← Book details Zazzafar Kauna By Mhiz Innocent Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 52

Sashe 30

Zazzafar Kauna By Mhiz Innocent Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

... Driving yake yi amma har lokacin tunani yak'i barin ruhi da k'wak'walwar sa, shi likita ne yasan illar da tunani kan iya haefarwa dan ya kan sha bawa mutane shawara akan hakan, amma a wannan karon shi kan sa ya kasa hana kan sa, se yanzu ya fahimci ashe idan k'wak'walwa na son yin tunani ba mutum ke tsarawa kan sa yin tunanin ba ita da kan ta take yin tunanin kuma babu yadda ka isa kayi da ita. A haka dae har ya k'arasa unguwar ta su yana tuna kwatancen data masa, a d'an nesa kad'an ya tsaya da gidan yana kallan cikin layin da babu kowa kasancewar safiya ce dan kuwa har lokacin ko 8 ba tayi ba, seya d'aga lumsassun idanun sa dake d'auke da bacci ya dubi gidan a ran sa yana sak'a tabbas nan d'in ne in dae yabi kwatancen data masa dae_dae, wayar sa ya janyo da take ajje kan kujerar kusa dashi ya danno number ta cike da fatan ta d'aga wayar, se dae addu'ar sa bata kar6u ba dan kuwa har ta gama ringing d'in bata d'auka ba tana kuma jin wayar na ringing ta san me kiran shiyasa tak'i kula wayar, wani kiran ne ya sake shigowa seta mik'e daga kwanciyar da take tana ganin blocking d'in da tayi niyyar yi tun d'azun shine kawae mafitar da tasan idan tayi ze dena kiran ta, kafin takae ga aekata abinda tayi niyya Umma ta d'aga labulen d'akin ta lek'o

"Ayrah ki fito ki samu wani abun ki ci" se ta d'aga kae da sauri sannan ta furta

"Toh.." kawae, itama Umman bata takura ba dan tana so ne ta bari ta gama kukan ta sannan ta rarrashe ta, idan ba haka ba tasan yanzu tunzura ta kawae zata yi, Umman na fita Ayrah ta maeda kallan ta kan wayar dae_dae lokacin da wani sak'o ya shigo cikin wayar, seta dakata ta shiga cikin sak'on, gajeren sak'o ne daga number Rk a hankali ta shiga karantawa

"Don Allah ki fito ina k'ofar gidan ku, inaso naji tabbacin maganar dake fitowa daga cikin bakin ki, ina so na tabbatar da abinda kunnuwa na suke ji" fuskar ta a matuk'ar tamke haka zalika ran ta ya sake 6aci, tana ga lokaci yayi da zata kira shi da sunan dake ta yawo a cikin k'wak'walwar ta koda hakan zesa ya fahimci ta gane wanene shi da mahaefin sa, ko kuwa ya d'auka saboda son da take masa zata iya fatali da umarnin iyayen ta? Ko kuwa me yake nufi da ita?

"Butulu" shine sunan dake ta yawo a k'wak'walwar ta, wayar ta ta ta d'auka ta danna number sa a blocking sannan ta jefar da ita gefe ta mik'e tana sanye cikin doguwar rigar atamfa ta zari hijab ta saka sannan ta lek'o tsakar gidan tana hange, babu kowa a tsakar gidan taji dad'in hakan dan bata so ta sake 6atawa Abba ko Umma rae daga dawowar ta jiya bayan 6acin ran data saka musu a jiyan, a hankali ta shiga takawa cikin tsakar gidan har zuwa sanda ta fice daga cikin gidan...

... Wanda ke driving d'in ya kalli Muttala yace

"Nifa na gaji wallahi, tun jiya muke a wajen nan amma har yanzu banga alamar zata fito ba" tsaki Muttala yaja kana yace

"Gaggawar ta menene? Wallahi idan ta nine bank'i mu sake kwana cikin motar nan ba tunda dae babu wanda ya ganmu har yanzun" Muttala ya fad'a har lokacin idanun sa na kan k'ofar gidan su Ayrah.. A dae_dae lokacin ne Ayrah ta fito daga cikin gidan, a hankali ta shiga bud'e manyan idanun ta dan hango inda motar sa take. A lokacin ne shi kuma kiran Abbu ya shigo wayar sa, seya d'auki wayar yana karawa a kunnen sa idanun sa a lumshe dan yanzu kuma be san da wanne Abbun yazo ba gashi kuma rok'on da yayi wa Ayrah baya tunanin taji ta kar6a zata fito, se abin ya sake masa yawa, daga can 6angaren Abbu yace

"Ka shiga asibitin ne?" shiru yayi na d'an wani lokaci kafin a hankali ya bud'e bakin sa bayan ya kae hannu ya shafa kwantaccen sajen dake kwance luff luff akan fuskar sa

"Abbu ban shiga ba tukunna" shiru Abbu yayi yana sake karanto yanayin Rk d'in daga cikin muryar sa, yace a hankali

"Ko dae akan maganar dana maka jiya ce?" shiru yayi dan ko ya bud'e bakin sama be san abinda zece ba, Abbu yace

