← Book details Soyyayar Mutun Da Aljan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 6

Sashe 4

Soyyayar Mutun Da Aljan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shirun da naji babana yayi ne yasa na ɗago kaina dan ganin makomar magana ta. Ai kuwa abinda naci karo da shi ya yi matukar Razana ni ya kuma tashi hankalina...

*Nasmat* ✍
[23/1 17:53] Yar Mutan Arkillah: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*MARUBUCI...*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari.

👩🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________

📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
[email protected]

Dedicated to the loved Frnds 'yan uwa abokan aiki:
King Boy Isha
Kamala minna
Bamai A Dabuwa Kkm.
Zaidu Ibrahim. Mr. Zaid
Ramadan Mubarak (Mubson)

Mu gudu tare mu tsira tare. I am proud of you guys. Always 🤝

*Page 5*

* * * * *
Hawaye ne na gani fall sun ciko idon baba Malam, kasancewar kansa a sunkuye ya kara bawa hawayen damar surnanowa suka biyo kuncinsa. A take zuciyata ta harba hankalina ya kara tashi. A 6angare ɗaya kuma naji ina nadama da danasanin tunkarar mahaifina da wannan maganar. Kaico na da wannan rayuwar tawa, tunda na kasa samawa iyayena farin ciki. Gashi yau har na kai ga zama silar zubar hawayen Babana.

Sai na fashe da kuka na karasa ga mahaifina na rungume kafafunshi kasancewar yana zaune ne bisa kujera. Cikin kukan na fara magana "na shiga uku babana ka yafe min, dan Allah ka min aikin gafara. Da na san magana ta zata kona ranka da ban zo maka da ita ba baba. Wannan wace irin rayuwa ce dani? Ina son ku ina son yi muku biyayya baba dan Allah kayi hakuri wlh zan janye wannan kudurin nawa koda kuwa zai zamo sanadin fitar numfashi daga gangar jikina. Baba ka yafe min nayi alkawarin kawar da bukata ta Na rungumi taku bazaka koma zubda hawaye akai na ba, sai dai ko in na mutuwa ta ne."

Ahankali baba ya ɗago ni ya zaunar da ni bisa kujerar dake gefensa. Na lura da sauyi sosai a tattare da shi, jikinsa yayi sanyi zuciyarsa ta karaya. Tsawon dakiku babu wanda ya koma yin magana a cikin mu. "Na'eema" baba ya kira suna na cikin sanyi da alamun tausayi a fuskar shi. Ban iya ɗaga kaina ba saboda wata kunyar mahaifina da nauyin sa da nake ji. Na amsa "na'am baba." baba ya fara magana cikin jimami da mutuwar jiki yace "Na'eema kin tuna min da ɗan uwana Jamal ne ta dalilin wannan yunkurin da kike yi akan soyayya. Nasan kinada labarin inada ɗan uwa guda ɗaya jal a wannan duniyar." yaja numfashi tareda sararawa niko nayi nutso a kogin tunani tabbas inada labarin yayan babanmu mai suna Jamal wanda aka ce ya bar gida tun yana saurayi kuma har yau ba'a koma ganin sa ko jin labarin shi ba.

Tsayawar tunanina yayi dai-dai da cigaba da maganar baba. "na san baki san cikakken tarihin wannan ɗan uwan nawa ba, baki san bisa dalilin da ya bar gida ba to yau zan gaya miki. Wannan labarin da zan baki shine dalilin mu ni da mahaifiyar ki na hana ki wata masaniya akan maganin cutar wannan bil'adaman da kike so.

Na tabbatar koda ke ce a matsayin mu irin matakin da zaki ɗauka kenan." baba ya sarara kafin ya fara bani labarin yayansa wato babana Jamal wanda labarinsa kawai na sani ban san shi ba.

"Kamar yadda kika daɗe kina ji Jamal yayana ne uwa ɗaya uba ɗaya, wanda mu kaɗai ne Allah ya azurta iyayenmu da haihuwa. Ba tare aka haife mu da Jamal ba, amma muna da matukar kama. Kasancewar ba wata tsera ce tsakaninmu ba yasa nayi kusa iso shi a girma. Hakan ne yasa da yawa idan suka ganni sai su ɗauka Jamal ɗin ne, gurare da dama nakan amsa sunan shi ga duk wanda ya kira ni da shi. Saboda son da muke wa juna yasa ko kaya za'a yi mana sai iri ɗaya muke sakawa. Haka muka taso har zuwa girman mu. Inda a nan ne mummunan lamarin ya afku."

Baba yai shiru yana share hawaye cikin tsantsan kunan rai ya ci gaba... "soyayya!" ya faɗa da karfi da kuma nauyin gaske. Kafin ya ɗora "soyayya da kike gani abu ce mai matukar hatsari Na'eema, wata irin rikitacciyar soyayya ce ta 6alle tsakanin yayana Jamal da wata gimbiya 'yar sarkin birnin Durgas mai suna Sunita. Sunita ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance wadda masu ittafaki sun faɗa a wannan zamanin babu wata kyakkyawa kamarta a duk faɗin nahiyar nan. Ɗan uwana Jamal ya mace sosai akan son Sunita wadda tunda take bata ta6a jin murya ta wani ko wata ko kuma wani sauti a duniya ba.

