Sashe 36
Zazzafar Kauna By Mhiz Innocent Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kiyi hak'uri ki dena kukan haka nan kin ji?" ya fad'a yana kallan ta
"In Sha Allah, zan yi k'ok'ari naga hakan ta kasance.." Umma ta fad'a tana sake goge idanun ta.
... Driving yake a nutse kamar koda yaushe, jefi jefi yana juyawa yana duban inda take a takure cikin hijab ko k'wak'wk'waran motsi ba tayi, bece mata komae ba dan baya so ya tado da rigima tun yanzun dan haka ya mata shiru a ran sa yana tunanin mafita. Tafiya me tsayi suka yi kafin suka fara shiga garin Kano, zuwa lokacin kam mamaki take bashi ganin har lokacin bata motsa ba, a hankali ya fesar da iska daga bakin sa sannan yaja motar ya gangara gefen titi ya kashe ta ya d'an jinginar da kan sa akan steering na tsawon sakanni kana ya d'ago kan nasa ya dubi inda take, seda ya lumshe idanun sa kafin a hankali yace
"Ayrah!!" beji ta amsa masa ba ko kuma ta d'ago har bayan wajen minti 1 sannan a hankali ya kae hannun sa kan hijab d'in nata ya d'an yi tapping nata, nan ma dae ba tayi motsi ba, seya ware manyan idanun sa akan ta sannan ya kae hannun sa a nutse gaba d'aya ya rik'o ta, se kuwa tayo baya zuwa jikin sa, k'irjin sa ya wani irin buga lokaci guda yana mamakin yadda yaji jikin ta yayi wani irin zafi daya wuce na k'a'ida, idanun sa akan kyakykyawar fuskar ta da tayi fayau kamar wadda tayi wata da watanni tana rashin lafiya, idanun ta a rufe suke, dogayen zara zaran eye lashes d'in ta sun kwanta sunyi luff akan idanun ta, a hankali ya sake bud'e bakin sa se dae yanzu a cunkushe ya furta
"Ayrah!!" nan ma dae ba tace komae ba, runtse idanun sa yayi yana jin wani abu me kama da tsoro na shigar sa
"Meya same ta?" ya tambayi kan sa, seya kae kunnen sa saetin dogon hancin ta da yayi ja kamar me mura, cikin lokaci k'ank'ani hucin numfashin da take fitarwa me zafi da kuma hucin zafin dake jikin ta ya sauka akan fuskar sa, seya sake lumshe idanun sa yana d'an tsayar da numfashin sa har lokacin cike da tsoro, cikin ikon Allah yaji numfashi kad'an na fita, be san sanda ya saki wata ajiyar zuciya ba sannan ya maeda ta kan kujerar ya kwantar kana ya tashi motar da gudun gaske ya wuce asibiti, sam gaba d'aya ma ya manta, haka zalika beyi tunanin komae ba ya wuce asibitin sa. Parking d'in motar sa yayi har lokacin bugun zuciyar sa be koma dae_dae ba, ya fito daga cikin motar cike da sassarfa wanda komae abin ka baka isa ka gane a yanayin da yake ciki ba, dan kuwa fuskar nan haka take babu yabo babu fallasa amma cikin zuciyar sa shi kad'ae yasan abinda yake ji, bud'e inda take kwance yayi beyi wata wata ba ya d'auke ta gaba d'ayan ta a hannun sa, sam be lura da kallan da en cikin asibitin ke bin sa dashi ba, yama manta abinda ya aekata haka ya wuce da ita cikin Office d'in sa, duk wad'anda ke kallan sa mamaki ne ya kamasu yadda suka ga Doctor Rk d'in da kan sa ya d'akko wata mace a hannun sa, nan take aka fara gulmammaki cikin asibitin, seda ya tsaya ya kar6i spare key d'in Office d'in sa dake ajje sannan ya wuce ya bud'e ya shiga har lokacin tana rik'e a hannun sa ya kwantar da ita kan gado.
.. Hannun ta har rawa yake yi ta d'auki wayar ta ta nemo number Abbu ta kira, babu jimawa Abbu ya amsa wayar
"Yalla6ae Doctor Rk ya shigo yanzun nan" daga inda Abbu yake ya saki ajiyar zuciya yana jin dad'i har cikin ran sa dan kuwa tun d'azun yake kiran layin Rk d'in amma se ace masa a kashe yake
"Ohk ina nan zuwa nan da 10 minutes" shine kawae abinda Abbu ya fad'a yana katse wayar sannan ya chanja akalar tafiyar tasa zuwa asibitin.
.. Kamar wanda aka jefo haka Abbu ya fad'o cikin asibitin, dae_dae lokacin da Rk ya fito daga cikin Office d'in sa, Abbu ya sake sauke ajiyar zuciya ganin d'an nasa, seya k'arasa kafin yace
"Raj!" muryar wanda yaji ne ta sanya k'irjin sa ya d'an buga sannan ya d'aga idanun sa ya kalli Abbun dake k'arasowa inda yake
"Ina ka shiga ne haka? Kasa hankalin mu duka ya tashi?" d'an yatsine fuska yayi lokaci guda kuma yana kae hannun sa kan sa sannan yace
"Amm... Abbu ina so ne nayi settling abubuwa da dama, bana buk'atar takura ne yasa na kashe waya ta, ina fatan dae ban yi laefi ba?" ya k'arasa maganar yana kallan Abbun
"Ohk tohm muje cikin Office d'in akwae maganar gaggawa da nake so muyi" be san sanda yayi gaba ba yana tarewa Abbu k'ofar shiga Office d'in ba sannan yayi wani murmushin yak'e yace
"Abbu pls.."
