← Book details Tales Of Wazeeris Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 65

Sashe 18

Tales Of Wazeeris Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

snn ba aza a ba shi hutu sosai ba kuma bazaa abar shi yafara sabawa da uban kowa ba Domin a nan ana so aginashi ne bawai dan kawai yazama dan sarki ba saidai ya zama irin mutumin nan da maqiyansa bazasu iya rushe shi ba sbd tushen tarihi dukiya da matsayin tharim vale yana da bukatar kariya anan gaba sosai.

washe garin isowarsa dahrul zarah da safe aka kai shi babban harabar cikin gidan inda dattawansu na hukunci da horo suke zaune cikin nutsuwa.

Ɗaya bayan ɗaya ya gaishesu a matsayin tsari na iko saidai kowanne kallo da kuma tambaya dayake cinkaro dashi awajen kamar gwaji ne.

kowani irin yaro zai iya jin tsoro a irin wannan wuri Amma Shamsan bai nuna musu alaman haka ba saidai sosai ya fahimci abu ɗaya, ya lura kamar anan wajen ba'a ba da girmamawa wa mutum kai tsaye ana neman girmane ta hanyar nitsuwa da kuma jajircewa.

dan haka yake lura da komi a zuciyarsa da kwakwalrsa msmn ma da kai tsaye suka bashi official title dinsa na SULTAN shamsan waxeeri ma'ana the crown prince,shi dan sarki ne amma wanda zaina daukar wasu hidimomin mulki, iko kasuwanci, siyasa, da kuma hukunci agefen mahaifinsa ana nufin bazai kuma sake amsa yarima kawai ba..

sbd sunan yarima yayi kadan yakuma kasa ma reponsiblitynsa.

dan karamin gwajin hutu aka bashi inda aka killace shi awajen da babu kowa he had just few servants to communicate with, Ba a barkowa yazo kusa dashi ba har Saida ya dan fahimce kanshi anan snn aka tabbata a shirye yake babu kewan gida ko tsoro a yanayinsa sai snn aka tsara masa abubuwan da zainayi kowani rana

tun daga ranar farawa rayuwar Shamsan ta sauya gaba ɗaya anan dahrul zahra aka fara masa darasinsa na farko wato tarihi na asalin Gado Ana koya masa zurfin tarihin zuriyarsu ta waxeeris, yaƙeyaƙe,yarjejeniyoyi, da yadda aka kafa iko da ƙarfin mulkinsu.

wani ranar kuma sai a koya masa dabarun Sarauta kamar Yadda ake magana da iko da yadda ake sarrafa taro, da yadda ake iya ɓoye rauni a fuska ko agabn maqiya.

shiyasa dolene saida uwarjini tabar tharim vale tazo nan dahrul zahra dakanta tadan yi musu sati biyu sabida da akwai abubuwa da dayawa wanda dole itace dakanta zatazo ta koya masa game da tarihin zuriarsu musnm irin abubuwa da yawa wanda taso ace ya iya ma tsafi da kuma wasu wanda takeso ya musu kallo da idon basira.

sati biyu tay anan tare dashi masu kyau har sai bayan komawarta tharim vale ranar da dare aka wuce dashi wani waje waishi yankin FES, Tsohon birni ne sosai acikin moroco da tasamu waje a tarihi tana da wasu sirrika acikinta
dan anan garin ne kawai ake koya musu hidden knowledge kai tsaye daga bakin old scholars, wanda sune zasu bashi asalin Ilmi arabi da na boko da Sirrin Ancient Power na zuriarsa wanda zaina amfani dasu wajen shawo kan duk wani abuna barazana da zai tunkarosu nan gaba

dakin dayake kwana anan Fes azagaye yake da wani irin Rare herb ana cemai flower of memory it is Said to heighten pattern nd recognition speed ana shukawa domin zallan royal heirs ne na ahalin jinin wazeeris ayayinda sukenan wajen training phases dinsu.

