Part din shi ya nufa yana huci yana cicika ya bugo kofan da karfi ya shige ciki baiko san dani a wurin kofan falon ba.
Abu Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 32 min read
Da sauri na nufi waje don jin karan halimatu danayi daga gefen garden din muka hade da ita zata shigo ciki a tsorace.
Hannunta na rike muka shiga ciki direct sai part din su anty fadila na gyaran dakin muka shiga yadda muka shigo a firgice yasa ta gane akwai wani abinda ke faruwa lokacin.
Take tambayan mu ya na ganku haka a tsorace wani abune ya faru saidai na zauna na kalli kofa nake fadin .
Wallahi anty ina daki kwance ya jafar ya shigo ya dauki wayana baimun magana ba ya duba abinda zai duba ya fita nabi bayan shi sai na hangoshi yana dukan wanan mutumin dakw zaune a gidan nan.
Meya hadasu haka ta fada hankali a tashe kafin tace yanzu mijin naki yana ina zainab ?
Yana part din shi na bata amsa a takaice babban magana ta fada akwai rikici sosai a gidan nan ashe ?
Waima ya hakan ya faru ne wai har yakai su ga hakan don nidai tunane shine wanan video din abinda ya faru tsakanin ku ne ya kawo wanan rikicin haka.
Yaya zai san da wanan video tunda ban fada mai komai a kai har yanzu wata kila dai wani abin na daban ne ya faru.
Zainab duk yadda akayi ya samu labarin wanan video din a wani wuri sai kuma ta juya inda halimatu take tana fadin sadiya kin fada mai wanan maganan ko ?
A yadda yanayin ta ya nuna kawai zai tabbatarwa mutum amsan abinda ake tambayanta da din.
Kafin tace a sanyayye ban fada mai ba na dai ce dashi bana son wanan mutumin yace saboda me ?
Nake fada mai abinda yaiwa yayan mu yake fadin bai yar, , , ki muna shiru waya aike ki fada mai wanan zancen sadiya ?
Tayi wani wiki wiki da ido na fada maki ba komai ne sadiya zata sani ba daya shafi mijin ki a yanzu.
Halimatu meyasa kika faye surutu haka waya aikeki fada mai wanan zancen barta ai idan surutu ta iya ai sai an dafa wanan bakin mai yawan surutun tsiya fadila ta fada a dan hasale.
ZAINAB IDRIS MAKAWALITTAFIN KUDINE YAR UWA KADA KI DAUKARWA KANYI NAUYI KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA.
BA TARE DA DAUKAN NAUYIN KOWA A KANKI BA DON ALLAH, , ,
Bayan anty fadila ta karewa halimatu fada taja mata kunne sosai tare da tsoratar da ita illan yawan surutu a gaban kowa haka.
Ban kara jin duriyan shi ba har dare muma dari dari muka koma a gidan don abinda ya faru ranan don hankalin mu ya tashi ga baki daya a gidan .
Can cikin dare ne sosai ina barci nake jin hayaniyar su sama sama har na kai ga mikewa tsaye don firgitan da nayi saboda a tsorace na kwanta dama.
Takawa nayi zuwa kofa har na bude zuwa inda nake jin sautin na tashi sosai na hayaniya a gidan.
Muryan ya Jafar naji yana fadi a cikin fada duk son da zan ma ba zai taba kai wanda nakewa yan uwana ba .
Tun farko ban yarda ka shiga rayuwa naba saida na fada ma muhunmancin yaran nan a gurina ka yarda amma yau kaine da samun daman warning din ta akaina waya baka wanan matsayin na taba min family na .
Me kake tunanen kaika a gidan nan idan baka sani ba yau ka sani yarinyar nan she is my everything in dis world mu ba haka traditional din mu yake ba dole ne namiji ya zauna da mace ko yayane kuwa.
Muryan Nabil din naji kadan kadan da alama yasha wahala sosai a wurinyana fadin kayi hakkuri son kane ya rufe min ido har nake jin ban son ganin ta a gidan nan.
Amma hakan ba zai sake faruwa ba insha Alllahu nayi ma alkawarin hakan kayi hakkuri kada ka koreni don Allah ya fada a dan marairaice.
Kamar ma kuka yake yana magana motdin da naji a bayana ya sa tsoro ya kamani har na tashi kurma ihu sai ji nayi an rufe min baki da hannun maishi.
An jani zuwa part dina fadilace ashe itama hayaniyar nasu ya tayar da ita ta fito saida muka shiga dakin take fadin .
Ke baki tsoro su fito su sameki a wurin kijawa kanki wani laifi wanan ai ba abin saurarara bane ga mutum don abin babu dadin ji wallahi.
Anty a cikin barci naji hayaniyar tasu shiyasa na fito kada fa yaya ya illata abokin nan nasa nake gudu a kaina na karasa a dan maraice.
Ya nakasa shi mana ina ruwan ki ke wanan su ta shafa ki koma ki kwanta kuma kiyi kamar bakiji komai ba don kadama ki soma yi mai wanan zancen kashe gari.
Tana fadin haka ta fice dakin nabi bayan ta na rufo kofan da sauri na koma bakin gado na zauna ina tunanen irin kalaman da naji suna fada.
Karshe dai mikewa nayi daga wurin na nufi ban daki na dauro alwala na fito na fara sallah har tsawon wani lokaci kafin barci ya saceni a gurin danayi sallah barci ya daukeni nan.
