← Book details A Gidanmu Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 12

Sashe 7

A Gidanmu Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka akayi kuwa bayan juma'a saiga Abful yazo, yayi kyau yasa brown na shadda da hula brown yayi kyau sosai,
Bintu kuwa tasa Abaya pink da gyallenshi tasa flat shoe pink tayi kyau kamar asace a gudu.
Tana zuwa wajenshi yaji ƙamshin turarenta a hankali ya lumshe idonshi, ya buɗe yace
"Tsarki ya tabbata ga ubangijin dayayi wannan halitta"

Bintu tayi dariya har kumatunta ya lotsa tace godiya nake masoyina.

Abdul yayi dariya yace ranki ya daɗe dolene yau nayi snapping naki ko ɗayane Bintu tarufe fuskanta tace banason hoto, Abdul yayi yayi ta ɓuɗe fuskanta taƙi, ahaka ya ɗauketa hoton ta rufe fuskanta da hanunta, tana dariya.

Haka sukaci gaba da hirarsu cikin farin ciki, suna cikin hiranne Abdul yanata dariya, dan Bintu yau tana ta bashi labarai,
kawai saiga Beebah tazo wucewa,
da Alama mommy ce ta aiketa.

Bintu tayi shiru zuciyarta tana bugawa tana tsoron kar Beebah ta wulaƙanta Abdul irin na rancan.

Beebah tana isowa wajensu ta tsunkuya har ƙasa tace "ina wuni yaya Abdul"....

✍🗒️ *jiddah S Mapi*
[6/23, 12:49 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*dedicated to my love ❤️*

*WATTPAD*
Jiddahpretty

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

Page 33&34

"A firgice mommy taɗago kanta tana kallon Beebah tace ke Beebah bakida hankali ne? Ya 'yar uwarki tana nuna miki saurayinta zaki faɗi maganan banza akanshi? Idan nakarajin irin wannan maganan daga bakinki saina ɓata miki rai tashi kibani waje"

Beebah tafita a ɗakin, mommy tace kiyi hakuri Hassana na kinga 'yar uwar taki batada hali me kyau, bani hoton nashi nagani, Binta tace to saita nunawa Mommy hoton mommy tace kaii amma gaskiya sirikinan ya haɗu masha Allah ya sunanshi? Abdul inji Bintu, masha Allah Babban suna Allah yabarku tare, kuma Allah ya nunamin ranar Aurenku Ameen.

_Ahmad_

Habeeb ne yasashi agaba yayi ta mishi nasiha, Ahmad yace nagode Habeeb Allah yabar zumunci.

_HABEEB_

"Habeeb kuwa acikin zuciyarshi yana tunanin yafaɗawa Ahmad damuwarshi amma yana tsoron kar ayi mishi mumunan fahimta, azuciyarshi yace kai garadai nafaɗa mishi ko zai nema min mafita,
Wani abu yace mishi Aa karka faɗa ka riƙe sirrinka, ba lalle bane kowa yayi maka kyakkyawan zato"

Yana cikin tunanin yaji an dafashi, Ahmad ne yace "abokina kasan bana ɓoye maka komai a rayuwata? Habeeb yace eh, to kaima banason ka ɓoyemin komai inason kafaɗamin damuwarka,
na lura tin Wancan zuwannaka kana ɓoyemin wani abu"
Habeeb yace babu komai Ahmad dama wata 'yar matsalace agida amma in Allah ya yadda za'ayi solving nasu very soon.

To Allah yasa Ameen

_Bintu_

Yau ce ranan dasukayi da Abdul zaizo wajenta dan haka tasha wanka tasa atamfa ja da jar gyale sai jar takalmi tayi makeup, idan kaganta kamar kasace ka gudu.

Abdul yazo gidansu Bintu anyi mishi tarba me kyau, Bintu ta ajeshi a babbar falo suna hira sai Abdul yace

"Babe tinda nazo banga twins nakiba ki kirata mana mu gaisa".

Bintu tace tom, saita ɗau waya takira Beebah tace kiseni a falon Mom, Beebah tace ok
Jim kaɗan saiga Beeba tasha doguwar rigar material ja itama jar gyale tasa, tana zuwa falon ta tsaya akan Bintu tace gani,

Bintu tace Abdul ne yakeso ku gaisa, tace to bagani ba! Bintu tayi shiru Abdul yace ya kike ƙanwata? Beebah tace Aa niba ƙanwar ka bace ni ƙanwar Habeeb ce, Abdul yayi dariya yace toya kike ƙanwar Habeeb? Tace lafiya

"Yace ok saiya cire kuɗi yace gashi ko ƙanwar Habeeb,
Beebah tace Aa ai gidanmu ba'a yunwar kuɗi.

