← Book details Sawun Giwa Part 8 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 6

Sashe 5

Sawun Giwa Part 8 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wani irin murmushi tayi wanda ke nuna tsananin jin daɗinta nasamun nasarar datayi akanmu, kana ta tasarma kawarta ɗaya, sukuwa wasu yammatan suka farwa junansu, cikin zalama da ɗaukewar imani suke aikata wannan mummunan saɓon,,,, ɗaya ƙawarta ce tace na ajiye wayata kafin sufara. Aiko na ajiye ba musu nazuba musu ido ina kallon wannan rashin imanin,,,,,yayinda sweetheat keta rusar kuka kanta aƙasa....wani irin abu sukeyi kamar ba Musulmai ba yadda kasan jama'ar annabi lud da akafitarwa da imani arai, se ihu sukeyi da gurnani sabida suɗauki hankalinmu mushiga cikinsu babu shiri,,,amma sukaga har suka gama sheƙe ayarsu ba wanda yamotsa acikinmu, domin inaga hankalinsu yayi nisan zangon da bazasu tantance muna wurinba ko bamanan, seda suka gama duk abinda zasuyi suka samu nutsuwar dasuke buƙata kana anty Rukky ta ɗago tanamin murmushi tace "maisoon yanzu kunganiko ina Fatar kun ɗauki darasin daya dace seku nuna mana mugani, tafaɗa tana kashemin ido....wani malalacin murmushi nayi wanda yafi kuka ciyo ina takowa ahankali zuwa inda wayata take ina faɗar "tabbas kuwa anty Rukky kun koyarda darasi, acikin gulɓataccen tunani, yanzune zan koyardaku asalin darasinda zedaki ƙwaƙwalenku, cikin hikima, naƙarasa zancen ina danna wayata, atake video duk abinda sukayi ya bayyana tun daga farkon shigowar mu har yanzu...wani irin waro ido sukayi cikin mugun tashin hankali sukayo kaina. Dasauri na ɗaga musu kana naɗora da faɗar "tako ɗaya idan kuka ƙara yana Dede da fitarda video ku ne a social media domin yana kan tictok ne motsi kaɗan zakuyi nayi sending ɗinshi Wlh duk duniya seta gani, banzaye masu ƙwaƙwalwar kifi...cak duk suka tsaya suna kallona cikin mamakin yadda akayi nayi video bayan babu waya a hannuna, kamar nasan abinda suke tunani na ɓalle ƙarfe dake tsakiyar rigata anan sukaga ƙaramar Camarar leƙen asiri aciki, murmushi nayi kana na kalli Anty Rukky bayan natako har gabanta, nace "Hajiya Rukayya dikko dillah kinyi gangancin cewa zakiyiwa maisoon barazana ko sharri domin duk inda kika dosa ni atafe nakwana nafiki iskanci da iyashege kawai nabawa kaina lafiya ne, kuma kisani Wlh sedai kumutu indai sekin koyardamu wannan mummunan ɗabi'ar zaki rayu, domin kuwa Aisha da maisoon sunfikarfi duk wata sheɗaniya irinki, ɗan juyawa nayi ina kallon ƙawayenta dasukayi mutuwar tsaye aciki kuwa hadda sweetheat dakebina da kallon mamaki, kana najiyu gun anty Rukky na ɗalla mata yatsuna biyu agefen fuska inda suka bada sauti metashi Sosai, ɗass,ɗass. kana na ɗaga mata gira ɗaya nace "kiyi abinda yadameki muyi namu karki ƙara gigin nuna kinsanmu balle ba'asin shiga rayuwarmu idan kunne yaji jiki yatsira, ina gama faɗar hakan nakama hannun sweetheat mukabar gidan,,,,,tun daga wannan ranar bamu ƙara saka Anty Rukky a idonmu ba har mukabar Saudia, kuma musan gabaki ɗaya mun fiddata daga cikin lissafin rayuwarmu, Ashe ita abin naranta sam bata barshiba kawai tayi shirune alokacin domin bata da yadda zatayi.

Bayan mundawo Nigeria muka shiga harkar gabanmu bayan wani lokacin akayi auren Anty meenah da Dr Hareesh wanda yakasance anan Saudia yake aiki Hakan yasa Anty meenah dawowa Saudia da zama, wanda zan iya cewa shine sanadin ƙara haɗuwa ta da Hajiya Rukayya dikko dillah ta hanyar surukarta wato uwar mujinta dana temaka dakuma ɗanta yaseer dayake sona asanadin wannan kakar tashi, kuma shine sanadin haɗuwa ta da sheikh sudais, bayan mun koma Nigeria abubuwa dayawa sun faru asanadin neman aurena da ɗanta keyi, Anan naƙara bawa yarima junaid labarin abinda yafaru tun farkon ganina da hajiya Rukayya dikko agidansu yaseer matsayin mahaifiyarshi, harkawo saceni datayi izuwa aurena da sheikh sudais nadawo Saudia harkuma jiya da Hajiya Rukayya tasaka ana bibiyata ataƙyaice dai bata haƙuraba kenan wannan dalilin ne yasa nasaka aka kamata domin ahukuntata abisa laifin datayimin wanda take aikatawa kuwa wannan tsakaninta ne da uban gijinta. Maisoon taƙarasa bawa yarima junaid labarin tana miƙewa tsaye domin taje tashirya sabida lokacin tafiyarsu yakusa....Shima yarima junaid miƙewa yayi yana jinjina girman abin afili yace "tabbas taso cutardaku Anty kuma Hakan dakikayi shine Dede in sha Allah seta karɓi hukuncin yadda gobe koda mahaukaciya tagani akan titi bazatayi kwaɗayin lalata mata tarbiyaba balle kuma me cikakken hankali, yana gama faɗar hakan yafice daga parlor.

