← Book details So Halitta Ne Part 1 Complete Hausa Novel.doc Local reading mode
CHAPTER 2 OF 4

Part d'ina na koma,kishin aunty na tasomin na dinga karanta hasbunallahu wani'imal wakeel" har na samu sassauci.

So Halitta Ne Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 26 min read

Acan kuwa Daddy ne ya bita, yana ta faman rarrashi duk ya shiga damuwa, Zainab ta kallesa tace",ni ka koma can kawai, wana dare ne jemage bai gani ba,ka gama siyamin raini a wajen yarinya"
Daddy yace"ke banason wannan abun da ki ke min, ba ma dole ta rainaki ba tunda kin ringa da kin zubar da girmanki, kuma ba ri kiji Wallahi ba saki a tsarina,duk matar da na aura tazo kenan, sai dai wani ikon Allah"
Zainab ta shiga tunanin, wannan yarinyar fa idan nayi sake rainin da za ta yi min kare ma bazai ci ba, dan naga ta k'ara wayewa da alama wannan Usainan ce ta ke zugata ai nasan ba ta da kunya, amma zan gwada hak'urin da ake cewa nayi, Daddy ne yace" idan kin gama tunanin inason magana da ku baki d'aya a parlor'n da ke compound"
Fita ya yi ya nufi part d'in Husnah.
Su Usaina da Hajiya ta aikosu ya samu a parlor'n sun
baje ragowar kajin su ke ci, su na ta chapter daga wannan tace wa Husnah ba ni labari dan Allah,sai Hassana tace "Allah nasan da k'ar idan ba kwanan zaune ta keyi ba" hahhhh su ka shek'e da dariya su na tafawa.
Daddy ya shigo parlor yana hararrar 'yan biyu yace"watukun zuwa ku ka yi ku had'a min mata na ko?
Shiru su ka yi kowacce ta sun kuyar da kanta k'asa, Usaina tace" Wallahi Yaya aiko mu Hajiya tayi" Husnah ma ta yi shiru ta na cuno baki, k'unk'une takeyi ita kad'ai Daddy da yake kallonta ya girgiza Kai sannan yace"idan kin gama k'un k'unen ina nemanku a parlor'n compound" shiru ta yi ta tashi domin binsa a haka, kallon ta ya yi yace"a haka za ki fita ko,saboda ba ki san kinyi aure ba ko?"
Hijab d'in Usaina na saka idanuna har ya kawo hawaye dan banason ya had'ani da aunty dan duk abinda ta gayamin zan rama ne, dan sai na fito mata a mutum zamu dai-daita. Tare muka fito hawaye na ke yi dan nagaji da abinda aunty take min, shine ya ke damuna, idan ban taka mata burki ba, bazan samu kwanciyar hankali ba.
"Magana fa nake miki ko?" Daddy ya fad'a.
Kuka na fashe da shi nace"Hindatu ta yi aurenta cikin kwanciyar hankali, hakama Yaya Hadiza, ni kuwa sati d'aya na fara fuskantar matsala" Daddy da yake tunanin ina da sanyi ashe duk kanwar ja ce, sanin yadda Hindatu da Hadiza su ke ya sa yake ganin kamar ni kad'ai na fita zakka dan tunaninsa mahaifiyata na biyo ashe dole ya dai-dai ta matansa, dan ko wacce da alama ba za ta d'auki k'ask'anci ko cin fuska ba...........
Ranar suna yaro yaci sunan Malam Musa ana kiransa da (Iman) mai jego tayi tsaf da ita duk hidimar nan da akeyi ba'a sanar wa da su Husnah da Hajiya ba, dan Baba yace kwanan nan aka gama hidimar biki,kar a sanar da su dan yasan sai sun zo sunan.
Hindatu ranar suna Hadiza wuni tayi rigima Salisu da ya koma aiki sai dawowa ya yi ya tarar da ita akwance zazzab'i mai zafi ya rufe ta, mamakin wannan rigimar ta ta yake, har yanzu ba ta daina ba to ko sai yaushe oho.
Baba na zaune a k'ofar gida ya ga driver 'Danliti ya zo shi kad'ai motar cike da kayan abinci, cikin farin ciki Baba ya tare shi, 'Danliti ya nemi almajirai su ka tayashi shigar da kayan cikin gida.
Gaishe da Baba ya yi ya zaro kud'i masu yawa yace"gashi maigida ne ya ce akawo,ya na gaishe ku sosai sannan yace a sanar da ku ma'aikata za su zo gyaran gidan nan ku kintsa idan yazo za ku tafi tare ne can burnin, bayason zamanka kai kad'ai ka koma cikin danginka"
Baba Malam da ya rasa bakin magana kawai sai share k'walla yake yi, shikuwa mai zaice da 'dan kasuwa a rayuwa, yaron ya gama yi masa komai. Godiya da addu'a ya shiga yiwa Daddy ba adadi, 'Danliti ya na ta amsawa da amin ya Allah.
