me kuma ya kawo taju part din sa tunda safe haka ban tsaya ba na fada ban daki nayi wanka na fito na shirya a cikin wani dogon riga baka ta mutanen kasan Egypt mai hannu shara shara rigan barci ne fam a idanuna don haka na kwanta don in rage nauyin da idona yayi min na rashin samun barci.
Barci sosai ya daukeni lokaci guda saida zasu karyane ya leka dakin nawa ya sameni ina rankon barcin da ban samu nayi ba da daren.
Baiso ya tashini ba saidai don asibitin da zamu gurin hjy dole yasa ya tayar dani din ta hanyar dan bubuga nin da yayi na falka dan razane.
Ki tashi ki karya zan kaiku ku duba jikin hjy ne yanzu ya fada har lokacin babu walwala a tare dashi ban tsaya bin ta nasa ba na shiga bandaki na kewaya na fito na samesu a dining zaune nima na zauna tare da gaidasu da kwana.
Kai kekan ai garin nan yayi maki barci haka kamar mai sabon ciki kodai dan nawa ya aje kwansa ne bamu sani ba.
Fuskana na daure don na fahinci me maganan ta yake nufi don haka ko idona ban dago na kalli wurin da take zaune ba.
Har lokacin da muka gama aka fito zuwa asibitin wanan karon bashi ke jan mu ba don yace akwai inda zai tafi zai samemu a can asibitin.
Mun samu hjy tana barci saidai bamu dade a dakin ba ta falka daga barcin muka shiga yi mata sannu da jiki tana amsa muna a hankali.
Ya Jamal ne yake fadin ko yazo yaja mata kafan da aka daureshi da wasu karafuna tace tunda kafi dan uwanka rashin tausayi.
Shida ya kawoni nan ban ganin kowa ko sallah asuba yanzun haka ban samu yinsa ba na rasa yadda zan masu bayanin ina son inyi sallah tun dazun.
Har muna hada baki wurin kiran subbahanallahi nida mama Ramatu mama tana fadin ashe bayi ke nan idan ba ibada shi bai fada masu idan lokacin ibada yayi su taimaka maki kiyi ibadan ki ba.
To ina nasani yar nan ni wanan abin ai ya koma min ciki yanzy kan ace mairai ba zaiyi ibadan sa ba yana kwance haka sharkaf.
Fita ya jamal yayi sai gashi sun shigo tare da likita yana masa bayanin ba za a bar ruwa ya taba kafan nata ba sai bayan kwana uku don hakane ma ake mata wanka a kwance.
Nan dai ya dan kara bayan nan shi ya fita ina zaune nayi tagumi can na nisa nake fadinb hjy ko za a kawo maki dutse kiyi niyar taimama akan sa.
Haka za a yi yar albarka kinga abinda yafi ke nan gareni yanzu ya jamal ya fita ya dan dade kafin ya dawo dauke da wani dan dutse a hannun shi karba nayi na shiga ban daki na sanke shi da kyau na fito dashi .
A natse tayi komai kamar yadda sharia,a ya fada har sallah a kwance tayi don nasan hankalinta ba zai taba kwanciya ba idan ba sallah ta samu tayi ba.
Mun dade a wurin hjy har karfe dayan rana kafin yaya din yazo tare da wanan bindin nasa yana biye dashi a bayan shi kamar jelan shi.
Ni yanzu yakai ma bana son sam naga wanan mutumin don haka kawai nakejin na tsaneshi a cikkn rayuwana na kula bani kadai na tsani wanan mutumin ba har ya jamal ma ya tsanesa sosai don ban taba ganin lokacin da suka gaisa dashi ba
Bayan tambayan jikinda yayi ne yake dan duba jikin nata musaman kafanta dake daure da karfe yace ya kike jin jikin ta dan dago tana fadin da sauki sosai saidai sallah da bata samun yine a nan.
Yanzuma sai zuwan mu ta samu tayi sallah ga shawaran dana bayar tana dan saka min albarka tare da fadin kaikan jafari kayi dacen mata wallahi tafi matar mamud sau dubu a gurina.
A gurinki kikace hjy shima ko mamud matar shi tafi mai kowa shima a wurin sa kai rabu dasu ka kara rike matar ka kaji wa yan nan suma a sannu zasu gane abinda nake nufi watarana.
Mama zaku tafi gida ku huta ko ya jafar ta fada kamar yana son a kawar da zancen zamu tafi kan ko don mu samu muyi sallah muci abinci.
Sai kuzo a mayar daku gida yanzu dan ni office zan koma daga nan ba gida nayi ba yanzu ina da aiki da zanyi sai dare sosai zan dawo gidan.
A tare muka fito dashi sai da ya dan tsaya da kaninsa sukai magana lokacin har mun kai bakin mota muna jiran a bude muna .
Kafin su tako zuwa inda muke tsayen har lokacin ban yarda na daga idona na kalleshi ba don tsoro shi dana fara ji a yanzu.
Cikin basarwa yace zainab lafiya ko kike ko dai ganin hjy a hakane yasa na ganki wani iri dake yau ?
Wanan haka take bata da sabo kullun a cikin jan jiki takewa mutane dan bambamcin su kadanne da matar mamud don ita din akwai girmama na gabanta gaskiya.
Karasowa yayi inda nake tare da dan dago habana yana fadin ki kula da kanki don Allah wanan shirun yayi yawa sosai.
Ya fada yana dan buga min kafadana a cikin wasa dan dariyan yake na sake mai na bishi a yadda yake so muyi gaban mutane da wasan basajan nasa.
Kamar ance in dago ido daga wurin motar shi taju ne ya kura muna ido kamar maye yana kallo abinda ke faruwa a tsakanin mu.
Wani kallo tsana na watsa mai yayi saurin kawar da kanshi gefe daya a raina nake fadin sai nayiwa wanan mutumin tsiya zai rabu dani da wanan kallon nasa na maita.
Saida muka wuce kafin su biyo bayan mu idona naga window mota idan ba idona yai min gizo ba zan iya cewa kamar na gansu suna kiss a cikin motan saidai bazan tabbatar da hakan.
Kuma ni san ban kawo komai a raina cewa wani abinda bai dace ba sukeyi a tsakanin su don ban zaci hakan ba ga ya jafar din gaskiya.
Innalillahi danaji ya jamal ya fada ya dawo dani ga dan tunanen da nakeyi a lokacin ne kuma naji mama daga gefena tana fadin kai jamal lafiya kake wanan tsabihin haka ?
No mama babu komai ya fada yana dafe kanshi a cikin takaici mama ta kara fadin ko mantuwa kayi a asibitin mu koma ?
Babu komai mama wani abu dai nagani ya daga min hankali kin dan kasan nan ba na musulmai bane tace nima haka nake gani ai kamar ma matan su a tsirara suke waisu wayewa.
A gidan ma bayan munyi sallah mun fito cin abinci kasa fitowa ya jamal din yayi a lokacin saida kyat mama ta samu ya fito.
Ina kula dashi bai wani cin abincin ba sai tasa shi gaba dayayi yana faman tunane shi kadai bayan kwana biyu da haka ina cikin dakin nan da nake kwana kamar wata manya a gidan.
Nake dan jiyo hayaniyan su daga falin dake tsakanina dasu wurin kofa na koma ina saurare wanan karon hausa naji anayi don haka na saurara dakyau ko zanci.
Wallahi wallahi kaji tsoron Allah ka guji ranan haduwan ka da Allah ya J ka dauka idan kayiwa mutane wayau zakaiwa Allah wayau ne ?
Ina zaka da alhakin wanan yarinyar da kake cutarwa a rayuwan ka ai gara ka saketa ka zauna kaita aikata sabon Allah ka zaifi ma sauki.
Jamal ni kake fadawa magana haka kai tsaye me kake tunanen ka taka a yanzu naji jamal din na fadin Allah .
Niko ya mamud ya sake hanyar Allah zan fada mashi gaskiya a yanzu balle kai da muke da shakuwa dakai ina zaka kai Alhakin iyayyen mu a kanka ga irin tarbiyan da suka bamu a baya.
Kudi ko ilimi ba hauka bane bazan fadawa kowa wanan abin ba zan dai tayaka addua idan kana da rabo a wurin Allah Allah yasa ka daina wanan harkan daga haka naji ya fita ya gaura kofan falon yafice daga part din.
Da sauri na koma saman gado na dafe bakina don kada sautin hawayena a fito fili sai can naji kamar ana taba kofan dakin Allah yasa ban yarda in kwanta ban sakawa kofan key ba har mai tabawan ya gaji ya daina tabawa.
Washe gari har na fito kamar mai sanda a falo na samu ya jamal a zaune yayi tagumi jin motsin fitowan yasa shi dago kai ya kalli kofan da yaji an taba din.
Mukai arba dashi a dan rikicewa nayi sai naga ya kawar da kanshi daga kallo hakan ya bani daman shigewa dakina dana bude hannuna na rawa kai tsaye na fada ciki.
Sauke numfashi nayi a hankali kamar wata barauniya da aka kama a lokacin nikan na shiga uku na fada a fili .
Ban yarda na fito ba sai wani lokaci dana kwatanci ya jafar ya bar gidan a lokacin na fito na rame sosai don damuwa da nake ciki a yan kwanaki nayi wani irin fari sosai saidan wuyan dan aje.
Yunwa ya fito dani babu kowa a falon duk da nayi mamakin rashin ganin halimatu yau da banyi ba wurin dining na nufa na hada ruwan shayi babu madara don bakina da nake jin shi babu dadi a ranan kamar na kwanta ciwo da dadewa.
Babu abinda nake tunane tun daren ranan sai kakamin ya jamal din ga dan uwan shi ina kuma tambayan kaina wani abune yaya jafar yakeyi boyayye da ba wanda yasan wanan abin.
Kisha tea din kada yai sanyi mana kin zauna kina tunane ke kadai a nan da sauri na dago idanu ina saukewa a kanshi.
A cikin daurewa nake gaidashi da ya jamal ina kwana saida ya zauna yake amsa min da lafiya zainab ya kika tashi ya bakunta kuma lafiya na fada ina dukar da kai kasa.
Zainab kisha kada tean yayi sanyi ya kara fadan hakan gareni da sauri kamar mai jiran umurnin shi na dauki cup din na fara kurba a hankali.
Mama Ramatu ne ta fito daki tana dan dariya halimatu na bayan ta tana fadin wanan yar akwaiki da wayau tsiya wallahi.
Dago kai mukayi muna kallon su har suka karasu inda muke na aje cup din hannuna a hankali tare da zamewa saman kujera ina gaida ita kamar yadda na saba a kullun.
Ta amsa min a cikin fara, a kafin tace dani lafiya kike kuwa yau naga kin rame lokaci guda haka ko wani abinne ya sameki kuma anya kuwa zainab ba shigan ciki ke gareki ba ?
Da sauri ya jamal ya dan kalleni sai kuma ya kawar da kanshi daga kallona sai naji na tsargu da wanan maganan bandai yi magana ba ina zaune na tasa kofin shayina a gaba ina dan wasa da bakin kofin a hankali.
Takon shine ya mayar da hankalinsu ga kofan part din shi yana saye a cikin kananin kaya da suka fitar mai da suran jikin shi har kurciyar shi ya kara baiyana a fili zakace ko dan shekara ashirin zuwa samane a lokacin.
Ya iso gurin tare da fadin mama an tashi lafiya cikin girmamawa a gareta ta amsa mai da fara,a tana fadin yanzu nake zance da matar ka kodai rabo ya shigane bamu sani ba gata sai faman rama takeyi haka a tsaye.
Da wani irin mamaki yace ciki a dan zabure sai kuma ya mike tsaye yana kallona a cikin mamaki yake fadin mama ciki ga zainab din ?
Kana mamakin hakan ne ga macen aure yanzu fa shekara da kusan rabi da aurenku meye abin wani mamakin hakan a nan Allah ya ingatar kawai musha buki wanda ka hanamuyi da aure sai muyi shi a sunan baby.
Kai mama bata dai da lafiya ne tace yanzu take fada min da dan zazzabi ta kwana jiya nace kila gajiyan tafiyane yaja mata hakan.
Amma kuna da abin dariya wallahi wai me kuke mamaki a hakanne gun matar aure har zaku tsaya wani zance ko baka shiryawa haihuwan bane a yanzu kana dabi,an ku na turawa.
Gyara zama yayi yana fadin kai haba mama har guda nawa wanan yarinyar take da zata haihu a yanzu at list dai ta kara yan shekaru nan gaba kafin ta haihu.
A naka tsarin kenan amma aishi Allah ba ai masa dabara idan ya tashi nuna ikon sa akan bawan sa ina cikin ne aimu muna maraba dashi.
Mikewa ya jamal yayi yana fadin zan fita daga can zan leka wurin hjy in dubata duk da yau nasan basa bari a shiga da safe.
Ba zaka jira yayan ka ku tafi tare ba ko akwai motan da zaka shiga ne a wajen yace zan shiga taxi daga nan ai ba nisa da gidan nan.
Barshi ya tafi mama ya jafar ya fada ba tare daya dago kai ya kalli kowa ba a wurin yaci gaba da hada tea din shi da yakeyi.
Wai ko lafiya kake da dan uwan ka kuwa mama ta tambaya tana kalon shi yakecewa lafiya mama me kika gani ?
🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
6️⃣0️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
LITTAFIN KUDINE DAN DARAJAN ALLAH KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA SHI HAKKI BAIDA KADAN MUSULMIN KWARAI KE GANE HAKA, , , ,
Kwana biyu na rasa gane mai ke tsakanin su yaya dan ko yaro yasan akwai matsala a tsakanin su don ya jamal idan ya fita baya dawowa gidan sai dare.
Daya shigo kuma ba,a sake ganin shi sai wata safiyan ko ance ya tsaya ya karya zaice yana sauri ne kada hjy taga ya dade zai karya idan ya isa asibitin.
Ashe mama Ramatu ta fahinci hakan a tsakanin sai gashi ta kasa hakkuri muna zaune muna karyawa bayan fitan ya jamal bada dadewa ba tana tambayana .
Zainab niko sai naga kamar yaran nan akwai abinda ya faru a tsakanin su kwanan don gaskiya ba haka na saba ganin su mussanman ma shi jamal da jafar akwai shakuwa na sosai a tsakanin su.
Kofin dake hannuna ina dan kurban ruwan shayi na aje tare da fadin mama nima na kula da hakan saidai ban tsamani abin yayi nisa haka sosai ba a tsakanin su.
Gaskiya suna da matsala don shi jafar baya ko zancen kanin nasa idan ya fito bai ganshi ba da safe idan da dane da mukazo baya karyawa sai ya nemi dan uwansa sun zauna tare.
Ke mijin ki bai fada maki abinda ke faruwa bane tsakanin su da sauri na girgiza kai ina fadin ba muyi wanan zancen dashi ba gaskiya.
Tsuki tayi tare da fadin ina zakuyi wanan maganan don ko yaushe fuskan shi a daure idan bashi yaga daman yin raha don kansa ba.
Zanwa jamal magana idan ban fahinci komai ba zan fadawa hjy ko zata san maike faruwa a tsakanin su haka.
Nidai ban kara tofa komai ba naci gaba da kurban tea din dake hannuna a hankali har nakai rabin kofin na aje.
Yau ma banga shi jafar din ba ko sakkon fita yayi ne don kwanakin nan naga da wuri yake fita sai dare kuma yake dawowa wani lokacin ma bamu haduwa.
Ina ganin kamar ya fita tun dazun don yace yau yana da meetinga office na shara mata karya ina Allah Allah kada kuma ya fito ta gane karya nayi mata ashe.
Sai Allah ya taimakeni ashe ya fita din don na sara a gaba gashi ranan bamu zuwa asibiti duba hjy don tana bukatan hutu don alluran da akai mata tana son dan hutu ya sa sukai muna gargadi da hakan.
Don haka bayan karyawan mu a falo muka zauna da mama ana dan hira da kallo wanda kusan hiran na mutanen kasan da muke muke zancen irin shigan su da yadda suke magana kuma a cikin sauri.
Can mama ta fara jefo min zance kan zaman mu da yaya sai na rasa amsan da zan bata lokaci guda don haka kawai na dan daure fuskana ina dariyan yake.
Amsan da ban bata ke nan din na gane nugun cikina take son tayi taji wani abu a dangane da zaman mu ko shi kanshi yaya din .
Ganin naki bata amsa yasa ta kawar da zancen da fadin ai ban tsamani hjy zata barku ku koma a tare damu ba don naji taja fada tun kafin tafiyan nan wai ya kamata ace kin biyoshi nan kema, sai ku zauna tare a nan.
Amma mama ni nafi son in zauna Nigeria don nan din babu wanda na sani babu dadin zama a kasan nan ga baki daya wallahi.
Budan bakin halimatu dake kallo kamar tana jin yaren su sai cewa tayi amma dai anty aida mu zauna nan din tunda mijin kima yana nan ai inna fa tace kada ki yarda mijin ki yayi nisa dake.
Da sauri na kalli halimatu din ita kanta tasan irin hararan da nayi mata sai ta koma ta kwanta da sauri saman kujeran da take kwance da farko daga haka bata kara jefa muna baki a zancen mu ba .
Barci ne ya dauki mama don haka hiran namu ya tsaya a nan ina zaune sai faman tunanen maganan da mama ta fada min na rashin jittuwa a tsakan yan uwa biyu da basayi a yanzu.
Tunane nake ko a sanadiyana suke wanan fitinan indai hakane kuwa zan tun kari ya jamal da yadaina damuwa da zancen mu don nima hakan yayi min daidai wallahi don ni har yanzu tsoron ya jafar din nakeyi da ganin girman shi akoda yaushe.
Da wanan tunanen har lokacin sallah yayi na tayar da mama do muje muyi sallah kads mu shagala don a rayuwana bana yarda inyi wasa da lokacin sallah ko kadan.
A gurin dana sallame sallah nayi zaune ina ci gaba da tunane a raina na yadda zan tunkari ya jamal din karshe dai na daure dole in hakan garesu a yanzu kada hakan ya kawo masu matsala.
Ban fito ba sai bayan da nayi sallah la,asar koshi na fito ne don halimatu da har lokacin banga ta shigo dakin ba tunda tayi sallah azahar ta fita.
Bata falon danake tsamani don haka kai tsaye na nufi dakin mama da sallama tun kan na tambaya na hango halimatu din kwance tana barci saye da hijjab din datayi sallah.
Wayancewa nayi da gaida mama tare da tambaya ko taci abinci kuwa tace tun dazun mukaci da mutumiyar tawa aini naji dadin zuwa da yar nan kasan tunda gata tana debe min kewa sosai wallahi.
Mama tana dai damun ki da surutun ko yaushe indai halimatu ne shiyasa suke dasawa da ya jafar idan yana gari ai.
Yarinyar tana da shiga raine mahaifiyar ku gaskiya tana ba yaro tarbiyab daya dace wallahi kunyi sa,an uwa tagari ba kadan ba.
Mama mu gode kamar yadda anty fadila tace in dinga fada idan wani ya yaba wani abu nawa daya shafeni.
Yanzu mama yau ba zamu je gun hjy ba ke nan sai ranan da suka bayar za,a ganta yayi wanan kasa gaskiya suna da doka mai tsauri wallahi.
Ai inda sukafi kasan mu ke nan wurin sanin aiki da canne kyale duk wanda zaizo zasuyi a dameta sai idan an hadu da likitan da yasan kansa zai dan tsawatawa mutune su daina shiga.
Dan wanan hiran da mukeyi da mama yasa naji har zuciyana ya dan sake don hira sosai mukayi da ita har lokaci yaja bamu sanda hakan ba.
Zaune a office din shi ya mike kafafuwan shi saman table din dake gaban shi yana rike da kanshi da hannu daya irun zaman da yayi yana nuna yayi zurfi a cikin tunane.
Don alal hakika yana cikin damuwa da maganan da sukayi da dan uwan nasa kwanakin da suka wuya har ranan ya kasa samun natsuwa a tare dashi.
A karo na barkata yana kiran layin kanin nasa yaki ya daga a karshe ma sai computer ke fada mai wai layin na busy ko yaushe idan ya kira.
Yanzun ma daya kira computer din daine ke fada mai yadda ya saba fada mai layin na busy haka yasa yagane dan uwan ya sashi a black list din wayan shi.
Kararawan office din nasa ne yayi kara hakan na nufin akwai mai son shigowa office din a lokacin.
Da kamar ya kyale maishi ya koma ya dai daure ya ya danna alaman ba mai so shigowa daman ya shigo.
Yana budewa suka baiyana mai su uku aboka shi ne tun na kurciya da suke shashancin su a tare wanda kusan ta sanadiyar sune ma ya samu aiki a kasan nasu a yanzu saboda hazakan shi da kuma basu son rabuwa dashi don zaman shi star a cikin su.
Ko wanin su yana cikin shiga ta alfarma kamar yadda suka saba shiga saidai na kananan kayane irin suit.
Ya matsa kadan daga kofan ya basu wuri don su shigo daga ciki basu shiga ba illa kokarin hugging dinsa da sukayi daya bayan daya.
Kafin su wuce suka karasa cikin office din kujerun dake officen din zube gefe daya suka zube a sama.
A sabule ya biyo bayan su zuwa ciki shima ya samu daya daga cikkn kujerun ya zauna a kai dayan mai suna philis yake fadin ya labarine na ganka a haka kuma.
Sai dayan ya karbe da fadin kwana biyu bamuga ka leko club ba yasa yau na gaiyaci friends muzo mu duba ka ko lafiya.
Jafar din bai amsa kowan su ba illa mikewan da yayi zuwa wurin firdge din dake office din ya bude tare da fito da kananan kwalabe ya dire a gaban su ya juya ya dauko kofuna hudu ya dawo inda yake zaune da farko ya zauna.
Ido ya zuba masu mai nuna alamun shi a gajiye yake ba zai iya zuba masu abinda ke cikin kwalban ba a lokacin.
Kallon shi dayan da baiyi magana ba tun shigowan su yayi yana fadin cikin kulawa wai ya nagan ka hakane gaba daya ka birkicewa sanin ka damu.
Jafar din ne ya dago idanunsa da suka kade sukai jawur alaman yana cikin tashin hankali dai sosai.
Mikewa yayi ya nufi wurin window din office din nasa ya zuge wani haske ya baiyana a office din lokaci guda ya gyara tsayuwan shi yana kallon motocin dake wucewa kasan office din nasu.
Binshi sukayi da kallo tare da mikewa suka nufi inda yake din tsaye don da alama jafar din baison damuwa cikin halin da yake ciki din a lokacin.
Ji yayi daga bayan shi a dafashi hakan yasa shi juyowa ga wanda ya dafa shi din cikin su gaba dayan sune a tsaye a bayan shi suma fuskansu ya nuna sun shiga damuwa kan damuwan shi.
Whatff bro wai meke faruwane dakai haka ka fada min damuwan ka mana ko zamu samu mafita akan matsalan dake damun ka ?
Dan dariyan yake yayi yana kallon su kafin ya girgiza kanshi yana fadin banyi tsamanin zaku iya min amfani ba a yanzu don wanan family issue ne ba maganan ku bane ko na wani.
Da matsalane dakai da family din kku ke nan a yanzu ko hakan yana da nasaba da zuwan yan uwanka da tj yace sunyi a gidan ka akan sanadiyar kakanka da bata da lafiya wai ?
Da manaki ya juyo yana kallon su watau taju har ya kasa hakkuri yakai karanshi ke nan a wurin su yanzu wanda shine dalilin zuwan su ashe ?
A dan zafafe ya buda baki da kyat don ranshi ya gama baci dasu yana fadin oh ashe kunzo ne yanzu kuyi min fada ke nan ?
No no no ka fahince mu jackson munzo nan ne yanzu a matsayin abikan ka bawai munzo muyi wani maganan daya shafi tj din bane.
Nima ai a yanzu nafi ma sha,awan ka samu sabon dan hannu dan shi tj din kakai shekuru dashi kuna harkan nan.
Hannu ya daga mai tare da wani irin tsawa yana fadin stop that nose's jooo, wuu bana cikin mude din wanan zancen a yanzu don zuciyana a jagule yake da komai.
Kallon juna sukayi kafin dayan yace dashi ko zaka samu fita yanzu muje kadan sha wani abu ko zaka samu relief a zuciyar ka ?
No ba bazan iya shan komai a yanzu ba don gidana a cike yake yanzu da family dina shan wani abu a gareni yanzu hadarine sosai.
Zaka iya don ba bakon abu bane sha a gareka don haka ka daure kawai mu fita yanzu kadan samu relief a rayuwan kan ko tunanen ka da damuwan ka zai gushe maka na dan lokaci ka koma daidai.
Tun bai yarda da hakan ba har yakai ya yarda ya biyewa son zuciyar su sukaci karfin shi akarshe suka fita tare zuwa inda sukan hadu su hole.
Ranan don bai cikin dadin rai shi ruwan kwalba yaita dinkirawa cikin sa yana kuma jan coicane har ya fara fita cikin hayacin sa.
Da haka har ya raba dare a waje cikin mayen kuma yajawo motar shi zuwa gida don shi din dan hannu ne sosai a wanan harkan.
Ina dakina da nake kwana a kwance na kulle kofa na dinga jin kamar a dukan kofan duk da nasan kofan a bude yake don bani na saba rufe part din ba .
A cikin daurewa da fargaba da tashin hankali na fito a cikin sanda zuwa falon part din babu tantama kofan ne ake duka da karfi.
Allah ya sako min wani dauriya na nufi kofan na bude saidai abinda na gani shine yafi tashin hankalin da nake ciki.
Don ya jafar ne a cikin maye yake dukan kofan gashi rataye da corth din rigan shi a kafadan shi sai layi yakeyi.
Innalillahi wa,inna alahim raj,un na ambata tare da da duban bayan shi ko akwai wani a tare dashi ko wani a falon sam na manta da darene sosai lokacin kowa ya shige part din shi ya kwanta.
Ina can ina tunane ji kawai nayi ya fado min a jiki yana fadin take me to your room zee i want sleep now.
Gabana ne ya fadi jin shi a jikina da nayi lokaci guda ya kara fadi cikin wani murya na maye take me to your bakiji ba ne ?
Ni kan ina zan iya kama mutum kamar ya jafar mai karfi haka da jin koshi a tare dashi a cikin dabara na samu na kaishi dakin nawa ya zube da takalman shi da komai saman gadon ya kwanta rub da ciki ba bata lokaci naji ya fara sakin nasari.
Da sauri na dafe bakina tare da sakin wani irin kuka lokaci guda kamar daga sama naji yana fadin are you crying zeey ?
Dago kai nayi na dan kalli inda yake kwance har lokacin yana kwance a yadda yake din ba tare daya motsa ba yake wanan maganan tashi nayi na sawa kofan dake bude key.
Ban daki na nufa a can na raba dare ina darza kuka a cikin tashin hankali sai maimaitawa nake ya jafar dama dan giya ne ashe.
Don babu tamtama nasan yadda yan giya suke mayensu idan sun sha don muna da yan giya a kauyen mu idan sun shawo muna kanana zamu bisu muna waka sunyi marisa sun sha kwaya har sai manyan gari sun kore mu zamu bar mutum.
Ashe nima zan auri mashayi da zai rika min marisa a gida ina kallo a cikin tashin hankali da fargaba.
Yanzu ni yaya zanyi wani irin hukunci zan daukarwa kaina kan zama da mashayi a gida daya ya zama dole gareni tun ban makara ba insan inda dare yai min daga hannun ya jafar din.
Dama abinda mutane ke yawan fada min kalman inyi hakkuri da hakayan sa da zan gani nan gaba ?
Dama ashe sun san komai suka boye min shima yasan yadda yake ya aureni a hakan don kawai ya cutawa rayuwana ke nan.
Dama wai mami tasan danta haka yake kuwa har ta tsaya tana nuna min wanan kyamar don kawai ina yar talaka ni ko ina yar talakka ai talaka yasan mutuncin kansa da kuma abinda Allah ya hanemu yi.
