← Book details A Gidanmu Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 12

Sashe 1

A Gidanmu Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[6/23, 12:43 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_story/written by_
_jiddah S mapi_

_Follow me on wattpad_ jiddahpretty

Hi guys this is my first story hope I will have your maximum co-op ration ❤️

*NOTE:* Banyi wannan littafin sabida wani ko wata ba, labarin kirkirrarre ne sabida haka akula sosai.

_dedicated to fateemahsardauna_

Page 1&2

"Haba Ahmad meyasa bazaka dauki kaddara ba, kasani fa kowani dan Adam da irin tasa kaddarar, na wani yafi na wani amma Sam kai baka dauki kaddaraba.

Nan naga Wanda aka kirada suna Ahmad ya dago kanshi, yana hawaye fuskarshi tayi ja, buɗe baki yayi yanason yin magana amma ya kas, sai kuka yake kamar wata mace, hadda shesheka dakyar ya iya cewa "Haba Habeeb ya bazanyi kuka ba, bacin kai kasan abinda yake damuna, idan Banyi kukaba me zanyi?" Yaƙare maganar cikin sanyin murya.

Gyara zama Habeeb yayi haɗe da cewa.
"Addu'a ya kamata kayi Ahmad, domin itace abinda yakamata kowani musulmi yayi, a lokacin daya samu kanshi cikin yanayi na kunci."

"Ya isa haka Habeeb, ka ƙyaleni naji da abinda yake damuna, bawai ka cikani da surutunka ba, sanin kanka ne nayi babban rashi a rayuwata, rashin daba zan taɓa mantawa ba, tunda narasa FATEEMAH narasa komai,
na wulaƙantata, na ƙuntata mata, nayi mata abinda bazata taɓa mantawa daniba, Ina zanga Fateemah? Ina zanji labarinta? tana raye ko Tana mace?" Ɗan jinkirtawa da maganan yayi, kana ya cigaba da cewa.
"Idan Tana raye Ya Allah Ka bayyana min ita, idan kuma tamutu Allah Ka kai haske kabarinta!!" Ya ƙarashe maganan yana wani irin gunjin kuka.

Awannan lokacin har Habeeb ba'a barshi abaya ba, duk dauriyanshi shima seda yayi hawaye, yana me tausayawa abokinnashi.
*** ***

"Wai Ina kike ne BINTU? kiyi sauri dan Allah kinsanfa mommy Tana jiranmu a mota."

"Ina zuwa Sis HABEEBA, gyalena nake dubawa ban gani ba." Naji wata siririyar murya Tana fada.

"Kiɗauki nawa a wardrobe mana bintu." Habeeba tafaɗi haka cikin yanayi na ƙosawa.

"Okay nama dauka ae ganinan." Beentu tafaɗi haka tana mai ƙoƙarin yafa gyalen ajikinta.

"Okay dama koban ce kidauka ba zaki dauka kenan?" Habeeba tafaɗa tana ɗan kallon gefen da Beentun take.

Nan naga Beentu na sauƙowa daga kan step, cikin takunta mai ɗauke da nutsuwa. Farace sol doguwa siririya, tana da manya manyan idanu, bakinta dan karami, ƙoƙarin gyara gyallen take, tayadda zai zauna akanta.

Cewa tayi "Haba My Hussaina, Kinsan fa bama haka dake, kuma naga kema ay kinasa abuna ko my sis?"

"Da ma ay haka zakice, kullum se kinwa mutum laifi kizo kina mishi sanyin murya, to yanzu de muje kinga Mom nata kirana, kusan 6 missed calls tayi min" Habeeba tafaɗi haka tana mai duban wayarta dake riƙe a hanunta.

"Okay to muje" Cewar Beentu.

A tare suka fito daga falon suna sauri.

