← Book details Sawun Giwa Part 5 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 7

Sashe 1

Sawun Giwa Part 5 Complete Hausa Novel · about 7 min read

🐘🐘🐘 *SAWUN GIWA*🐘🐘🐘

Book 3

Page 47 & 48

"Yace yaya Ishaq minake shirinji hakan? Waye sudais ɗin daka aurawa maisoon kahanawa ɗana? Wacece humaira daka aura masa kuma? Mihakan kenufi? Kenan tsanarda kakeyiwa fawan yakaiga kahanashi cikar burinshi...ya isa hakan yaya Umar plesse bayanzu yadace ayi wannan zancenba kabari musallami baƙi tukkunna. "Cikin hasala yace "yimin shiru Usman ai bakinku ɗaya duk atare kuke shirya munafurcin to wlh dukkanku baku isaba Allah sena ɗauki mataki akanku dani kuke zancen yana gama faɗar hakan yayi fuuu zebar parlor kamar zetashi sama...dasauri abbey yadoka mishi wata muguwar tsawa duk seda parlor ya ɗauka cikin ɓacin rai yace "wlh Umar karka yadda kabar parlor nan kaji nagayama idan kuma kafita tokasani ranka seyayi mummunan ɓaci feyeda yadda kake gani ayanzu, yana gama faɗar hakan ya kalli manyan sara kunan dake wurin zaune yace "dan girman Allah ranka yadaɗe kuyi haƙuri da wannan abin ɗaya faru damashine abinda nagaya muku tunfarko amma komai zededeta in sha Allah...murmushi kawai sarki Muhammad bilal yayi batareda yace komaiba hakama sarki Hassan, megirma shugaban ƙasa ma bece komaiba wannan faɗan ahaline.....shi kuwa abba tunda yaji abinda abbey ke faɗa kuma cikin muryar da betaɓa jinshi da itaba yatsaya cak batareda yayi gababa kuma beyi bayaba, hakan yasa Alhaji Ahmed buba wato wanda abbey ya aurawa fawan ƴarshi, miƙe tsaye tareda zuwa yajanyo hannun abba yana faɗar "plesse Dr Umar yihaƙuri kazauna mubi komai ahankali dan Allah. Becewa Alhaji Ahmad komaiba yabiyoshi kawai yazauna.

Acan kuwa sosai mutane kegaisawa da general muhseen da kanal fawan dudda baya cikin nutsuwarshi amma faɗan da yaya jafar yayi masane ne yasa yaɗan nutsu yana jiran kowa yawatse yaje yasaki kowacce shegiyace aka aura mishi, kafin yaci ubanda yahaife mijin maisoon 😳🙆 humm hakan taron yawatse wasu cikin farin ciki wasu kuwa da tarin tambayoyi aransu....anan cikin gidan kuwa tunda Aisha taji sanarwar an ɗaura aurenta da yaya muhseen tazube aƙasa tana sujjada agun Allah, sedai alokacinda taji anɗaura na maisoon da wani sudais hankalinta yayi mummunan tashi kaddai auren doline akayiwa ƴar uwarta? waye wannan sudais ɗin? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, atake fargaba ta rufeta sedai batayi gigin sanarda maisoon ba domin tana bathroom sam batajiba....a parlor mama ma hakan anty meenah tazabura tana faɗar sheikh sudais kuma dama shine abinda yakawo su memartaba agarinnan, tafaɗa cikin giɗima..dasauri anty zainab tariƙota tana faɗar "mikike nufi meenah? "Humm kedai bari zee wlh tun a Saudia naɗora ayar tambaya azuwansu sedai banyi tunanin abin hakan yake ba amma shakka babu da biyu akayi aurennan bara kiji abinda yafaru, nan anty meenah takwashe duk abinda yafaru azuwan maisoon Saudia tagayawa Anty zee. "Tirƙashi, shine abinda yafito daga bakin anty zainab alokacinda tagamajin bayanin da anty meenah tayi mata, "lallai meenah akwai ayar tambaya anan kodai ya auretane dan yayi maganin rashin kunyarta kokuwa ita wannan ƙanwar sarkince tasaka aka aura mishi ita domin ta ƙuntata mata ze iya yuwa shima besanda aurenba tunda kince babban mutun neshi me daraja a idon duniya, cewar anty zainab..."humm nima tunanin danakeyi kenan sedai kuma idan dawata manufar akayi auren to kuwa sunyi ganganci domin basusan wacece Autar mom ba, abu ɗaya nake jima tsoro kartajanyo abinda za'akashemu dukkanmu komu ƙare rayuwarmu a kurkuku domin dai base anfaɗaba kinsan wacece maisoon, anty meenah tafaɗa cikin alhini