Gudawa daga garshi ne yazauna min a zuciyana saida kuma ta ya zamu iya gudawa yanzu daga kasan nan tunda shiga jirgima sai idan mutum ya shiryawa hakan.
Ina ko yaya zanyu zanyi ne don mu gudu dani da kanwata daga hannun wanan mashayin tun baikai ga illanta min rayuwa na ba.
Haka nayi rabin kwana a cikin makewayin can na dauro alwala na fito ashe ina ban dakin anyi ta dukan kofan ina ban daki a lokacin banji ba.
Ashe taju ne ya falka yaji dukan kofan da akeyi kamar a cikin mafalki kafin ya nemi tufafi ya saka a jikin shi har mun nufi dakina kamar yadda ya bukata in kaishi dakin nawa.
Ya fito bai ganshi a waje ba ya nufi kofana yana duka don yaji kamshin turaren a falon ya dade yana dukan kofan nawa ba,a bude ba har ya hakkura ya koma daki .
Ranan ba karamin hauka yayi a dakin ba shi kadai dan ya tarwatsa kayan dakin da dama yana hauka wai mun kasance a tare da yaya a daki daya yana zaton wani abu zai wakana a tsakan nin mu ke nan idan mun kebe din mu kadai.
Har washe gari ya jafar din yana kwance bai falka ba ni kuma ina takure a wuri daya naci kuka har idanuwa na sun canza kala don kukan danasha tun dare har zuwa safe ban runtsa ba ga barcin da ban samu ba shima yana barazana a idona.
Karfe taran safe a lokacin nasan su mama sun tashi ko dan ita ta saba fitowa tun safe a gida ko nan din ma da sunyi wankan safe sukan fito falo su zauna.
Ina cikin wanan tunanen lokaci guda naji ya motsa sai kuma ya sake komawa ya lafe ido na tsura mai daga inda nake zaune din a takure.
Can kamar wanda aka tsikara ya mike zubur tare da dafe goshin shi yana murza idanun shi lokaci guda kuma ya bude su ya fara bin dakin da kallo.
Zubur naga ya sauka daga kan gadon tare da karewa kanshi kallon mamaki har lokacin bai ankara dani a inda nake a zaune ba .
Zama ya koma yayi bakin gadon tare da jan wani irin uban tsuki lokaci guda kafin kunnuwa shi ya fara jiyo mashi sautin kukana a inda nake takure.
Da sauri ya mike tsaye tare da nuna ni da yatsa yana fadin ke ke lafiya na ganki haka mske faruwane wai ?
Ya akayi nazo dakin nan wai a nan dakin na kwana kome juyawa yayi ya dan kalli gadon na dan lokaci guda tare da juyowa gareni ya sake kallona yana fadin .
Wai wani abu ya farune kike wanan kuka haka ki fada mi ina tambayan ki kin yi shiru jin da yayi banda lokacin bashi amsa yasa shi jan wani itin uban tsoki ya duka yana daukan riganshi dake saman gadon.
Kai na dago ina kallon shi tare da mamakin shi wai yana nufin baisan abinda ya aikata bane a daren jiya ko me yake nufi da wanan basarwan ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
6️⃣1️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
Littafin kudine yar uwa don girman Allah da darajan Annabi kada ki karanta idan baki biya ba don Allah da son da kikewa Annabi.
Ranan nayi kuka har na gaji a daki ba wanda ya sani don na kulle kaina a cikin daki ni kadai kada wani ya fahinci hakan.
Tunane kala barkatai nayi a zuciyana ina nemawa kaina mafita saidai abu dayane ya tsaya min a zuciyana shine ta yaya zamu gudu daga wanan kasan yanzu ?
Gashi ko yanayin tafiyan da mukayi ya nuna ba a kusa da kasa mu muke zaune ba a yanzun don tunawa da nisan tafiyan da mukayi kafin mu iso nan.
Wayyo ni Allah wayyo kaina na fada a fili tare da kara sake wasu sabbin hawaye masu dumi daga fuskana lokaci guda.
Ya jafar me yasa ka kasance a haka dama don shine ka yaudareni ka nace saini zaka aura don ni din na kasance ba yar kowa ba ko kuma don ni din yar kauyece daba zan fahinci halin da kake ciki ba Allah masani.
Ya Allah ka kiyashe aikin aikata sabo komai kankantan shi a rayuwan mu don kawai biyewa duniya ko wayewa mutum yana dan musulmai ya jefa kanshi ga mahalaka irin wanan .
Tir da hali irin naka ya jafar dama mai hali irin naka idan kuma kai mai shiryuwane ubangji Allah ya gagauta dawo dakai hanya madaidaiciya a rayuwan ka.
Mu kuma Allah ka tsaremu daga fadawa halaka itin wanan duniya da rahira na karasa da amin ina share hawayen dake zubo min a fuskana.
Shima ya jamal ranan ya kasa fitan safen da yakeyi don ashe akan idon shi dan uwan nasa ya dawo a cikin mayen sa gida yaga komai yadda ya wakana a lokacin.
Don yana shirin zuwa kofan ne ya samu ya izashi cikin part din a lokacin ne yaji fitowana daga dakin ya kara labewa yana kallon yadda muka kwashe dashi har shigan mu part din nasa.
Baiyi barci ba don damuwa da tashin hankalin daya shiga a lokaci don bai dauka abin dan uwan nasa ya girmama haka ba sai yanzu da idon sa ya tabbatar masa da komai ya gani da idon sa kuma.
A, lal hakikanin gaskiya yaso auren dan uwan shi da wanan yarinyar da farko saidai a yanzu yana jin tsoron kasancewar shi da yar mutane.
Kada yazo ya jefawa mutane yarsu a cikin halaka da dana sani a karshe duk da yana shedar zainab din da hakkuri da juriya ga ladabi gami da biyayya .
Ko wani namiji zaiso ya samu mace mai irin wanan halin nata saidai shi dan uwan nasa gashi Allah ya basa irinta mai hali na kwarai da kowani namiji yake fatan ya samu din.
Wanda yasan hakan na daga cikin abinda yaja dan uwan nasa ga zaben wanan yarunyar don juriya irin na zainab din a yadda ta zauna a gaban mahaifiyar su suna gani.
Dama ace ya mamudne yayi katari da irin wanan mace mai hali irin na zainab din yasan da yanzu lafiya lau take zaune da kowa a gidan nasu.
Yaja wani dogon tsuki yana juyawa daga inda yake kwancen a fili yace mami da ace kinsan halin da dan ki ke ciki da yau kin daina tsanar yar mutane da hattaran ta don kawai wani akida naki can na daban.
Da kinyi nasaran aura mashi yar kawar ki da kike da burin yi har yanzu akan dan naki da yanzu asirin ki dana kowan mu ya gama tonuwa a kasan nan ga baki daya .
Don babu macen da zata zauna da miji mai hali irin na ya j abin kyama ga kowa a zauna lafiya haka kamar yadda yarinyar nan ta kawar da idonta a kan hakan gareshi.
Wani tunane yazo mashi zubur ya mike zaune yana tambayan kanshi wai dama zainab din tasan halin ya j dinne take zaune dashi a haka ko kuwa dai a yanzu ne ta fara gani da idon ta ?
No no no yarinyar nan bata san komai ba don batayi wayyon da zata gane hakan ba da yanzu ta nuna wani alama kan hakan ai.
Lailai ya zama dole ya tunkareta kai tsaye da wanan zancen yaji ra,ayinta kan halin dan uwan nasa kai tsaye idan da shawaran da zasuyi suyi shi a tare tun kan wani ya ankoro da wannan halin na yayan nasa su shiga bakin mutane.
Wanan dalilin ne ya hanasa fita gidan ranan ya fake ya tsare yana jiran fitan yayan nasa da fitowan ita zainab din ya samu su maganta wanan babban maganan daya taso masu din yanzu don shi yafi komai daga masa hankali saboda yaga yayan nasa yayi nisa ga harkokin nasa ko a yanzu taron shi sai an shirya masa sosai.
Sai dai gashi a gidan yau baiga fitan ko wani daga cikin su ba haka dole ya hakkura ya tafi duba tsohuwar dake asibiti don yasan zuwa yanzu tana can cikin damuwan rashin ganin shi akan lokaci da batayi ba.
Barci mai dadi ya kara daukan shi bayan ya samu ya watsa ruwa a jikin shi tare da kokarin yin sallah da ya kubce masa don yanzu wurin tara da wani abu na safe ya koma gado ya sake kwanciya don nauyin da idon sa yake dashi har wanan lokacin na barci.
Abokin shi philis ne ya kirashi a waya yasa ya daure ya mika hannu a hankali ya dauki wayan nasa dake daga gefen shi a yashe saman gado wanda ya zama masifa yanzu ga mutane.
Don mutum yana tashi barci shedan zai zugashi yakai hannu a waya kafin yai yunkurin yin komai a rayuwannshi.
Yoou bros philis ya fada dayaji ya dauki wayan nasa a lokacin don jin muryan shi da yayi lokacin a cikin magagin barci.
Wai har yanzu baka gma barcin bane karfe sha biyu da wani abu yanzu fa na rana ko yau a kwance kake nufin zaka wuni don dan abinda ka taba a daren jiya din ya kare a cikin dariya.
Jafar din ya mitsike idanu dakyau yana kallon agogon dakin nasu can ya tuna da waya a hannu shi yace jiya nasha wanan abin over kan kun zugani da yawa.
Uhumm philis dinyace ta bangaren shi yana dariya tare da fadin kada ka zamo raggon maza fa don ban sanka da wasa ba mutumina ?
Zan sauka kasa yanzu inga mai gidana ke ciki idan na watsa ruwa zan fito zuwa karfe biyu nan idan na samu time ya bashi amsa da hakan tare da kashe wayan shi.
Mikewa ya daure yayi daga kan gadon a hankali sai lokacin idon shi ya sauka ga ta,asan da taju yayi mashi a dakin a daren jiya.
Dakin yabi da kallo ko ina tare da jan tsuki mai karfi yana fadin zanyi maganin wanan gay din dan iska duk akan me yayi min wanan barnan haka a daki.
Daidai zai mikene ya tuna da zancen kwanan da yayi a dakina ya kara jan tsuki don fahintar dalilin taju nayi masa wanan aika aikan haka a daki.
Daurewa yayi ya shiga wanka tare da kara tsarkake jikin sa ya fito kara bin dakin yayi da kallo yana mamakin taju din a ransa.
Tsuki ya kara yi ya nufi wurin tufafin shi yana dauka tare da magana kamar wanda ya tabu yana fadin duk ba komai ke jefani a tashin hankalin nan ba sai sakaci da addini na da nakeyi kan wanan shegun abin kyamar dana jefa kaina a ciki saboda abokai da ba addinin mu daya ba giya da wanan harkan da mukeyi.
In banda sherin wa yan nan ai da yanzu yana zaune lafiya a cikin salamansa kamar kowa amma komai a yanzu zaiyi sai a boye jamar wani mara gaskiya a cikin yan uwan shi.
Gashi saboda shan da yayi daren jiya ya jawo mai har yar mutane ta kamashi a haka saboda fita hayacin shi dayayi kan giyar da cocaine din.
Ahaka har ya shirya ya fito sai sai gidan tsit yake kamar babu kowa a cikin sa a lokacin don su mama basu dade da shiga dakin su ba lokacin.
Abinci ya fara nema don jin cikin sa da yakeyi kamar ya yi kwanaki baici abinci ba a cikin sa yake jin yanayin kansa a lokacin.
Ina kwance a dakina duk da hasken ranan daya gauraye daki a lokacin ni duhu nake gani a dakin ko ina saboda daci da radadin da nake ji a zuciyana.
Ga tunane ya tsaya wuri daya cak don ban san abin yi ba a yanzu don banda wani mafita da zai fisheni ga kangin shi a kasan mutane.
Ina daga kwance kaina na kallon sama saboda nayi kukan har na gaji nabawa kaina lafiya don idona daya fara yi min dishi dishi a lokacin.
Jin an budo kofana baisa na dago kai naga mai shigowa dakin ba a lokacin illa ina kwance a yadda maishi ya sameni.
Tun daga kofa ya hangoni yadda nake kwance din nayi motsu mutsu dani alaman nasha kuka har nagaji tun daren jiyan.
Jikinshi yaji yai mai sanyi a lokaci guda shi kanshi yasa bai kyauta min ba yana tsaye ya rasa abinda zaice min sai faman kallon .
Kallona ya tsaya yakeyi ya rasa kalman da zai fara min magana dashi wanan ne rana na farko daya taba jin kunyar wata ya mace a rayuwan shi bayan mahaifiyar shi.
A da kan bai dauki abinda yakeyi a matsayin wani abu ba face holewarshi da lokaci kawai sai gashi yau yarinyar daya raina ma wayau a da ya fara jin kunyarta a duniya.
Da kyar ya iya kaiwa zaune a bakin gadon a kusa dani yayi gyaran mutya yana fadin lafiya kike zainab na ganki haka ?
Ban dago kai na iya kallo shi ba tunda ya zauna a wurin ina a yadda nake a kwance din har lokacin dan girgiza kai yayi kafin yace .
Wai bakiji ina magana dake bane zainab meke faru dakene kika koma haka lokaci guda ?
Jin abinda ya fada yasa na dan juyo kadan na kalleshi a cikin takaici da jin hsushi da tsanar shi lokaci guda daya sauka min a zuciyana.
Da kyat na daure cikin sanyin murya nace damuwata ba matsalan ka bane yaya abinda ya shafeni ni ya shafa.
Yanayin muryan da nai magana dashi dole yaba mutum mai saurare a lokacin tausayi a lokacin don gaba daya muryata ta dakushe dan kuka.
Yace amma ai hakkin ki yanzu a kaina yake duk wani damuwan ki ya shafeni ko don haka ki fada min damuwan ki nace ko menene ?
Ko kuma a yadda kika ganni a daren jiyane ya sakaki daukan wanan matakin a yanzu kina son ki halaka kankine ko kuma addu,a ya kamata ki min a matsayina na mijin ki a yanzu.
Addua ?
Addu,a fa kace ?
Kai bakaiwa kanka addu,a ba ka daina wanam halin sai nice zan ma addua a karba min ?
Yaja dogon numfashi bayan jin abindana fada ga mamaki daya hanashi kwakwaran motsi don dai yasan girma ya gama faduwa ke nan .
Inaga nasan sauran abinda yake aikatawa bayan wanan ashe da rashin kunyar yafi wanan da bai taba zato ba a wurina.
Numfashi ya sake ja tare da fadin to tashi muje asibiti a dubaki idan lafiya kike a yanzu ?
Barshi don ni lafiyata kalau a yanzu yaudaran ka kawai ne abinda ya dameni a zuciyana .
Ya jafar ka cuceni ka yaudareni ka yaudari iyayyena da suka aura min kai a matsayin miji yau suji mijin da suka aura min suke kiranka da surukin kirki ashe tsohon mashayin dan giyane haka basu sani ba.
Haba ya jafar ya kake son nayi da rayuwana da halinda muke ciki da mahaifiyar ka da yan uwanka zanji ko da wanan halin rayuwa naka na boye da Allah ya baiyana min a daren jiyana gani.
Lokaci daya yaya kazo kashiga rayuwana ka nuna isa da gadaranka a kaina don kawai ina karkashin mahaifiyar ka ba tare da kayi tunanen nawa rayuwan ba.
Na hakkura a hakan nake zaune tare dakai don biyayya ga iyayyena duk da mutane da dama sun san da wata manufa ka aureni don ni din ba ajin auren ka bace ai.
Amma haka na hakkure nake zaune tare dakai duk da mami har gobe ta nuna bata ra,ayin zamana dakai.
Wace matakace da kai yaya ranan da ka tsaya gabab mahalicin ka don kare kanka a wanan rayuwan ka tuna fa shi mutum ba a bakin komai yake ba ga Allah.
Yanzun nan Allah na iya ikonsa a kanka kana takama da lafiya da arziki da ilimin ka zai iya mashe ka gawa lokaci guda.
Ko kuma ya karbe lafiyan da kake takama dashi lokaci guda zai iya maisheka miskini mara moriya kana kuma a raye.
Kukane yazo min har na kasa karasa zancena na juya na fara kuka sosai a cikin tashin hankali da bacin rai ga abinda ya faru din.
Kai ya dukar a kasa don wanan maganan dana fada yafi komai nauyi a wurin shi sai yaji wani irin gumi yana feso mashi lokaci guda gashi ya rasa abinda zaice dani don yasan gaskiya na fada mai .
Don nauyi mami da yan uwanshi a iya su zancen zai tsaya idan sun san da haka nawa iyayyen kuma da wani ido zai iya kallon su idan har sunji.
Don haka sai ya zuba min ido kawai yana kallona da mamaki kamar ranan ya fara ganina a duniya.
Nima ban fasa kukan takaicin da nakeyi ba can naji yakai hannun shi saman kafadana yana fadin is OK kukan ya isa haka nasan na aika abinda Allah ya haramta ga musulmi .
Saidai ina rokon ki da ki taimakeni ki mun adduan Allah ya rabani dashi har abada a rayuwana yadda ya fada a cikin wani murya mai ban tausayi zakace bashi yake maganan ba.
Majina na share da kyalen dana aje a wurin don share hancina tunda safe kafin na dago kai ince ko nayima addu,a yaya tunda kai baka da niyar bari ba fasawa zakayi ba ai.
Shikan yau mamakin zainab din yakeyi a ransa sai fadin yake ashe haka wanan yayinyar take ina kallonta shiru shiru ashe akwai aiki ja a gabana rana data gama gane koni waye ?
Saidai a fili yace waya fada maki bana addua akan hakan ko yaushe abune dai idan Allah ya jarebaka dashi yana da wuyan sha,ani.
Duk cikin maganganun da yai min a lokacin babu kalman ban hakkuri ko nadama a tare dashi don a gadarance yake fadan maganan shi kamar yadda ya saba idan yana magana.
Kinci abinci yau ya tambaya a karshe banza nayi dashi ba tare dana bashi amsan tambayan nasa ba sai ajiyan zuciya da nakeyi don kukan dana sha a ranan.
Kinga yanzun dai ki tashi kiyi wanka ki fito mu sauka kasa kici abinci don kada wani ciwo yazo ya kamaki kuma ?
Ba zan iya cin komai ba don bakina bai da dasin cin wani abu a yanzu na fada ina gyara kwanciya ta hanyar dunkulewa a wuri daya.
Yana zaune shiru banji ya motsa daga inda yake zaune ba sai can naji yayi ajiyan zuciya da karfi ya mike tsaye.
Ni a zatona ya fice daga dakin ne a lokacin ashe ban dakina ya shiga ya hada min ruwa mai zafi sai ji nayi mutum yana kokarin cicibana lokaci daya.
Don Allah yaya ka bari bana jin yin komai a yanzu zan tashi idan zuciyana ya sake min bai tsaya saurara min ba sai daukana da yayi dani yana shiga ya tsomani a cikin bahon wankan dake ban dakin .
Lokaci guda na sake wani irin ajiyan zuciya a tare dani juyawa yayi ya fita ya ban wuri a yanzu kan idona ya bushe don na nemi kuka na rasa a idona.
Haka na daure na watsa ruwa tare da alwal bayan na cire tufafin dake jikina na samu har na gama na fito a zatona yana dakin har lokacin don haka ban yarda na fito ba sai dana leka naga baya dakin.
Zani da hijjab dina na dauko a wardrobe na nufi inda nake sallah na tada sallah ina sallah naji an kwankwasa dakin an shigo.
Ashe julie ce ya umurta da takawo min abinci ganin ina sallah tana ta mamakina har tana tuntube a dakin wurin aje kayan abincin da ta shigo min dashi.
Saida na gama sallah na mika kuka ga ubangiji kafin na mike na samu wasu kaya na zura a jikina ban ko kalli abinda ta aje min a dakin ba.
Na koma bakin gado na zauna ban koma kwanciya ba sai ga mama da sallama a dakin a karon farko data shigo dakin nawa ke nan tun zuwan mu kasan.
Amsa sallaman nayi halimatu na biye da ita a baya mama ke fadin zainab ashe bakiji dadin jikin ki bane sai yanzu mikin ke fada muna.
Ni na dauka yau yana hutune ai kuna tare shiyasa ma ban yarda wanan yar taragagan tazo inda kike ba don yau banji fitan shi ba shima.
Dan dariyan yake cikin katfin hali na kakaro a fuskana ina fadin tun darene bana jin dadi mama .
Tace haka dai shima ya fada muna ai kwa fadawa mutane tunda gamu a gidan ai yanzu ina dadin hakan da kukayi ai ko sannu kawa mutum.
Tana kai aya ta dora da fadin yace kinki cin komai tun safe ga abinci nan yasa a kawo maki sai ki daure kici don Allah don yace yayi yayi kici kin kiya.
Badon naso ba don biyayya ga mama Ramatu na daure na kurba ruwan shayin bayan shi ban taba komai ba a kayan ina gamawa na koma na kwanta har lokacin suna dakin tare dani.
A bakin su nake jin wai ya fita zuwa asibiti ya duba hjy amma ba zai dade ba zai dawo a raina nace shi dai ya sani don ni na tsane shi a yanzu.
ZAINAB IDRIS MAKAWAKwana biyu ina daki kwance a cikin damuwa bana fitowa ko falon gidan a inda muka saba dan zama dasu mama muna hira.
Asibitin ma suke zuwa su duba hjy don ni ban iya fita yanayina kamar nayi jinyar kwanaki nake jin kaina.
Ya jafar yakan shigo ya dubani na dan lokaci saidai zai kare tsayin shi har ya bar dakin ban dago kai na kalli inda yake tsaye ba hakan kuma bai nuna fushin shi ga yadda nakeyi mai din ba.
Ranan dai dana kwatanci ya fice gidan na dan ja kafana na sauka kasa babu kowa a falon haka yasa na dan nufi wajen gidan don nasha iska kadan ko zanji jikina ya kara sakewa.
Wasu tsuntsaye dake kiyo ne a haraban wurin suka dauki hankalina har yakai na shagala ga kallon su sun dauke min hankali yadda suke ciyar da junan su abinci.
Barka da fitowa matar yaya naji an fada a bayana koda ban juya ba nasan ko muryan waye don muryan su yana da kama dana dan uwanshi hakan bai hanani gane ko waye a wurin ba yake gaidani.
Dan juyowa nayi tare da kakalo murmushin don dole ina fadin ya jamal ina wuni a cikin ladabi shima dan gyara tsayuwan shi yayi yana amsa min lokaci guda.
Tare da fadin ashe kwana biyu baki da lafiyane duk da nasan sanadin rashin lafiyan naki mijin kine ya jawo maki shi .
Da sauri na dan dago kai na sauke a kanshi don jin abinda ya fada yace yes zainab na sani shine yaja maki wanan ciwon don halaiyan shi da kika fara gani wanda da farko yake boye muna hakan ko ?
Don mu kanmu bamu san da hakan ba saboda ya boye muna koshi waye a wurin mu saidai ni tun ganin yadda auren ku ya wakana dashi na sa ido ga harkan yaya don in gano dalilin shi na bijerewa mami.
Da kuma dalilin dayasa ya zabe ki a matsayin wace yake son luluba a cikin bargon arzikin ta ya fito a mutum sak kamar kowa.
Wai zainab kinsan ke din mai arzikine arzikin da ba kowa Allah keba irin sa ba sai kebabu daga cikin bayin sa .
Shifa arziki da kike ji a wurin Allah kala kalane gun mutanene suka dauka arzikin dukiya shine arzkin da kowa zai samu yayi alfahari dashi.
Allah nama bayin sa arzikine ta hanyoyi daban daban akwai masu arzikin "ya"ya akwai arziki na hali akwai mai arziki na baiwa da arzikin hakkuri da arzikin wadatan zuciya da dai sauran su.
Kamar ke zainab kina da arziki dana fahinta wanda Allah ya baki wanda ba kowane zai iya fahintar haka ban sai mai natsuwa zai gane baiwan da Allah yai maki zainab.
Kallon da nayi masa na ban fahince ka ba yasa yace yes Allah yai maki arzikin bawai da hakkuri wanda ba ko wace mace take da irin wanan baiwan ba haka.
Ki duba duk da karacin shekarun ki zainab amma kin iya rike sirin mijin ki a zuciyar ki ba tare da kin fadawa kowa yasan halin da dan uwana ke ciki ba.
Na gani da idona ba wani ya fada min ba irin halin da ya dawo maki a ciki gidan nan last two days da suka wuce don a buge ya shigo gidan nan ya tayar dake.
Ban sani bako wanan ne karon ki na farko da kika ganshi a cikin wanan halin idan kuma har kin sani tun baya na dai yaba maki wurin kokarin boye masa siri da kikayi.
Idona ne ya kawo kwalla lokaci guda yace no bana son kiyi kuka a yanzu don kuka ba naki bane zainab a yanzu.
Saboda yakine ja a gaban ki dake tunkaran ki a yanzu don sai da taimakon ki zamu samu har mu shawo kan wanan matsalan don wanan yakin zainab ba naki bane ke kadai yanzu ya shafi kowan mu a yanzu.
Yanzu yin fushi ko kauracewa ya J baya da amfani a garemu baki daya don ni nan na nuna mashi bacin raina yan kwanaki da suka wuce kan fahintar wasu halayan shi danayi da yake boye muna.
Sai na fahinci fushi ko bashi baya baya hanashi aikata sabon daya samu kansa a ciki saidai ma ya kara kangare muna ta wanan hanyan.
Zainab a yanzu ya zama dole muja ya J a jikin mu fiye da yadda muke a yanzu dashi mu sanman ma keda kike zama matar shi.
Don ta hakan har Allah ya taimakemu ya bamu sa,a akan wanan halaiyan da yake aikatawa a boye don zainab gaskiya matakin da kike kokarin dauka bashi zai sa auren ki dashi ya rabu ba a yanzu.
Yin hakan kuma kamar kara turashine ga abinda yakeyi a yanzu shike nan kinga rayuwan shi ya kara shiga wani hali ta sakacin mu ashe ?
Don ke kanki ba zaki so kiga wani cikin yana irin wanan halaiyan ba kinga shike nan ko yaushe kina cikin damuwan hakan fiye da kina gidan sa ashe.
Dama alkawarin Allahne duk wanda ya kama hanyar aljanna zaita haduwa da abubuwan da zuciyar shi bata so haka kuma wanda ya hanyar wuta zaita haduwa da abubuwan da zuciya keso .
Shi yasa akace daga cikin hakkuri da akeso mutum yayi cikin rayuwan sa harda hakkurin biyyaya don Allah .
Don hana zuciya aikata sabon data ginu akanta farat daya abune mai wahalan gaske sai a hankali ana jan hankalin maishi anayi masa nasiha da addua a hankali tare da nuni ga hukuncin da ubangiji ya tanadar kan abin sai kiga maishi ya bar abin ba tare da wani tashin hankali ba.
Don haka zainab ina rokon ki a yanzu kada kice zaki bar yaya don wanan halin da idanunki ya gane maki a kanshi dama wanda baki gani din ba a yanzu bana fatan hakan a gareki.
Don ni kaina bazan so mami ko wani namu musanman ma mama Ramatu dake nan yanzu tare damu har ta fahinci wanan abinda yaya keyi ko taji hakan daga bakin ki.
Don haka zainab hakkuri zan kara baki kan hakan saifa kin jajirce gami da masa addua da saka ido kan duk wani al,amarin daya shafi rayuwan shi.
Ki nuna kedin matar sunnace a gareshi wace tasan right din ta na aure bawai ina nufin sai kin fito fili kin nuna ya baki hakkin ki na matsayin ki na mata a garshi ba.
A,a a cikin hikima da basira irin naku na mata ya kamata ki fata yakin da kika shirya a kansa yanzu ta hanyar sake jiki dashi ki daina wanan ja bayan da kikeyi a yanzu gareshi.
Mijin kine zainab idan yayi ba daidai ba ki fito fili ki fada masa abinda yayi din baida kyau ga Allah da al,adan mu a sannu in yana da rabo sai kiga ya bari.
