Part din shi ta nufa tana fadin bari in dubashi ko yana ciki har yanzu idan ba fita yayi ba.
Abu Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 28 min read
Murda kofan tayi taji kofan a bude yake haka ya bata daman shiga dakin kai tsaye tsab falon yake kamar kullun sai kamshin dake tashi a cikin sa.
Cups har biyu ta gani aje saman dan table din glass din dake gaban kujera sai fararen takardu dasu laptop a gefen kujera aje.
Kai tsaye ta nufi dakin kwanan shi ta fara kwankwasa kofan ta fara kwankwasawa sai gana ukune ya amsa da kyar ya iya yin magana ya tambaya da waye ?
Nice ta bashi amsa a gadarance ba tare da ta kara furta wani abuba a kai.
Kofan a bude yake ya fada yana kokarin cire bargon dake jikin shi rufe mami ta tura kofan ta shiga daga cikin dakin.
Ta hango shi yadda yake kwance saman gado ya dan rufe rabin jikin shi da bargon.
Lafiya kake kwance haka a rufe tun dare baka leko muba baka kuma shigo da safen nan ba mami ta fada tana karasawa bakin gadon nasa tana zama.
Sai daya dan dago daga kwancen cikin yanayin yamutsa fuskan shi yace yau bana jin dadi ne amma yanzun nake son in shiga.
Baka jin dadi shine zaka kwanta a daki kai kadai haka ba wanda ya sani kamar karamin yaro mami ta karasa fadan nata da tambayan wai meke damuwan kane.
Cikin dauriya yai magana da kyat yana dafe kirjin shi mami ina jin kirjina na ciwo da zazzabi.
Wani kallo tayi mashi kafin tace dashi ai saika tashi kaje likita ya dubaka ko ?
Mami ba sai naje asibiti ba nasha magani dazun da zan kwanta tace ka karya ne da kasha maganin ?
Baida matsala mami yanzun zan fito ya fada yana maida kanshi ga filon da ya dago akai.
Ido mami ta dan kura mai kafin tace zaka jawa kanka matsala akan wanan yarinyar har da kwanciya ciwo don kawai na fadama gaskiya.
Murmushi kawai ya danyi tare da lumshe idanun shi ba tare daya iya mata magana ba ta mike tana fadin idan ba zaka iya fitowa insa lami ta kawo ma abin karyawan ka nan ka tashi ka karya ko zakaji saukin jikin.
Sai lokacin ya iya magana yace ba sai ta kawo min ba mami zan fito da kaina ai ya sake lumshe idon shi a hankali.
Mami a cikin dakewa take da karfin hali a lokacin don gaba daya hankalinta ya tashi ga halin data samu dan nata a ciki wanda take tunanen maganan su najiyane yaja masa wanan kwanciyar haka.
Hjy na zaune falo tana dakon fitowan hjy sai gata tun kan ta karaso take tambaya kin same shi a ciki ?
Yana nan hjy wai ashe baya jin dadin jikin sane yakw kwance daki shi kadai bai fadawa kowa ba.
Subbahanallahi me ya sameshi haka har yaron nan yake kwance bamu sani a cikin gidan nan.
Ciwo yake son jawa kanshi kawai hjy don nayi masa fada jiya shine yake wanan ciwon don batacin zaijawa kanshi ciwo ya halaka kansa akan abinda baikai ya kawo ba.
Hjy bata ba mami amsa ba sai mikewan da tayi tana fadin bari na leka shi inga halinda yake ciki tabar mami na kiran lami daga falon.
Dakin shi hjy ta nufa daga kofa ta tsaya tana kwala sallama daga can ya jiyo muryanta ya yunkura da kyar ya taso zuwa falon.
Da kyat ya iso yana kokarin zama saman dogon kujeran tare da fadin hjy kin tasone yanzun nake son tashi in shiga mu gaisa dake ai.
Kai da baka da lafiya aikai ya kamata azo a duba koda yake uwarka tace kaine kajawa kanka ciwon bansan dalilin ta na fadin hakan ba.
Hankalinshi yaji ya kara tashi lokaci guda idon shi suka kada sukai jawur gashi abinda yake ji a zuciyar shi kamar ya fita a lokacin ya aikata saidai baison ya biyowa mami ta wanan hanyan da yake ganin ranta zai mugun baci a karshe.
Gashi hundred pacent ya amin a zuciyar shi da zabinshi yasan da farko ba son yarinyar yakeyi har cikin ranshi ba.
Illa tausayinta da taimakon kanshi ya zauna lafiya a rayuwan shi don itace kawai fufin asirin shi a rayuwan shi.
Zai iya samunta da sauki fiye da wace mami ke shirin aura mai yasan ko wacece indai yaran ire iren kawayen mamine dole idanun yarinyar a bude yake itama.