Sanar da Inna Gaji Baba ya yi, murna tashiga yi "wayyo ni Gaji yanzu Malam can burni za mu koma da zama kenan?" Baba ya ce "a'a ni dai bazan koma gidan siriki na zauna ba Gaji,da zarar angam gatta gidan za mu dawo"
Inna Gaji ta gyara soke zaninta ta k'ank'antar da ido tace"Alkur'an ba zan dawo ba, kaji Malam da wani zance, Allah ya k'ara mana matsayi zama a maraya ai sai mai rabo,mun samu za ka yi mana bak'in ciki,to Alkur'an sai dai Kai ka dawo, ni kam na tafi kenan har abada ba ni ba zaman k'auyen nan" ta k'arasa ta na buga cinya.
Baba ya koma wajen 'Danliti ya ba shi tsarabar k'auye dangin su barkono, manshanu da su daddawa duk Inna Gaji ta had'a tace akwai Hajiya Batulu. Cikin mutunci da jindadi 'Danliti ya baro 'Danmarina..............
[4/18, 1:27 PM] +234 803 362 6868:
SO HALITTA NE
TSARAWA DA RUBUTAWA
NA
R.HUSSAIN DA NOORY
ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
_MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FA
AKARWA HA
I DA NISHA
ANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA, HUMM WANI ABUN SAI ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION
RUWA KA
AI KE MAGANIN
ISHI
*"AL
ALAMINMU YANCINMU
SADAUKARWA GA DUK KANIN MASOYAN LITTAFIN SO HALITTA NE
Page7
.........................
Zaune suke a parlor'n compound d'in Daddy ya na tsakiyar su ko wacce ta had'e rai, da sallama ya fara sannan yace" Alhamdulillah dukkan yabo da godiya ya tabbata ga Allah(SWT) tsira da aminci su k'ara tabbata ga shugabanmu annabi Muhammad (SAW) kamar yadda ku ka sani duk kan ku mata na ne idan kun so ku zauna lafiya idan baku so ba ku kashe ni ku huta, nidai zan k'ara tabbatar muku da cewa babu wacce zan iya rabuwa da ita a cikin ku,kuma duk kanku so ne yasa na aure ta, dan haka ina umartaku da ku had'a kanku, banason nayaniya"
Kallon Zainab ya yi yaga ta nutsu sosai ta na sauraronsa hakama Husnah tayi shiru ta na jinsa,numfasawa ya yi yace"yanzu kwana nawa ku ka raba wa kanku?"
Zainab d
a ta ke jin ba dad'i a ranta tace"duk yadda tace shikenan"
Husnah ma tace"a'a aunty duk abinda ki ka ce ya yi" murmushi ya yi ganin sun fara saukowa, yace"kwana d'aya d'aya ko bibbiyu ku ke so?"
Husnah tace" aunty ki fad'a masa"
Zainab tace"a'a ba ke ce amarya ba ki fad'a dai"
Daddy da abun ya burgeshi yace"to ni in zab'a ?" A tare su ka ce "eh" Daddy yace"to kwana d'ad'dai ya yi muku ko?"
Gaba d'ayansu su ka ce"a'a kwana biyu biyun dai" dariya su ka bawa Daddy yace"Dan Allah ki had'a kanku, tunda kun fison hakan to shikenan"
Husnah tace"aunty Dan Allah Ina neman alfarma"
Zainab ta kalleta tace"tame fa?"
Husnah tace" ki ba ni Ikram"
Zainab tayi dariya tace"Ikram dama ai 'yarkice na baki kyauta Husnah,Allah ya tayaki rik'o" dad'i ne ya kama Husnah ta hau godiya "nagode Aunty Allah ya saka da alkhairi, bari inje mu tafi sai da safen ku"
Da gudu ta fita ta nufi part d'in Zainab don d'aukan 'yarta.
Zainab tayi murmushi tace"Allah ya ba ni juriya da hak'uri Abban Ahmad ka kasance mai adalci a tsakanin mu, Allah ya bamu zaman lafiya " Daddy ya rungumeta ya na sa mata albarka dan zaman nan da su ka yi ya fuskanci duk sun dangana.
A parlor su ka tarar da Ahmad da Hamid da Ikram da Husnah su na ta dariya dan hira su ke sosai Ikram na ce musu ta canza d'aki ta bar musu nata, amma kar su tab'a mata kayan games d'inta za ta na zuwa ta yi, shine su ke ta dariya. Ganin su Zainab sun dawo yasa Husnah kama hannun Ikram tace" sai da safen ku"
Zainab tace"ka raka ta mana" Daddy yace" anjima na shiga, ya nufi sama. Zainab tace wa su Ahmad" to a ci gaba da hirar mana" gaba d'ayansu su ka sa dariya.
Bayan wata d'aya kowacce ta kwantar da hankalin ta, Husnah ta mai da Zainab kamar 'yar uwa komai aunty komai aunty . Shirye-shiryen yafiya Dubai su ke domin ma'aikatansa na can sun matsa ya zo yaga yadda su ka k'ara samun ci gaba, kasan cewar Zainab ma ta yi yawo sosai tasan companies d'insa, ba ta damuba sai fatan alkhairi ta ke musu.
