← Book details Tales Of Wazeeris Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 65

Sashe 15

Tales Of Wazeeris Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin katseshi da iko da taurin kai sarki murad yace "wann ne dalilin gayyatar da aka min?

kai tsaye sheikh haroun ya daga kai ya kalle kwayar idonsa yace "don kwantar da wannan yanayi na qiyayya, tsana, domin tsaftace abin da aka tabo na mutuwa akan ahalinmu gabaki daya ruhi me tsarki ya nemi hadin jini.

sarki murad bai wani fahimce inda maganr ya dosa ba sai baice komi ba ya xuba masa ido..

anitse tsohon yace daya daga ‘ya’yanka mata za ta shiga cikin ahalin wazeeri.

dedenan numfashin gimbiya amani noorain ya dan tsaya cak ta dago kanta da sauri kuma a raxane ayayin da idanuwan Arisha suka haskaka da wani irin tsnnin mamaki mai tattare da wani irin tsananin farin ciki aranta ganin burinta na kasncewa agidan nan zai samu cika acikin sauki

sheikh haroun ya cigaba da cewa idan lokaci yayi da yayanka mata duka suka isa aure zamu zo da yarima daga jininmu zai zabi daya acikinsu za'a kulla wann alaqa ta auren jini da zata kare ahalinmu duka.

sarki murad dayajima da shiga shock ya saki wata karamarr dariya data kufce masa abazata gabobin jikinsa har na rawa kar kar yamike tsaye da tsananin fusata a yanayin sa yana kallonsu duka da karfi yace

“Hakan Bazai taɓa yuwa ba baxan taɓa mika yaya na ga wann zuriar taku ta zalunci ba..idan ku kun mata baya to mu bamu mantashi ba
..na rantse da...

kafin ya karasa dire rnsuwar shugaba imran ya katseshi ba tare da daga murya ba yace"..Enough. ba tambayar ixininka akeyi anan ba..doka ce...idan lokaci ya yi jinin wazeeri zai dauki daya daga cikin ‘ya’yanka mata dan haka kaje ka shirya kana da lokci mai tsayo dazaka fahimtar dasu iya abunda ake bukata daga garesu tun kafin lkaci ya kure.

sarki murad dake ɓari kar kar da tsananin bacin rai xai magana nan kenan yaga take security sun zagaye shi da bakin bindiga technology ce irin wanda bai taɓa gani aruyuwarsa ba..

gimbiya amani noorain tay sauri ta miƙe tsaye taje kurkusa dashi ta rike gefen rigarsa da alaman sassaita shi kafin nan Arisha ta taso itama ta tsaya agefensu tay shiruuu

uwarjini data gama karewa arishan kallo daga sama har kasa ba ta kara magana ba sbd ko kadan yarinyar bata mata tsari da kyaun da ma zata iya haɗata jininta da su ba.

tasan yaran murad guda biyu ne and she wonders why d oda girl was not brought here..

koda shike kmr ance mata sun turata qasar waje karatu...koma miye ne bataga alamr wann ahalin suna da kwarjini da kyaun da zasu hada kafada da yarima shamsan

dan haka koda anyi auren duk wacce shamsan zai aura saidai ta tsaya musu a matsayin baiwa kuma bazata bari ya haihu da wann kaskantacen ahali masu snyin jini ba.

adeden nan taron ya kare babu wani dogon salama tsakaninsu nan dattijn nan suka saka hannu atakarda aka manna hatimi.

sarki murad ya doshi kofa fuskarsa a mugun daure...

zafi da kunci na balain tafarfasa a ransa jin wai zaa dauki daya daga yaransa mata gashi babu abin da zai iyayi anan duba da yafi kowa snin cewa ahalin waxeeris basuda imani zasu iya sakawa aje akashesa agidansa yau yau snn abar matarsa da yayansa su rayu kuma azo yi auren babu shi, kai koda zai fada ko musu dasu ba a wannan wajen ba dole ne saiyaje yay tunani dan wallh bazai amince data daga yaransa daya haifa su kare a matsayin bayi da sunan aure ba.