_see me next page_

✍️🏻 *Jidderh S Mapi*
[6/23, 12:43 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

_story written by_
Jiddah S mapi

_dedicated to fateemahsardauna_

_wattpad jiddahpretty_

Page 3&4

Suna fita daga falon habeeba ta kwalawa driver Kira yace gani hajiya

tace Ina mommy yace ay hajiya ta dade da tafiya tace bazata iya jiranku ba idan kun gama ku sameta agidan abinci
ok to kaimu driver yace to nan suka shiga motar suka tafi
bayan driver yayi parking naga sun shiga wani waje me kyau Wanda naga ma'aikata da uniform suna rabawa mutane abinci wasu kuma suna dafawa

Wasu na wanke plates daga gani de wannan gidan abinci ne Wanda yayi suna agarin

ADAMAWA Ina daga kaina naga an rubuta HASSY and HUSSY'S KITCHEN

suna fita a motar idanun mutane suka dawo kansu Ana tacewa kaga 'yan biyun hajiya bada kunku asare

Kuje gida kuce yafadi habeeba ce kadai me cewa sannunku

Samarai barka da war haka ita kuma bintu sai murmushi take nan naga sun nufo wata kykkyawar mata wacce zatakai shekara 40 habeeba tafada kan cinyar matar

Tace mommy shine kikayi tafiyarki kika barmu

matar da aka Kira da mommy naga tayi murmushi nan naga tsananin kamanta da habeeba tace ba dole natafi ba

Kun tsaya kunata shirme kuma kunsan yau ranar biyan ma'aikata ne

Mommy ai bintu ce ta tsayar damu kinsan yanayinta dayin Abu kamar karkashi

Aa karki sake kizagammin ya zo maya my bintu kizauna anan

Bintu tayi murmushi tace mom inason yau zanyi stew da kaima
Mom tace Haba bintu yazaki gajiyar da kanki kizauna kihuta kinji my bintu

Aa mom kibari zanyi
Toshikenan bazan hanakiba jekiyi

Ahmad dama nayi niyan tafiya yau amma bazan iya tafiya nabarka awannan yanayin ba

Nagode habeeb Allah yabarmin kai dan Allah habeeb ko bayan na mutu idan kasamu my teemah dan Allah ka aureta sabida kai Kadai nayadda dakai Kai Kadai nasan zaka riketa da amana tinda kasan bakar wuyar datasha kasan na zalinceta naci amana dan Allah kayimin wannan alkawarin🙏🏻

_see me next page_
[6/23, 12:44 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

_story/written by

Jiddah s mapi

_dedicated To fateemahsardauna_

_wattpad_
Jiddahpretty

Page 5&6

Ahmad kadaina irin wadannan maganganun

Banajin dadinsu Sam meyasa kake maganar mutuwa bayan bakaga fateemahn kaba

Ahmad insha Allah Bazaka mutu ba seka ga fateema

Ka nemi yafiyanta Sannan ku Gina rayuwa me kyau

Kuma inada tabbacin fateemah zata yafe maka

Habeeb bana tinanin my teemah Zata yafemin koda bayan raina ne

Habeeb babu abinda yake damina kamar yanda mommy tadau

Zancennan da zafi ka duba kagani

Yau kusan shekara daya ban sa mommy a idona ba

Yazanyi da rayuwa ta ya karashe maganan yana me hawaye

Abin tausayi

Habeeb kam ba bakin magana

Shi mamaki ma abun yake bashi wai ace yau

Ahmad ne yake kuka yana fada mishi damuwanshi

Shida magana ma be dameshi ba

Gsky dayana da yanda ze taimaka mishi daya yayi

Amma shi besan ma ta ina ze fara ba

Allah ka gaggauta kawo mana karshen

Matsalarnan Ameen

*BINTU*

Mommy wai meyasa bintu take zubar mana da class ne

Kiduba fa yanzu wajen masu aiki zataje suyi tare

Gsky mom abinda takeyi bata kyautawa wannan aji down ne😏

Habeeba kibi rayuwa a hankali

Ita duniya a hankali ake binta

Wanda batazo bama Tana jiranshi bale muda muke cikinta

Ni gsky mom kina daurewa bintu gindi dama nasan

Niba sona kike ba

Bawai bana sonki bane beebah babu Wanda ze haifi da

Yakishi sede idan kaddara ne

mom tafada idonta yana cika da hawaye

A hankali tajuya kanta yanda bintu bazata ganta ba ta goge idonta

Bintu kuwa iyayen son aiki tanata girki suna dan hira da ma aikatan

Dan ita ba ma'abociyar son magana bace

Cikin hiranne wata Wanda suka dan saba da bintu

Take tambayan bintu

Friend dama inason inyi miki wata tambaya

Ok nabeela inajinki

Amma Allah yasa ranki baze baci ba

Aa ba komai yi maganarki ok

Dama inason tambayanki tum bayau ba

Hajiyace ta haifeki!!!?

