← Book details A Babban Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 20

PROLOGUE

A Babban Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read

*PAGE* 0️⃣2️⃣

Wannan shafi naki ne masoyiya
AISHA MB (Baby Isha) marubuyar littafin _aljanar ruwa ce_
Thanks a lot for ur selfless actions friend, loads of love🤩😘
Barka da Sallah

SHARE AND COMMENT PLEASE!
_______________★★★________________

Anyi sallar azahar kenan sai ga Yaya Ishaq ya zo kamar dai yadda ya faɗa, ya rasa ma ta yaya zai kira cutie ɗin tazo. Wani yaro ne yazo wulgawa ai kuwa da sauri ya dakatar da shi.

“kai yaro zo” ba tare da musu ba yaron ya je wurin yaya Ishaq
Ɗan kallon yaron yayi sannan yace
“ka ɗan shiga gidan nan kace Zahrah ta zo inji yaya ta”

Ba musu yaron ya buɗe ƙofar gidan sannan ya shiga ɗauke da sallama a bakin shi.

“Salamu Alekum”
Maamahn Amira da ke shara ita ta amsa masa tana mai dakatawa da sharar don jin neh yaron yazo yi

“wai Zahrah tazo in ji yayan ta a waje”
Bai jira amsar da maamah zata bashi ba ya fice abun da.
Yayah Ishaq kuwa har kuɗi ya bawa yaro.

Maamah ce ta ƙwala kiran amirah da suka wuce can filin bayan gidan suna wasan su. Jin shiru basu amsa ba yasa ta wuce a fusace

“ke ƴar karuwai ki fito yana jiran ki a waje”
Cike damamaki take kallon mamah. Shin meh yasa ake danganta ta da karuwanci?, Menene laifin ta da za'a ke mata hakan? tunawa da sabon yayan ta Ishaq da tayi, ai kuwa da gudu ta fita tana yi wa amirah sai da safe.

Tana ganin yaya Ishaq ta ɓare baki kamar gonar auduga yayin da shima yake jin ta ajikin shi. Babu abun da yake yi sai aika mata da saƙon murmushi.

“cutie, kin ce zaki kai Ni wurin Mamah koh?”
Zaro ido Zahrah tayi kamar wata munafika. Shi kuwa yaya Ishaq jin. Shiru yasa ya ƙara kallon ta tare da faɗin
“cutieeee...”

Ɗan tunani tayi da ƴar ƙaramar ƙwaƙwalwar ta sannan tace
“toh yaya muje”
“yauwah cutien yaya.”

A hankali yake driving ɗin yayin da hankalinsa kwacakwam ya dawo gare ta.
“cutie mai Mamah take ji a kasuwa da yamma”
Ɗagowa tayi da har zata yi shiru wata zuciyar tace ki faɗa masa wataƙila sanadiyyar haƙa sai ya samar muku sauƙi daga muguntar Kawu.

“mamah fah masa take soyawa a kasuwar kasan saboda meh?”
Kai ya girgiza kamar wani yaro yayin da ta marakraice fuska

“idan taje tayi Masar ne take samun kuɗi, sauran Masar kuma muna ci da daddare saboda Kawu baya bata kuɗin abinci, sai dai shi ya shigo da ledar abubuwan sa da tsire da irin lemon jarkar man ammah baya taɓa ko sanmana..” can ta ɗan yi shiru

“kuma da kuɗin Masar Mamah take min kayan sallah, sannan tana wankin gidan Cancellor ma saboda ta samu kuɗi”

Jikin yaya Ishaq sanyi yayi jin irin wata rayuwa. Yana nanata wa a ranshi wai baya basu abinci.
Kai anya wasu mazan ko zasu shiga aljanna?
Ka auro mata ka rabata da gidan su ammah ba zaka iya ciyar ta ba?
Haba maza ai kuwa zan taimakawa waɗannan ahaki ko meh zai faru.

Zahrah kuwa da taji shirun yayi yawa sai ta ɗan taɓo fuskar shi
“ka fasa zuwa ganin Mamah koh?”
Jijjiga kai yayi sannan yace
“aah cutie, zanje naga mamah”

Isar su kasuwa keda wuya suka fito, Zahrah ce gaba sai yaya Ishaq da ke bin bayan ta. Directly rumfar da Mamah ke ƙosai ta nufa.

“Mamah ga sabon yayah nah”
Mamah da ta ke kwashe Masar da ta soyu ta ɗago ɗan bata fahimci meh Zahrah ke faɗi ba.

