← Book details Sawun Giwa Part 8 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 6

Sashe 6

Sawun Giwa Part 8 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan sunyi wanka sun hutu maisoon ta ɗora da rigimar zuwa gidan yah muhseen gun Aisha domin gabaki ɗaya hankalinta na gunta. Daƙyar tabari taci abinci, inda sheikh sudais yace Shima zashi domin yanaso duka yaga family ta, Hakan yah fawan ya ɗauke su zuwa gidansu. Humm zokuga murna gun Aisha da humairar yah fawan dudda batasan maisoon ba afuska amma tanajin labarinta sosai agun Aisha. Yah muhseen yayi farin cikin ganin ƙanwar tashi damijinta. Hakan suka baje a parlor yah muhseen ɗin sunata firar yoshe gamo. Maisoon ta kalli Aisha cikin Farin ciki tace "wayyoo Allah sweetheat Ashe nakusa zama mama shine baki taɓa gayamin ba dasedai kawai naji haihuwarki? Dariya sosai Aisha tayi kana tace humm "kema dabakizoba ai bagayamin zakiyiba maybe ma naki yariga nawa, ko Anty humaira? Ta tambaya tana kallon humaira. "Wlh kuwa Aisha nima dai Hakan nagani. Damamaki maisoon tace "banganeba mikike nufi sweetheat? "Abinda kike nufi mana ko kinaso kicemin bakisanda cikin jikinkiba dudda ya bayyana kanshi? Ido maisoon tawaro tareda ɗora hannunta akan cikinta tana faɗar cikidai sweetheat? Sekuma tajuya tana kallon sheikh sudais dashima ita ɗin yake kallo yanason tabbatarda zancen Aisha, kwaɓe fuska maisoon tayi kamar zayi kuka. Shi kuwa sheikh sudais gira ɗaya yaɗaga mata yana wani miskilin murmushi aranshi yana Fatar zancen Aisha yazama gaskiya. Hakan yasa Maisoon maida kallonta gun yah muhseen tace "kaganta ko my one bro. Murmushi yayi cikin sanyin halinshi kana yace "my life kin takurawa ƙanwata ko? "Allah my only bro bazancen takura Wlh sweetheart na ɗauke da ciki wanda nake tunanin yayi nisama itace bata ankara dashiba dudda kasan cewarta doctor, sekuma ta kalli sheikh sudais dake danna wayarshi yana tasbihi kamar besan abinda sukeyiba tace "Allah yatemaki Dr sheikh dan Allah ba gaskiya nake faɗa ba? Ko kaima dai likintancin beyi aiki akan sweetheat ɗita ba? Ahankali yaɗago da cat eyes ɗinshi yana kallonsu da murmushi kwance akan kyakkyawar fuskarshi kana ya ɗauke kanshi kamar bazeyi magana sekuma yace "kinada gaskiya Aisha kun kusa zama manya, daga Hakan ya ɗauke kanshi. Ido maisoon tawaro zata komayim magana kenan taji yarima basam na faɗar "wow masha allah amma Anty gimbiya shine kuke mana ɓoyo aikuwa yanzu zanyiwa Ammi albishir yafaɗa yana ciro wayarshi tareda dokawa gimbiya zaitun kira, domin sim ɗinshi ko wacce ƙasa yake aduniya ze iya magana da wata ƙasar, jin gimbiya zaitun ta ɗauka yasashi fara mata albishir batarema da ya gaidataba...aiko tayi Farin ciki sosai kamar tazuba ruwa aƙasa tasha, yana kashewa yakira gimbiya Rumaah itama yayi mata wannan dadda ɗan albishir wanda baya da tabbas akanshi 😂 zokuga murna da Farin ciki agunta hadda taka rawa kamarba matar sarki ba.... Maisoon kuwa gabaki ɗaya tashige wani yanayin ganin abin takeyi kamar almara, ganin shirunta yayi yawane yasa yah fawan cewa "rabidasu ƙanwata bara idan mundawo daga gidan abbey nakaiki hospital kiyi gwaji dakanki semu tabbar kinji. Hakan yasa tasauke ajiyar zuciya amma bini, bini tana shafa cikinta tareda kallon sheikh sudais, wanda dasun haɗa ido yaɗage mata gira ɗaya yana murmushi.