"Shikenan, kayi k'ok'arin gamawa, koma dae baka gama ba ka tabbatar ka dawo gida dan akwae muhimmiyar maganar da zamu yi bamu da ishashshen lokaci" Abbu ya fad'a yana d'an nazarin d'an nasa, ganin yanda idanun sa suka d'an tasa kamar wanda baya samun bacci, se kuma daya tuna yanzu yake fad'a masa aeki ne ya rik'e shi sannan ya d'an ji dama dama
"In Sha Allah" shine abinda Rk ya fad'a yana d'an kaucewa kallan da Abbun ke masa, dan gani yake kamar yana kallan k'wayar idanun sa ze karanto rashin gaskiyar dake tattare da shi
"Allah ya yadda" Abbu ya fad'a yana juyawa daga wajen, se a lokacin Rk ya saki ajiyar zuciya yana lumshe idanun sa, se yanzu ya gane shirmen daya aekata na zuwa da ita asibitin nan, me ya shiga kan sa ya kawo ta nan d'in? Hannu ya saka ya bud'e Office d'in ya shiga sannan ya kulle, idanun sa akan ta lokacin da idanun ta ke a rufe tana sauke numfashi a wahalce, daga yanayin yanda ta 6ata rae kawae zaka fahimci ba dad'in baccin take ji ba, ga kuma yanda ta d'an tura red lips d'in ta gaba kamar me shirin yin kuka, seya samu kan sa da lumshe idanu na tsawon second 10 sannan ya bud'e ya k'arasa bakin gadon bayan yaja wata kujera ya zauna, duk da yanda take sake had'e jikin ta waje d'aya hakan be hana gumi tsatstsafowa daga fuskar ta ba, ya sake sauke idanun sa kan fuskar ta sannan ya maeda kan jikin ta da har lokacin ke d'auke da hijab, a hankali ya kae hannun sa kan hijab d'in, kamar me tunanin wani abun ya dakata da hannun sa a sak'ale, ya kae wajen second 30 a hakan sannan ya k'arasar da hannun nasa zuwa kan hijab d'in nata ya fara janye shi sama, be sake shi seda yazo dab da fuskar ta, se a lokacin kuma ya fara tunanin yanda ze cire shi daga wajen fuskar ta dan baya so ya tashe ta dan kuwa be shiryawa abinda ze fad'a mata ba, be kuma shiryawa rigimar ta ba, a hankali ya d'an mik'e tsaye sannan ya rank'wafa ya kae hannun sa k'asan kan ta da nufin d'ago kan nata, dae_dae lokacin data bud'e idanun ta da suka mata nauyi, se rumfar mutum kawae ta gani a kan ta, duk da yanda kan ta ke cigaba da mata ciwo hakan be hana ta sake ware idanun ta ba, duk da bata fahimci menene ba amma ta tsorata matuk'a dan haka bata san sanda ta mik'e zaune ba tana sakin k'ara, lumshe idanun sa yayi yana jin k'arar ta ta har cikin jikin sa, sanda ya ida bud'e idanun sa se nata idanun suka sauka cikin nasa, cikin wata rud'ewar ta saki k'ara tana yin baya gami da sake jan hijab d'in ta ta lullu6e kafatanin jikin ta tana sakin kuka kamar wadda aka daka, lokaci d'aya kuma jikin ta na cigaba da rawa, runtse idanun sa yayi saboda yadda yaji kan sa ya sara da k'arar da tayi har sau biyu, ya d'an dafe kan sa sannan ya bud'e idanun sa ya sauke su a kan ta lokacin da take cigaba da mak'urewa a jikin bango hannun ta rik'e da hijab d'in ta kamar zata maeda shi cikin ta, cikin karyayyiyar murya me had'e da kuka ta furta
"Ina takadda ta? Meyasa baka maeda ni gidan mu ba?" tayi maganar sanda wasu hawaye masu d'umi suka samu damar zubowa akan kuncin ta, idanun sa yayi saurin janyewa daga cikin nata narkakkun idanun dake zubar da hawaye kamar an kunna famfo haka kuma sun cika taff da hawaye duk da wad'anda ke zuba, baya so tun yanzu raunin ta yaci galaba a kan sa dan haka ya d'an runtse idanun sa sannan ya bud'e su, ya d'auke su ya aza su a kan ta sanda ta cigaba da mutsu mutsu akan gadon tana cigaba da kukan ta
"Me kike ci na baka na zuba Madam? Ae har yanzu yinin be k'are ba!" ya fad'a yana sakin wani miskilin murmushi..
Mhiz Innocent.....✍️
https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd
*CHAPTER TWO*
*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*
*FREE BOOK*
Page 033
___Ganin da yayi tana cigaba da bin sa da kallan tuhuma lokaci guda kuma tana sake kwa6e fuskar alamar koda yaushe zata iya sakin kuka ya sanya shi sake lumshe idanun sa sannan a hankali ya d'aga hannun sa dake d'auke da wani had'ad'd'en agogo ya juya mata dashi dan ta gani, bin hannun tayi da kallo dan fahimtar abinda yake nufi da hakan