Sai dai kuma daga jiyan da mami ke kara ikirari akan ya janyewa yarinyar nan zeey abinda ya faru tsakanin su yasa yana jin wani irin feeling yana matukar jin yarinyar a ranshi.
Fiye da yadda bai taba tsanmanin faruwan haka ba a tsakanin su tunda yake mu,amulan shi da mata a rayuwan shi badai wani abune ke shiga tsakani su ba sai dai hugging da dan kiss a tsakanin su kawai.
Hannun shi yakai a kai yana dan shafan kanshi tare da jin wani wutan son yarinyar na kara ruwa akansa.
Tankar yadda wutan kara yake kamawa gadan gadan yana saurin yaduwa a duk lokacin daya kama a cikin jeji.
Jafari ka sassauta zuciyar ka kabi lamarin nan a sannu kamar yadda na fada ma da farko kada kajawa kanka ciwo idan har iyami bata yarda da bukatan ka a cikin lalama ai tana da magabata ko, wa yanda zaka iya gani bayan ita.
Saida ya sanye harshen shi ya lashi labbansa da suka bushe masa yana cike da takaici da kunan ran wanan lamarin da mami ta bijiro masa.
Kafin yace hjy mami bata sani ba idan har tace a yanzu ba zata yarda da zabina ba sai dai in fasa auren duk wata yarinya da take fadin zata hadani da ita a kasan nan.
Ni namiji ne fa ina da daman da zan zabawa kaina abinda nake son rayuwana dashi don ba wani ne zai zauna da ita ba saini.
Ta bangarena ranan dai naje school ne amma babu abindana iya tsinta a cikin abinda akai muna don tune biyu daya tsaya min a rai.
Na farko shine mami yadda take min din nan abin ya fara tsoratani sosai duk a kan danta take nuna min wanan kyamar dana kasa gane dalilin ta nayin hakan gareni idan nayi dubaiya ga yadda muke da, da ita.
Amma sanadiyar bullowan wanan maganan gaba daya mami ta sauya min ga sabon halin disgani ko agaban waye data dauko yi min yanzu wanda hakan ya fara taba min zuciya duk da ina yarinya.
Sai nabiyu abinda ya jafar yai min a jiyan ya tsoratani matuka gaba daya ya dasa min tsoron shi a zuciyana.
Haka muka dawo gida ina a cikin damu tun daga ranan na daina fitowa falo idan ina gidan har ma in na fito sai idan zan shiga kitchen dauko abinci ko wurin su mama kande mudan taba hira.
Gashi tun ranan ban kara saka yaya a idona ba saidai nasan yana gidan ba tafiya yayi ba don ina ganin security din shi da safe idan zamu tafi makaranta.
Ta hakan na gane yana gidan bamu dai haduwane dashi ko kuma mami ta shawo kanshine ya yarda zabinta gareshi.
Yanzu ya gane niba ajin sa bace ya wuce ajina ga aure saidai diyan manya irin su can irin wanda mami keson ya aure har hakan ya jawo matsaloli a tsakanin mu.
Na fito ina tafiya kamar yadda na saba zakace ko ina tsoron kasa ne yadda nake takona, ga uniform din jikina sun karbeni sosai.
Kamar ance in daga kai in kalle saitin dakin ya jafar daga inda nake tsaye jikin mota ina jiran fitowan yaran yaya mamud mu kama hanya.
Caraf idona ya hadu da nasa daga inda yake tsaye jikin aindon shi yana sanye da bathrobe a jikin shi ya bude gaban rigar yadda zaka iya hango six pack din shi na kiran maza a waje.
Yana rike da cup din farin glass a hannun shi idanun shi a kaina da sauri na juya na bashi baya daga kallon shi da gujewa nashi ganin kuma.
Kai ya girgiza cikin dan murmushi yana mai jin dadin yanayin danayi din don shi abin nawa ma dariya yake basa ko yaushe a yadda nake nuna tsoro idan na ganshi.
Yasan bayin kaina bane hakan mami ce ta riga da ta dasa min tsoronta a raina akan shi don hakan dole inyi hakan don tserar da mutuncina a furin mami din.
Har muka shiga mota yana tsaye a gurin yana dan kurban abinda yake sha a hankali a cikin cup din.
Sai da motar mu ta daga na sauke wani irin nauyayyan ajiyan zuciya a fili tare da lumshe idona a hankali ina mai jin wani iri a raina.
Haka shima ya jafar din bai daga, daga wurin ba saida yaga motar tamu ta bace ga ganin shi ya sauke wani irin ajiyan zuciya lokaci guda tare da juyawa yabar wurin da sauri.