Katse shi nayi da fadin to amma ya jamal kana ganin a matsayina na ba kowa ba a gareshi yaya zai yarda yaji nasiha ta ?
Me zai hana zainab ya bani amsa zai saurara maki don nasan shi di yana son ki kuma yana tausayin ki a zuciyar shi.
Wanda hakan nema har ya yanke shawaran ya aureki ya kawoki gidan shi ku zauna a tare ku kuma rayu a tare dashi duk ritsi duk wahala.
A karshe ina mai kara baki hakkuri ka wanan kaddaran da kika samu kanki a ciki a matsayina na dan uwan ki yayan ki bawai kanin mijin ki ba.
Hawayen da nake dannewa ne suka zubo min lokaci guda nace ya in sha Allahu zan gwada sharanka a kansa nima a matsayina na kanwarshi kuma matarshi a yanzu.
Nagode zainab da kika fahinci ne kafin wani yasan wanan abi kunyar da yaya ke kokarin sakamu a idon duniya nima zanyi iya kokarina in dinga fadakar dashi kan abinda yake aikatawa din a yanzu.
Na barki lafiya ni zan je asibiti yanzu sai dai ina son wanan damuwan da tashi hankalin ki daina yinsa daga wanan lokacin ki fito a matar auren ki sak a gidan nan ba tare da kin damu da warning din kowa akan hakan ba.
Nina barki lafiya ya fada ya juya ya tafi ya barni a wurin ina binsa da kallo zuciyana kuma da dinbin tunane kan aikin daya dangantani dashi din a yanzu.
Duk da nasan dama wanan din aikinane yin hakan inda hali kuma da jajircewa ya zama dole in shanye duk wani damuwa don in ba haka ba zuciyana tana gab data tarwatse a yanzu.
Sake tambayan kaina nayi ta yaya zan iya duk wanan abubuwan yanzu don ni mace ce mai kunya da sanin ciwon kaina.
Don haka ko zanyi ba zan iya zubar da kimana da darajana don kawai ina son wani ya gyara halinsa.
Yana zaune ya dafe kanshi da hannu daya kamar yadda ya saba idan yana cikin damuwa a hankali ya juya yana dan sauke ajiyan zuciya.
Ya zubawa desktop din dake gaban shi ido ya rasa gane me yasa ya kasa cire tunanen wanan yarinyar a zuciyar shi haka ?
A hankali kifa kansa saman hannun shi tabbas yana da yakinin yanzu ba tausayin zainab da kuma son ya taimake kamar yadda yai alkawari da farko bane.
Yana jin burbushin wani yanayi daba zai iya fassara ko me ye ba a zuciyar shi don yarinyar ta zame mashi kamar wani bangare na rayuwan shi a yanzu don yana jinta kamar ba zai iya rayuwa mai farin ciki ba idan yai nisa da ita.
Sai dai yana matukar tausayawa kansa da yarinyar domin kuwa yasan idan zasu tabbata a haka rayuwan su a cikin garari zai tabbata don ba zai iya tabukawa kansu komai ba a zaman su.
Kamar an tsikare shi ya dago a yadda yake da sauri yana fadi a fili idan ta gujeni fa don sanin koni waye a yanzu ?
Ko kuma ta kasa boye hakan a zuciyar ta har ta fadawa wani wanan maganan da yake siri a tsakanin su don yarintan da yake a kanta tayi kankanta rike wanan sirin a zuciyar ta yanzu.
Wayan shi ya zaro daga gaban aljihun yana kokarin kiran layina sai a lokacin ya tuna ai banda layin kasan nan da zai kirani dashi a yanzu.
Wani wawan tsuki ya sake tare da fadin Oh shit wanan wani irin wauta nayi da sakaci ai hakan sai na kara saka zargin wani a kan hakan .
Mikewa yayi tsaye lokaci guda yana shirin fita daga office din tare da tatara kanyan shi dake yashe saman table din.
Daga haka ya fito da sauri drivern shi daya hangoshi ya karaso inda yake don ya karbi yar jakkan dake hannun boss din nasa.
Mota ya shiga baya an bude Allah Allah yakeyi ya isa gida yayi mata warning kan zancen don ya fahinci ta dan warware da safe kafin ya fita.
A falo muke zaune muna hira dasu mama da suka shigo suna ban labarin sun hadu da wata yar kasan data dinga zuba masu yare a cikin masifa suna mayar mata da zagi da hausa.
Muna cikin dariyan hakan sai ganin shi mukayi a daidai lokacin ya shigo duk da ba a daidai lokacin yake dawowa gidan ba.
Idon shi a kaina daya shigo falon yana mamakin yadda ya sameni yau ina dariya don bai taba samuna a haka ba tun zama a gidan nasa.
A cikin daurewa da danne zuciyana na samu kaina da masa sannu da zuwa ina danne zuciyana don har lokacin ina mai jin kyaman shi don ina kallon a cikin yanayin dana ganshi a ranan.
Amsawa yayi a cikin basarwa kamar yadda ya saba yi ako yaushe yana kokarin shihewa muka samu muryan shi yana fadin ke zainab zo ki sameni a ciki daga haka ya shige zuwa part din sa.
Ina mamakin jin haka a raina na tsinkayi muryan mama tana fadin kai wanan yar da shirme kike har yanzu miji ya dawo baki tashi ki taresa irin na yan zamanin nan har sai ya bukaci hakan a gareki ?
Dan turo baki nayi a gaba ina nuna bazan iya hakan ba halimatu ta saka min dariya na juyo ina fadin mama zan mari wanan yarinyar fa idan bata daina ba.
Jeki zan mata fada mama ta fada itama tana kunshe dariyan ta dan wautan yarintar data gani a fili a gareni tare da fadin shi kuma jafar abinda ya sayawa kansa ke nan yanzu ?
A part din nasa na sameshi a falon shi tsaye yana sintiri kamar wani abu na damunsa a lokacin na shigo na sameshi a hakan.
Banyi magana ba ya juyo yana kallona na dan lokaci kafin yace me kike fadawa su mama ?
Ban fahinci tambayan ka ba na tambaya a hankali naji yace kin fada masu ke nan ko ?
Me na fada na sake tambayan shi cikin karfin hali ido ya tsura min kamar yana son fahintar wani abu a gareni kafin ya juya yana fadin shike nan ya fara tafiya.
Ai basai na fada masu ba inshine tunanen ka kai da kanka idan baka daina ba zaka sheda masu kokai waye watarana.
Wani irin juyowa yayi lokaci guda yana kallona ni babu fa,idan fadin wanan yanzu a bakina do abin kunyane a gareni don haka inama fatan Allah ya rabaka da wanan kazamin hali naka a yanzu yaya.
Daga haka na juya na fara tafiya na barshi a wutin cike da mamakina nima tafiya nake ina mai yaba karfin halina na yaba bajinta na haka a gareshi lokaci guda.
Ina fadi a fili ashe zan iya kamar yadda ya jamal ya gaya min saina cire tsoro a zuciyana na dasa mashi shakkana da tsoro a ransa.
Dakina na fada na mayar na rufe tare da fadawa saman gado ina runtse idona wasu hawayene suka silalo min lokaci guda.
A fili na furta yaya meyasa ka zabi wanan rayuwan a tsakanin rayuwan da zata zubar maka da darajan ka da kimarka a idona lokaci guda.
Me ake da dan giya a rayuwa gara in rufe ido in koyi tujara akan hakan tun yanzu don in samu makamin yakarshi akan wanan harkan.
Shima mamaki ne ya kasheshi a wurin wai haka yarinyar nan take dama koko yanzu ne ta fara hakan don ganina da tayi a cikin wani yanayin da bai dace ba.
Zanyiwa tufkan hanci tun kan raini da wullakanci ya shiga tsakanin mu nan gaba da ita don ba zan lamunci karamar yarinya ta rainani ba.
Zuciyar shice ta bashi amsa lokaci guda da fadin kai ka ja da baka yarda ta ganka a wanan halin na buguwa ba.
Ido ya runtse lokaci guda yana maijin zafin kansa akan hakan ya bude kofa ya shiga dakin ya bi da kallo lokaci guda.
Sai lokacin taju da yaima korar kare a ranan ya fado mai a zuciya don gashi yanzu yana son shi a kusa dashi ba halin hakan don yadda yake jin kansa yau ba zai iya daure hakan ba.
Kayan jikin shi ya dan tage ya shiga bandaki ya watsa ruwa a jiki shi ya fito sallah ya gabatar kafin ya fito don yaci wani abu a cikinsa don rabonshi da yaci abinci tun daren jiya daya dan sha wani ferfesun da suke sha wanda ke kara masu karfi a jiki.
Falon ya fito tare da danna kararawan kitchen don kiran daya daga cikin masu dafa abinci a gidan julie ce ta fito da sauri don tasan kiran maigidan ne a lokacin don shi kadai ke danna kararawan kiran su bakinshi basu taba kiransu haka ba.
Tazo ta dan duka cikin girmamawa tare da fadin can i help you sir ba tare daya dago kanshi yace ta kawo mai abinci yaci ta juya da sauri tana fadin an gama.
A daidai lokacin ne kuma na fito daga part dina zuwa falon wanan karon na sauya kayan jikina zuwa wando da riga masu kame jiki don fara gwada shawaran anty fadila dana yanke a raina.
Tafe nake kamar bansan yana falon ba zaune na nufi wurin tv ina kokarin kunnawa tun shigowana falon ya sauke idon shi a kaina.
Da sauri ya kawar da kanshi kamar wanda yaga wani abin tsoro a lokacin yana dan shafan kanshi don dan kwana biyun nan da yayi bai sha komai ba ko shakawa.
Yana jin kansa a wani irin yanayi na daban da ke sakasu a cikin wani hali har zuwa lokacin da julie din ta kawo mai abincin kanshi na duke a kasa yana shafa a hankali don yanayin da yake jin kansa a lokacin.
Tana ajewa take sanar mashi ya dago kai da jajayen idon shi da suka rine masa yakai kallon shi ga abincin .
Kiran ta yayi don har ta juya zata wuce ciki yace ta dawo ta bude abinda ta dafa din daga inda nake ina jiyosu nace ta tafi ta barni in bude mai na fada cikin dakewan zuciya.
ZAINAB IDRIS MAKAWAA hankali na fara takowa daga inda nake tsaye zuwa dining din a cikin tafiya mai kama dana hawainiya da nakan yi idan ina tafiya don sayin halina bai tsaya iya halina ba kwai har yanayin magana na da tafiyana a cikin sanyi nakeyin sa wanda sai mutum ya dauka sallone ya mayar dani hakan.
Ba iyanan abin ya tsaya min ba don har yanayin kukana idan ina yi a kusa da mutum sai zuciyar mutum ya shiga wani hali a lokacin don tausayi.
Gabana na faduwa na karaso inda yake zaune a gurin daning din a cikin tafiyana mai kama dana hawainiya da zaka dauka sallone ya mayar min da tafiya hakana.
Har na karaso inda yake zaune yana mamakin sauyina a cikin lokaci guda na yadda na sauya ma sanin da yayi min da farko na mika hannu a hankali na fara bude warmer din dake gabana har lokacin yana zaune ya rike haban shi da hannayen shi duka biyu ta hanyan yin tagumi dasu yana kallona.
Wani irin ferfesu na gani a ciki tare da wasu irin ganyayyaki da wani icce da ban san ko na meye ba na nufi dayan kulan zan bude naji ya dakatar dani yana fadin zuba min wanan din.
Da mamaki na juyo na dan kalleshi har lokacin yana zaune a yadda yake saidai wanan karon bani yake kallo ba.
Plate na jawo na soma zuba abinda ke cikin warmer din a hankali saida yagaji ya bude baki da kyat yana fadin ya isa hakana mana a cikin dakewa.
Mayar da marfin nayi na rufe naja kujera daga gefe daya na zauna ya dauki spoon ya fara kurban ruwan a hankali ta hanyar ja a cikin sallo.
Duk ina zaune gefen shi ina kallon shi ba tare dana motsa a inda nake zaune ba shi kuma ya mayar da hankali yana kurban abinsa hankali kwance.
Sai mamakin haka nakeyi a zuciyana a daidai lokacin ne wayan shi yai kara kamar ba zai daga ba ya dauka daga inda yake zaune.
Turanci mai kama da yaresu na chaina yakeyi naji yace outside da dan karfi kafin ya kara magana aka shigo gidan a daidai lokacin.
Mutum hudune dukkan su uku suna da kama da yan kasan sai na hudun nasu ne launin shi ya dan bambamta da sauran.
Tunda na daga ido na kallesu naji sam basu kwanta min a rai ba don yanayin shigan su ma yana nuna basu da tarbiya ko kadan.
Ina zaune a yadda nake a wurin ban ko motsa ba balle alaman tashi don shigowan su din sai dai a cikin daurewa nake zaune don yadda suka sameni a lokacin jikina babu hijjab a tare dani.
Duk wani iskancin da suka shigo dashi lokaci daya suka shanyeshi a fuskan su sai sukayi wani irin sayin a wurin.
Barin ma shi philis daya fi kowa iya iskancin don baida kunya ko kadan shi a gaban kowa yana iya nuna halinsa.
Addua nake a bakina kamar yadda malam yace inyiwa wanda duk ban yarda dashi da zarab zamuyi arba da maishi.
Yar uwa addua kan gaskiya ne don shi philis din da numfashinsa ya kusa daukewa yake tambayan zuciyar shi wanan wace irin kyaune da ita haka kamar ba black girl ba ?
Tun kan su zauna dayan ke kallona yake fadin wanan queen din fa kanwar kane Jackson ko yar uwarka koko ka fara harka da matane kuma ?
Sai dai wanan din ai tayi kankanta da yawa gaskiya sai dai idan sister din kace ko ?
Wani kallo ya watsawa philip din lokaci guda yana fadin wanan ba business din ku bane kun shigo muna gida haka babu notices bayan kun san family dina na gidan nan.
Mu kuma ba haka addinin mu ya koyar damu shiga gidan da yan uwa suke tare da yardewan mutanen gidan.
Dukkan su dariya sukayi idon su na a kaina kara daure fuskana nayi garesu don kar suga damana a lokacin .
Mikewa nayi a lokacin Allah ya taimakeni ina saye da wani bakin dogon riga nawa na larabawan jordan mai shara sharan hanaye sai dan dinkin maternity daga zuwa wuyan rigan don yana da fadi bai matse min ba a jikina.
Cikin wani irin murya da ba yaya din ba harsu din sun mutu a saurare duk da basu jin yaren da mukeyi nida shi nake fadin.
Ka karasa ci ne a kwashe kayan yanzu aifa tuni yanayina ya tafi da imanin su lokaci guda har wasun su na rayawa a ransu wanan ai mutum zai iya gwadata ya gani a cikin mata.
Ki barshi julie zata fito ta kwashe ki koma ciki kawai yanzu ya fada fuskan shi a daure saida abin yaso ya bani dariya sai na fuske na fara tafiya don barin wurin.
Shima yaya mikewa yayi yana kallon agogon hannun shi yana fadin kuna nan ke nan don ni fita zanyi yanzu.
Duk wani kallo suka bishi dashi lokaci guda suna mamakinshi don yin hakan da yai masu kafin su mike subi bayan shi zuwa waje don shi har yakai kofa a lokacin.
A wajen gidan suka sameshi ya dafa kan mota ya dan bada nauyin shi ga motar suka sameshi a wurin suna fadin.
Kamar bakai murna da zuwan mu ba yau gidan naka bayan babban tukwicin da mukazo ma dashi har gida bayan ka kori tj a gidan ka musan yanzu kana cikin matsuwa a dan kwana biyun nan da kayi ba harka a tare dakai.
Sai lokacin ya dago daga yadda yake yana sauke idon shi akan saurayin da suka kawo mashi har gida wanda suke kira da sunyi mai sabon kamu har gida.
Don yaron dan kasan Egypt ne sabon dan hannune shi farkon shiga harkan shi ke nan a yanzu don haka sukaga ya dace da jacksom din .
Wani irin kallo yakewa saurin da yake tsaye yana dan wani kame jikin shi kamar wata mace sabon shigan karuwanci a fagen maza.
Tsab ya gama kallon saurayin kafin yayi murmushi yana fadin a cikin wani yare kasan nafi son baki kamana don nafi ganewa hakan.
Dariya suka saka tare da fadin ka dai gwada wanan din ka gani zakaji dadin zama dashi sosai don yaron zai iya dakai a yadda yaken nan sosai.
Dan murmushi ya kakaro a karo na farko a fuskan shi tun zuwan su gidan ya bude baki da kyat yana fadin ya gode da kulawan su gareshi.
Ya riko hannun yaron zuwa gareshi tare da jawoshi jikin shi a daidai lokacin ya jamal ya shigo gidan idon shi kan abinda yake faruwa.
Bai tsaya kulasu ba ya wuce abinsu cikin jin haushin su gabadaya don ya gane mai ake kullawa a wurin .
Saboda yasan taju yabar gidan tun washe garin daya dawo gidan a buge yaji suna fada sosai da taju din har yakai yai mashi korar kare ta yadda ba zai iya dawowa ba gidan lokacin.
Bin ya jamal din sukayi da kallo kafin yace kai wanan lafiyayyen guy din fa haka ko kayi sabon kamune ko bamu sani ba ?
Wani kallo ya sakewa mai maganan kafin yaji dayan na fadin amma wanan ai suna da kama sak da jackson wata kila dan uwansa ne na jini ai.
Sai gudan yace amma guy din ya hadu ya shima dan hannu ne in tayashi don nidai guy din yayi min wallahi.
What ya fada da karfi tare da fadin blood brother dinane fa kake fadan wanan maganan a kansa.
To meye a ciki don na nemi dan uwan ka a harka bro ina duk karuwan kan mune hakan da inje waje ina neman wasu .
Zuwa lokacin ran yaya jafar din ya kai kololuwar baci don ji yake kamar ya shake abokin nasa a wurin saboda takaici.
Kadai rigani magana ne don ni gaba daya ya tafi da imanina a wurin nan don guy din ya hadu sosai.
Dayan ya karbe da fadin saidai baku ganin cewa duka yan uwan nasa suna da jin kai sosai don gaba dayan su babu wanda ya gaida mu.
Don ko kallo bamu ishesu ba dukko yadda muke da daraja a gari nan ake girmamamu sai gashi su ko kallo bamu ishesu ba ai.
Cikin wani tsawa ya dakatar dasu yana fadin zan halaka mutum a wurin nan idan baku rufe min baki ba yanzu da kazamin maganan nan naku.
Kallon yanayin shi sukeyi don sun fahinci ranshi ya gama baci a lokacin ga baki daya kafin suji yana fadin.
Ai wanan wullakanci ne da cin zarafi ku rasa wanda zaku danganta da wanan abin sai dan uwana na jini.
To bari kuji shi wanan harkan da kuke ganin munayi kowan ku nan yasan da addinin shi bai yarda da hakan ba.
Idan baku sani ba yau ku sani a kullun ina mai nadaman shiga wanan harkan naku da kuka koya min wanda addinina da al,adana duka ya haramta wanan abin ga wanin mu.
Yau gaskiya nayi nadaman sanin ku a rayuwana tunda har zaku iya kallon kanina ku nuna mashi sha,awan ku a fili babu dayan ku nan da ban ganin girma da daran dan uwanshi koda yan aikin gidan ku ne.
Daga haka ya juya rai bace ya bude motarshi ya shiga yana kokarin barin su wurin ranshi a bace.
Ganin hakan yasa suka san ranshi ya gama baci sosai alokacin da maganan su don sanin halin shi da sukayine zai iya sharesu har abada ga baki daya daga wanan lokacin.
Ganin ya shiga mota yana kokarin tayarwa ya wuce suna bashi hakkuri ta hanyar daya dace yasa ya jamal din sauke numfashi yana barin wurin da yake tsaye yana sauraren su a cikin takaici ya shige gidan.
Babu kowa a falon kai tsaye ya wuce zuwa part din shi yana mai jin zafin hakan daya faru a zuciyar shi.
Yana jin da zai iya a ranan zai bar gidan dan uwan nasa ya koma Nigeria saidai hakan ba zai yiyu ba don dole ya tsaya kodon hjy dake asibiti da kuma mu da muke zaune a gidan cikin rashin sani.
Don haka yaba kanshi hakkuri yana mai fadi a ranshi cewa fushi yanzu ba nasa bane idan shi yai fushi da dan uwan nasa mu yaya zamu kasance kuma ?
Bamu hadu dashi ba bama wada yasan da dawowan shi gidan a lokacin sai bayan sallah magariba da muka fito falo muka ganshi ya fito falon ya samemu muka gaisa dashi a wurin.
Mamane ke tambayan shi kona biyun nan wai meke damun shi ita fa batagane yadda ya canza ba akwana biyun nan idan anyi magana yace ba komai alhalin ba haka tasan shi ba a baya.
Mama banu komai wallahi ni dai kawai yanayin garin nan ne bai mun ba mun saba a gida muna ganin yan uwa da abokai ko ina.
Ta katse shi da fadin kai banda abinka baka ganin yaran nan matane basa fita ko ina amma a haka sun sake jikin su suna sha,anin su a gidan nan cikin rashin damuwa.
Balle kai na miji kamarka kana nuna haka a yanzu mu mata muce me ta fada a cikin raha.
Daga inda nake na saci kallon shi na fahinci akwai wani abinda ya bata masa rai a lokacin saidai banyi magana ba fun zaman shi a wurin suna ta hiran su da mama kan ciwon hjy da ake samun saukia yanzu kan jikin nata .
Don ko yanzu za a iya sallaman ta ta dawo gida saidai dan binciken da suka tsaya yi a kanta ya hana a sallamota daga asibitin yanzu.
Mikewa nayi don tunanen daya addabi zuciyana a lokacin na dan kallesu ina fadin mama ni zan shiga daga ciki .
Ke ko tun yanzu muna nan muna rage dare don ni wanan shiga kwanan da wuri haka ya fara isata wallahi aiba jamal shi kadai zaman garin nan ya isa ba a yanzu harni nan zama wuri dayan nan ya isheni wallahi.
Gashi mijin ki dawowan shi ba maza ba a gidan nan niko yanayin aikin nasane yake haka har dare ko wani lokaci dan gara yau ma ya dawo gidan nan yau da wuri.
Dan murmushi nayi ina gyara zamana ba tare da yin magana ba a lokacin sai naji ya jamal na fadin kila ta gajine da zama ai.
Ina fa gajiya ai bata dade da fitowa ba kazo kila dai don ta ganka zaune wurin nan ne take son ta tashi.
A,a mama ya jamal ai tun ina gidan mami mun saba dashi yana daga cikin masu tausaya mi a lokacin dashi dasu ya mamud .
Mu din ne bama tausaya maku ashe ta fada tana kallona a cikin zolaye nace da sauri a,a mama ba haka nake nufi ba wallahi kowama yana sona sosai wallahi.
Ai baki sani ba zainab wallahi ban gama danin halinki ba sai a dan zaman nan namu nan yanzu na kara tantace koke waye.
Gaskiya jafar yayi dacen mata idan kun dore a haka don ba ko wace sarakuwane tasan darajan iyayyen mijinta kamar yadda kike nunawa din.
Dadin wanan yabon da mama tayi min a yanzu naji na dukar da kaina ina dan murmushi kasa kasa naji tace kai gaka ba wani sakin fuska kakewa dan uwanka ba kwanan nan aida gobe sai mu rokeshi mu dan fita yawon mike kafa .
Tunda hjy dai taji sauki ba kamar yadda mukszo kasan nan da ita ba a cikin tashin hankali lokacin.
Taji sauki yanzu kan sai dai kuma yanzu data dawo zata fara fitina da mutane kamar yadda ta saba yi a kullun .
Dakuwa mama ta mika mai daga inda take zaune tana fadin ja,iri ai kuma naga hankalin ku ya tashi ai data kwanta ciwo.
Yana dariya ya mike tsaye yana fadin mama ni zan shige akwai dan wani aiki da zanyi matar yaya saida safe ke nan ya fada yana kallona.
Har muka tashi a gurin ya jamal dake dakin shigewan mu yana jin mu nikan ina shiga dakin ban daki na shiga na dauro alwala na fito.
Nafilan da na saba yi duk dare kafin in shiga wanka nayi kafin in dora da shafa,i da wutiri na mike na gyara jikina tsab yau da yake mun dan dauki lokaci muna fira a falon sai yasa ban samu zuwa na kwanta a makwancina da wuri ba.
Na gama tsab na jawo kofana lokacin wata zuciya tana fada min inyi kwanciyana kawai a dakina tunda dare yayi a yanzu.
Saidai na wuce kada hakan ya jawo min laifi a wurin shi kuma tunda mun aje hakan dashi tun zuwan mu garin.
Na fito na jawo kofana na rufe na nufi hanyar part din shi kai tsaye sai dai nayi mamakin ganin kofan a rufe a ranan.
Murdawa nayi don ina jin dan kida yana tashi a ciki yasa nasan baiyi barci ba a lokacin idon shi biyu wata kila yana falke yana sana,arshi ta latsan waya ko computer.
Kofan na dan duka kusan sau uku a lokaci daya naji na a bude ba don haka nayi niyar juyawa in koma dakina.
Naji ana bude kofan haka yasa ni waigo don na koma in shiga tunda ya bude part din a yanzu.
Saidai ana budewa ne idona yayi tozali da wani farin matashi a tsaye daga shi sai tawul daure a kungun shi yana rike da kofi a hannun shi da wani abu a cikin sa.
Da mamaki nake kare mai kallo a cikin wani yanayi dana kasa gane koshi waye da har ya shigo part din yaya din kuma gashi daga shi sai dan tawul a jikin shi.
Muryan yaya naji daga bayan shi dake fitowa daga cikin daki yana fadin who is there ?
Cikin tambayawa sai saurayin ya jaye daga kofan don yaya din ya hangoni shima dai yana daure da towel kamar daurayin na farko.
Wani irin faduwa gabana yayi lokaci guda nake kallon shi da mamakin ganin haka karara a fuskana.
Yanayin fuskan shine ya canza lokaci guda munayin arba da shi a wurin yake fadin ke mekikeyi har yanzu baki kwanta ba.
Saida nayi mai wani kallo na raini na sauke akan cup din dake hannun shi na juya ba tare da na bashi amsa ba na koma dakina na rufo da makulli.
Saman gado na fada lokaci guda wanan karon ban iya yin kuka ba sai tambayan kaina nake me nagani me sukeyi haka a ciki ?
Ta yaya shi yaya zai yarda ya kawo wani bako a part din da muke kwana a tare har zai yarda wani bako yazo haka ya kwana a ciki harda tubewa haka dashi.
Anya waiko yaya yasan addini kuwa yasan abinda shari,a ya tanada kuwa yau aiko matsayin kanwarsa nake bazai kawo wani kato a part din shi ba yasan ina cikin part din kuma.
ZAINAB IDRIS MAKAWABan fito daga dakin ba sai dana kwatanci fitan shi a gidan don wanan abin na daren jiyan daya tsaya min a raina.
Ina mamaki duk dakunan dake wanan gidan ya jafar ya rasa inda zai sauke bakon shi sai part din shi alhalin yasan bashi kadai bane a part din nima a nan nake kwana.
Anya kuwa ya jafar yasan addini kuwa sosai ai ko ba matar shi nake ba zaman kanwarshi nakeyi a gurin shi balle wanan kasan mutane da nazo ta dalilin shi.
Ya kamata ace ya tsare min mutumcina da kimana na ya mace a gurin kowa balle kuma ina zaman matarshi ta sunna a yanzu.
Idona kodai kodai sai dan fuskana daya kara yin fau ya wani zuke saboda kwana a kusan rayen da naye a daren jiyan .
Nayi mamakin ganin ya jamal a gida shi da yake fita tun safe zuwa duban hjy a asibiti sai gashi yau na ganshi a gida tare dasu mama a falo zaune.
Gaba dayan su ido suka zuba min har na karaso inda suke zaune ban zauna ba saida naje gaban mama na tsugunna na gaida ita da kwana.
