← Book details Sawun Giwa Part 8 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 6

Sashe 3

Sawun Giwa Part 8 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tayi wani irin tako ɗaya Segata agaban kursum, ɗagowa tayi da zimtar yin magana taji kawai am fisgeta daƙarfin gaske tareda nufar pert ɗin gimbiya zaitun da Ita...ido yarima junaid yawaro ganin yadda Maisoon ɗin tafigeta, kafin yayi wani tunanin ta buɗe ƙofar parlor ta jefeta aciki, kuma tana jefata sheikh sudais na fitowa daga mota... gimbiya saudat har gimbiya zaitun miƙewa sukayi tsaye da sauri ganin yadda aka jefa kursum..ido gimbiya saudat tazaro cikin mugun bala'i tace "ke dan ubanki agabana zaki illatamin ƴa? lalle ko zanyi maganin rashin kunyarki agidannan shegiyar banza karuwa ƙasƙantacciya, ƙarasa faɗar hakan tana yowa kan maisoon,,,,yarage saura tako biyu taƙaraso gunta ta tsaya cak inda takasa gaba balle baya, sakamakon wata muguwar shaƙa da maisoon tayi mata seda duk idonta suka firfito waje...sheikh sudais dake takowa zuwa wurin ta dakatar cikin ɗaga murya, domin yarima junaid ne yake sanar mishi ba lafiya ba...itako cikin alamun gargaɗi take faɗar "my sheikhh data irin murya tace "karka ƙaraso nan wurin shiga pert ɗinmu kawai daga baya kafito karka ƙaraso nace, tafaɗa da ɗan ƙarfi...sororo sheikh sudais yayi yana nazartar kalamanta...itako gimbiya saudat dake halin rayuwa ko mutuwa sabida muguwar shaƙar da aka mata, tace "maza kursum tashi kihaɗu da banzan gayanan inajin muryashi tashi kiganshi koda namutu zanyi farin cikin cewar kinsamu muraɗinki, tafaɗa cikin har haɗa magana..ido gimbiya zaitun tazaro hakama yarima junaid dasuka soma fahimtar wani abun..shikuwa sheikh sudais ko motsi beyiba yazubawa saurautar Allah ido kawai yana kallo...yunƙurin tashi gimbiya kursum tayi cikeda Gwarin guywa, sedai cikin takaici gimbiya zaitun ta hankaɗeta takoma faɗuwa cikin dakiyar zuciyar tacewa junaid maza "zo zakamin ita bedroom ɗin can ka kulle sheikh sudais yazo yacire matarshi ajikin wannan mushirikar kafin takasheta nauyin miyagun laifukanta sukoma kanta wanda bana Fatar hakan gara tagirbi duk abinda tashuka da hannunta, taƙarasa zancen cikin dakiya dashiryawa fito nafito da memartaba sarki Hassan akan wannan lamarin domin izuwa yanzu gimbiya saudat takaita makurarda bazata iya kyaletaba.

Junaid najin umurnin mahaifiyar tashi yaraɓa gefensu maisoon dake tsaye shaƙeda gimbiya saudat data jima da somewa yashiga,,,yana shiga yaja kursum ɗin kamar yaja kayan wanki, tana ihu tana ƙarawa yajefata acikin wani bedroom dake cikin parlor ya kulle ƙofar..ganin hakan yasa gimbiya zaitun faɗar "sheikh zo kacire matarka daga jikin wannan, tafaɗa cikeda bada umurni furkarta babu alamun wasa...bece komaiba yashiga takowa haryazo inda suke bakinshi ɗauke da sunayen Allah, yana isowa yasaka hannunshi na dama yadafa maisoon, kafin yace wani abun kawai yaga tasake gimbiya saudat ita kuwa tayi baya luuuu zata faɗi, cikin sauri yatarota dawo jikinshi, bata sumaba kuma batayi bacci ba idonta tar akanshi sedai kallo ɗaya zaka mata magane cewar ba ita kaɗai take ba amma ga dukkan alamu ba'ataɓa sanin tanada makaraiba sabida basa bayyana sedai takan birkicene aduk lokacinda ranta yaɓace. Suna haɗa ido tasakar mishi lallausan murmushi tareda kai hannunta kan kyakkyawar fuskarshi tashafo sajenshi..shima martanin murmushin yamaida mata dudda cewar ranshi duka ba daɗi kuma yana ayyana cewar gobe zasu bar masarautar sukoma Dubai domin sam shi bayason tashin hankali da hayaniya, daga wannan abin se wancan sam bayaso...da wannan tunanin ya isa pert ɗinshi yana ɗauke da ita ajikinshi, yawuce har bedroom ɗinshi ya kwantarda ita kana yadawo parlor yana dannawa yarima junaid kira...bayan yaɗaga ya amsa sallamar shi kana yace yazo kawai yana nemanshi daga hakan ya yanke wayar.