Mami na zaune dakin ta tana shiryawa adaidai lokacin yayi sallama ya shigo dakin direct inda take ya nufa ya danyi hugging din ta.
Tare da fadin morning mami kanshi ta shafa tare da fadin dan albarka ka tashi lafiya lafiya kalau mami ya fada ya koma bakin gadon ya dan kidinshida tare da daga kafan shi daya yana duban wayan shi.
Friend wai gaba daya ka sauya dabi,un ka yanzu har abincin dare ka daina zama dani muci ka kuma san wanan time din ne kawai nake dashi danake dan kebewa daku.
Tunda ba fitowa kake da safe ba kafin in wuce wurin aiki balle in ganka shiru yayi bai bata amsa ba sai ta dauka hankalin shi yaga wayan hannun shine hakan yasa ta juyo tana kallon shi.
Saidai ganin sabanin hakan garshi lokacin data juyo din yana kallon wani wurin na daban tare da yanayin tunane a fuskan shi.
Friend wai me yake damun kane haka ina magana ka lula wani duniyan tunane me kake tunane hakane wanan kwailar yarinyar zeey ka saka a zuciyar ka ko ?
Kan shi ya dago a hankali ya dubi mami tare da fadin babu komai mami me kika gani halan.
Kai ta girgiza tare da juyowa gareshi gaba daya tana fadin babu yadda za ayi kace babu komai duk mutum mai hankali da zarar ya dubeka yasan kana cikin yanayi na damuwa.
Amma dai tunda ba zaka fada kuma ni nasan zancen yarinyar nan ne har yanzu ka saka a ranka kamar yar wani da wata.
Kai yanzu kana ganin kafanka ya kama kasa ban isa kai min abinda nake so kayi a matsayina na mahaifiyar ka balle har kace ba zaka fada min abinda ke tsoce ka ba sai dan dogon wuya kake ajewa kanka.
Mami na fada maki bani tare da wata matsala kirjinane kawai har yanzu bana jin dadin sa zancen zeey kuma aini na fita wanan zancen yanzu, don shirin komawama nakeyi tunda an fasa zancen auren kince bakyayi da zabina sai a fasa auren a yanzu sai na laluba wata kuma.
Mikewa mami tayi tana fadin kaima kasan hakan ai ba zai yuyu ba ka koma ba tare da aje iyali ba .
To mami ki bari in auri zabina don shine rufin asirin daki dani daku ga baki daya ba ko wace mace bane zabin namiji ko wani namiji da kalar macen da yake so a rayuwan shi.
Haka kace ke nan ni bansan abinda zuciyar ka keso ba ke nan na zaba maka nawa ra,yin ko to tashi ka ban wuri .
Ga mamakin mami sai taga ya mike don barin dakin kamar yadda ta umurceshi ya bari din.
Har ya fice daga dakin mami tana binshi da kallon mamaki da tsoron abindaya fada yanzu a gabanta wanda ta kasa gane me hakan da yaron nn ke fadi yake nufi ne ?
Ya dan jima tare da hjy a falo suna fira inda yake fada mata zai koma bakin aikin shi bada dadewan nan ba.
Hjy ta dago kai tana fadin har tafiyan ya karaso ke nan yaya zancen auren naka don idan ka koma a yanzu wayasan ran dawowan ka wanan kasar jafari ?
Hjy zan dawo a daidai lokacin daya dace sai dai wanan sirine tsakanina dake ki kula min da yarinyar nan yadda ya dace zan dan barta ta kara wayau da sanin kanta.
Yanzu zan nunawa mami ni yarinyar bata gaba sai daidai da lokacin daya dace in dawo gareku da wanan zancen zan dawo da nuna mata gaskiyata.
Ban fahinci maganar kaba jafari tsohuwar ta fada yacs zaki fahinta hjy don koma a bayane zaizo maku hjy.
Mikewa tsaye yayi yana kallon agogon hannun shi tare da fadin zai soma tafiya a rude tsohuwar ke fadin don Allah dan son manzon tsira ka saurareni kada ka je ka dan dakata mu kara fuskantar iyami na dan lokaci.
Shu,umin murmushi shi kawai ya sakar ma tsohuwar ba tare da ya tsaya ya furta wani abuba akai yai mata Allah bamu wuni lafiya yasa kai ya fita daga gidan.
Ashe hjy ta samu mami ta yi mata tas akan ya jafar tare da lurar da ita halinda take son jefa danta a ciki takare da fadin idan kin kashe shi ko kika bari ya tafi yabar kasan nan kan wani dalili naki can baku fuskanci juna ba kanki zaki tarawa bakin ciki.
Shi auren gatan da kike fada bashi bane kukaiwa mamud yanzu ki fada min dadin da kukaji a cikin wanan hadin na mamuda din.
