← Book details A Babban Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 18 OF 20

PROLOGUE

A Babban Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 12 min read

*PAGE* 1️⃣8️⃣

Dedicated to mah sister Shaheedah, I love u endlessly ƙanwa am.

*Masu Neman labarin daga farko, kuyi following channel ɗin nan zaku samu*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X

*WhatsApp group*
https://chat.whatsapp.com/IWQW3ytbVc611XLon2sn66


SHARE AND COMMENT PLEASE
_______________★★★______________

AFTER FEW MONTHS....

Abakin wani makeken hotel motar tayi parking, na cikin basu fito ba for more than 10minutes, can wanda ke driving motar ya buɗe ya fito, wani ƙatoton shiregegen mutum ne wanda ya kai shekaru 45years a duniya. Maimakon ya shiga ciki ya zagaya ɗaya sure ɗin ya buɗe, a hankali ya miƙa ma na cikin hannu yayin da shima na cikin ya miƙo nasa sai naga hannun kamar mace.

Ɗago ta yayi ta miƙe still dai hannun shi riƙe da nata.
Wata fitinanniyar shiga ce da ko a ƙasar Turai ban jin ana yin ta. Wata lalatacciyar maroon gown ce a jikin ta wacce bata ɓoye komai nata ba. A haka suka shiga hotel ɗin har suka kai ɗaki room 48, ba tare da ta juyo ba suka shige ciki. Hour uku cikakku suka kwashe kafin suka fito kayan jikin mutumin duk sun yaƙushe..

Sau al lokacin na ƙarewa budurwar kallo Bibalon Baba AMARYA ce.
Tun daga nan na ja ƙafafuwa na na gudu kada Baba AMARYA tace ina sakawa ƴar ta ido.

On the other hand ✋

Ɗan gaba da majalisar su Kawu a nan ta kafa murhun da take soyawa Baba AMARYA awarar sayarwa. Hijabin jikin ta da yaji jiki ka ɗigo ɗigon maiƙo nasha nasha.
Wani saurayi da ake kira da Bubby ya zo ya tsaya kan ta ce
“yah Zahrah zubo min ta ɗari biyu gobe zan baki”

Saurayin da kana kallon shi kaga ɗan duniya ta ƙura wa big eyes nata, cikin ranta kuma tsoro take saboda har yanzu bata manta su waye maza ba musamman yadda Kawu ya wulaƙanta rayuwar ta.
“kaga Bubby in na baka Baba AMARYA ta ga babu ko ta biyar ne sai ta jibge ni, don Allah kayi haƙuri..”
Cikin kallo na baki isa ba yace
“zahrah yau ko uba amarya ne ba Baba amarya ba kwarangwatsa sai kin bani.”
Yana faɗa yaja matsamin da take zubawa ya fara ci...

Hawaye ne suka fara zubowa Zahrah don babu yadda ta iya gashi bata don Baba AMARYA ta yi ta bugun ta akan awarar nan ga kuma dukan Bibalo da zata ƙara mata wai ta yi wa uwar ta asara.
Sai da yaci kusan ta ɗari biyar ya tura abun gaban ta kafin ya miƙe yana cewa
“shegiya ba dai kin ƙi ki zo ɗaki na ba saboda tsantsar wayon ki?, Toh wallahi kullum sai naci iya ci na asawanyar taki ta kashe ki ƴar ɓakin ciki kawai"
Yana faɗar haka ya ja ƙafafuwan shi ya wuce, sunkuyar da kai Zahrah tayi ta fara kuka tun ma kafin ta isa gida.

Tana cikin wannan yanayin ne motar da na gani a hotel ɗin nan tayi parking, tare da mamakin motar Bibalo ta fito suna jerawa ammah kayan jikin ta yanzu atamfa ce. Sun tafe suna hira tamkar couples ɗin nan har suka zo gun awara....sai da ta tsaya ta yi tsaki tana tofa yawu a daidai jikin Zahrah. Zahrah da hankalin ta baya kan su jin sauƙar abu ruwa ruwa hannunta yasa ta juyo don ganin wa ya watso ruwa.....maida kanta ƙasa tayi ganin Bibalo ce.

Mutumin da suka zo da Bibalo, Alhaji Yunusa Budawa kenan, mutum ne mai kuɗi ba laifi amma ba can ba kuma yana da mata huɗu har da yaran shi kusan takwas ammah duk da haka basu ishe shi ba, bin matan banza kuwa kamar wanda aka saka shi.
Yau ina kin ganshi da wannan gobe kuma wata zaki ganshi da ita. Ya maida mata tamkar motar hawar sa amma yana kashe musu kuɗi in suna tare.

