← Book details A Babban Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 16 OF 20

PROLOGUE

A Babban Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*PAGE* 1️⃣6️⃣

Dedicated to Aunty fateemah (oum sa'eem)

*Masu son labarin daga farko kuyi following channel ɗin nan:* https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X

SHARE AND COMMENT PLEASE
_______________★★★_________

A hankali Zahrah ke buɗe idanuwan ta yayin da suka buɗe ras sun sauƙa kan Ammi da Badi'a.
Juya idon tayi don gane a wani wuri take, ganin I.V line maƙale hannun ta ga kuma ruwan da ke zuba a hankali yasa ta fahimci a asibiti take. Ammah me ya kawo ta?
A hankali ta fara tuna last scene nata ta shiga duba Mamah gidan Ammi kuma bata ganta ba daga nan ta manta yadda take.

Katse mata tunani Ammi tayi ta hanyar zuba cips and fried egg da ta soyo mata a plate. Kujera ta na ta zauna yayin da ta miƙawa Badi'a plate ɗin wacce fuskar ta ke ɗauke da murmushi.
A hankali Ammi ta ɗago Zahrah bayan ta zaunar da ita da kyau ta amso plate ɗin hannun Badi'a ta fara feeding Zahrah, bata Musa ba ta buɗe baki ta naɗi child ɗin tas.

Bayan ta kammala ci Ammi ta dama mata tea Mai kauri ta Sha, daga nan nurse da ke duty ta shigo, ganin IV fluid ɗin ya ƙare yasa ta zare mata shi kada jini ya zuba. Daga nan ta turo doctor.
Dr. Yayi farin ciki sosai ganin ta ji sauƙi har ya jata da zance. Tuni ta ware kamar babu abun da ke damun ta.
Da zai fita ya kira Ammi zuwa office ɗin shi, a nan ta sanar da ita abun da ke damun Zahrah
“ba komai ke damun ta ba sai anxiety Wanda yayi sanadiyar faɗawar ta shock ammah abun bai yi nisa ba Alhamdulillah, sai dai yarinyar taki na buƙatar kulawa ta musamman in ba haka ba akwai matsala. So yanzu na rubuta drugs sai ku bi pharmacy ku amsa. Don Allah Hajiya a kula da ita kuma a nuna mata soyayya”

Daga nan Ammi tayi mishi godia ta koma ward ɗin cike da fargaban ina Maman Zahrah ta je yau kuma, sannan menene dalilin faɗuwar Zahrah.

Basu ɓata wani lokaci ba aka yi discharge nasu, bayan shawarwarin da nurse ɗin da ke duty ta Basu.
A gajiye suka wuce gidan Ammi. Ɗakin Badi'ah Ammi ta raka Zahrah, ta haɗa mata ruwa mai zafi ta sata tayi wanka. Bayan ta shiga wanka ta turo Badi'a wurin ta sannan ta koma gidan ko mamah ta dawo sai dai shaaaaam kamar yadda taga ɗakin Mamah yanzu haka yake.
A sukwane ta dawo gidan lokacin Zahrah tayi wankan ta ta saka light gown na Badi'a.

Ita dai Zahrah baki ƙimmm bata ce komai ba tunda suka shigo gidan, ganin haka yasa Ammi ta bar ta zuwa safiya suji meh yasa ta faɗi.
“daughter ki kwanta ki huta, sai da safe.”
Kaɗa kai Zahrah tayi daga nan suka kwanta ita da Badi'a.

Ɓangaren Ammi da Abba abun ya ɗaure musu kai. Abba tun bayan Ammi ta sanar da shi mamahn Zahrah fah Bata nan shima ya shiga halin mamaki.
Daga ƙarshe suka yanke shawarar neman ta gobe bayan sun ji damuwar Zahrah ɗin.


★★★★★★★

“gaskiya ƙawata aikin boka Bulebule kamar yankan wuƙa yake”
Tafawa suka yi ita da Asabe kafin Asabe tace
“ke dai ki bari yanzu bani labarin abun da ke faruwa manah, shegiyar ta mutu ne”
Kallon ta baba amarya tayi kafin tace
“ke har kin manta boka Bulebule baya kisa ne?,”
“ooooh haka fah” ta faɗa tana riƙe baki alamun ta tuna
Baba amarya ta Kamo hannun Asabe ta riƙe sannan tace
“ina baki labari, ban san yaushe shegiyar matar ta fita ba ammah dai zancen da nake miki an rasa ta....wataƙila yanzu kam ta riga ta kama bolar zama”
Ta faɗa suna sheƙewa da dariyar shaƙiyyanci.
“baki da dama ƙawa ta, toh ita ƴar tata fah?”
Ɗan zare ido tayi sannan tayi fari
“ohoooh Ni ban sani ba, ammah na sani babu makawa aikin boka ya yi ina jira ta dawo ta sane ni nan”