Ke kanki ba dadin yarinyar nan kike ji ba ina gani sai taga dama take shigowa nan koshi sai da wani dalili mai kwari shi mamudan basai ya fada ba da ganin sa kasan a tauye yake da ita duk dai saboda ku a gidan nan.
Iyami da zaki gane abinda nake nufi a nan da sai ince ki kyale yaron nan ya auri zabinsa tunda dai hakan ba haramun bane.
In kin hanashi auren wacce kika san halinta ai zai kwaso maki fitsarariya da zata zo ta wargaza maki gidan ki.
Kindai ji ikirarin da yaron nan keyi a gaban ki ko yaushe da yarinyar nan itace daidai dashi kinsan abinda hakan ke nufi a zuciyar shi ke baki kwantawa ki auna me hakan da yake fada ko yaushene yake nufi.
Maza fa ba ayi masu dole ba kamar mata suke ba su ki barshi da zabin sa abinda yagani da idon sa yace yana so.
Ai gara wanan din ma daya zaba kinsanta kinsan ta kinsan halinta ciki da bai kina yi tankwasa ta aduk yadda kike son ta ba kamar wanan ta wurin mamudan ba.
Sannan har idan itama yarinyar nan ta kamu da son yaron fa kinga kin zalunce su tunda itama a karkashin ki take.
Har in kina gudun tayar da alkawari ne ga iyayyen wacan da kika nema masa ki barsu dashi shida kanshi zai nuna masu halinshi ita din ba zabinsa bane amma ina amfanin ayi abu adawo ana danasani akansa haka.
Iyami ki rabu da dan yau idan ya furta baison abu to ki kyaleshi yai wanda yake so matukar ba abinda zai sabawa mahaliccin shi bane abin.
Gaba daya jikin mami yayi sanyi lokaci guda hankalinta da natsuwa suka zo mat lokaci guda ta bude baki tace hjy ni kaina kalamin yaron nan yana sakani a duhu ko yaushe idan na zauna nayi tunane mai kalman nan da yake yawan fada min haka yake nufine gareni .
To kin gani ABU A CIKIN DUHU SIRINE shi yasan me hakan ke nufi ya kuma barwa kanshi sirin abin a zuciyar shi maza ba kamar mu mata suke ba yaron nan shi yasan me yagani gun yarinyat nan ya dahe mata har baijin kwabon ki a yanzu.
Hjy zan ga iyayyen yarinyar mu zanta zancen dasu in Allah ya yarda hjy tace ba sai na shiga zancen ba ke nan yanzu.
Hjy basai kin kara magana ba in Allah ya yarda zan zauna da yan uwana muyi duba dakyau ki barmu da kaina zan gyara kurakurena zan shirya komai.
Hjy tace koke fa Iyami Allah yayi maki albarka ya daukaka maki zurian ki ya kare ku daga sherin makiya da mahassada.
Naji dadi kwarai da kika fahinci mai nake nufi kafin wani abinda ba a so yazo ya faru kan maganan nan yanzu.
Duniya yanzu idan zaka biyewa mutanen cikin ta ba zaka taba aikata daidai ba a rayuwan ka sai a baka gurguwan shawara idan ta kwabe adawo ana zunden ka a baya.
Sai yarinyar nan ya zama dole yanzu ki gyara mu,amulan ku da ita tunda kin riga da kin bata komai a tsakanin ku don dai yarinyar ma mai hakkurice da sanin yakamata.
Ba kowa bane za a nunawa hakan ya iya shanyeshi a zuciyar shi ki gyara tsakanin ku kada yazo ta rike abin a ranta ki nuna mata mu ba butulai bane kuskure aka samu a baya hakan ya faru.
Nayi mamaki sanin kankine aurene fa yarin ga yace yana so da yar nan taki don yarinyar ta zama yarki halal malal sanan aure sunnan ma,akin Allah ne.
Bai kamata kiyi shishigi da nuna iko a cikin lamarin aure ba hakan nan kizo ki mutu akuma yi wanan auren idan da rabo a tsakanin su azo ana fadan da baki mutu ba ba za,ayi wanan auren ba.
Idan ma baki mutum ba ayi ba acikin yardan ki ba kikuma gansu a tare da babu yadda zakiyi da hukuncin ubangijin ki a kansu.
Wani hawayen bakin cikine ya zubu a idon mami lokaci guda tace wallahi nima hjy na rasa me yasa bana son wanan auren ko nayi niyar barin shi yayi abinsa.
Don zeey har ga Allah abin asone a gida dubaga irin hakkurin yarinyar da sanin yakamatan ta kamar ba karamar yarinya ba da ita.
