Part d'in Zainab ya shiga hankali a tashe Zainab tace Haihuwar ce Daddy?"
So Halitta Ne Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 42 min read
Eh yace mata itama hankalinta ne ya tashi, ta kashe gas ta d'auko mayafi Daddy ya d'auko kayan haihuwa sai asibiti.
A asibiti kuwa labour room akai da Husnah sai salati take ta na tunano mahaifiyarta da a haka ta rasu, jin k'aunarta take sosai. Su Zainab na zuwa Husnah ta haifi d'a namiji wata sabuwar nak'udar ce ta tashi kira take a kira mata mijinta dan Allah, doctor Imran da Daddy yasanar da shi, tun kafin haihuwar ta zo kar ya k'arba da akansa, ya bawa Dr.fatima shatatima ta karb'a yasa Dr.Imran bai shiga d'akin ba.
Dr fatiman ce tasa a Kira Daddy yana shiga ya nufi wajen Husnah rik'e masa hannu tayi gam gam tace"ka yafemin mutuwa zanyi ba zan iya haihuwar nan bahhhh wani nishi ne ya tawo mata kan d'a ya fara fitowa Dr.fatima tasa hannu ta fara taimaka mata dan zaro d'ayan Daddy da ya fara hawaye yana cewa sannu my baby zaki haihu lafiya inshh.....kukan d'ayan jaririn ne ya katse shi da farin ciki ya karb'i yaron da ke hannun Dr. fatima d'ayan da wata nurse take gogeshi dan ta shiryashi shima ya yi kuka, Daddy ya kalli na hannusa ya kalli na hannun nurse d'in yace du nawa ne likita?"
Dr.fatima tayi murmushi tana gyara Husnah tace"du naka ne Mr.A.S Yunus, congratulation"
Yaron hannunsa ta k'arb'a ta d'ora akan k'irjin Husnah, ta yanke cibi,Husnah da taji kamar an zare mata k'aya sai gumi take yi. Daddy ya rik'e ta yana ta faman jera mata sannu sai albarka ya ke sa mata.
Yaran aka shirya Dr.fatima tace zatayiwa Husnah d'inki, Husnah tasa kuka ta ce "Dan Allah kar ka bari su yimin har yanzu wahalar bata k'are ba" kowa sai da ya yi dariya ganin yadda take wa miji shagwab'a a labour room d'in.
Daddy yace"Dr. karkuyi mata d'inkin nan ku barta da wahalar da tasha mana" Dr.fatima tace "A.S.please ka tafi mungode" yaron d'aya ta bashi nurse ta rik'e d'ayan suka fito daga d'akin.
Dr.fatima tace"kina kar a d'inke ki haka za'a barki gabanki a bud'e to Wallahi idan ba'a yi ba, kinta ganin wulak'anci kenan wajen miji, duk wannan rawar gindin dayake wannan abun yake yiwa ingayamiki dallah gyara,Ina da abin yi".
Haka Dr.fatima ta d'inke ta tas,duk kunya ta ishi Husnah gyarata su kayi tsaf toilet ta shiga ta wanke jikinta ta fito kaya masu kyau tasa kamar ba ita ta haihu ba aka fito da ita zuwa d'akin hutu.
Zainab ta rik'e d'aya tace"Ni dai wannan ne babana dear" .Hajiya Batulu ta d'auki d'ayan tace "Masha Allah ga Malam ya iso duniya Allah ya ra'aya mana ku"
Daddy da farin ciki ya cika shi yace"Allah ya yi musu albarka".
Su Usaina da su ka ji Haihuwar daga sama dan ba su fara fita ba, Baba Malam ya hana suma a barsu fita sai gasu a asibitin kafin wani lokaci asibiti ya cika da MalamYunus's family sai murna ake an samu k'aruwa......
Bayan su Hindatu sun shirya da Salisu aka ci lgaba da zaman ibadah.
Mutanan Ikeja ma da cikin yakai wata takwas waya Daddy ya yiwa Salisu ya sanar da shi haihuwar Husnah, Hindatu ta rik'e baki tace"lahhh daman Husnah itama ciki ne da ita,tai tamin tsiya har da cewa mijina k'iris yake jira ashe, ashe nata mijin ne mai jiran k'iris wata Tara da aure ta haifi 'yan biyu" Salisu yace"Wallahi kuwa muma Allah ya sauke mu lafiya, ai damu za'ayi suna insha Allah sai garin Kano nan da kwana biyar,Amma yanzu sai mun fara zuwa 'Danmarina sai mu wuce" . Hindatu tace"ai Wallahi sai na rama duk tsiyar da ta dinga yimin nima" Salisu yace"da wannan abun yana nuna cikinta da ya girma" baki ta turo tace"ai dai bai Kai naka ba" Salisu ya yi dariya yace"tab wayaga mai ciki"
Hadiza ma da Inna Gaji ta sanar da ita murna tayi tayi ta kira Husnah dan yi mata barka wayar tayi ta ringing ba'a amsa ba,dan tana gida a kan mirror, haka suma su ka ce sai zuwa kano sunan autarsu.
A gida Husnah take jegonta, ranar suna yara suka cu sunan Mahaifin Zainab da Malam yunus ana kiransu Hassan da Hussain, ansha sha'ani kowa ya zo dangi na kusa da na nesa, su Hindatu ma duk sun zo, akayi taro lafiya kowa ya koma gidansa lafiya.
.bayan wata d'aya da sati d'aya Hindatu ma ta haihu ta samu 'ya mace, itama gida Salisu ya kaita wanka wajen Inna Gaji, yanzu komai lafiya tayi arba'in Salisu ya zo su ka koma Lagos Ikeja.
Husnah ma ta koma gidanta da yaranta, yawanci wuni a part d'in Zainab su ke nono ne kawai ya ke kaisu wajen uwarsu, zaman su suke cikin fahimtar juna.
Bayan wasu kwanaki Halima ta sake haihuwar mace aka sa mata sunan mamanta Aisha.
Hassana ma ta haihu namiji Muhsin, Usaina ce dai sai kwanan nan ta samu ciki, sai dai fatan Allah ya raba lafiya.
Su Inna Gaji anje makkah an sauke farali, angyara musu gidansu ya zama na zamani kaf unguwar gidan Inna Gaji ya fi kyau da tsari komai Daddy ya zuba musu agidan har solar.
Rayuwa ta sauya musu, cikin kwanciayr hankali da jin dad'i Hadiza ma ta sake haihuwar mace aka sa mata sunan Inna Gaji Maimuna ana kiranta da Islam.
Bayan shekara biyar
Ahmad ne ya zama saurayi dan shekara ashiri gaba d'aya ya koma Daddy sak,har had'e ran irin na ubansa ne, d'akinsa yana part d'in Husnah, Hamid da 'ya biyu ne a part d'in Zainab Ikram ma tana wajen Maminsu, Husnah ta sake Haihuwar mace, an sa mata sunan Mahaifiyarta Fatima ana kiranta da Mukarrama.
Yanzu Ahmad da Ikram da Mukarrama ne awajenta.
Zainab kuma Hamid da Hassan da Hussain ne nata Hussain shine ya biyo babban yayansu Ahmad komai nasa ya yo, har rashin son hayaniyar su ma ansa su a school Ikram na k'ok'arin koya musu home work.
.Husnah ta koma karatu yanzu haka ta na karantar Journalist a bayero University Kano.
Hankalin Daddy ya kwanta iyalisa lafiya lau.
Hakama wajensu su Hadiza da Hindatu Dan duk sun koma karatu, sun k'ara wayewa Hindatu da zama cikin k'abilu ya k'ara nutsar da ita, duk wani sharme ta daina shi....
ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
duk kan yabo da godiya sun tabbata ga Allah da ya bani ikon gama wannan kittafi mai suna SO HALITTA NE. Lafiya
Ina fatan za'ayi koyi da abu mai kyau da ke cikin littafin sannan a yi watsi da mara amfanin da ke cikinsa.
Sai mun sake had'uwa a littafina na gaba mai suna 'DAUKAR FANSA............
Bayan sallah. Zaku samu littafin akan kud'i k'alilan insha Allah. N200ne kacal
Domin karin bayani ki tuntub'emu ta wannan number 08107916039.
Ina fatan Allah ya sa muyi azumi lafiya mu gama lafiya, Allah yasa muna daga cikin 'yantattun bayin ake 'yan tawa a watan, ya biya mana dukkakn buk'atunmu na alkhairi Amen.
Writing by R.Hussain and Norry
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*
J.A.W
DEDICATED TO OUR FANS
Page 1
Zau ne take kofar d'aki kan wata yank'wananniyar tabarma sai faman uban hamma take kai da ganin ta kasan yunwa ke dawainiya da ita
"Salama alaikum marka marka ko ba kowa ne a gidan?
Husna tai saurin tashi "wa'alaikummussalam sannu da zuwa Baba" dillaliya, ta bini da harara "ke ina mutan gidan ne? Tsoro da fargaba ya kamani ta.....na...tana ta tafi barkan haihuwa makwabta"
"Gafaranku dai aaaaaaah wana ke gani kamar dillaliya? Inna gaji ke fad'a cikin tsananin farinciki yau burinta xai ciki zata bayar da Husna akaita birni ta huta da ganinta cikin gida hmmm "Nice d'in dai Gaji , lale
Kano state G.R.A quarters
Wata shaharriyar mace ce Ke ta faman kai kawo a bed room d'inta da ganin ta tana cikin damuwa ta kasa zau ne ta kasa tsaye why? why? My loml gaskiya impossible "kamarni Hajiya ZAINAB ka dinga wa haka
Me kanema ka rasa a rayuwa ni kam gaskiya ba zan bari dan ginka su d'au ke ma hankaliba
Mutsiyata Wallahi basu isa suyimin kutse cikin plan d'ina ba
Hmmmmm tayi wari irin Jan numfashi ta fesa.........
D'and'ano daga littafin SO HALITTANE
Yawan comments yawan typing
[4/18, 12:22 PM] +234 803 362 6868:
SO HALITTANE
Writing by R.Hussain and noory.
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantaw
a ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_

DEDUCTED TO OUR FANS
Page 2
Tafe yake yana ta sauri kamar zai kifa Tun da ya tashi da safe yake jin jikinshi ba kwari ,haka dai ya daure ya fita nema dan yasan idan ya zau na yau to ko ruwa Inna Gaji ba za ta bashiba bare yasa ran matar qaninsa marka zata ba shi. ga marainiyar 'yar shi Husna da tazama baiwa a gidan ba me kaunarta
Kaf gidan
A haka ya shigo cikin garinsu Dan marina da ke qaramar hukumar ringim ta jahar jigawa
"A'ahhhh malam Musa sannu da zuwa " "yauwa malam tanimu" malam musa ya fad'a yana me
mika masa hannu suyi musabaha
Ya wuce gidan shi
Sallama ya yi yana ajiye buhun sa
Husna ta tashi da sauri "sannu da zuwa Baba ta duka ina wuni ? lah......,.. Keeee!! tsawar da inna gaji ta daka ne yasa Baba kasa magana ya wuce d'akinshi
Bak'ar munafuka ta fad'a tana me tashi tsaye
Baba dillaliya ta yi saurin riqota.
Haba Gaji so kike ki rusamana shiri ta fad'a cikin rad'a
Tini jikina ya hau rawa
Knocking d'in da akeyine ya dawo da shi cikin hayyacin shi Alhaji Abubakar mai gold kenan Yong man ba zai haura shekara arba'in da biyu ko d uku ba
Amma naira ta sa ba zaka ta6a tunanin ya haura talatin da biyar ba lumshe sexy eye din shi ya yi "yes come in"
Ya fad'a tare da yin balancing a kan chair d'in
Sakatariya ce ta shigo "yes sir you have a guest"
Ya dago cikin damuwa who?
"Mrs. Galandanchi" ce oh my God ya fad'a yana dafe foreheard d'in shi,
OK......,.
Dandano daga littafin SO HALITTANE.
Yawan comments yawan typing
[4/18, 12:22 PM] +234 803 362 6868:
SO HALITTANE
Writing By R. Hussain and noory.

DEDUCTED TO OUR FANS.
Jinjina a gareku
IKLIMA(Kyauta daga Allah)
UMMU AMSAD.
Allah ya bar Zumunchi
Page 3
GARIN 'DAN MARINA
Inna Gaji ta wuce fuuuuuu ta shige d'aki " Dillaliya shigo mana"
Toh toh" ga ni nan Gaji tana me garasa shiga 'd'akin, Zau ne ta tadda Gaje gefen gadon karfen ta.
Dillaliya ta zau na kan ta barmar da ke kasa.
"Yan zu ga shi malam ya dawo
Ya maganar mu ne Dillaliya? Gaji ta fa'da ta na kallon aminiyar ta ta.
" ai yau d'in nan zamu shirya komai na barin Husna gidan nan, kafin Marka ta dawo kinsan batasan da wannan maganar ba,
duk da dai dalilinta nasan ki
Amma nafison 'kulla harkar arziki da ke.
Sabida Kinga wannan yarinyar muddun ta higa burni za ki samu alheri Alqur' an."..
"To ai baki sa ni ba, kinga dai su Hadiza da Hindatu su ne manya ko?
Amma malam ya fi kaunar wannan hegiyar yarinyar ni kuwa ba zan bari 'ya'yana su wulaqanta ba.
Idan ta 6ace ai dole a dawo kan nawa 'ya'yan duk da dai nasan Ba su ji, yo amma ai Tahen balagane za su de na ne" Ta fa'da irin I don't care din nan
" ai kuwa gaskiyar ki Gaji, yan zu dai aike ta rafi d'iban ruwa
Ni kuma zan hilace ta ta bi ni sai mu tafi can burnin da ita, yan zu magariba ya kawo kai mu kwan tasha asuban fa ri mu ta fi"
"Hahhahhahh
hikenan kam kin kawo shawara.
Sai a ce ta gudu yawon dandi wa yan gari akayi a ka ga ta gudu yawon dandi"
Hmmm" ba ri ki gani
Husnah! Ke Husnah !!
"Na'am na amsa cikin hanzari ga mi da tawo wa dakin Gaji salama alaikum, inna gani"
Ki he ki 'debo ruwa ko so ki ke mu rasa na alola ne da safe eyeee? Ko kuwa sai mangariba ta yi Ki sa mutane zagina a gari Eyeeee?
"A'a inna to na miqe ga mi da gyara cukurku'de'd'den zani na na dau bokiti ta fita ina sauri kar duhu ya yi.
" To Gaji ni dai zan koma sai kuma ankwana biyu kuma"
" har za ki koma dillaliya to hikenan ki gaida gida, idan ansamu turmi me 'dan sauk'i ki ka wan"
"To mu kwan lafiya,dillaliya ta fa'da ta na fi ce wa daga gidan.
* * * *
"Okay shigo da ita " "OK sir," sakatariya ta fad'a ya juya.
Hajiya Halima zau ne a reception, ta yi a do kana ganin ta kaga manyan mata Mrs.Galadanci kenan.
" Hajiya ki shiga" sakatariya ta fa'da
Hajiya Halima ta Mik'e ta na gyara mayafinta ta bita office d'in Al.Abubakar, abokin mijinta Habib Yakub Galadanci.
