← Book details Zazzafar Kauna By Mhiz Innocent Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 52

Sashe 16

Zazzafar Kauna By Mhiz Innocent Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ayrah mun yi gaba, kiyi sauri ki shirya ki taho kafin 8 tayi" Ruks ta fad'a sanda take d'aukar jakar ta, jinjina kae kawae tayi ba tare da ta sake cewa komae ba, ta bisu da kallo sanda suke ficewa daga d'akin. A hankali ta mik'e ta sake fad'awa toilet ta wanko fuskar ta sannan ta fito ta shirya cikin riga da skirt na atamfa kana ta saka hijab, ta d'auki sabuwar jakar da Yah Sadeeq ya siya mata wadda ta zuba littafan ta a ciki ta fito daga d'akin. A hankali take takawa a cikin filin makarantar cikin nutsuwar ta, duk da babu abinda ta shafa akan fuskar ta amma tayi kyau sosae, bayan ta d'auke da jakar goyo yayin da ta rungume wasu text books guda 2 wanda suma duk Yah Sadeeq ne ya siya mata saboda ta samu sauk'in karatu. Tun kafin ta k'arasa inda ze sada ta da ajin nasu taji shiru kamar babu mutane cikin ajin, har seda ta fara tantamar anya kuwa ba tayi 6atan kae ba?, dab da zata isa wajen ajin sassanya kuma daddad'ar muryar sa ce ta fara dakar mata kunnen ta, ba'a iya jiyo abinda yake fad'a d'in amma tana iya jiyo sautin yadda nutsatstsiyar muryar tasa ke fita, haka kurum taji k'irjin ta ya buga da wani irin k'arfi har seda ta dakata daga inda take tafe na wasu en mintuna kafin ta lumshe manyan idanun ta kana ta bud'e su tana mamakin yadda bugun zuciyar ta ya sauya cikin k'ank'anin lokaci. Da sallama akan la66an ta ta sanya k'afa cikin ajin nasu ba tare data kalli kowa ba, dan bata jin zata iya kallan kafatanin en ajin dan tasan duk idanun su na kanta ne

"Hey!" nutsatstsiya, sanyayyiya kuma daddad'ar muryar sa me dad'in saurara ta daki dodon kunnen ta, a take kuma a lokaci guda k'afar ta ta d'auki rawa wanda har yanzun ta kasa gane dalilin wannan rawar da jikin nata ke yi

"Ko dae da ita ake?" ta tambayi kan ta, gudun kada taje tayi laefi ya sanya ta dakatawa daga inda take, a hankali kuma ta shiga juyowa zuwa inda yake tsaye sannan ta d'aga raunannun idanun ta ta aza su inda ta tabbatar yana tsaye, ba ita yake kalla ba idanun sa na kan wani littafi dake gaban sa ne, kyakykyawa ajin farko, fari me kyakykyawan jiki kuma cikin kyakykyawar shiga, sanye yake cikin wasu riga da wando da suka dace da k'irar jikin sa, a saman kayan kuma suit ce itama me kyau, kansa babu komae se kwantacciyar bak'ar suma da tasha gyara na musamman, kamar yadda take a gyare haka kyakykyawan bak'in sajen sa ma yake a gyare kuma a kwance wanda hakan ba k'aramin k'arawa kyakykyawar fuskar sa kyau yayi ba, ganin da tayi ba ita yake kalla ba dan ita kanta bata ganin fuskar sa se gefen fuskar ta sa, seta d'an lumshe idanun ta kafin a hankali ta fara k'ok'arin juyawa