Wanan ya jawo min makara gashi a ranan zamu koma makaranta hutun mu ya kare late na fita daga gidan sukuku dani jiki ba karfi.
Duk zirga zirgan da nayi a school wanan zancen bai fita a zuciyana ba sai faman kulawa nake ina warwala a cikin zuciyana.
Sai yamma lis na dawo gidan a gajiye don ba abinda nake bukata a lokacin sai wanka da bukatan hutu bako zancen cin abinci a raina.
Gashi kuma magariba ya gabato a lokacin don haka na fada bayi nayi wanka dana fitone na zauna wurin mirrow ina gyaran jikina sai naji an turo kofan dakin nawa.
Dan waigawa nayi kadan halimatu ne ta shigo tana fadin yayan mu ashe kin dawo tun dazun nake duban dawowan ki ai.
Eh na fada ba tare dana dago kai na kalleta ba a inda take tsaye taci gaba da fadin yau kin dade sosai yayan mu.
Eh na fada ina rufe man dana shafa tare da fadin kin san yau dole mu dade ai tunda yau muka koma school din.
Tace yaya Jafar ma ya dawo naga ya murda kofan ki yaji a rufe ya sake fita amma bai tambaye ki ba ya fice.
Don kamar ma ranshi a bace yake muna gaidashi da kyar ya amsa muna gaisuwan ya fita abinsa bai tsaya kulamu ba.
Mikewa nayi a wurin ina fadin halimatu kin faye surutu wallahi ba anty ta fada maki ba komai ne zaki fada ba wai.
Tace ta fada min na wuce ta kai tsaye zuwa wurin kayana ina dubawa ta sake fadin yayan kin sani wanan shegen Nabil din yau ya tafi naga ya dauki jakarshi da yamman nan ya bar gidan nan.
Wani irin juyowa nayi na harareta kafin in juya naci gaba da neman rigan da zan saka a jikina ba tare da yi mata magana ba.
Saidai can kasan zuciyana na cike da zargin maganan data fada min ke nan yaya ya koreshi saboda wanan case din namu dashi ke nan.
Riga na saka kafin na tayar da sallah magariba tare da umartan ta ita ma taje tayi sallah yanzu zata fice na kirata na nuna mata kofan bandaki koda ban fadaba ta gane me nake nufi da hakan don haka ta shige simi sim ba tare da wani magana ba.
Anan tayi sallah mun idar muna zaune kowa na addua anty fadila ta turo kofan ta shigo tana fadin wai ashe tana nan ?
Dama wanan yar rigiman ce ban gani ba nake neman ta don ban san kin dawo gidan ba ma sannu da dawowa ta fada tana kallona.
Sannu anty na fada ina shafa addu,a a jikina tare da fadin yau zirga,zirga yai min yawa a gajiye na dawo gidan nan don driver ya dade shima yana jiran na fito.
Karatu ko ina sai an daure kafin dadin shi yazowa mutum sai kiga wata rana sai labari insha Allah.
Zo muje ki ci abinci ta fada tana kallon halimatu dake zaune a gefena a wurin da mukai sallah din.
Idan nayi isha,i zan taso yanzu ta fada tana kallona nima ban tankata ba jin abinda ta fada lokacin.
Halimatu ta fara mikewa ta fice ni kuma na tsaya nade kayan danayi sallah don bana barin su a wurin idan nayi sallah.
Na nufi kofa ke nan ya shigo dakin ba tare da yai magana ba yake miko min wayana dake hannun shi kaina dago ina karba nake kuma gaidashi lokaci guda.
Ya amsa min a yanayin yana a cikin damuwa har lokacin nake fadin a cikin karfin hali yaya yau ko lafiya kake naga yanayin ka a haka ?
Tambayan nawa yazo mai a bazata don ba wani dogon zance mukeyi a tsakanin mu ba dama ya dan buda baki da kyar yana fadin .
Kawai na gajine daga wurin aiki nake yanzu ina son in watsa ruwane Allah ya taimaka na basa amsa dashi ina bin bayan shi bayan ya juya zai fita.
Kusan lokaci daya muka fito daga dakin nawa ina binshi a baya baisan dani ba saida muka kawo kofan part din shi.
Mamaki a fuskan shi yake kallo na ya dan kauce na shiga ban tsaya ba na nufi bedroom din shi direct ban dakin na nufa na hada mai ruwan zafi.
Na fito daga bandakin naga dakin a hargitse ko
ina dan dakin yana bukatan gyara a lokacin don haka na zage na fara gyara yana tsaye da waya a hannun shi yana magana a wayan dakin na shiga gyara a hankali kamar yadda yanayina yake nake aikina.
Ya gama ya cire kayan shi ba tare da damuwa da ina dakin ba a lokacin ya shiga ban dakin har na karasa gyaran dakin na fita bai fito ba.
Gashi ina aikin ina tunanen irin yadda yaya yake durawa cikin shi ruwan barasa don irin kwalaben dana gani a dakin bazakace shiya durawa cikin shi giyan ba haka.
Nikan da mamaki na bar dakin idona yana kokarin zubar da hawaye lokaci guda dan tausayin halin da yake ciki kuma gashi a matsayin mijina yake zama gareni da wanan halin.
Na gyara dakin ne dan kawai abinda naji yana fadawa Nabil a dare jiya game da matsayina gareshi daya fada.
