← Book details Sawun Giwa Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 5

Sashe 5

Sawun Giwa Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Suka fito harabar gidan...da sauri secrety ɗin suka fito suna buɗe motocin, megirma shugaban ƙasar ne yafara fitowa se menistern tsaro Alhaji Ahmed buba, sekuma manyan sarakunan wato memartaba sarki Muhammad bilal da memartaba sarki Hassan, daga ƙarshe junaid yafito tareda yaron sugaban ƙasar wato mujaheed, tareda Dr Hareesh se anty meenah da yaransu. Habawa zukuga murna gunsu abbay cikin farin ciki dasakin fuska suke tarbar manyan mutanenda duniya gabaki ɗaya ke alfahidasu yau gasu agidansu, sunrasa inda zasu ɗorasu kamar zasu maidasu ciki,,,ahakan sukayi musu jagora har general parlor, suka zauna aka sake sabuwar gaisuwa kana abbay da dady dakansu suka shiga gabatar musu da abin motsa baki wanda abbey yasaka mama da maisoon suka haɗa cikin hanzari...bayan sungama ne suka zauna suna ƙara yiwa manyan baƙin nasu sannu dazuwa dakuma gaisuwa ta girmamawa ga sara kunan dudda basajin larabci seyakasance komai da Turanci sukeyinshi tunda shine yarenda kowannensu keji.

Bayan duk angama gaisawa ne Alhaji Ahmed buba yafara gabatarwa su abbey da sarakunan suda basu saniba, kana yagaya musu buƙatar dasukazo da ita bayan yabasu labarin sheck sudais kamar yadda memartaba sarki Hassan yabasu labarin suma...tunda suka fara zancen abbey yayi shiru kawai yana saurarensu har suka gama, nandai suka tattauna wanda basu bani damar jin abinda suka tattana ɗin ba, sedai kawai naga sunfito su abbey na musu Rakiya amma fuskokinsu dukansu kamar ba walwala irinna ɗazun, hakan suka shiga motocinsu suka tafi bayan suyiwa abbey alƙawarin zuwa ɗaurin auren yaransu agobe kamar yadda suka sanar dasu.

Shima dady ciki yakoma suka ƙara tattaunawa da yayan nashi kafinnan yatafi shima.

Maisoon kuwa koda Anty meenah tashiga bedroom ɗin mama zaune tasameta tana risgar kuka kamar ranta zefita,,,domin Allah yagani taji baƙin cikin abinda Hajiya Rukayya dikko tayimata gaya asanaɗinshi Ana gayawa iyayenta magana har cikin gidansu,,,,sosai hankalin anty meenah yatashi ganin yadda ƙanwar tata ke kuka babu ƙakkautawa, abinda keda bala'in wahala ganin hawayen maisoon yau kan gasu a arha...cikin tashin hankali tajanyota jikinta tana bubbuga bayanta domin tasan muddin tana wannan kukan inzasu kwana tana tambayarta damuwarta ba tanka mata zatayiba, kusan minti 15 suna ahakan seda taji tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya ne kana tafara tambayarta abinda ke faruwa? Aiko tashiga bata labari tundaga farkon fara zancen auren itada yah fawan harkawo ga auren yaseer ɗin dakuma abubuwan da abba yarinƙa yimata a hospital ɗinshi, duk yau seda tagayawa yayar tata har inda akazo Hajiya Rukayya dikko tasaceta....damugun mamaki anty meenah ke saurarenta hartakai ƙarshe inda tace ita idanma anty meenah tatashi komawa saudia biyarta zatayi se hankalinta ya kwanta tukkunna tadawo,,,azahiri hakan tagayawa Anty meenah amma a baɗili bahaka abin yakeba da biyu zatayi tafiyar na farko ta haɗu da wannan ustaz ɗin acewarta nabiyu kuma tasamu damar yin maganin Hajiya Rukayya dikko domin inda aka fara anan ake ƙarewa. Tofa 🤔 komiye tsakanin maisoon da Hajiya Rukayya dikko dillah??🤔 To muje zuwadai idan ana zuwa ruwa ai ɓari akeyi🤷

Itadai anty meenah haƙuri kawai take bata amma aranta tana mugun mamakin wannan al'amarin daga gefe ɗaya kuma zuciyarta fal fargabar abinda yakawo su sarki Hassan gun iyayensu akan maisoon ɗin.

Abba kuwa yana isa gida yasamu fawan bayanan seda yakirashi awaya, Aisha ma batanan domin yana shigowa itakuwa tana fita zuwa gidan abbey gun maisoon....abba kuwa yakasa zama jira kawai yakeyi fawan yadawo yayi mai albishir, ai yana shigowa parlor dasauri abba ya rungumeshi yana faɗar "congratulasion my son burinka zecika na mallakar maisoon kosunƙi ko sunso kuwa...ai wani irin ihu fawan yasaka yana faɗar miyafarune abbana gayamin nidai asanina gobene aurenta miyafaru? Wata irin dariya abba yasaka kana yashiga bawa fawan labarin abinda yafaru agidan abbay na zuwan abban yaseer. Aitunkamin abba yakai ƙarshe fawan ya ɗauke shi sama yana juyi dashi cikin farin ciki da jin daɗi, tofa haka suka ɓata lokaci suna murna da farinci, kafin fawan yashiga kiran abokananshi yana faɗa musu gobene ɗaurin aurenshi sabida yasan abbey baze canja lokaciba, wannan kenan.

