← Book details Sawun Giwa Part 5 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 7

Sashe 5

Sawun Giwa Part 5 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yauma kamar kullun yana zaune a parlor shi yana aikin nashi wato tunani, ahankali yake buɗe baki yana tasbihinshi daya saba, idanuwanshi alumshe kamar me bacci amma sam ba bacci yakeyiba,,,,,yarima basam na gefenshi yana danna wayarshi kira yashigo wayar sheikh ɗin kusan karona huɗu kenan, amma ko kallon wayar beyiba,,,,shikuwa yarima basam jin na huɗun na neman ɗaukewa ne yasashi ɗagawa ganin talal ne kekira wato abokin sheikh sudais dake Dubai, "assalamu'alaikum yah talal inawuni . "lpy qalau basam ne? "Eh. "Okey yarima dakansa ina sheikh ne? Kunga abinda ke faruwa kuwa? "Yana lpy bamu ganiba minene yah talal? "Humm ku kunnan tv zakugani yanzu, yana gama faɗar hakan ya yanke wayar cikin mugun mamakin abinda yagani...shiko yarima basam jikinshi har rawa yakeyi wurin kunna tv, yayinda sheikh sudais dake jinsu ya ƙara lumshe idonshi amma bece komaiba koma motsi beyiba,,seda yaji yarima basam na faɗar"whatt? Yah sheikh duba kaga, se alokacin taɗago da cat eyes ɗinshi yana kallon tv sedai Bashiri yamiƙe zaune ganin mahaifinshi riƙe da hannun wata budurwa wadda ko fuskarta ba'a gani yana faɗar surukarshi ce, cikin mugun tashin hankali da mamaki yake tambayar kanshi "surukarshi to matar waye? Atake ƙwaƙwalwarshi tace mishi kai mana yanada wani ɗanne bayan kai? Kuma seya tunada Nigeria fa sukaje kamar yadda abbeyn nashi yagaya mishi, to wacece ya aura mishi? Kaddai garin neman maisoon akwaso mishi wata daban, kai ina sam bazeyuba, wata zuciyar tace mishi idan kuma yayufa yazakayi? Zaka butulcewa abbey ne? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un yafaɗa da ɗan ƙarfi kuma abayyane kafin yamiƙe tsaye dasauri yaɗauki ɗaya wayarshi yanayi waje...ganin hakan yasa yarima basam kashe tv yakwashi sauran wayoyin yabi bayanshi...a harabar gidan yasameshi yanufi perking space kotakan hadiman dake gaidashi beyiba, sukansu sunyi mamaki domin dai sheikh sudais kobaze amsa gaisuwaba yakan ɗagawa mutun hannu alamar ya amsa kenan amma yau kam babu ko ɗaya,,,,shima yarima basam motar yashiga inda driver yaja sukabar gidan tareda rakiyar masu tsaron lafiyarsu.

Seda suka cilla motocin akan kwalta kana driver yace "ina muka nufa yallaɓai sheikh? " filin jirgi, yafaɗa ataƙaice, yarima basam najinshi amma bece komaiba hakan suka nufi filin jirgin, suna zuwa suka hau jirgi zuwa Dubai batareda wani ɓata lokaciba tunda yanada jirginshi na musanman aciki idan zeyi tafiya...jirginsu na tashi wanda ya ɗauko memartaba sarki Hassan nasauka, sekuyi rabuwar makaho da majayi😂

Basu wani ɓata lokaciba jirginsu yasauka Dubai kasancewar bawani tazarane tsakanin Dubai da Saudia ba...secrety ɗin masauratarsu ne sukazo ɗaukar shi domin basam yaturawa ɗaya daga cikinsu text ɗin sheikh sudais nahanyar zuwa garin, hakan yasa suka sanda zuwanshi....aiko yana fitowa daga jirgin ƴan jarida sukayomai chaaa suna mishi tambayoyi akan zancen aurenshi da memartaba sarki Muhammad bilal yafaɗa musu,,,amma ko kallonsu beyiba yashige mota gabanshi na ƙara dukan tara tara, basam ma shiga yayi suka ɗauki hanyar masarautar, suna shiga hadimai da excout ɗinsu suka taso sunata gaidashi amma sauri sauri hakan yake taka matakalar benen dazata sadashi da pert ɗin mahaifin nashi, shikuwa yarima basam yanufi pert ɗin gimbiya Rumah.