Sun haɗu da Bibalo ne a wajen wani Dije da aka yi bayan layin su, da yake Bibalo ƴar duma-dumar nan ne tuni ya ƙyaso ta...ita kuma don abin duniya da ya rufe mata ido gashi dama ita da bin maza kamar wata karya tun bata kai haka ba ta san maza.

Ɗan kaɗa kan sa yayi ya matso saitin kunnen Bibalo yace
“darling wannan kyakkyawar yarinyar fa?” ɗan haɗe fuska tayi haɗi da yamutsa ta kamar wata tsohuwa tace
“bebi mai aikin gidan mu ce, sam na tsane ta don Allah mu bar gurin warin jikin ta ya dame ni”
“toh kawai yace saboda shi ya riga ya hango abu kuma ko zasu rabu da Bibalo toh sai ya san yadda ya samu fine babe ɗin nan duk da cewa iya fuskar ta ya gani ammah har ya hasaso yadda yarinyar zata kasance.

Ganin bashi da niyyar tafiya gashi ya tsira wa Zahrah ido yasa Bibalo hasala, a lokacin ta cire takalmin ta ta buga wa Zahrah a ka
“shegiya mayya wai ke duk wanda ya kalle ki sai ya tsaya ne...toh wallahi ki sake shi don kuwa auren shi zanyi”
Ƙasa hana ta yayi saboda ya riga ya faɗa fa shikam.
Dukan da ta kai mishi a ƙeya ya dawo da shi hankalin shi nan da nan ya fara kame kame.
Babu kunya a bainan nasi Bibalo ta fizgo hannun shi, kamar wani raƙumi kuwa ya bi ta har sai da ta kai shi mota ta zaunar da shi ita ma ta shiga tayi ta surfa mishi Bala'i daga ƙarshe ta bar shi ya tafi.
Yana tafiya ta yi kan Zahrah da ke zuba wa wani awara a leda ta wanka mata mari har sau biyu left an right kafin tace
“zaki shigo ki same Ni mayya kawai” tana huci ta shige gidan.
Saurayin da take sallama ne ya bata haƙuri Saboda tun ba yau ba suka fuskanci yarinyar na cikin damuwa ga irin cin kashin da matar baban ta da ƴar ta suke gabza mata koda kuwa a wurin tallan awarar ta ne.
Ita sam ba damuwar ta dukan da Bibalo tayi mata bane sai dai uban Bala'in da zata tarar, ga Bibalo ga Baba AMARYA ma kuɗin da Bubby bai biya ba. Daga ƙarshe dai Zahrah yanke shawarar ƙin shiga da wuri tayi har sai sun kwanta.

Ɓangaren Bibalo tunda ta shiga ta fara kututtuma ashar wai ita ala dole mai kishi...mutumin da ko zata mutu bashi da niyyar auren irin ta ma infact Bata kai ba kawai dai yana rage zafi da hutawa da ita ne.

Baba AMARYA ce ta dakatar da ita da faɗin
“ke kuma fa Bibalo, ke da kika fita neman abun arziƙi kuma ya zaki dawo kina masifa? Ko dai bai biya ki ba ne?”
Hararar Baba AMARYA Bibalo tayi tace
“rabu da Ni kema, wannan ƴar abu ta kazar ubance mai ƙirar mayu....”
Nan ta kwashe komai ta faɗa wa Baba AMARYA
“shegiyar yarinya kinga irin kallon ta da yake yi?” ta faɗa tana ƙara banka harara kamar Zahrah na gaban ta.

Salallami Baba AMARYA ta fara
“innalillahi, Ni Saudatu ina ganin bariki yanzu duk irin rayuwar bariki da nayi yau sai da nayi mamaki, shegiyar yarinya bari ta shigo”
“si kuwa nimah cin uban ta zanyi Saudatu ” ta faɗi sunan gatsau babu ko girmamawa.

Shiru shiru Zahrah ta ƙi shigowa har wajen 10:00pm tana waje gaban murhun ta da already ta gama sayar da awarar tsoro ne ya hana ta shiga. Ba ita ta shiga ba sai around 12:00am lokacin har sun yi bacci, a hankali ta lallaɓa ta shige ɗaki bata ƙara fitowa ba coz lokacin da take shigowa da kayayyakin aikin ta taji motsi kuma ta san ba Kawu bane tunda Baba AMARYA ta riga ta haramta masa kwanan gida.