Sunjima agidansu yaya fawan kafin sutashi dukansu sunufi gidan abbey, sosai mama tatarbesu domin taji daɗin zuwansu hakama abbey yayi Farin ciki sosai daganin sheikh sudais amatsayin mijin ƴarsu, sosai yakejin alfahari akan wannan auren dayayiwa Maisoon domin doline zefi kowa Farin ciki, sabida shine yabada Ita, da Ace akasin Hakan aka tadda mijin shine wanda mahaifanta zasuyi kuka dashi, sosai suka sha fira gidan abbey yanata saka musu albarka. Hakan suka fito sukaje gidan Abba, acanma sunsamu tarba me kyau gun umma da Abba, se nan,nan sukeyi da maisoon kamar zasu maidata ciki, sukuwa yayunta mazan motsi kaɗan zasuce "autar mom minene? Kinason wani abunne? Harsu yah Jafar da yah jawal Hakan suke mata bayama yah fawan da yah muhseen, abin har mamaki yake bawa sheikh sudais ganin yadda family ta ke matuƙar bata kulawa. Sunjima sosai agidan basu suka barshiba se yamma liss, amma ahakan maisoon tace se sunje hospital tukkunna sukoma gida, Hakan suka ɗauki hanyar hospital ɗin Abba, suna shiga jikinta na rawa tawuce ɗakin da ake hoto, domin ita sam takasa yadda da abinda suke faɗa. "Sweetheat kiyimin hoto yanzu please inaso na tabbar da zancen ku. "Tayaya sweetheat kokin manta ba gefena bane ina likitan ido inani ina hoto kuma. Juyawa tayi gunda sheikh sudais ke tsaye yana kallonsu tahaɗe hannunta biyu cikin shagwaɓa tace "please my sheikh. Murmushi kawai yayi tareda miƙawa yarima basam wayoyinshi kana yanufi gadon datake kai, sekuma yajiyo yana kallon yarima basam da yah jawal wanda sukawai suka rage a ɗakin se Aisha. Juyawa yarima basam yayi yafice yana faɗar "yah sheikh badai kishiba, shikuwa yah jawal dariya kawai yayi yanajin daɗin yadda yake hango soyayyar ƙanwar tashi a ido sheikh sudais. Bayan sun fita se ɗakin yarage dagasu se Aisha. Ahankali yafara mata hoton cikeda kwarin guywar samun abinda yakeda muradin gani, aiko dai Sega ciki raɗau ya bayyana harna tsawon wata 5 amma basu kulada akwaishiba sabida yashige cikin hips ɗinta, wani irin waro ido sheikh sudais yayi ganin watannin cikin kenan aurensu da wata ɗaya akasameshi? Yatambayi kanshi, afili yake maimaita alhamdulillah alhamdulillah alhamdulillah jin Hakan yasa daga Aisha har Maisoon kallon computer ɗin cikin mugun mamaki dukkansu suka zaro ido suna kallon abinda suka gani tabbas cikine harna tsawon wata biyar sedai Allah yaɓoye musu ganin ko minene acikin. Wani irin ihu Aisha tadoka tareda kwasa aguje tanufi yayan nasu, dasauri ya muhseen yatareta yana faɗar "ke idan kikayi mana wata barnar fa wurin murna. Murmushi tayi wanda ke nunida tsananin fatin cikin datake ciki kana tace "Wlh my only bro sweetheart na ɗauke da ciki harna tsawon wata biyar. Ido duk suka zaro tareda haɗa baki wurin faɗar"haba dan Allah? Wlh kuwa, tafada cikin tabbatarwa. Aiko Anan aka shiga murna da Farin ciki kamar ba gobe, sunjima suna yiwa junansu murna kafin sukabar a asibitin bayan duk sun kira iyayensu maza da mata sun sanar musu, kuma Hakan yayiwa iyayen daɗi domin sosai suka bayyana Farin cikinsu, Hakan suka koma gidan mom cikeda ɗimbin Farin ciki. Bayan sun ajiye maisoon da Aisha harda humaira domin Aisha tacewa yah muhseen itafa bazata koma gidaba har se sweetheat ɗinta ta koma, bekuma hanataba domin yasan shaƙuwar dake tsakaninsu. To shinefa bayan sun ajiyesu Sheikh sudais yace yah fawan yakaishi hotel baze iya zama Anan ba, bayadda beyiba amma san yaƙi acewarshi gidan iyayenshine, ganin Hakan yasa yakaishi gidan yah muhseen tund Aisha ta gudo...Hakan suka rayu a Nigeria seda sukayi kusan sati ɗaya kana suka koma Dubai bayan su mom sun cikasu da abubuwan buƙata wanda babusu a can, hakama sheikh sudais yayiwa su Abba alkhairi na ban mamaki, dakuma yayun matarshi, Hakan sukabar Nigeria cikeda ɗimbin kewar ahalin matarshi da karamcinsu..ahakan jirginsu ya sauka ƙasar Dubai inda tun kafin su isa excout ɗinshi da fadawan masauratarsu tuni sukayiwa airport ɗin dirar mukiya suna jiran ƙarasowarsu..suna fitowa daga jirgin suka nufi motocinsu suka shiga tareda barin filin jirgin gaba ɗaya......!

Autar alheri ✍️
Chapter 6 · 0% Book details