Kafi in juyo wurin ya jamal shima na gaida shi ta amsa tana fadin yanzun ko maman ku ta bugo waya tana tambayan ki nace baki tashi ba tukun.
Ashema kina falke ban sani ba na tashi tun dazun mama bandai fito bane kawai ina ciki ina fitar da kayan wankina.
Wurin halimatu na juya ina fadin halimatu lafiya kuwa don yanayin ta danaga ya canza lokaci guda.
Ta dan nisa tare da fasin yayan mu ina kwana ashe ba barci kikeyi ba ma ?
Lafiya kalau take don yanzu take muna zuba a nan tana bamu labarin karatun ta ana dariya kece ma dai yanayin ki ya nuna kamar dai baki da lafiya yau.
Lafiya ta kalau mama na bata amsa ina mikewa tsaye sai naji halimatu na fadin yayan mu ina wanan rigan da nazo dashi sabo shi nake son in saka yau jumma,a.
Yana daki mana ki duba na bata amsa ina zama sai take fadin ban ganshi bane tunda mukazo kuma naga kin dauko min shi.
Na dauko mana yana daki ki duba kafin in gama magana mamata mike tana fadin barin kdan kewaya na fito yanzu da wanan rigiman na sadiya don ni kadai ke kiranta da halimatu kamar yadda muka saba tun a gida.
Barin mama wurin yayi daidai da barin halimatu don haka aka barni dagani sai ya jamal zaune a wurin.
Sai dan shiru ya biyo bayan hakan can na dago kai na dan kalleshi nace ya jiya ya jafar ya ban mamaki a gidan nan.
Banso na fada ma wanan maganan ba amma ya zama dole in fada mashi a yanzu don shi kanshi yaya yasan haramun ne sauke bako haka balagage a part din shi kuma yasan ina a cikkn part din.
Wani kallon mamaki ya jamal ke min hakan ya hanani ci gaba da maganan da nake son fada a lokacin.
Kai naga ya girgiza yana fadin nasan ba zaki so hakan ba idan kin gani don ke ba jahilan addini bace zainab don nasan kinsan kanki duk da kina yarinya karama.
Da sannu zaki fahinci abinda ni na kasa fada maki daga cikin halayai shi saidai ke wani mataki kika dauka da kikaga hakan ?
Na bude baki da zuman magana naji halimatu na fadin nifa ban gani ba yayan mu sai kuma muryan mama tana fadin kijeki duba mata tunda yau fitina take ji kan riga kamar karamar yarinya dake tana hararan ta.
Mikewa bayi don bin umurnin mama din muka jera zuwa ciki da halimatu din muna shiga dakin take fadin nafa ga rigan yayan mu.
Dama ina sin ki tasone in fada maki abinda mami ta fada a kanki da ta kira wayan wai cewa tayi dake wai kece yar mulki dan tallaka bai iya samun wuri ba za a ce har yanzu kina kwance kina barci.
Inji mami din ta fadi hakan don Allah daga yau kome mami ta fada a kaina kada ya kara damun ki kuma ki bar fada min don in banji ba banji bane kin gane ko ?
Ta gyada min kai alaman eh nace ai sai ki dauki rigan ki saka a jiki kada su fahinci abunda kikazo fada min ke nan yanzu a daki.
Tace ai ya jamal ya ce mata mulkin me kikeyi bayan ke ake cuta a kullun don dantane ai mai mulki sai tayi dariya tana fadin yai min daidai ai ba dai taji dadi a gidan nan ba wallahi tunda tace ita yar naci ce da kwadai zataga wullakanci saita raina kanta wallahi.
Niko basu san ina jin komai ba don ina tsaye daga kofan shiga part din mu nake jin komai.
Ido na tsura mata ina mata wani irin kallo kafin ince watau halimatu bakya ji ko saidai da kika fada min komai yanzu.
Ai na bari tunda kince in bar fada maki wanan din ne kadai na fada tana wani turo baki a gaba tare da daukan kayan dake gabata data fitar ta saka ta fice a dakin.
Zaune ta barni ina faman tunane sai yaushe mami zata daina hattarana kan dan ta ne dan da ba wani dadin zama dashi nake ji ba a tare dashi.
A hankali na mayar ds idona na runtse wuri daya don yanzu na daina wanan ruwan hawayen da nakeyi saidai yawan tunane kawai da shiga halin damuwa.
Duk aikin da yakeyi a ranan rashi bace yake idan ya tuna abinda ya faru a daren jiyan tsakanin mu ya rasa laifin waye a cikin mu har hakan ya faru.
Shin laifina zai gani ko laifin Nabil daya bude kofan ko kuma laifin shi da sakacin shi yasa har hakan ya faru.
Da bai bada daman in shigo shiyan in dinga kwana saboda dan maganan da mama tayi ba da duk haka bai faru ba a daren jiyan.
Inda Allah ya gyara banga komai daya faru ba a tsakanin su da tashin hankalin da zai shiga a yau yasan yafi wanan girma.
Da yanzu asirin shi ya gama zubewa a idon kowa don yasan ba zan iya rike kaina ba a lokacib mutane zan tara masa a gida don wauta.
Gashi har raini yana son shiga tsakanin mu don dan abinda idona ya ganar min ranan yakai yanzu ban tsoron shi kamar da can baya.
Ji itin kallon dana watsa mai a daren jiyan da sauri ya tambayi kanshi ko dai yarinyar nan tasan abinda nake yine tayi min irin wanan kallon ya tambayi kansa.
Da sauri ya girgiza kanshi tare da fadi a cikin hausa kai ina bata gane komai ba kawai dai nike tunanen hakan.
To wanan kallon tsanar fa na meye take min shi haka a daren jiyan don kawai ganin wanan gay din a karo na farko a part dina ?
Koma dai meye ya zama dole in canza komai yadda wani bazai taba fahintar komai ba saidai jamal fa ya tambayi kansa yana dan murza goshin shi.
Idon shi ya lumshe yana dan juya kujeran da yake zaune a kai ya zurfafa a cikin tunane.
Karshe ya furta a fili wama zai yarda da wanan idan har sun fada tunda ba ganina akayi dumu dumu ina aikatawa ba ai.
Zan fara da zainab don dole in tsawata mata kan ta fara zargina da wani abu na tabbatar da haka zata ja bakinta ta rufe gum.
Har yamma ranan bai samu tsinana komai ba a office ya dai kula zuwan su a garin nan yana son ya jawo mashi koma baya aikin shi a yanzu don haka sai ya jajircewa abin.
Dama hakan yake gudu ya faru dashi gashi kuma yarinyar da yake dauka ba wayau komai a tare da ita tana shirin jawo mashi matsala babba.
Ya mike yana mamakin kansa wai yau shine da jin kunya da nauyin arinyar daya raina ma wayau ya fito daga office din driver shi yazo ya jashi saida suka hau hanya yake tambayan shi inda zasu tafi asibiti ya bashi amsa ba tare da dago kai ba.
Ya samu hjy a zaune tana shan fruit salad da jamal ya sayo mata don tana yawan shan yayan icce sosai tun a gida yasa tun ranan data fara sha take sa ya sawo matashi tasha don yafi mata wanan abincin nasu na kasan dadi a bakinta.
Turo kofan yayi da sallama sukai arba da jamal dake zaune a gefen gadon yana duban yadda take shan fruit din a cikin tausayin ta.
Shima idon shi ya mayar kan tsohuwar data dago tana amsa mashi sallaman shi tare da fadin a,a maigidan ka samu isowa ke nan ?
Ina nan tare da wanan sabon mijin dake son kwace maka ni a yanzu don naji na fara son shi a yanzu fiye da kowa.
Dan murmushi jin abinda take fada ya karaso bakin gadon dashi yana fadin kinji sauki ke nan tunda har kin fara zancen miji yanzu.
Yo za a fasa zancen mazane tunda gaku har ku biyu a gabana ai duk inda kaga mata sun kai uku a zaune zancen ke nan balleni da har biyu ke bori a kaina koma ince uku don mamud ma kullun muna gaisawa dashi a waya.
Kice ke kasuwane dake haka ashe ban sani ba zan jaye don ba zan iya takara da kowa ba akanki don haka daga yau a fitar dani a cikin lissafin mazan.
Mikewa ya jamal yayi zubur ba tare da magana da kowa ba ya nufi hanyar fita daga dakin hjy ce tasa murya tana fasin kai kuma jamilu ina zaka a zaune kalau.
Fuskanshi ya dan bata kafin yace zanje nan wajene in dawo ba dadewa zanyi ba ai ya fada yana kokarin tafiya.
Yaka zo nan nawa ta fada a cikin damuwa don tana lura a yan kwanakin nan kusan haka suke da dan uwan da zaran ya shigo sai jamal din ya fice daga dakin.
Daga inda yake tsaye yana kokarin zaunawa yace barshi kawai ya tafi ba gani ba a a jafari ba yau ba ina kule da abinda ke wakana a tsakanin ka da dan uwan ka yanzu ?
Zama yayi yana murmushi ba tare daya kalli idon tsohuwar ba jamal din dake kofa a tsaye bai juyo ba bai kuma wuce ba.
Ta yaya kuke zaton zumunci zai dore a haka kai karami har kayi karfin halin yin fushi da yayan ka meyayi zafi haka tsakanin ku har ya kawo wannan ?
Kaine babba jafari a sanadin ka kuma muke zaune a kasan nan yanzu don me ba zakayi hakkuri da kanin ka ba koma me yayi ma matukar abin bai sabawa addinin ku ba .
Wani irin malolon bakin ciki jamal din ya hade kafin ya juyo yana fadin a cikin daurewa nifa hjy babu komai a tsakanin mu .
Don haka zan tafi ya fada yana kokarin juyawa ta mika mashi dakuwa da hannun ta tana fadin karbi nan dan nema ka maidani tsohuwa ban san komai dake wakana a gabana ba ko yanzu ?
Bajin dadin uwarku bane ta sameku a wanan halin don babu uwarda keson ganin rashin jittuwa a tsakan yayayen ta ba a duniyan ko wacecw kuwa.
Basai naji abinda ya hada ku fada kaida dan uwan ka ba kuyi kokari dai ku dinga tausa zuciyar ku don Allah .
Koma meya faru a tsakanin ku don Allah babu komai hjy shi yarone ai yasa yake wanan fushin dani haka ya jafar ya fada.
Wani irin kallon tsana ya watsawa dan uwan nasa kafin yace in ni yarone ai Allah ba sa,an kowa bane yana kallon duk abinda bawan sa keyi a ko ina yake daga haka ya juya ya bar dakin tare da barin hjy da mamakin shi.
Don bata taba ganin yayi fushi irin haka ba a gabanta ta juya tana kallon jikan nata dake zaune a gefen ta tana fadin.
Akwai wani abinda kake aikatawa ne mara kyau jafari don wanan kalamin nasa ya sakani a cikin duhu sosai.
Ki tambayeshi mana hjy shida ya fada ni dai nasan ban aikata komai ba da har zai fadi hakan ya fada cikin daure fuskan shi.
Dan hira mai kama da nasiha hjy ta dinga jansa dashi har suka kai wani lokaci kafin ya mike yana fadin shi zai tafi don zai biya wani wuri kafin ya karasa gida.
Sai bayan fitan shi ba a dade ba jamal ya shigo mata da leda a hannun shi yana sallama ta kalleshi ta kawar da kanta gefe .
Au fushi kike dani don kawai na batawa masoyin ki rai hjy to tunda bakya son gani na bari in koma inda na fito ashe.
Ka koma Nigeria idan ka tashi tafiya dan nema marasa ta ido har zaka tsaya kana daukan wanan zafin haka da dan uwan ka dake gaba dakai.
Hjy ke nan ya fada yana girgiza kanshi tare da fadin bai fada maki abinda ya hadamu ba ke nan ya tafi ?
Saida ta dan harare shi take fadin kai ka tsaya ayi maganan ne daka fita ku dai daina hakan baida kyau wallahi irin haka ke kawo matsala a cikin zuria kaga na baya yana raina na gaba dashi idan an saka ido sai abin yai girma.
Hjy badai gaisuwa bane ya jawo hakan to zan gaidashi zancen ya kare hakan yai maki ko ya fada yana kallon fuskanta.
Dan mere baki tayi tana kallon shi daga saman har kasa tana fadin zauna naga kamar abinci ka sayo zakaci yanzu ko ?
Naci a waje ya bata amsa wanan kena sayowa shi yana kokatin bude ledan daya aje a gefen shi kamshi ya bure dakin.
Muna zaune a falon don mama tafi son taga mun hadu wuri daya tana jan mu da hira har hakan yakai mun dan saki jiki da ita tunda ma halimatu da yanzu suke daki daya da ita.
Ya shigo da sallama shi duka muka waigo muna amsa sallaman tare da gaidashi da dawowa .
Zama yayi akan daya daga cikkn kujerun falon suna dan hira da mama wanda gaisawane tare da tambayan ta idan ba matsalan komai ?
Naso na share shi amma sai naga rashin dacewan hakan a gaban mama don ko a lahira wani nacin albarkacin wani.
Na mike zuwa kitchen din gidan wanda baifi shigana daya ba tun zuwan mu gidan sai kuma yau din dana shiga.
Na fito daga kitchen din ina saye da dogon rigar atampa a jikina wanda akai mai dinkin free haka tunda na sanyo kai a falon gaba daya ya maida hankalinsa gare ni.
Ya zuba min ido yana mamakin irin girman dana kara lokaci guda har na iso gareshi bai kawar da idon saba a kaina.
Cup din da goran ruwa dana dora a tire na aje agabasa ina fadin ga ruwa yaya bai iya amsa min ba na dago na wuce ta gaban shi.
Ga ruwa nan matar ka ta ajema a gaban ka mama ta fada tana kallon shi duk da ya nuna bani yake kallo ba a lokacin .
Saidai hakan bai hanata fahintar abinda zuciyar shi ke raya masa ba a lokacin sai ji yayi mama na fadin ai haka ya mace take dama.
Gata kamar ba zainab ba dai a yanzu gaba daya ta sauya wa wanda ya santa a baya a hankali ya dauki kofin tare da wani irin yar sanyayyar ajiyan yana bude ruwan.
Falon na bari gaba daya don nasan kons zauna karshe mama zata ce inbisa ne yasa na bar falon ga baki daya na shige ciki.
Wani tunane yayi a zuciyar shi yana kai ruwan a bakin shi da sauri ya aje cup din kamar wanda ya tuna da wani abu a lokacin a ransh ya nufi hanyar part din shi da sauri ido mama ta bishi dashi tana tausaya mashi .
Mutum baida hutu a rayuwa kullun yana cikin aiki haka kamar injin ko lokacin kansa baida shi.
Wanka ya shiga ya fito ya shirya falon shi ya zauna waya yakeyi da mami sun gama ya kira ya mamud sun dan dade a wayan kafin suyi sallama.
Ya dan zauna ya mike dakina ya nufa baiyi zaton ina ciki dakin ba koda ya shiga sai gashi ya hangoni akwance saman gado nayi rub da ciki kamar ina barci.
Kamshin turaren shine ya sanar dani shine ya shigo min daki a lokaci ba halimatu ba dake yawan shigowa wurina idan ina dakin.
Sani hakan baisa na dago a yadda naken ba ina kwance naji yana fadin jiya ina maki magana don kin rainani kika wuce kika barni a tsaye ko waima me kika zauna jira a daki baki shigo da wuri ba ?
Ban iya bashi amsa ba don jin tambayan da yayi min saida ya kara fadin watau ke yanzu ki rainani ko ?
Don kawai kinga in tausayi ki ko har kike son ki wuce matsayin ki a wurina raini nason ya shiga tsakaka .
Sai lokacin na dago ina fadin ni kaina ban san kana da bako ba a part din don da ban shiga ba nayi kwanciyana a nan.
Bakon ki ko nawa ya fada a dan hasale nace kayi hakkuri haka ba zai sake faruwa ba insha Allah.
Don dukkan mu musulmai muke haramune wani bako ya shiga dakin da yake kebabbe a wurin mu koda yarone balle wanan din da yake baligin kansa ya zauna a tsakiyan mu.
Dabi,un shi ma sam basu hallata ba yadda ya zauna kusan tsirara a gidan daba na muharamin sa ba yana yawo a hakan a tsirara dashi.
Rasa abinda zaice dani yayi yana sauraren yadda nake fada masa magana haka akan abinda shi ya kasa ganewa nake nufi ko ?
Wanan maganan ya kona masa rai sosai a cikin dakewa yake fadin kinsan ni bansan abinda ya dace ba sai ke .
Kada ki kara gigin kai dare kuma idan baki manta ba na fada maki banda saka min ido a gidana ga duk abinda kika gani.
Ban saka ido ba yaya asalima da nasan da zuwan sa na zanyi gigin shiga maku daki ba don hakan ya sabawa addinina ai.
Wani kallo yai min ya juya don a yanzu babu abinda zai fada min da zai kare kanshi ga abindana fada bayan wanan don haka fita dakin shine alherin sa.
Don na fara wuce tunanen sa a yadda ya daukeni da farko ashe kallon mai saman ruwa yake min don na wuce nasa tunanen ke nan shi yana min daukan karamar yarinya sharr ashe abin ba haka yake ba.
Lalai iyayyen arewa na bawa yayansu tarbiyan sanin kai tun suna kana zasu fara fahintar addinin su.
ZAINAB IDRIS MAKAWAYau ya kasance jumma,a tun safe danayi wanka na saka wani dogon riga silk mai taushi bakin a jikina rigan baida kwaliya ko ina a jikin shi.
Falo na fito don ingaida mama da kwana anan din na samesu zaune wanan karon harda ya jamal suna zaune.
Mun gaisa na zauna da kur,ani a hannuna ina jiran karfe tara ya buga indanyi karatu don mun saba da hakan koda nake gidan mami ina karatu duk ranan jumma,a da alhamis a wanan lokaci.
A hankali na bude dama da alwala na nafito na fara karatu a hankali jin suratul kafi nake ja yasa halimatu dake gefena karbewa tana bina a cikin daga murya sosai ta yadda duk wanda ke gidan zai iya jiyo muryan mu.
A kasa nake zaune sai itama ta zamo ta dawo kasan a kusa dani ta zauna munayi a tare har yakai matan dake kitchen din gidan da mamakin mu suka fito suna leken mu daga kofan.
A daidai wanan lokacin ya fito part dinshi a hankali yake takowa jikin shi yana saye da farar suith kal sai yar jakar da yake fita da ita rike a hannun shi.
Da mamaki yake karasowa inda muke jin yadda muke karatun mu hankali kwance kuma cikin rashin damuwa da kowa muke karatun mu.
Take yaji jikin shi yai sanyi lokaci guda sai faman tunane yake a zuciyanshi tare da fadin yaran nan haka suke da ilimin addini ashe ?
Idan ko hakane akwai aiki a gabana don dole watarana zata fahinci wani abu daga gareni wanda iliminta zai iya haska mata hakan.
A hankali har ya sauko ya kai zaune saman kujera hankalin shi yana gurin mu yana jin karatun yana taba mashi zuciya kafin ya juyo yana fadin antashi lafiya mama ?
Kafito mama ta fada tana dan gyara gyalen jikinta data yafa a jikinta tare da gyara zaman ta sai halimatu ta dago tana gaidashi ya amsa tare da fadin yau karatu ake munane a gidan nan haka ?
Ta danyi dariya tana noke kai mama ke fadin ai gara suyi don karatu a gida yana saukar da rahaman ubangiji ga kowa dake gidan.
Sadiya ai akwai kokari ko karatun bokon nan haka takan dameni dashi a daki wani lokaci har ta isheni.
Ya kara kallon halimatu din yana dan murmushi sai a lokacin ya jamal da hankalin shi kega waya ya dan dago kai yana gaidashi.
Ya amsa kafin ya mike ya nufi wurin cin abinci don ya karya ba tare da kara furta wa dan uwan nasa wata kalma ba daga gaisuwa da sukayi kawai inda shima ya jamal din ya mayar da hankali ga abinda yakeyi.
Ina kai aya na mike a hankali na nufi dining din na sameshi zaune yana waya da wanda naji ya kira da philis.
Abincin na soma budewa har lokacin ban bude bakina munyi wani magana ba dashi sai kokari zuba mai abincin da nakeyi a plate.
Ina gamawa na juya don in koma in karasa abinda nakeyi na jiyo muryan shi yana fadin zanan zainab.
Cak naja na tsaya a wuri daya kafin in juyo inda yake ina fuskantar shi don jin abinda zai fada min a lokacin.
Kujera ya nuna min da hannu saida na kalli kujeran duk da na gane me yake nufi da yin hakan na dan gusa zuwa wurin kujeran na zauna.
Kin karyane ya tambayeni kai na girgiza mai alaman a, a da sauri yace sai zuwa yaushe zaki karya din ?
Sha biyu na bashi amsa a takaice ina kokarin tashi naji ya kara fadin ke baki gudun yunwa yaja maki ciwone, ki debi abinci gayanan gaban ki kici ya fada cikin daure fuskan shi gareni.
Ba musu na jawo plate zuwa gabana na fara diban abincin na zuba kadan duk yana kallona na mayar da warmer din na rufe naji yace wanan ne abincin da zakici din ?
Kai kawai na gyada don ban son maganan komai dashi a yadda nake jin kaina don na gama fahintar yana da rauni a bangaren addinin mu sosai
Tunda har zai iya nuna tashin damuwa kan abinda ya aikata min na kawo wani kato a dakin da nake a cikin sa nayi magana ya nuna hakan ba komai bane a gurin shi.
Ko yanzu ma shiyasa na koma ga Allah don yayi min mafita gareshi dama wa yanda yake mu,amula dasu baki daya ko ranan haka maza suka shigo muna gidan kai tsaye bai nuna wani damuwa akan hakan ba .
Gashi kuma shidin ashe mashayine na kwarai ban sani ba wanda nake zaton ko yan uwanshi da iyayyensa ma basu sanda hakan ba dan dama dama ya jamal da shima a lokacin yace ya fara sanin halinsa ke nan.
Wata kilama yana da wasu halin na boye da ban sani ba tunda ina jin yadda anty fadila take yawan fada a kanshi ko yaushe.
Inko hakane ni wace irin wawiyace da ban fahinci mai take kokarin nuna min ba a lokacin to ta yaya zan sanda hakan tunda bata fito fili ta fada min gaskiyan maganan ba kai tsaye.
Da babu abinda zai kaini biyo shi kai ko gidan shima ba zan zauna ba don abin kunyane a kauyen mu aji wai mashayi nake aure ni Abu.
Bansan sanda na girgiza kaina ba na furta bani ba zama da mashayi a rayuwana sai naji yace me kike fada ?
Sai lokacin na tuno a gaban shi nake na dago ido na kalleshi ya dago kai ya tsareni da idon shi sun kada sunyi ja a lokaci guda yana son tantance sanadin maganana na zuciya da har ya fito fili.
Why zainab kike son ki ja matsala a tsakanin mu har mutane sunyi muna dariya musanman mami idan taji wani abu yana wakana a tsakanin mu haka sai suyi muna dariya ita da abokanta damasu mara mata baya.
Nasan kinyi hakuri sosai da kika iya boye wanan zancen a zuciyar ki kin nuna min ke din mace ce jaruma a cikin mata duk da karancin shekarun ki kuwa .
Don haka ki daure ki min addua Allah ya rabani da wanan halin don kece mutun ta farko da nake bukatan adduan ta bayan mami, don ni kaina bansan lokacin da nayi zurfi ga wanan dabian ba a rayuwana.
Idan ka hangomu zaune wurin dining din zaka dauka wani hiran mata da miji mukeyi a tsakanin mu a lokacin.
Don har mama dake kallon mu daga inda take zaune don shi ya jamal tuni yabar falon ya fice daga gidan tun zaman mu a wurin.
Cikin mamaki na dago kai ina mashi kallon mamaki don jin ya ambaci waini matarshi ce a yau a karo na farko zamana dashi.
Nace am not your wife dan dama dama ka kirani da sister ka zaifi sauki garemu hakan .
Cikin daga hannu kada mama ta fahinci make faruwa a tsakanin mu yace dani to to naji dama aike kanwatace tunda ke din yar mamice.
Yana fadin haka ya mike don gudun kada asirin shi ya tonu a gaban mama da halimatu dake can zaune dan nisa damu.
Nan ya wuce ya barni zaune na tasa abinci a gaba ina kallo naji mama na fadin har zaka fita ke nan yau dai ka saka zainab karyawa da wuri haka.
Bata son cin abinci bansan meyasa hakan ba ta saba zama da rashin karyawa da wuri tun a gida.
Tun daga wanan ranan ya saka min ido kan karyawa da safe na dai gane yana neman wani hanya na dan shakuwane a tsakanina dashi don haka na kara shan nin jikina dashi.
Allah da ikon sa sai ga hjy an sallamota gida taji sauki sosai kamar ba ita bace akazo kasan da ita a tallabe.
Dawowan hjy gidan ya kara muna sakewa da an,nashuwa ko yaushe muna kusa da ita tana kara jan mu a jiki tare da bamu dariya da barkwanci kamar yadda muka saba a baya da ita a gidan mami kafin mu bar gidan.
Saidai tsakanin ya jafar da ya jamal har yanzu babu jittuwa a tsakanin su suna dai gaisawa sama sama a tsakanin su.
Tun hjy bata farga da har yanzu babu shiri a tsakanin su ba har yakai yanzu ta soma fahintar suna nan a yadda suke sai ta soma zargin akwai wani abu dake faruwa mai girma a tsakansu.
Babban abinda yafi damunta shine ni kaina ta fahinci irin zaman da mukeyi dashi na wasa da hankalin mutane gashi idan ta fambayeni sai ince mata lafiya muke zaune dashi.
Don haka tasha alwashin tambayana don jin irin zaman da mukeyi a tsakanin kafin shi ta tunkareshi tasan ba zata fahinci komai a bakin shi.
Ranan ya jamal zai fita da mama data matsa ya kaita wani shago daya bata labari nima nace zan bisu zuwa shagon muyi kallo.
Saida muka shirya hjy tace na zauna gida ba zamu barta a gida ita kadai ba badan naso na zauna din don naso fitan tunda a gaban yaya mukai maganan fitan har nace nima zan bisu y yarda.
Bayan fitan sune tasa na debo fruit muna na debo a cikin bowl biyu na shigo dashi falon hjy kan tana shan nata saidai ni na saka nawa a gaba sai wasa da spoon din hannuna nakeyi ina faman tunane.
Hjy ta aje cibin dake hannun ta ta tsura min idanu na dan wani lokaci sai ta lura ban ma san tana kallona ba a lokacin.
Abu lafiya kike kuwa shiru ban dago kai ba ta kara fadin Abu nace meke damuwan ki haka kike wanan tunane haka ?
Abu fa ta fada a karo na uku tana tafa hannayen ta idon ta a kaina firgigit na dawo a cikin hankakina ina dago kai tare da duban inda hjy take zaune.
Ni take kallo a cikin mamaki baiyane karara a fuskan ta kafin tace dani me kike tunane haka yar nan kinga mu kadai ne a gidan nan yanzu.
Ki saki jiki ki fada min abinda ke damun ki a rai ki dauka ni din mai baki shawaran da zai fitar dake daga hakin damuwan da kikene .
Ko yanzu kin daina daukana a matsayin kawarki jafari ya kwace min ke kin daina yayina sai shi kadai ?
Da sauri nace a, a hjy har gobe kina nan a matsayinki na kakata a zuciyana yanayin fuskana kawai ta kalla ta fahinci akwai wani abinda ke faruwa a tsakani mu da yayan.
Duk sai nabi na tsargu da irin kallon da take min a lokacin don haka sai na dukar da kaina kasa ina ci gaba da wasa da cibin dake hannuna.
Zainabu hjy ta sake kiran suna na dago kai a hankali ina amsawa da na,am tare dan kallon ta tace .
Kinga ki fada min meye damuwan ki da mijin ki kada ki boye min komai ki daukeni tankar nice na haifi mahaifiyar ki ko mahaifin ki.