Ta juya tayi tafiyarta Bintu tayi shiru tarasa yazatayi,
Abdul yace karki damu my dear nasan yaranta ne yake daminta karkiji komai.
A rayuwar Bintu ba abinda tatsana kamar wulaƙanci haka suka ƙarashe hiransu da Abdul tarakashi wajen motarshi tace mishi sai yaushe Kenan yace gaskiya ba rana Babe, tace dan Allah kayi hakuri da abinda twins nawa tayi maka yace ba komai babe, haka sukayi sallama yatafi tana ɗaga mishi hannu.

Tajuya tashiga cikin gida ta samu Beebah kwance suna waya da Habeeb, tana zuwa ta wupce wayar ahanun Beebah Tace "bakida hankali Ko? to yau zan koya miki hankali har Zaki wulaƙanta Abdul kuma kinsan shi zan Aura? Beebah tace bani wayata! Baza'abada ba! Ki ƙwace Beebah tafara ƙwatar Wayar suka kwashe da dambe!

_HABEEB_

Habeeb suna waya da Beebah yaji duk Abinda sukeyi yanatayi Musu magana su daina amma ina sai ihun Beebah yakeji alamun tana dakuwa, aranshi yace me hakuri fushinshi babu kyau!

Beebah bakaramin duka takesha ba awajen Bintu, gashi bakinta baya shiru, tana ta zagin Abdul, da Bintu taga Beebah ba shiru zatayi ba saita fita falo ta tsinƙa sucket na TV tashiga ɗakin da gudu...

✍️🗒️ *jiddah S mapi*

_pls share🙏🏻_
[6/23, 12:49 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Story/written by
*Jiddah S Mapi*

*dedicated to my love❤️*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Wattpad*
_Jiddah S Mapi_

Page 37&38

"Abdul ya saki baki yana kallon Beebah a Azuciyarshi yace wataƙila ma sabon salon iskancine takoya zatayi mishi, taƙara cewa ina wuni yaya Abdul, Abdul yace lafiya kanwar Habeeb ya kike ya gida? Tace lafiya lau yaya, Yace ina zuwa haka? Beebah tace Mommy ce ta aikeni G.R.A zan kai aika, yace ok dama nima tafiya zanyi me zai hana na sauƙe ki acan? Tace tom nagode,
Abdul sukayi sallama da Bintu yashiga motar Beebah ma tashiga suka tafi"

A hanya Abdul yake tambayar Beebah yace
"ƙanwar Habeeb meyasa kika sauya alokaci ƙanƙani? " Beebah tanason tayi mishi rashin mutunci Amma tana tsoron karya faɗawa Bintu takara shan dukan mutuwa.

Tace mishi babu komai

yace "ok"

yaje ya ajeta a G.R.A yayi tafiyarsa.

_Ahmad_

"A kwana biyun da Habeeb yazo wajenshi yaɗan samu sauƙin abunda yake daminshi, Amma har yanzu bai dawo daidai ba, yau yaɗan buɗe data yace bazi yaɗan ganin Abunda yake tafiya a social media, yana buɗe datan yaɗan aje wayar sabida messages ɗin sugama shigowa, bayan wasu 'yan mintuna yaɗauki wayar yana duba messages na abokai da kuma 'yan uwanshi saiya shiga message na Abdul wanda yaga hotone yatura mishi, yana buɗewa yaga hoton wata faran yarinya doguwa tsiririya ta rufe fuskanta tana dariya da Alama batason hotonne aka ɗauketa,
Duk yanda yaso yaga fuskarta yakasa"

Yabuɗe voice chat ɗin da Abdul yayi mishi yaji Abdul yace "dude ga hoton matana danake Auran" Ahmad yayi mishi reply da Allah yasa ka Aureta dude, yatura mishi.