Gashi yanzu nima ina jin a raina na na fara son kasancewa da mijina tunda dai a zaman mijina dai yake gashi idan yayi wani shiga ya fito kokai waye sai ka kalleshi ka kyasa mai dan kyau da kamala da baiwa irin na kyau da Allah yai mai ga zati da kamala a fuskan shi .
Ban nufi dakina ba falo na sauka wurin su fadila na samu sun ci abincin na zauna take tambayana bazakici abincin bane ?
A koshe nake na bata amsa da hakan ina kaiwa kwance don aikin dana danyi yanzu jikina ya saba da hutu dan bana aikin komai.
Shiyasa da na danyi aiki kadan jikina zai yi ciwo don rashin sabawa da hakan da banyi ba a yanzu.
Gashi a kullun wani irin kyau da kwarjini nake karawa sai wani haske da annuri da nake karayi ko yaushe.
Makerin budurcina a lokacin yagama fitar min da duk wani sura da akeso daga jikin diya mace su baiyana na cikan budurci sun fito min fili.
Ni kaina nasan a yanzu nakai lokacin shiga tsarana idan ana kwatance a fagen kyau da kira na ya mace.
Kawai ba zato ba tsamani aka shigo gidan kai tsaye ba sallama ba komai sai ganin katan maza mukayi su uku a kanmu sai wani binmu da kallo sukeyi kamar mazurai.
Gashi dan rigan dana saka a jikina na shan iska mai dan hannun shimi ne a jikina sai tsagan dake kasan rigan daga gefe daya.
Irin dai rigunan matan su na zuwa wani taro na muhinmin din nan shine lokacin saye a jikina wani purple dashi haka mai laushi.
Mun razana da ganin su haka yasa ni mikewa tsaye da sauri sai bin jikina sukeyi da kallo irin na yan iskan turawa din nan.
Who are you people ?
Na fada a razane a cikin bacin rai sai dayan yace dani we are jackson Friends .
Na kallesu a yatsune ina fadin wanan gidan Muslim ne bamu da jackson a gidan nan na basu amsa a cikin gatse.
Muryan ya Jafar ne ke saukowa daga sama yake fadin kai ku koma dakin ku yanzu ina da baki a gidan.
Juyawa nayi na kallo inda yake fuskan shi a daure tamau kamar bai taba dariya ba a rayuwan shi.
Jin abinda ya fada yasa na mayar da fuskana inda suke su duka na bisu da dan harara kafin ma inyi magana har fadila ta fara takawa don barin wurin duk a tsorace take a lokacin da ganin bakin nasa.
Dakin sa muka shiga basu ba har yaya din bin mu yayi da kallo saidai shi din kallon don me muka tsaya dasu muna magana haka.
Kafin ya juyo don yace dasu su zauna sai ya samu sun mutu a tsaye suna kallon mu ya fara magana a daidai lokacin suke sauke numfashi tare da fadin.
Waaawooo wanan ai ba kowa ne zai sameta ya kyaleta ba sai dai kai jakckson da baka son harka da mata sai maza kawai da ka hada both da zaka more a wurin wanan yarinyar gaskiya.
Wani irin mugun kallo ya watsa masu yana kaiwa zaune tare da jawo remote din tv dake aiki da muka bari a wurin yana aiki.
Ya juyo ya kallo su lokaci sun kai zaune daga tsayen da suke suna shakiyanci a tsakanin su fuska daure ya kallesu yana fadin meya kawosu wurin shi.
A cikin dariya dayan dayafi zama shakiyi a cikin su yake fadin ai da ganin mu gidan ka kasan maganan daya kawo mu tunda kaki daukan wayan mu tun dazun.
Don me zakaiwa sabon guy din ka haka jackson kana son ka zama mai kamawa da sakewane ko yaushe.
Gaka da sa,an samun gayu irin da kowa ke son ya samu amma sai ka dinga sakacida wanan daman naka.
Kodai yanzu ka fara canza ra,ayine ka fara sharing din both side samun wanan zukekiyar yarinyar a gidan ka ?
Don ba kowa zai zauna da wanan bai morewa rayuwan shi ni,imar dake jikin ta ba na mata koda kuwa baya jin dadin hakan a zuciyar shi.
Stop it philis,
She is my wife you can't talk haka a kanta kamar yadda kaima kasan ba zan taba fadin wani zancen banza ga family din ka ba ya fada yana mikewa tsaye.
Suma din mikewa sukayi don sun san shi sarai zai iya ficewa ya barsu wajen hakan ba karamin aikin shi bane wanan.
Da sauri dayan ke fadin haba man kada kai fushi damu mana mun san ba,a kyauta da hakan don kowan mu nan baya wasa da sister shi ko wata yar uwansa.
Jin hakan yasa ya koma ya zauna yana huci tare da kallon su daya bayan daya kafin ya sauke ajiyan zuciya.
Ya hade hannayen shi wuri daya yana sauraren abinda zasu fada dayan dayake abokin shi na sosai yace man dazun wanan sabon guy din naka ya samemu da wani zance .
Mun kira wayan ka yafi a kirga kaki ka daga yasa mukazo har gidan nan don mu baka hakkuri kan abinda yai maka don bai boye muna komai daya faru ba a tsakanin shi da sister din ka.
Wani irin kallo ya dago kai da idanun shi da sukai masa ja ya jefesu dashi kafin yace masu ku barshi kawai bana son kowa a kusa dani a yanzu.
Kada kace hakan jackson kasan baza mu iya daina wana harkan ba a yanzu don haka kayi hakkuri da wanan guy din don rashin sa gareka babban hasarane a wurin ka.