Husnah kuwa neman fasa tafiyar take dan bikin su Usaina yazo, bataso ayi shagalin biki bata k'asar hakan yasa tace ya tafi kawai shi kad'ai
Daddy yace yana da mata har biyu, ba zai je wata k'asar ba mata ba.
Husnah tace ya tafi da Zainab,ita biki za ta yi,yace bata isa ba.
Su twins ma ba su so ba, amma sun san ba za'a k'ara ba,da anbari sai Husnah sun dawo.
Har yanzu Usaina ba ta shiri da Zainab, dan ko zuwa su kayi gidan Hajiya sai su ja Husnah d'aki, ita kuma tace"aunty zo muje mu huta" haka Zainab za ta bisu idan taso, wani lokacin kuma tace su barta anan d'in ma ya yi.
Hindatu kuwa da laulayi ya sata a gaba komai sai anyi mata, wataran ta sa Shi a gaba da kukan ita ta gaji da cikin nan haka zai ta faman bada hak'uri da rarrashi so ya ke cikin ya yi k'wari su je ganin gida 'Danmarina. Laulayi take amma tayi kyau sosai dan Salisu ba abinda ba ya yi mata, haka itama tana k'ok'arin k'yautata masa dai dai iya warta.
Garba ne ya kawo wa Hadiza sabuwar waya dan ya gaji da yawan Kiran da su Hindatu ke yi mata,lokacin da Husnah taji haihuwar ta har kuka tayi na ba'a fad'a mata ba Dan kar ta zo, Garba da Daddy su kai ta ba da hak'uri Baba kuwa yace"kar ya ga k'afar kowacce a cikinsu Husnah da Hindatu daga aure bayason yawo, shiyasa ba wacce taga Imam sai dai a hoto.
Tunda ya ba ta wayar shikenan suke zumuncinsu, sanin rashin lafiyar Hindatu ya sa Hadiza cewa ciki ne da ita, a wayar Hindatu da Hadiza su ka yi fad'a.
"Idan ke kikayi cikin sai ki fad'a ai cikin ne, daga zazzab'i za ki cewani ciki a'a ciko ne ba ciki ba"
Hadiza ta tintsire da dariya tace"oho dai an yi tuntub'e da abu a k'ofar d'aki" kashe wayar Hindatu tayi, ta dira rigimar Salisu ne ya fad'a musu.
Yau saura kwana biyu su tafi Dubai, rigima suke tsakanin ta da Daddy dan a d'akinta yake Husnah tace" Ni dai yau na yafe,kaje part d'in aunty ka kwana sai kuyi sallama" Daddy yace "kamarya intafi can?"
Husnah tace"na barta mata kwanan ni"
Daddy yace"to ni ban bari ba, banason rigima fa baby" Husnah tace"Allah ni dai yau ba za ka kwana anan ba" Ganin da gaske ta ke Daddy yace"Wallahi ba inda zanje, naga yau na dawo nan d'in ko?"
Husnah tace"ai ni na barmata saboda tafiya zamuyi ita za'a bari,ni ka koma can" tsawa ya daka mata bazan koma d'in ba,ke kullum sai anyi rigima da ke akan kwana,in da sabo ai ya kamata ki saba,banason shirme...............
[4/18, 1:27 PM] +234 803 362 6868:
SO HALITTA NE
TSARAWA DA RUBUTAWA
NA
R.HUSSAIN DA NOORY
ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
_MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FA
AKARWA HA
I DA NISHA
ANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA, HUMM WANI ABUN SAI ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION
RUWA KA
AI KE MAGANIN
ISHI
*"AL
ALAMINMU YANCINMU
*2nd to the last page*
Page7
..............................
Haka dai dole Husnah ta hak'ura anan ya kwana. Da safe bayan sun gama breakfast yace ta shirya su ajiyeta a gida domin yin sallama idan ya tashi daga office zai biyo su tafi, Husnah ta rasa inda zatasa kanta don murna tunda akayi auren bata tab'a fita ko da bak'in gate ba ne. "Wayyo Allah dad'i da gaske ka ke my love?" Daddy ya fara zagaya yatsansa a fuskarta ya na murmushi yace", eh mana, dan ma Baba ya hanamu zuwa 'Danmarina Kuma nayi-nayi ya dawo nan yak'i, kinga aikin ma da ake musu a can yace shi ba inda za shi, oh Baba ma gaskiya akwai rigima"
Cuno baki Husnah tayi tace"Baban nawa?"
Daddy yace"ai nima Baba na ne, ke bari ma kiji tun kafin a haifeki ya same ni "
Dariya Husnah tayi tace"ashe ma sunanka d'an kasuwa" Kai ya d'aga mata yace"waye ya fad'amiki?" Cinyarsa ta hau ta sak'alo hannunta ta wuyanshi su na facing juna tace"Hajiyanmu ce mana" zaren rigar da ke jikin ta ya fara ja alamar zai cire 'yar rigar da bata fi a Kira ta da have best ba, purple colour da mini d'inta,kayan cikin Wanda Galadanchi ya kawo ne.