kamar yadda suka shigo haka suka fice..

daga Cikin fadar iko kuwa Ummu salma ce ta fara kawo kananan magana akan yanayin Areesha, tareda nuna wa a fili cewa sarki murad baida yara mata da suka dace da auren shamsan. tabbas wnn dokar hadin aure na ruhi ya kaskantar dasu

atake mutane dayawa suka bi bayanta, uwar jini ce kawai dai batace komi awajen ba sbd itama sosai ta karewa arishan kallo amma bataga wani cikakken royal energy ko wani muhibba ajikinta ba.

wann maganar ne ya jawo Nana A, ta shigo da siyasarta, na cewa daga zarar anyi wnn hadin auren yakamata abawa shamsan wata matar auren daga cikn jininsa da yar uwarsa leelah wazeeri dansu gyara masa irinsa da jinin xuriarsa.

snn ta kawo shawarar cewa yakamata ma akara karfafa auren zumunta acikin gidan domin kawo cigaban ahali.

uwarjini bata wani amshi batun sosai ba amma kuma shugaba imran da zafar sun nuna hakan yay musu sosai sai batace komi ba...

yau din wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar ummu salma dan har aka tashi a fadar iko tanaji kamar zata xuba ruwa kasa tasha dan dadi.

Bayan kwana uku da faruwar haka angama kulla yarjejniyar aure snn sarki abdallah yana can kano da matarsa hajarat sakeena suna mulkar masarauta dayankin dala gabaki daya

saida kusan komi ya lafa snn uwarjini ta sake zuwa jeji dan takai ma ruhi me tsarki ziyara snn ta sanr da shi duk wani hukunci data yanke game da bukatansu

ganin ta jima da ficewa agidan yasaka Nana A ta tako taho sashen ummu salma dan su tattauna muhimmiyr shiri data tsara musu dazai kaisu ga cin nasara.

a hadadden garden din ummu salman suka keɓe da yamma an kawata gabansu da madara da dabino da kuma zuma da kofin shayi dayaji kayan qamshi masu dadi..

suma zaune bisa kan lallausar dadduma fuskr ummu salma na cike da annuri cos all she can think abt shine jikarta leelah ynx ta samu wata mafaka a rayuwar shamsan tunda har uwarjini bata kushe zancen agaban kowa ba.

yau da nana A tazo mata da wata magana gameda shirun da uwarjini tay sai abun ya dan dameta, gashi batason ta tunkareta kai tsaye, batason wani abu na rashin fahimta ya gifta tsakaninsu barema har uwarjini tace bazata bari yarima shamsan ya hada jini da ita ba duba da jininta da zuriarta basu taba haihuwar ɗa namiji ba.

wann kalman ya sake daga mata hankali sosai dan tariga tasan hakan kawo mata wani irin baraza anan gaba

batada tabbacin leelah ma zata iya haifar wa shamsan ɗa namiji koda anmusu aure.

atake murnan ummu salma ya koma ciki, farin cikinta ya rikide ya dawo sabuwar damuwa da tashin hankli

wann fargabn ne ya jawo har nana A ta gaya mata wani sirri,..

ta fito mata da wani madubin sihiri tare da nuna mata cewa wani malami ya mata bayani cewa nan gaba kanwar shamsan wato rihanna zata haifi ɗa namiji ne a haihuwarta na farko idan tay aure, dan haka dolene ta jawota jikinta snn ta hadata aure da kanin mijinta farees salman, ya zamo ajininsa aka samo da namiji, tunda farees salman yana da alaqar jini da tsohon mijin yarta marigayi suhaila waxeeri, babu tantama hakan zai kore zargin cewa leela bazata haifi namiji wa shamsan ba a zcyar uwarjini.