Tura door din tayi tare da sallama
Alhaji Abubakar ya gyara zama "barka da zuwa Hajiya Halima" hmmm barka dai Alhaji. Ya aiki?
"Alhamdulillah Mrs.Galadanci, ya hanya?
" Fine" ta fa'da a takaice.
Sukayi shiru na d'an lokaci .
"Hajiya lafiya dai ? Inji Alhaji.Abubakar "
Hajiya Halima ta d'ago kanta ci ke da damuwa sabida halin ko in kula da mijinta ke ma ta.
"Alhaji. Nagaji da abin da Abban yazeed ke min sai hawaye.
" Subhanallah Hajiya meyafaru, Ina baya 'kasar ma ko?
"Eh yau ki manin four months kenan rabon da mu sa shi a idon mu.
Tun meenal, na tambayanshi har ta dena, kullum cewa ya ke wani aiki
ya rik'e shi idan nace zan zo ya hau ni da fa'da".....
" ikon Allah
Alhaji Abubakar ya fa'da aranshi (Ni ina fama da damuwa a kan Zainab
Ita kuma akan mijin ta).
Ki yi...,..
Yasan comments yawan Typing
[4/18, 12:22 PM] +234 803 362 6868:
SO HALITTANE
Writing By R.Hussain and noory

DEDUCATED TO OUR FANS
Jinjina gare ku
ILKIMA(Kyauta Allah)
UMMU AMSAD.
Allah ya bar Zumunchi
Wannan Page din naki ne my qawa maman iklas(Mrs soldier).
Mun godiya da comments din ki
Page 4
and 5
"Ki yi hak'uri Hajiya Zainab zan yi ma sa magana insha Allah komai zai dai-daita. Pls stop crying, sorry pls"
Ya fadya ya na mik'a ma ta tissue, ta kar6a "nagode Alhaji
Ba ri nakoma"
Ki sha ruwa tukun na
"A'a nagode Azumi na ke yi ne"
Okay don't worry, ki kara hak'uri"
Ba komai nagode ta fad'a tana barin office d'in.
Ethiopia
Alhaji.Habib Yakub Galandanchi ne zau ne akan plastic chair a compound din gidan shi, idon shi sanye da medical glass ya na duba magazine,
Wayar shi ce ta fara ringing.....
Samuel da ke gefe ya yi saurin duba wa
"Sir Alhaji.Abubakar on the line"
Okay pick it yana me kar6ar wayar
"Aslamu alaikum
Lafiya lau, ya Nigeria?
Mashaallah.
Daga can gida Nigeria kuwa Alhaji.Abubakar ne zau ne a falon shi ya na waya da aminin nashi Alhaji. Habib Galadanchi
" Haba Alhaji. Habib ya'za ka yi haka?
Da iyalinka da komai ka tafi Ethiopia ka yi zamankan ka
Ka k'i dawo wa,
Ga matar ka hankalinta ya k'i kwanciya kasan mata"..
"Hmmm Alhaji.Abubakar kenan ,
Inshaallah next week I will come back, Wallahi wa su abubuwa ne su ka rik'eni, Ni ma na matsu na dawo gida ai.
"To ya dai kamata ka dawon, daga
Can Alhaji. Abubakar ya fad'a"
nagode"
Okay yana mik'awa Samuel wayan.........
* * * *i na ta sauri in debo ruwan
"Husna! Husna!! Baba Dillaliya ke ta 'kwala min kira
" Na'am" zo nan
Na 'ka rasa gurin ta
"Ajiye bokitin nan mu je,
Wani aiki za ki yi min.
Haka nan na ji gabana ya fad'i
ga tsoro da ya kama ni.
" ajiye mana mu je,
Na ajiye bokitin, ina addu'ar Allah ya sa kar a sa ce min kafin na dawo
na bi ta.
Cikin ikon Allah har muka bar garin ba mu had'u da kowa ba
Har mu ka isa tasha .
Tu ni cikina ya murd'a na shiga uku !!!
Ina za ta kai ni hawaye ya fara bin fuska ta, wa ta rumfa na ga mun shiga.
" a'ah Dillaliya har kin dawo ga shi sun gama lodi kuwa"
Wata ma ta ke fad'awa Dillaliya.
"Yo banda abinki Hauwa ai na sa ni sakko zanyi ne ai
Shigo ma na Husnah"
Na shiga cikin rumfar na raku6e a gefe cike da fargaba na ce "Baba dillaliya ni zan ko ma, kar a ga na dad'e ban koma ba.
" Ina za ki koma kuma Husnah?
Burni fa za ki"
Burni? Na Mike cikin tsanin tashin hankali...
"Eh kun ji hegiyar yarinya arziki na kiran ki ki na shurewa, yo idan kin zau na nan d'in Uban me ki ke tsina na wa?
Ga ki dai da kyan da dirin jiki
Amma na ban za
Na ban za ma na.
Bak'in jini ya mi ki katutu a jiki,
Ko tallah ki ka d'auka ba ki Sai da shi sai dai ki ta jawa Gaji asara kinyo gadon bak'in hali irin na uwarki to burni Za ki je ki yi aikatau ko a samu kud'in da za'a yi miki magani a cire jinin mujiya a jikin ki ko kya sa mi mashinshi ni a heeeee!!!!!
Duk abinda Baba Dillaliya ke fad'a ba ji na ke ba sabida tsanin tashin hankali da na shiga. Ga shi ba damar guduwa, dan Masan wannan shirin inna Gaji ne.
" wayyo Baba na na shiga uku kuma na ke yi tamkar rai na zai fi ta.
Hajiya mai rumfar na ta ba ni hak'uri ta na gayamin mahimmancin aikin da zan je yi a burni
da kuma abin da za'a min da kud'in
Magani da a ne ma min da kayan d'aki.............,.

SO HALITTA NE
Writing By R.Hussain and noory
DEDUCTED TO OUR FANS
Page 6
Yara ne zau ne a falo su na T.V game Ahmad da Hamid su 'yaya ne ga Alhaji.Abubakar da Hajiya Zainab,
Ahmad dan k'imanin shekara sha daya,
Hamid ke bin shi dan shekara tara
su na tayi game din su cikin nishad'i
sai autarsu Ikram wacce ta ke 'yar shekara hudu sanye ta ke da riqa da wan do ma su kyau
da tsa da ta na ta baccin ta a kan one setter, kan ta yasha kitso mai kyau da ribbon.
'Ya'ya ne ga Alhaji Abubakar mai gold da Zainab.
Hajiya Zainab ta kasan ce mace ce mai tsananin kishi, da kuma son abin duniya,
Dalilin haka ne ya sa ba ta son dan gin mijin na ta su ra6e sa, don duk cikinsu shine mai kud'i.
Amma dai su na da rufin asirin su dai
misali.
Zainab 'ya ce ga honorable Sammani Kura, fitaccen dan siyasa ne .
Alhaji Abubakar ya aure ta ne dalilin zuwanta shagon shi za ta siyi Gold, lokacin ya na zama a d'aya daga cikin shagunan shi.
anan su ka had'u suka K'ullah alak'a har ta kai su ga aure,
Alhaji.Abubakar d'a ne ga malam inusa da Hajiya Batulu.
Shine D'a na uku a gidan Muhammad ne babba,sai mai bin shi Hamza, sai Abubakar, sai K'an war su Asiya, sai kuma Hassana da Hussaina. Su shida ne sun taso da tarbiyya da k'aunar juna.
Malam Inusa asalin shi d'an k'asar Niger ne cikin garin Marad'i , fatauci ya kawo shi garin Kano
Anan ya had'u da Batulu wacce ta ke kawo tallan fura da nono kasuwar kwari da ke kano,
Anan su ka hadu har ta kai da soyayya ta shiga tsakanin su har ta kai su ga yin aure.
