Sashe 5
Yar Kwalliya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
'YAR KWALLIYA Page 6-10 . Can saiga Binta ga gare sarkin kwadayi da umman ta suna ta howa Yauwa Allah na gode maka ga binta cewar Abu Dan rainin wayo da sassafen nan a aiko gidan mutane ace suzo ko uwar me za a mana cewar Binta Abu tace Kema dai kya fada gamunan ana surfo mana zancan banza Eh waye yake zancan banza ke kuma Binta ba a koya miki gaisu waba bakya ganin manyane a gurin nan cewar liman dake zaune a gefen me gari Binta da umma suka samu guri suka zauna Abu tace Wanda yatsargu dahi nake Babba bangan shiba saidai naga me gari tinda ba a barni naci abinci ba nazo nan to kowa yayi hakuri da abinda zeji koya gani cewar binta Liman yace kaji yara da rashin kunya Barsu dani liman cewar megari Umma ta gaida me gari binta kuwa aikin gun guni kawai takeyi Sauran mutanen gurin hanci a to she sun kasa cewa komai daga liman sai megarine kawai suke magana Binta kinji wai dan mun daki wa yancan 'yaran hine aka kawo mu nan gasu 'ya'yan kuli da mai cewar Abu Binta tace Kan uba Yasin bazan zauna ba akan su aka hanani cin abinci tafiya zanyi Yasin karki yarda binta kanki tafi kizo ki daki rabon ki zan taya ki cewar Abu Sukayi kansu zasu daka liman da megari mutuwar zaune sukayi wato kanhin jikin Abu dana binta da itama tafara hawa layi sukaji sukayi lup kamar basa gurin Megari yace Karku sake Ku tabasu kuna jiko wai warin me nake ji haka ina kuke kusa baki mana meye aikin ku liman Caraf Abu tayi da cewa nice nan kanhin tirarena babu inda baya zuwa megari ka gode Allah tinda kaji kanhin tirarena Megari yace Tirare kuma tab Wannan uban warin shine tirare . liman ba lbr yakasa cewa komai sai kallo da ido sauran ma sunyi shiru Megari cikin bacin rai yace waime nake gani haka kun dena magana ne kuma banson sha shanci kunwani zuba min ido me kuke nufi Me gari sai hakuri binta Abu kuzauna cewar inna da umma Binta hannu a dun kule tana shirin kai naushi take cewa Inna kubar mu dasu yanzu mu koya musu hankali Nura cikin muryar tsawa yake cewa kuzauna karku bari na kara magana Ganin fuskarshi ba alamar wasa yasa suka zauna Megari yace gaskiya yaran nan abin naku azimun ne kuma da laifinku wajan bata yaran nan kuduba fa Ku gani baruwansu da babba koyaro duk wanda ya musu yi mishi zasuyi Me gari ayi hakuri zamu gyara insha Allah cewar umma Me gari yace To shi kenan gaskiya kudau mataki inba haka ba ni da kaina zandau mataki Wani yaro ya fito daga gidan me gari hannun shi rikeda samira Tinkafin ya karaso Binta sarkin kwadayi tafara hadiyar yawu wayanda suke kusa da ita saida sukaji karar Yaron ya gaidasu ya ajiye kwanon a gaban liman Binta idonta na kan kwanon ko kiftawa bata yi ta janyo kwanon kusada ita Kanshin abinci yadawo da liman daga dogon suman da yayi Liman yace Ke me kike nufi yajanyo kwanon gaban shi Binta ko magana ta kasa hankalinta nakan kwanon Liman Allah ya yanka maka binta taga abinci ranta ya biya dan haka ka bata taci cewar Abu Liman yace In naki fa dawani bakinki dayake zuba wari anya kina wanke shi kuwa Abu tace Yasin wanke baki kahe hakori yake hiyasa bana yi liman kaida kanka kace hi bakin me azumi kanhin Almuski yakeyi hiyasa nima na dena wanke baki saboda Almiskin yazauna a bakina nafita daban daku nawa basai ina azumiba ta fada tana Dariya Liman baki yasaki yana kallon Abu Megari yace ke Abu anya kina da kai kuwa Abu tamika mishi kanta tace shafa kaji Inna ta rufe bakinta tana kallon Abu Megari ina fada maka saika dauki babban mataki akan Abu da binta cewar liman Bakomai kubani lokaci zansan abinyi kuna iya tafiya amma kubar binta da Abu liman ze musu fada cewar megari Waaaanii gaskiya babu abinda zan iya fadawa wayan nan yaran banshirya takun saka da suba sunyi nisa basa jinkira cewar liman Yi shiru liman nagama magana cewar megari Inna,umma da Nura suka tafi Binta batama San tafiyar suba itadai burinta taji abinda ke cikin kwanon a cikinta Liman kabata abincin nan taci yasin tanada cutar duka idan aka hanata abinda takeso hine suke tahi cewar Abu Liman Ya kalli binta dake zaune hannu a dunkule ido akan kwano tana sude baki Liman yace Me gari Abuya tabbata duka zatayi kalli kaga . Liman karka zama soko mana kayi musu fada sutashi su tafi ita kuma binta ka bata taci cewar megari Kwanon ya miki mata ta ansa tabude tana ci kamar kura yaga nama Binta ta gama ci tasa kafa ta ture kwanon ta kalli 'yar me gari tace jeki kawo min ruwa Niii kalle ni sama da kasa nayi kama da 'yar aikin gidan Ku cewar yar me gari Zancen banza meye dan kin debo min ruwa yan matan