Haba nabeela wannan wace irin magana ce yazakimin wannan tambayar?

Bacin kinsan mu 'yan biyune nice babba

Gsky bintu ba kowane ze yadda ba

Duba da irin yanayinki Kiga beebah mana

Tana Kama da hajiya

Amma ke Sam babu abinda yahadaki da hajiya ta kamanni ko hali gsky akwai abun dubawa anan

What are you saying nabeela!!!?

Cewar mom Wanda tin farkon maganarsu takejinsu

Ta taso tambayar bintu kota gama hadin?

See me next page

_Wattpad_
Jiddahpretty
[6/23, 12:44 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

_story/written_by
Jiddah S mapi

_dedicated to fateemahsardauna_

Page 7&8

A take suka juyo ganin yadda mommy tayi maganan da karfi

Nan take jikin nabeelah yayi sanyi ganin yadda yananayin mommy yacanza a lokaci kankani

Haba nabeelah wannan wace irin magana ce meyasa kike son sa shakku a zuciyar

'Yar da Nina haifeta a cikina? shin bakida labarin Akwai 'yan biyun da Sam basa Kama da juna?"

"meyasa ku mutane
Bakwa gane abune yanzu da ace bani na haifi bintu ba dazaki hada abinda Baza'a taba cewa ke kika hada ba" saikuma tsaya

"Gsky bana son irin wannan tambayar"

Kai daga yau ma kada nakara ganinki da bintu Dan nan gaba bansan mezaki ce mata ba

"Kiyi hakuri hajiya in Allah ya yadda hakan bazata Kara faruwa ba...." inji Nabeela

"Banason dogon magana nabeela nariga nagama magana" hajiya ta mayar mata

"Bintu wuce mutafi"
Tafada cikin bacin rai

"To mommy" cewar bintu wacce tinda mommy tafara fada ta Sunkuyar da kai saida zasu tafi ne takuma ɗaga kai tadubi Nabila wacce duk kunyar momy ya isheta

*AHMAD*

Dakyar habeeb yasamu ya lallabashi yai shiru

"Ahmad gobe idan Allah yakaimu kafin in tafi dan Allah inason muje asibiti Aduba lfyrka dubi yadda karame" inji Habeeb

"Aa base naje asibiti ba maganin cutana bana asibi bane Maganin cutana my teemah ne idan nasameta zan warke insha Allah" inji Ahmad

"Toshikenan yanzu de ka kwanta kahuta sannan karage damuwa saboda zata haddasa maka cuta" inji Habeeb

"Nima Bari nakira agida nafada musu na shaida bazan samu dawowa ba sai gobe"

Mommy na isowa wajen Beebah tasamu sit nata ta zauna rai ɓace

Beebah bataga fuskar tambaya ba

Sai takarasa wajen Bintu tace "Bintu yanaga ran mommy a bace"

"babu komai sis" inji Bintu saboda tasan idan Beebah taji maganarnan bazata ɗauka da sauki

"Yazakice min ba komi bayan gashi ranta a matukar ɓace"

"Nace miki ba komai ke meyasa kin fiye naci ne? Inji Bintu

"Ko zaki dake nine to?" cewar Beebah

"Nibance zan dake kiba dan haka kimatsa min anan" Bintu ta mayar mata

"Zaki fara ko beebah meyasa bakya girmama tane tagirmeki fa" inji mommy

Beebah ta zumburo baki tana kunkuni wai datayi magana sai ace ta girmeta abinda baifi ƴan mintuna ba

"Yanzu de kutashi mutafi gida sabida yau yayanku ze dawo" cewar mommy

"Yee mommy dagaske kik?"cewar beebah

"Dama nataba miki karyane?"

Nan wayan mommy yafara ringing

"Yawwa ga shima yana Kira"

amsawa tayi takara a kunnenta

"Hello my son yakake? ok se gobe? Amma meyasa yau bazaka dawo ba? Ok to Allah yakaimu goben" saikuma ta kashe wayar

"Kunga yayan nakuma yace se gobe ze dawo" mommy tafaɗa musu

"Kai amma naji haushi mommy" cewar beebah

Mommy tace "Yau da gobe duk dayane beebah kawai muyi addu'a Allah yakawo shi lafiya"

"Ameen" cewar bintu

_See me next page_
Chapter 1 · 0% Book details