"Toh ka bud'e kunnen ka da kyau kaji, in dae akan maganar nan ce ka kwantar da hankalin ka kamar an riga an d'aura muku aure ne da Muneerah, dan haka ina ganin ka ajje komae a gefe ka koma bakin aekin ka" kafin yace komae Abbun ya katse wayar, seya jefar da wayar yana sake jin yadda yanayin nasa yake sake ta'azzara, abubuwa na neman yiwa zuciya da k'wak'walwar sa yawa. A hankali ta cigaba da takawa har lokacin fuskar ta babu walwala manyan fararen idanun nan nata sun yi zuru zuru kamar mara lafiya, da sauri wanda ke driving cikin motar ya bud'e k'ofa ya fita yayin da Muttala ya koma mazaunin driver, seda ya kalli cikin layin ya tabbatar babu kowa sannan ya k'arasa inda Ayrah take, ita sam hankalin ta be kae kan sa ba yana kan motar Rk da take kalla dan tabbatar da tasan ce, beyi wata wata ba ya matsa bayan ta ya shak'a mata wani abu dake jikin handkerchief d'in hannun sa, lumshe idanun ta tayi tana jin wani irin yanayi cikin kan ta kafin a hankali ta kae hannun ta tana shirin dafe kan ta, take wani jiri ya d'ebe ta cikin sakannin da basu wuce 10 ba ta fice a hayyacin ta se kawae tayi baya zata fad'i mutumin ya saka hannun sa ya tare ta ya jata zuwa cikin motar har lokacin yana d'an juyawa bayan sa dan tabbatar da babu wanda ya gan shi, dae_dae lokacin da yake k'ok'arin k'arasa shigewa da ita cikin motar Rk ya bud'e idanun sa daga lumshe sun da yayi tun d'azun, kamar ance ya kalli wajen se kawae ya hange ta jikin wani mutum yana cusa ta cikin mota, seya sake rufe idon ya bud'e dan tabbatar da abinda ya gani d'in gaskiya ne ko kuwa idanun sa ke masa gizo, cikin wani irin zafin nama ya tura k'ofar side d'in da yake yana shirin fita zuciyar sa na wani irin zafi tana cigaba da harbawa kamar zata faso k'irjin sa, Muttala yaja motar da k'arfin gaske tun kafin ma mutumin ya gama saka Ayrahn cikin motar, seya koma da sauri zuciyar sa na bugawa yama kasa tunanin komae kawae ya figi motar da wani irin gudun da tunda yake ze iya cewa be ta6a yin irin sa ba, sosae su Muttala suke gudu kamar zasu tashi sama yayin da shima ya cigaba da bin su, kawae burin sa ya san inda zasu je, ina zasu kae ta? Me zasu mata? Meyasa suka d'auke ta? Kwata kwata tunanin sa be kae ya kira police ya sanar dasu ba kawae shi dae burin sa ya cim masu. Sosae suka cigaba da tafiya kuma inda Allah ya taemake su kwata kwata basu samu traffic jam ba, mamaki ya sake kama shi ganin se tafiya suke yi kamar baza su dena ba, har lokacin kuma bugun da zuciyar sa take be ragu ba, haka ya cigaba da bin su zuwa lokacin da yaga sun fara barin gari suna shiga cikin wani waje daya fi masa kama da k'auye, mamaki ya sake kama shi amma da yake baya so su gane akwae wanda ke bin su seya dakata har zuwa sanda suka masa nisa sannan ya cigaba da bin su a nutse yana yi yana lumshe idanun sa saboda yadda yake jin jikin sa ya masa wani iri ga yadda bugun zuciyar sa ke ta k'aruwa. Dae-dae wani madaedaecin gida ya hango su sun yi parking d'in motar su, ze iya cewa tunda suka shigo k'auyen bega gida me kyan sa ba dan kuwa duk gidajen k'asa ne yayin da wannan d'in ya kasance ginin bulo ne, Muttala ya fita ya bud'e k'ofar gidan da mukullin hannun sa sannan ya dawo ya tashi motar zuwa cikin gidan kana ya saka mukulli jikin gate d'in sannan ya sauke ajiyar zuciya

"Da alama mun tsira fa" ya fad'a yana fesar da iska daga bakin sa, mutumin da shima ya fito daga cikin motar yace

"Wallahi kuwa, kayi maza ka kira mana Alhaji ka sanar dashi mun gama aekin mu" murmushi Muttala yayi kana ya fito da wayar sa ya lalubo number Alhaji Mato, tun kafin Alhaji Mato yace komae Muttala yace

"Yalla6ae albishirin ka?" daga inda Alhaji Mato yake ya saki wani murmushin jin dad'i yana shafa tumbin sa, ko Muttalan be fad'a ba yasan sun yi nasara, amma saboda ya sake tabbatar wa ya sanya shi fad'in

"Goro.."

"Mun gama aekin mu, yanzu haka gamu a cikin gidan yalla6ae"

"Weldone, ku jira ni yanzu zan taho.." Alhaji Mato ya fad'a yana jin wani irin dad'i na ratsa shi, yasan tabbas yau d'in Ayrah zata kwana ne a matsayin matar sa, baya shakkar wannan tunda dae an riga da an samo masa ita.
Chapter 30 · 0% Book details