Babu taɓa lokaci yarima junaid yaƙaraso anan sheikh sudais ke tambayarshi abinda ke faruwa, nisawa yarima junaid yayi kana yabashi labarin tun abinda yagani tsakaninta da sojojin dake get na ukku dakuma cewa da sukeyi anty saudat ce tace suhukun tata, har kawo hukuncin dayayi har suka iso inda kursum take har shi sheikh sudais ɗin yasamesu, duka yasanar dashi beboye mishi komaiba...tunda yarima junaid yafara magana mamaki yacika ran sheikh sudais akan wannan al'amarin "to miyayiwa gimbiya saudat ne takeyiwa matarshi mafi soyuwa agareshi wannan danyen aikin...yanacan yalula duniyar tunani ɗan aiken memartaba ya isa akan cewar sheikh sudais yazo da matarshi yana son ganinsu, harda yarima junaid. Tashi yayi yasaka maisoon agaba da yarima junaid suka nufi pert ɗin memartaba zuciyarshi duk acakuɗe yana ayyana matakin da ze ɗauka domin sam baze lamunci wannan abin ba

Koda yashiga turakar memartaba sarki Hassan dukkansu suna zaune domin gimbiya zaitun ce dakanta a wannan karon takawo zancen wurinshi ba ƴar lelenshiba, sabida ita seda gimbiya zaitun ɗin tasaka wasu bayi suka saka mata ruwa kana tafarfaɗo amma kamar bata hayyacinta har yanzu...shine yafara shigowa yana riƙe da hannun maisoon se yarima junaid, zama sukayi agabanshi tareda gaidashi cikin girmamawa...seda ya amsa tukkunna yakafe maisoon da ido yanason gano wani abun gameda ita amma yakasa, nisawa yayi kana yace "sheikh Mike faruwane agidan nan marar daɗi hakan? Yanzu amminku tazomin dawani zance. Shiru sheikh sudais yayi kamar bazeyi magana domin wlh daba memartaba bane Allah baze amsa mishiba, cikin kamalarshi yace "nima bansan Mike faruwaba zuwa kawai nayi nataradda abin. Kafin memartaba yayi magana sukaji muryar gimbiya saudat tana faɗar "eh ai doline hakan zakace tunda shigiyar matarka ƙasƙantacciyar baƙar fata rayiwa ƴata duka har sau biyu nima tayimin amma kace bakasan Mike faruwaba sabida muna furci, sekuma tajuya gum maisoon da jikinta yafara cira tace "wlh komi baƙin halinki se kursum ta auri mijinki badukaba komi zaki mata sedai kiyi, bari ganin kin ɓata wannan shirin kin hanata ganinshi Allah Indai ina raye seta aureshi. Cikin tsawa sauki Hassan ya dakatar da ita tahanyar faɗar "ya isa hakan saudat bakiraki nayi kiyimin shirme ba anan..jin abinda yayan nata yace yasa doli tayi shiru badan tasoba sedai tana ayyanawa aranta doline tafidarta maisoon agidan domin akanta ne memartaba sarki Hassan yafara mata tsawa....cikin girmamawa junaid yace pappu duk abinda yafaru kowanne ina tsaye akayi na farko nida yaya basam duka muna gun yau kuma nine kawai awurin idan kayimin izini zangayama iya abinda nasani, yafaɗa kanshi aƙasa sabida biyayya wa mahaifin nashi......nisawa memartaba yayi kana yace "inajinka junaid Mike faruwa ne? Jin hakan yasa junaid bashi labarin tun jiya data zuba magani a black Tea har yadda suka ƙare da maisoon har kawo yau da duk akayi hakan.

