← Book details A Babban Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 6 OF 20

PROLOGUE

A Babban Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read

*PAGE* 0️⃣5️⃣

Ina ƙaunar ki Qawa ta AISHA USMAN (Baby) namecy.
Allah ya kula min da ke a ko ina ya cika miki burin ki. Much ƙauna ƙawa ta ta kaina.. wannan shafi dai naki ne tawan....🤩😘

SHARE AND COMMENT PLEASE!
_______________★★★________________


Ammi ce ta taimakawa Mamah ta kwantar da ita, sannan ta hango thermoflask Allah ya so akwai ruwa a ciki, a ɗan baho ta haɗa tayi mata tapid sponging. Mamah kuwa kuka kawai take yi. Ta rasa meh yake mata daɗi, Ammi kuwa sai aikin lallashi take tana danasanin abinda mutanen unguwar ke yi wa Mamah duk da cewa ita bata ciki.

”Tabbas matar nan na buƙatar taimako kuma zan taimaka mata iya iyawa ta.”
Ɓangaren Zahrah kuwa Abban Badi'a ne ya riƙe hannun ta suka fita zuwa gidan shi yana Allah wadai da irin halin Idrisu. Tare da fatan Allah ya saka wa iyalen shi da abun da yake musu.

Asubar fari hankalin ta ya dawo jikin ta, ganin ta a ɗakin ƴan gayu yasa ta zaro ido waje. Tunani ta fara MEH ya kawo ta nan sai ta tuna abun da ya faru daren jiya.
“Toh asibiti aka kawo Ni kenan”

Ƙafar mutum da taji a kan tata yasa ta duba,
“Badi'ah, MEH nake yi a gidan su kumah?
Oh ashe jiya Ammin su ne suka taimaki Mamah”

Banɗaki ta nufa wanda yake cikin ɗakin tana mamakin gayu irin nasu Badi'a hala shi yasa ko a islamiyya bata kula Ni saboda gidan masu kuɗi take.
Duk cikin ranta take zance.

A hankali ta buɗe ƙofar ɗakin ta nufi waje. Cikin sanɗa ta ke tafiyar kamar wata ɓarauniya.

“Zahrah ina zaki je asubahi haka”
Abba ne ya dakatar da ita lokacin dawowarsa kenan daga masjid.
Sunkuyar da kan ta tayi kafin tace
“ina kwana"

Murmushi yayi
“lafiya ƙalau Zahrah, ki koma kiyi sallah in gari ya waye sai ki koma"
Bata yi mishi musu ba saboda kwarjininsa. Wucewa tayi simi simi kamar ƙadangare ta koma.
Alwala tayi sannan ta ɗan taɓa Badi'a.

Itama tashi tayi ta shiga toilet Tana mamakin meh wannan maras kunyar take yi a gidan su.
Sai da ta jira fitowar Badi'a cikin sanyin murya tace

“ki ɗan bani hijab nayi sallah”
Bata ce mata komai ba ta buɗe wardrobe ta janyo hijab ta miƙa mata. Buzu buzu tayi sallar Badi'a na mamakin yadda take yi.
Sai da ta idar ta ce mata ai ba haka ake sallah ba.
Duk rashin mutunci irin na Zahrah sai ta ce toh koyamin.

Sai wajen ƙarfe 6:10am ta koma gida. Abun mamaki gidan tas.. ɗakin Mamah ta shiga. Abun mamaki kwance taga Mamah. Kusa da ita ta zauna can tace

“mamah”
Cike da don manta abun da ya faru tace
“zahrah! Kiyi wanka da wuri kafin Ishaq yazo."
Sarai ta gano Mamah shi yasa tayi shiru abun ta.

Wanka tayi ta fito, a ɗakin ta tarar da Ammi zaune gefen Mamah tana bata abinci, haka kawai ta tsinci kanta da farin ciki maras misaltuwa.

“ina kwana Ammi"
“lpia ƙalau Zahrah, ki saka kayan sai ki je ki ɗebo abincin.”

Tana shirya wa ta ɗebo abinci taci sai lokacin Ammi ta wuce gida. Mamah kuwa godia tayi ta shaƙa mata.

Da misalin ƙarfe 9:49am yaya Ishaq ya zo gida.
Sun gaisa da Mamah kamar ko yaushe cikin sakin fuska.
Basu ɓata lokaci ba suka nufi wata private school Mai kyan gaske. Makarantar ta matuƙar burge Zahrah kawai sai ta tsinci kanta da murmusawa..