Don akwai masu son su kasance dashi na mika kudi masu yawa aka bakashi don haka kada kayi sakacin dazai kubce maka.
Let him go ya fada da karfi tare da mikewa tsaye kallon juna sukayi suma suna mikewa suna kallon shi .
Kada kaiwa kanka sakaci da wanan guy din don kowa sonshi yake a garin nan ya juyo ya kallesu yasa kai ya fice daga gidan.
Basu fita ba saida biyun suka juyo suka kalli dakin dana shiga kafin subi bayan shi shida abokin shi da sauri dama sun fi shakuwa a tsakanin su.
Ban yarda na fito dakin ba sai da zan kwanta na dauki drink da snack na shige dakina dashi sai bayan na gama abinda nakeyi nasha na kwanta.
Washe gari nayi samakon fita school acan ma na bata lokaci sai yamma na dawo gidan.
Bayan sati da yin hakan monday na shiga school a dan makare tun daga nesa nake jin hayaniya na tashi department di mu na hanzarta na shiga.
Abin mamaki na tarasa a wurin wai ana taya wasu ma,aurata murnan aure a tsakanin su .
Dan murmushi nayi na gefen fuska na ratsa mutane ina neman wurin zama daga can baya na samu wuri na zauna a wuri daya.
Wata na samu irin yan ra,ayin rikau din nan na addinin buda su na kasan jin hayaniyar yai yawa yasa na dan juya wurin ta duk daba wani shiri mukeyi a tsakanin mu ba ina tambayan ta ina ango da amarya don ni duk maza nagani a wurin gaba dayan su babu amaren.
Saida ta tabe baki take fadin wai a tsakanin sune sukai auren ai ga ango nan da bakin kaya amaryan kuma da fararen kaya a jikin ta.
Na dan gyara zama tare da kallon ta da kyau ina fadin kai shirme ke nan ina aka taba aure tsakanin namiji da namiji kuma in ba shirme ba ?
Sunayi ta fada tana runtse idanuwan ta a daidai lokacin da ake bi ana raba alawa bayan dogon adduan samun zaman lafiya da akai masu a tsakanin su.
Malami ya shigo aka fara lectures ni dai zaune nake tunane ranan nayi kala kala a raina kafin a fito don yin break.
Wanan matar mai addinin buda na sama take kara wayar min dakai game da auren jinsi da akeyi yanzu a tsakanin maza da maza ko mata da mata.
Driver na kira ya mayar dani gida don yau banjin za a karasa lectures din dani don irin rudanin da zuciyana ya shiga tun bayan bayanin da naji daga wanan matar.
Gidan na shigo suku suku dani gaisawa kawao nayi da fadila na wuce zuwa dakina jiki ba kwari .
Don gaba daya zuciyana da kwakwalwana sun fara kawo min wami zargi akan ya jafar din.
Sai nake tariyo wasu abubuwa can kasan zuciyana wanda nake ganin zargine kawai nakeyi alokacin ba gaskiya zuciyar nawa ke fada min.
ZAINAB IDRIS MAKAWALITTAFIN NAN NA KUDINE KIWA ALLAH KI BIYA KAFIN KI KARANTA DON FITA HAKKIN JUNA BA TARE DA SHIGA HAKKIN JUNA BA.
Washegari na kasa tashi don zazzabin daya rufeni lokaci guda saboda tunane daya tsaya akan lalai akwau ayan tambaya akan ya Jafar da wa yan nan mazan dake zaraya a dakin shi.
Ba tare da wani shamaki ko tsoro ba wanda koni matar shi banda halin yin abinda sukeyi a gidan kai tsaye sai tare da umurnin shi.
Wanan dogon tunanen ne yasa na fashe da kuka lokaci guda ba tare dana sanda zuwan shiba a lokacin.
Har yakai zazzabi ya sauka min hakana dunkule ni daya a daki ina rawan dari gashi na kasa tashi in kashe AC dake aiki a dakin.
Washegarin ma da kyat na iya tashi nayi sallah na koma na nade saman gado har saida halimatu ta shirya zata tafi ta shigo sallamana ta sameni a hakan.
Taje ta fadawa fadila suka dawo tare dakin tare da ita da kyat na tashi nasha tea din data hado min a lokacin.
Da kyat na samu na kurba sau biyu na koma na kwanta ban dade da kwanciya ba wani irin amai yazo min lokaci guda.
Da gudu na mike zuwa bandaki saidai kafin nakai bandakin har na sake aman ko sai da kyat na karasa ciki.
Hankalin fadila ya tashi sosai don halimatu ta rigada ta wuce kada ta makara bus ya wuce yasa aka turata ta tafi ba don taso tafiyan ba a lokacin.
Fadilace ta gyara dakin har ban dakin ta saka kamshi tare da bude dakin don iska ya shigo haka yasa shi sanin cewa ina gidan ban fita ba.
Don ya fito a cikin shirin shi yana sauri har ya zauda kofan part din nawa sai kuma ya dawo baya da mamakin ganin kofan nawa a bude .
Hakan ya sanar dashi ban fita zuwa school ba ranan ke nan ya shigo cikin dakin tun daga nisa ya hangoni saman gado a kwance ina rawan dari.
Lokacin fadila ta fita zuwa dakin ta don ta dauko min magani da tazo dashi irin namu na Nigeria da muke sha a can gida.
