← Book details Soyyayar Mutun Da Aljan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 6

Sashe 5

Soyyayar Mutun Da Aljan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sunita ma tun daga lokacin ta shiga kunci da kunan zuciya na rashin dawowar masoyinta. Ta kuma yiwa kanta alkawari har ta mutu ba zata so wani namijin da ba Jamal ba. Yanzu haka ita take mulkin birnin Durgas saboda tsufa daya riski mahaifinta sarki Ashwar.

Masu ganin ta sun ce har yanzu tana nan da kyawun nan nata kamar na da, sai dai shekaru da suka ja. Ance kuma har yau tana kan bakar ta na jiran masoyinta Jamal inko ya mutu ta yi alkawari itama sai dai ta mutu a hakan nan amma itada aure har abada."

"Wannan shine cikakken labarin ɗan'uwana Jamal. Shin kin san me yasa na baki wannan labarin, har ma na ce miki yanada nasaba ga hanaki labarin maganin cutar Muhsin da muka yi?" na girgiza kai cike da jimami nace "a'a" ina sharar kwalla. Domin gaskiya labarin soyayyar baba Jamal da gimbiya Sunita ya ta6a zuciyata ba kaɗan ba.

Babana ya gyara zama ya fuskance ni da kyau yace "Na'eema maganin nan na warakar cutar Sunita shine maganin warakar Muhsin ɗinki. Babu wani magani a duniya da zai tashi kwakwalwar Muhsin tayi aiki yadda yake buri sai wannan ruwan na tsibirin darul iks wato ma'al dawa'u."

Sororo nayi ina kallon baba wanda ya dasa aya a maganarsa idonshi a kain na. Matsanancin tsoro da tashin hankali ne su yi min dirar mikiya. Zuciyata ta shiga dukan uku-uku ina kara juya maganar baba ina jinjina ta a ma'aunin tunani.

Lokaci ɗaya naji jiri na ɗiba na tunanina ya gauraya kaina yayi mini nauyi sosai har ina ji kamar zai rinjayi gangar jikina...

*Nasmat* ✍
[23/1 17:53] Yar Mutan Arkillah: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*MARUBUCI...*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari.

👩🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________

📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
[email protected]

Sadaukarwa ga
Ama Alhj Kabir
Zeenat Deen (Shazee)
Beauty Queen
Zuwaira Madara
Zeety Mmn Hanan
Mmn Noor
Mom Heebah
Mum Namma
Ina son ku Sisters thanks for the love and support.

*Page 7*

* * * * *
Cikin dauriya da cijewa na mike tsaye lokacin da azababben bakon ciwon kaina ya kara tsananta. Ban ko dubi inda baba yake ba na danna kaina ta cikin bangon ɗakinshi na bayyana nawa ɗakin. Hannuna na dafe da kaina da ke juya min wanda nake ji bisa dukkanin alamu yau nema yake ya faskare ya rabe gida biyu. Na zube kan gadona ina mai ambaton sunan Allah, daga nan kuma ban koma sanin komai na duniya ba. Na dai ji ni kamar ina bacci sai na shiga addu'ar Allah ya tashe ni ya kuma sanya duk abinda na jin nan ya kasance mafarki ne.

Lokaci mai tsayi na shafe a yanayin fitar hayyaci ni ban mutu ba ban kuma suma ba, dan sama-sama nakan ji motsin shigowar iyayena har ma da maganganun da suke a kai na. Wasa-wasa na ci gaba da rayuwa a haka har na tsawon mako guda bana magana da kowa, ba kuma na iya cin komai. Babu abinda ke kai komo a rayuwata sai soyayya, tunanin Muhsin da lalurar sa ne suke kara yi min babakere a kowane lungu da sako na zuciyata. Tunanina ya gagara kawo komai gameda hanyar da zan bi in taimakawa Muhsin, a saboda haka na koma kamar mai cutar mutuwar 6aren jiki, bana iya yiwa kaina komai sai ummy ta yi mini. Iyakacina bin su da ido in na gaji kuma in sufe idon.

Babu abinda yake burge ni dangane da abinci, da kyar ummy na take matse bakina ta zuba min ruwan kwakwa a safe da rana da kuma yamma, a yadda nake ji waɗannan ruwan sune suka taimaka min wajen hanawa 'yan cikina mannewa su bushe saboda rashin cin abinci.

Ranar da na cika sati da kwana biyu a ranar yarima Haiman ya zo shi gidanmu cikin matsanancin tashin hankali da kaɗuwa na jin halin da nake ciki, da kuma irin lokacin da na ɗauka a hakan. Allah sarki so, ni kam na sallamawa soyayya. A ranar yarima ya bani tausayi duk da babu ɗingon son shi a raina, amma na jinjina mishi saboda bawa soyayya muhimmanci.

