← Book details Soyyayar Mutun Da Aljan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 6

Sashe 2

Soyyayar Mutun Da Aljan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ummy lafiya?" na tambaye ta cikin karfin hali da dakewa. "wai ke wacce irin kafaffiyar yarinya ce Na'eema?, kin kuwa san irin wahalar neman ki da aka sha yau? Duk faɗin nahiyar nan babu inda ba'a watsa Barade neman ki ba, ashe wai kina nan gun wannan bil'adaman kina gadin sa." maganganun Ummy basu bani mamaki sosai ba domin na saba da jin ire-iren su har ma da waɗanda suka fisu daga gareta a kan Muhsin. Abu ɗaya ne ya tsaya min a maganarta inda take cewa 'babu inda ba' a watsa Barade nema na ba'. To yau kuma me na yiwa Sarki da har za'a baza Baradensa nema na?.

Ummy ta kalle ni rai a 6ace "to tunanin me kike kuma? Maza ki zo mu tafi tsawon awanni Sarki da jama'arsa suna zaman jiran ki." tana kaiwa nan ta kama hannuna daga ni har ita muka 6ata 6at!.

Al'amura sun cakuɗe a matashiyar kwakwalwata, ban gama warware sarkakiyar farko ba Ummy ta koma saka ni a wata. To me kuma zai sa sarki da jama'arsa jira na?. Ina cikin wannan tunanin ne nida Ummy muka bayyana a babban ɗakin baki na mahaifina Malam. Inda naci karo da wani sabon abin mamaki wanda ya haɗu da maganganun Ummy ya cure min a kwakwalwa. Duk da cewa waɗanda da naci karo da su ba bakin fuska bane a gurina, amma ina mamakin taruwar su a gidanmu kuma har ake nema na.

Babu yanda na iya haka na adana tambayoyi da mamakina, na zube kasa na kwashi gaisuwa ga sarkin Aljanu na nahiyar baki ɗaya sarki Shadad. Da uwar gidansa Ummu Haiman da kuma shi kansa babban ɗan nasu Haiman. Suka amsa mini gaisuwar cikin sakin fuska da kauna kamar dai yadda suka saba musamman Haiman wanda shi kallon so ne karara yake jifa ta da shi. Ni kuwa na basar nayi kamar ban san abinda yake ba. Sauran kuyangin gimbiya Ummu Haiman da fadawa yan rakiyar sarki suka zube kasa suna gaishe da ni. Na amsa cikin nuna kulawa sannan na mike na matsa can kusa da kujerar da mahaifina yake kai na zauna dab da kafafunshi ina mai sunkui da kaina alamar girmamawa gareshi.

Baba Malam yayi gyaran murya ya 6oye 6acin ransa na nema na da aka yita yi tsawon lokaci, saboda yasan na wuce ayi mini faɗa a gaban sarki. Duk kuwa wanda yayi to zai ga 6acin ransa, domin sunan mahaifiyarsa gareni.

Ba tare da ya kalle ni ba ya fara da godiyar Allah sannan ya fara magana kamar haka: Allah ya ja zamanin sarkin sarakai ga yar' taka nan an samo ta. Saboda haka sai ka yi mata bayanin maganar da ka zo da ita domin taji daga gareka. Sarki Shadad ya gyara zamansa ya dubi inda nake zaune fuskarsa ɗauke da murmushi yace "maraba dake ya'ta kuma uwa'ta Na'eema, kamar dai yadda kika sani yaron wajena Haiman yana matukar kaunar ki wannan ba maganar yanzu bace abu ne da kowannen mu ya sani. To bisa wannan ne yau na ɗauko kafa da kaina nazo neman auren ki yake wannan yar mai daraja da cikar kamala da fatan zamu sami amincewa, haɗin kai da kuma goyon bayanki." jin ya kai aya a zancensa yasa na ɗago a hankali na fara da kallon iyayena waɗanda nake ga kamar basu yi mini adalci ba, na nemo ni da suka yi suka zaunar a gaban sarki har ya tunkare ni da wannan magana a matsayinsu na waɗanda suka san sirrina sama da kowa. Sannan na rausaya kaina na kai duba ga yarima Haiman wanda yake jin kansa kamar a aljanna saboda tsananin daɗi da farin ciki na abinda yaji mahaifinsa ya ambata. Kasancewar a rayuwarsa babu abinda yake son ji da gani sama da ni. Wani kasaitaccen murmushi ya sakar min mai kunshe da sakonnin so da kauna. Hakan yasa nayi gaggawar kawar da kaina gareshi. Duk da cewa nasan yarima Haiman na tsananin kaunata amma hakan bai ta6a sawa na kalle shi kallo na masoyi ba, balle har na yi tunanin kasancewa mallakinsa. Ni kam bil'adaman nan da basa so Muhsin shi kaɗai na ta6a jin son shi a zuciyata kuma shi kaɗai nake ji zan yi farin cikin kasancewa da shi.

Jin shirun yayi yawa ne yasa mahaifina ya fara magana "kin yi shiru Na'eema?" na kara yin kasa da kaina dan ban san kalar amsar da zan basu ba, na tabbata yin shirun nawa zai fi buɗar bakina zama alkhairi domin bana so iyayena su yi kunya ta dalilina.

Can na jiyo murmushin mahaifina yace "Alhamdulillah dama na san ya'ta ba zata watsa mini kasa a ido ba. Allah ya taimaki sarkin sarakai a matsayina na mahaifin Na'eema na bawa yarima Haiman aurenta. Kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci a shirye nake da aurar da ita gareshi, yanzu wuka da naman suna hannunka."