kowani safe za'a bashi ganyen mint da apple as meal staters dinsa, awajen Study sesssion dinsa kuma green tea ne da almonds wata rana kuma sage tea ko sidr da honey ko black grapes ko zallan olive da figs kominsa daga abubuwane da suke kara kaifi da karfin jiki da kuma boostin mmry da kuzarin kwalwalwa

Littattafan da yake karantawa Ba a bar masa kowani tarukuce ya karanta ba An zaɓa masa Littafan siyasa, dabarun sarauta, yaƙi, da mulki,Tarihin dauloli yadda suka tashi da yadda suka faɗi, da psychology,manipulation, negotiation,sau ɗaya kawai yake da buƙatar karanta book sai kaga ya haddace

saidai Amma abin da ya fi nauyi a horonsa shine Addini da ilimin
Qur'an dan ba karatum kawai bane akeso yay ana bukatan ya fahimci abubuwa dayawa daga rayuwar Manzon Allah ﷺ da yadda ake yanke hukunci da adalci anan
Aka koya masa cewa ba'a mulki da iko sai da tsoron Allah.

kafin yaci wata hudu anan Fes kusan dukan Malamansa sun lura da abu ɗaya shamsan baya maimaita kalma kokaga yay tambaya sau biyu, snn ba ya mantuwa cikin sauƙi, baya kuma karatu cikin gaggawa amma yana da matukar fahimta maizurfi Wani lokaci kafin agama bayani
yariga ya fahimci in da aka dosa he had dis photographic memory with a hypercognitive mind hakan yana nufin yana iya koyan abu extremly fast, zai iya haddace complex systems snn zai iya processing many possibilities at once almost like parallel thinking.

wann special baiwar tasa yasa akasauya tsarukan horonsa dayawa abubuwnda zaiyisu a shekara guda anga yana iyayinsa a watanni, dan haka suka yanke hukunci gajararta lokacin yimasa horo dan nan da shekara biyu suke so samu a turasa yaje United states yay aiki ya kara nisan karatu.

universal languages shida sune abu na karshe da aka koya masa fannin ilimi.

yaren larabci harshen addininsa, da english domin diplomaciya sai yarukan french da spanish domin siyasa da hulda da al'adu da kasashen yamma, sai turkiyanci don fahmtr tsofin daulali akarshe aka koyamai mandarin domin kasuwanci da duniya,wanda acikin watanni suma ya iyasu sosai after many days and sleepless nights of practise nd training

bayan nan aka fara hade mai schedules dinsa da Horar da Jiki kamr Koyon yaƙi, tsaro, da juriya,domin yarima bazai taɓa zama mai rauni ba

sai can dare aka kaisa yankin ouarzazate inda ake musu desert survival training,.

ranar farko ya dawo daga sallan fajr kenan yana kkrin kammala karatun qur'ani da ya sabayi acikin dakinsa kullum yana dago kai ya hango wani yaro jarumi kusan kamrsa
a shekaru saida yaron yafishi girman jiki dan kuwa murdaddem dantsen sa akarfafe yake, suna haɗe ido yaron ya masa wani irin kallo wanda ya isa ya razana shi amma ko ajikinsa ganin hakan yasaka yaron ya wurgo masa takobi cike da kwarewa direct zuwa saitin zuciyarsa yay sauri ya capke tareda mikewa tsaye suna kallon juna batare da sun furta komi ba sai can kafin nan shamsan ya aje qur'ani ya bude kofarsa ahnkli ya fito....
TALES OF THE WAZEERIS

BY

SURAYYAHMS

2026
08060712446
[19/05, 05:59] Annah-Anya: *13....🦋*
Tales of the wazeeris
sanye dawasu irin bakaken wuluk din kayan horo yaron yatsura ma shamsan Ido zuciyarsa na kan aunashi harya gama takawarsa acikin nitsuwa ya iso daf gabansa da takobin a hanunsa fuskrsa batareda wani hayaniya ba

acikin kankanin lkci suka karewa junansu kallo daga sama har kasa yaga tabbas yaron nan ya ɗan fi shi girma kaɗan snn jikin sa a ƙarfafe yake hatta motsin numfashinsa cikin sauri yakeyinsa kominsa da zafin nama har wano rawa rawa hannunsa yake kamar wanda yake zuba zancen zuci.

daga ganinsa kasan Wnan ba ɗalibi bane ko dan sarki yaro ne da akariga aka gina shi da horo mai tsanani.