garin nan kaf yan aikina ne saboda na fisu haduwa cewar Abu Ya isa kunutsu kuyiwa kanku fada kungirma aure zakuyi gidan wani zaku kuyiwa Allah kudena abinda kukeyi Dariya suka yi suka tafa kinji wai aure cewar Abu Binta tace kaika sanshi nidai tinda ba a bani ruwaba bangode ba taso mu tafi To tace suka tashi zasu tafi Binta tarike ciki tace washiii cikina ya motsa Binta tayi nishi saiga tusa ya biyo baya Megari yatoshe hanci yace liman Sa a kamo min yarin yarnan Binta da Abu najin haka suka sa gudu **** *WACECE BINTA DA ABU* ABU 'yace ga munzali malam munzali fatauci ne sana arsa shikadai yake tafiya inya tafi saiya jima kafin ya dawo sai matarsa Suwaiba yaranta na kiranta da Inna yaransu 4 Ramatu itace ta farko tana aure a garin da suke me suna *DARAUDAU* sai zulai itama tayi aure sai Nura da Zainabu Abu itace auta ABU yarin yace mara tsoro duk girman mutum inya mata saita mai farace tas amma qazanta ya maida ta baka dan qazanta kokitso intayi saiya dankare layin ya bace kafin inna tai mata ta karfi ta tsefe Binta 'yace ga murtala Malam murtala mahaucine Allah ya masa rasuwa tin Binta tana karama a hannun ma hai fiyarta ta tashi sunan ta Baraka binta kadai ta haifa BINTA yarin yace mara nutsuwa ga kwadayin tsiya idan taga abinci jikinta har rawa yakeyi itama bata barin ta kwana dan haka tasu tazo 1da Abu gasuda taurinkai ***** Binta da Abu na cikin gudu wata yarinya kanta dauke da buhu ta tsaya a gaban su ta shaki wuyan Abu Ke meye haka a ina nasanki cewar Abu Tace idan maye ya manta uwar diya bazata mantaba nice wadda kika daka kika cimin gyada kika kuma zubarda sauran Abu tace Kinsan abin da yawa yanzu me kike nufi da kika shaki wuyana Dukanki zanyi na kwashi saura nakai gidanku cewar yarin yar Banga Alamaba ance da kuturu a gama lpy ni Abu banga wanda ya isa yamin abinda kika fada ba ba a hai fehiba Binta tace ke ware inba haka ba hmm jiki zeyi tsami Ke waya sa dake ni din nan da kike jida gani ban tinkare kuba saida na samo makarin ki ke binta dan nakula kema matsalace ta daban cewar yarin yar Makarina kuma ni binta banganshiba anan gurin yau banga abinda zesa na bar kiba batareda na sosakida bulala ba Ko to shikenan nida ke za a ga me gaskiya yarin yar ta Bude buhun taciro goriba,kurna,magarya da gyada Tinda ta Ciro Binta ta hadiyi yawu kamar yanda ta saba tabi hannun yarin yar da kallo Abu tace Ke karki sake ta rudeki da abin hannunta Binta nizan siya miki fiye dahi Ko jinta binta bata yiba Tamika hannu alamar ta bata harya rinyar ta miko mata saita janye Binta tace meye haka kuma bana son irin Wannan Kina zaton kai tsaye zan baki batareda na kafa miki doka ba Meye dokar cewar Binta Yarin yar tace zakiyi Alkawarin cewa bazaki sa hannu a fadana da Abu ba inkikasa hannu zan kwace abina Binta ta kalli Abu ta kuma kalli ledar hannu yarinyar da irin abinda ke ciki Nan tashiga raba idanu . Jikin Binta sai rawa yake Na amince bani Yarin yar tace in na baki ki tafi ko juyowa karkiyi Binta tace to bani dai Tana ba binta tawuce ta tafi Yarinyar tace yanzu daga ni seke Abu tace hakane kuma zam miki dukan tsiya kamar mu2 muka miki Yarin yar ta kama Abu da duka Abu na ramawa Abu ta Bude baki ta sakar mata cizo a hannu Waiyoo kika cizeni Yasin bazan yarda ba koni koke a gurin nan cewar yarin yar Saukar duka yarin yar taji bazata koda ta juyo Binta ta gani zatai magana binta ta dauketa da mari binta da Abu sukayi mata taron dangi saiga yarin yar a kasa wanwar tana kuka Abu ta bude buhu ta leka taga garin tuwo tayi dariya Binta ta daga ta juyewa yarin yar a jiki Inkinje gida saikiyiwa tsohuwa bayani yanda Akai da garin tuwo cewar Abu Suka tsalla keta suka wuce Binta tace Abu kina jin abinda liman yayi mana dan yaga me gari waimun girma aure zamuyi Rabu dashi nasan abinda za muyi mihi damu yake magana ba a taba mubama munyi fada bare ka ta bamu zomuje cewar Abu Ina zamu cewar binta Zaki gani cewar Abu Koda suka tafi basu tsaya ko ina ba sai gidan liman Abu tace Sallama Alaikum goggo me tuwo Goggo me tuwo ta amsa da Wa'alaikumus salam Abu Binta yaukune agin namu Eh wlh cewar Binta Goggo me tuwo tace Gashi kuma ban gama tuwonba yanzuma na dora Bakomai mu abindaya kawo muma daban ne bansan ta yanda zanfara fada mikiba goggo cewar Abu Kar kuji komai kufada min idan baku fada minba wazaku fadawa bayan nasan Ku tin kuna yara nan kuke zuwa cintuwo cewar goggo Binta tace Hakane munsan da wannan goggo hine dalilin da yasa mukejin nauyin abinda zamu fada miki Binta Abu kufada min bakomai komai girmanshi zansan abinyi Abu tafashe da kukan karya taceTo