Zainab ya fada a dan rude yaji ban tankashi ba yasa yakai hannu ya kware bargon da nake rufe dashi ya kai hannun shi a hankali kamar mai tsorona yana taba jikina daya gama gashewa lokaci guda da zafi radau.
What ya fada a razane a cikin dan rudewa tare da fadin baki da lafiya kike kwance haka zainab baki fadi an kaiki asibiti ba ?
Nan ma ba amsa sai kara lefewa da nayi don kware bargon dayayi yasa na kara jin sanyi na shigana lokaci guda.
Fadila ce ta shigo da saurin ta dakin dauke da magani cikin karamin plate sai goran ruwa da cup a hannun ta daya.
Tana ganin shi ta kadu da sauri zata juya ta bar dakin sai ya dago kai yana fadin meye wanan kika dauko ?
Paracetamol ne da maganin amai na dauko zan bata tasha don jikinta da yai zafi ko zai taimaka mata ya sauka.
No kada ki bata barta na kaita asibiti yanzu zaifi waina yaya akayine ina gida baku fada min bata da lafiya har haka ba sosai.
Sir nima yanzune Sadiya ke fada min tazo sallaman ta zata tafi ta sameta kwance haka a dakin zazzabi ya rufeta.
Mayar da kanshi inda nake yayi ya dan tsura min ido kadan kafin yace dani tashi ki shiya muje asibiti yanzu.
Kamar banji me yake fada ba don duk da halin ciwon da nake ciki hakan bai hanani jin wani irin takaicin shi tare da tsanarshi ba a kasan zuciyana.
Kara maimaita maganan shi yayi da fadin tashi ki taimaka mata ta shirya ina waje ina jiran ku.
Da karfi na dago a hasale ina fadin wallahi ba zan tafi ba na kwanmace na mutu a hakan da ka kaini asibiti.
Mene yace da mamaki yana kallon yadda nake magana da kyat a cikin karfin hali na koma na kwanta ina kaduwa saboda sanyin da nakeji a lokacin.
Ke wani irin sakarci ne wanan kije asibiti zaki tsaya kinawa mutane gardama haka ?
Ba za a tafin ba na kara fada a yadda nake kwance ina kaduwa da kyar kake jin magana na idan inayi.
Wai meke damuwantane ya juya yana tambayan fadila ta girgiza kai tare da fadin nima haka na ganta yau sir ban san meke damunta ba.
Juyawa yayi ya fita dakin fadila ta matso kaina tana fadin tashi kisha wanan din mu gani ko zai taimaka maki kafin ku tafi.
Sai lokacin nayi magana ina fadin bazan tafi ba wallahi anty na tsani yaya jafar bana son ganin shi don, , , .
Wani irin yun kurin amaine yazo min lokaci guda ya hanani karasa zancen danake son fada a lokacin.
Da kyar na mike na shiga ban daki wanan karon yellow din amai nake alaman dai fever mai karfi ya kama jikina lokaci guda ko.
Da kyar da bin bango na samu na fito daga ban dakin na koma na samu wuri na kwanta ina mayar da nunfashi da kyar tare da lumshe idona ina jin wani irin takaicin kasan zuciyana.
Ba barci ne ya daukeni ba amma haka na lafe kamar mai barci a lokacin don yadda nake jin kaina na saramin lokaci guda.
Haka dai nake kwance tana tsaye a kaina cikin damuwa sai can kamar bayan awa guda naji ya sake shigowa dakin.
Wanan karon tare da wani likita suke shida kanshi ya hau gadon ya dagoni na bude idanuna da sukai ja don bacin rai ga ciwo na sauke a kasan zuciyana.
Likitan ne ke fadin meya sameki pretty girl tare da juyawa ya tambaye shi is she your sister ?
Yace dashi yes yace yaushe na fara ciwo haka yace da dare kamar yasan hakan sai likitan ya ciro kayan aikin shi ya shiga aunani na dan lokaci guda tare da yi min tambayoyi ina bashi amsa da kyar.
Allura yai min da magani nasha sai barci na dauki lokaci mai tsawo ina barci kafin in tashi ina neman abinda zanci ga zufa yana fetso min a jikina.
Tea nasha sai naji dan karfin jikina na tashi nayi sallah azahar kasa tashi nayi sai kuka don tunanen abinda ya tsaya min a rai.
Fadila ce ta turo kofa ta samu ina kuka ni kadai a cikin dakin da sauri ta karaso inda nake tana fadin zainab lafiya wai meke faruwa ne dake haka ?
Alama ya nuna akwai wani abinda ke damun ki a zuciyar ki kike boyewa kai na dago a hankali na kalleta tare da fadin.
Ba komai anty fadila na fada ina mayar da kaina wasu hawaye masu zafi suna fito min ido kawai ta tsura min kafin ta sauke ajiyan zuciya ta juya ta fita.
Bata dade ba ta dawo dauke da abinci ba tare da tayi magana ba ta aje a gaba kafin ta samu wuri takai zaune kasa a kusa dani.
Zainab kome ke damun ki don Allah ki daure kici abinci kada wani ciwo kuma ya shige ki a yanzu don nasan tun jiya baki ci komai a cikin ki ba.
Kai na dago da niyar yin magana sai ta dakatar dani da hannu tana fadin don Allah ki daure zainab kome meye da baya mayi zancen a tsanake dake.
Jin haka yasa na kai hannu a hankali na jawo abincin na fara ci a hankali badon yai min dadi a baki ba duk da itace ta dafa don irin abincin mune na gani.