Tunda junaid yafara magana mamaki yarufe memartaba har inda yakai ƙarshen dagashi har gimbiya zaitun, sedai besamu zarafin yin maganaba gimbiya saudat tayi saurin cewa "tokadai kaji dabakin ɗanka kaji abinda yake faɗama yanzu inbanda samun wuri daneman fitina inaruwanta dan kursum tazuba abu a abinshan sudais? ina ruwanta dan kursum tazauna sudais yaganta? batare tazo tasamesu ba? Shine zatayi mata mugun duka hakan harda sumarda ita? Nima abin be ishetaba hardani? Gaya duk tajamin asara batasan iya wahalar da nayiba kafin nasamu abin amma tawargazamin komai to Wlh Allah bazan yadda ba doline a kaɗauki hukunci akanta yaya doline tasan cewar akwai tazara tsakaninmu da ita..tasss, tasss, kakeji memartaba sarki Hassan yaɗauke gimbiya saudat da kyawawan marukan dasukayi sanadiyyar haɗiye sauran kalamanta, tana zare ido dalaluben ta inda sautin kunnenta zedawo mata...cikin takaici dajin kunyar abinda ƴar uwar tashi ta aikata kuma wai akan ɗan amininshi yace....!

Autar alheri ✍️

🐘🐘🐘 *SAWUN GIWA*🐘🐘🐘

Book 4

Page 85 & 86

"Yace haƙiƙa ke zama ƙazanta acikin ahalina saudat wannan wanne irin rashin imanine darashin tarbiya? Kaicona dana kasance yaya agun azalumar mace irinki, kincutarda yarana da matata saudat nayi shiru domin ina kallon ke ɗin amanata ce shiyasa duk abinda kikeso shinake miki amma sam bakyagani wannan ne yabaki damar taka wanda kikeso sedai banyi tunanin abin naki zebar kan ƴaƴana yaje har kan yaro mefi soyuwa agareni ba, ɗan aminina wanda inada tabbacin kinfi kowa sanin waye sarki Muhammad bilal akan yaronshi, amma tunda kika take saninki harkikaga zaki iya cutardashi da matarshi to tabbas yau kuwa zan nuna miki keɗin bakowa bace face mutun kamar sauran al'umma zan hukuntaki abisa laifukanki kamar yadda nake hukunta duk wanda yayi laifi dede da laifinshi banza marar tunani, yaƙarasa zancen yana ɗauko wayarshi domin ya saka aranshi doline seya hukuntata abisa wannan laifi.

Ganin hakan yasa sheikh sudais da kanshi ke ƙasa yayi saurin ɗagowa yana kallon memartaba murya araunace yace

"Dan Allah memartaba abbarta kayi haƙuri plesse kamar yadda Manzon Allah sallallahu Alaihi wasallam ya umurtaddamu, nidai nayafe mata sabida hakan nake nema mata alfarma awurinka ayafemata plesse, kuma nida take abin akaina aiyazo ƙarshe domin Dubai zan koma gobe in sha Allah badan wannan dalilinba sedan kiran dana samu agun abbey na to inaga zamu ɗan jima bamu dawoba kafin wannan lokacin ai komai yawuce in sha Allah. Yaƙarasa maganar cikin tsananin ladabi agun sarki Hassan tareda fargabar karyayi tunanin sabida wannan abin ne yahanashi zuwa koyaji ba daɗi.

Nisawa sarki Hassan yayi cikin dattako yace "shikenan sheikh tunda hakan kaga yadace bazan hukuntata ba, tafiya kuma Allah yakaiku lpy cikin amincinsa.

Sekuma yajuya gun kursum dake zaune rakuɓe gefen uwarta yace "kiyi gaggawar fitarda mijin aure nanda mako biyu, idan ba hakanba zan haɗaki da koma waye nasamu sha'sha shar banza wadda batasan kantaba....dasauri suka kalleshi daga ita har uwar tata sedai ayadda sukaga yanayin memartaba yasa dole sukayi saurin maida kansu ƙasa atake wani mugun tsoron sarkin yashigesu wanda basu taɓa jiba tun tsawon lokaci se a yau...ahakan memartaba ya sallami kowa bayan yayi musu nasiha me ratsa jiki da zuciya, wasu sun ɗauka wasu ko sedai muce Allah ya kyauta.

Aranar dai hakan suka kwana zuciyar kowa ba daɗi, washe garin ranar misalin ƙarfe 5 jirginsu zetashi zuwa Dubai hakan yasa maisoon gayawa sheikh sudais tanason zuwa wani wurin kafin suwuce..shikuwa betsaya binciken komaiba ya amince mata, tareda bata sojojin dazasu rakata. Hakan tafito bayan tanemi rakiyar junaid domin hakan kawai taji dashi takeso sutafi. Kusan mota 6 hakan suka fita tamkar sheikh sudais ɗinne dakanshi zeyitafiyar.
Chapter 3 · 0% Book details