idan sukaci nasarar haɗa auren farees salman da rihanna kuma aka haifi da namiji dolene agane cewa leelah ma zata iya gado jinin ubanta bana uwarta ba tunda ita da farees kusan cousins ne ta fannin uba.

sai yanxu ummu salma ta asalin fahimce dalilin dayasaka nana A tace akawo farees salman gidan snn tafara cusa shi acikin rayuwar rihanna waziri dan su kulla wata abota.

wannnan shawara da nana A ta kawo mata bakaramin zama a zuciyarta yay ba dan kuwa shine musu kawai mafita dolene ma ta hada auren nan.

hira me tsayi kuma me cike da sirri tskanunsu har yamma ya rufa snn suka rabo, nan ummu salma ta koma cikin chambrta da tunanin yadda abubuwa zasu kasance. dole ta bi shawarar nana A, snn dole ta gamsar da zuciyar jikarta leelah dan tasan cewa shamsan wazeeri shine kawai ta zaba mata amatsayin mijin da zata aura itama anan gaba.

dayan bangaren kuwa komawar sarki murad zamkora saida yay kusan kwana uku yana cikin baqin ciki baya kuma magana da kowa dan duk sadda ta tuna cewa tharim vale zasu taho nan gaba dan dauki daya daga cikin yayansa su aura sai yaji kamar yakashe kansa atake kawai ya huta da dumbin baqin cikin duniyar nan

dan yariga yasan wnn fa ba auren daraja ko mutunci bane, auren bauta da kaskanci ne yafi kowa sanin cewa muddin uwarjini tana raye koda zai mutu ne bazata kaunace jinin baiwa acikin zuriarta ba.

bai kuwa dauki lokaci ba abubuwan suka fara dakule masa

manyan takardu daga masarautar dala sun fara taruwa a kan teburinsa da hatimin dokoki dala ajiki

umarnin sauya tsari da
umarnin dakatar da wasu manyan shirye shiryensa da kuma shirin mayar da mafi karfin rundunarsa na tsaro zuwa karkashin iko na tsakiya da gaggawa ba tare da jinkiri ba.

wann takardun nasu sosai ta fara daga masa hankali duba da baiga jin sassauci a zuciyarsa nasanin cewa wai yau sarki abdallah wazeeri shine shugaban dala ba.

wanda ya gimesa da kusan shekara biyu wai yau shine yake mulkansa tsabar an raina masa wayo..

tunda sarki murad yau ya shigo cikin fadarsa ya tsaya atsaye yana kallon takardun dokokin dake hannunsa jikinsa yana rawa rawa ta ciki zuciyarsa na tafasa sosai bana kadan ba

dan wani lokaci da ya wuce shine yake bada manyan rinduunonin sojojinsa umarni amma yanzu kuma wai makiyinsa ne zaina saka masa dokoki akan komi.

akarona farko da sarki murad ya ji wani irin rauni wanda bai taɓa ji a duniayr nan ba amma dake yana da taurin kai sai ya bar abun aransa yana kona shi a hankali..

ME KUKE GANIN ZAI FARU???

SHARE UR OPINIONS..

AS EDEY GET MORE ND MORE INTRESTING

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*

*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*

#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES

[19/05, 05:59] Annah-Anya: *11.*
Dagata dayan bangaren kuwa sarauniya Arisha ce a dakinta ita dayanta tana kwance bisa royal bed mai laushi yanayin jikinta a sakarce kamar wacce bata da wani damuwa a duniyar nan

dan tunda suka dawo daga cikin mansion din wazeeris take cikin wani irin yanayi na tsananin jin dadi da nishadi, bata sake kulawa da halin baqin ciki da mahaifinta da mahaifyta suka shiga ciki akan sharudan yarjejnyn aure da tharim vale ta bayar akan yayansu ba.
Chapter 15 · 0% Book details