Muhammad shine Babba ya na da mata biyu Aisha da Maimuna, su na zau ne lafiya ta re da yaransu Aisha ita ce uwargida ta na da 'ya'ya biyar,
Khadija, Hafsa, Fatima,Najib, da kausar.
Maimuna ta na da uku iliyas, umar, usman.
Khadija ce babab sai Hafsa
Sai iliyas, sai Najib ( sa'anni ne su)
Sai umar sai usman sai auta kausar....
Hamza kuma matar sa d'aya ya Binta
Yana da yara biyar, Yusuf, saifullahi,safiyya, saratu,da kuma maryam.
Sai Asiya ita a Kaduna ta ke aure ta na auren Malam. Isma'il shi malamin makaranta ne.
Su na da yara shida,
Nazifi,Aliyu, yasir, Batulu(momy) da ummussalma.
Kasan ce war duk sun rugashi aure sai yaransu yawanci sun girmi 'ya'yan sa. Qananan 'ya'yansu su ne suke sa'annin su Ahmad da Hamid da ikram.
* * * *
WACE CE HUSNAH?
Malam musa shi ne sunan mahifin Husna ya kasan ce talaka ne ya na sana'ar kayan koli a can wajen garin su Dan marina, Malam Musa ya na da mata mai su na Inna Gaji, Inna Gaji ta haifi 'ya'ya da dama, amma ba su tsawon rai sai su koma.
Sai akan Hadiza da Hindatu su Allah ya bar ma ta daga nan sai haihuwar ta tsaya.
Katsam ya je gaishe da K'anin mahaifin shi (kanin kakan su Husna)
Sai ya ga Fad'ime K'anwa ce a wajen sa.
Sai Allah ya sa ma sa son ta a zuciyan shi (SO HALITTANE)
Nan da nan ya bayyana ma ta, Allah ya halitta ma sa son ta a zuciya, tun ta na kunya har ta ware da 'yayan na ta,
'Yan uwa sunyi murna da wannan Al'amarin.
Ba a dau lokaci ba a ka sa ranar aure,
Malam Musa ya ra sa yan da Zaiyi ya sanar da Inna Gaji
Katsam inna Gaji ta ji labarin an sa ranar aure.
Ta hau bori da bala'in " Wallahi malam ba ka is a ka auro min yarinyar nan ba, sai da ka ga ma lalatamin mahaifa 'ya'yan su na mutuwa, shi ne zaka auro min yarin ya ta zo tai ta haihuwa ina kallo , to k'arya ka ke yi malam"
Malam musa Ya yi ya yi ta fahimci shi SO HALITTA NE.
" Gaji shi fa aure nufin Allah ne"
"Nufin Allah?
To alk'ur'an wannan niyyar ka ne, kuma baka isa ba"
An kai ruwa rana kafin ayi auren malam Musa da Fad'ima.
Da yake abin na Allah ne sai ga shi anyi, fad'ime ta sha wahala a hannun inna Gaji, Gaji da zarar Malam Musa ya ta fi kasuwa,
To kuwa fad'ime ba ta da kwanciyar hankali, dai_dai da abincin rana ba ta da rabo a gidan nan,
Ko da kuwa ita ta girka shi.
Fad'ime yarinya ce me hak'uri da juriya.
A haka ta sa mi ciki.
Cikin me k'wadayi da yawan amai, haka tai ta fama har ciki ya isa haihuwa.
"Malam da ma na ce ko na koma gida ne wala Allah idan na sauka lafiya na dawo nan din"
Ta ke malam Musa ya had'e fuska, da alama maganar ba tai ma sa dad'i ba.
"Ba inda za ki je, anan za ki haihu fad'ime ga Gaji nan duk wata d'awai ni ya ai naga ta d'auke miki "
Hmmm Malam kenan fad'ime ta fad'a a cikin ran ta,
Makirci ne amma na san ba za ka ga ne ba.
"To shikenan malam , ka yi hak'uri"
Ta fito daga turakar ta koma na ta d'akin.
Wata Laraba fad'ime ta ta shi da nak'uda.
Tun ta na iya fita ba yi ta yi fitsari abun har ya gagara, inna Gaji na ankare da ita se yatsine - ya tsine ta ke " mtswwww ta na tsaki aikin banza, wa ya gayamiki Barno gabas ta ke, kin bud'e ma sa k'afa ya dirka mi ki ciki yo ai ga ranar jindad'in nan ta zo
Bazan ki ra wata unguwar zoma ba aheee ki haihu da kan ki, wa ni ya raka ki turakar?"
Ta ci gaba da wak'ar ta..
Jin nishin fad'ime ya yi yawa ne ta na Jan tsaki mtswww!!!!! Ta shiga dak'in
" yaya ki temakamin" fad'ime ta ke fad'a ta na mik'awa Gaji hannu don ta rik'eta,
"Ke dallah yi min shiru, ni na ce kiyi cikin?
Bari na temaka mini dai fuuuuuuu ta fita daga d'akin.
Ta d'ebo garwashi(rushi) da barkono ta dawo kan fad'ime ta zuba barkonon a garwashin ta tura kan fad'ime nan da nan ta fita hayyacinta.
Cikin ikon Allah ta haifi 'ya mace.
Da Sauri Gaji ta duba ta ga me fad'ime ta Haifa ganin mace ce sai ta cika da farinciki, duk da dai task a haifi cikin ba rai
Amma hakan ma ya yi mata dad'i tun da ba namiji ba ne.
Jim kad'an da haihuwar Jini ne ya tsinkewa fad'ime, ganin haka Gaji ta fita don kar a zarge ta, ta kira me kosai da Rabi mak'otansu..
A gaban idon su fad'ime ta mutu, ga jaririya sai kuka ta ke hannun baba Rabi.
Abun gwanin ban tausayi.
Malam Musa ya ji mutuwar matar shi, har se da ya yi jinya ta kwana biyu kafin ya ware,
Dangi son su a ba su Husna amma Inna Gaji tai ta zu ga malam musa.
Abar ma ta ita su ma zasu iya rik'eta haka aka hak'ura a kabar Ni hannun Inna Gaji.
Hakanan na ta so hannun ta ana ba ni kunu da koko, Baba ya shiga kasuwan cikin gari ya tambayi madarar jarirai ya siya, ya ajiye a shagon shi,
Idan zai dawo sai ya d'ebo kadan ya dama min a dakin sa ya ba ni.
Haka da safe kafin ya fita zai sa ke d'auka ya ba ni madarar. Ba tare da inna Gaji ta sa ni ba sabida idan ya ba ta yasan shanyewa za suyi ita da 'ya'yanta
Hadiza ta tsani Husna tun ranar da Baba ya ba ta ita ta yi mata wanka,
Ta na kar6arta ta yo mata kashi a jiki shikenan ta ke dukanta tun daga ranar ba ta sake d'aukan ta ba.
Hindatu ce me dan tausayin yi mata wanka, da wanki hakan ne kuma ya sa suke d'asawa da Baban na su.
Yan zu Hadiza ta zama me bin shagunan maza, inda za su lallatse ta su ba ta kud'i ta na murna.
Hindatu kuwa tallanta ta ke, idan ta sai da abincin ba ta kawo wa Inna Gaji kud'in du, sai ta raba gida uku ta kai wa inna Gaji kashi biyu ta rik'e kashi d'aya, ga rashin kunya ko Inna Gaji ba ta bari ba
Bare uban kowa.