"Hey, go out!" ya sake fad'a har lokacin be kalle ta ba, kawae se tayi shahada ta tabbatar da ita yake, har lokacin bata kalli kowa ba taja k'afafun ta ta fice daga ajin. Kae tsaye hostel ta koma har lokacin tana tuna sautin muryar sa a cikin kwanyar ta sannan kuma tana hana k'wallar data tarar mata a idanu zubowa, tana shiga ta ajjiye jakar ta ta haye kan gadon ta jinginar da kanta a jikin gado, iska ta fesar daga cikin bakin ta tana d'an jan numfashi kafin ta sanya hannu ta goge hawayen da suka fara sakkowa akan fuskar ta, a hankali ta cigaba da jan sheshshek'a tana jin wani irin zafi wanda da farko bata ji shi ba se yanzun, ta tsani yarfi, ta tsani dizgi, se gashi her first day in University wani yayi embarrassing na ta a baenar nasi, d'an mitsitsin bakin ta ta murgud'a kamar wani na kallan ta sannan tace akan la66an ta

"Bashi da kirki". Tafi awa 1 a cikin hostel d'in seda ta kitanci lokacin da tasan ya fita sannan ta mik'e ta fita zuwa ajin nasu, cikin sa'a kuwa babu kowa cikin ajin a lokacin, se students kawae da kowa ke harkar gaban sa, koda ta shiga cikin ajin duk seta ji ta a takure musamman da taji a jikin ta idanun mutane da dama na yawo ne a kan ta, se take ganin kamar kowa kallan ta yake da wadda aka kora d'azu, duk se ta ji tana neman sark'ewa a tafiyar da take, gaba d'aya ma ta rasa inda za taje ta zauna, tsintsiyar hannun ta taji an kama se ta juya da sauri ta d'aga idanun ta ta kalli wadda ta rik'e mata hannun, Jidda ce, seta sauke ajiyar zuciya hadda lumshe idanun ta tana bud'ewa lokaci guda

"Muje ki zauna" Jiddan ta fad'a tana cigaba da jan ta zuwa cikin ajin, babu musu kuwa kamar wata doluwa ta bita cike da sassarfa, wani dake zaune kan wani bench yace yana kallan Jidda

"Hajiya Jidda an samu wata kenan?" seta juya ta watsa masa harara sannan tace

"Shishshigi ba kwarjini" dariya yayi hadda dukan bench yace bayan ta wuce wajen

"Yoh shishshigi kuma ya kae wanda kika yi?" ita dae bama taji shi ba suka k'arasa inda suke zaune sannan tace tana Kallan Ayrah

"Yawwah ki zauna, nan ne kusan permanent seat namu dan tunda muka zo anan muke zama" murmushin yak'e Ayrah tayi dan har ga Allah wajen be mata ba, dan kuwa a baya ne bench d'in nasu yake, se dae ta nemi waje ta zauna kawae.

Basu suka koma hostel ba a ranar se wajen k'arfe 6, dan haka suna komawa Ayrah ce ta fara fad'awa toilet tayi wanka dan sosae ta gaji tana fitowa ta zira doguwar riga mara nauyi ta maeda hijab d'in ta tayi sallah kana ta nemi waje ta zauna still dae da hijab d'in , dan haka kawae tunda tazo d'in tafi jin ta comfortable idan ta saka hijab d'in.

"Toh mu dae kinga had'a girkin mu muke, kawae kowaccen mu zata kawo abincin tane duk abinda muke so se mu dafa muci, kema ayi hakan dake?" Ruks ce me maganar tana kallan Ayrah, seda ta d'an yi jimm, saboda haka kawae taji basu wani kwanta mata can ba musamman daya kasance hirar su gaba d'aya rabin ta ta samari ce, tun jiyan kuma da tazo ba taji wata a cikin su tayi maganar karatu ba, amma kuma suna da kirki yadda suka tarbetan kawae ma ya mata dad'i dan haka se tace

"Tohm.."