Na dan tsakura na mayar na rufe tare da daukan ruwa na kurba sai can na sauke ajiyan zuciya ina fadin na tsani yaya jafar anty fadila.
Subbahanallahi zainab meye maki haka da har zaki tsaneshi irin haka lokaci guda.
Ban iya magana ba illa fadawa jikin ta danayi ina sheshekan kuka har nayi nagaji na kyale don kaina tayi shitu tana kallona kawai tare da nazarina.
Ki daure ki tashi a kasan nan kada sayin kasan ya kamaki ki koma saman gado ta fada tare da mikewa tana dauke kayan abincin dana ci.
Mikewa nayi kamar yadda ta ban shawara na koma saman gado na kwanta a haka wani barcin ya daukeni don barcine a idona saboda rashin samun barcin dare da banyi ba.
Wasa wasa kwana biyu nayi a kwance ina jinya idan ya shigo dibani bana yarda ko in kalli inda yake haka kuma yayi maganan shi ya gaji bana tankshi haka zai fita daga dakin.
Akarshe dai koya fahinci wani abune baya shigowa sai idan ya dawo daga wurin aiki zai lekoni ya yai min sannu a tsatsaye ya fice.
Har naji sauki na fara fita school kamar yadda na saba saidai duk wanda yasan ni yasan na rame sosai a lokacin.
Don nasawa raina tsanan komai na yaya a gidan ko abinci banda yadda zaiyi ne da ba zanci abincin gidan shi ba yadda nakeji tsanarshi a raina.
Ashe wanan matar yar gargajiyan kasan kwana biyu da banzo ba ta damu da rashin ganina kuma bata san wani da nake hurda dashi ba a school din balle ta tambayeshi ni.
Bayan mun fito daga lectures ne muna break ta sameni zaune ta gaidani itama ta samu wuri ta zauna tana tambayana dalilin rashin ganina kwana biyu da batatyi ba.
Nake fada mata tun ranan nan da muka rabu banda lafiya ina gida kwance yasa ban shigo ba tayi min sannu da jiki na amsa da godiya.
Muna nan wurin zaune don na fahinci itama irinane bata son hayaniya itace ta dauko hiran lectures din da akayi bana nan har ta ban handout din ta na kofa don karatu tare dayi min bayani.
Saidai taga hankallon ya dauke ga kallon wasu mutum biyu da suka wuce mu suna rugume da juna yasa ta kura min ido na dan lokaci tana nazarina.
Dafani naji tayi na waigo da sauri take fadin lalai ni bakuwace a wanan kasan wanan ai yanzu ba komai bane a nan don yanzu basa ko boyon wanan abin.
Gashi kuma babu wani addinin daya yarda da wanan dabi,an na auren jinsi suna dai yine don ko wani addini suna da tarihin mutanen farko da aka halaka kan wanan dabi,an.
Dan murmushin yake nayi tare da fadin ni abin ya daure min kaine ai tun ranan da tayi min wanan bayanin ina mamakin yadda mutum zai auri dan uwan shi namiji haka ?
Me mutum zai gane ga hakan nan dai ta shiga bani musalan abubuwa da dama wanda ban sani ba da ace tasan halin da nake ciki da ta bar duk wani bayanin da take min a lokacin don yadda zuciyana yake tafasa.
Dala dala tayi min bayanin su a gurguje tare da irun alamoninsu da yadda sukan fara approching din mutum har su ja ra,ayin shi ga abin.
Haka na koma gida bayan mun rabu a cikin wani sabon tashin hankali har yakai na kasa rike abin a zuciyana.
A weekend din na samu anty fadila da zancen a dakin su ina kuka nake mata bayani ban boye mata ba nace na fara zargin ko yaya Jafar shima wanan akidan yakeyi da yake yawan mu,amula da maza yan uwan shi a daki daya.
Kai haba zainab yaya zaki saurin zargin mijin ki da wanan dabi,an marakyau haka har ma idan kina zargin sane ai zaki iya saka ido ki fahinci wasu halaiya nasa harki gano hakan .
Amma baki yankewa kanki hukuncin da baki sheda ba irin hakan da sauri don kinga yanzu kece dakin fada mutane zasuyi saurin yarda da maganan ki.
Wanan zancen da mukayi yasa na tsiro gyaran dakin yaya da kaina a wanan lokacin duk naci karo da wani abinda ba daidai ba a dakin zan kwashe in zubar dashi .
Haka kuma giyan shi har yakai yanzu ya boye abinsa a inda ban sani ba sai ga wautana na dauka ya barsha ne a yanzu.
Sai ranan ko yaya akayi ya shigo dashi dakin ban sani ba na gasu a falo ya aje su a cikin leda washegari na shiga gyara na gansu na kwashe duk na farfasa su.
Wanan abinda nayine ya kawo muna matsala a tsakanin mu karo na farko a zamana dashi don ina zaune a daki da dare ina karatu ya shigo min dakin kamar mahaukacin zaki yana fadin.
Ke ina abinda kika daukan min a dakina suke kamar ba zan dago kainba saida ya kara tambayane.
Na dago kai na dan kalleshi nace wani abune ke nan nidai nasan abin haramun na gani a dakin na dauke na zubar.
Ke kada ki kawo min maganan banza a nan tun kan a haifeki na haddace alkurni balle ke yanzu kizo min da wani maganan banzaki can .