ALMUNAUWARA ACADEMY

Yara ne ke wasa gwanin ban sha'awa, wasu bisa lilo Wanda da gani nursery students be. Wasu kuma ta wani ɓangaren waɗanda uniform ɗin su ya bambanta da na sauran wasu na guje guje wasu kuma suna wasanni mabanbanta.

Biye take da yaya Ishaq yayin da zuciyar ta ke mata wani irin sanyi. Yau ita ce a cikin ALMUNAUWARA ACADEMY, “makarantar su Badi'ah fah kenan.”
Ta faɗa tana sake wani irin ƙayataccen murmushi.

Daidai wani building suka nufa wanda da alamu shine staff room. Wani room Wanda aka manna signboard jiki ɗauke da “ADMIN" yaya Ishaq yayi knocking, izinin shiga ya samu suka shiga tare.

Sai da ta gaida mutumin kafin ta zauna kamar yadda taga yaya Ishaq ya zauna.

“Mallam Muhammad, Barka da safiya” yaya Ishaq ya faɗa tare da miƙa wa mutumin hannu.
“barka mutumi na, wannan ce yarinyar da muka yi magana da kai kenan"
“eh ita ce”
Wasu takardu ya fitar ya miƙa wa yaya Ishaq. Bayan ya kammala cike su ya ɗauko books cikin wani bag ya miƙa mata.

Haka dai aka gama komai a ranar aka bata uniform ɗin ta set II, farin ciki wurin Zahrah ba'a magana.

“ki jira Ni waje zan yi magana da malamin ku”
Ko amsawa bata yi ba ta fice zuwa jikin motar yaya Ishaq ɗin.

“Yauwah Man Please Please ka sanya wa yarinyar nan ido, ina so tayi karatu sosai”
“Alright I'll in Sha Allah”
Daga haka suka yi sallama.
Direct gida ya yi dropping ɗin ta.
“ki shiga zan shigo gobe na miƙa ki, ki gaida Mamah"
“toh yaya Allah ya kiyaye hanya”.

Kar kuso ku ga murna wurin iya Zahrah! Duk sai wani rawar kai take, Mamah kuwa kallon ta kawai take tana ganin ikon Allah. Yayin da wani ɓangare na zuciyar ta ke tausayawa yarinyar Tata.

Da yamma yaya Ishaq yazo.
Sabbin sandals da socks da wata school bag ya kawo mata.
yayi mata ƙarin bayani a kan makarantar sannan ya ja hankalin ta kan ta maida hankali.

“cutie na!" Ɗagowa tayi ta kalle shi
“ki dage da karatu kinji, ina so ki zama wata abu a rayuwa, ki zama abar alfahari gare mu baki ɗaya. Banda wasa, karatu kika je ba wasa ba, ki saboda haka ki maida hankalin ki ga karatun. Banda kula maza babu ruwan ki da su.... sannan banda faɗa. Kin gane ko?”

“eh na gane, in Sha Allah zanyi karatu da yawa"
Murmushi yayi yace
“Alright in naji labarin kinyi faɗa, hmmm”

Sallama yayi wa mama ya wuce shima don ya fara preparations na tafiyar shi London don yin masters ɗin shi. Haka kawai yake jin faɗywar gaba ko dan kawai sabon da suka yi da cutien shi ne ko kuwa,
“only God knows” ya faɗa can ƙasan maƙoshi.

Washegari tun 6:30 ta gama shirin ta. Kayan sun matuƙar ƙarɓan ta tamkar ɗin ita aka yi, Coffee brown trouser be sai Brown coloured hijab da riga. Sun matuƙar haska kyakkyawar fuskar ta tamkar wata sarauniya.

Horn ɗin da taji ne yasa ta ruga a guje zuwa waje.
Ko sallama bata yi wa Mamah ba ta fice abun ta.

Tun daga nesa yake hango ta tana tahowa. Ɗan lumshe idanuwan shi yayi ƙasan maƙoshi ya furta.
“She look so breathtaking, tabarakallah”.
Tana zuwa ta buɗe motar ta shiga

“ina kwana yaya Ishaq"
Cike da zolaya yace
“lafiya ƙalau zumuɗa, live kin daɗe da shirya wa.? Ehnn”
Fuskar ta ta rufe da hijabi tana turo baki
“kai fahimta kace na shirya da wuri”
“shine kika biye min?, Damah dai zumuɗin kike yi faɗa min gaskiya cutie" ya faɗa yana ɗaga mata gira..

