← Book details A Gidanmu Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 12

Sashe 9

A Gidanmu Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari ranar jumma'a ranar da za'a ɗaura Auren Abdul Muhammad da Bintu Umar, shirye shirye ake na musamman, kawayen mommy sunzo daga wani gari 'yan wanka ne kuma hajiyoyi ne.
Bintu kuwa tasa leshi jaa me kyau tayi makeup kamar asace agudu, Beebah ma ba'a barta ba wajen kyau, kawayensu ma sunyi kyau sosai. Kawayen mommy suma leshi suka ɗinka garin mata dashi, idan kashiga gidan saika raina kanka.

2:30pm cif aka ɗaura auren Bintu da Abdul akan sadaki dubu ɗari lagadan ba ajalan ba, Anyi Aure an kammala komai da mangariba abokan ango sukazo su ɗauki amaryarsu.

Tofa nan akeyinta Habeeb dayaga za'a tafi da Bintu yadinga suma kamar me farfaɗiya, har mutanen wajen suka fara mamaki, mommy ce tacewa Bintu takoma gida, Beebah ce tazama amaryan karya taje tashiga mota aka tafi da ita, bayan mutane sun watse ne mommy takira Habeeb cikin ɗakinta da Bintu ta ajiyesu, mommy ce tace Habeeb? Yace na'am tasake cewa Habeeb? Habeeb yace na'am Mommy tasake cewa Habeeb? Yace na'am, Mommy tace sau nawa nakira sunanka? Yace sau uku, mommy tace tom nataɓa kiran sunanka sau uku? Yace Aa tace inason kafaɗamin gaskiya. Meye a tsakaninka da Bintu?..

Habeeb yayi shiru sai kawai yafara kuka, mommy tace ba kuka natambayeka kayi ba, idan har nina haifeka kafaɗamin Abinda yake ranka?

Habeeb yace Mommy inasonta ne!!! Kuma Aurenta nakeso nayi!!!

Tass tass tass kakeji Bintu ce taɗago ta dallawa Habeeb mari tana huci... Bakada hankali ne yaya? Ko kafara shaye shaye ne? Ko ka sami taɓin hankaline? Ko bakasan ciki ɗaya muka fito dakai bane? Duk waɗannan tambayoyin tana yinsu ne cikin hawaye.. Yaya kai mahaukaci ne bakada hankali, sai yau na tabbatar da haka kanka ya taɓu.

Ke Bintu kece me taɓin hankali bani ba! Kece kanki yasami matsala bani ba! Ina matsayin yayanki zaki kirani mahaukaci? Kece mahaukaciya! Yana magana yana hawaye,
Kinsan iron son danake miki? Kinsan baƙin cikin danake ji idan naganki da saurayi? Kinsan yaya nake kwana acikin kwanakinnan da Auranki ya iso? Kinsan yanda nakeji kamar na kashe Abdul idan naganku tare? Duk nasan baki sani ba.

"Mommy ce ta tsaya awajen ba bakin Magana sai zazzare ido datakeyi kamar wata taɓaɓɓiya, idan wannan yana magana tajuya ta kalleshi idan wannan yanayi ta juya ta kalleshi tarasa ya zatayi da duniyarta tarasa ina zatasa kanta ayau, jitake kamar ta tara kayanta tabar gidan kafin su fara mata tambayoyi, juyawa tayi zata bar musu ɗakin taga mutum akwance kasa ba alamar numfashi! Beebah ce kwance kasa, wanda ta daɗe da dawowa ta dalilin faɗa dasukayi da Abdul bayan ankaita gidanshi ta tsigeleshi tayi gaba abinta, tana dawowa shine ta tarar da abinda yafi karfin kunnenta. Jin kalaman Habeeb yasa tafaɗi ta suma!

Mommy ta tsala ihu ta iso wajen da Beebah take kwance ƙasa!...

_✅ote comment and share pls_

✍️ *Jiddah S Mapi*
[6/23, 12:50 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Story/written by
*Jiddah S Mapi*

_Dedicated to all my fans_

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*WATTPAD*
_Jiddah S Mapi_

Page 45&46

"Mommy ce tayi kan Beebah dagudu tana ihu, ganin haka yasa Bintu tayi sauri ta ɗauko goran swan a frij tazo aka shafawa Beebah afuska, a hankali ta sauke ajiyar zuciya tana buɗe idonta tafara tambayan Habeeb, yaya me naji kana cewa? Kamar naji kace kanason Hassana kuma da Aure? Kamanta mu 'yan biyu ne da ita? Ko ka manta ciki ɗaya muka fito da ita? Allah yasa dai wasa kake, duk tabayoyin datake mishi tanayine cikin hawaye sannan ta Zubawa Habeeb ido,
Mommy tayi shiru tanayi wa Habeeb kallon tuhuma.