Saurin rik'e masa hannu tayi tana cewa"kabari mana, kaga fa unguwa zamu tafi,bari ma inje in shirya" yun k'urawa tayi zata tashi ya rik'eta, yace"ke fa ki ka tsokanoni ga inda ki ka zauna min,kinsan yadda nake,Kuma yanzu ki ce ba hakaba, haba baby na, my hot honey" shafa ya farayi ya na jan zaren rigar dan ba zai iya jurewa ba, hakan yasa Husnah fara taimaka masa,dan kar ya yi dogon zango, ayi a tafi wajen su Usaina dan tasan ba da ita za a yi ba.
'Daukanta ya yi ya nufi bed room d'insa da ita, gaba d'aya sun rikita junansu, ta inda Husnah tafi Zainab kenan dan ta na da juriya sosai, hakan ke k'ara wa Daddy'n k'aunar kasancewa tare da ita, ba'a binda ke tashi a d'akin sai nishinsu idonsu duk ya rufe da soyayyah, sai da su ka k'ara gamsar da junansu sanna su ka yi wanka, wankan ma da k'ar a ka yi saboda ana yi ana tab'e-tab'e kamar mayu sai da Husnah tayi da gaske akayi wankan aka fito,shiryawa su kayi Daddy cikin wani yad'i milk colour mai taushi, ya fito Husnah ta sa atamfa orange mai ratsin fari ta sa mayafi da takalmi fari ta sa sark'a da d'an kunne masu kyau ,kyau ta k'ara na d'aukan hankali, shagala ya yi da kallonta yana jin yadda son da aka halitta masa a zuciyarsa na k'ara k'aimi, hannunsa cikin na juna suka nufi part d'in Zainab.
Zaune take tana waya da Galadanchi akan Jamb d'in da Husnah take so tayi dan tace ita ce ta hana ta yi karatu a baya yanzu a shirye take da ta dafa mata ta cimma burinta na zama yar jarida, duk da oga bayason aiki,Amma tace karatun kawai take so ta samu, shine Zainab ta ce tare da ita za'ayi ta faman. Sanar da shi tayi Daddy ya ce bayanzu ba sai sun dawo daga tafiya, Galadanchi da ya san zancen ya nuna bakomai, ai da sauran lokaci ma.
A haka su ka shigo bayan sun raba hannu dan duk abinda zai sosa ran matan nasa yana k'ok'arin kiyayewa,da fara'a ta tare su" a'a ga zara ga wata kunga yadda ku ka yi kyau kuwa?" Husnah tayi murmushi tace"Ina kwana aunty" . Zainab ta amsa "lafiya lau my k'anwa, ya oga"
Dariya kawai Husnah tayi.
Zainab tace "dear anfito, kenan" Daddy yace"eh su ya yaran?" Zainab tace"sun tafi school ai, tun da Ikram ta shigo ta na musu dariyar ta rugasu shiryawa, su ka shirya da kuwa nayi nayi su tashi sunk'i". Murmushi su ka yi Daddy yace"za mu je yiwa Hajiya sallama, sak'on me za ki bayar?" Zainab ta tafi tunani can tace"kace Ina gaisheta,Kuma za mu zo mata wuni ranar lahadi,Dan nasan gidan nan ba wani dad'in zama zai mana yanzu ba" da to ya amsa, Husnah tayi mata sai sun dawo.
Acan Husnah ta wuni, d'akin Baba Malam ta fara shiga ita da Daddy,har Daddy ya fito ya shiga ciki tana tare da Baba Malam, kamar kakanta haka ta mai dashi, sannan ta shiga cikin gidan, 'yan biyu ne su ka fasa ihun ganinta cikin jin dad'i da murnar ganin ta, Usaina ta kalleta up and down tace"kan bala'i kice har Yaya ya kashe arna sakamako ya bayyana"
Husnah ta d'aka mata duka "to uwar sharri za ki fara ba,ni Ina ta missing d'in ku,kin tare ni da wani zance"
Hassana tace"bari in latsa mararta in jiyo mana Bloody" da sauri Husnah ta matsa tana "Allah ya shirye ku, sa i di nawa" d'akin Hajiya ta fara shiga ganin Daddy ya sunkuyar da kai k'asa a gaban Hajiyan uwa na Allah ya na mata zance k'asa-k'asa, abun ya kusan bata dariya,tino yadda su ka kasance a safiyar da yadda yadda yake mata sammatu da kukan dad'i amma kalleshi anan Dan Allah.