"Ohk guys..me zamu dafa?" Ruks ta fad'a tana kallan su su duka, ta6e baki Jidda tayi kana tace

"Kawae mu dafa indomie, dan ni yunwa nake ji"

"Nima dae kam" Bahijja ta fad'a itama, mik'ewa Ruks tayi ta nufi inda kayan abincin nasu ke ajiye cikin d'an k'ank'anin lokaci ta d'ora musu Indomien, sanda take zuba Maggi a ciki ne ta jiyo muryar Jidda na fad'in

"Ke ni tun d'azu nake so mu tattauna akan shigar Doctor RK ta yau, amma wannan Abeedar ta mana k'erere, don Allah befi wancan satin kyau ba?" ajiye maggin hannun ta Ruks tayi sannan ta juyo tana rik'e ha6a kana tace tana murmushi

"Umhum wallahi ke kam ki bari kawae.., shi fa kowacce shiga yayi naga alama kyau take masa, wallahi guy d'in ya had'u iya had'uwa" ta fad'a tana jan baki kamar wadda taci abu me yaji, daga nan fa hirar tasu ta soma, maganar tasan nan dae da kullum ita suke yau ma dae ta san suke, da alama basa gajiya da hirar tasa kamar wani abinci

"Wae Bahijja meye haka naji kinyi shiru?" Jidda ta fad'a tana jefa mata harara, seta yamutse fuska kana tace

"Ke kam ki bari kawae, kae na ke ciwo" itama tayi maganar tana yamutse ta ta fuskar

"Toh Allah ya sawwak'e.. Ayrah ki sauko muci abinci" Ruks ta fad'a tana kallan Ayrah dake kwance kamar me bacci, se a lokacin ta tashi dan daga inda take zaune tun d'azu ji take kamar ta tashi ta musu duka, tana jin kamar tace musu sun ishe ta da maganar wannan mugun mutumin, haka dae ta mik'e ta sauko suka ci abincin.

...... Washe_gari k'arfe 7:40 dukan su suka gama shiryawa har da Ayrah, yau ma cikin hijab d'in dae ta shirya kamar jiyan, suka fito tare suna tafiya su Jidda na hira yayin da ita dae tayi shiru kawae, a dae_dae inda ze sada su da ajin nasu dukkan su suka ji wata murya na fad'in

"Ayrah Ibraheem Khaleel.." kusan a tare dukan su suka juya, se duk suka tsaya suna kallan mutumin daya kira sunan nata kafin suka kalli Ayrah, itama da kallan rashin sani take bin sa dan tunda take bata ta6a ganin fuskar ba

"Sak'o aka bani na kawo miki.." yayi maganar yana kallan ta

"Sak'o kuma? Ni ban sanka ba" ta fad'a cike da sakarcin nan nata, se yayi murmushi kana yace

"Ehh Hajiya, dama nasan baki sanni ba ae amma daga makarantar ku ne aka turo ni" seta d'an samu relief amma duk da haka tace

"Toh mene?"

"K'awa ta zo mu tafi 8 ta kusa, kuma kin san yau yana da first period a farko" Ruks ta fad'a tana jan hannun Ayrah, seta d'an maraeraece fuska sannan tace

"Uhmm daga makaranta ne fa.."

"Kinsan yadda za'ayi? Mu bari muyi gaba ke kuma kiyi sauri kiji abinda ze fad'a, but u should make sure dat kin shigo class before 8" seta jinjina kae tana bin su da kallo sanda suke wucewa ajin kana ita kuma ta dawo da duban ta inda mutumin yake, kafin tace komae yace

"Kayan abinci ne dana sakawa Hajiya akace mu kawo miki daga makaranta" seta tsaya ta cigaba da kallan sa kamar me tunani se kuma tace

"Kaya kuma?" yace

"Ehh.."

"A'ah Abba ya siya min" ta fad'a tana girgiza kae, seya sake yin murmushi kafin yace

"Ehh wannan ae daban yake Hajiya, kuma kinga daga makaranta ne" seta d'an yi jimm kafin tace

"Toh zan kira Yah Sadeeq na fad'a masa tukunna" mutumin ya sauke ajiyar zuciya yana mamakin wannan yarinya haka amma gudun kada ya takura ta shinshino wani abun ya sanya shi fad'in

"Toh kira shi"
Chapter 16 · 0% Book details