Na dan gyada kai a hankali alaman gamsuwa a gareta kan abinda ta fada taci gaba da fadin tun zuwan mu ina kule da yanayin yadda kuke zaune dashi.
Nayi shiru na tsayin lokaci kaina na a duke a kasa ina dan guntun tunane anya zan iya fada mata matsalan mu kuwa ko banza fa itace ta haifi mahaifiyar shi.
Kuma ta nuna tafi son shi a cikin jikokin ta kaf idan na fada mata a wani yanayi tsohuwar zata shiga don jin jikan nata ashe mashayine na gaske.
Don haka na yanke shawaran fada mata wani abin na daban na dan dago kaina tare da fadin hjy bana cikin matsalan komai dashi
Ta dan tsura min ido na tsawon lokaci kafin tace kin tabbatar da hakan zainabu na gyada mata kai kawai sai naga tayi murmushi kadan a fuskanta kafin tace dani.
Amma ni ga dan nawa fahintar sai naga kamar har yanzu babu wani mu,amulan aure dake wakana a tsakanin ku illa kawai gaisuwa da dan kulawa a gaban mu koba haka bane zainabu ?
Da sauri na dago kai na kalleta sai kuma na dukar da idona saiga hawaye yana zubo min daga idanuwana lokaci guda.
Ai kinga irin ta zainabu ina son ki sani ni mace ce yar uwan ki kuma manya sunce kowa ya rigaka kwana yana rigaka tashi.
Hjy babu komai da dawani matsala ai zan sanar dake kawai dai ni karatu nake son inci gaba dashi yasa nake tunane na tsunci kaina da fadin haka a gareta.
Hjy ta kalleni ta girgiza kai tare da fadin to shike nan amma kada ki dawo da baya kina dakin sanin kin fada min gaskiyan da bakiyi ba.
Koda yake dai mai daki shiyasan inda ruwa ke masa yoyo ai idan kinfi bukatan ki tafi a hakan dake dashi aiga fili ga mai doki sai mu zuba ido mu gani zainabu.
Ban yarda abinda kika fada ba a yanzu domin ni nasan kin boye min ne kawai don kina daukana ta bangaren jafari nake.
Amma ni nasan da akwai abinda kike boye min a zuciyar ki namiki tambayan amsan daya ce ki bani sai baki ban ban ba kina kawo min wani zancen karatu.
Karatu kan ai dole kiyishi zainabu tunda kina auren wanda boka ya huda ko jiyan nan naji yana magana akan karatun ki har nace ya barki a nan basai kin koma gida kinyi a can ba nan kusa dashi zaifi mai saukin yawan sintirin da zaiyi idan kina can Nageria din.
Da sauri na dago kai a karo na barkatai na sauke kan hjyn don jin abinda ta fada na wai in zauna nan tare da yaya a kasan mutane inda bansan kowa ba.
Eh hakan nace kuma ya amince da hakan don haka idan zamu koma ba tare dake zamu tafi ba a nan zamu barki keda kanwarki.
Amma hjy da baki fada masa haka ba don shi kanshi yayan zaifi bukatan zamana a can gida da nan din ya dai amsa makine don baya iya mussata maki zancen ki gareshi .
Eh hakan yana da kyau tunda harkin fahinci hakan keda kanki sabanin ke da yanzu kika fara daukana a wani matsayi na daban.
Zainabu nasan ki nasan halinki don haka ban yarda da abinda kika fada ba a yanzu.
Domin ke kullun yar ba komai ne saidai duk wanda yasan ki ya dubeki a yanzu yasan da akwai matsala a tare dake zainabu.
Na dauka nice mutum ta farko da ko ban tambayeki ba zaki iya budan bkin ki ki fada min halinda kike ciki da mijin ki a gidan shi.
Tunda ninayi tsaye har wanan auren naku ya kullun a tsakanin ku saboda ni nasan halinki da nasa da kyau don ke yarinyace da bata gama mallakan hankalinta ba har yanzu.
Hawaye naji sun taru min a idanuna lokaci guda ina tausayawa kaina halin kuncin da nake ciki a wanan lokacin da abin zai fadu tabbas hjy kece ta farkon da zan fara fadawa wanan maganan a yanzu.
Amma a fili nace da sauri na mayar da hawayen nawa ban yarda sun digo a gabanta ba sainace hjy addu, a kawai zaki tayamu dashi a yanzu nan gaba idan bai daina ba zan fada maki insha Allahu.
Bayan ta dan tsura min ido tace to shike nan Allah yai maki albarka kin nuna min kedin mace ce ta gari mai rikon amnan mijinta ako wani hali ta tsunci kanta zata iya rike mai sirin sa a rayuwa.
Madalla dake zainabu insha Allahu hakkuri ki ba zai tabe a banza ba kici gaba da hakkuri da addua kuma kada ki yarda ki saka damuwa a ranki kinji.
Har muka bar wurin hjy tana min kallon tausayi don nasan tana da magana a zuciyar ta saidai ban bada daman hakan ba a lokacin.
To me zan fada mata ince ga yadda jikan ta yake ai saidai tajishi a bakin wani na sani ko in fada ta sake ribcewa ciwon dayafi wanda ta taso a yanzu.
Dakina na shiga cike da tunane na dan watsa ruwa tare da dauro alwala na fito na tayar da sallah azahar sai uku da rabi su mama suka dawo da sayyaya mai yawa tare dasu.
Ban fito ba don tunanen da nakeyi kan zancen mu da hjy ba abinda ya tsaya min a rai sai zancen karatuna da zanyi a nan .
Shike nan yanzu babu zancen komawa gida a garemu ke nan sai tsawon wani lokaci anya kuwa zan iya daurewa in zauna da wanan mashayin haka?
Idan na zauna a nan dagani sai shi ta yaya zan iya shawo kansa babu kowa nasa a kusa dashi irin ya jamal da zai saka mai ido kan abinda yakeyi tunda ni ba zaiji magana na ba.
Ya zama dole ke nan a gareni in kara jajircewa akan yadda zaman mu zai kasance a yanzu bayan tafiyan su hjy da mama.
Zan kuma kara sa mai ido inyi iya kokarina wurun rabashi da wanan halin da yardan ubangijin mu sai dai babban matsalana a yanzu shine rashin layin waya da banda shi a tare dani.
Don ina son muyi siri da malam mijin mai zube sai kuma matsalan anty fadila da nake son ya dawo da ita kusa dani don da taimakon ta zan iya samun nasaran abinda na dosa a yanzu.
A takw dabara ya fado min a rai nace da hjy ya kamata na hada wurin shawo kan shi ya yarda fadila ta dawo nan mu zauna tare da ita .
Ko abunuwa zasu zo min da sauki yadda nakeso don tafini sanin ta kan duniya ko naso yin abu bazan iya ba don hankalina baikai na hakan ba a yanzu.
ZAINAB IDRIS MAKAWAYa fito daga wanka da safe ya samu wayan shi dake ajiye saman bedside din shi yana ringing yayi saurin kai hannun shi ya dauka kada ya katse.
Bakon lamba ya gani yayi kamar kada ya daga saidai ya daure ya dauka don baisan wanda ke kiranshi da wanan layin ba.
Don tsayin kwanaki biyu ke nan maishi yana yawan kiranshi a daidai wanan lokacin don haka maishi yasan shi kenan farin sani yasa ya kirashi a wanan lokaci .
Ya dauka da hello muryan taju ne akan layin ya fara magana da fadin nasan kayi fushi dani sosai yasa na kiraka na baka hakkuri don banzaci hakan zai faru ba ni kaina zafin kishine ya sakani yin hakan a lokacin.
Saida ya gama sauraren shi yake fadin ka dauka dolene nake tare dakai dama ko kuma bazan iya zama idan babu kaiba.
Taju ya saki wani dan ajiyan zuciya yace kayi hakkuri bana iya rayuwa idan bada kai ba boss kasa ka maye gurbin na da son wani bayan ni.
Hankalina a tashe yake tun ranan da haka ya faru a tsakanin mu kayi hakkuri ka rike kaunar dake tsakani da kai bana iya jure ganinka tare da wani kuna rayuwa ina kallo.
Ya jafar yayi murmushi a tausashe kafin yace taju ke nan kana sane kayi kokarin tona min asiri don kawai wani bakin kishin ka na banza can.
Taju ya katse shi yana fadin Iam sorry boss banyi haka a cikin hankalina ba a lokacin kasan irin son da nake maka a rayuwana.
Jafar din yaja wani uban tsoki tare da furta is too late now don na dade maye gurbin ka da wani so ka manta da wanan a tsakanin mu.
Yana fadin haka ya kashe wayan shi taju ya kalli wayan yaga ya kashe abinsa idon shi ya runtse yana jin wani zafin son jafar din na ratsa zuciyar shi lokaci guda.
Don tunda ya samu jafar ya bar sauran abokan harkan shi don jafar mutum ne har mutum yana da tabbacin idan jafar ya barshi rayuwan shi yana cikin gararari ke nan.
Shiko jafar din wayar ya jefar saman gado ya koma gefe ya zauna ya tallafi kanahi da hannayen sa biyu zuciyar sa tana masa azalzala.
Don shi yanzu zuciyar shi ta kasu biyu don yasan kirsis yake da asirin shi ya tonu muddin wanan yarinyar mai wayau na gidan nan.
Bai mu maganan zancen karatun mu ba ko zancen tafiya ai bada mu za a tafi ba asalima dai dan kwana biyun nan na kula da yana yawan daure fuskan shi ga kowa a gidan.
Ni hakan bai dameni ba tunda dama ba wani shakuwa bane tsakanin mu saidai abinda na zata ko hjy ta zauna dashine shima kamar yadda ta zauna dani tana bincikena kila shima sunyi hakan dashi.
Ranan dai da safe muna zaune a dakin hjy yake cewa mu shirya zamu fita karfe hudu na dauka badani yake magana ba saida ya kalloni yana fadin bakiji bane na dago kai ina fadin naji a sanyayye.
Daga inda hjy take zaune naji tace umhumm kawai tana dan kawar da kanta gefe daya daga barin kallon kowa a dakin.
Mama Ramatune tayi karfin halin da matarka zaka fita ko damu duk don kayi magana ta baibai bamu fahince ka ba gaskiya a nan ?
Da ita nake mama akwai inda zamu tafi tare yau ya bata amsa daga haka ya fice ya bar dakin hjy ta bishi da kallo tare da fadin miskilin banza kawai ya kama daure fuska kamar bai taba dariya ba.
Fushi yake don nayi masa nasiha yake faman daure fuska haka don yasan yayi laifi yana gudun naci gaba da fada.
Jin hakan yasa na dago kai da sauri ina kallon hjy don bansan me tayi mai fada a kai ba itama din ni take kallo kafin ta kawar da kai tana fadin .
Ni dai na fada mai gaskiya don kada yaga kamar amana wasane duk wanda yai sakaci da rikon amana zai fada ranan lahira.
Karfe hudu shaf na shirya don gudun kada inyi laifi a gareshi saida na dan zauna zaman jiran shi kafin ya fito daga part din shi.
Ina dakina kwance ina jiran fitowan shi ya shigo dakin tun daga nisa yake karewa kyakyawan surana kallo.
Kyakyawan suran kafafuwana da ya dan fito har zuwa sharaban kafana suna waje don yadda na kwanta din a lokacin.
Ya tsaya ya shagalta da kallon su saboda yadda ya hangosu sunyi bul bul dasu tankar bana taka kasa dasu a yanzu.
A hankali ya tako zuwa inda nake kwancen na shagalta da karatun wani littafi dana tsunta a gidan na labarai.
Banji shigowan shi ba dakin haka ma takon shi zuwa bakin gadon duk ban ji shi ba a lokacin.
Sai ji nayi girshi a na ja min rigar jikina daya tattare har zuwa sharabana dake waje tunda ni kadaine a dakin sai ban damu da hakan ba.
Wani irin zabura nayi lokaci guda ina kokarin sake ihu don nasan halimatu dai ba zatayi min wanan haukan haka ba.
Na juyo da wani irin sauri ya jafar na gani tsaye a kaina ya mayar da hannayen shi ya rungume saman kirjin shi.
Da sauri na yunkura na tashi zaune ina kokarin gyara rigan nawa ya sauka da kyau kafin in dago kai in jefeshi da wani irin fitinannen kallo.
Yace cikin daure fuska ki tashi mu tafi kina nan kwance lokaci yana kurewa gaki nan kwance ?
Yana fadin haka ya juya ya fita daga dakin kai tsaye nima tashi nayi saida na gyara fuskana irin dabi,an mata kafin in fita na sameshi cikin mota zaune yana jiran fitowana.
Nayi mamakin ganin shi a gaba wurin mazaunin driver ke nan mu kadai zamu fita yau ba tare da kowa ba na tambayi kaina .
Kafin in iso ya bude motar na zagaya zuwa dayan gefen na zauna tare da rufo kofan bai tsaya jiran komai ba yaja motan muka bar gidan.
Tafiya mukayi mai nisa da gidan hankalina yana gun motocin danake gani tankar masu shi suka kera abinsu don kyau kafin naji yace may kika fadawa hjy har take tambayana zaman mu dake ?
Da sauri na juyo na dan kalleshi tankar bashi yai maganan ba don hankalin shi gaba daya yana ga tukin da yakeyi lokacin.
Kaina na mayar a wurin window motan naci gaba da kallon da nakeyi na motoci da gidajen su har ma da al,umman garin da nake gani kamar aljannu a idona.
Yaci gaba da fadin na dauka kina da wayau da farko ashe abin ba haka bane don na manta ke din karamar yarinya ce da bata iya rike siri a cikinta ashe ?
Daga cikin tsakiyan kaina nake jin sautin kalaman shi wanda babu tamtama idan nace zan bashi amsa a lokacin bazan fadi daidai ba.
Barin fada maki kiji daga yau sai yau ba hjy ba ko mami data haifeni kika kara fadawa magana na sai kin kwamce da baki sanni ba wallahi.
Wani irin juyowa nayi tare da kallon shi lokaci guda ina fadin kana dai wahal da kanka domin ni banga riban fadawa wani abinda kake aikatawa ba bayan Allah.
Allah kadai ya kamata nakai kukana gareshi ba wanin Allah can ba don shi daya halice ka kuma ya kawoni karkashin innuwan ka na zauna shi yasan yadda zaiyi dakai.
Naci gaba da fadi cikin muryan dake son nuna kuka nason zuwa min bakaji tsoron mahalincin kaba nawa zakaji yaya ?
Ya dago kai yana kallona ido da ido tare da sauraren abinda nake fadi babu kuma alaman tsoron shi a fuskana ko kadan.
Da sauri ya maida kanshi ga tukin da yakeyi zuciyar shi yana tafasa tare da jerowa kanshi tambayoyi wanda basu da amsa gareshi a lokacin.
Wani irin fisgan motan yayi lokaci guda saida tsoro ya kamani a zuciyana amma a fili saina dake da hakan ban yarda na nuna mashi hakan ba.
Fuskan shi kawai zaka kalla kasan rayuwan shi a bace yake wani babban moll ya packer motar sai daya dan sako iska daga bakin shi ta hanyar furzoshi da karfi lokaci guda alaman hade bakin ciki ya dan fadi a dake ki fita mu shiga nan ba tare daya kallo inda nake zaune ba.
Fita nayi kamar yadda yace dani din shima ya fito muka jera zuwa cikin wurin inda mutanene birjit wasu na shiga wasu na fita da kwalaye mai kama da jakka a hannun su.
Bai tsaya ba sai fannin kayan mata naga ya danyi magana mai kama da yare kafin matar ta nufoni tana washe baki.
Kaya take daukowa sai ta zaba tana gwadawa a jikina tare da yaba yadda yayi min kyau nidai ina tsaye kimkyam kamar an dasani a wurin muka koma fannin takalma nan ma tana biye damu a baya da taimakonta har saida yace sun isa.
Halimatu ma ta samu nata rabon don sayayya sosai mukai mata su man shafi da turare masu tsadan gaske ya saya muna .
Bayan ya biya mun fitone ya biya wani shago a nan ya barni ya shiga naga ya fito da shigen jakar da aka sako muna kaya a wancan shagon sai dai ya riko daya a hannun shi yana zuwa wanan din ya saka a gaban mota kusa da kafan shi sauran aka sa a bayan mota.
Hanyan gida ya dauko a lokacin har magariba ya dan gwauta ga yadda yanayi ya nuna na garin don wuri ya fara duhu ko.
Mun shigo gidan babu kowa nasan sun shige yin sallah a lokacin don haka nima na nufi dakina don sauri in gabatar da nawa sallah kada lokaci ya kara kurewa
Idan kin tafi kayan ku fa wazai shigo maki dashi dakin naji muryan shi yana fadin haka a bayana.
Naja na tsaya wuri daya ba tare dana juyo ba ban kuma wuce part dina danayi niyar tafiya ba duk da ina sauri.
Naji takon tafiyan shi sai muryan shi naji gap dani yana fadin banyi wanan maganan dake ba don ki fadawa hjy munyi.
Ba halina bane fallasa sirina wanan abune daya shafeni a yanzu ni daya har in baka tuba ka daina ba nasan watarana idon su zai ganan masu kamar yadda Allah ya nuna min nima .
Don Allah ba ai masa wayau ga duk wani abinda mutum yake ganin yana boyewa dole akwai wata rana da Allah zai fallasa shi ga mugun aikin sa.
Allah ya baka ikon ganewa ka tuba ka daina don kan ka juyoni yayi da karfi har saida na dan firgita don ban zaci haka daga gareshi ba a lokacin.
Da sauri nayi kokarin ja baya daga rikon dayai min din saidai na kasa hakan don ba karamin riko yai min ba a lokacin.
Wani zafi hakan naji har kasan raina.
Na dago a fusace don mashi kashedin hakan da yai saidai muna hada ido dashi kwarjinin shi da zatin shi ya hanani hakan gare shi.
Kaina na mayar kasa da sauri don ba zan iya jurewa irin wanan kallon da yake min ba a lokacin wanda na kasa fassara hakan a raina.
Shiru na dan lokaci kafin muryan mama ya shiga kunnuwan mu tana fadin kuma nan kuka tsaya ina dai lafiya na ganku haka ?
Lafiya mama muna dan maganane a nan yana fadin haka ya sakeni da sauri na juyo ina fadin sannu mama tace har kun dawo ashe ?
Mun shiga yin sallah ne yanzu ma wayana na manta dashi a nan inda na zauna nazo dauka shiko a lokacin har ya kai kofan part din shi don haushi.
Don ba haka yaso ba yasone ya ban wahala sai na raina kaina sai ga mama din ta kwafsa mashi don fitowan ta a lokacin.
Kayan da yake maga wani daga cikin yan aikin gidan ya fara shigowa dashi niki niki a cikin dan guntun turanci na ce dashi ya kai part dina mama tabi kayan da kallo.
Tace ashe ku sayayya kuka fita waini wanan abin naku na daure mun kai yau ina antyn mu dake fadin sai kuma tayi shiru ganin haka nace banyi sallah ba mama.
Jeki ki sallah kada ki makara don lokaci yaja sosai na juya da sauri na barta wurin na wuce zuwa part dina.
Sallah nayi kafin na samu wuri na zauna a dakin ban fito ba don injin nauyi da kunyan mama a yadda ta samemu dashi a falon dazun don haka nai zamana a dakin kawai.
Wanka nayi na shirya kwanciya na saka hijab saman kayan dake jikina na nufi part din shi har na shiga falon nasa .
Sai naga wanan dan jakkan daya riko da kanshi aje saman kujera har na dan wuce wata zuciya tace na koma naga meya sayowa kanshi ne haka bai bari wani ya dauko mashi ba.
Saida na kai zaune na bude ledab a hankali idona yai arba da kwalaben dake ciki kwalban kawai abin kallone.
Zuciyana bai yarda da hakan ba ina kkkarin karata ko meye a cikin kwalban naji an fisge kwalban a hannu na tare da fadin get out from dis part stupid yana nuna min hanyar fita.
Har abin naki yakai kiyi min bincike who give you dis right da zaki taba min kayana a hasale yake magana kamar zai mareni ko me ya tuna kuma oho.
Ya duka ya dauki saurab kayan nasa nima mikewa nayi da sauri na fice daga part din sauri zuciyana cike da zargin shi.
Ina shiga dakin na rufo kofa tare da saka ma kofan key na nufi gado na fada saidai ban kwanta ba ni ban kwance kuma bana zaune sai tunane nakeyi a raina.
Dama wai haka aure yake ne nake ganin mata suna walwala ko wani lokaci kaga kamar basu da damuwa a tare dasu.
Meyasa ya jafar yake min hakane koba komai yakamata ya rikeni tankar kanwarshi ta jini a gidansa tunda yasan yadda mukai aure a tsakanin mu.
Tunane kala kala nayi shi a wurin karshe na mike na dauro alwala don barci ya kaurace min gaba daya a idona ranan.
Sallah nayi raka,a hudu na dade wurin ina addua ina mika kukana ga Allah kafin naji sanyi a raina har barci ya daukeni.
Naso makara ranan don ban kwanta da wuri ba a gagauce nayi sallah na koma na kwanta sai barci kuma.
Kodana tashi shadaya na safe wanka nayi na fito bayan na shirya na fito don gaida hjy don nasa zata damu da rashin ganina da batayi da wuri ba ranan.
Da sallama na shiga dakin ta saidai ita daya na sama tana zaune tana nafila na samu wuri na zauna harta idar bandade da zama ba naji tana fadin zainabu kin fito ?
Eh hjy ina kwana ta amsa min a cikin fara,a tare da fadin ai mijin ki daya shigo nan nake tambayan shi yace jiya baki kwana da dadi ba.
A raina nace makaryaci ke nan shikan ya hada duk wani abin ki da Allah ya hana Allah dai ya shiryoshi ya daina wanan hakin .
Saidai a fili dan murmushi nayi ina fadin ciwo kaine kawai ai hjy kuma nasha magani ya bari.
Dole ki ciwon kai jiya kun fita kun dade tunda baki saba fita irin haka ba dama kin dai kara cin wani abuko yanzu bayan kin tashi.
Zan daici hjy na fada a cikin ladabi to kinga ga wanda suka kawo min niba dadin abincin su nake ji ba ki tashi ki diba kici yanzu.
Dole haka na mike na dan dibi kadan na zauna nan gabanta kinga da haka zaki ta kamo zuciyar shi don kinga yanzu shi na masa fada ya nuna min yayi biyayya ga magana na yanzu .
Don haka kiyi ta hakkuri bana son har uwarku ta gane wani rashin jittuwa yana shiga tsakanin ki da mijin ki ta yadda zata dara muna.
Kinga Ramatu da kike gani diya tace nasan halin abinna kamar me yanzu tana zaman idon uwarku ne a gidan nan nasan duk abinda suka kitsa kan zuwa nan da ita .
Don baki san yadda tafiyan ya wakana bake ta nuna idan bada Ramatu ba saidai a fasa tafiyan dole mijin ki ya yarda da hakan mukazo tare.
Don haka nake son kafin mu tafi ta koma ta fadawa uwartaku zaman lafiya kukeyi tare dashi kinga duk wani shirin su sai ya tafi a banza ke nan.
Saidai abindake wakana tsakani shi da dan uwanshi na rasa ko menene ya hadasu haka a yadda nasan su a tare nasu yafi zuwa daya.
Sai gashi yanzu naga suna wasan kura da kare kamar wani abu na faruwa a tsakanin su ko kinsan meya hadasu haka wanan abin ke faruwa ?.
Da sauri nace nima hjy haka na fahinta don ranan ma naji mama nawa ya jamal fada kan hakan yace da ita ba komai .
Saboda na gane hjyn tana son tayi min wayau manya taji wani abu daga gurin yasa na fasa mata hakan don ta barni.
ZAINAB IDRIS MAKAWAAkwana a tashi ba wuya a wurin Allah sai gashi har hjy ta gama shan maganin da aka bata suka koma da ya jamal don shi yayi tafiya wata kasa a lokacin yasa yabar komai a hannun jamal din.
Suka bata sallama da sharadin zata dinga zuwa checkup duk bayan wata uku lokacin da naji hakan nayi murna kwarai don a zato zata zauna damu nan ke nan ga baki daya har lokacin da asibiti zasu sallameta baki daya.
Saidai me ranan daya dawo daga tafiya baiko shiga dakin shi ba ya zarce wirin hjy sun gaisa tare da dan taba hira dashi har ta sako mashi zancen da asibiti sukayi.
Shima cewa yayi da ita ashe zama chaina ya kamaki ke nan yanzu zaki shakara tare damu a nan ke nan ?
Da wani irin sauri ta dago kai tana fadin ai in kaga na kara sati daya a kasan nan to bansan hanyar gida ba kenan idan kuma har ban sani ba sai in buga gida suzo su dauke ni.
Hjy kamar wace dai ake kora ya fada a dan galabaice yana dan mika don zama cikin jirgi da yayi yasa shi gajiya don har dubai suka je bayan sun gama meeting.
Hjy ta kalleshi tana fadin jeka ka huta mana tunda ka debo gajiya haka da yawa ni bance kuma da kai ana korana ba a nan.
Iyakar gata dai kan aikun nuna min shi a duniyan nan nikai na godewa Allah na godewa haihuwa don yai min albarka.
Ya mike yana fadin ni dai kan baki haifeni ba uwata dai ta iya haihuwa tunda itace ta haife ni ai hjy tace ja,iri waya haifi uwar taka da kake yabo da ban haiho ta ba har zata haifeka.
Yau dai na gane fitina wanan tsohuwar kike ji dashi zuwa Nigeria kuma baki zuwa sai ranan da likita yace ya sallameki kwata kwata mama ce kadai zata koma ke ko kina nan tare damu.
Dakai da likitan kunci gidan ku na gane abin naku hadin baki ne ni ko da kafa sai in karasa gida ba matsala bane a gareni.
Zakiko hadu da kura dasu zaki hanya in takaman ki zuciyana ya fita yana dariyan yadda ta takankare tana masifa dashi don yace ba zata tafi ba.
Ance sabo turken wawa bansan dan zaman mu tare ba har akwai sabon da ya shiga tsakanin mu hakan sai bayan tafiyan nan nasa .
Duk ko da yatafi bamu cikin dadin rai dashi don har lokacin akwai fushin daukan mai kaya da nayi ina dubawa ya dauki fushi dani sosai a gidan.
Har tafiyan nan ya kamashi yana cikin fushin haka dani ko zancen tafiyan a bakin hjy na farajin zaiyi tafiya wai.
Na nuna mata nasan da zancen sai dai na manta da sunan kasan don yana da wuya mama Ramatu ke fadin ni dai yar nan kada wata rana ki ba dana kunya da wanan kauyancin naki.
Hjy tace haka yarki tayi kafin ta waye itama aishi jafari ya mai da tarihin ubansa ne a rayuwa don haka ku bar ganin laifin shi haka.
Da zai tafi kuma sai safiyan ya shigo min daki bayan ya shirya har an fita mai da kayan shi ina zaune saman dan stol din mirrow dakina ina shafa mai da nayi wanka.
Ya shigo dakin ba tare da tsayawa ba yake fadin zaiyi tafiya zai kwana biyu a can idan muna da wani matsala in kira Samuel in fada mashi ko menene .
Daga haka ya jiya zai fita a dakin na samu na bude bakina da kyar ina fadin Allah ya kai lafiya Allah yasa abinda akaje nema a samu .
Na gode ya fada ya fita da sauri nabi bayan shi da kallo tare da sauke ajiyan zuciya na mayar da kaina ga mirrow ina kallon kaina a cikin madubin dake gabana .
A hankali na raya a raina wai ina nake da matsalane a jikina da ya jafar bai min kallon mace ne har yanzu yadda naga wasu maza sunawa matansu dai ?
Nidai banga inda na kasa ba da bai ma son ko ya kalleni idan har ya tsura dani haka a dakin da sauri kuma na kawar da wanan tunanen a raina ina fadin .
Kenan har na damu da ya tabeni ke nan kamar wata jarababba dani nikan ina zan yarda da wani tabi kazami dashi yana shan giya kuma ya dawo ya tabani.