Gidan Alhaji dikko dillah
Abirkice yashigo gidan ko sallama babu tun abakin ƙofar parlor yake faɗar "Rukayya Rukayya Rukayya, hakan yake kiranta babu ƙakkautawa...atare suka fito itada Hajiya kakar yaseer agiɗime suna haɗa baki wurin faɗar lafiya? Wani mugun kallo ya watsa mata cikin tuhuma da takaicinta yace "mi ƴar mutane tamiki zaki saka asaceta? Kuma ma yoshe kika koma mesatar mutane bansaniba? Wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi cikin inna inna tace "wace ƴa kuma Alhaji? Mikake magana akai? Dasauri ya katse ta da faɗar "kinfini sanin abinda nake nufi Rukayya karki wani renawa kanki hankali, shine kikazo kikamin zancen banza da karfarku ta mata a she kece babbar munafuka kuma makira, to seki tanadi amsar bawa yayunta tundani bazaki gayaminba su zasu tuhumeki dakansu, sekuma babba albashir izuwa gareku sun suke auren ƴarsu da ɗanki seki zuba ruwa aƙasa kisha munafukar banza me fuska biyu,,yana gama faɗar hakan yawuce fuuuu kamar yakifa dan baƙin ciki,,dudda yanajin Hajiya na kiranshi amma ko waigowa beyiba, babu tunanin dayakeyi aranshi irin yazeyi da taron jama'ar daya gayyata gobe? Yazeyi da kunyar aminin nashi daya aminta dashi wato Alhaji Ishaq, wanda yahanama ayi binciken ɗanshi kawai suka bashi auren ƴarsu batareda wani fargaba,,,amma yanzu shi yakasa fahimtarsu ma balle yayi musu uzuri akan abinda matarshi ce ma silar komai, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un da wannan tunani yakwanta yana saƙawa da kwancewa......yaseer kam mutuwar tsaye yayi jin kalamanda abban shi ke faɗa, domin ze shigo kenan yaji wannan zantukan masu rusa ƙwaƙwalwa, ganin Alhaji dikko yawuce batareda yasamu taka mammiyar maganar kamawaba yasa yanufi Hajiya Rukayya yana faɗar "momsy mi abba ke faɗa hakan? Wakika sace? Auren waye aka fasa? Duk atare yake jera mata tambayoyin y
Yana Fatar Allah yasa kar abinda zuciyarshi ke gaya mishi yazama gaskiya, domin Allah yasani dudda rashin mutuncin dayayiwa yah muhseen becire rai daga auren maisoon ba tunda yasonta sedai kimarta dayake gani kaso 60 yafita acikin ɗari,...amma kuma yamakaro domin ko kallonshi batayiba tawuce bedroom ɗinta cikin mugun fargaba,,,hakan yamara mata baya amma kafin ya isa tarufe ƙofar ta da key....hakan yazube a bakin ƙofar yana nocking amma tayi banza dashi..Hajiya kuwa binsu kawai takeyi da kallon mamaki domin ita tama rasa abin faɗa..

Washe garin ɗaurin aure...afarfajiyar gidan Alhaji Ishaq maina, jama'ane tako ina ancika cinjim babu masoƙa tsinke domin har tawagar gidan shugaban ƙasa sun hallara a wannan ɗaurin auren ko ina kaduba jami'an sojojine se moba, abindai se wanda yagani,,, ancika babu masoƙa tsinke su yah muhseen, yah fawan, yah jafar, yah jawal dukkan yayunsu maza sunzuba shiga taban girma gwanin sha'awa, hakama su abba iyayen ango😅 ga abbey maɗauri auren gakuma dady baban amare💃💃 acikin parlorn abbey anan akayiwa duk wani babban mutun masauki ciki kuwa hadda manyan baƙi kuma manyan sara kunan duniya masudaraja, anyi addu'a daduk abinda yadace na ɗaurin aure inda dubbannin jama'a suka shaida ɗaurin auren MUHSEEN ISHAQ MAINA DA AISHA UMAR MAINA, AKAN SADAKI DUBU ƊARI BIYU,,,,,sekuma *SHEIKH SUDAIS MUHMD BILAL DA MAISOON USMAN MAINA AKAN SADAKI DUBU ƊARI BIYU* 😱 sena ukku, wanda aka Daura kuma naƙarshe FAWAN UMAR MAINA DA HUMAIRAH AHMAD BUBA SHIMA AKAN SADAKI DUBU ƊARI BIYU 😱, tab dijam chakwakiya kenan semuce Allah yabasu zama lafiya💃💃💃 wata irin muguwar zabura abba yayi jin wannan ɗaurin auren hakama fawan acan waje se riƙeshi abokananshi keyi amma yanason kuɓucewa yaje cikin parlor....acan ciki kuwa wani irin kallo abba keyiwa abbey kafin yabuɗe baki cikin tashin hankalin da rashin M yace...!

Autar alheri ✍️
Chapter 5 · 0% Book details