Tun a general parlor yake kiran abbey abbey abbey amma cikin taushin murya dudda hankalinshi yake atashe... memartaba sarki Muhammad bilal na turakarshi yaɗan kwanta yaji sassanyar murya yaron nashi meratsa zuciyar me sauraronta wadda hasken alqur'ani yagama ratsata daji base katambayaba kasan ma mallakinta ma'abuci karanta kalamaine mafi girma kalama da daɗin sauraro aduniya da kuma lahira wato alqur'ani me girma...ahankali memartaba yamiƙe zaune fuskarshi ɗauke da kyakkyawan murmushi yana jiran ƙarasowar ɗan nashi,,,tura ƙofar yayi yashiga inda yasameshi zaune yana kallonshi... ƙarasowa wurinshi yayi ya rungumeshi kamar yadda yasaba tareda manna mishi kiss, kana yaɗago yana duban mahaifin nashi...cikin kalama memartaba yace "sheikh ɗin abbey miyasameka naganka abirkice? Kodai haryanzu yar tawace ke dawainiya dakai ? Yayi maganar cikin barkwanci.

Shikuwa. Shiru yayi yana ɗan taune lips ɗinshi yana tsotsa kafin yace "abbey aure kamin dagaske? Wacece ka auramin abbey? Yayi maganar kamar ze saka kuka? Ɗan kallonshi memartaba yayi na ɗan lokaci kana yace "miyasa kayimin wannan tambayar sheikh bayan nagayama aure zanje nema ma? "Ajiyar zuciya yasauke cikin nuna damuwarshi yace "abbey neman aure Bashine ɗaura aureba ayanzu kuma senaji ana faɗar wai an ɗaura auren abbey wlh banason ganin ko wacce mace se ita a rayuwata itama bawai sonta nakeyiba kawai na yadda da aurenta ne sabida tafita daga rayuwata amma abbey bazan iya zaman aure da kowacce maceba sabida bazan iya sauke hakkinta dake kainaba kuma banaso Allah yatuhumeni akan hakkin wanima balle na mace plesse abbey miyasa zakamin hakan? Cikin mamaki da tashin hankalin memartaba yariƙoshi yana faɗar "bangane bazaka iya sauke hakkinta ba sudais bakada lafiya ne? Yatanbaya Aɗan ruɗe...yamutsa kyakkyawar fuskarshi kawai yayi kafin yace "lpy qalau nake abbey kawai de bazan iya bane gaskiya inajin kunyar hakan koku da kuke mahaifana inajin kunyarku balle kuma wata mace plesse abbey wacece aka auramin dan Allah akwanceshi plesse 😥 humm kawai memartaba yace yana wani miskilin murmushinsu na manya kafin yace "shikenan yadda kakeso hakan za'ayi za'a kwance amma sekun zauna na sati ɗaya kar iyayenta suga munyi musu rashin adilci kana daga baya se akwance yanzu kaje pert ɗinka kayi wanka kahuta sekaci abinci yadda duk kakeso hakan zanyima yarona, abbey yafaɗa yana shafa lallausar sumar kanshi...se alokacin yasaki murmushi kana ya sumbashi abbey ɗin yafita zuwa pert ɗinshi.