Shamsan ya tsaya calk yana karantarsa batare daya motsa ba kwasam sai yaron ya kalli takobinsa dake wajen shamsan din ya wani hade rai yace“i believe this isnt urs..

still shamsan bai amsa atake ba yabishi da wani irin sting silence nd dead stare irin direct kallon izza da shirun nan mai masifar ɗarsa bugun zuciya da fargaba

harsaida yaron ya hadiyi yawu snn yakara matsowa kurkussa dashi a hankali zuwa gabansa snn yace "..hey..are you deaf?...

dede nan ruwan Idanunsu suka kara haɗuwa dana juna basu ce kala ma junan sun ba har saida wani ɗan lokaci mainauyi ya wuce snn shamsan ya dauke idonsa a bazata yajefar da sword din akasa a walaknce dan yaga meye yaron zaiyi

da kallo yaron yabishi kafin nan ya tsuguna ya daga takobin yana ɗan murmusawa kɗan fuskarsa a dore cikin karkada kai ahnkl yace "hmmm..Taurin kai ko..

yana daga takobinsa sama da kyau ya nuna shamsan din dashi da ƙarfi yace 'You..Bloody royals! daga gani baka cancani tsayawa anan wajen ba why dont u show me who you are

tun begama rufe bakinsa bayaga yadda Shamsan din yabishi dashi da takobin nasa dawani irin kllon wlknci dana rainin wayo snda zazzafar huci me ƙara ya kwace ma yaron ma baisani ba.

batare da wani gardama ko tsoro ba ya shiga tsakiyar fili babu wanda yace musu start yaron ya fara kawoma shamsan hari tako ta ina da sauri sauri kuma kai tsaye batare da jinkiri ba duk dama yaga da hannu kawai Shamsan din yake tarewa wani lkci da ƙyar ma sbd shi baidauki wani takobi ba karantar move din yaron kawai yakeyi atsanake,sai can da yaron ya samu yabuga masa kasar takobin a hannunsa snn Idanun sa suka ɗan canza kala yagane wannan fa ba wasa bane aransa yace hmm

Hari na biyu yazo da sauri fiye da na farko shamsan still yasake bashi dama amma yanayi yana karkata jikinsa tareda kaucewa sukar wukar akan lkci

akaro na uku ne komai ya Canza salo yaron yana kawo hari baiyi zato ba shamsan daya gama karantsesa yay wuf ya kama hannunsa daya riqe taqobin cikin nuna masa girman jiki bashine ƙarfi ba,atake ya murda hanunsa sai da yasakashi yay ƙara yasaki takobin kasa bai sani ba..

cikin yan mintina shamsan ya dauki takobin akasa ya fara kai masa hari da irin salonsa zak xak amma cikin nuna masa cewa yafi iya sauri da iya kai hari mai hatsari, dan kai tsaye ya yayyanka masa rigarsa yacire hannun rigar da jikin rigar gabaki daya ya kusan yimasa tsirara awajen atake..

ganin yaron ya matukar tsorota yana jajja da baya yana haqi nan wani murya daga sama ya dakatar da su da sauri sauri yaron ya ja can baya yana wani irin razannen haqi

shamsan ya hade rai kamar bai taɓa dariya ba yana kallon yaron daga sama har kasa can ya sauke takobin kasa ahnkli yace baka shirya ba kake tunanin sanin koni waye..hmm

yaron yana haqi bai ce komai ba har sai dai ya gyara tsayuwarsa yana kallon shamsan kai tsaye ya mika masa hannu with respect yace

i am...Itban bin Maleek.

shamsan baice masa uffan ba yamiƙa masa takobinsa
Chapter 18 · 0% Book details