Sharewa tayi ta je jikin Hajiyan ta kwantar da kanta a cinyarya tace"Hajiyanmu Ina kwana" Hajiya Batulu tayi murmushi ta tuno mahaifiyar Husnah yadda Husnah take da son jiki, haka mahaifiyar ta take. "Lafiya lau Husnah,ya gidan naku ya yayarta ki?" Husnah tace "lafiya Alhamdulillah, tace a gaishe ku, zasu zo ma ranar lahadi".
Daddy da ya jinjinawa son jiki irin na Husnah,sai yanzu ma yake k'ara sanin halittarta ce haka,ko bacci su ke tana kwance a side to kuwa sai dai ya ganta d'are -d'are a kansa shine gadon, idan ya so ya barta idan baisoba ya tasheta da fitina, ta na fara k'orafi yace ita ta takaleshi.
Sallama ya yiwa Hajiya bayan sun d'an tab'a hira ya tafi domin k'arfe takwas na dare jirginsu zai tashi.
Wajen su Usaina ta dawo su na kitchen su na aiki, haka su ka sata a gaba d'aya wannan tace kaza sai wannan k'arshe sai da ta fito musu a mara kunya irinsu sannan ta samu sauk'i, Kuma tace bashi ne dan sai ta rama.
Sai yamma su Daddy su ka dawo d'aukarta ganin sallama fa tazo yi musu, tasa kuka, Daddy da ransa ya b'aci ganin tana kuka dan za su tafi gida ya sa yace"wani abu muke miki a gidan da za ki sa kuka,ko salon Baba Malam da Hajiya su ce muna cutar da ke?"
Cikin kuka Husnah tace"ni na fasa tafiyar nan, biki fa zs muyi"
Ajiyar zuciya ya yi,jin shirmenta ne ya tashi, sallama ya yi musu ya fita Hajiya da tasa 'yar sudan ta had'o mata kayan gyara na matan aure na musamman da tazo kawowa twins nasu, ta d'auko ta bawa Husnah, tace" ki kula da kanki da mijinki kinji, Allah ya tsare ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya"
"Amin nagode" ta fad'a cikin kuka, har bakin mota su twin's suka rakota suma su na jin kewarta tun yanzu, driver ya bud'e mata kusa da Daddy baya ta zauna, ya rufe ta na kuka tana d'aga musu hannu tasan ita da ganinsu sai dai gidajensu ta je.
Rungumota Daddy ya yi yana rarrashinta dan sun bashi tausayi, a haka su koma gida.
K'ara shiri su ka yi Galadanchi da matarsa su kazo domin yi musu rakiya, haka Zainab ma da yaranta duk sun shirya domin rakasu airport, Husnah ta rik'e Zainab tana kuka"aunty ki ba ni Ikram mu tafi tare" Zainab tayi murmushin yak'e tace"Mami school shiyasa ba za mu tafi tare ba ai, sai kuka ki ke kamar kuntafi kenan, wata biyu ne da kawai"
Halima tace"oh ni Halima wannan amarya tamu da shagwab'a take"
Murmushi kawai Daddy ya yi Galadanchi yace" nima dai zsn k'ok'arta"
Halima tace" Wallahi in dai irin Husnah ce,ba damuwa Allah ya bamu zaman lafiya"
Zainab tace" mukam dai Alhamdulillah"
Rankayawa su ka yi su ka nufi airport d'in, ba su dawo ba sai da jiransu Husnah ya tashi zuwa Dubai...............
Ciki yasa Hindatu komai fad'a abu kad'an sai masifa Salisu dai yace ya ji ya gani, tattakinta ya ke yi sosai, in dai su na tare ba shi da aiki sai shafa cikin Hindatu da surutai wai hira su ke yi da d'ansa ko 'yarsa, Hindatu tai ta dariya wani lokacin tace"wai sai kace yana jinka,cikin da ko rabin naka baiyi ba"
Dariya Salisu kawai ya yi yace"da sannu kema zai girma,kin manta abun cikin nawa na d'ura a cikin ki?" Cuno baki Hindatu tayi ta yi masa banza.
Shi kuma sai ya yi ta dariya yadinga fad'ar abinda take yi, lokacin da yake yin cikin, "kinsan dai kema kinji dad'i ko karya ne?" Kukan shab'awab'a za ta sa masa. Y fara cewa"Allah ya baki hak'uri, ni kad'ai naji dad'i na, Kuma kina haifa za ki ba ni abuna, daman ba ke za kiyi rainonba, na yadda ai kiyi hak'uri" haka zai ta fama har sai ta huce.
Rayuwa suke cikin soyayya su na ta rainon cikinsu, kullum sai anja masa kunnen kar ya gayawa kowa tana da ciki,ita kunya takeji, haka zai ta amsawa da to,nan kuwa tunda likita ya tabbatar musu da cikin na sati shida, ya ya yata a d'anmarina da su Hadiza har Husnah tasan Hindatu na da ciki, Amma haka kowa ya yi shiru. Dan Salisu ya ce Dan Allah kar su gayamata ya fad'a musu.