A ƙasa ta kwanta saboda Baba AMARYA ta sa an sayar da komai na ɗakin Mamah a cewar ta ai ba dawowa zata yi ba kayan gado ne. Kuɗin kuwa a cike aka bata dubu uku wai ta fara awarar a ƙofar gida kuma kullum ita take dafa awarar, ta yanka tun a gida a lissafa in ta kawo kuɗin da bai kai ba kuma taci uban ta da duka gashi ba wani isasshen abinci take ci ba shiyasa ta zama wata solo-solo kamar raƙuma.

Da yake kullum da asussuba take tashi in Bata tashi ba ma za'a zo a kwara mata ruwa. Tana cikin bacci taji ruwa a jikin ta....ba shiri ta miƙe, ko sallah ba'a barta tayi ba taji duka ta ko ina
Suna dukan ta suna tsine mata.
“shegiya karuwa jiya har da ƙin shigowa wato kin bi kwarton naki Koh!”
Tana ihu suna ƙara bugun ta sai da taji jiki suka barta. A wurin ta sume baba AMARYA ta lalume ta ta kwashe kuɗinta.

Ta kwashe kusan awa guda tana kwance babu wanda ya damu da sumar ta ballantana su watsa mata ruwa. Sai da lokacin ɗaura girki yayi Baba amarya ta watso mata ruwa.
Ajiyar zuciya Zahrah ta sauƙe yayin datake buɗe idanuwan ta da suka yi mata nauyi, gashi kuma bata jin ƙarfin jikin ta.
Ganin ta farfaɗo yasa Baba AMARYA taka ƙafafuwan ta, babu shiri ta saki ƙara.
“don ubanki waye zai yi girkin mayya kawai ki fito ki mana abinci”
Cikin rawar murya Zahrah tace
“ki....yi....haƙu...ƙi....ri...ba...nida.....lafiya....”

Wani sabon bugu baba AMARYA ta ke yiwa Zahrah ita kuwa bata da ko ƙarfin ihu daga ƙarshe ta ce lallai lallai ta fito tayi musu girki. Sai can da ƙyar Zahrah ta miƙa ta fito, ga wani irin jiri da take ji a haka tayi musu abincin.

Ko ɗanɗan ba'a bata ba wai tayi laifi kuma ta cinye kuɗin awara. Haka suka lamushe abun su.
A daddafe Zahrah ta koma ɗakin ta tunawa da awarar jiya da ta ɓoye kamar ta san ba zata samu abinci ba tayi. Ɗauko ta tayi taci ko ruwa bata iya sha ba ta kwanta ...sallah kuwa yau ko asuba bata yi ba gashi la'asar ta kusa.

Bayan la'asar haka ta fita tayi musu girki tayi awara wanda kawai ƙarfin hali ne ammah sun riga da sun nakasa ta.

Bayan tayi wanka da ƙyar ta iya ɗauko ƙanzon da ta kankare na awara ta cinye shi gaya kamar mayya. Tana kuka tana hawaye har ta ɗan ɓigire tana bacci, Baba AMARYA ce ta zo ta canke ta da ƙafa a zabure Zahrah ta miƙe
“don ubanki assrar waken zki min, ki fito ki fice da awarar” tana faɗin haka ta fice.

Zahrah bata samu fitowa ba don kuwa kanta wani irin juyawa yake....sai da ya ƙara wajen 40minutesa wajen, Baba AMARYA kuwa tunanin ta Zahrah ta fice da awarar don kuwa ta san bata mata magana biyu.

Lokaci ɗaya taji kanta ya yi wasai saboda haka ta fito sannan ta kwashi kayan suya.... Alhamdulillah yau da wuri ta sayar ta dawo gida tana bawa Baba AMARYA kuɗin zata juya taji tace
“akwai wankin kayan mu Ni da Bibalo yanzu ki zo ki wanke”
Marairaice fuska tayi ko Baba AMARYA zata ji tausayin ta tace
“don Allah Baba ki bari sai gobe da safe kinji, wallahi bani da lafiya”
A hasale Baba AMARYA tace
“mayya yau in asibiti ne kan ki sai kin yi wankin nan, shegiyar mai siffar aljanu.