Gata abin tausayi to hjy na rigada nayiwa hjy saude alkawari akan yar ta duba da yadda muka dade da ita muna amintaka yau ace naki hadin da take so a tsakanin mu.
Hjy tace ai itama ta haifa tana dasu ba zataki abinda danta zaiso ba har in son gaskiya take maki bazata taba ganin laifin ki kan zancen nan ba.
Tunda ba kece maiyin auren ba wanda zaiyi yace yarta batai mashi ba sai dai tayi hakkuri yanzu kan.
Tana fadan haka ta mike tana fadin ni zanje inyi alwala inyi nafila lokaci na kure min.
Nan tabar mami zaune da dinbin tunane a ranta na yadda zata bullowa wanan al,amarin da yaronta ya bijiro mata dashi a yanzu.
Don ko ita dadin tane ta sani nan gaba don samun yarinyar garesu ba karamin alheri ba wurin jafar sai dai kawai ace babu good backgraund gareta ne na iyayyen da suka isa gare ta shine kawai abin duba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
3️⃣0️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAR UWA BARKA DA WARHAKA SHI KO KINSAN LITTAFIN NAN NA KUDINE DON ALLAH DON KAUNAN ANNABI IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KASADAN KARANTA SHI DON KINSAN BAKI BAN HAKKINA BA UBANGIJI ALLAH YASA TUNANEN KI NA ALHERI YA RINJAYI SHEDANI DAKE TARE DAKE KODA YAUSHE ALLAHUMA AMIN ALLAH 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA 08036959257 ALLAH YA BADA IKON BIYA ALLAHUMA AMIN, , , , , ,
Tiryan tiryan hjy ke mayar mai da yadda sukayi da mami zaune yake kawai yana sauraren hjy din ba tare da yai magana idon shi na kan wayan hannun shi.
Sai idan ta fadi wani abin tambaya ta dago kao tayi magana ya danyi murmushi kawai ta gefen fuska.
Bai bari ta gama fadin labarin duka ba ya mike yana fadin hjy zan dan fita akwai ida nake son zuwa kafin rana yayi sosai don gobe kaduna zamu akwai abinda nake sonyi a can.
Kace gobe gida kayi ke nan ni likitan bai gama dubana ba ai da nabika mun tafi tare zaman garin nan wuri daya ya fara isata yanzu.
Wa zai tafi dake ya fada yana kallon fuskanta tace bandai tashi ba yaro idan na tashi ai dole kaje dani.
Hannun rigan shi yake gyarawa tare da fadin wa ni in jera dake ki zama min matsala sai wurin fita jirgi kice min naki san hakan ba.
Dakuwa tayi mai da hannu tana fadin wani munafukin ne ya fada ma dama yaran nan biyu akwai bakin gulma ko kuma Indo ce don dai takwarana ba zata taba fadin wanan labarin ba.
Kinyi ke nan ya fada yana fita daga dakin tace miskilin banza nagama ma yaki a wurin uwarka, yanzu ka dawo zakai min sheri kuma.
Yana fita ya daga wayan shi dake ringing da security din shi yai magana na minti daya bai karasa fitowa ba har sun kawo mai mota bakin kofan shiga gidan.
Ya fito kamar mai kare rana fatar jikin shi yayi sumul dashi kamar jikin larabawa don farin shi na daban ne .
Bai tsaya jiran komai ba ya fada mota suka rufe a hankalin motar tafita daga tangamemen get din gidan mami din a hankali ya lumshe idanun shi yana tuna kalaman hjy data gama rabtabo mashi yanzu.
Wani shu,umin dariya ya sauke yasan waye mami don mahaifiyarshi ce ya kuma san halinta don ita hjy sanin da can baya tana karama taiwa mami din.
Lalai da akwai wani plan da mami ke kullawa tayiwa hjy wanan dadin bakin har yar tsohuwar tayi saurin yarda da maganan ta.
Gyara zaman shi yayi yana gyara lumshe idanuwan shi tare da fadin mami sai dai kiyi hakkuri dani don tun ranan dana fara dora idona kan yarinyar nan tausayinta ya rikede ya zama soyayya a zuciyar danki.
Shi kanshi yasan akwai kyawan mata dasukafi wanan yarinyar da idan yau yace a aura mai aure dasu zai yuyu.
Sai dai shikan ubangiji ya dagwara mai tausayin ta da sonta a yanzu don bai taba fadawa tarkon son wata mace ba irin wanan yar abin da mami ke rainawa.
Shiya idan mami na korafinta a kaina bai iya furta komai a yanzu don son da yakewa yarinyar baki ba zai iya furta shi ba har abin yakan bashi mamaki.
A wani babban shago motar ta tsaya ya dan dade kafin ya fito motae ya shiga shagon biyu daga cikin security din shi na bayan shi duk inda ya bi sai binshi ake da kallo.