Kaina na sunkuye a kasa ban san lokacin da na ɗago shi ba ina kallon fuskar babana Malam. Na rumtse ido cikin tsananin karfin hali da jarumta domin yadda naji saukar kalaman nashi sun fi kama da yayyafin ruwan narkakkiyar dalma bisa fatar jiki. Duk da cewa baba Malam ya gano halin tashin hankalin dana shiga amma sai yayi biris kamar ma bai san ina yi ba.

Sarki Shadad ya saki fara'a cikin jin daɗin maganar ya kalli babana "na gode Malam Allah ya kara girma da ɗaukaka, Ubangiji yasa auren Haiman da Na'eema alkhairi ne." "ameen" fadawa da kunginsu suka amsa. Da haka suka yi sallama zasu wuce inda yarima Haiman ya nemi a bar shi yana son magana da ni.

Takaici da bakin ciki kamar zasu kashe ni amma ya zan yi? Har in koma ga Allah bana fatan bijirewa umarnin iyayena. Wani ke6a66en lambu dake can bayan gidanmu muka tafi da yarima Haiman wanda duk wani motsi nawa bisa kwayar idonshi. Duk wanda ya kalle shi a yau ya san yana cikin farin ciki mara misaltuwa. Sa6anin ni da kallo ɗaya za'a gano ina cikin damuwa. Domin duk yadda na kai ga son farantawa iyayena ba zan iya danne damuwata in hana mata bayyana ba.

Muka zauna kan lallausar shimfiɗar dake baje bisa korayen ciyayi a bakin wata korama. Na kalli wurin da ni'imarsa, hakika wannan shine wurin da ya kamata a ce masoya sun kasance a cikinsa yayin yin hira irin ta soyayya. Amma ni gani a ciki ni kaɗai ba tare da masoyina ba. Na koma kallon yarima Haiman idanunshi a kaina, na kauda nawa idon ina jin haushin kasancewa ta da shi a wannan wurin.

Ganin banida niyyar yin magana yasa ya buɗi bakinsa cike da tsumi na soyayya yace "yake masoyiyata Na'eema shin har yanzu kina nan a kan bakarki ta ki na?, naga duk wannan batu da ake bai sa farin ciki ko kalilan a zuciya da kyakkyawar fuskarki ba."

Na kawar da kaina gefe sannan na buɗi bakina wanda tun ɗazu nake ko'karin kulle shi, saboda na tabbatar duk abinda zai fita a cikinsa yau ba mai daɗin saurare bane. Nace...

*Nasmat* ✍
[23/1 17:53] Yar Mutan Arkillah: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*MARUBUCI...*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari.

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
Yar'mutan
Arkilla✍
____________

📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
[email protected]

*Page 3*

Alaka alaka ce kamar yadda so yake rikiɗewa ya zama kauna. *ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION* Na yarda da kaunarku GAREMU. Babu shakka aminci ne mai karfi tsakani mu *ZAMANI WRITERS* daku. Fatan mu a nan Allah ya bar zumunci da kaunar juna. Nasmat da ɗaukacin members na *ZAMANI* suna yin ku irin totally ɗin nan, ku huta 🤝 *Shamsiyyah Salis* naki daban ne Allah ya kara basira da zakin hannu.

Cikin zafin rai da ɗacin zuciya "kaicon ka yarima Haiman, shin me ka yiwa wannan zuciyar taka ne da har take ingiza ka take tursasa ka son wadda kake da yakinin cewa bata sonka ba kuma zata ta6a sonka ba?." dama nasan a rina. A madadin Haiman yaji haushin kalamaina sai na tsinci wani lallausan murmushi a kan fuskarshi.

Al'amarin da ya kara zafafa zuciya ta kenan, da har zan koma wurga masa wata mummunar maganar sai zuciyata tayi gaggawar kwa6a ta, tare da yi mini tuni a kan ko wane ne Haiman. Nan da nan sai na sassauta fushina na fara kirkirar abinda na san shi kaɗai ne zai sa Haiman ya saurare ni kan wannan batu. Kuka na fara yi ina zubda hawaye. Ai kuwa da sauri Haiman ya tashi daga kishingiɗar da yayi ya zauna da kyau ya fuskance ni, cikin tsananin ruɗani.

Dama na sani idan kalamaina basu ruɗa shi ba kukana zai nutsar da shi. Sai ya shiga magiya yana roko na a kan in taimaka in daina kukan nan zai fahimce ni. Ni kaina ina mamakin tashin hankalin da Haiman ke shiga idan ya ga zubar hawaye na wannan shi ne dalilin da yake sawa na yarda cewa Haiman *son gaskiya* yake yi mini. Amma fa sanin hakan bai ta6a sawa na ji tausayinsa ko da na rana ɗaya ba, wannan ne yake tabbatar min cewa bana son Haiman ba Kuna zan ta6a sonsa ba.

Na kalli yadda hankalin jarumin ɗan sarkin ya tashi saboda ganin zubar hawayena. Tabbas so na musamman ne, duk wanda kaga bai girmama so ba to bai tsinci kansa a ciki bane.

"Haiman" na kira sunansa cikin muryar kuka. Ya amsa idanunshi da nutsuwarshi duk suna gareni. "Haiman wallahi bana sonka, ba kuma na tunanin zan so ka koda a gaba ne. Ban san ya zan yiwa zuciyata ta so ka ba da nayi Haiman. Dan Allah ka taimake ni ka bar ni, ina da wanda nake so. Muhsin shi kaɗai zuciyata ta yarda da shi a matsayin masoyi ka taimaka min yarima." na tashi na tsuguna a gabanshi ina ko'karin kama kafafunshi.
Chapter 2 · 0% Book details