Hadiza yanxu ta na shekara sha takwas ta ki makaranta sai son maza Kuma duk cikin su ba na aure
Hindatu ta na da sha shida sai fitsara Kuma ta CE makaranta zatayi idan ta so ta na zuwa yanxu ajinta uku a secondary Dan marina
Husnah Kuma yan zu shekarta sha hud'u inna Gaji ta hana ta zuwa makaranta. Shiyasa ba ta iya komai ba.
Yawan comments yawan typing
[4/18, 12:22 PM] +234 803 362 6868: *
SO HALITTANE
Writing By *R.Hussain* and *noory*

Page 7
Hassana da Hussaina k'anne ne ga su Alhaji Abubakar, ba su wuce shekara sha biyar ba, kyawawan yammata.
Suna karatu a AL_HUDAH INTERNATIONAL COLLEGE. School ce da ta tara 'Ya'yan manya,
Kasan ce war su ne Auta a Gidan ya sa duk Yayun su burunsu su inganta rayuwar k'annen na su,
Alhaji.Abubakar shi ne ke daukan nau yin duk wa ni abu da ya dangan ci school d'in su, dalilin haka ya sa Hajiya Zainab ta k'ara jin tsanar su a ranta.
Yansu na S.S.2
Hassana ta na science class, burinta ta za ma doctor.
Usaina ta na art class ne ita kuma burinta ta za ma journalist.
Zau ne su ke a dakin su.
" my sis wannan hutun fa Gidan Yaya Abubakar zam mu je ko?" Hassana ke fada'
" Tabdijan!!! Ni kam bazan je Gidan shi ba, ba re a dinga min kallon wulak'anci, ni da Gidan d'an Uwa na, kin san ba bari zan yi ba.."
"Hmmm kai bloody kenan, to me ye don Allah ba sai ki yi hak'uri ba.
Kin San dai Aunty Zainab d'in nan ha ka take ba sai mu kyale ta ta yi ta yi ba, mun yi ma sa alk'awari fa za muje in mun sa mi hutu fa."
"Sai kuma ki yi tayi ai Usaina ta fice ta na banko ma ta kofar.
" Hum!!!! Allah ya shirye ki bloody..."
Falo ta yi ta na kumbure
ga nin Hajiyan su a zau ne akan praying mat ta na karatun k'ur'ani,
Kyakyawar dattijuwar me shekaru hamsin da biyar,
Idon ta manne da medical glass, domin k'ara k'arfin ga ni, sabida matsalar idanu da ta ke da shi sabida girma ya zo.
Zama Usaina ta yi ta na jin yadda mahaifiyar su ke karantun ta cikin nutsuwa, ba ta tsaya ba har sai da ta kai aya, ta yi Addu'a su ka shafa tare.
Hajiya Batulu ta juyo ta na kallon Autar ta "ya a ka yi ne Auta?
Usaina ta turo ba ki gaba " bloody ce "
" Toh yau kuma, me ta yi mi ki?
Wai wannan hutun Gidan Abban su Hamid za mu je, wai sabida mun yi ma sa alk'awari ran nan...
"Ai kuwa Hassana ta fi ki gaskiya, dole ne ku ci ka alk'awari, kin manta da Hadisin manzon Allah(S.A.W) Wanda ya ke gaya mana alamomin munafiki guda ukune:
Na farko idan ya yi zance sai ya yi k'arya
Na biyu idan Ya yi alk'awari sai ya sa6a.
Na uku kuma idan aka amince ma sa, sai ya yi ha'inci.
" ki na so yanzu ki za ma daga cikin munafukai ko Usaina?
Jikin ta ne Yayi San yi "a'a Hajiyan mu Insha Allah ana yin hutun za mu je ..."
Amma Wallahi Hajiyan mu Matar sa ce....... " Auta ya Isah! Hajiya ta katseta
" tashi ki ban guri.."
"Yi haquri" ta fad'a ta koma d'akin su.
* * * *
Tun ta na kukan a hankali har bacci ya d'auke ta a wajen, Dillaliya na ankare da ita sabida kar ta matsa Husnah ta gudu, haka ta kwana a ba ta runtsaba ta na gadi na.
Kiran sallar farko ne ya farkar da ni da ya ke ba sa ba ta shi sallar Asuba..
Sabida Baba kan ta shin mu idan zai ta fi masallaci...
Yaya Hadiza da Yaya Hindatu su gyara kwanciyar su, sai su k'i tashi ni kad'ai ke ta shi na yi sallah, sabi da ha ka ne na sa ba da ta shin.
Bude idanu wa na nayi, mai ma kon na gan ni kan tsohuwar ta barma ta sai gani na na yi a k'asa cikin rumfar me kosai.
A hankali na ta shi don yin alwala,
" ke Husnah I na za ki?
Baba dillaliya ta mi'ke cikin sauri.
" fitsari zanyi, in yi Alolah"
" To sallau ai kya jira ko? mu je in raka ki can ki yi dan yan zu za mu ta fi..."
"Toh"na fad'a hawaye na bin kun ci na
" wayyo ni jikar me k'uli wai K'afa ta, mu je in ra ka ki, ni ma na yi mu ta fi...
Ko kar ya wa ba mu yi a tashar ba mu ka hau mota, kuka na ke kamar raina zai fi ta a hanya ta siya ma na bread da k'osai, na ka sa ci sabi da damuwan da ke rai na.
Hanya na ke kallo hawaye na zu bo min hikenan na san inna Gaji sai da ni ta yi...
Ba mu muka iso Kano ba sai karfe 12:36 na rana mu ka sauka a wata tasha da ban San sunan ta ba.
Baba Dillaliya ce ta ka ma hannu na,
"Gwangwazo Malam za mu..
"To"
mu ka hau mota me kafa uku..
Sai raba idanu na ke , na ga jama'a ana ta harka kowa yana ta sabgar sa(Kunsan Kano akwai jama'a ga kasuwanci da albarka jallah babbar Hausa)
Ta fiya mu kad'anyi mu ka je Unguwar dai
k'ofar wani gida mu ka sau ka.
"Na wa ne?
" 'Dari biyu"
" kai d'an nan 'yer wannan tafiyan ka ce min ja ka guda"?
Ga 'dari dai, ungo..
"Gaskiya Tsohuwa ba zan karb'i 'dari ba.
" to alk'ur'an kai wa kan ka
Ta na ban kad'a zani za ta mai da kud'in ta.
Ni dai ina kallon k'arfin hali irin na Baba Dillaliya.
"Ke tsohuwa Wallahi zan miki d'an yen aiki, kawai ki ba ni kud'i na...
" kai wannan d'a anyi ma ra albarka
Ungo nan ta fad'a ta na ba shi Dari biyun.
"Mu je Husnah.
Kofar gidan mu ka bubbuga
"Waye"?
Dillaliya ce
Wata budurwa ta bud'e mu ka shiga .
"Assalam alaikum..
"Wa'alekumus'salam
ta amsa ma na,
Uhmmmm Hajiyan na nan ?
" Eh ku shiga ta na zama Yan zu za ta sakko.
' toh toh' mu shiga mu ka zauna.
Ba mu jima ba wa ta k'atuwar mata fara tas da ita ta sakko da hak'orin Makkah ta biyu a ba kin ta "A'a Dillaliya ke ce ke tafe?
" ai kuwa dai Hajiya heehh tana washe ja ja yen hak'oranta..
" Au tare kuke da Yarinya a she?
"Ina wuni na fad'a cikin gajiya da yunwa
" lafiya lau Y'an Mata, Dillaliya ita ce?.....
Comments din ku
Shike ba mu k'arfin gwiwa,,,,,,..
Ya wan comments ya wan typing
[4/18, 12:22 PM] +234 803 362 6868: ****
SO HALITTA NE
Writing By *R.Hussain* and *Norry*

DEDUCATED OUR FANS.