"Hakane kam gaskiya amma in sha Allah koma minene zamuyi addu'a Allah yakawo munashi da sauƙi. "Ameen ameen. Daga hakan suka shiga sha'anin gabansu.

Su dady kuwa bayan sun sallami baƙin dasuka zo musu ɗaurin auren ne suka yiwasu memartaba iso pert ɗin abbey dake sama, anan suka zauna dukkansu inda suka tara har yaransu mazan duka, bayan kowa ya zauna ne abbey yadubi jawal yace "kiramin maisoon da Aisha amina dakuma zainab. To abbey jawal yace kana yamiƙe zuwa pert ɗin mama, a parlor yasamu anty meenah da anty zainab yasanar musu saƙon abbey kana yawuce bedroom ɗin mama inda yasamu duk suna zaune tareda wasu ƙawayensu, cikin girmamawa sukace yah jawal ina kwana. Lpy qalau ya amsa musu kana yace "kuzo parlor abbey yana kiranku Aisha keda maisoon, yana gama faɗar hakan ya juya abinshi amma aranshi fal tausayin ƙanwar tashi...sukuwa miƙewa sukayi dukkansu suka fito kowacce sanyeda hijab ɗinta harƙasa sedaifa maisoon inbanda dukan tara,tara babu abinda ƙirjinta keyi,,,suna shiga parlor gabanta yaƙara tsananta faɗuwa ganin taron mutanen dake ciki,,,jiki a sanyaye suka zauna kusan yah muhseen domin dukkansu sunfi sakewa dashi, cikin girmamawa suka shiga gaida iyayen nasu tareda baƙin dasuka gani a wurin dudda bazuce gakusuwayeba. Duk suka amsa amma Banda sarakunan domin basuji abinda sukaceba sedai sunyi murmushi domin sunyi tunanin gaisuwace yaran sukayi dubada yadda kowa a wurin ya amsa musu...kana Aisha tace abbey gamu. "To Aisha kuzauna magana zanyi daku amatsayina na mahaifinku ina Fatar bazaku watsamin ƙasa a idoba...kansu aƙasa suka amsa da in sha Allah abbey....daga hakan shikuwa ya kalli abba dake cika yana batsewa kafin ya girgiza kanshi yace "Umar dudda cewa kana taka iyakarka akaina amma ina maka uzuri sabida sanin halayyarka amma kasani awannan karon idan ka kawo min wargi acikin wannan al'amarin wlh ranka zeyi mummunan ɓaci, sabida da muhseen da fawan da duk sauran yaranda muka haifa ni ɗaya suke aguna bawani banbanci amma kai agunka ba hakan abin yakeba domin kana ganin kamar ina nunawa yaronka banbanci, humm. Ɗan murmushi yayi kana yaci gabada faɗar, shiyasa kukeda banbanci kaida Usman domin bantaɓa yin hukunci akan ƴaƴanshi yace wani abunba dukkan hukuncin dazan musu dedene shi awurinshi bawai yaraba koshi nayiwa hukunci baya musamin balle kuma yaran, domin kuwa idan baka mantaba wannan abin dayake tsakanin fawan da maisoon yafaru tsakanin zainab da jawal amma hakan nayi hukunci akansu naƙi amintada aurensu tunda narigada na karɓi kuɗin aurenta dudda kuwa suna son junansu, awannan lokacin miyasa shi Usman bece natsani ɗanshi bane na hanashi auren ƴata tunda ai zainab nina haifeta, amma har ila yau wannan zancen betaɓa haɗani da Usman ba, sabida hakan kaima yau nayi wannan hukuncin akan ɗanka fawan zangani idan na isa dakai dakuma abinda ka haifa.