Yau ma daya dawo ina kwance ina tunanen shi ashema yana cikin gidan ko a lokacin ban sani ba saida zai shiga part dinshi ne kamshin turaren da yake amfani dashi ya bugo hancina don kofa a bude halimatu ta barshi da zata fita .
Saida naji gabana ya fadi sosai shiru na saurara banji motsin shi ba a dakin na sauke ajiyan zuciya a hankali tare da gyara kwanciya naci gaba da karatuna da nakeyi.
Har wani lokaci hankalina bai kwanta da rashin ganin sa ya leko ba kuma ban daina jin kamshin sa a hancina ba saina dauka kewan shi kawai ke damuna nake jin hakan.
Karshe dai waya ta na jawo na fara gamen a ciki tunda layin da nake dashi na Nageria ne bai zuwa ko na kira dashi.
Nayiwa ya jamal magana ya saya min da zai fita ranan mama ta hana ya sayo min wai kila mijina baida bukatan na rike wayane a nan yasa bai sayo min ba don haka kada ya soma ya sayo min su samu matsala dashi.
Don haka ya jamal din yaki sayo min layin da zanyi amfani dashi amma bayan wanan duk abinda mukace muna so idan zai fita yakan sayo muna yazo muna dashi.
Wani lokacin ma idan bamu ce ba zai sayo din tundawa halimatu da take mai oyoyo idan ya dawo tkan zauna ta mai surutu sai ya gaji ya barta.
Shikan gaskiya bamu da matsala dashi ko kadan don a kannensa yake daukan mu wani lokacin ma har ya tsawata wa halimatu idan tana wani abin.
Hankalina ya dauku sosai ga game don haka banji shigowan shi dakin ba sai dai kamshine ya sanar dani hakan yasa na dago kai da sauri na sauke a kanshi.
A lokacin yana tsaye daidai kaina ya sanya fararen kaya a jikin shi farin wando da wani riga mai kama da t shirt din maza saidai yadin shi mai laushi sosai saidai hannun rigan bai sauka har kasa ba.
Saida na dan firgita dan ganin shi girshi hakan a gabana cikin rawan baki nake fadin yaya sannu da zuwa ya hanya ?
Idon shi akan wayan dake hannu da nake game ya amsa min tare da fadin ina sadiya banganta part din su hjy ba dana shigo.
Ban san inda ta shiga ba na basa amsa yasa yai min wani kallo kafin yace kila suna tare da mamane don itama ban ganta a dakin ba.
Kokarin sauka daga kan gadon nayi ina ganin ya juya zai fita don hankalina ya tashi da cewa da yayi halimatu bata gidan.
A daidai lokacin da muka sauko falon ne kuma naga ana shigowa da kayan da ya dawo tafiyan dasu yana tsaye yana magana da Samuel akan kayan.
Dan ganin Samuel di na kallon direction din daya fito yasa shi dan juyowa yana kallon wurin nice nake kokarin gyara daurin gyalen dana rufe kaina dashi lokacin.
Na karaso ina jin yana fadin ku kai wanan part din ta wanan kuma ya nuna part din hjy da nufin su kai can sauran yace su shiga mai dashi wurin shi su adana.
A kawo abinci ko fita zakayi na fada cikin karfin hali da daurewa yace ba yanzu ba sai da dare zanci daga haka ya juya zuwa part din shi ni kuma na shiga wurin hjy don jin abinda ya fito dani.
Na samu hjy tana kallon kayan da suka aje a gabanta tana mamaki nayi sallama take fadin ni wanan menene kuma a ciki suka shigo muna dashi haka ?
Ya jafar yace su shigo dashi nan na bata amsa ina zama zan tambayi su mama sai gasu sun shigo mama na fadin ashe jafar ya dawo yanzun muka ganshi a waje zamu shigo .
Ya dawo yana tambayan ku nake fada mashi kun fita mike kafa da jamal yake fadin ku rage fita a garin nan sosai.
Da gajiyane man kullun mutum yana guri daya a zaune mama Ramatu ta fada tana kaiwa zaune fuskanta a abinda ta gani daure.
Wanan kuma fa hjy ta tambaya tana kallon mahaifiyar tasu hjy tace miskilin danku yace a shigo dashi bai min bayanin ko meye a cikin sa don baima shigo ba tunda ya fita dazun.
Fita halimatu tayi sai gata ta dawo dauke da cup cike da milk a cikin sa sai snack a dayan hannun nata.
Allah yagani ina jin kunyar wanan rawan kan na halimatu a gaban su duk dako nayi mata fadan haka a dakina don ban manta da gorin da mama tayi muna ba a farkon zuwan mu gidan kan abinci.
Yanzu ko tana nuna muna ba komai saidai ni ban yarda da hakan ba tunda har hjy ma data haifeta tace min nayi hankali da mama din ke nan ba sona da gaske takeyi ba.
Shiyasa a kullun nake cikin jawa halimatu kune da ita din kada taje tana sake maganan gidan mu a gunta watarana a samun abin mana gori dashi.
Nikan mikewa nayi da niyar ficewa daga dakin sai naji mama na fadin ai jafar din naga ya fita ina kuma zaki ana zaune ana hira.
Ikon Allah ke haka kikeyi a gidanki idan mijin ki yana gida wanan saka idon har ina kuma Ramatu ?
Haba dai hjy don na fada mata ya fita ai laifine kuma hakan yanzu gani nayi dai ko ta fita baya gidan ai .
Ki barta ta tafi nace maki bana son wanan saka idon tsiya akan yaran nan bansan dalilin ku nayin hakan ba ko kukan mata kuma kuna da diya mata ne a gaban ku.
Yanzu kuma hjy meya kawo wanan maganan daga fadin baya nan ta zauna shine na wanan maganan haka ?
Ramatu ina dai horon ki da wanan dabian ko ita wace kike tayawa din wata rana zatai nadaman hakan mujuri zuwa rafi dai akace inji hausawa.
Tashi kije mama ta fada a dan hasale tana kallona nace dama daki zan koma in dauke kayan dana bari a gurin.
Jeki kawai ban tanbaye ki ba kada kuma kija min wani laifin gun hjy yanzu nikan jikina yayi sanyi haka na fita na bar masu dakin.
Ashe hjy taji wayan mama Ramatune da mami da take fada mata ya jafar baya garin yai tafiya sai mami kecewa da ita.
Ta kara saka ido a kaina ta kula da kyau kada ta bari in samu wani sakewa ko kadan dashi don ta tsani ta bude ido taji muna tare da danta wallahi.
Ta kare da fadin sai yanzu nake yarda Ramatu da ake fadin asiri sukai min ita da iyayyenta tun kan tazo ki duba fa.
Yadda na dauki yarinyar nan kamar ba yar aiki ba a gidana tankar wata jinina na jiki na mayar da yarinyar nan wai lokaci guda jafar yazo ya birkice min a kanta.
Yau itace a kasan chaina zaune abinda ke kara ban haushi da takaici muga namu yayan zaune a gida Ramatu yau wa yaki nasa yasamu miji kamar jafar wai ?
Mama Ramatu tace shine abin da nake fada maki ai anty lokacin nace irin yaran nan ba abin yarda bane wallahi kinki ki gane hakan a lokacin.
Sam ban yarda ai tayi wani abin sakewa ko kadan tana nan yadda kika santa har yanzu saima dawowan hjy gidane ai ta dan sake jikin ta.
Sun dauki lokaci suna magana a kaina itako hjy tayi kamar tana barci ne a lokacin basu sani ba don ta dade da kwantawa a lokacin yasa mama ta dauka barci takeyi har lokacin.
Jin hakan shine dalilin da hjy take samata burki ga duk abinda tayi ta gane da manufa take min shi sai ta taka mata burki a take.
Kayane na ban mamaki na shiga tsara saidai duk kyausu nikan basu min ba don sai na dauka shigan yan iska yake son mu dinga yi kawai a kasan nan yanzu duk da dogayen rigunane basuyi kama da wanda na saba amfani dasu ba masu gyale da nake yafa gyalen a kaina wani lokaci.
Haka na halimatu dana gani a ciki suma dai din masu tsadane sosai daganin su na tattara na saka muna a wardrobe hakama takalma da jakkunan na aje a gurin ajesu.
Sai da dare na shiga part din bada niyar kwana ba kamar yadda na saba shiga yana zaune na sameshi da waya a hannun shi sai cup din daya rike yana shan abu a cikin wanda bansan ko meye ba yake sha a lokacin.
Har na karaso inda yake zaune yana kallona a cikin tsarguwa da daure fuskan shi gareni nima duban kofin nayi na kawar da kaina tare da kaiwa kasa na rusun na ina fadin munga kaya mun gode Allah ya karawa dukiya albarka.
Ya gyada min kai yana zaune yadda yake saidai wanan karon ya mayar da kanshi a makarin kujeran yana mai lumshe idon shi a hankali.
Ina fadin haka na mike ba tare da wani jinkiri ba na juya na fito daga part din zuciyana cike da zargin abinda naga yana sha din a lokacin .
Ya Allah ka kawo wa wanan bawan naka dauki ka rabashi da wanan hali da duk wani abin hani daka hani al,umman Annabi ka dashi ya Allah.
Na fada idona yana mai cikowa da hawaye haka na kwanta na dunkule a wuri daya zuciyana yana min tunane kala kala lokaci guda.
Yanzu koda ace muna kwana a tare ne nayi fushi dashi haka yaya zai barni cikin rashin kulawa ko damuwa da hakan?
Ashe da gaske ne da yake yawan fadin shi mace bata gaban shi asalima saidai yai mata kallon yar uwa ko abokiya kawai a idon shi.
Idan ko har hakane akwai aiki ja a gabana don ba zan zauna a rayuwa haka da miji kamar kurman maza ba.
Shin wai shi wani irin mutum ne haka koko shan giyar dayakeyi ne ya mayar dashi hakan ba,a sani ba ko kuma wanan dalilin ya zabeni a matsayin matar shi don ya cutawa rayuwana haka dai nayi ta faman tunane barkatai har barci yai gaba dani.
Bayan kwana biyu da faruwan hakan nake jin zancen tafiyan su hjy wanda hakan ya tayar min da hankalina sosai.
A cikin hakan ne ranan sai gashi ya shigo muna da takardun karatun mu wanan abin ya ban mamaki matuka.
Duk ina karama haka bai hanani fahintar hikiman shi na kyautata min a gaban su don kawai su dauka kwai fahinta a tsakanina dashi.
Idan ka gani zakacd duk dadin duniya ya kare a guna yadda yakan sayo min abu mai tsada ko ban kulawa a gaban su.
Nikan da abin yakanzo min bambarakwai bana iya boye mamakina a fili ko rashin sabo da haka daga gareshi.
Na samu hjy a daki ita kadai muna hira nake fadin hjy tafiya zakuyi ke nan idan kun tafi nasan rayuwana yana cikin garari a gidan nan.
Hjy ta dago kai tana fadin akan wani dalili har zaki shiga garari yar nan sai lokacin na farga da kato baran da naso yi a gaban ta ashe.
Da sauri nace hjy idan ba wani da zan dan dinga hira dashi haka ai sai damuwa ya kamani ko tunda shi yaya ba zama yakeyi a gida.
Tare da fadin kuma din yace karatu zaku soma ai bada dadewa ba saidai tunanen gaskiyane don nima ban amince na barku haka daga ku sai wa yan nan yan arnakun ba a gidan nan gunda shi din dai bai zama.
Zan kara mai magana kan wace zata zo ta zauna daku nan don kwanaki nayi mai bai ban amsa ba kan hakan.
Barshi dani nasan yadda zan fito masa a yanzu dole ya yarda da hakan ai tunda dai ba zama zaiyi ba daku a gidan.
Ana gobe zasu tafi dagani har halimatu mun kasa tsayar da hawayen mu kuka sosai mukayi ranan saida muka ba kowa tausayi.
Shi da kanshi yaya ya rarashi halimatu don tace ita bin su hjy zatayi ta koma Nigeria da zama daya tambaye ta dalilin ta tace nan din yaya ba a fita kuma bama jin yaren su ai suma basa jin namu kuma.
Da kyat ya samu ya rarashe ta hanyar cewa muma bada dadewa ba zamu je Nageria yanzun ta bari su hjy su fara tafiya don kada tayi fadan zuwa damu.
A airport ma ban iya tsayar da hawayena ba sai faman kuka nakeyi hjy ma hawayene yazo mata tana sharewa da gefen gyalen dake jikin ta.
Ta dan dafani tana fadin zainabu wanan shine aure dakike ji ana fada a rabaka da iyayyen ka da kowa naka zuwa inda baka taba rayuwa a ciki ba sai halin da kaje dashi.
Shiyasa kike jin ana fadin aure yakin mata don idan ba mace ba babu namijin da zai iya barin gidan su har abada sai kadan da suke shigewa duniya.
Gidan ya koma muna ba dadin zama mu biyu kawai ke rayuwa a cikin sa haka zamu suni zungun a gidan idan dare yayi kuma kafin ya dawo ma mun shiga kwana koda kuwa ba barci zamuyi ba a lokacin sai mu zauna muyi ta hira ko labarai a tsakanin mu muna dariya.
Har ranan da zamu fara fita zuwa school din yayi a zatona shine zai kaini school din sai gashi driver yasa ya sauke mun don an gama biyan komai a lokacin.
Sai gamu a bakon wuri muna faman robon ido don ganin bakar fata a wanan wajen sai can ba a rasa ba zaka gansu jefi jefi kuma ba yanayin musulunci a tare dasu.
ZAINAB IDRIS MAKAWAKaratu kab zance ba dadi gaskiya da farko har ina shawaran fasawa a raina don kalubalin launin fata na farko da nake gani.
Sai nabiyu yanayin shigana da ya zama masu abin kallo a can don na kasa amfani da kayan da yaya ya sayo min ko guda har wanan lokacin.
Sai na uku shine karatun gaskiya ba fahintar shi nakeyi ba gashi dai turanci ne amma sai yake min kama da yare sukeyi idan suna bayanin su.
Wanan dalilan yasa na saka damuwa a raina sosai har nake shawaran na daina fita kawai idan yayi magana nace dashi fasa kawai.
Wanan shawaran na yanke a raina bazan kara zuwa daukan lectures ba shike nan nasan ma ba zai tambaya tunda baida lokacin mu sam.
Itama dai halimatu kusan wanan matsalan take fuskanta sosai a karatun ta tana yawan min korafi kan challenges din da ake mata a school din da take zuwa din.
Ranan da nake wanan tunanen a ranan ne ya shigo muna dakin mu har mun kwanta ya buga min kofa misalin karfe takwas na dare kenan a kasan.
Da mamaki a fuskana nake kallon kofan kafin inyi karfin hali na mike daga inda nake zaune a kasa ina bitan karatuna don banson a tambaye ban sani ba yasa nake kwakwafewa da bita duk dare.
Kofan na bude a hankali yana tsaye har lokacin sai dai yanayin shi ya nuna ya gaji da tsayi a wurin don bugun kofan.
Zan iya cewa kwana kusan uku ke nan bamu hadu dashi ba a gidan do lokacin da muke fita bai fito daga part dinshi ba da safe.
Ko idan mun dawo har dare bai shigo ba don haka bama haduwa kuma bana gane meke faruwa a kidan da dare.
Ina wuni nace a sanyayye daga can cikin daki kuma halimatu ne ke gaidashi ya barni a tsaye wurin ba tare da amsa min gaisuwa na ba yana kokarin shiga dakin.
Da sauri na jaye jikina na bashi hanya ya karasa shiga daga ciki yana fadin sadiya karatu ya boyeki yanzu ba a ganin ki ko ?
Dan dariya tayi ta kara gaida shi na juyo zuwa cikin dakin daga inda ya barni a tsaye yana tambayan halimatu din I hope karatun dai sauki ko ?
Tace ba, ba dadi yaya don bana fahintar me suke fada sosai dan dariya naji ya kwashe dashi kafin yakai tsugune yana fadin.
Sadiya in kin daure zaki fahincesu ai kin taba ganin wanda ya samu a cikin sauki kowa kikaga ya zama wani abu a duniya jajircewan shi ne takaishi ga hakan.
Ki daure ki fahinci me ake koyar dake zaki gane watarana har kizo ki fisu ga baki daya ajin ko baki son inna da Abba suyi alfahiri dake wata rana .
Kai maddala da haihuwan da sukai maki yan uwa su huta ta gareki bakiga mamina yanzu itace abin kwatance a dakin su.
Kai halimatun ta daga mai kamar tasan komai yace good wata rana kema sai kin fita a rayuwa amma fa hakan bai samuwa sai kin daure kin natsu zaki gane hakan.
Ilimin mace ko da bata aiki bai taba tafiya a banza don zata waye tasan mai duniya ke ciki har ta taimakawa yayan ta itama .
Halimatu ne ta katse shi da fadin ai yanzu yaya na fara ganewa kuma sun daina tsokana na da sukeyi da tunda na fasawa wata baki a cikin su ranan.
Yace subbahanallahi sadiya ki daina fada fada ba kyau nan ba ruwansu sai su kulleki ba matsala bane a garesu nan.
Alaman tsoro karara ya baiyana a fuskanta lokaci guda don jin abinda ya fada tace na daina ai yaya bazan kara ba.
Kada ki kara kinji tashi kije falo zakiga wasu kwalaye da komai saman kujera ki kwaso kizo dasu nan ta mike da sauri zuwa inda ya aike ta kafin shima ya dago kai ya juyo gareni yana fadin.
Baki dai da matsala wurin karatun ki ko na dan girgiza kaina a hankali alaman a,a ga sytem nan na sayo maki don su nan komai saida shi sukeyi zakiji saukin karatu.
I hope kin san yadda ake amfani dashi dai ya tambaya nace eh duk da ba iyawa nayi sosai ba gana Anty Aisha da nake gidan mami takan dan bani in jagula kafin matsala ya shiga tsakanin mu dasu.
Halimatu ta dawo dakin dauke da kwalaye niki niki ba bita da kallo ya karasa bakin gado ya zauna ta zubesu a gefen shi zata juyo yace dawo nan ki zauna .
Karamin kwalin ya dauko yana kokarin budewa tare da fadin wanan naki ne sadiya zai taimaka maki wurin karatu sosai.
Da sauri na dago ido ina kallon shi da mamaki halimatun ce za a bawa laptop haka karami mai kyau da tsada.
Halima ta dan rike mai hannu tare da fadin yaya na gode Allah ya saka da alheri ya kara yawan arziki mai albarka yayi murmushi kawai.
Wanan abin yaban mamaki gaskiya shiru nayi da bakina har ya fita a dakin ya dago kai yana kallona tare da miko min sauran kwalayen dake gefen shi.
Nima ba wani magana ko nuna murna kan kyautan haka na karasa na amsa a can kasan makoshi nace dashi angode.
Na nufi gefen shi na aje tare da juya na duka ina tattara takardun dana bari a kasa ya bini da kallo yana dan girgiza kai ya mike tsaye zai bar dakin.
Sai kuma ya juyo yana fadin idan idan fa abincin da kuke tafiya dashi bai maku ba zaku iya magana su canza maku akwai komai idan babu zasu sayo ma.
Yayi kawai na basa amsa don ni haka kawai yanzu nake jin wani irin haushin shi a raina wanda na rasa dalilin hakan ni dai kawai haushinsa nakeji kawai.
Shima ya fita yana tunane a zuciyar shi don ya zaci zanyi murna sosai da wanan kyautar saidai kuma yaga sabanin hakan.
A fili yake fasin kai mata dai suna da kama da hawainiya yau ka gansu fari gobe baki ji wanan yarinyar har tasan wani abu can fushi da mutum yanzu .
Toma wai me akai mata take shan wanan kamashi da mutane haka ta nisanta kanta da shiga mutane ta kuma hana yar uwanta sakewa yanzu.
Ban yarda halimatu tayi amfani da su ba don yana fita dakin da murnan ta ta shiga budewa ina kallon ta saida ta gama budewa ta koma ga nawa ta fara budewa.
Laptop ne samfarin Apple da abin cajin shi sai wasu tarkace nasa a cikin kwalin ta koma ga dayan kwalin ashe wayace kiran iphone ya sayo min nina dauka duk takarcen laptop din ce duka ashe wayace a ciki.
Mamakine ya kamani kwarai da ganin haka bayan wanda ke hannuna baiyi komai ba a lokacin.
Haka na dauka ina kallo cike da mamaki sai naji banji dadin rashin godiyan da bai ma da muhinmamci koma dai me yakeyi kanshi ruwansa ai tunda har yai min alheri haka ya kamata in gode mashi sosai ai.
Muryan halimatu ne ya dawo dani ga tunanen tana fadin yayan mu sai ki ban wanan tshon naki ke nan ko ?.
Haba halimatu ya kamata ki tsaya a matsayin ki ko kin manta da cewa mu din diyan tallakawane wai ?
Koni kina gani da taka tsantsan nake takona a gidan nan don ban yarda na zurewa komai ba tunda auren nawa kila wa kala ne kindai san komai.
Ko yau ko gobe mami na iya cewa danta ya sakeni kinga sai mu koma gun iyayyen mu da zama ki fada min idan mun saba mun shagala a cikin daula haka ?
Idan mun koma gida halimatu waye zai bamu wanan dadin wani hali kikeson mu shiga a lokacin idan mun saba da wanan gatan haka ?
Kai ta dukar kasa tana wasa da hannayen ta nace niko wanan laotop din daya sayo maki ba zan yarda kiyi amfani dashi ba a yanzu balle wata waya can.
Saidai idan nawa zaki dauka ki dinga amfani dashi ba zan hanaki ba halimatu amma ki rike wanan abin sam wallahi ba yanzu ba gaskiya.
Ta dago kai da sauri don jin abinda na fada nace eh haka nace ko baki yarda da hakan bane yanzu in kira Inna in fada mata tunda ga waya na samu yanzu ?
Tace na yarda mana yayan mu baga shi zamu dinga amfani da naki ba nace haka nake son ji halimatu shiyasa nake jin dadin ki wallahi yar kanwata.
Haka na kwana da wanan abin har washegari banji dadin yadda ban nuna mai jin dadin abinda yasayo min ba.
Karshe dai na yanke shawaran inje in sameshi tunda ranan ba aiki nayi masa godiya don yasan na yaba da kyatan nasa gareni.
Na shirya tsab dani waini a dale zan shiga wurin maigida yasa na danyi kwaliya daga cikin ire iren kayan da yake sayo min a yanzu.
Halimatu na barcin ta hankali kwance saman gado har na gama shirina na fita dakin bata sani ba na jawo kofa na rufo.
Tunda na tun kari kofan haka kawai naji gabana yana faduwa bansan dalilin hakan ba gareni cikin daurewa har na karasa na tura kofan falon yana bude na sa kai na shiga da sallamana.
Duk da nasan ba lalai bane in sameshi a falon lokacin don yau ranan hutu ne ga kowa saidai ina shiga idona yai arba dashi a zaune saman kujera daga shi sai tawul a jikin shi daure.
Wanan Nabil din dan kasan Egypt yana kwance shima kamar yadda ya jafar din yake sai dan karamin tawul a jikin shi ya dora kan shi saman cinyar yaya danin suna dariya.
Innalillahi na fada da karfi tare da saurin juyawa na bar falon gurin sauri ma ban ko rufo kofan ba a yadda na sameshi haka na bar masu shi a bude don gigita.
Daki na koma na mayar da sauri na isa bakin gado na zauna gabana sai faduwa yakeyi fa fa fa fa kamar zasu iya biyoni nake gani nakai kallona ga kofan naga ai na saka sakata dana shigo.
Gudun kada ya biyoni a baya shi kanshi karo na biyu ke nan da nake ganin sa ba tufafi a jikin shi ko wani lokaci kuma tare da wanan shedanin mai abin mata.
Don ni yagin yan daudon garin mu dake suyan kaji da masa nake gani a gareshi ko yaushe idan na gansa a gidan.
Haka kawai nake jin tsanarshi a raina balle yanzu da nake yawan ganin sa a gidan tun da su hjy suka bar garin .
Yake yawan zama a gidan ko yaushe ko zamu hadu bangaidashi shima bai gaidani saidai ya wuce in wuce na kumayi warning din halimatu sosai kan kowa itama bata kula sha,anin sa sam.
Don ya koma kamar dan gidan don wani lokaci zaka ganshi a dining zaune yana cin abinci ko yana falo mu yana kallo ko wani abindai a gidan.
Tambayan kaina nagi wai ashe maza suna haka dama to aini banga mata suna wanan rashin kunya ba koda yan uwane .
Da zarab sun fara girma zasu fara boyewa junan su tsiraicin su su kuma nisanta jikin su ga kowa koda kuwa daki daya suke.
Wanan din hakan shine wayewan ko turancin koko zama da jajjayen fata yasa yaya yake kokarin barin addinin shi ne wai haka ?
Gaskiya shi kan yaya ya fita daban nake gani da yan uwan sa wai dama haka yake baida kunya ashe kana ganin sa da farko zaka dauka mutumin kwarai ne yasan addinin shi.
Ka ganshi kamar kamili a idanu wallahi na dauka shidin wani uztazune farkon ganina dashi da sanin danayi masa.
Gashi da tausayi ga idanu da kawar da kai ga kowa da yake tare dashi bai shiga harkan kowa kona yan uwansa kuwa.
Amma zuwan mu nan duk na raina wa yan nan halaiyan nasa ga baki daya sam baida riko ga addinin shi nake gani.
Ni banyi barci ba kuma ban fita ba ban yi wani abu a dakin ba har lokacin da halimatu ta tashi ta sameni a hakana.
Ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin wani dan riga a jikin ta take fadin yayan mu muje mu karya a kasa ina zaune kamar an dasani a wurin .
Ban motsa ba kuma ban bata amsa ba har ta kara maimaita abinda ta fada ki je kici na fada ba tare dana kalleta ba .
Itama wani irin kallkn zargi take min lokaci guda har lokacin idona sai hasko mi yanayin dana samesu a ciki yake min.
Ko naje na hado muna ne ta fada na girgiza mara kai tare da mikewa don ban yarda in barta ta fita da wanan dan iskan dake gidan ba a yanzu tunda na gane nan ya kwana tunda a tube na gansa ai.
Irin tarbiyan da innan mu tabani na nisantamu da maza dama kowa nake kokarin ba halimatu a yanzu don sam ni ban yarda da tarbiyan su ba a kasan.
Tare muka fito muka zauna har saida taci ta koshi take fadin yayan mu ba zakici bane nayi dan murmushi na fara tsiyaya ruwan tea a cup sugar kadan na zuba na kafa kai ina kurba a hankali.
Shine ya fara fitowa nayi saurin kawar da kai daga kalon su saiga dayan ya fito wanan karon sunyi wanka sun saka tufafi a jikin su saidai ina ganin bai kula damu a wajen ba don ya fito yana waya tare da sauri ya fita.
Saiga shi Nabil din ya biyo bayan shi shima suka fice a tare na aje cup din ina jin wani iri a raina godiya na ga Allah halimatu bata kula dashi ba kartace zata gaidashi.
Tun wanan lokacin nikan ban fito ba ina daki haka nayi weekend din kumshe a dakin sai ko idan na dan fito da halimatu ba zan dadeba zamu koma ciki.
Bansan kome ya gani ba da daren lahadi muna shirin kwanciya sai gashi ya shigo dakin namu kallon halimatu da hankalinta ke gun waya yayi yana fadin halimaru .
Ya kamata dai a saka maku kayan kallo a part din nan tunda baku fita falo yanzu ku zauna ka barshi muma ba jimawa zamuyi a kasan nan ba gida zamu koma.
Yaushe ke nan ya tambaya ko gobe ne idan ka shirya sallaman mu na basa amsa ina kawar da idona garshi .
Baki shirya tafiya ba ke nan idan dai nine zan sallameku ashe na gane bakya son a zauna lafiya dai ?
Idan dai wanan dan isk, , , sai kuma nayi shiru kafin in sake fadin gaskiya ba zan iya zama gidan nan da wanan katon daka aje muna ba a gidan nan .