*Nabaki wannan* *page din kyauta* *mysister* *A.Aisha* *Bauchi Munayabawa* *sosai*
Page0
"Hello Assalam alaikum , ina jin ki Hajiya Sarah, Eh yan zu akwai Yara uku, kwarai kuwa duk wacce ki ka d'auka ba ni da matsala..
To sai kun zo din. Hajiyan Gwangwazo kenan me samawa 'Yan birni Yaran da zasu na musu aikatau.
Tsaye na ke ina mopping a tsakar Gida domin Hajiyan ta fa ra nu na mana yadda akeyi, don kar mu je a dinga k'in d'aukar mu.
Duk da zaman nan d'in yafimin zaman K'auyen mu, amma ina son in koma Garin mu ko dan Baba na, nasan ya na cikin damuwan rahin gani na.
"Keee Husnah!
Muryar Hajiya ce ta katsemin tunanin da nake.
"Baza ki dena wannan tunanin na ki ba ko? Ke bakyason ki samu alheri ne ko kuwa Iyayen na ki kike wa bak'in ciki? Ki shiga hankali fa, ba ni da kyau humm! Ta ja k'wafa.
Cikin hanzari naci gaba da aikin da nakeyi, Indo na kitchen ta na gyaran kayan miya.
Sallamar wa su Mata ne su biyu ta sa mu ka juya " wa'alaikumus'salam..
Wasu Hajiyoyi ne 'yan gayu idon su sanye da bak'in gilashi Wanda d'an me Garin mu ya ke sa kalar sa. Hajiya Sara da Hajiya Zainab kenan.
"Oyoyo oyoyo Hajiya Sarah har kun k'ara so, sannun Ku da zuwa Ku shigo mana...
Cikin nuna isa da k'wank'wami Zainab ta Zau na, duk da Gidan tsaf ya ke yana ta k'amshin turaren tsinke, amma Zainab ta raina bayan sun gaisa da Hajiyan Gwangwazo.
" Hajiya ga k'awar ta wa da take son Yarinyar da zata dinga kulawa da Yaran ta da aikace
"Ai kuwa ba matsala, Husnah, indo, Rashida, Ku zo nan..
Ni da indo mu ka kalli juna sannan mu ka nufi d'akin, Rashida na bayi ta na wanke wa ba ta jiba. "Rashida ki zo" indo ta kira ta mu ka shiga d'akin da Sallama.
Cikin nutsuwa mu ka sake gaishe su.
" Yauwa gasu nan Hajiya idan da wacce ta yi miki shikenan inji Hajiyan Gwangwazo.
Rashida ce ta shigo d'akin kamar an jefo ta.. "keee! Mahaukaciya ni Wallahi da nasan ba ki da hankali ba zance zan d'auke ki ba, Kuyi hak'uri Hajiya gasu nan dai ki zab'a.
" Ku mik'e tsaye duk mu ka tashi kallon mu ta ke d'aya bayan d'aya "wannan za tayi, nu na Ni ta yi ta na yatsine -ya tsine....
" kai ai kuwa kin iya zab'e Husnah ke nan Yarinyar akwai hankali sai dai ba ilimi.
"Ni me ya shafeni da rashin ilimin ta ta d'age kafad'arta irin I don't care din nan, ke za ki iya kula da Yara da Ku ma aiki?
Hajiya Sarah ta fad'a.
" Eh zan iya Hajiya na amsa cikin sanyin jiki, dan ni har ga Allah ba su yi min ba na tsani Mutum me wulak'anci.
" Ku tashi Ku fita"
Mu ka fita da Sauri.
Husnah tafiya zakiyi indo ta fad'a
" hmm to indo tafiya zan yi mana, tunda ni Tace"
Allah kinji dad'in ki za kije Gidan Y'an burni, ni ma Allah ya sa in samu Gidan 'Y'an Burnin nan in dinga hawa sama kwas! Kwas!! Kwas!!!!hahahahh Allah kuwa...
Murmushi nayi Wanda har sai da kyawawan hak'ora na su ka bayyana tare da hushirya ta, har dimple di na sai da ya lotsa sosai, ina ganin k'ok'arin Indo, a girme ta girme ni amma ba na iya Abin da ta keyi.
" To Hajiya Sarah Husnah dai Y'ar talakawa futur ce domin Iyayen ta sun ce duk wata za'a dinga zuwa karb'ar kud'in aikin ta a nan Gidan, nidai fatana Allah ya fitar da ni jin kunyar Ku ta yi aikin da kyau....
Cikin izzah da jin kai
Hajiya Zainab Tace" No problem I will give you, her salary every month, But I don't like dirty please ki gayamata banson K'azan ta gaskiya"
To Amman na wane kudin ta?
Hajiya Sarah ta tambayi Hajiyan Gwangwazo.
"Haba Sarah ai ke za ki fad'a "
Alright zee nawa za ki dinga paying din ta?
Fifteen Thousand far month, okay?
" Hajiya duk wata za'a bata dubu goma sha biyar, amma idan mu ka ga ta na k'ok'ari za mu k'ara akan hakan"
" to shikenan Hajiya Sarah hakan ma ya yi ai.......
* * * * *
Ethiopian air line
Mr.Galadanchi ne ke hawa stairs d'in da zai mai da shi Gida Nigeria sanye ya ke cikin wani yadi smooth milk colour,
Samuel na rik'e da briefcase d'in shi da phones d'in shi, shiga cikin jirgin Ya yi yana jin nutsuwa da farin cikin zai ga Iyalin shi,
Wanda rabon da ya gansu four month kenan sai dai ta video call V.I.P ya zau na ya na d'aura belt d'in set d'in.
Magazine ya d'auka wadda ta ke ajiye a wajen ya na dubawa.
Large 3:10am jirgin su ya yi landing a airport da ke Abuja.
Masallaci ya shiga Ya yi alwalah ya fara na filfili har Asuba , Bayan an idar ne ya d'ora da karatun K'ur'ani har 6:00 na safe
Sannan ya fito cikin airport d'in don shiga jirgin da zai kai su Kano.
Aminu kano international airport.
Drivern sa ne ke tuk'oshi ya na ta farin cikin dawowar Boss d'in na su, horn Ya yi yayin da ya nufi wani dank'areran gate black colour da ke Unguwar Lamid'o Cristan da ke kano....
Gateman ne ya bud'e ya na d'agawa mai Gidan na su hannu " Barka da zuwa yallab'ai " cikin murna da walwala, duk sauran Ma'aika tan ma fito wa su kayi su na ta sannu da zuwa.
A b'an garen Hajiya Halima kuwa, tunda su ka yi waya ya sanar da ita dawowar shi gobe ta kasa zau ne ta kasa tsaye ita da duk 'Y'an Gidan gyara su kai ta yi sai da suka ga komai Ya yi kyau.
Mai k'unshi har Gida ta zo tayi mata da kitson Ghana weaving.
Yaran ta ma Yazeed da Yusrah sun sha ado sosai.
Kitchen ta shiga da kanta ta dafa wa Mijin na ta favourite meal d'in shi da drinks.
Sai da ta tabbatar komai ya yi ready sannan ta shek'a wanka, ,light make-up ta tsara kasance war ta 'Yar gayu , wani Uban less ta sa d'inki buba ta Murza daurin kai mai kyau Wanda ya k'ara ma ta kyau sosai.
Jin horn d'in driver shi ya Sanar da ita isowar tauraron na ta da ta ke missing d'in shi.
Falon ya shigo ya na amsa wayar Aminin nashi Alhaji. Abubakar ya na sanar da shi isowar shi Gida.
Da sauri
gudu -gudu ta zo ta fad'a jikin shi ta na sauke ajiyan zuciya, saurin kashe wayar Ya yi yana cilli da ita kan kujera, Rungume ta Ya yi sosai saboda shima ba k'aramin jigata Ya yi da rashin Iyalin na shi kusa ba.
