← Book details Zazzafar Kauna By Mhiz Innocent Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 52

Sashe 18

Zazzafar Kauna By Mhiz Innocent Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na'am, ehh haka ya kamata muyi kam.." daga haka basu sake cewa komae ba suka yi shiru se dae kowa da abinda yake sak'awa a cikin ransa. A hankali ta k'arasa bakin gadon ta chanja hijab d'in jikin ta da wani sannan ta kalle su su duka tace har lokacin fuskar ta ba yabo ba fallasa

"Zan d'an je na dawo" ta fad'a tana shirin ficewa daga d'akin, mik'ewa Jidda tayi tace bayan ta d'auki mayafin ta

"Muje na raka ki.." kamar tace ta barshi se kuma taga kamar hakan be dace ba dan haka seta dakata ta jira Jiddan har ta k'araso inda take suka fita tare. Ba laefi yanzu suna tafiyar suna d'an ta6a hira, hirar da se Jidda ta d'auko ta sannan Ayrah kan amsa mata har zuwa sanda Jiddan tace

"Ina zamu je wae?"

"Mango zan siyo.." harara Jidda ta jefa mata sannan tace

"Amma shine baki fad'a min ba, toh ae mun wuce wajen masu siyarwar"

"Aou mantawa nayi" ta fad'a tana dariya gami da sanya hannun ta akan bakin ta, daga haka suka juya Jidda ta kae su wajen da masu saeda fruits suke sosae, kae tsaye wajen me mango d'in suka je, Ayrah ta fad'a masa adadin data ke so, shi kuma ya fara zuba mata cikin leda. A hankali wata bak'ar had'ad'd'iyar mota ta gangara ta tsaya kusa da me siyar da mangon, su biyu ne cikin motar Rk zaune a wajen me zaman banza yana danna waya, yayin da Yaseer ke driving, kallan sa yayi sanda yaga yayi parking motar a wani waje daban, da mamaki yace

"A'ah meye haka?" Yaseer yace

"Fruit zan d'an siya, sun min kyau gaskiya.."

"Oh god, ji wani kuma" Rk ya fad'a yana watsa masa harara, Yaseer yace

"5 min pls.." ya fad'a sanda yake bud'e motar yana kuma d'aga hannun sa, Rk bece komae ba se d'aga kafad'a da yayi gami da ta6e baki lokaci d'aya yana maeda kansa kan wayar sa, wajen minti 2 da fitar Yaseer d'in, a hankali ya d'aga manyan idanun sa ya kalli wajen, acan ya hango shi tsaye wajen me siyar da mango yana ta zuba shi da me mangoron, seya samu kansa da jan tsaki gami da furta

"Yaseer!!" ya fad'a yana shirin d'auke kansa idanun sa suka sauka akan fuskar ta sanda wani sassanya kuma kyakykyawan murmushi yake tashi akan fuskar ta wanda ya matuk'ar k'awata kuma ya sake fito da aenahin kyawun ta, cikin en sekonnin da basu wuce 2 ba yaji yanayin bugun zuciyar sa ya sauya wanda har be san sanda ya rintse idanun sa ba yana sanya hannun sa saetin zuciyar sa, seya maeda kansa jikin kujera yana sake lumshe idanun sa kafin a hankali ya fesar da wata iska daga bakin sa

"What happen to me?" he asked him self still dae idanun sa suna a lumshe haka zalika hannun sa dafe da k'irjin sa, yafi minti 2 a haka kafin bugun numfashin sa ya fara komawa dae_dae, dae_dae lokacin kuma da Yaseer ya bud'e murfin motar ya shigo, da mamaki ya kalli Rk da har lokacin be bud'e idanun sa ba yace

"Rk.. Lafiya?" se a lokacin ya shiga bud'e idanun sa dake d'auke da dogayen bak'in gashin idanu masu matuk'ar kyau sannan ya sauke su kan Yaseer yace muryar sa a d'an ciki

"Babu komae.."