“ya Hajiya Balaaba ɗin”

Ɗan yamutsa fuska tayi da ta tuna wulaƙancin da maamah ɗin tayi mata sannan tace

“lafiyar ta ƙakau, tace a gaishe da ke”

murmushi Mamah tayi sannan ta zuba masa uku a plate ɗin roba sannan tace

“ga Masar nan kici,, nadan baki ci komai ba”

Amsa tayi ta ajiye sannan tace

“mamah ga sabon yaya nahiyar yazo gaishe ki”

sai a lokacin Mamah ta lura da yaya Ishaq dake tsaye harɗe da hannayen shi a ƙirji. Shi kam hankalin shi baya kan shi, in ba da kallon su Mamah babu abun da yake yi.

Gyaran murya Mamah tayi, sai lokacin ya ɗan miƙe da kyau sannan ya nufi rumfar Masar.
Duƙawa yayi ya gaida Mamah cike da girmamawa.

“ina wuni Mamah, ya aikin”
“lafiya ƙalau ” kawai Mamah tace fuskar ta na ainihin bayyana mamaki da kuma kuɗin da ta shiga, idan bata yi ƙarya ba ai wannnan yaron gidan Cancellor ne.

Ganin yanayin Mamah yasa yaya Ishaq ya murmusa..

“mamah nimah ki ɗauke Ni kamar ɗan ki, ki ɗauke Ni kamar yadda na ke jin ƙanwa ta Zahrah a jiki na, bani da niyyar cutarwa a gare ku sai dai ina don tallafa wa rayuwar ku.”

Murmushi mamah tayi
“babu komai yaron nan ammah kai ɗin waye, kuma a ina kaga zahrah.”
“mamah Ni ɗa ne a wajen Cancellor sannan kuma na haɗu da Zahrah ne hanyar tafiyar ta zuwa gidan su Amira ƙawar ta”
Tun daga farko har kaita gidan su amirah da yayi ya labarta wa Mamah. Salallami ta fara
“shikenan Ita dai Zahrah ba zata taɓa sauya halin ta ba kenan, toh Allah dai ya shirya”

Murmushi yaya Ishaq yayi sannan ya matso cikin rumfar, gefen matackn da take ajiye soyayyiyar masa yayi sannan ya kwashe ledodin,, duk wanda yazo siya da kan shi yake zuba musu har lokacin maghrib yayi. Masallacin da ke cikin kasuwar yaje yayi Sallah ya dawo. A lokacin Mamah har ta gama haɗa kayan suyar ta zasu dawo gida.

Ƙarasawa yayi ya ce
“mamah a kwaso kayan sai mu tafi.”
Ƙasa musu mamah tayi kawai ta umarci Lauwali almajirin dake taimaka mata da su wuce. Har wajen motar suka nufa sannan ya jera kayayyakin suka wuce ɗiiiiiiiiiii sai gidan Kawu.

Mamah kam lumshe ido tayi yayin da zuciyar ta ta karye, tunanin when last tashiga mota take yi tun ranar da aka kawo ta gidan masoyin ta Abdulkarim Kuru. Lokacin da ta cire tsammanin wahala a rayuwar ta sai gashi yanzu ɗan uwan masoyin ta na gasa mata aya a hannu.

Suna isowa Lauwali ya ciro kayan ya shigar da su gida, abun mamaki lokacin dabar su Kawu babu kowa sai Aminu Aljan. Basu mishi magana ba suka kutsa cikin gidan. Bayan sun ajiye komai Mamah ta shimfiɗa wa yaya Ishaq sallaya ya zauna sannan ita ma taje tayi sallah.
Mutuniyar kuwa kwantawa taje tayi.

Har Mamah ta idar da Sallah bata ga giftawar Zahrah ba yasa ta ƙwala mata kira
“zahrah, Zahrah fito ki je ki siyo wa Ishaq ruwa gidan su Badi'ah.”
Zahrah da bacci ya ɗan fara kwashe ta ta turo baki gaba sannan ta fito. Mamah sake baki tayi tana kallon ta ganin ko Sallah bata yi ba. Harara ta ɗan yi mata sannan tace
“wuce kije kiyi sallah”

Juyawa Zahrah tayi tana ɓata fuska kamar wainar fulawa sannan taje tayi alwala don yin Sallah. Lauwali kuwa ya gama wanke kayayyakin kamar yadda ya saba yayi ma Mamah sai da safe. Yaya Ishaq ne ya ƙira shi bayan yazo ya zaro 5k a aljihun shi ya bashi.
Godia sosai Lauwali yayi sannan ya wuce.

Zahrah na idar da Sallah ta fito, gefen yaya Ishaq ta zauna sai wani tura baki gaba take yi kamar wani pipe😄.
Harara Mamah ta maka mata kafin ta ce
“tashi kije gidan su Badi'a ki siyo masa ruwa da lemo.. ba musu ta miƙe duk da cewa bata don zuwa gidan.