" Welcome my happiness I really miss you" ku ma k'ank'ame shi ta yi, shak'ar k'amshin juna su ke yi muna jin dad'i da farin cikin sa ke ganin juna.
Hannun shi ta ka ma " Dear mu je ka yi wanka, your food is ready"
Kallon ta ya ke cikin so da sha'awa " Anya zan iya yin komai ba tare da naji d'umin jikin Mata ta ba kuwa?
Ya fad'a ya na mai kashe ma ta ido, ina su Yazeed ne?
Murmushi ta sakar masa "su na sama su na jiran ganin Daddyn su"
Saman su ka nufa hannu su cikin na juna...... ......
Comments ke bamu k'arfin gwiwa yin typing
[4/18, 12:22 PM] +234 803 362 6868:
SO HALITTA NE
*Written* By *R.hussain and Noory*

*Wannan page din sadaukar wa ne a gare ki Aisha Aliyu(humaira) mungode Allah ya bar zumunchi
JUMMA'AT MUFEEDA FANS_
Page 0
A can kuwa garin 'Dan marina.
" ayyiriiii yiririii yiririii!!! Oh Ni Gaji duniya sabuwa da ga ni sai 'ya'ya na na huta da kallon 'yar kihiya ita na jin takaici.
" inna Gaji lafiya Ku wa ki ke ta wanga abu haka? Hadiza ta katse ta.
"Ke dallah matsa sai yanzu za ki dawo saboda Allah Hadiza, Tun safe da ki ka sa k'afa ki ka fita sai magariban nan.
" mtswww!! To idan na zauna cikin gidan me zan yi miki, ko kuwa za ki bani wannan ne?
Ta fad'a ta na d'agawa inna Gaji ledar da ke hannun ta.
" a'ahh hehehe ka ga 'yar arziki irin albarka, ka ga farar 'ya me farar Aniya,
Yo ai sai ki ce min yau ma da tsiran ki ka dawo, to hige ki huta hadizu wa ta"
Hadiza ta wu ce ta na yatsine - yatsine d'akin inna Gaji ta shiga ta ajiye mayafin ta da ke kafad'ar ta, ta tu je d'an kallabin ta.
Gashinan ta mai tsaho da ci ka ne wa ta tsohuwar kalba ce a kan na ta rashin gyara ya sa duk ya cukur Ku d'e.
Zama ta yi ta janyo ledar tsiran ta da lemon kwalba ta bud'e tsiran da 'Dan maigari idris ya sai ya ma ta.
Bayan ya ga ma mammatse ta a d'akin sa da ke soro.
" ke 'yar nan kuma cinye wa za ki yi ke kad'ai?
" a'ah fa inna Gaji ni kam banson takura, ga na ki, ki d'ibawa Hindatu a ciki.
Ta mik'awa uwar takardar tsiran da ta d'iba musu...
Ta ja saura ga ba da lemon kwalban ta a gefe ta na ci ta na korawa.
Baba be shigo gida ba sai da ya yi sallar magariba a masallaci, San da ya shigo a lokacin ana kiran sallan shiyasa sai da aka idar sannan ya shigo.
" Aslamu alaikum "
"Wa'alaikumus salam Baba sannu da zuwa" Hadiza ta amsa ta na tu re takardar tsiran da ta gama ci.
"Yauwa Hadiza ina 'yan uwan na ki ne?
Ta watsa hannaye
" Oho Ni ma tunda na higo ban gan su ba"
"Husnah! Husnah!! Ke Husnah ki na ina ne? Shiru Baba ya ji, tunda ya ji haka ya san ba ta nan, don da tana nan da tun shigowar shi za ta fito yi ma sa sannu da zu wa.
'D'akin Gaji ya shiga ya ji inda ta aike ta har bayan magariba
Tunda ita ma yau ba yi ma sa sannu da zuwan ba, da ma yasan sanda ta ga dama ta ke yi ma sa.
Fitowar ta ne daga bayi ya dakatar da shi " Malam sannu da zuwa" yauwa ina yaran su ke ne?
Ta 6e baki inna Gaji tayi "Hindatu na aiketa Hayi wajen kawu Bala, nasan yan zun nan za ka ganta ma"
"To Alhamdulillah ita ku ma Husnan fa?
" Hmmm Husnah ai tun safe rabo na da na ganta ni anya ma na ganta yau?
Kasan daga sallan asuba ka ce min za ka wuce can kasuwa, za ka yi sare -sare to alk'ur'an ko ganin ta ban yi ba, ba na jin ma ta kwana a gidan nan.
Da ma na gayamaka ranar nan na aike ta na ga ta ji ma ba ta dawo ba na dau gyale na biya bayanta sai ga nin ta nai ta re da lawan me rake ya na sa ma ta hannu a wando, da nace fad'a ma ka ai k'arya ta ni ka yi gaban 'yayan ciki na, ta hau kukan gulma.
Gaban Baba ne ya fad'i me Ki ke fad'a ne Gaji?
"Abinda kunnen ka
ya ji ye ma ka.
" Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un, juwa ce ta fa ra d'aukar
Baba sai ganin sa su kai ya fad'i k'asa .
Da gudu Hindatu ta k'arasa shigo wa, wayyo min shiga uku Baba Baba gaba d'ayan su su ka yo kan sa su na jijjiga shi su na kuka
Inna ce tai saurin zu ba ma sa ruwan butar da ke hannun ta, Hummmmmm ya ma numfashi........
* * * *
Hajiya Zainab ce Ke hawa kan stairs domin zuwa d'akin mijin ta Alhaji.Abubakar
Sanye ta ke cikin night gown me masifar kyau pink colour sai k'amshi ta ke zuba wa ta yi kyau sosai.
Burin ta ta ji su wa zai rabawa buhun hunan shinkafan da ya sa a kawo ma sa guda d'ari.
Domin so ta ke ta yi bajinta da ita ba wai ya ce dangin sa marasa k'arfi zai raba wa ba.
Tura k'ofar d'akin na sa tayi " Aslamu alaikum"
Ganin sa ta yi zauna tsakiyan bed din sa ya yi nisa cikin tunani.
Allah ya sa ni ya na son k'ara aure sabida shi mutum ne me tsoron Allah ba ya son ya je fa kansa ga halaka ga shi mutum ne mai tsafta da muskilanci.
Har yan zu bai ga yarinyar da ta kwantama sa a rai ba.
Hajiya Zainab ta K'arasa Ku sa da mijin na ta, da fa kafad'un shi ga mi da kwantar da kanta a bayanshi.
Ajiyar zuciya ya sauke.
Humm ya na mai zagayo da ita, Idanun ta ta zuba ma sa, ta na so ta karanci damuwar shi.
" my luv me ke samun ka ne please tell me mana?
Ta k'arasa fad'a cikin shagwa6a.
Murmushin sa mai tafiyar da ita ya sakar ma ta " Baby na me Ki ka gani ne ba komai fa kawai gajiya ce"
"No I knew akwai damuwa a ran ka, ba ka so na sa ni ne ta k'arasa maganar cikin kukan kissa.
Saurin rungume ta ya yi yana shafa tattausan bayan ta alamar rarrashi.
" Haba sweetheart so Ki ke na yi miki k'arya?
Already I told you Nothing, please my zee believe me.
'Dago wa ta yi da fuskar ta ta na shafa gyararren sajen shi da hannun ta " are you sure?
kiss ya yi mata a goshin ta "yes am sure.
" Ina yara na ya tambaye ta don ya kawar da zancen
" sun yi bacci"
"Okay ba ri inje in duba su"
Ya fad'a ya na me d'aga ta daga jikin shi jallabiyya ya d'auko ya zura a kan boxer din sa ya fita......