Wani kallo yai min da sauri yake fadin wani katon ko bakon nawa kike son kira da kato yanzu kina da hankali kuwa ?
Shiru nayi ban kara magana ba na dukar da kaina kasa shiru yayi shima ya ya tsura min ido na dan lokaci kafin ya juya ya fice a dakin.
Muryan halimatune ya dawo dani daga tunane yayan mu zamu koma gidane ko ?.
Wallahi nima ina son inje gida sa,adatu taga yadda na koma a yanzu duk sun san nafisu wayewa yanzu ?
Halimatu ki barni don Allah kin cikanu da surutu wallahi na fada a dan hasale yarinyar fa bini da idanu don tasan batayi min komai ba na hauta da fada haka.
Munyi haka dashi kwana biyu sai na bar ganin Nabil din a gidan nasa din maganan da mukayine dashi ya sallameshi .
Tun dana kula da hakan na danji sanyi a raina ranan har muka fito falo muka zauna a cikin sakewa don yan aikin sukan ba ruwan su damu basu kuma shigowa inda muke kasafai sai idan sun shigo yin wani abu a gurin mu din.
Tunda na samu waya yanzu akai akai nake kiran innan mu saidai ban fada mata matsalan danake fuskanta a gurin shi ba.
Idan ta tambaye mu muna lafiya nakance lafiyan mu kalau nakan bawa halimatu suyi ta hira da yan uwan mu tana basu labarin abubuwan da muke gani a nan.
Suma sukan labarta mata abindake gida har sukan zolayeta da ta dawo gida tace dasu sai tare da yayan mu idan zata zo mu koma tare.
Hakan nawa innan mu dadi a ranta takan nasa muna zaune cikin salama da jin dadin rayuwa nida mijina ke nan wanda take alfahari da hakan ko yaushe.
Idan mutane sun tambaya takan ce muna lafiya ita kan gaskiya sai sam barka don yanzu ta huta gaskiya don haihuwan diya mace yai mata rana a rayuwan ta.
Da ace innan mu ta sanda zaman hakkurin da nakeyi da bata furta hakan a kaina da zata kwanmace in dawo gida gabata zaifi.
Irin wanan tunanen nakanyi idan na tuna da alfaharin innan mu din a kan auren nawa da zata san halin da mijin nawa ke ciki dayi tir da Allah waidai da halin sa.
A nan falon ya shigo ya samemu nayi mamakin ganin sa gida a wanan lokacin don rabona ma da ganin sa tun ranan da mukayi wanan zancen dashi.
Ya shigo muna gaidashi ya amsa muna da kyat ya shige part dinshi binshi mukayi da kallo halimatu ke fadin kamar dai yayan mu baida lafiya fa ?
Nikan ban kara bi ta kansa ba tunda banga ya fito ba har muka shige dakin mu bai fito ba dare yayi ina shirin kwanciya naji waya na ana kira na dauka bakon layi ne na kasanbake kiran dashi.
Da tsoro na dauka na kara a kunnena muryan shine naji murya a ciki ciki yana fadin.
Zainab ki shigo banda lafiya sosai ki taimaka min don Allah ?
A dan razane na mike tare da jan hijjab dina na fita a firgice na bar dakin wanan karon ma a tsorace na shiga part din.
Baya falon nasa don haka nasa kai zuwa dakin da nake zaton shine na kwanan sa don nan din nake tsanmani dakin sa.
Da sallama a bakina na shiga na hangoshi saman gado sai faman juyi yakeyi yana wani irin nishi da kugi mai sauti tun daga kofan nake iya jiwo shi.
Da sauri na karasa kusa ina fadin yaya meya sameka a rude nake magana don bansan irin taimakon da zan bashi ba a lokacin.
Da kyar ya iya dago kai ya dan kalleni tare da min nuni da hannu yana fadin da kyar duba cikin fridge ki dauko min magani nan a wani kwalba fari.
Na juya da sauri zuwa inda fridge din yake na bude idona ne ya fara tozali da kwalaben giya dako ba a fada ba nasan na giyane duka.
ZAINAB IDRIS MAKAWAHannuna na rawa nake daga kwalban a hankali ina kallo daga wanda yai rabi sai wanda ya kusa karewa saiko wanda ba,a ma bude ba.
Wani iri nake ji a zuciyana naga kwalban da yai min kwatance in dauko mashi na dauka na koma da sauri har lokacin yana a yadda na barshi yana nishin .
Mika mai nayi zan juya naji yana fadi cikin wani yanayi ki taimaka ki bude min don Allah ki bani ba zan iya komai ba yanzu.
Dan hararan shi nayi babu wanan tausayin nasa a fuskana irin na dazunna balle marfin roban na zuba mai a marfin na mika mai ina kawar da kaina gefe daya.
Don na gane shi din ba abin tausayi bane gama wani labari dana karanta na wani mashayin giya da yadda giya take wahal dashi kuma bai daina sha ba.
Ki taimaka ki kaini bandaki na watsa ruwa ko zanji dan karfin jikina bayan ya miko min marfin ina kokarin rufewa.
Dago kai nayi da sauri na dan kalleshi kamar zanyi magana sai dai na dake don alama ya nuna yana jin jikin nasa sosai a lokacin.
Cikin daurewa na juya ba tare da yin magan ba na nufi bandakin na hada mai ruwan mai dan zafi
Na dawo na sameshi a kwance wanan karon saman kafet yake kwance a tsakiyan dakin shi.
Ban san lokacin dana kai durkushe ba gaban shi take idona ya fara fitar da hawaye lokaci guda.
Sai wani nishi yakeyi mai ban tsoro wanda hakan ya kara firgitani a fili baima san ina gaban shi ba don idon shi a rufe yake yana faman juyi.
Ko yaji kanshim jikina ko kuma zuciyar shi ta bashi ina gurin ne ya bude ido a hankali ya sauke a kaina.
Cikin wani irin murya yake fadin ki daure ki taimakeni zainab zan mutu yana mika hannun shi zuwa inda nake gurfane muryan shi tankar ba nasa ba.
A cikin rudu nace yaya mai zan ma yanzu wa zan kirama ya kaika asibiti shi zaifi ba zama gida da wanan ciwon ba tun kan dare yayi.
Ji yayi tankar ya rungumeni don wani irin sha,awan dake taso mai lokaci guda kamar ransa zai fita.
Ya lumshe ido ya mika hannunn shi ya riko hannuna yana fadin kirjina da marana kamar zai fashe wani irin ciwo yake min.
Ya danke hannuna sosai ji nayi jikin shi na wani irin kadawa tausayin shi ya kamani lokaci guda har na manta da haushin sa da nake ji a raina ina jin tankar na yaye masa ciwon ya huta da wahala.
A hankali na runtse idona don tausayin shi da nake ji ga kuma hannun shi daya rike nawa ina jin wani yanayi a tare dani.
Ga jikin nasa da yanayin zazzabi gashi yayi wani irin rama lokaci guda jikin shi kamar ba nasa ba babu kuzari a tare dashi.
Ya dan dade rike da hannuna a jikin shi a hankali yake sauke ajiyan zuciya alaman ciwon na lafawa a lokacin.
Nace yaya tun yaushe ne baka da lafiya haka baka kula har ciwon yai nisa haka a jikin ka ?
Da kyat ya bude ido ya kalleni a sanyaye idon shi da kyat yake iya budan idon yake fadin zainab yau two days ke nan ina fama haka.
Idona na runtse runtse lokaci guda na shiga wani irin damuwa da dan tunanen halin da yake ciki din.
Cikin daurewa nace kaci abinci kuwa yace na dan sha ruwan coffee da safe na mike tsaye ina fadin bari na debo ma wani abu kadanci yanzu.
Sai lokacin na tuna hannun mu yana sarke dana junadashi da sauri na kalli hannun don har lokacin bai sakeni ba na dago na dan kalle shi muka hada ido nayi saurin dukar da kaina kasa.
Nace bari na kara hada ma ruwan dumin ka watsa ko zakaji jikin ya sakema yace to zainab tunda kina son inyi a yanzu.
Tsikar jikina naji ya tashi don irin kallon da yake min a lokaci na zare hannuna dake sarke da nasa na juya ya dan bini da kallo.
Ruwan dumi na kara hadawa wanan karon yafi na farko zafi don zazzabin da naji a jikinshi dazun.
Na matsa mai maclen ga brush sanan na fito na sameshi har lokacin a inda na barshi kwance a kasa.
Murya kasa kasa nake fadin na hada ruwan a bandaki yaya ka tashi kayi wankan ko ?
Jin yayi shiru gabana ya fara faduwa na dauka wani abune ya sameshi kuma lokacin ganin yadda ya lefe baya ko motsi .
Hannuna nakai saman wuyan shi a hankali ina tabawa naga ya dago kai a hankali yana kallona cikiin wani irin yanayi na zafin ciwo nacin sa sosai.
Ya mike yana mai mika min hannun shi na kamashi ya mike tsaye yana dafani har zuwa bandakin saida ya fara alaman tube tofafin jikin shi nayi saurin fitowa naja masa kofan.
Ina fitowa na nufi gadon da yake a yamutse na gyara mai shi tsaf na kara gyara mai ko ina na dakin sannan na daga filo na aje mai kudaden dana gani a dakin.
Saidana shirya komai tsab a dakin na fitar mai da wasu kaya masu laushi na dora saman gadon sa.
Kitchen na shiga nasa julie ta hada mai kalar abincin sa da yakw ci idan baida lafiya a take jiki na rawa ta fara hada mai abincin na koma in gani ko ya fito daga bandakin.
Sai jin kakarin amai naji shi yana yi daga cikin bandakin da sauri na isa kofan bandakin ina kiran sunan shi a hankali.
Da kyar ya amsa min a wani irin yanayi sai can ya bude kofan ya fito yana rangaji ya nufi bakin gado ya zauna.
Da sauri na karaso wurin ina masa sannu ya kai kwance daga shi sai tawul a jikin shi yana maida numfashi a hankali.
Sannu da jiki na kara mai na dan dade a tsaye saman kanshi ina kallon yanayin da yake ciki na ciwon dake damunsa din.
Kafin in juya in fita zuwa kitchen inda na samu julie ta hada abincin tana kokarin dauka takai masa na karba tare da yi mata godiya na bar kitchen din.
Still dai a kwancen yake ya dora hannayen shi saman goshin shi ya rufe fuskan shi dashina aje abincin tare da fadin yaya ka daure ka saka kaya a jikin ka mana sai ka danci wani abu.
Da kyat ya mike yana gyara tawul din dake jikin shi na kawar da idona da sauri daga kallon shi don abinda naga yanayi ban taba ganin namiji tube a haka gabana ba sai wanan ranan.
Da kyar ya iya saka kayan a jikin shi ina mashi sannu a yadda nake kaina na duke ina kallon kasan ties din dakin dake sheki da daukan ido.
Shima hankalin shi na gurina don yana tausaya min saboda ganin yadda na damu cikin dan lokaci kananki da ciwon shi.
Yaci gaba da kallon yanayina bai iya magana ba har ya gama shirin shi ya dawo gaban abincin dana ajemai ya zauna .
Da sauri na mike ina kokarin zuba mai yana kallona yana mamakin yadda na sa aka hada mai wanan abincin don gaskiya shi kadai zai iya ci a lokacin.
Nagama na juya zan bar gurin ya dago kai ya bini da kallo can naji muryan shi yana fadin kada ki fita ki barni ni kadai yanzu.
Jikinane yayi sanyi don jin abinda ya fada nace zan duba halimatu ne in dawo don bata san na bar dakin ba tana barci.
Daga haka na fita na barshi a dakin ina tunanen yadda lokaci guda yayi laushi haka kamar bashi ba.
Tana kwance abinta tana barci har lokacin hankali kwance na kara ja mata abin rufan ta data rufe dashi na shiga bandaki na kara wanka don dan aikin danayi naji jikina ba dadi.
Na fito na gyara jikina na shirya na fito tare sawa kofan key ta baya zuwa part din yaya yana kwance share share saman gadon.
A hankali na mayar da kofa na rufe na karasa bakin gadon ina kallon shi kafin in mayar da kallona wurin abincin dana zuba mai.
Baici komai ba nake fadin yaya bakaci abincin ba ai ya dan dago da kyat yana fadin amai na kara yi danaci.
Allah ya sauwaka nace mai tare da nufa wurin kayan ina hadawa yace ki barsu har da safe a fita dasu bari na fita dashi yanzu kada ya bata dakin na dauka ba tare jiran jin abinda zai fada ba.
Na dawo tare da rufo kofan a hankali na samu gefen gado na zauna tare da tsura mai idanu ki kwanta zainab na gode ya fada a sanyayye.
Zan kwanta a can na nuna sofan dake can gefe daya a dakin naji yace No ki kwanta kawai a nan bari nina koma can yana kokarin mikewa tsaye.
Ni dai ido na kura mai har yakai ya kwanta tare da dunkulewa a wuri daya na dade a zaune ina kallon shi kafin na dan kwanta a hankali don dare yayi sosai a lokacin.
Barci ya daukeni a yadda na kwanta din har bansan a inda nake ba sai can cikin dare cikin barcin nake jin wani irin nishi a gefena.
A hankali nake bude idona na dauka da farko ko mafalki nakeyi saida kara bude idon naji a fili nake jin nishin na fitowa a gefena.
Idon na ware gaba daya sai a lokacin na tuna a inda nake tare da dan dawo da hankalina wurin danake jin nishin nasa.
Ban fahinci halinda yake ciki ba nayi yunkurin mikewa zaune ya kankame min jikina yana fadin please kada ki tashi zainab ki taimaka min in samu relief daga gare ki .
Hakana daure yana kankame dani har lokacin da naji ya sake wani ajiyan zuciya mai karfi kafin naji jikin shi yayi lakwas na dan lokaci.
Nidai ina wuri daya a takure a cikin tsoro da fargaba sai naji ya sakeni ya juya yana gyara kwanciyarshi sai lokacin na sauke wani irin ajiyan zuciya tare da dan juyawa.
A hakan har na koma nayi barci na sai asuba na falka don lokacin tashina sallah yayina sauka saman gadon a hankali don kada na tayar dashi ya falka don a zatona ya samu barci.
Sai na ganshi a wurin sallah shi yana sallah abin ya ban mamaki ganin hakan fasa shiga bathroom din nasa nayi na juya zan fita yake fadin ki shiga nan kiyi mana.
Kamar munafuka na shiga nayo alwala ban dade ba na fito sallah nayi kafin in mike na bar dakin zuwa namu.
Ina budewa halimatu na dagowa take fadin yayan mu har naji tsoro na falka ban ganki ba da dare tsoro ya kamani .
Kai halimatu ina zani yanzu ai gani na dawo na bata amsa ina cire hijjab din dake jikina na nufi bandaki kai tsaye don in kewaya.
Saida na fito ina shafa mai nake fadin jiya jikin yaya ya matsa mai saida ya kirani da dare na sameshi tace da sauri yaya jikin nasa yayan mu ?
Yaji sauki yanzu na barshi yana sallah kafin in fiti na bata amsa naci gaba da abinda nakeyi na bata baya.
Idan zaki koma zanje in gaudashi naji ta fada nace ba tare dana juyoba ki bari idan ya fito falo ku gaisa ban yarda da zuwa part din shi ba.
Nima kinga ai saida ya kirani na tafi aka hada mai abinci nakuma hada mai ruwan wanka shine har ya samu barci.
Na dade ban koma dakin ba har wani lokaci banji motsin shi har kusan sha dayan rana kuma ban koma na lekashi ba.
Na dai yanke shawara a raina in lekashi inga halin da yake ciki yana barci sosai lokacin saidai na kula da baici komai ba tun safen .
Sai kofin dake aje a saman dan table din glass din dake dakin da kwalba a kasa a raina nace Allah yasa dai ba abin yasha ba da sasasafe haka a cikin shi watau giya.
Na juya zan bar dakin ya bude idon shi a hankali ya kira sunana na juyo inda yake kwancen ina fadin sannu yaya ya jikin ?
Naji sauki ya fada yana kokarin mikewa zaune daga kwancen nayi saurin fadin akawo ma abincin ne ?
No ki barshi yace tare da yunkurawa ya mike na bishi da idanu kasa kasa ina kallon shi a yanayin da yake tafiya a cikin rangaji.
A zuciyana nace ka sha ka bugu ina zakaci wani abincin a yanzu Allah dai ya rabaka da wanan halin ga baki daya.
Ya dan jima ya fito ya sameni a zaune can gefe ya samu daga karshen gadon ya dan kwanta ta hanyar daga kafan shi daya yana dan kadawa a hankali.
Gaskiya yaya yakamata ace ka daina wanan abin yanzu na fada kamar am matso bakina in fada mashi hakan.
Ido ya kura min sai na kasa karasa fadin abinda nayi niya kao tsaye da farko don tunanen danayi tayi ke nan dama a dakin.
Don sai nake gani kamar giyance har tayi mai over ya sakashi a wanan rashin lafiyan da yakeyi a yanzu.
Ina jin ki ya fada sai na dago kai na dan kalleshi ya tsura min ido yana kare min kallo cikin wani irin yanayi dana kasa fassarashi kona meye haka yake min.
Kafin inji yace dani me kika daukeni ne zainab kin dauka ban san me nakeyi ba har kika samu matsayin da zaki fada min magana kai tsaye haka yadda kike so.
Ni sa,an kine zainab ko shike nan don ina auren ki yanzu kike ganin kina da right din da zaki fada min maganan da duk yazo maki a baki.
Ganin yadda ya taso yana fada dani yasa na dukar daina tunda ya fara maganan sa ban dago kaina ba.
Wasa wasa saida ya kwana biyu bai fita ko kofa ba yana dakin sa a kwance ni kuma ina faman jinyar shi har yaji sauke ya fara fita .
Gashi ya rame yayi baki dan lokaci guda ya fada sosai ga wanda yasan yadda yake a baya da yanzu din.
Ranan mun fita zuwa school sai gaahi kwatsam ranan mun dawo daga school mun sami anty fadila a gidan kamar a mafalki muka ganta a falon kwance tana barci.
Ga jakkata na kaya ajiye gefe daya da farko ban ganeta ba sai muka kama mata kallon mamaki don ganin mace bakar fata irin mu a gidan kwance tana barci.
Halimatu ne da rigiman ta taje ta dan leka fuskanta a hankali ta sake wani ihun murna daya falkan da ita daga barcin tana fadin lah anty fadilace.
Anty fadila na fada a daidai lokacin da itama ta falka a cikin tsoro dama da tsoro tayi barcin don sai bata gaskanta cewa gidan da muke bane a ciki.
Munyi murnan da ihun ganin juna kafin in shige ina fadin ina zuwa na nufi part dina kai tsaye na bude na shiga da jakkan dake hannuna.
Yau kan yaya ya gama min komai tunda har ya kawo muna anty fadila wanan kasan sai nakeji kamar innan muce yakawo muna a lokacin.
Sai bayan mun gama murnan mu na ganin juna ne aka fara gaisawa da juna tare da tambayan ya bayan rabo ?
Wanan part din dasu hjy suka zauna na kaita dakin a share yake don a kullun masu aikin shara mutum biyune suna gyara ko ina na gidan tsab.
Munyi wanka da sallah kafin mu fito falo mu hadu har lokacin yaya bai dawo gidan ba duk da jikin shi bai gama warwarewa ba a lokacin don zakace yayi wani jinyane a gida.
Fadila kan sai mamaki takeyi a yan watannin da mukayi bama tare da ita wai mun kara girma mun waye haka lokaci guda a nata ganin.
Irin shirmen hjy tayi tana fadin wai ko ciki nake dashi a jikina na koma haka na cicciko nayi fresh dani farina ya karu sosai gwanin ban sha,awa dani.
Murmushi nayi kawai itama dariya tayi tana fadin gaskiya a binciki wanan sauyin naki zainab, don ni gabaki daya kin sauya min ne ai ga sanin danayi baki.
Lafiyanyyen aka shirya muna a dining don haka kai tsaye muka nufi wurin cin abincin halimatu ne ke fadin lokacin dana fara bude abincin.
Anty yau zakici abincin kasan nan kiji tunda muka barku mukai missing din abincin muna gida wallahi kila naman kawai zaki iyaci sai ferfesu.
Ta kalli halimatun tana dan murmushi tare da fadin nima nayi missing din ku sosai sadiya daga inda nake na harari halimatu tagane me nake nufi ta mike batare da cin komai a wurin tana fadi bari je inyi assigment dina ta barmu a wurin mu biyu.
Ga mamakina sai naga taci abincin sosai ba tare da nuna komai ba kamar yadda mu muke nunawa ga abincin don har yanzu ba komai muke iya ciba sosai.
Sai bayan mun gamane mun bar wurin zuwa wurin kujerun falon muka dasa hira yaushe rabo kamar munyi shekaru bama tare.
Da alama dai zainab komai yana tafiya daidai a yanzu tsakanin ki da mijin ki sabanin yadda kuka baro mu gida.
Don alamun sauyawan ki kawai ya nuna min hakan a yanzu don ance labarin zuciya a tambayi fuska naga farinciki sosai yanzu a tare dake.
Wata karfafan ajiyan zuciya na sauke tuni annurin fuskana ya dauke na dan kalleta ina murmushin dole lokaci guda.
Tace haba dai zainab kada kice min komai na nan har yanzu a yadda kuka barmu dashi don ni nayi zaton ai zaman ku wuri daya haka zai kara kawo shakuwa a tsakanin ku yanzu ?
Kai na gyada mata ina fadin kwarai akwai canji sosai yanzu ba kamar baya ba anty don yanzu akwai dan shakuwa a tsakanin mu dashi.
Sai dai wasu halaiya nasa ne na boye dana sani a yanzu suke tayar min da hankali sosai wallahi ban a cikin natsuwa ko kadan anty ga ba wani najikina da zan fadawa ya taimaka min da shawara.
Kina nufin yanzu kin gane abinda na dade ina kokarin fahintar dake game dashi ke nan zainab ?
Kai na gyada mata alaman na gane hakan sai ga halimatu tana fadin yayan mu nikin ban gane me ake nufi da wanan ba.
Na juya gareta cikin kulawa ina karban takardan dake hannuta take nabi komai da akai masu na fara yi mata bayani a tsanake yadda zata gane.
Wanan ne ya dauke min hankali na bar zancen hiran da mukeyi da anty fadila muka buge ga kararu dama aikin mu ke nan idan mun dawo ko kafin mu gama har lokacin dawowan yaya gida yayi.
Nan dai muka gaida shi da dawowa ya amsa muna yadda ya saba karbawa sai fadilace ta gaidshi a karshe yasa ya dan juyo yana fadin.
Af sorry kun iso lafiya ta amsa cikin danjin nauyin shi da lafiya kalau boss mun same ku lafiya ?
Lafiya ya bata amsa a takaice ya bar wurin zuwa part din shi kai tsaye ta sauke ajiyan zuciya tana kallona ko zan mike nabi bayan shi a lokacin sai taga sabanin hakan.
Ina zaune munci gaba da hiran mu da halimatu kafin inji tace mijinki fa yadawo daga aiki zainab kina zaune ?
ZAINAB IDRIS MAKAWAZuwan fadila garin yayi muna dadi sosai dan yanzu muna sakewa sosai har mun fara fita mu kaidai da kafa muna dan zaga unguwa.
Saban da can da muke zama a tauye a gidan bamu fita da mun dawo school munci abinci muka shiga sallah magariba bamu fitowa sai kuma gobe idan Allah ya kaimu zamu fita.
Ranan da babu karatu kuma a daki zamu wuni zaune sai mun gaji zamu dawo falo mu zauna mu danyi hira kafin mu shige.
Yanzu gidan ya koma muna kamar muna gidan mune Anchau a gaban iyayyen mu don yadda muka dauki fadila takar wata jinin mu.
Abu na farko data fara yi bayan zuwan ta shine karban girkin tana girka muna irin abincin mu wanda muke iyaci.
Don komai akwaishi saidai dafuwan ba iri daya bane da nasu na can sai masu girkin suka koma kallon ta kuma idan tana aikin.
Suma sai ya kasance basa iya cin kalan abincin mu idan ta girka wanan ba karamin jin dadin hakan nayi ba don yanzu kan muna cin abincin mu cikin sakewa ba wani kyamar komai a gare mu.
Ranan muna zaune da dare fadila ta jeho min tambayan da banyi zato ba wai zainab sai naga kamar har yanzu ba a dakin mijin ki kike kwana ba ?
Tambayan yazo min a bazata da sauri na dan dago kaina dubeta kafin in saki murmushin dole ina fadin kai anty fadila ke nan.
Ina kwana a can mana saidai ba kullun nake zuwa part din nasa ba na bata amsa a sanyaye ko ta fahinci wani abune ga amsan dana bata .
Sai cewa tayi amma ya kamata ki mai da hankali sosai ga mijin ki baki tunanen haihu ne har yanzu a rayuwan ki.
Buri ko wace ya mace ne idan anyi aure taga an fara aje iyali tsakanin ta da maigida tundai wanan uwar mijin naku da bata son ki da danta ko kadan.
Ko yanzu ta daina nuna maki wanan tsanar da take nuna maki da farko ne don irin su wani lokaci idan sunga an fara aje iyali a tsakani suna zubar da makaman yakin su su so matar a karshe ko dan haihuwan dake tsakani.
Shiru nayi ban tankata ba har ta gama bayanin ta tadaro a karshe da fadin na sha fada maki tun tuni ki dinga kutsa kanki gareshi zainab ko zaku samu shakuwa da juna.
A hankali na dago kai sai ga hawaye suna sulalo min a fuskana da sauri tace ki rufa min asiri ki daina kukan nan banzo kasan nan ba saida wasu sharuda da aka kidaya min su.
Yarda da amanan dake tsakani mu yasa har na fito maki da wanan maganan a yanzu don dan fahintar danayi na yadda kuke zama a tsakanin ku.
A hankali nakai hannuna ina share hawayen dake fuskana tare da fadin insha Allahu anty ba zan ja maki matsalan da aikin ki zai tabu ba a wurin shi zan dinga kiyayye duk wani abinda zai jawo maki matsala a wurin shi.
Zancen gaskiya kuma anty tsakanina da yaya babu sakewa ko shakuwa a tsakani mu har yanzu muna nan yadda kika san mu dashi sai ma wasu halaiyan da ba,a san yana dasu ba a can sai a na nasan su.
Don gaskiya sai nayi shiru na kasa fada mata komai don rashin ganin dacewan hakan ko yayane dai shi din miji ne a gareni kuma tankar dan uwa yake a wurina.
Tona mashi asiri kamar tonawa kaina ne yanzu don ko inna ba zan iya fadawa maganan nan haka kai tsaye ba don haka sai naja bakina nayi shiru ga fada matan.
Itama bata matsa ba sai ta sani sai naji ta dauko wani zancen tana fadin kinga ai dama dole kiga wasu halaiya na daban dabaki saba dashi ba don haka ki daure kici jerabawan ki zainab.
Allah ya nufa na bata amsa saiga halimatu ta fito da wayana ga hannu tana fadin an kiraki ga waya na karbi wayan daga hannun ta ina dubawa.
Layin Nigeria ne aka kirani dashi don haka nayi kira nima kira uku aka dauka nayi sallama muryan sa,adatu ne a layin .
Ina dauka take fadin yayan mu nayi waya yau innan mu ta saya min da kudin da mijin ki ya aiko mata dashi shine ta diba ta sai mun waya dashi.
Nace Sa,adatu nayi maki murna da samun waya ina innan mu da sauran yan uwa tace duk suna lafiya kalau nace innan mu tana kusane ?
Ta amsa min da gata nan nace a bata wayan ta karba muka fara gaisawa nace inna kin daina kirana .
Bana son ina damun kine yar mairo kada mijin ki ya daukemu marasa hankali tunda shi yana kira lokaci lokaci shekaran jiya ma ya turo muna kudi nida mahaifin ku.
Don Allah kiyi muna godiya nace to inna sai kuma tace ni kan nace ba wai yanzu cikin ki yakai wata nawa ne musan shirin da zamuyi.