Acan pert ɗin gimbiya Rumah kuwa koda yarima basam yazo yasamu baƙi,,,cikin girmamawa yagaidasu kafin yanufi bedroom ɗinta inda yasameta zaune itada yarima junaid, shima zama yayi bayan yagaidata yake sanar musu tareda sheikh sudais suke ga abinda suka gani a tv shine yakawosu...murmushi gimbiya Rumah tayi kana tace "tabbas hakane basam ga junaid nan taredashi aka ɗauro auren, junaid bashi labarin daka bani, tafaɗa tana kallon junaid ɗin...aiko yagyara zama yashiga bawa yarima basam labarin yadda auren yakasance da duk yadda akayi kafinma abawa su memartaba auren kana yaƙara da cewa kasan babban abinda yafimin daɗi a auren nan ? "Cikin matsanancin mamaki yarima basam yace "a a... ɗan murmushi junaid yayi kana yace "yarinyar dataje gidanmu duba waccan banzar doctor danacema itace tayi mata theater aranar yarinyar nan marar tsoro wlh Allah itace abbey ya aurawa yah sheikh...ido yarima basam yazaro cikin wani sabon mamaki yace "dagaske? Wlh kuwa itace yah basam. "Alhamdulillah Allah nagodema wlh Allah nadaɗe ina tunanin son yarinyar nan yah sheikh keyi kuma najima ina masa addu'ar samunta domin ita kaɗai ce zata iya zama da wancan mutanen...hum kaide bari kawai ai memartaba ya kyauta mana wlh,,,,hakan suketa firarsu cikin jin daɗin wannan auren,, gimbiya Rumah na kallonsu tana murmushin jin daɗin kowa nason surukarta.☺️ Sheikh sudais kuwa yana fita daga pert ɗin memartaba kaitsaye pert ɗinshi yanufa kamar yadda sarkin ya umurce shi batareda yashiga pert ɗin gimbiya Rumah ba....maisoon kuwa bayan fitar gimbiya Rumaah ankawo mata kayan lefe bila adadin akwatuna kusan set 5 seda aka cika wani bedroom dake kusan na sheikh sudais,,,su anty meenah sunzo sungani suda su mama bayan sungani su mama sukayi tafiyarsu pert ɗin gimbiya Rumah sukuwa su anty meenah da anty zainab suka shiga tayata shirya kayan seda suka shiryasu tsab kana suka ficewarsu,,,itako tana dawowa bedroom ɗinshi tashiga wanka bayan tafito tabaza jikinta da sahihan turaruka masu sanyin daɗi kana taɗauki wata arbian guwn tasaka wadda tabi jikinta talafe kamar seda aka gwada kotunnah aka ɗinka mazaunanta sun zauna aciki ɗas dasu hakama breast ɗinta har nipples ɗinta kina iya hangowa,,,wurin mirro tanufa danufin tagyara gashinta kana taɗan kwanta ta huta,,to tabaje gashin kenan inda yazubo har gadon bayanta tana tajeshi,,,shiko yaturo ƙofar bedroom ɗin yashigo da sallama ɗauke a bakinshi, badan yasan akwai mutunba kawai de yanayin yadda shari'a tacene yin sallama idan zaka shiga wuri koda babu mutane aciki,,,,wani irin faɗuwa gabanta yayi lokacinda taji saukar sassanyar muryashi acikin dodon kunnenta, haka shima zuciyarshi tashiga bugawa tunkamin yasan da waye acikin ɗakin....!

Autar alheri ✍️
🐘🐘🐘 *SAWUN GIWA*🐘🐘🐘

Book 3

Page 55 & 56

"Takowa yashigayi haryazo bakin bed ɗin ya ajiye wayoyinshi cikin mamaki yake kallon mayafin mace a ɗakin hakan yasa yaɗagoda cat eyes ɗinshi yanabin ɗakin da kallo, wani irin warosu yayi duka lokacinda idonshi suka sauka cikin nata ta madubin, domin ko ame yaganta fuskarta bazata taɓa ɓacemaiba sabida takafa mishi tarihi arayuwarshi. Da yatsa yashiga nunata bakinshi narawa yanaso yayi magana amma yakasa faɗin komai, ganin hakan yasa taturo ɗan ƙaramin bakinta gaba tana ƙuƙunai domin duk ganinta renin hankaline sedai tunawada datayi da abinda ke jikinta yasata saurin jiyowa domin ta ɗauki mahaifinta, sedai ta makaro domin yana gab da ita abaya kaɗan ta faɗa mishi, ƙasa tayi da kanta cikin ɗan jin haushi tace "zanwuce. Bece mata komaiba kumabe bata hanyaba sema ƙara ware cat eyes ɗinshi dayayi akanta, kafin yabuɗe baki daƙyar yace "maisoon yafaɗa cikin wata irin murya meratsa jiki..dasauri ta ɗago tana dubanshi sedai takasa yimai rashin kunya sabida kwarjininshi.

Lallausar sumar fuskarshi yashafa zuwa ɗan gemunshi me kyau na sunna wanda yayi dede da fuskar tashi kana yace "shine kika gudu bayan kinshigo rayiwatako? Yafaɗa kamar Bashine yayi maganar ba...da mamaki taƙara ɗagowa tana kallonshi amma batace komaiba aranta dai take maimaita nagudu kamar yaya? Wai mi wannan ustaz ɗin kenufi dani? Bata gama tunaninta taji yace "nemanki nakeyi kamar zan zare amma bansamekiba segaya abbey na yasamominke har nashiga fargaba domin sam banyi tunanin ze iya samunkiba ashedai kuwa ke ɗin ce plesse minayi miki kike wahalar da ruhina maisoon? Yatambaya yana ɗan dafe gefen kanshi, irin surutun yaɗan dameshi amma kuma yanason yinshi domin hakan kawai yaji wani irin farin ciki da gushewar fargaba alokacinda yaganta domin sam beyi tunanin itace abbey ya aura masa ba shiyasa yaketa tambayarshi wacece amma dayace ze yadda araba auren seya share tambayar dudda be gaya mishiba.
Chapter 5 · 0% Book details