Hakan kuwa ya samo asali ne ga kasancewarta kurma, da cutar aka haife ta. Babu wanda ya ankara da haka har saida ta girma ta kai munzalin yi da kuma jin magana. Sai a lokaci kowa ya fahimta da Sunita kurma ce bata ji daga nan mahaifinta sarki Ashwar ya shiga fafutukar nema mata magani tun yana yi da malamai har ya koma kan bokaye, na ruwa dana tudu. Amma ina biyan bukata ya gagara. A cikin haka ne ya sadu da wani hatsabibin boka wanda ya gaya masa Sunita fa bazata ta6a warkewa ba har sai an ɗiga mata sihirtaccin ruwan nan na (ma'al dawa'u) waɗanda can binne a tsibirin Darul iks a cikin kunnenta. Ruwan ko yana can bangon duniya ne a karkashin ikon shahararre kuma azzalumin sarkin nan na bakaken sheɗanu sarki Dawwaz, wanda a wannan duniyar har izuwa yanzu ba'a sami na biyunsa ba a karfin sarrafa miyagun dodanni da sheɗanu na jinni. Baya ga tsagwaron karfin tsafi dana dantsen da yake da su. Jin hakan yasa mahaifin Sunita sarki Ashwar ya saka wata doka ga manema auren tauraruwar 'yar tasa

Cewa duk mai son ya mallaki Sunita da gaske to ya je ya nemo mata waraka ta hanyar samo mata wannan sihirtaccen ruwan na ma'al dawa'u. Wannan ne yasa duk masu tururuwar neman gimbiyar suka ja da baya saboda sanin ɗinbin hatsari da masifar dake cikin tafiya nemo wannan ruwan.

Ya kasance babu kowa a manemanta sai yayana Jamal. Saboda shi tashi soyayyar ta sha bam-bam da wadda sauran suke mata. Wato shi son gaskiya yakewa Sunita."

Babana yaja numfashi yana sharar kwalla. Wannan karon hadda ni kukan nake yi domin jin inda soyayyar gaskiya take, kasancewata ma'abociyar soyayya ina son mai maida hankali gareta da kuma bata muhimmanci.

Tunanina ya yanke ne lokacin da naji baba ya numfasa zai ci gaba da bani labarin...

*Nasmat* ✍
[23/1 17:53] Yar Mutan Arkillah: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*MARUBUCI...*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari.

👩🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
'Yar mutan
Arkilla✍
____________

📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
[email protected]

Dedicated to my sweet Sister *Maryam (Ummu Hanan)* banida wata kalma da zata isa wajen yin godiya ga karamci irin naki. 'Yar uwa ta gari, ɗaya bayan ɗaya kika dinga saudaukar min pages gaskiya Nasmat bazata manta dake ba. Allah ya kara ɗaukaka min ke yasa kifi haka. Sabon littafi 👄SURAYYA👄 kuma Allah yasa an fara shi a sa'a yasa a gama shi lfy. 'Yar mutan arkilla na yin ki Maryam ki huta ta wajena. 🤝

*Page 6*

* * * * *
"To a lokacin ne Sunita ta kamu da tsananin son Jamal domin bayyanar mata da yayi a matsayin masoyinta na gaskiya. Ya zamana bata son rabuwa da shi, kullum suna tare dare ne kawai yake yi musu shamaki.

Cikin wannan hali ne ɗan'uwana ya yanke hukuncin tafiya nemo wannan ruwan domin samun Sunita ta zama mallakinshi na har abada. Fama sosai yasha da iyayenmu a kan wannan tafiyar domin su basu lamunta ya tafi ba. Har saida ya haɗa da turo musu manyan garin nan da dattijan da ya tabbatar suna jin kunyar su sannan ya samu suka amince bisa dole badan ransu ya so ba. A wunin da ya samu amincewar su a wunin ya shirya tafiyar domin dama ya daɗe da fara shiri." hmm baba ya sauke numfashi yana daɗa matso hawayen dake idon shi sannan yaci gaba "a wannan ranar nayi kuka irin wanda ban ta6a yin irinshi ba na shiga tsoro da ɗimuwa musamman da naji babanmu na bashi karin haske gameda inda zai tafin. Tunda naji jerin hatsarurrukan da babanmu ke lissafowa yaya Jamal na kan hanyar ma kafin ya kai ga isa tsibirin na darul iks wanda can kam sai abinda Allah ya yi. Sai na kankame shi ina kuka kamar zan mutu, nace babu inda zai tafi dan na tabbata yadda naji labarin wannan hanya in ya tafi ba zai dawo ba. Na tabbata mutuwa zai yi. Domin ni a gani na gwara ka kashe kanka da kanka yafi ka tunkari tsibirin darul iks.

Amma ina kukan ina karawa yaya Jamal yayi sallama da dangi da iyayenmu ya rungume ni ya sumbaci goshina yana faɗin "inda rabon ganawa wata rana Jamal zai dawo gareka Uffar" wannan ita ce kalma ta karshe d'aya furta kafin tafiyarsa. Bai koma cewa kowa komai ba ya juya yana mai karanto addu'ar nan ta neman tsari ya 6ata 6at!. Wannan shine gani na na karshe da yaya Jamal da ni da duk wani dangin mu. Iyayenmu har suka koma ga Allah maganar Jamal suke yi kullum sai sunyi maganar sa. Tun muna koke-koke muna tuna yaya Jamal har muka dangana ga Allah muka daina kukan sai dai addu'ar Allah ya dawo mana da shi. Domin har babanmu ya cika yana gaya min cewa ɗan'uwana yana nan a raye bai mutuba, amma yana cikin mawuyacin hali. Wasu lokutan har ji nake kamar nima in fita inbi bayan Jamal dan nemo shi, amma idan na tuna ni kaɗai na rage a zari'ar mu sai inji ina son zama donmi tada gidan nan.
Chapter 4 · 0% Book details