Da kallo maisoon tabishi har yafice daga parlor tana hango tsananin ɓacin rai atare dashi, Hakan tanufi bedroom ɗinta tashirya kamar yadda sheikh sudais ya umurceta, bata jima da shiryawaba yadawo Shima wanka kawai yayi yashirya kana suka fito, seda sukaje sukayiwa memartaba da gimbiya zaitun sallama kana suka tafi bayan sun haɗawa maisoon tsaraba takece raini, Hakan sukayi tafiyar koyanzu tareda yarima basam domin duk inda sheikh sudais yasaka ƙafarshi to ta yarima basam na wurin, ahakan jirginsu yaɗaga zuwa Nigeria wanda sam maisoon batasan cewar Nigeria suka nufa ba duk ita atunaninta Dubai zasuje sedai tayi mamakin yadda yazo da excout ɗinshi dake nan domin tsakanin Dubai da Saudia duk inda zashi baya zuwa da excout ɗin sabida ko ina akwaisu, to yanzu dai jirginsu ya lula semuce Allah yasaukesu lpy......!

Autar alheri ✍️

🐘🐘🐘 *SAWUN GIWA*🐘🐘🐘

Book 4

Page 89 & 90

"Jirginsu na sauka Nigeria suka soma fitowa, da kallon mamaki maisoon kebin filin jirgin kafin tajuyo tana kallon sheikh sudais baki sake...gira ɗaya yaɗaga mata tare kashe ido ɗaya kana ya ɗauke kanshi kamar Bashine yayiba...wani irin mugun daɗi ne yaziyarci Maisoon wanda batasan lokacinda tafaɗa jikinshiba tana bashi wani irin hugg me matuƙar birgewa dashiga rai...ido yawaro hango yah jawal na tinkarosu, sekuma yasaki murmushi yana shafa bayanta tareda cireta ajikinshi...Shima yarima basam murmushin yayi, domin Allah yagani sheikh sudais da matarshi suna matuƙar birgeshi.

Cikin Farin ciki yah jawal yaƙaraso gunsu suka rungume juna shida sheikh sudais domin shi kaɗai yasanarwa da zuwansu, "sannuku dazuwa ƙasar Nigeria sheikh sudais ina Fatar kunzo lpy? Murmushin fuskarshi ya faɗaɗa yana jinjina kanshi alamar lpy qalau...Hakan yasaki sheikh sudais yarungume yarima basam, sosai sukayi Farin cikin ganin juna,,bayan yasaki yarima basam ya kalli Maisoon data kwaɓe fuska kamar zata rusa ihu tana turo baki gaba. "Ikon Allah 🤔 ke kuwa miye Hakan? Yatambaya yana kallonta..cikin shagwaɓarta data saba yimusu tace "bakaibane kashareni 😥 yah sheikh kawai kake tarba, tafaɗa tana turo baki. "Ayya sorry autar mom amin afuwa nikuwa nayi missing ɗinki over ƴar ƙanwata, yaƙarasa zancen yana riƙo hannunta. Hakan yasa tasaki murmushi tareda rufe idonta jin sheikh sudais na faɗar "my butty duk kishinne Hakan?. Dariya sukayi dukkansu kana suka tako zuwa inda motar yah jawal take, excout ɗinshi natake musu baya. Tsaye maisoon tayi tana kallon yah jawal cikin tabe fuska tace "yah jawal mota ɗaya fa kazo da Ita tayaya zata kwashemu Hakan? Murmushi yah jawal yayi kafin yanuna mata fawan dake ƙarasowa da zugar motocin shi harda guzurin yaranshi sojoji. Da mamaki tace "yah fawan. Dede lokacinda yayi perking kusansu. Buɗe motar yayi yafito murmushi kwance akan kyakkyawar fuskarshi yabawa sheikh sudais hannu suka gaisa kana yabawa yarima basam, daganan yace "autar mom munyi fishi nidai karma kicemin komai, yana gama faɗar hakan yajuya zuwa motarshi yanayiwa su Sheikh sudais alamar da sushiga motar yah jawal dayake buɗe mishi

Hannunta sheikh sudais yakama suka shiga motar kana yarima basam ya shiga motar yah fawan, sauran excout É—in su kuwa suka shiga sauran motocin, ahakan suka bar airport É—in suka nufi gida cikin jin daÉ—i.

Lokacinda suka isa gidan baƙaramin Farin ciki mom tayi daganin autar tataba hakama Dady yaji daɗin zuwan sheikh sudais sosai domin se yau ne sukaga mijin yar tasu. Mom tashirya musu tarba ta musamman domin yah jawal yasanar da Ita zuwansu. Sheikh sudais da yarima basam kuwa pert ɗin Dady aka saukesu, sosai family maisoon suka basu kulawa ta musamman suna ƙarajin daɗin kasan cewar ƴarsu matar wannan malamin....mom kuwa tinda sukazo takebin maisoon da kallo tana addu'ar Allah yasa hasashenta yazama gaskiya domin sosai take mata kallon me ciki wanda har yafara bayyana kanshi amma dudda suke likitoci daga ita har mijinta Allah be ganar dasuba se mom.
Chapter 5 · 0% Book details