Sayayya yayi sosai a shagon saga turare sabulun wanka manshafi da sauran kayan gyaran jikin mata ya biya suka fito daga shagon daga nan ya shiga wani shago na sayar da redmed nan ma ya duba ya zabo ya fito.
Bai dawo gida ba don ya wuce kallon ball sai bayan sallah isha,i ya shigo gidan ga security din shi har biyu da kaya niki niki a bayan shi suna biye dashi.
Daga mami Aisha da hjy duk suna falon sai ya jalal suna zaune a dining suna cin abinci suma.
Welcome ya J suke fada yana amsawa a cikin basar ya nufi kujera ya zauna security din suka shiga gaida mami da hjy.
Suna tsaye saitin inda yake zaune a bayan kujeran tsaye da ledojin da suka shigo dashi a hannun su.
Ya kalli Aisha yana fadin a cikin turanci karbi kayan nan ki shigawa yarinyar nan dasu dakin su.
Ba Aisha ba har mami saida ta dago kai a cikin mamaki tana kallon shi, shiko fuska a daure ya kara bata umurni yana fadin ki karbi kayan nan ki kaiwa zainab daki nace.
Ta mike simi simi don bata hango sassauci a fuskan shi ba lokacin idan taki tasan kwanan wasan a wurin shi.
Meye a cikin mami ta tambaya a hasale ba wani abu bane ya fada yana mayar da kanshi saman kujera tare da fadin john kuna iya tafiya yanzu and make sure by six kun fito don bakwai jirgin mu zai tashi zuwa kaduna.
Aisha dawo da kayan nan, nan mugani mami na fada maki ba wani abu bane a ciki perfume ne da kayan body odor da kikace tana wari na saya mata .
Ido waje mami ke kallon shi waje don jin abunda ya fada don ita har ta manta da tayi wanan maganan a cikin fada ashe shi yana rike da zancen a ranshi.
Wari kuma wake wari a gidan nan hjy ta tambaya a cikin mamaki saida ya mike tsaye bayan ya tabatar da shigan Aisha dakin namu yake fadin.
Tare da duban hjy har lokacin fuska a daure yace wai yarinyar nan zainab shine na sayo mata kayan kamshi.
Jafar zaka fice min a ido tun kan na feto ka ko sai kayi min rashin kunya a nan na fada bata warin ne ko wani oud take shafawa daba za aji warinta ba.
Ok fine mami shine ai na saya mata yanzu don ta dinga kamshi kamar kowa ya dan juyo ya kalli hjy yana fadin ya kike hope ba wani matsala dai ko ?
Ba matsala dan duniya hjy ta fada tana dariyan draman shi da mami din don ita abin ma dariya ya bata kuma.
Mami kan binshi tayi da kallon mamaki har ya bacewa gani ta ta juyo da kallonta wurin hjyn ta .
Iyami na fada maki kibi zancen yaron nan a sannu yanzu ina dadin wanan zancen da yaron nan ya fada koda yarinyar na wurin shi fada zaiyi abinsa namijine bai damu ba.
Hjy gaba daya yaron nan ya sauya akan yarnan don wanan ba halin shi bane musaya min magana ta.
Amma yanzu kan zeey yake kokarin saba min tun kan aje ko ina inaga ya riketa ta zama tasa ke nan.
Don nace zeey din tana da body odor shine ya nuna min shi yasan hanyar gyaranta ko ?
Wanda yaki jin bari ai bayaki gani ba dan zamani ne fa kike jayayya dashi iyami tunda baki jin zance ai yanzu sai ku zuba dashi namu ido.
A karshe idan an zugaki kin ma dan naki baki ya lalace sai ki dawo ku zauna a gidan ina shike nan dai tunda haka kike so.
Daga haka ta juya ta mayar da hankalinta gun tv dake aiki duk daba fahintar abinda ake ciki takeyi ba.
Daga hakan kowa yayi shiru a falon ba wanda ya kara magana sai Aisha data dawo tana zuburan baki take fadin gaskiya ya J ya jamin raini mami nice zankaiwa zeey sayayyan daya yo mata daki.
Ni wallahi dana sani da ban zauna falon nan ba yanzu ke enough kada ki cikamu da surutun banza a nan dan Allah mami ta fada a hasale.
Kafanta ta dauka ta dora saman dan karamin table din dake gaban ta tana karkadawa a hankali kafin ta juyo wurin zeey din tana fadin.
Jeki kira min zeey din tazo nan da kayan da kika kai mata dakin mu gani ikon Allah iyami yaushe kika zama haka.
Ashe bawa yakan canza rayuwan sa yanzu wani zubar da mutunci zai sa ki karbi kayan toshin yarinyar nan don baki data ido.