Da Habeeb yaga duk shi suke kallo, ciki kuwa hadda Bintu, sai kawai yafara kame kame, yajuya yafita a ɗakin.

_Ango_
Abokansa ne suke ta zagin Abu wai an raina musu hankali, yaza'ayi ranar Aure a nemi Amarya arasa, Abdul yatsaya yakasa yin komai sai gyara gari yake tin ɗazu da goge zufa,
Yakira numban Bintu yafi sau 20 ba'a ɗaga ba! Azuciyarshi yace kodai yaudarana dama takeda niyan yi?

Ahmad ne yadafa kafaɗan Habeeb yace "kadaina tunani dude" insha Allah gobe Zamuje gidansu Amaryar tafaɗa mana meyake faruwa, domin kasan lamarin Aure yanzu, kowa yana kokarin yaga an ɓata,
Abdul ne yace "Haba Ahmad kana gani fa yarinyannan tadinga wulaƙanta ni a idon duniya, Aure wasane? Hakafa ranan kamu ta tafi tabar wajen saida ɗayar 'yan biyunta tazauna awajen, yanzu kowa yazata Beebah ce Matata!... Wani irin magana ne kake faɗa dude? Kana nufin wannan ba itace kake Aura ba? Kuma ai naga pre-wedding pics ɗin da ita akai.

Abdul ne yayi mishi bayanin duk abinda akayi, Ahmad yayi shiru yana tunani can yace "Amma Abdul ka tabka kuskure Babbah! Meya kaika ɗaukan hoto da 'yan biyun wacce kake Aura kuma kace Ba itace matarka ba! Kana ganin mutane baza suyi maka mumunan fahimta ba? agaskiya ka aikata Babban kuskure!

Abdul yace "hakika Ahmad na aikata kuskure to amma tayaya zan wanke wannan kuskuren danayi"?

Ahmad yace mafita ɗayane garemu shine kaje gobe ka ɗauko matarka koma muje tare, kacewa kanwarta ta ɗauko duk kayan da kukayi hotunan dashi saimu tafi tare dukanmu huɗu, Ita matarka saitasa kayan da wancan tasa ranar dazakuyi hoton koda shike ai su 'yan biyu ne, bazasu rasa kaya kala ɗaya ba,
Idan munje wajen ɗaukan hoton, ni saina ɗauka da Beebah kai kuma ka ɗauka da matarka, sannan muɗauka dukanmu huɗu, kaga zamu juya kan mutane, ba kowa ne zai gano bakin zaren ba, idan aka tambayeka saikace ai Bintu itace matarka!

Abdul wani sanyi yaji azuciyarshi, yacewa Ahmad to insha Allah haka za'ayi, nagode da wannan shawarar.
Suka sallami abokanansu suka basu hakuri, kowa yawatse.

_washe gari_

Ahmad ne da Habeeb suka buga wanka, sunsa anko gaba ɗayansu shadda ne fari da zubin baƙi, sukasa hula baƙi da takalmi baƙi sai agogo baƙi, bakaramin kyau sukayi ba, suka shiga motar Ahmad baƙi, suka ɗau hanya sai gidansu Bintu.

Suna zuwa Abdul ne yashiga daga ciki dan Ahmad yace shi baze shiga ba! Yana jiransu awaje, Abdul yana shiga ya gaida mommy afalo, mommy take bashi hakuri tace kayi hakuri Abdul wata 'yar matsala aka samu, shiyasa kaga ba'a kai maka Bintu ba! Abdul yace ba komai, mommy ce ta tashi afalon taje takira Bintu aɗakinsu, Bintu ce ta tashi tasa dogon riga, gaba ɗaya ta rame tin jiya take cikin kuka da tinani tarasa meyake mata daɗi.