Indai gyaran ke nan da kike min daga yau sai yau idan bani na bukaci da ki shiga min part dina ba.
Ba tare dajin komai ba a raina don duk wani tsoron shi ko nauyi ya kawo a zuciyana nasa don haka na kalleshi ido da ido nace yafi min nono fari yaya don dama don Allah nake maka.
Idan badon Allah me zai kaini gyaran dakin da Allah kasa na fushi da mai shi don abin haramun din da ake aikatawa a ciki.
Har ya juya ya waigo da wani irin karfi tare da fadin me kike nufi da wanan zancen naki kina nufin dakin nawa haramun ne ko me ?
Ba dakin ba yaya kai kanka haramun ne don shi kake aikatawa ga shan giya ga babban abin da Allah ya haramta da kakeyi a dakin.
A cikin wani irin tafiya ya fara takowa zuwa inda nake zaune ina karatun daya sameni a dakin banji tsoron shi ba ko kadan ban kuma motsa ba daga yadda nake zaune.
Hannun shi ya mika kamar zai cafkeni ban san abinda ya tuna ba kuma ya fasa tare da dan kafeni da ido na dan wani lokaci.
Nace idan kayiwa kowa wayau yaya kana ganin zakaiwa Allah ne yau gashi har nayi wayau gane abinda kake boyewa mutane na halin ka.
Ka tuba ka koma ga Allah tum kan lokaci ya kure maka zaifi na yarda ni yarinyace ban san komai don ka yaudareni ka yaudari iyayyena.
Amma yanzu idan na zauna da kai da wanan halin naka nina jawa kaina idan wani abu ya sameni.
Don haka yaya na rokeka ka mayar damu gurin iyayyen mu don Allah tun kan masifan ka ya kai ga shafan mu.
Gara in zauna a cikin talaucin gidan mu da in zauna a cikin wanan sabon Allah tare dakai nayi ma alkawarin in dai nice babu mai jin wanan zancen a bakina har duniya ta tashi.
Na fadi hakan don kawai ya kyalemu mu koma Nigeria don yakai yanzu tsoron lamari shi nakeyi ga baki daya.
Wani irin kallo yai min ga idanun shi sun kara rinewa lokaci guda ga baki daya halittanshi ma ya sauya lokaci guda .
Naga ya juya ya fice yabar dakin da sauri wani irin kuka na fashe dashi lokaci guda ina mulmula saman gado kamar mai iska.
Tunda wanan abin ya faru tsakanin mu ban kara sashi a idanuna ba har tsawon sati biyu gashi nasawa kaina damuwa da tsoro duk nabi na lalace lokaci guda.
Ashe tafiya yayi bamu sani ba don bani kadai ce na shiga damuwan rashin ganin sa ba kowa ma a gidan ya damu da hakan.
Ranan sai gashi kwaran ya dawo ana shigo da kayan sa gidan muna zaune a falo suke mashi sannu da zuwa da kyat na iya budan bakina na gaidashi.
Ya amsa shima a dakile ya shige part din shi kai tsaye sai daga baya aka shiga mai da kayan shi part din shi.
Har kwana biyu da dawowan shi babu wani sakewa a tare dashi nima ban bi ta kansa ba do yanzu banda damuwa a gida ga anty fadila tare damu.
Can kuma school ga kawata da yanzu muka saba da ita sosai muna kula junan mu sosai da ita kamar mun dade da sabawa .
Idan ma ina da damuwa bai wuce son komawa gida Nigeria dana sawa kaina a yanzu don hankali ga baki daya ya koma gida.
Yakai kamar sati daya da dawowa sai gashi dakina da yamma ya shigo ina zaune ina waya da Amaya kawata ya shigo.
Wuri ya samu ya zauna ganin haka nima na natsu ga sauraren shi do jin abinda zai fada a lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWAALLAH YAI MUNA DAUKI YA KAWO KARSHEN WANAN TASHIN HANKALIN DAYA ADDABI AREWA DAMA SAURAN KASASHEN MUSULMI NA DUNIYA ALLAHUMA AMIN 👏🏻👏🏻👏🏻
DON ALLAH YAN UWA KUYI HAKKURI KU KAI ZUCIYA NISA KAN SHIGA HAKKIN WANI KI DAURE KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALLAMA ALLAH YASA MUFI KARFIN ZUCIYAR MU AMIN, , , , , ,
Juyuwa nayi na kalleshi a hankali yana zaune kamar mai tunane ya harde hannayen shi a guri daya kanshi na kasa sade.
Banji tausayin shi ba sam ko kadan a raina saboda yadda nakejin shi a raina illa shirun da nima nayi na dan lokaci ina sauren shi.
Gyaran murya kafin ya fara magana murya ciki ciki naji ya furta kalman sunana da zaina....b .
Ban dago kai na kalleshi ba saidai yadda na natsu yasan ina sauraren shi a lokacin maganane kawai banyi ba lokacin .
Magana nake son muyi dake a tsanake dan wanan zancen na ranan ya daure min kai a ranan saboda ban fahinci abinda zancen ki ke nufi ba.
Don naji kina kokarin kafirtani yasa na fice na bar dakin nan ko kuwa kina tsamanin don har yau ban dubeki a matsayin mace ba kike dauka wani abu nakeyi na daban.
Da farko naji tsoro da kunya don jin abinda ya fada sai dai a cikin karfin hali nace yanzu fa yaya na wuce daukan da kake min na yar kauye kuma diyan talakawa.