Lokacin da yayi arba da ni da kuma halin da nake ciki sai ya fashe da kuka, yayi zaman dirshan a gaban gadona kamar yaro ya ci gaba da kuka yana rero mini baitoci na zallar soyayya da bege. A ranar da kyar baba maalam ya lalla6a yarima ya koma gidansu. Washe gari aminiyata Rumana ce ta zo ta ganni itama cikin halin bakin ciki da nuna damuwa da ni. A nan suka wuni ita da yarima Haiman suna famar ɗawainiya da ni. Ana gab da sallar magariba ya fita domin halartar sallar jam'i shi da baba. Ɗakin ya rage daga ni sai kawata Rumana

Wadda itama take shirin tashi tayi tata sallar. Tana mikewa nayi saurin riko hannunta bayan na tattara dukkan karfi da kuzarina, Rumana ta juyo da matukar mamaki tana kallona. Dawowa tayi ta zauna bakin gadon hannunta rike da nawa, tace "sannu Na'eema kina bukatar wani abin ne?" na girgiza kai lokacin da idona suka kawo kwalla buɗar bakina na farko cewa nayi "Rumana Muhsin, nayi kewar masoyina Rumana." shiru tayi tana kallona da yanayina, hatta maganar a wahale nake yinta cikin ɗan lokacin duk na rame na fara fita hayyaci na. Hawayen dake fita daga idona ta fara share min. Tace "ki kwantar da hankalin ki Na'eema Muhsin yana nan lafiya, kar ki karawa kanki damuwa yar'uwa Allah ya baki lafiya." na girgiza kai ina kallon kawata aminiyata Rumana wadda bama 6oyewa juna sirri nida ita. Mahaifin Rumana da babana abokan juna ne wanda zan iya cewa amintakar su ce ta haifar da tamu.

Nace cikin sanyi da raunin murya "Rumana ki taimake ni ki je ki gano min halin da Muhsin yake ciki, ni kam ina jin karshen taka kasa da kafata ne ya zo." Rumana tayi gaggawar kai hannunta ta tsoshe min baki "a'a kawata, kar ki cire rai da rahmar Allah, ai cuta ba mutuwa bace da iznin Allah zaki tashi har ma ki taka kasar." ita kanta cikin dauriya take maganar tana shanye hawayen dake ko'karin zubo mata. Na yi murmushin karfin hali nace "ba zaki gane ba kawata, ni kaɗai nasan yanda nake jin jikina. Gani da rai amma banida damar mikewa ko tankwasa ga66aina, Ruma tunda nake ban ta6a jin ciwo makamancin wanda nake ji yanzu ba. Ke koda Allah ya tashe ni ma na san rayuwata batada wani amfani. Rumana ba zan rayu da Muhsin ba, ba kuma nida hanyar nema masa warakar cutarsa." hawaye masu zafi suka zubo mini yayinda wani kululun bakin ciki ya tokare mini makogwaro. Kuka nake son yi amma ya gagara sai wani tukuki na zafi da nake ji a makoshi na, wanda nake ji kamar in fasa ihu.

Rumana ma kukan ne na tausayi na ya kwace mata kallo na take irin kallon tausayi tace "ki hakuri kawata komai da kike gani a wannan duniyar mukaddari ne daga Allah, Na'eema kina da ilminki kar ki bari sheɗan ya ribace ki. Ki dage da gayawa Allah matsalar ki na tabbata zai ji6anci lamarin ki. A matsayin ki na musulma ki rungumi kaddara a yanda ta zo miki, ki yarda da yarima Haiman matsayin abokin rayuwar ki ki..." duk da cewa ina cikin yanayin ciwo mai kama da mutuwar sassan jiki, amma jin kalmar kawata saida yasa na yi karfin halin motsa jijiyoyina na ɗaga mata hannu alamar dakatarwa "ya isa haka Rumana, na gode da kauna da kike min. Amma ki bar maganar nan haka domin in kika ci gaba da yinta na tabbata cikin biyu zaki kaini ga rasa abu ɗaya. Ko dai in rasa ji na, ko kuma in rasa rayuwar gaba ɗaya. Barni da wanda nake ciki yanzu ma, na roke ki kije ki aiwatar da abinda na nema a gurin ki.

Ki nemo min labarin masoyina ko zan sami sassauci na halin da nake ciki." Kawata bata koma cewa komai ba ta mike. Sai da ta fara gabatar da salla tukunna sannan ta nufi birnin lumui ta kuma sauka a garin gabas. A lokacin yarima Haiman ya dawo daga salla shi da baba, baban ya wuce turakarsa yariman kuma ya iso gurina. Maganganun da naji daga bakinsa su suka tabbabar min da babana ya riga ya gaya masa dalilin kwanciyata a yanzu ya san abinda ya assasamin ciwon da nake yi wanda ban ta6a yin irin shi ba, ban kuma san ranar warakarsa ba.

Bayan shigowar tashi tsayuwa ya fara yi akai na na tsayin lokaci, sannan daga baya ya juya ya nufi gaban madubin dake ɗakin nawa yana karewa kansa da halittar jikinsa kallo, ya juyo ya kalle ni cikin kunci da ɗacin rai yace "yanzu saboda Allah kin min adalci kenan Na'eema?" ban tanka masa ba sai ma binsa da nayi da kallo ya ci gaba da magana "me wancan bil'adaman yake da shi wanda ni bani da shi? Ni ɗin nan fa nine jinsin ki, bayan wannan ina da martabar da za'a so ni dan ita, a halitta ma Allah bai hana ni komai na cikar kamala ba. Amma Na'eema ke duk ba kya ganin waɗannan. Na ɗibi tsayin shekaru ina nuna so da kaunata gareki amma hakan bai ta6a burge ki ba. Na'eema na yarda so ɗaya ne kuma kin bada shi ga jinsin da ba naki ba, na san har abada ba zaki soni ba." ya tsagaita maganar yana matse kwalla a idonsa.

Ni kuwa ido kawai na zuba masa kalamansa na yawo a kwakwalwar kaina ina kuma mamakin raunin zuciya irin na Haiman, shi ba wahala yayi kuka sai kace mace. Ci gaba da maganarsa ne ya katse min tunani
Chapter 5 · 0% Book details