Daga yau ba zan kara saka maku baki a cikin zancen nan ba na fada tundazun karki dauka wasa nakeyi a zancen nan .
Hjy kiyi hakkuri yaran nan ne da abin bacin rai bawai karban kayab zanyi ba ai dubawa kawai zanyi idan babu na assha a cikin sa.
Barwa yar nan kayan ta a hannun ta koma meye a ciki ina kinfi karfin shi a yanzu hakan kamar zubar da kimar kine a idon ta ai.
Koda Aisha tazo daki ina zaune ina assgment na baje saman gado hakalina ya dauku ga abinda nakeyi.
Naji shigowan mutum dakin haka yasa na dago da sauri don jin karan ledan dake motsi a hannun ta don nasan ba hjy bace wanan mai karfine ya shigo.
Anty Aisha na fada ina niyar gayar da ita take fadin ke dan raini nine zan kawo maki kaya kallonta nake da mamaki don jin abinda take fada daga kofa ta dangwara min kayan tana fadin you will pay for this.
Kiyi hakkuri Anty na fada tare da fadin ba kayana bane don a zatona bata tayi dasu.
Ke dan Allah ja can ya J yace a kawo maki wai kazama kawai ta fada tana juyawa don barin dakin.
In kalli inda kayan suke aje a kasa in kalli bayan anty Aisha dake fita daga dakin ina mamakin kalaminta a fili.
Ni zainab na fada na tare da sake biron dake hannuna na kurawa ledan kayan idanu kamar mai nazari.
Da kyar na iya furta na shiga uku ni zainab me wanan bawan Allah yakeso danine a duniyan nan koso yake sai rayuwana ya salwantane ?
Shiru nayi cikin dakin na kasa cigaba da assigment din da nakeyi sai tunane da nakeyi barkatai a dakin.
Nasan sai tara hjy zata bar falon mikewa nayi na dauki kayan na nufi dakin mami dasu a hannuna bata dakin yasa na aje nafito ba tare dana bude ledan don ganin abinda ke ciki ba.
Gaba na faduwa na fito sai muka hade da mami saidana kadu don tsoron mami da nakeji yanzu a raina .
Gaida ita nayi ta amsa min da kyat na zata zatayi min magana me na tafi nema a dakin nata sai naga ta wuce ta shiga dakin.
Hjy na hango a falo na nufi wurin ta don tsoron zama dakin ma nake ni kadai don ban san abinda mami zata fada idan taga kayan dana kai mata dakin.
Yauwa yar albarka kin zo a lokacin daya dace yanzun nake shirin tashi yau sun watse sun barmu ki kama min kofin nan zuwa daki na amsa da to hjy na dauki kofin da sauri muka jera zuwa dakin.
Ina tsaye saidata zauna na aje mata kofi a gefenta na nufi bandaki don a tsure nake lokacin ina sauraren kiran mami a lokacin duk cikin tsoro nake don bansan abinda zata fadamin ba kan kayan da bansan dalilin su ba.
Na fito na dauke littafina dana bari saman gadon na koma sama kujera na zauna hjy na dan dube dube a cikin aljihu bujen yadi dake jikinta.
Don ko yaushe a cikin kidayan kudi take kamar wani na taba maga gashi idan ina kusa nice mai lissafa mata su kullun.
Duk da babu abinda take saye da kudin ta a gidan komai takeso saidai mami ta sayo mata ko daya daga cikin yaran mami din.
Yauma lissafin muka fara don anyi baki sun bawa hjy kudi da bana nan shi take son mu lissafa da ita.
Mamine ta tsaya daga kofa tana kwala min kira ke zeey na amsa da sauri ina fadin na,am mami tare da mikewa lokaci guda.
Nasamu tako daki ko duk saurin danayi na amsa kiran don naso kada mu kauce a gaban hjy lokacin.
Ina shiga ta zauna a bakin gadon ta kafunta a harde mami gani na fada bayan na shiga dakin da sallamana.
Wanan kayan fa da kika kawo min nan tana nuna kayan take tambayana ba tare data dago kai ta kalli inda nake ba.
Shiru nayi saidata sake fadin kayan nan fa me sukeyi a nan tafada a cikin dan tsawa.
Mami nima yanzu anty Aisha ta shigo dashi dakin mu wai ya J ne ya ce ta kawo nan .
Zeey ta fada tana dago kai ni sa,arki ce ita Aisha data kawo maki bata fada maki naki bane dauke min kayan nan a na tun kan ranki yabaci.
Da sauri na duka na dauki kayan ina kiciniya da ledojin saboda nauyin ledan su yi yawa sosai bazan iya dauka ba .