Babu yadda ta iya ta juyo ga cikin ga sai ƙugi yake mata, yunwa kamar ta hallaka ta. Bayan Baba AMARYA ta shiga ciki Zahrah ta faki idon ta ta je wurin tukunyar da suka yi abinci. A hankali ta buɗe ta tsoma hannun ta, jin taliya ce yasa ta wawusa a baki kamar mayya, ta ƙara ciko hannun ta ta kai baki, sai da tacinye tass ta rufe a hankali ta zo ta haɗa ruwan wanki.

Tana cikin wanki Bibalo ta shigo, hara ta banka wa Zahrah yayin da ita kuma ta sunkuyar da kan ta ƙasa. Wankin ta take hankali kwance duk da kayan sun ci uban datti. Bibalo ce ta fito ta wullo mata pants ɗin ta wai ta wanke, a lokacin kuwa Zahrah bata san MEH ya faru da ita ba tace
“in na wanke miki shegiya nake” ta faɗa babu alamar tsoro a fuskar ta.

Bibalo ta jima tana mamaki saboda iya sanin ta Bulebule yace ba zata taɓa yi musu musu ba ya mallaka musu zuciyar ta sai yadda suka yi da ita. A tsorace ta koma ta sanar da baba AMARYA, babu shiri su biyu suka fito a ɗan tsorace, saboda kuwa Bulebule yace ina dai asirin kan Zahrah ya warke to uwar ta ma zata warke, kuma aikin ba zai ƙara yiyuwa ba sai Bibalo ta aure shi. Abun da baba AMARYA ba zata taɓa yarda ba.

Hankali tashe suka nufi ɗakin mamah coz Zahrah ta bar wankin ta koma ɗaki abun ta. Wani haushi kanta take ji ta yaya aka yi har suke dukan ta suke azabtar da ita haka....
Toh wallahi sai tayi maganin su.
Cikin ƙarfin hali da saddaƙarwa Baba AMARYA ta ce
“ke fito ki ƙarasa wankin nan”
Kallon da Zahrah ta aiko mata yasa ta zaro idanuwa ba shiri. Wani tsoron Zahrah ne ya ɗarsu cikin zuciyar ta. Babu shiri ta kamo hannun Bibalo suka taho ɗaki. Ita kanta Bibalo a tsorace take.

Ɓangaren Zahrah kuwa kuka ta saka bayan fitar su
“kun cuce ni iyakar cuta....kun azabtar da ni, kun ɓatar da mahaifiya ta yayin da kuka kulle min baki har na kasa faɗa wa masu ɗaukar min mataki.....kun shiga tsakani na da karatu na....tun hana Ni cikar buri na....billahil Azeem bazan zauna da ku ba, zan tafi na barku da halin ku daga ku har Kawu bazan yafe muku ba.....yau ba gobe ba zan tafi kun ƙuntata rayuwa ta na tsawon shekaru biyu....kun bautar da ni kooooooooo. Tunda knce Mamah ta ta mutu bazata dawo ba yasa kika sayar da kayayyakin ta shikenan, Allah mafi sani in da gaske ne bazan yafe ba in kuma tana nan zan ci gaba da addu'ar Allah ya haɗa Ni da ita.

Haka Zahrah tayi ta surutai daga ƙarshe ta tashi tayi wanka ta rama sallolin ta ta kwanta.
Safiya mai albarka Zahrah.

MUNA GAB DA SHIGA TAKUN ƘARSHE WANDA CIKIN SA NE LABARIN ZAI FARA, WANNAN DUK PROLOGUE NE!
SHAFI BASU FI BIYU BANE SUKA RAGE, IN KIN SAN KINA BIBIYAR ALƘALAMIN DIAMOND LADY TOH KI ƘARA HIMMA DA COMMENTS, IN BAKI BI TOH KI FARA KADA AYI BABBAN GIDA BABU KE... COMMENTS SECTION GROUP DUK WACCE BATA CIKI TA SHIGA IN NAGA BA A COMMENTS BA ZAN YI POSTING PART TWO BA KUMA ZAN MAYAR DA SHI NA KUƊI....What I need is ur comments saboda ƙarfafa guiwa.
DIAMOND LADY CE 💎
BHATOOL ADERM.
[08/10, 11:58 a.m.] 💎Diamond Bhatool 💎: ️______________★★★_______________
Typing 📲
🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡
_(All in a big family🏠)_
★TAKUN FARKO★
_[Labari/Rubutawa]_
*©Fadimatu Adamu Hassan*
*A.K.A DIAMOND BHATOOL*💎

_______________★★★________________


Chapter 18 · 0% Book details