Yau Salisu ya tashi da fushi, kusan sati, Hindatu tak'i yadda da shi, ya lallab'ata amma a banza, ya rasa yanda zaiyi ya shawo kanta, da ciwon mara ya kwana kamar zai mutu, ba abin da tayi masa sai kukan Dan Allah kar ka mutu inasonka, dabaru yasa ta d'an yi masa,San nan ya samu ya yi bacci shine yau ya ke ta fushi,ko kulata baiyi ba.
Hankalinta duk ya tashi,sai magana take masa ya yi mata banza, ko abinci yak'i ci da ke Sunday ce ba lacture ba aiki, k'arshe ma waya ya d'auko ya yi kamar da budurwa ya ke waya" hello Ina jinki baby, haba dai, ai mata biyu ya zama dole,idan baka samu kulawa a wajen wata ba sai ka samu a wajen wata" ya kalli Hindatu ta gefen ido,da hawaye ya jik'a mata fuska.
"Hahhhh habadai ai ni d'in jarumi ne ko mata hud'u ne zan iya da su, ke nifa k'arfi ne da ni, ai dole ne hahhhhh shiyasa nake son auro ki my sweetheart nasan duk abinda nakeso za ki bani" ji ya yi Hindatu ta f...........
[4/18, 1:27 PM] +234 803 362 6868:
SO HALITTA NE
TSARAWA DA RUBUTAWA
NA
R.HUSSAIN DA NOORY
ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
_MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FA
AKARWA HA
I DA NISHA
ANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA, HUMM WANI ABUN SAI ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION
RUWA KA
AI KE MAGANIN
ISHI
*"AL
ALAMINMU YANCINMU
*THE END*
Page 7
......................
Tunda su ka je Dubai suke honeymoon d'insu,Daddy dawowa ya yi ruwa tsundum kamar saurayi dan shekara talatin soyayyah gami da tattalin juna suke, watan su biyu a Dubai ya kammala duk kan abinda ya kai shi, Shirin wucewa saudiya su kayi domin umarah, Husnah ta k'ara fari da k'iba.
Kwance su ke a kan threesitter Daddy da ya fuskanci ciki ne da Husnah Amma ita bata san da shiba, hannu ya d'ora a mararta yace"baby'n baby kana lafiya, ya kamatamu gaisa yanzu" Husnah da bata fuskanta ba, dan ita tasan ba haka ake ciki ba dole sai anyi cuta kamar yadda Hindatu take yi, Kuma ita k'alau take,sai k'ara murjewa skin d'inta da tayi.
Husnah "tace lalaima sweetheart wana ganawa bayan yanzu ma tare muke?" Daddy ya yi murmushi yace"kinji nace baby ne, nifa da baby'n baby nake magana ta"
Husnah tace"waye baby'n baby kuma?"
Rad'a ya yi mata akunne yace" 'dana da ke nan mana,yana son ganawa da ubansa ne tun d'azu yake sanar da ni"
A zabure Husnah ta mik'e "tabdijan ni Wallahi ba ni da wani ciki, to kai haka ake ciki ma?" Daddy ya tintsire da dariya yace"haka akeyi mana baby watan ki nawa yanzu?" Nikam ba haka ake ba ko zazzab'i banyi ba fa" murmushi yayi yace"Allah ne ya bamu mai sauk'i" ganin bata yadda ba ya fara shafa mararta ya d'an latsa kad'an k'ara tad'anyi kad'an. Daddy da yaji tauri ya yi murmushi yace"Allah baby akwai baby'n A.S. Yunus anan"
Mamiki tayi sosai ta rufe fuskarta a k'irjinsa tana murmushi wai ita nan kunya.
Bayan kwana biyu su ka sauka a garin Makkah, Husnah ji take kamar a mafarki wai yau itace a d'akin ka'abah, tun da suka sauka a hotel d'in kusa da harami su ke.
Sai da su kayi ibada suka koma masauki, ai kuwa a ranar amai yace salama alaikum, dan ko bacci ba su yi ba, zazzb'i ne ya rufeta sosai, duk Daddy ya shiga damuwa, Almustashpha ya kaita, karb'arta akayi aka shiga bata kulawa. Cikin nata da yake wata hud'u a jikinta basu gane ba, dan watan aurensu watannin cikin, Daddy da ya duba yaga a daren farkonsu ta samu cikin ma, ta riga Hindatu yin cikin ma ashe, take tayiwa yayarta tsiyar Kai Hindatu daga zuwa sai wannan abu,kai amma Yayan nan nawa ya cika zalama. Haka za tai tayiwa Hindatu k'arshe sai Hindatu ta yi fushi ake rabuwa.
Daddy da yake ta murna kamar bai tab'a haihuwa ba, sai zumud'i yake Galadanchi ya kira ya sanar dashi ai cikine da su tsawon wata hud'u Halima na kusa da shi itama ta na fama da nata k'aramin ciki tace "Masha Allah Allah ya inganta ya raba mu lafiya" Daddy da ya ji ta yace"Amin maman Yusrah mungode" Galadanchi yace" nima fa na k'ara jefa kwallo a raga Daddy yace"da gaske?" Galadanchi yace "eh sati uku kenan, kaganni Ina ta fama da laulayi ta mintsine shi, tana harararsa, fatan alkhairi su ka yiwa junansu, dan nan ya ajiye wayar.