"Sure?" seya jinjina masa kae kawae yana sake lumshe ido, shi kansa ba zece ga dalilin da yasa yaji bugun zuciyar sa ya chanja tafarar d'aya ba

"Ohk.." Yaseer ya fad'a yana kunna motar ya fara driving, seda suka yi nisa da fara tafiyar sannan Yaseer ya kalli Rk kana ya maeda duban sa kan titi yace

"Ina tunanin gobe zan koma Kano fa.."

"Saboda?" Rk ya fad'a bayan ya d'an kalle shi

"Madam ta matsa wallahi, ni kuma bansan 6acin ran ta, so dole na koma a goben gaskiya" murmushi Rk yayi wanda ya sake fito da aenahin kyansa kana yace bayan yaja k'aramin tsaki

"Idan ba kayi haka ba ae bazan gane kae ne ba"

"Me kuma nayi?" Yaseer ya fad'a yana dariya, shiru Rk ya masa dan yasan dama da biyu yayi maganar

"Mutumi na kae ma ka daure kayi auren nan wallahi.." kafin ya kae ga k'arasawa Rk yace

"Bismilllahi.., pls wae kae baka gajiya da zancen nan ne? Ka dae san bazan k'ara shekarun da nayi a baya ba tare da nayi aure ba koh?"

"Yawwah mutumi na yanzu kace dae na fara shiri kenan?" Yaseer ya fad'a duk da yayi mamakin jin zancen Rk d'in

"Kamar haka kake so na fad'a koh? Toh ae gashi nan na fad'a maka" Rk yayi maganar cikin basarwa, tsaki Yaseer ya ja yana fad'in k'asa_k'asa

"Ae seka yi ta zama" duk da ya ji shi amma bece masa komae ba ya cigaba da danna wayar sa..

.... Da sallama ya shiga cikin parlourn, Mummy dake zaune kan kujera ta taso tana fad'in

"Sannu da zuwa likita, ka dawo lafiya?" murmushi yayi kana yace

"Lafiya k'alau Mummy, Daddy fa?"

"Be shigo ba tukunnah" seya jinjina kae kawae, can ya jiyo Mummyn na fad'in

"Ka dad'e da shigowa ne?" d'an ta6e baki yayi kana yace bayan ya girgiza kae

"Nop, ban wuce 1 hour ba.."

"Ohk bari Muneerat ta kawo maka abinci yanzun nan" seya d'an yi shiru kad'an, baya son Mummyn ta dinga had'a harkar sa da yarinyar ballantana har suyi tunanin wani abun, se dae 'ya 'ya ce, ko yaya ya nuna baya son hakan yasan ba zata ji dad'i ba, so ko dan kulawar Mummyn a gare shi ya sanya ya dinga d'auke kae akan wasu abubuwan, dan haka bece komae ba ya wuce dinning area, ya ja kujera ya zauna bayan ya ciro wayar sa daga cikin aljihu ya fara dannawa. Wajen mintuna 10 da zaman nasa, wata madaedaeciyar budurwa er kimanin shekaru 22 ta fito daga cikin kitchen sanye cikin riga da skirt na atamfa wanda suka yi cif cif a jikin ta, se dae kasancewar haka take a tsaye yasa kayan basu wani mata kyau ba sun dae yi mata cas cas kamar a jikin ta aka d'inka, daga fuska babu laefi tana da nata kyan dae_dae misali, bak'a ce se dae ba can ba, amma saboda man da take shafawa yasa fuskar ta ta ta fito tayi haske sosae kuma take wani irin shek'i, sannan kuma doguwa ce babu laefi, kan ta babu d'an kwali se wata hula data saka ta zame ta har wajen rabin kan ta, wanda ya fito da kusan rabin kitson attach d'in dake kan ta, a hankali ta k'arasa ta ajje cooler data d'auko sannan ta koma ta kwaso ragowar kana ta dawo taja kujera ta zauna tana kallan sa cike da matsananciyar k'aunar sa tace