Girkin da take yi ta ƙarasa ta zuba musu shi duka a tray, suna ci suna magana kamar wasu mahaukata. Bayan sun cinye suka ji gaba da hirarrakin su.
Baba amarya ta dubi Asabe ta ce
“ƙawa ta yaushe ya dace na ɗauko Bibalo ne daga ƙauye don yanzu kam ita ma nan zata dawo NBmu zauna mu mulki ɗiyar shegiyar tare”
Dariya Asabe tayi tace
“ƙwarai ya kamata ki ɗauko mana Bibalo gashi kuma ba zata fi sa'ar ƴar kishiyar taki ba”
Jin kishiya yasa Baba amarya makawa Asabe harara. Da yake duk ƴan duniya ne tuni Asabe ta harbo jirgin ƙawar tata sannan tace
“Kaji uwar kishi, kin zo kin samu mata da ƴa gidan su ammah ke kike kishi ba ma ita ba”
“yo ai dole nayi kishi da ita, da ace irin banzayen nan ne ma tooooh, ammah baki ga matar ba ga kyau ga kamala ni wallahi bata yi min kama da ƴar talakawa daga gani ƴar babban gida ce”
“ai kuwa na lura da hakan, ammah ko ma ƴar jibgegen gida ne ba babban gida ba yanzu kam ai kin wulaƙanta ta ta zama kashi”

Tafawa suka yi suna dariya kafin Baba amarya tace
“yanzu dai gobe ki raka ni ƙauye mu ɗauko Bibalo mudawo nan saboda ina son mu gasawa shegiyar aljanar yarinyar nan aya a hannu, ta yadda zata daina rasar kunyar da ta zama mata jiki”
“Ai Ni ƴar nan tun ranar tariyar ki na ƙullace ta saboda abun da tayi ga kuma shegen kyau har ta so ta fi uwar fa”
Bana amarya ta ce
“hmm ke dai ki bari kawai, zamu ci uban ta ne ai”
Haka suka yi ta hirar su daga ƙarshe Asabe ta koma gidan mata da yake dama can ita a can take da zama.

★★★★★★

Asuba nayi Zahrah ta tashi a hankali tayi alwala tayi sallah bayan tayi ta tayar da Badi'a ma tayi.
Bayan sun yi sallah suka yi wanka saboda yau zasu koma makaranta bayan sun dawo daga Jos.
Basu shirya ba sai around 6:30am suka nufi kitchen don taya Ammi aiki sai dai Ammi ta kora Zahrah kan ta huta ai bata da lafiya ita kam.

Da wuri suka yi breakfast ganin akwai sauran lokaci mai ɗan yawa yasa Ammi tace
“zahrah” a hankali ta ɗago da kanta ta mayar da hankalin ta kan Ammi
“jiya MEH ya same ki bayan jin zo nan kika faɗi??”
Bata ɓoyewa Ammi komai ba daga baccin su da tashin ta daga bacci har zuwa rasa Mamah da tayi.

Rarrashin ta Ammi tayi tace mata kada ta damu Mamah za ta dawo coz Abba ya sa a nemo ta. Cike da farin ciki tayi a Ammi godiya sannan suka wuce school.

Har suka dawo babu wani labari da aka samu akan Mamah, hakan ya ƙara sanya Zahrah cikin halin damuwa duk da cewa Ammi da Badi'a har da Abba na ƙoƙarin kwantar wa Zahrah hankalin ta. A haka suka wuce islamiyya bayan sun dawo ammah Mamah shiru Babu it's Babu labarin ta.

★★★★★★

Kwanaki uku kenan da ɓatan Mamah ammah shiru babu labari, duk wani radiostation da aka sanar babu wani ci GABA. Gashi har TV stations an sanar harda picture ammah babu ko tari balle wani ya ganta.

Yau da safe Zahrah ta cewa Ammi zata je gida ta ɗauko wasu kayan ta. Tana fita Kai tsaye gida ta shiga, bata tsaya ko Ina ba ta ahiga ɗakin Mamah, cike da damuwa da ƙunci Zahrah ke kallon ɗakin Tana hawaye.

Ɗauko wanna bag din da Mamah ta Bata a daren da zata ɓata tayi tana manna shi a ƙirjin ta. Wani sanyi take ji tamkar Mamah tayi hugging.
“Allah sarki Mamah na, Ina matuƙar ƙaunar ki, Ina Kika tafi haka Kika bar ɗiyar ki ɗaya? Don Allah Mamah ki samu ki dawo kada ki bar ni Ni kadai a nan”
Tsagaitawa tayi da maganar sannan ta ci gaba tamkar Mamah take gani
“aah Mamah nafi so ko zan je gidan ku wurin su Hajjaty da Kika bani labari muje tare da ke tunda ke ce dolem su”

Haka zahatah tayi ta surutai wasa wasa sai da ta kwashe awa guda a wurin. Motsin da ta ji ne yasa ta miƙe ta waiwayo ko zata ga mamah ammah wayam, hakan yasa ta ɗauki bag din tare da haɗa wasu kayayyakin ta ta wuce gidan Ammi.

Baba AMARYA dake tsaye bakin ƙofar ɗakin ta ta Kama kunkumi sai wani jijjiga take tamkar wacce ta ke jiran abokiyar faɗa ta kawo mata dambe. Ashe tun shigar zahrah da taji motsi ta leƙo ganin shegiyar yarinyar da take jiran dawowar ta yasa ta tsaya Tana jiran ganin ko zata fito tace zata taho.

*Don't forget to react and share*
[06/10, 6:23 a.m.] 💎Diamond Bhatool 💎: ______________★★★_______________
Typing 📲
🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡
_(All in a big family🏠)_
★TAKUN FARKO★
_[Labari/Rubutawa]_
*©Fadimatu Adamu Hassan*
*A.K.A DIAMOND BHATOOL*💎

_______________★★★________________️


Chapter 16 · 0% Book details