Shawarwari aka ba su sosai akan cikin na Husnah,inda su kayi mata scanning su ka ce biyu ne a cikin nata. Daddy dai kamar me haka yake murna Husnah kuwa ba bakin magana, taya za ta iya kallon aunty da cikin mijinta a jikinta,har kunya take ji.
Sai da ta d'an samu dama-dama sannan suka fara shirin dawowa gida Nigeria.
Husnah tayi shiru Daddy yana ta magana bata ji shi ba,tab'ata ya yi tayi firgit ta d'ago
Zama ya yi kusa da ita yace"me nene baby?"
Sai hawaye tace"yanzu da wana ido zan kalli aunty, cikin mijinta,wanda take tsananin kishi a jikina" Daddy ya had'e rai yace" ko shege nayi ba d'an sunnah ba ne?" Girgiza Kai Husnah tayi tace"Amma da kunya my love, ni Wallahi ba ruwana kai ne kayi min"
Daddy yace" da nayi miki, ke ba kyaso?" Husnah tace" inaso mana,amma ni kunyarta nakeji ne"
Daddy yace "Kai k'uruciya, cikin mijinki ne ai kema dan haka kar in k'ara ganin ki na tunani, so ki ke in rasa my sisters d'ina k'awayenki?"
Dariya ta tintsire da ita tace"su Hassana da Usaina zan haifa?" . Daddy yace "insha Allah" nan da nan Husnah ta ware.
Bayan sati hud'u da tafiyarsu aka sha bikin 'yan biyu Inna Gaji da Hadiza ma sun zo, ganin gidan surukan Husnah yasa Inna Gaji jikinta ya k'ara yin sanyi, ta Kuma k'ara tabbatarwa da kanta, hassada takice, da tak'i Husnah ta hurawa rayuwarta wuta yanzu gashi ta na cin arzikinta, Daddy yasa Galadanchi ya yi musu passport da visa ita da Baba Daddy ya biya musu hajj ba na za su je sauke farayi, tare da su Baba Malam da Hajiya Batulu za su koma.
Ranar Inna Gaji yini tayi kukan nadama, Hadiza ta dinga godiya da son barka k'aunar 'yar uwarta na k'aruwa a ranta, Hindatu ta kira ta yiwa albishir, Hindatu ma tayi farin ciki sosai, idan za su tafi, za su rok'i Baba ya barta tazo, su yi sallama, Salisu ma yaji dad'i sosai ba dan cikin jikin Hindatu ba da tare zasu tafi dan shima yanzu Alhamdulillah komai ya na tafiya dai-dai yana samu sosai.
'yan biyu kuwa da aka kai su gidan miji kowacce sai da ta yabawa aya zak'inta dan Usaina sume wa barrister tayi, sai da ya kaita asibiti aka d'inketa, dan tara ta yayi, duk d'age -d'agen auren da tasa ya dinga aikawa a dole a daren sai da ya fanshe a kanta, bakin ta ya mutu murus, haka barrister ya yi ta jinya kafin ta warware a ci gaba da kwasar roman democracyn aure.
Hassana ma da doctor Idris d'inta su ke ta cin amarcinsu da tsinke gaba d'ayansu su na cikin kwanciyar hankali da fatin ciki, kawai tunanin ramuwar Husnah suke dan yanzu ta fisu iya tsiya, a waya take yi musu ma, ta dinga cewa to Usaina ya kikaji?" Usaina tace bansaniba Allah ke yayar nan ma ba kya rik'e girmanki, sai dai Husnah tayi ta dariya Daddy kawai ya yi murmushi dan shima baisan haka take da baki ba sai yanzu da suka zama ma'aurata.
Hassana kuwa salaha sai dai tace"ba dai kyau jin sirrin ma'aurata ahee Yaya ya koya miki daman wannan lumshe idanun da yake irin na my doctor nasan akwai jaraba kema kiji da naki aikin ahee"
Haka za su yi ta yiwa kansu tsiya idan Daddy na kusa yace"za ki sa su rainani baby ke kike gayamusu ni jarababbene ko?" Husnah tace"a'a ni ban fad'a ba, kawai dai ina rama abinda suka dinga yimin ne lokacin da aka kaini gidanka"
Dariya ya yi yace"tsokanarki su kayi ?" Tace"hummm ai Wallahi abinda su ka yimin ni rabin sa banyi musu ba, Usaina fa har tafiya ta ta dinga kwaikwaya tana ta dariya sai da suka sani kuka"
Shi kansa Daddy dariya ya shiga yi yace"Allah ya sauke ki lafiya su ga result d'in ranar da su ke kwaikwayonki"
Yau girjinsu ya sauka a gida Nigeria, cikin Husnah ya d'anfito ya yi mata kyau sosai drive da su Ikram ne su ka zo tararsu a airport gidan Baba Malam suka fara sauka dan Husnah tace ita sai taje wajen Baba Malam da Hajiya tayi missing d'insu, aikawa karb'a mai kyau ta samu wajen surukan nata, Husnah tace"wayyo twony na gidan ba dad'i da babu su" Hajiya Batulu tace" daman duk mace 'yar wani gidan ce ai,komai daren dad'ewa indai da rai da rabo sai ta bar gidansu ta tafi gidan wani ai Husnah" Allah ya sanya alkhairi ya ba su zaman lafiya, tsarabar turaruka masu tsada da dogwayen riguna masu kyau na manya ta kawo wa Hajiya Batulu baba Malam ma ta akawo masa na maza da turaruka da carbi har da zuma dan tasan Baba Malam akwai son zuma, wannan kad'an ne kafin a aje d'auko musu kayan su dan ba wanda ba su yiwa tsaraba ba, dan ma ciki ya na d'an takura mata.