Goga powder tayiwa fuskarta tasa baƙin kwalli acikin Idonta tayafa baƙin gyale, ta fesa turare ajikinta masu kamshi, tasa flat shoe, duk abinda takeyi Beebah na kallonta tace ko zamuje ku gaisa ne? Beebah tace no, tace dan Allah muje, Beebah data tuna dukan rannan saita diro akan gadon tace bari nasa hijab sai naje mu gaisa.

"Suna zuwa falon Beebah tafara tsayawa abaya baya dan tasan rashin kunyan datai tamishi jiya, shi kuma saiya basar yace ya kike kanwar Habeeb? Beebah tace lafiya ya gajiya? Yace babu,
Abdul ne yayi gyaran murya yace amm Hassana da Hussaina? Sukace na'am yace wata alfarma nazo nema awajenku, duk da Bintu yanzu ita matatace amma dole na nemi alfarma,
Sukace ba matsala kafaɗa muji in Zamu iya,
Yace dama inason ku ɗibo kaya waɗanda kukayi anko,
da wanda mukayi pre-wedding pics dashi, yanzu zamuje ayi sabon hoton sabida wancan akwai matsala"

"Bintu ce tace ita bazatayi hoto ba! Abdul yadinga haɗata da Allah taki, da Abdul yafusata yace look Bintu karkiga dan inasonki kice zaki wulaƙanta ni, yanzu miji nake awajenki umarni nake baki kitashi ki ɗebo kayanki zamuje ayi sabon hoto! Yafaɗa cikin fushi.

Bintu ce tahaɗa rai ta tashi tashiga ɗaki ta ɗebo kayan dana Beebah,
Beebah ce takarɓi kayan ta tafi sawa a mota, ita kuma Bintu tashiga cikin ɗakin mommy domin sanar da ita.

_Ahmad_
Shikuma ya zauna yanata jiransu amma har yanzu basu fito ba! Ganin haka yasa yajuya kanshi yadaina kallon kofar gidansu Bintun, dayaji karar buɗe kofar saiya juya yaga Beebah ce takesa kayansu aciki, tace ina wuni? Yace lafiya, daga cewa lafiya be kara komai akaiba kuma be sake juya bayanshi ba, yayi readyn jan mota idan sun fito.

Beebah ce tashiga cikin motar tazauna tana kallon side view na Ahmad.

Abdul da Bintu Kuwa sunata rigiman fitowa.
Bintu tace sai Abdul ne zai fara fitowa shikuma Abdul yana tsoron kada yashiga gaba ta gudu, shima yace sai ita zata fara fita.

Da kyar Bintu tayadda tafara fitowa rai aɓace taje ta buɗe motar tashiga wajen da Beebah take.

Shikuma Ahmad ko juyawa ya kallesu baiyi ba, yana ganin Abdul yashiga,
ko gama rufe marfin motan baiyi ba! Yaja motar cikin fishi yafara watsa gudu akan titi....

_✅ote, comment and share pls🙏🏻_

✍️🗒 *Jiddah S Mapi*
[6/23, 12:51 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Story/written by
*Jiddah S Mapi*

_Dedicated to my Facebook fans_

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Wattpad*
_Jiddah S Mapi_

Page 47&48

"Ahmad gudu yake akan titi kamar zai tashi sama, Abdul ne yayi mishi magana yace, haba Dude wannan wani irin gudu kakeyi? Baka tsoron muyi hatsari? Ko kuma mu bugu da bishiya? Shiru Ahmad yayi mishi,
ganin haka yasa Abdul yaja bakinshi yayi shiru, sabida yasan halin abokinnashi"

Bintu kuwa acikin zuciyarta haushin wanda yake tuka motar takeji, mutuminnan wani irin mugu ne? Yana gani muna cikin motar amma yake irin wannan gudun? Duk yanda akayi wannan baisan darajar mutum ba, mugu azzalimi, duk acikin zuciyarta take wannan maganar.

Beebah kuwa duk gudun da akeyi batama saniba sabida hankalinta duk ta tattarashi akan Ahmad, gayen yamatuƙar tafiya da imaninta,
Haka har sukayi parking awani waje me kyau, saman wajen an rubuta "Adamawa special photos" Ahmad yanayin parking ya buɗe motar yafita ko juya bayanshi baiyi ba, yana fita su Bintu ma suka fito, dukansu suka shiga cikin ɗakin da ake ɗaukan hoto, suna zuwa sukayiwa me hoton bayanin yanda akayi, yace musu ba matsala za'asan yanda za'ayi.
Chapter 9 · 0% Book details