Ciki inna na tambaya da mamaki tace eh a sanyayye ciki mana banaji kamar ana fadin cikine dake ba kwanakin baya da mukayi waya daku.
Banda komai inna na fada ina dan dariya Allah ya kawo mai albarka naji ta fada a sanyayye kamar bataji dadin abinda na fada ba na zancen cikin.
Muka daiyi sallama na kashewan ina ajiyan zuciya koda na dago kai anty fadila na kallona tun lokacin dana ambaci cikin .
Kinga zance na ya fara fita ko duk wata uwa ta aurar da yarta tana son jin wanan albishir din mai dadi a bakin ta don samun karuwa.
Ranan wanan tunanen ne ya hani barci sai juyi nakeyi ni kadai a daki don halimatu tana dakin anty fadila tun zuwanta a can ta koma kwana.
Babu kuma daman ince ta dawo daki ta gane a dakin nake kwana ba wurin shi ba ashema duk boyona ta gane hakan do wayau babba bai daya dana yaro.
Nayi tunane sosai kan sakon da yake turawa iyayyena a kai a kai kinga ke nan ko na fadi wani hali nasa na daban ba lalai bane a yadda da hakan.
Don haka na bar wanan zancen a raina tunda nasan wanan abinda yakewa iyayyena yana daga cikin abinda mami bata so a gareni dama.
Tun zuwan fadila garin ba wani sakin fuska a gareta dashi sai dai gaisuwa ya amsa mata kamar yana tsanan ta fuska daure.
A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah har gashi mun samu hutun makaranta mun gama zangon farko.
Halimatu ta rigani samun hutu don haka take gida a zaune tare da anty fadila kula kan yana bamu shi yadda ya kamata har nakan ji mamakin hakan a raina.
Har yakai muma mun samu namu hutun zamu dan huta a gida na kwana biyu ke nan duk da hutun ba mai yawa bane sosai.
Mun fara hutun mu dadi dadi sai nazo na fara samun matsala da ganin wanan Nabil di ya dawo gidan namu kamar da can baya.
Har yakai yanzu ma yana nuna min tsana irin wanda na fuskanta a wurin taju da farko shina wana sai yazo min da sabon sallon daya fara saka zuciyana a tunane.
Ranan dai na yanke shawara a raina zan gwada shawaran anty fadila in gani idan zai yi amfani a gareni.
Tun kan ya dawo gidan na caba kwaliya da ire iren rigunan da yake sayo min bana sawa don nuna tsirecin su a gareni.
Doguwar rigace mai guntun hannu baikai wuyan hannu har kasa ba sai wani uban tsaga dake iya nuna har cinyar mace idan ta zauna ko tana tafiya.
Na daure kaina da ribon ta baya don gashina yanzu yana samun gyara sosai saboda ina gyara a kai akai don zuwa school wani lokaci ma daga school zan tsaya in gyara kaina kafin azo daukana.
Kaina ba dan kwali dawowan shi yayi daidai da gama shafa komai na kamshi a jikina koda ya dawo bai samemu a falo ba daki ya nufa kai tsaye.
Na mike nabi bayan shi saida na tsaya na saita kaina a falin kafin in sa kai in shiga masa kai tsaye na tura kofan na shiga.
Yana tsaye a wurin fridge yana saka kankara a kofin daya dura ruwan giyan shi ciki har na karaso bayan shi bai sani ba sai ji yayi na kwanto mai a baya ina fadin sannu da dawowa yaya.
Wani irin zabura yayi cikin kaduwa da mamaki ya juyo yana kallona har ruwan nasa na kokarin zubewa lokaci guda.
Ya juyo yana fadin what is this noses zainab zaki zo min haka kin raini da yawa ko har yaushe kika fara irin wanan wasan haka dani.
Kaina na dukar kasa a hankali ina maijin wani iri a raina na disganin da yayi haka a lokacin .
Godiyana ga Allah mu biyune a part din lokacin babu kowa da bansan yadda zanyi ba ranan don da kunya ya rufeni gaban maishi a lokacin.
Dan marairace fuska nayi cikin daurewa duk da raina ya baci nace yaya kewan gida yau nakeyi yasa nayi hakan tunda kaine dan uwana a kusa yanzu.
Hannu naji ana tafawa a bayan mu da mamaki na waigo ina kallon mai shi wanan dai Nabil din ne a bayan mu daga shi sai tawul daure a kugun shi.
Yana takowa inda muke tsaye ganin shi a tube yasa nayi saurin dukar da kaina kasa da sauri dafa kafadan shi yayi tare da fadin .
Wellcome home dear yayi saurin baudewa tare da barin wurin da muke tsaye din ya nufi kujera da kofin shi a hannu ya zauna.
Wani irin juyowa nayi na watsawa Nabil din kallon tsana ido da ido yace a cikin yar murya ta yadda ni kadai dake kusa zan iya jin shi.
Mind you or else ya nunani da dan yatsar shi na hannu sai a idon yaya jafar din naji ya daka mai wani tsawa yana fadin .
Don't be silly Nabil dont you know she is my wife in life ko ka manta da warning din danayi ma a kanta ne tun farko.
Cikin wani irin murya ya dan rausaya kai yace Owoo wifery sam na manta da hakan ita din ne tana son min shishigi a rayuwa.
Ina tsaye sororo imani ya cika min zuciya da kalaman su lokaci guda na rasa maganan wanda zanyi nazari a cikin su yanzu.
Ko ma dai meye shi ya jafar din ya tsaya min a lokacin ya nuna ni wani abune ai a gareshi ga Nabil din.
Sai dai zancen Nabil din dake min warning a kan yaya din ne na kasa fassara ma,anan hakan gareni dayasa yake ban warning haka ?
Da karfin halin dana fara koyo a dan shiga mutanen dana fara yanzu sai ban yarda na fita falon ba don inga abinda Nabil din zaiyi idan na tsaya din.
Wurin da yaya yake zaune na nufa na zauna gab dashi ya kurbe abinda yake sha din tare da aje cup din yana fadin .
Zainab wai meke damun ki hakane yau kike wanan halin da ban sanki dashi ba da farko ?
Nace just ina dai son zama a kusa da kaine na fada ba tsoro ko kunya a idona ko kadan naga Nabil din ya juya zuwa sama.
Nabishi da kallo kafin in mike tsaye na bar wurin batare da kara furta komai na bar falon nasa zuwa part dina.
Gado na fada a yadda nake ban sauya komai nawa ba don bacin rai ina nazarin maganan Nabil a raina da yadda ya nuna min kishin shi a fili yau din.
Har nagaji barci ya daukeni a hankan ban sani ba sai ji nayi ana gyara min kwanciya na bude idona da sukai min nauyi ga barci ga kuma damuwa a tare dani lokaci guda.
Shine a kaina tsaye yana fadin zaki kwanta ki bar kofan abude haka kowa ya rufe kofan shi sai ke ?
Ka barshi hakan ba matsala bane na bashi amsa tare da komawa na kife a kwance ina jin shi saida ya dan dade a kaina tsaye kafin ya juya ya fita tare da rufo min kofan.
Saida na dan dade kwance a wurin kafin in daga a hankali zuwa kofan na rufo don tsoro hakan ya kamani lokaci guda.
Ban kwanta ba na cire kayan dake jikina zuwa rigan barci na na shiga ban daki na dauro alwala sallah nayi ranan sosai ina mika kukana ga Allah .
Kafin in daga saida naji duk wani damuwa ya fice min a raina lokaci guda na lalaba zuwa gado tare da kashe wutan dakin.
Washe gari ban leko waje ba don yanayin dana tashi a ciki haka kawai nake jin gabana yana faduwa min sosai.
Kamar banda lafiya da kyat na iya tashi na bude kofa misalin tara da wani abu na safe.
Komawa nayi na kwanta saidai kuma ba barci nakeyi ba nadai lefene kawai a saman gadon.
Naji an turo kofan yayan mu barci ne kuma kafin in dago in ce ba barci nakeyi ba anty fadila take fadin rabu da ita idan barci takeyi mana.
Ba barci nakeyi ba idona biyu na tashi tun dazun na fada ina dagowa daga kwancen mukai arba dasu.
Suna tsaye alama ya nuna sunyi wanka a lokacin don kowan su tsab yake a cikin shirin shi ina kwana nayiwa fadilan ta amsa tare da tambayana lafiya kike kuwa yau ?
Fuska na dan bata ina fadin jikinane dai wani iri nakw jin sa yau kuma haka kawai nake jin faduwan gaba a tare dani.
Kiyi addua koma meye Allah ya mayar muna dashi alheri daga haka mukaji takon takalman shi ya shigo dakin nawa.
Da sauri fadila ke gaishe shi ya amsa mata a irin yadda ya saba amsawa dan dama da halimatu ta gaidashi ya amsa mata din cikin dan sakin fuska kadan.
Takowa yayi har zuwa bakin gadon da nake a zaune tsakiyan gado yace ba zaki gaisheni bane ko har kin gama kewan gidan naki ?
Shiru nayi masa a raina nake fadin kai kuma kagama watsewan ka ba a yanzu ka fito kamar wani mutumin kirki dashi ?
Ai in babu me ganin ka Allah yana ganin ka bansan na fada a fili ba har ya jini ki min adduan hakan in daina nima ba yin kaina bane hakan.
Wani kallo nayi mai ina turo baki gaba tare da dan murgudawa ina kokarin kwanciya na bashi baya .
Ya juya ya fice daga dakin har na gaji da kwanciya natashi nayi wanka sai to one na fito falon gidan ban samu kowa a falon ba yasa na wuce zuwa dakin su kai tsaye.
Barcin su sukeyi hankali kwance don haka ban tayar dasu ba na dawo dining don duba abinda ke akwai na danci.
Waya na dauka ina video dashi ni kaidai a falon na rasa abinda zanyi inji sanyi har na aje wayan yana ta daukan abubuwa da kanshi a dining din saman jikina cikin mantuwa.
Bread na dauka da jam na dan fara cizawa jin shi nayi ba dadi a bakina duk son shi da nakeyi sosai ranan sai naji bai mun dadi ba sam a bakina.
Na dan taba hakana na aje ina wurin zaune kafin inji tako a bayana wani na tafe wurin na dan juya kadan don ganin mai zuwa a lokacin mukai arba da Nabil da yai kusa dani kamar zai shakeni.
Da sauri na mike tsaye tare da fadin innalillahi wa inna alaihim raji,un are you going to kill me cikin wani murya mai sauti na fada ina nuna shi da yatsa.
Ya nunani da yatsa shima yana fadin ki fita hanyar man dina idan ba haka ba nayi sanadin ki a gidan nan gabaki daya wanan shine warning na karshe da zan maki man bayayi dake.
Dan yatsana na daga sama ina nuna mashi nace Allah kadai yakai can ba wani mahaluki ba wallahi inkuma kana mamakine hakan ne ka gwada ka gani idan kaima baka bar duniyan nan with fulconfideces nake magana na.
Wani irin shu,umin murmushi ya sauke a fuskanshi kafin yace yarinya kina da karfin halin sosai nake gani.
Yatsun shi ya dan kada yana fadin nayi warning dinki akan jackson for the last time idan baki ji ba kuma ke kika sani.
Har ya juya nace bakaji ba mana sunan shi jafar ba jackson ba kuma ni din matarshi ce ta sunnan annabi don haka a yanzu dai banga wani mahalukin da ya isa yai min warning akan mijina ba sai mahaifiyar shi dake raye.
Wani kallo ya watso min yana kada kai nace kwarai zan rubuta in aje ko wani abu ya sameni a kasan nan kaine don ka fadi hakan da bakin ka .
Kafada ya daga min alaman ko oho nina sani yana sauke wani shu,umin murmushi na zaki gane kuren ki ai yarinya.
Ni kuwa a kasan zuciyana karfin hali nakeyi kawai don duk lokacin a tsorace nake dashi ina Allah Allah wani ya fito daga cikin dakunan gidan ya ceceni don na gama tsorata dashi saidai ban yarda na baiyana hakan ba a fili har ya gane hakan.
Ya juya ya tafi yana wani tafiya sai a ranan na gama kwankwance yadda yake ashe, zakace mace ce shi sak don in ba karya nakeyi ba ni har wetlips nagani a baki shi.
Ya tafi da kamar minti goma saiga halumatu ta fito inda nake tana fadin yayan mu kin fito ashe yanzun na fitone in dubaki ai.
Tana zama a kusa dani saman daya daga cikin kujerun falon ta kai hannunta ta dauki wayan dake saman jikina tana tabe tabe a cikin sa.
Ashe zata shiga ta samu wayan na recording sai tayi min serving din shi don kada tayi laifi a gurina idan ta fita kai tsaye.
Surutu take min ban iya bata amsa ba don sabon fargaban daya darsu min a zuciyana kuma na shi Nabil din kan abinda ya fada min kafin ya tafi.
Mikewa tayi da wayan a hannun ta ta nufi part dina tana shiga gado ta haye ta kwanta tana jagulan wayan haka na shigo na sameta a dakin.
ZAINAB IDRIS MAKAWAYana zaune yana sauraren wayan da mahaifiyar su takeyi da dan uwan shi tana wani lalashin shi a cikin wayan tare da kara warning din shi kan abinda take bukata.
Daga inda yake zaune yaja wani irin tsuki yana kawar da kai gefe daya wanan yasa mami dago kai ta dan kalleshi taci gaba da magana da danta tana nanata mashi zancen guda da cewa wanan kidahumar yarinyar daka dauko da kanwar ta.
Kana faman kashe masu kudi idan sunyi karatu a can uban wa zasu yi da karatun turai a kauyen su.
Wani kallo jamal yaiwa uwan ya kara kawar da kai daga kallon ta karshe ma yayi kwanciyan balance kanshi na kallo sama yana tunane.
Waikai jamal meye tsakanin ka da dan uwan ka ne ina lura tun dawowan ku kasan nan baka son zancen daya shifi jafaru sam.
Wani irin dago kai yayi daga yadda yake kwancen yace wa mami waini ina ruwana da zancen kuni.
Kaga jamal Ramatu ta fada min komai daya faru a can don haka yau ka fada min dalilin fadan ku da dan uwan ka kafin shima in kirashi inji meya hadashi da kai.
Mami ni babu abinda ya hadani dashi fa ita maman bata fada maki bane ita data kawo maki wanan labarin.
Ba wani zance na tambayeka ba illa ka fada min meya kawo wanan a tsakanin ku don na fara fahinyar abin naku gaba gaba yakeyi a yanzu.
Mami ba zakije ba kikace idan kinje zakiga abinda ya hadani dashi ai da idon ki don ni ba zan iya furta komai ba a yanzu.
Me kake nufi wai ko har yanzu bai daina shan giyan dana haneshi din bane wai dako hakane sai ya hadu da bacin raina.
Mami da ace ya tsaya ga giyaje kawai aida abinda sauki don yaya jafar gaskiya a yanzu yana cikin wani hali da abin bai faduwa.
Jamal me kake son ka fada min ne wai akan dan uwan ka a yanzu wani hali mai muni ya fada ko me ko matar daya daukarwa ransa ne matsalan shi ko ?
Ta tambaya cikin son ji idan nice matsalan dan nata har suke wanan rikicin a tsakani su haka aiko da ta raba wanan kazamin auren kowa ya tsaya masa akanshi.
Haba mami zainab fa matar rufin asirine a wurin mu da badon ita bace ya aura da ace wata ce da yanzu duniya tasan abinda yake ciki ai.
Don babu macen da zatayi hakkuri da hakan ta zauna lafiya ba tare da anjisu ba .
Ko ita din ai kwadaine daba haka ba ai ba zata yarda ba don kawai yana sha tace zata zauna ko tayi masa tonon asiri.
Wai jamal me hakan ke nufine kana mun magana haka a dunkule kafito fili mana ka fada min abinda ke faruwa na sani.
No mami ya mike tsaye tare da fadin nifa ba zakiji komai a bakina ba gara dai kije ki zauna kwana biyu ki fahinci komai da kanki zaifi.
Yana fadin haka ya juya ya fice daga falo mami ta bishi da kallon da bata san tanayi ba a lokacin don zuciyan ta daya lula a cikin tunane kafin ta sauke wani irin ajiyan zuciya na dan lokaci .
Tana jin kanta na wani irin sarawa lokaci guda da sauri ta jawo wayan data aje gefe tana neman layin mama Ramatun ta a lokacin.
Kira daya biyu gana uku ta daga tare da sallama da gaida ita lokaci guda ta katse ta da fadin Ramatu tambayan ki zanyi don girman Allah kada ki rufe min idan ma hjy ce ta haneki da sanar dani wani abu daga cikin halaiyan da jafar yakryi a can.
Ramatun tace jafar kuma anty me akace maki yayi muna van na assha kuma don daini gaskiya harga Allah banga wani abinda yakeyi ba daidai ba muna gidan sa.
Zan binkita in san ko meye yakeyi har yai sanadin hadasu fada da jamal haka yanzu jamal ke min wani bayani a dunkule wanda ban gane hakan ba har idon shi na kklarin kawo hawaye lokaci guda.
Gaskiya iya abinda na sani na fada maki ran nan don dukkan su sunki su fada muna kome ke faruwa a tsakanin su.
Bata bari ta gama bayanin ta ba ta kashe wayan din wani iri da take jin kanta a lokacin ba zata iya tsayawa ta saurari zancen yar uwan nata ba sam.
Ranan kan haka mami ta kwana tana tunanen duniya a karshe dai zuciyan ta yake fada mata kodai wanan tsintaciyat magen yarinyar ne ta kawo rigima a tsakan yaran nata
Da wanan tunanen ta kwana a ranta haka ta tashi washe gari cike da damuwa a ranta sallah kawai ta idar ta dauki waya ta kira ya mamud.
Yayi mamakin jin kiran mami da sassafe haka sai abin ya daga mai hankali sosai bai tsaya ba ya nufo part din mami din yanayin muryan ta ya nuna tana cikin tashin hankali.
Direct dakin ta ya nufa yayi nocking aka amsa mai ya shigo tana zaune a saman dogon kujeran dake dakin ta jikin ta saye da hijjab dark blue wanda ya kara haska farin ta a fili.
Mami lafiya ya tambaya a rude yana turo kofan dakin idon shi a kanta cikin nuna kulawa a gareta.
Bakin gado ta nuna mai da hannu kafin ya karaso inda take yakai ya zauna a wurin yana kallon ta ido da ido tare da kara maimaita tambayan shi a gareta.
Sai can ta dago kai a hankali ta kalleshi tana fadin jiya muke magana da jamal kan dan uwaka yai min hausa a dunkule dana kasa gane abinda yake nufi da hakan.
Don amsan daya ban shine inje kasan da kaina zan fahinci may ya hadasu fada da idona don shi yaki fada min kasan kuma halinsa tunda bai fada ba ba zaya fadi din ba ke nan.
Hakan yasani a rudani daren jiya banyi barci ba sai karshe nake hasashen idan ba a kan wanan yarinyar zainab bane haka ya faru a tsakanin su ?
Ya mamud ya dago kai yana kallon mami din cikin rashin fahinta abinda hakan ke nufi yace mami akan me zasuyi fada don zainab ?
Shine abinda na kasa fahinta nima idan bashi ba har me zai hadasu fada haka kafasan tsakanin shi da jamal sai Allah.
Kai ya mamud din ya girgiza yana fadin sai dai idan wani abin na daban ya hadasu amma banyi tsamanin wanan zai iya hadasu ba gaskiya.
Amma koma meye mami ki kwantar da hankalin ki zan binciki shi jamal din a tsanake ya fada min komai.
Amma baka ganin kamar yadda shi jamal yace dani da farko wai ya kamata naje na saka ido akan abinda ke faruwa da rayuwan dan uwan naku wani abune daya danganci hakan a tunanen ka ?
Mami duk da hakan dai ki kwantar da hankalin ki zanga shi jamal din muyi magana zai fada min komai insha Allahu.
Na jima a zaune falon kafin in mikewa zuwa daki don lokacin sallah da yayi nan na samu halimatu a kwance tana kallo nake fadin ba zaki tashi kije kiyi sallah ba.
Ina shiga ban daki nake wanan maganan na tura ban dakin na shiga koda na fito halimatu bata dakin a lokacin.
Sallah na idar ina zaune a wurin ina jera addu,oi ji dawowan ta dakin don yanzu tun lokacin da sa,adatu ta samu waya take turo muna yan wakokin hausa da comedy a wayana.
Nayi fadan hakan bata daina ba shi yasa ko yaushe halimatu take lake da waya tana kallo cikin irin haka ne yau ma tana dube dube a wayan taci karo da video da wayana ya dauka na convesetion din mu da Nabil a dining.
Taso wuce shi sai kuma ta kunna tagani wani video ne kada ta wuce shi yake yadda mukayi da Nabil ne tiryan tiryan ke zuwa a cikin wayan har wucewan shi da zuwan ita halimatu din.
Ido ta fitar waje tare da mikewa kafin in shafa addu,ana in juyo gareta lokaci guda naga ta fice dakin da sauri ina mamakin hakan a raina.
Na idar na koma saman gado na kwanta da niyar inyi searching din wani abu a system dina naji an turo kofa da karfi na dago kai.
Na dago da niyar fada don nasan halimatu ce zatayi min haka sai na gansu tare da anty fadila sun shigo lokaci guda na dago da niyar yiwa halimatu din fada.
Sai dai yanayin fuskokin su ya hana inyi magana a lokacin ido kawai na tsura masu har suka karaso inda nake suka zauna.
Na dan dago ina fadin anty kin tashi ashe na shiga dazun na sameku kuna barci na barku kada in tayar daku.
Na tashi tun dazun ai zainab ta kalli halimatu tana fadin danje falo ki jiramu ko dakin mu sadiya.
Ba musu tace tau anty fadin haka yasa na san da magana a bakin ta lokacin na gyara zama ina saurarenta wayana ta miko min tana fadin zainab yaushe wanan abin ya faru haka ?
Wani abu anty na karbi wayan ina tunanen abinda ya faru din tace min hakan ki kunna ki ga abinda nake nufi a wayan ki.
Da sauri na kunna wayan don ganin abinda take magana a kai har gabana yana faduwa don bansan abinda take magana kanshi ba.
Tun zuwan shi ta bayana da harara da sanda kada inji motsin shi har irin abinda ya wakana a tsakanin mu dashi gaba daya wayata tayi recording.
Dago kaina nayi a sanyayye tare da fadin na rasa mai nayi wa wa yan nan mutanen suka tseni ganina tare da yaya nina me yasa wanan mutumin ya tsaneni kamar yadda wanan bakin fatan taju shima ya tsaneni hakan yake nuna min yanzu.
Wani kallo fadila tayi min tare da fadin kishi sukeyi dake mana ai sune yanzu kamar kishiyoyin ki gareshi ke har ma sunfi kishiya macev illa ai.
Saboda me anty nida banda power a gurin yaya da zansa a wani abu ya faru da aikin su don me zasu tsaneni hakan nan don Allah.
Ke nan ke har yanzu baki fahinci me sukeyi da mijin ki yake zama dasu ba haka ai dole su tsaneki tunda sun fiki sanin dadin shi ai.
Nace sun fini kan anty tunda suna tare dashi kowani lokaci suna kuma aikin suna samun a karkashin shi ko yaushe yasa suke ganin kamar zan tare masu wani abin.
Wani irin kallon takaici da tsuki tayi daga inda take zaune ta mike tsaye tana fadin a sannu zaki fahinci abinda yasa suke tsanarki din.
Harta fara takawa take fadin wanan video na wayan ki shedane a gareki zan turashi a wayana don wanan ba abin wasa bane idan ya gane kinyi recording din komai a wayan ki.
Ko anty na tambaya da dan tsoro a idona ina kallon ta nake fadin kina ganin zai iya min abinda ya fada din anty ?.
Tunda ya fada ai zai iya kishiyar kine fa shi don kamar a karkashin shi kuke dukan ku kinga ko komai zai iya maki ai kan yayan naki.
Har kwana biyu ina da tsoro da fargaba kan maganan na samu anty fadila ranan da zancen take fadin abinne da wuyan sha,ani zainab.
Idan baka iya kama barawo ba ance sai ya kama ka kinga wanan maganan sai nake ganin kawai ki barshi har wani lokaci .
Don akwai ranan magana sai dai kiyi hankali dashi kada kibada wani kafan da zai samu ya cutawa rayuwan ki ko kadan.
Nayi shiru ina nazari don na kasa fahintar laifin da nayi suke tsanana haka kawai sai na share zancen a raina.
Ban yarda wani dalili mai karfi ya hadamu hanya daya dashi ko wani abu kuma yana gidan zaune tare damu yana kuma abinda yaga dama a gidan fiyema da kowa.
Don haka zai ta dakawa masu aiki tsawa yana basu umurni har jikin su yana rawa idan ya buga masu tsawa da karfi kan dan kuskure kadan.
Ranan yaya ya fita waje a nan ya samu halimatu a zaune waje tana shan iska zama yayi da ita suna hira saiga Nabil din ya fito yana zuwa ya dan dafa kafadan jafar kamar yana sum batar sa.
A cikin kalaman hausa halimatu ke fadin wallahi yaya na tsani wanan mutumin tunda yace sai ya halaka yayan mu.
Ke sadiya akan me zai halakata kuma meye rusan sa da ita da zai halakata kodai kawai tsanarsa ne yasa kikai masa sheri ?
Wallahi yayan ba karya nakeyi ba shi ya fadi hakan idan baka yarda ba ka duba wayan yayan video din nan a ciki idan bata goge shi ba.
Hankalin shi ya tashi sosai lokaci guda yaji wani irin tsoro ya kamashi dajin hakan a bakin halimatu ga kuma shedan data fada na hakan.
Zubur ya mike ya barta a wurin zaune tabishi da kallo kafin ta mayar da kanta ga abinda takeyi kafin yazo wurinta ya zauna.
Ina kwance dakina na kunna kira,a a wayana ina karatu hankalina ya dauku sosai ga karatun naji an turo kofan dakin lokaci guda.
Ban damu nasan kowaye ba don a zatona ko halimatu ne ta shigo dakin don haka take min duk lokacin da taga dama a dakin.
Saidai hancina ne ya sheda min wanda ya shigo din a lokacin nayi saurin dago kai don in gaskanta shidin ne ya shigo min dakin nake jin kamshin sa.
Lokacin har ya kawo bakin sofan da nake kwance ya mika hannu ya dauki wayana dake gefena ya shiga duban abinda yake nema din cikin wayan.
Shiru nayi ina sauraren abinda zai fada game da wayan dake hannun shi can naji ya kunna video muryan warning din da Nabil yai min min ne ranan yake tashi.
Da wayan a hannun shi ba tare dayai min maganan komai ba ya juya ya fita daga dakin mikewa nayi nabi bayan shi.
Na zata part din shi zai nufa sai naga ya nufi hanyar fita daga gidan kai tsaye ban tsaya ba ina biye a bayan shi naja na tsaya da naga ya nufi guiden.
Halimatu na zaune ya wuceta ina mamakin hakan kai tsaye sai can inda Nabil yake saman kujera ya zaune ga cup din giyan daga gefen shi.
Wellcome dear ya fada yana wani shu,umin murmushi a fuskan shi yana zuwa ya dauke shi da wani irin wawan mari a fuskan shi sai da jini ya fito mai a hanci lokaci guda.
Yayi kasa tangal tangal zai fadi ya kara kai mai wani naushi tare da fadin dan iska sister nawa kakewa barazanan kashewa ashe ?.
Jackson me nayi maka kake dukana haka akan abinda ban sani ba, make faruwa laifin me nayi ma kuma, wani marin da shaka ya kara mai lokaci guda.
Take baki da hancinsa suka fara fitar da jini lokaci guda saida ya dan dade a duke kafin ya dago har lokacin da mamaki a fuskan shi.
Shikuma yana tsaye a cikin matsanacin fushi yana kokarin kara mai naushi a fuskan shi.
Karan da halimatu ta sake yasa ya shi dan jin wani iri yayi saurin juyawa da sauri ya bar wurin a cikin bacin rai.