Daga nan suka zarce gidansu part d'in Zainab su ka sauka, murna wajen Zainab na dawowar mijinta kamar me ganin cikin jikin Husnah sai da wani abu ya taso mata na kishin mijinta, yanzu Husnah ce zata haihu da dear,lallai duk abinda Allah ya a nufa ba makawa sai ya faru,naso na b'arar da damata Allah ya kiyaye,Allah ka k'ara sa mana juriya da hak'urin zama da abokan zaman mu, Husnah ta rungume Zainab tace"aunty nayi kewarku sosai"
Zainab cikinfara'a tace mu ma munyi taku ai Mami sannu kinji Allah ya raba lafiya" kunya ce ta kama Husnah ta yi saurin cewa "bari inje inyi wanka" ta nufi part d'in ta, Zainab da ta gane kunyarta Husnah taji, sai taji yarinyar ta burgeta, murmushi tayi tace "banda abin Mami meye na kunya, Ina zan kai wannan rabon idan na hana auren nan" Daddy yace"Wallahi da kuwa tsaf za ki mutu ki yimin asarar ki,kisa na fara hauka" kalamansa ya sanyaya wa Zainab zuciya, yaran da suka samu su sweet da chocolate da zam-zam da biscuits da bindigan da kayan wasa sai hidimarsu suke cikin murnar dawowar Daddy da Maminsu.
Zainab ce ta taimaka wa Daddy ya yi wanka, ganin ta kwantar da hankalin ta har kyau ta k'ara a idanunsa, shirya shi tayi, tace" bari a Kira Mami ku ci abinci " Daddy yace "ai ba ta cin abinci yanzu sai dai nama mi k'uli-k'uli (tsire) sai kuma kindirmo shikenan abincinta ruwa ma ba sha take ba sai ta sa lemon tsami a ciki Kuma shima kad'an take sha" tausayinta zainab taji tace"Allah sarki ka had'ata da aiki daman kai cikinka wahala yake bawa mutane" Daddy yace"nima ai da wahala nake yinsa ko, sai kuyi ya d'oramin laifi alhalin ba ni bane mai ba yarwa" dariya kawai Zainab tayi ta kama shi suka sauko domin cin abinci. Zaman lafiya suke sosai sun had'e kansu hankalin Daddy ya kwanta.
Bayan wata biyar da dawowar su Husnah ta ta shi da ciwon baya da mara tak'i fad'awa kowa, dan kunyar Hajiya Batulu take,shiyasa da tace a dawo da ita gida wajen ta Daddy ya gayawa Husnah tace ita dai ya bari sai ta haihu tukun nan sai ta koma, Hajiya Batulu ta zuba musu ido Amma hankalin ta yana kan Husnah yau take da niyyar zuwa har gida ta sakota agaba dan taga Sadduk'u ba shi da niyyar kawo mata 'yarta.
Husnah ita kad'ai a d'aki Daddy ya je part d'in Zainab dan yanzu ya koma kwana tare da Husnah Zainab tace ta yafe har sai Husnah ta haihu tukun nan.
Shaf ta manta edd d'inta yau ne, shi kuwa Daddy yana sane shiyasa komai da ake buk'ata na haihuwa Zainab ta had'a musu lokaci kawai su ke jira.
Tun da ya shigo parlor yake jiyo yadda take faman wayyo bayana wayyo marata, da gudu ya shiga dak'in nata a durk'ushe ya sameta daga ita sai wata 'yar riga ko pant da bra babu duk ta jik'e da gumi hankalin sa ne ya tashi kaya ya sa mata ya ciccib'eta zai sa amota motar su Hajiya Batulu ta shigo, cikin fad'uwar gaba Hajiya Batulu tace", haihuwar ce ko,tunda na kasa nutsuwa nasan akwai abinda ke faruwa, driver ne ya jasu Hajiya Batulu tace Daddy ya kawo kayan haihuwa, su suntafi.
Chapter 2 · 0% Book details