A haka suka isa sannan ya ja hankalin ta kan tayi karatu in yazo ɗaukar ta zata biya mishi.
“bye”

Hannu ta ɗaya mishi sannan ta juya ta shiga. A lokacin ne students da dama ke zuwa. Kai tsaye ita ma shiga tayiba tare da nuna bata san school ɗin ba.

Unfortunately wani staff ya ganta. Da gani bai jin Hausa ma
“hey!” ya faɗa yana nuna ta da yatsa.

Wurin da yake ta nufa sannan tace good morning"
“morning, are u new here?”
It's da bata san ma me yace ba kawai sai ta ɗan tura baki da ta tuna da new na yace sai tace
“yes”
“ohk which class?”
Wannan kam da yake ta sani caraf tace “jss one”

Da hannu ya mata alamar ta shiga wannan class ɗin
“go and keep your bag there”
Kai ta gyaɗa kamar ta ji meh yace.

(Nace zaki sani in ya gano baki jin turanci duk buge kike yi😂)

Yaji daɗin yadda suka yi da malamin kawai sai taji tana son ita ma ta ƙware a turancin nan wallahi. a hankali ta shiga class ɗin babu kowa, kawai sai ta ajiye Baga ɗin ta a front seat ta fita.

Hanyar ta ta fitowa taga Badi'a na tunkaro ajin kawai sai taji tana don jiranta..

“Zahrah a makarantar nan aka saka ki" kai kawai Zahrah ta gyaɗa. Badi'a ta ja hannun Zahrah suka shiga cikin class ɗin, dropping bag ɗin ta tayi ta ɗauko ta Zahrah da ta ajiye a left sided front seat zuwa middle raw daga nan suka fita tare.

Bayan anyi assembly suka dawo class. First period Basu English ne, gashi malamin bashi da kirki duk tsoron shi suke. Yana shigowa suka miƙa gabaɗaya

“good morning sir”
“morning how's the weekend?”
“fine sir"
“ohk have ur seats"

Lesson plan ɗin shi ya ɗauko daga nan ya buƙaci marker daga wurin class rep. Bayan ya bashi ya rubuta TENSES sannan ya juyo
“good morning once again, our topic of discussion today is TENSES.
Is there anyone who'll tell us something about tenses?"

Shiru class ɗin yayi babu alamar motsi tamkar ruwa ya cinye su. Jin shirun su yasa ya yi pointing Badi'a,
“Badi'ah Kabir Umar, please say something” shiru tayi tare da sunkuyar kanta.

“Alright, the girl next to Badi'a say something"

Bata san ma da ita yake ba saboda ba jin turancin take yi ba. Zaro ido ƴan class ɗin suka fara jin taƙi tashi. Zata jawo musu bala'i wurin Uncle Hashim. Badi'a ce ta ɗan buge ta hakan yasa ta yi tunani ko so take ta faɗa mata MEH abun yake nufi.

(Ku ji Zahrah, ke da baki san komai ba ke zata tambaya?😂)

Uncle Hashim da ya fusata cikin tsawa yace
“you should get out of the class now” still shiru ita ina ta san ma da ita yake. Zaman ta tayi ta ci gaba da jin abun da ake.
Ganin duka class sun zubo mata ido yasa ta galla musu harara.

Fita uncle ɗin yayi hakan ya baiwa ƴan clsss ɗin damar mata magana, wasu na zagin ta wasu kuma na cewa tayi sauri ta fita.

“Zshrah kina ji yana miki magana kika yi banza da shi ko?, Baya wasa ki fita in ba haka ba zaki ji a jikin ki" Badi'a ta faɗa tana ɗago hannun Zahrah alamun ta fita waje.

Ƙememe Zahrah tayi tace “toh Ni na san da Ni yake ne"
Ku ji ikon Allah fah😂

Wannan shine ZAHRAH'S FIRST DAY AT SCHOOL
MU HAƊU GOBE DON JIN YADDA ZATA KAYA TSAKANIN ZAHRAH DA KUMA UNCLE HASHIM
SHIN MAKARANTAR NAN KUWA TA DACE DA ƳAR KAWU?

JUST FOLLOW MY INK AND COMMENT & SHARE
ITZ DIAMOND LADY💎🤟
_Oum Zainab_

[27/09, 6:07 p.m.] 💎Diamond Bhatool 💎: ______________★★★_______________
Typing 📲
🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡
_(All in a big family🏠)_
★TAKUN FARKO★
_[Labari/Rubutawa]_
*©Fadimatu Adamu Hassan*
*A.K.A DIAMOND BHATOOL*💎

_______________★★★________________

️ ﷽
Chapter 6 · 0% Book details