Dan shiru yaƙarayi na ɗan lokaci kana yaci gabada faɗar, waƴannan bayin Allah dakake gani nasan dai kasan megirma shugaban ƙasarmu kuma kasan Alhaji Ahmed buba, waƴannan kuwa dakake gani bawai gama garin mutane bane kamar kowa wannan sarkin Saudia ne memartaba sarki Hassan kenan, wannan kuma saukin Dubai ne memartaba sarki Muhammad bilal kenan, wannan kuma ɗan sarkin Saudia ne Sunan shi junaid Hassan....ido abba yazaro cikin mugun mamaki da kunyar abinda ya aikata yasauko daga kan kujerar dayake kai yana cika yana batsewa tareda zubewa aƙasa, hakama fawan da duka sauran yaransu sun kaɗu sosai dajin mutanen dake gabansu, maisoon kuwa wani irin ɗagowa tayi cikin mugun faɗuwar gaba da fargaba, sedai babu wanda yakulada ɗagowarta da razanarta se mutun biyu wata Aisha da sarki Muhammad bilal dudda bawai yasanta bane amma yayi mamakin razanarta da jin sune agabanta....abbey kuwa bebawa abba damar yin wata maganaba yaci gabada faɗar, ajiyane sukazo gidannan neman auren maisoon wa yaronsu, nayi alhini sosai domin da farko ban amintaba kuma nabasu haƙuri akan zancen auren inda nagaya musu cewar nayiwa maisoon miji, mijinda nayimata kuwa bakowa bane face fawan domin tunda na soke aurenta da yaseer nasawa raina zan aurawa fawan ita,,,,,jin hakan danace yasa suka shiga bani haƙuri akan nabawa kowaye haƙuri dan Allah abawa yaronsu,,,,amma dudda hakan naƙi amincewa sabida abin yazo min abazata dudda bawai nafurta bane nacewar nabawa fawan ɗin,,,,ganin naƙi amincewane yasa memartaba sarki Muhammad bilal yashiga yimin magiya yana roƙana akan na amince nabawa yaronshi, tareda yimin bayanin halinda yaron yake ciki,,,,abin yabani tausayi sosai shiyasa doli na amince domin bazan iya kallon babban mutun kamar wannan yaduƙarda kanshi agabanaba yana roƙan abu agunaba wanda kuma inada yadda zanyi nabashi abin kuma na hanashi sam bazan iyaba. Ɗan shiru yaƙarayi yana kallon yanayin mutanen parlor kafin yaci gabada cewa, "shine dalilin dayasa na amince nabawa yaronshi maisoon bayan nayi musu bayanin komai gameda ita tundaga zancen auren yaseer har shigowar maganar fawan da ɓatan datayi harkawo bayyanarta da soke aurenda za'a ɗaura mata dakuma maidashi danayi akan fawan, kuma nagaya musu ne kar se anyi auren azomusu dazancen akaikaice kamar yadda akaƙulla yiwa Alhaji dikko,,,,bayan nagama faɗa musu sunyi jimamin abin sosai tareda tausayawa yarinyar ananne megirma shugaban ƙasa yace yanaso aɗaura auren yau kamar yadda akayi niyyar yi da yaseer tun farko, kana kuma Alhaji Ahmad yace yabawa fawan ƴarshi humaira domin shima a ɗaura mishi auren kamar yadda akayiwa yan uwanshi kar ayi bashi. gaskiya naji daɗin wannan karamci na Alhaji Ahmad domin damacan ina tunanin yarinyarda zan aura mishi kamar yadda nayi alƙawari tunda lokacinda nabashi yacika,,,,ananne akayi komai na shirin auren maisoon da yaron sarki bilal kana akayi na fawan da yarinyar Alhaji Ahmad kana suka tafi, amma har suka fito suna jimamin abinda Hajiya Rukayya dikko tayiwa maisoon shiyasa koda sukabar gidannan cikin alhini,,, yaƙarasa zancen yana kallon ƴaƴan nasu domin yaga yanayinsu.
Chapter 1 · 0% Book details