"Sannu da zuwa Yaya na" se a lokacin ma shi yasan da wanzuwar ta a wajen, ya d'an d'aga kan sa ya kalle ta da kyawawan manyan idanun sa sannan ya d'auke, seta lumshe idanun ta tana jin idanun nasa kamar wani abu ne a cikin su wanda ya sanya bata iya jure kallan cikin k'wayar idanun sa, sosae taji dad'in yadda ya kalle tan, kafin ta dawo daga wannan kuma taji yace

"Yawwah barka.." seta sake yin murmushi tana janyo plate ta fara serving nasa, Mummy da fitowar ta kenan daga d'aki ta kalli Muneerat dake zuba masa abinci cikin plate da gasken gaske, seta girgiza kae a ranta tana raya "Lallae soyayya me chanja mutum" dan kuwa tasan halin k'wuiwa irin na d'iyar ta ta, bata aekin komae cikin gida, koda abinci ne kuwa se dae a kawo mata idan an kawo kuma a zuba mata, ina ganin da da dama ma cewa zata yi a bata a baki. Plate d'in ta tura gaban sa sanda ta gama zuba komae a muhallin sa sannan ta koma kan kujerar tana fad'in

"Bismilllah Yaya na" seya ajje wayar sa a gefen sa, sannan yaja plate d'in a hankali yace

"Thank u" wani irin farr tayi da idanu tana jin dad'i mara misaltuwa, ko ba komae tasan tayi abin kirki tunda gashi wanda tayi dan shi d'in har godiya ya mata, zata so ace kuma wannan kwalliyar ma ya kalla yace tayi kyau da tafi kowa farin ciki, se dae tasan kafin ma ya kalle tan abu ne me wuya ballantana yace tayi kyau, wayar sa daya ajje tabi da kallo sanda ta kawo wani haske, tana jin kamar ta janyo wayar ta duba wani abu amma se dae ba zata iya ba musamman daya kasance idanun sa na wajen, se kawae ta cigaba da kallan had'ad'd'iyar wallpaper wayar tasa dake d'auke da tambarin "A" wanda ita har yanzu tayi tunanin ta fad'ad'a k'wak'walwar ta amma ta gaza gane abinda yake nufi da hakan

"Uhmm Yaya na ya d'alibae?" tayi k'arfin halin fad'in hakan dan katse shirun daya wanzu a wajen na wasu mintuna dan tasan ko da zata shekara ba tace komae ba, shi shirun baze dame shi ba balle yace wani abun, d'an ta6e baki yayi gami da yamutsa fuska ta d'auka ma ba zece komae ba se kuma taji yace

"Alhamdulillah, baza kiyi karatu bane?" yayi maganar sanda ya ajje spoon cikin plate d'in, bata bawa maganar daya fad'a muhimmaci ba seta kalli abincin daya keci da kallo sannan ta kalle shi sanda yake k'ok'arin mik'ewa tace

"Wae har ka gama?" ta fad'a itama bayan ta mik'e tsaye cikin maraeraece fuska, sake yamutsa fuska yayi kana yace

"Ehh, dama ba yunwa nake ji ba, kije kiyi karatun ki" ya fad'a yana d'aukar wayar sa, seta bishi da kallo sanda yake wucewa har ya fice daga d'akin, komawa tayi ta zauna tana jin yadda wasu k'walla suka tarar mata a ido, dae_dae lokacin Mummy ta k'araso taja kujera ta zauna tana kallan ta tace

"Muneerah meya faru?" seta d'ago idanun ta ta kalli Mummyn sannan tace

"Mummy kinga fa abinda yaci, kamar dan ina wajen ne fa yak'i ci da yawa fa"

"Ke waye ya fad'a miki haka Muneerah?" Mummy ta fad'a tana kallan ta, seta sake maraeraece fuska sannan tace kamar zata sanya kuka

"Toh Mummy se yaushe ne zamu saba, har yanzu kullum jiya i yau" ajiyar zuciya Mummy ta sauke sannan tace
Chapter 18 · 0% Book details