_Bintu_

"A duniya ba abinda takeso sama da Mommy dakuma Abdul yanzu har maganan Aure yashiga, domin Abdul yaturo iyayenshi anyi magana,
ansa rana,
wata biyu masu zuwa, idan an ɗaura Aure kuma a kaduna zasu zauna".
*************

"Yau Da daddare mommy tashiga ɗakin Habeeb Tanason tambayarshi maganin ciwon kai, Amma me? Tana zuwa ɗakin taga Habeeb yarungume hoto yana kuka Kamar ƙaramin yaro, be maji shigowarta ba!

"A hankali tajuya tafita a ɗakin ta tsaya a window tana leƙanshi, sai kuka yake harda sheshsheƙah, yana kukan yatashi yaje wajen kayanshi, ya ɗauko wani frame pink colour me kyau yasa hoton aciki ya buɗe kayanshi yasa frame ɗin ya fesawa kayan turare ya juya yashiga toilet".

Mommy tana tsaye tana kallon ikon Allah, nan ta tuna wata rana datazo takamashi yana kallon hoto, yana ganinta yayi sauri ya ɓoye hoton abayanshi,

Mommy tagaza ganewa Habeeb wani irin mutum ne? Idan tace ya kawo matar daze Aura sai yace mata "A GIDANMU TAKE" tarasa gane me kalman yake nufi.
Amma koba komai yau saitaga hoton dayake ɓoyewa ko ta halin ƙaƙa!
Tajuya tayi tafiyarta takoma falo.

Habeeb yana shiga toilet ya wanke fuskarshi yayi alwala yazo yayi sallah, yana idarwa yatafi falon mommy yana zuwa yatarar da ita da 'yan biyunta suna hira, yafara murmushi yace kaga Mommy da 'yan biyunta, mommy tace eh wallahi Habeeb Amma meya sameka naga kamar kayi kuka? Habeeb yace wallahi mommy yau bacci nayi tayi, Mommy tace ok.

"Da safe Mommy takira Habeeb awaya tace yazo falo zata aikeshi, Habeeb yana zuwa
Mommy tace GRA zakaje ka karɓomin saƙo yace tom Mommy, Habeeb yana fita agidan Mommy taje ɗakinshi ta buɗe kayanshi daidai inda taga jiya ya ajiye hoton,
Tana ganin hoton ta ɗauka ta tafi ɗakinta dashi, tana zuwa ɗaki ta buɗe frame ɗin.

Ta ɗauko hoton tana gani.

Amma me? Tana kallon hoton jikinta yafara rawa hanunta yakasa rike hoton kawai sai hoton yafaɗi.
itama tabi bayan hoton a sume...

*Share, vote and comment🙏🏻*

✍️🗒️ *jiddah S mapi*
[6/23, 12:49 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Story/written by
*Jiddah S Mapi*

_Dedicated to My love_

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Wattpad*
_jiddah S mapi_

Page 39&40

"Mommy takai minti talatin Asume, kafin Beebah tashigo falon tana sallama taga Mommy Akwance ƙasa ba Alamun numfashi, Ta tsala ihu tana kiran Bintu, dagudu Bintu tashigo ɗakin ganin Mommy asume tayi gudu taje frij ta ɗauko ruwa suka shafa mata afuska"

A hankali tasauke Ajiyar zuciya, tafara buɗe idanunta.

Ganin Beebah da Bintu tsaye akanta cirko cirko, tafara Addu'an Allah yasa basuga hotonba.

Tajuya tana dube duben inda hoton yake Amma bata ganiba, ta rikice tana neman hoton can taga hoton Agaban Bintu daidai ƙafarta, Bintu kuma bata lura da hoton ba burinsu suji me ya sumar da mom?

Mommy dataga Alaman basuga hoton ba tayi sauri ta kwanta rub da ciki akan hoton tana cewa wayyo cikina! Tafara ja da cikinta har ta iso wajen gado tatura hoton babu wanda yagani.

Bintu da Beebah suka rinƙayi mata sannu harta samu tayi bacci, Beebah ce takira Habeeb tace mishi "yaya mommy ba lafiya harta suma"

Habeeb yace meya sameta? Tace babu komai muma dai haka muka shigo muka ganta a sume, yace "ok" ina izuwa.

Habeeb yana zuwa yaga mommy akwance tana bacci yafara tambayan Bintu meya sameta?
Bintu cikin sanyin murya tace nima dai haka nazo naganta a sume! Amma naji tana cewa cikinta ne yake ciwo!
Yayi shiru yana kallonta yace "ok".
Chapter 7 · 0% Book details