Hakana ja su zuwa dakin mu na ajesu da kyat ina nishi hjy dake zaune har lokacin tana lissafi ta dago tana kallona tare da fadin.
Ina kayan nan suka fito kuma a cikin mamaki take tambayana na aje a gabanta na koma na zauna tare da tin tagumi don fargaban abinda zaije ya dawo gareni kan kayan nan yadda naga mami ta dau zafi a lokacin.
Yaushe aka kai kayan nan can ko can dakin Indo takai maki don bakin ciki yaron nan fa ya yo maki toshi dazun a gabab kowa ya bada kayan a kawo maki nan dakin.
Hjy don Allah kice ya daina min hakan kada mami tayi min fadan haka sai ta dauko koni ke rokon su abu.
Ina roko anan takwara kayan nan fa keya sayowa su don kansa kuma a gaban uwar taku ya bayar a kawo maki ai.
Maza tashi ki bude muga abinda ya sayo a cikin ledan mai nacin tsiya shine ai daidai da uwar taku .
Kamar ba zan tashi ba ta kara fadi na mike badon nasoba na fara fitar da kayan ledan da man shafa suke su turare da kayan shafe shafen jiki dana wankin kai wasu ban san su ba.
Ja,iri hjy ta fada so yake yakai uwar taku kul idan tace katobara ta iya a gaban yara dayan na jawo na fara budewa dogayen rugana ne masu kyau da daukan ido.
Sai kamahin sabontaka suke duk wanda na daga ko anty Aisha ban taba gani da irin su ba dukda ko irin su take sakawa.
Dayan ledan kuma karami ina dagashi saida nakai zaune don photon waya danagani a jikin kwalin haka ya tabbatar min da cewa wayane a cikin kwalin ko ledan shi ba a cire ba saidai andan yaga gefe da alama a dan budeshine an duba.
Komawa nayi na kai zaune tare da kurawa kayan ido ina tunane kala kala a raina karshe dai tasa na tattara kayan zuwa drower kayana naje.
Har hjy taga ba anta ban samu bakin magana ba don tsoron da fargaban ganin ran mami yana a bace sai na dauka akan yaya jafar din take cikin yanayin dana sameta din.
Washe gari ana public holiday don haka kowa na gida bamu fita zuwa school ba ina idar da sallah na koma na kwanta saman gado don hjy tana zaune a gurin sallah har lokacin.
Muryan shine a kofan yana sallama ta amsa mai daga inda take zaune din saiya shigo daga cikin dakin .
Kafito ke nan hjy ta fada a daidai lokacin daya karasa shigowa dakin idon shi na akaina yadda nake kwamce nayi tub da ciki saman gadon.
Wanan barci takeyi ne ya fada daidai yana zama saman kujeran dakin inda nakan kwana wani lokaci.
Yanzu dai ta idar da sallah ta kara kwanci kafin gari ya waye tafi aikinta.
Wai hjy aikin nan ba a neman wata ta dinga yinsane a barta haka da aikin nan don Allah.
Fadawa uwarku nima na dade ina shawaran hakan a raina duba ga irin sakkon da takeyi na zuwa makaranta tunda safe.
Amma hjy yakamata iyanzu ace ta daina hakana kuna, , , , , ina kwana yaya na fada a daidai lokacin dana dan mike zaune saman gadon.
Lafiya ya fada tare da kawar da kanshi daga kallona ko ya fahinci fita nake sonyi daga dakin ne oho ?
Zauna abinki yanzun fita zanyi ni hjy nazo sallama dama ana jirana a waje ya fada.
Dan satan kallon shi nayi yayi wanka fes yana saye cikin suit baka ga farar riganshi ta ciki ta dan fito waje don aninaiyan su a bude yabarshi.
Zan tafi hjy sai na dawo ya fada tare da mikewa zuwa inda take zaune ya aje mata kudi a gabanta ta shiga jero mai adduan kariya a gareshi kwando kwando.
Har yakai kofa nace da sauri nagode yaya naga sako jiya Allah ya karawa dukiya albarka.
Kisa wayan a caji ya fada daga haka yasa kai ya tafi hjy da har lokacin sai albarka take zuka mai tace tashi ki saka wayan caji yadda yace.
Hjy mami batace min komai akan kayan ba kuma ni naga kamar ranta a bace yake dani .
Yaushe zaki tsaya jiran cewar ta ki saka waya a caji kada kija hasara kuma kudi daine ya riga ya kashesu sai dai tayi hakkuri.
KADUNA
Gidab ya nufa kai tsaye saida yadda ya samu gidane ransa bai masa dadi ba sai sha biyu yake da meeting din dayazo yi anan kaduna.
Yadda ya samu falon kamar ba mutane a gidan musanman ma mata ko ina ga kayanan ajiye sun baza.