Wani kallo yai min don jin abinda na fada hawaye na zuba min a idanuwana shar shar naci gaba da fadin kaji tsoron Allah yaya .
Kada mutuwa ya riskeka acikin sabon Allah kai musulmine kuma musulunci ya haifeka gaba da baya yaya.
Kasan irin hukuncin da Allah ya tanadarwa wannan abin saboda wanan ubangiji ya kifar da mutanen wani zamani mai tsawo kana sane da ukuban kabari ga bawa mai sabawa fadan Allah.
Yaya bayan wanan yau idan mahaifiyar ka ko wani yaji wanan ko daga kasan ka na haihuwa aji abin ashan da kakeyi a nan yaya da wani ido zaka kallesu.
Wani dauka kake son duniya tayiwa duk ahalin ka saboda kai yau idan Allah ya baka zuria nan gaba a duniya yaya duniya zata daukesu yaya ?
Kasa cigaba da maganan nayi dan sheshekan kukan dazo min bazan iya furta komai a bakina ba ga lokacin.
Shiru yayi yana sauraren sautin kukan nawa yana dan girgiza kai a hankali tare da dan buga hannayen shi cikin juna.
Bai hanani kukana ba shima din a lokacin na zuciya yake yi don ya gama fahinta na ganeshi baro barone kawai ban fito fili na fada mai hakan ba.
Lalai mutum abin tsorone tunda har wanan abar da nake rainawa ta san yadda zata fahinci komai game dani .
Duk taka tsantsan din da nakeyi wai ace yau yarinyar nan sai data gano hakan ina ga mami idan har labarin nan yaje mata sai yaya ke nan.
Idanuwan shi ya runtse a hankali yana jin wani abu yana tokaro mashi kan zuciyarshi lokaci guda.
Cikin muryan kukan naci gaba da fadin ina rokon ka katai maka muna ka mayar damu gida wurin iyayyen mu don Allah.
Koda kuwa ta hanyan wani mumunan kazafine ko sheri zaka lakaka min ta hanyar da duniya ni zasu tsaneni na yarda da hakan yaya matukar zaka mayar damu hannun iyayyen mu din Allah.
Nayi ma alkawari har abada ba maijin wanan zancen daga bakina don ba abin alheri bane da zan fada har wani yai ma kallo dashi a duniya.
Yau nima laifin ka yaya ya shafeni don abinda ya taba mutuncin gidan ku a duniya ya taba rayuwana nima don alherin ku gareni ba abin mantawa bane.
Nasan kayi nisa a cikin wanan akidar fitan ka a yanzu sai Allah daya halicce ka yaya zan taya ka da addu,a Allah ya rabaka da wanan halin ga baki daya dakai da sauran yan uwa musulmai da suka bace suka makance a wurin sabawa Allah da munanan aiyukan da ubangijin mu yafi tsana ga bawa.
Yaya yau idan mahaifiyar ka ta samu wanan labarin da wani ido zaka iya kallonta a yadda mami take da mutunci da kima a idon mutane.
Ya isheki zainab ya fada da karfi a cikin wani irin yanayi na bacin rai yana min kallon ido da ido daga inda yake zaune nayi kasa da kaina kawai don ba zan iya jurewa kallon shi ba ko kadan.
Zaki iya fada min komai a yanzu amma kada ki yarda ki jefa sunan mami a wanan zancen wurin nan .
Zan iya sauraren don abinda zaki fada banda wanda kike fada min game da mami din yanzu wanan tsakanina ne da mahaifiyana.
Ni mutum ne mai yancin kansa kamar kowa ina da daman da zanyi wa raina duk abinda ya dace dani a rayuwana.
Ki sani ban auro ki don ki zaunar dani kina min guntun wa,azin ki ba a nan don tun kan ki sanda hakan na sani.
Kasa daurewa nayi don jin abinda ya fada na dago da sauri ina fadin yaya ka sani kake aikata abinda Allah ya la,aci maishi.
Ina zaka da wanan nauyin mai yawa a kanka ka tuba ma Allah shi mai karban tuban bawan sa idan har bawa zai tuba tubana tsakani da Allah har abada.
Nidai ina maka adduan Allah ya taroka yasa ka gane gaskiya ka daina wanan halin kafin mutuncin ka da kimar ka ya zube a idon duniya don Allah ba zai taba boyeka ba ga abinda kakeyi yanzu.
Saurarena yake yana mamaki yadda nake fitar da lafazi kamar wata tsohuwar mace a zuciyar shi.
Ki ci gaba da min adduan tunda har kin gane abinda nakeyi din mara kyau ya fada yana mikewa amma gida ba zan mayar daku gida ba kamar yadda kika bukata.
Bayan shi nabi da kallo lokacin da yake fita dakin sai dai a yanzu ba kamar yadda ya shigo yake tafiya ba.
Don yanzu a dan hasale yake takawa ya fice daga dakin rayuwan shi da hankalin shi a tashe don bai taba zaton zan gane hakan gareshi ba da sauri.
A tunanen shi wayau na da hankalina ba zai kai har in fahinci abinda yake aikatawa ba haka da wuri.
Sai gashi a bazata na fito mai a fili dana nasan da abinda yake ciki wanda bai taba kawo hakan a ranshi ba.
Mace mace ka barta komai kankantar ta ta wuce yadda mutum yake daukatan watau don wanan yarinyar yar kauye da yake gani gidahuma har ta iya zaunar da mutum kamarsa tana jero mashi zance haka.