Badi'a Sa'ar ta ce ammah basa shiri ko kaɗan saboda yadda suke treating nata. Gaba ɗaya unguwar babu wanda ke kyautata musu inda ka cire gidan Cancellor sai kuma Ammin Badi'a, ita dai bata tsangwamar su ammah bata shiga sabgar su.

Bayan ta siyo ta kawo gaban shi ta ajiye, Mamah ta zubo mishi Masar a plate sannan ya fara ci ba tare da jin ƙyamar su ba. Ita ma Mamah tace tare da Zahrah.
Bayan sun gama ci yaya Ishaq ya sanar da Mamah ƙudurin shi na maida Zahrah private school da ke kusa da su. Mamah tayi farin ciki sosai har da kukan ta zai aikin godiya take rabza wa Ishaq, shi kuwa duk kunya ta cika shi.

Da haka yayi musu sallama ya wuce zuwa gida zuciyar shi wasai.

★★★★★
Sai wajen ƙarfe sha biyu na dare (12:00pm) Kawu ya dawo, su kuwa lokacin sun riga da sun rufe gidan. Bugawa yake ta yi babu ƙaƙƙautawa sai kututtuma ashar yake yi.
Sama sama mamah ta jiyo ƙarar buga ƙofa,, a zabure ta miƙe zuwa hanyar waje.

“dan abu ta kazar ubanki ki kizo ki buɗe min ƙofar nan inda ba haka ba in na shigo sai na lahira ya fiki jin daɗi.

Jinjina kan ta tayi kafin taa nufi ƙofar. Tana buɗe ƙofar ko ya banko ta har sai da ta buge kan Mamah. Layi ya shigo yana yi alamun yayi mankas abun shi.
Mamah kuwa cikin zuciyar ta tana Allah wadaran wannan miji nata.

Ƙunshi ledar hannun shi ya ya ƙara ƙanƙamewa kamar za'a ƙwace mishi daga hannun shi. A haka ya nufi ɗakin shi cikin tangaɗi har ya isa bakin ƙofa.. juyowa yayi ya kalli Mamah before ya shige ya na banko ƙofar.

Hawayen da ke zuba kan fuskar ta ta gode haɗi da wucewa nata ɗakin. Ba ita ta ta kwanta ba sai da ta yi alwala ta fara jera nafila tana roƙon Ubangiji ya kawo mata ɗauki.


_______________**********_______________


Ina kuke bayin Allah masu buƙata! Ina waɗanda ke cikin damuwa, ina waɗanda suke buƙatar neman wani zaɓi wurin Ubangiji.

Toh ga damah nan wacce take guarantee.


Manzon ALLAH صلي الله عليه وسلم yana cewa:- “idan dare ya wuce tsakiya ALLAH ( Subhanahu wata'ala ) yana sauƙowa zuwa saman duniya sai ya ringa cewa:- ( shin akwai mai neman gafara a gafarta masa ? ) yana ta fadar hakan har zuwa ketowar alfijir.

( saheeh musleem )


Saboda haka duk wata damuwa da kike da ita, don't hesitate to ask Allah, baya gajiya da amsa buƙatun bayin sa. Ki tashi kiyi sallah, koda raka'āt biyu ne sun wadatar ki roƙi Ubangiji kina mai yaƙini da shi, sai kiga ya amsa miki.

Kina cikin damuwa? Matsalar gidan aure ko kuma jarrabawar rayuwa, toh kada ki kuskura ki cire yaƙini a addu'a.

YA hayyu~ya~Qayyum!! Kayi gafara agaremu da iyayanmu da 'yan uwanmu da masoyan mu da sauran al'ummar musulmai.

KO YA ZATA KAYA?
WANE NE KAWU?ME ALAKAR SHI DA ZAHRA?, MEH YASA YAKE CUTAR DA ITA?
YA KUKE TUNANIN ZATA KAYA IDAN KAWU YA FAHIMCI CEWA WANI NA ƘOƘARIN TAIMAKAWA MAMAH?

AMSOSHIN KU NA NAN TAFe, BA A FARA LABARIN BA HAR SAI MUN JE BABBAN GIDA.

KU CI GABA DA KASANCE WA DA ALƘALAMIN DIAMOND LADY DOMIN NISHAƊANTUWA DA KUMA ILIMANTUWA.

COMMENTS ƊIN KU KAWAI NAKE SO DON SHINE ƙWARIN GUIWA TA
ALƘALAMIN DIAMOND LADY 💎🤟
Oum Zainab ce!

[19/09, 10:21 a.m.] 💎Diamond Bhatool 💎: ️______________★★★_______________
Typing 📲
🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡
_(All in a big family🏠)_
★TAKUN FARKO★
_[Labari/Rubutawa]_
*©Fadimatu Adamu Hassan*
*A.K.A DIAMOND BHATOOL*💎

_______________★★★________________

Chapter 3 · 0% Book details