Comments din ko ke ba mu karfin gwiwar yin typing
Yawan comments ya wan typing
Share pls
[4/18, 12:22 PM] +234 803 362 6868:
SO HALITTA NE
Writing By *R.Hussain* and *Noory*

............Tunda malam musa(Baba) ya fad'i ya samu matsalar shanyewar b'arin jiki.
Haka su Hindatu su ka kai shi Asibitin k'auyen. Likitan k'auyen ya yi 'yan dabarun sa, sannan yace Sai dai akaishi asibitin birni, don b'arin jikin shi na hagu ya samu matsala.
Sun yi kuka sosai, musamman Hindatu, dan Baban na su yana k'ok'ari wajen sauke nauyin su amatsayin sa na uba.
"Duk inna Gaji ke ce kika janyo wa Baba wannan ciwon, ke kullum cikin masifa da bala'i ki ke aikin banza kawai".
"ke Hindatu zan ci ubanki fa naga rashin arzikin na ki Sai gaba ya ke"
Hakadai su ka d'auke shi su ka mai dashi gida, domin aje ayi maganin gargajiya ko za'a da ce.
Yanzu Baba baya iya komai Sai dai ayi ma sa, sauk'in Abin ma ya na iya magana amma ba sosai ba.
Mak'ota da Abokan kasuwancin sa Sai zuwa dubashi su ke.
Duk Wanda ya zo dubiya Sai Inna Gaji tace "Ai saboda bak'in cikin Husnah ne ya jawa malam wannan ciwon tun da ta sa k'afa ta tafi yawon dandi shikenan Kuma".
Haka Jama'a za suyi ta Allah wadai da Halin Husnah, su shiga bawa Baba hak'uri da amfanin dangana.
Baba baitab'a yarda da Hakan ba, domin ya fi kowa sanin halin Husnah, ba dai yadda ze yi ne, ga ba lafiya ba re ya je nemanta.
Hadiza ce zaune a d'akin saurayin ta idris, kaf Garin ya fi kowa gayu da chilling dan shi ya yi makarantar boko har secondary ma.
Gashi Baban shi, shi ne maigari shiyasa ya ke jin ya fi kowa a k'auyen 'Dan marina.
Dubawa ya ke ko akwai mutum a layin ganin ba kowa ne ya yi sauri ya shige d'akin sa da ke soro.
"Hahhhh Baby Hadiza ashe kin zo d'in, ai na zaci ba ki ga ne ba. Kinsan ba dama na fad'a awajen me awara ne hiyasa na yi miki alama da ido, hahhh a he kin gane..
"Hmmm lalaima idi me ka maida ni ne iyeee, yau gaskiya 'Dari uku zaka ba ni Kuma ka siyamin kifin haladu da nonon gora, kullum d'ari biyu ka ke ba ni ta fad'a ta na k'ifta idanuwa.
"Yo dan wannan ai me sauk'i ne, amma ni ma za ki yadda na saka yau?
"A'a idi gaskiya ba zan ba ka nan ba, so ka ke nayi ciki a sakani a wak'a a garin nan?
"Sau d'aya ne fa ai ba'a ciki.
" Bari na tafi indai hakane"
"Tsaya na ji bazan je nan ba ya fad'a ya na cire rigar sa, to tahi ke ma ki kwab'e ta mik'e ta cire.
Haka su ka gama abinda zasuyi ya bata 'Dari uku ,fitowa ya yi ya lallek'a ya ga ba kowa ya sa ta fito
Yace su had'u a wajen haladu mai kifi, zai bi ta kofar baya
" to ta ce ta tafi .
Hindatu kuwa duk ta damu da rashin lafiyan Baba, ga shi Husnah ba ta nan ta kasa dena zargin da sa hannun inna Gaji a b'atan Husnah, ba ta da sheda ne kawai .
Idan ta je tallah to Sai ta siyowa Baba wani abun kamar fura ko nama ko kifi dasauransu.don ya ci, haka inna y zatai ta bala'i.
"Hindatu Sai kin karya min jari ko?
"To ai ba kud'in ki ba ne nawa ne"
"To rasa kunya yimin fitsara"
Baki ta murgud'a ta wu ce d'akin Baba, d'agashi ta yi ta bashi furar da ta siyo ma sa, Sai da ya k'oshi ta bashi ruwa.
Jingina shi ta yi a jikinta dan ya huta da kwanciya, Sai da taga ya d'an huta sannan ta kwantar da shi.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya a 'Dan marina.
* * * * *
A yau ne aka bawa su Twins hutun makaranta.
Students ana ta murna xa'a huta baccin da aka ta ra sabida exam ansamu lokacin ramashi.
Twins ne tsaye a k'ofar class d'in su Usaina, Driver su ke jira ya zo.
"Yan biyu Ku yi haquri Wallahi go slow ne ya tsaida ni", "Haba Baba Audu ai ba komai" Hassana ta yi saurin bashi amsa, tasan halin Usaina idan ta fad'a to Mara dad'i za ta fad'a.
Motar su ka hau, su ka tafi.
Hajiyan su ce tana ta jera kayan da aka kawo ma ta daga guga. "Aslamu'alaikum. Sannu da aiki Hajiyan mu"
Wa'alaikumus'salam"
Sannun ku Auta na kundawo.
" Eh ance next week aje a karb'a ma na result d'in mu"
"To Allah ya nu na mana"
"Amin "Ba ri muje mu cire uniform din mu yi wanka mi yi sallah.
"To Sai Ku je kuci abinci Ku ma. Cikin biyayya duk su ka amsa suka ta fi d'akin su.
Anyi Hutu juma'a, lahadi Sai ga Alhaji.Abubakar da yaranshi Ahmad,Hamid,da ikram. Hajiya Zainab ce ba ta zo ba, wai ba ta da lafiya.
Da kan shi ya yi driving har compound din gidan na su. A parking space ya ajiye motar, da kanshi ya bud'ewa yaran na shi. Fitowa su kayi su na ta murnar zuwa gidan kakannin na su, part d'in Malam (kaka) su ka nufa da gudu kaka!kaka!! Kaka ga ni na zo, Hamid ke ta kiran malam inusa sabida su na k'aunar tsohon, Ikram ma sai murna ta ke ta na ta dariya yau za ta sha Zuma ta K'oshi.
Ahmad ne mai hankalin cewa " Aslamu alaikum "
Fuskar 'Dan tsohon mai cike da kamala ta cika da murnar ganin jikokin na shi.
"A'a'ah mashaallah yau abokai na ne su ka zo har da amaryar ta wa a gidan"
Dariya duk kan ninsu su ka saka su na k'arasawa gurin kakan na su.
Muktarul hadis ya ke dubawa, rife littafin ya yi yana ba su hannu su gaisa, ikram kuwa kan cinyar shi ta je ta haye ta na dariya.
Alhaji.Abubakar ne ya shigo d'akin mahaifin na shi
"Aslamu aikin"
" Daga zuwa za Ku da me shi da zance" Dur k'usawa ya yi ya na gaishe da Baban na shi " Baba barka da safiya"
"Barka dai mai gaskiya ya iyalin?
" Alhamdulillah"
"Mashaallah, Allah ya yi albarka", "Amin amin Baba"
"Daddy ba ri muje mu gaisheda Hajiya Ahmad ya fad'a
" Ku jira Daddyn na ku ma na" ,"A'a kaka yanzu za mu da wo nan mu sha Zuma"
"Ihumm daman na san wannan fara'ar ba da zuciya d'aya ake min ba,dan Zuma ne ko ikram, dariya ta ke ta yi tanajin dad'i.